ɗan ja hannun baya kamar wanda yaji zafin.
Ai da sauri Maanal ta kallesa a raunane ta ce, “Da zafi ko, I'm sorry”. Yanda tayi kamar zatai kuka yasa shi ƙara girman idanun nasa a kanta yana kallonta ciki-ciki. Kansa ya girgiza mata ganin yanda ta zuba masa idanun dake tara ƙwalla. Kan nasa ya girgiza mata kaɗan, sai kuma ya juya nasa hannun nata ya koma sama, ya matso da shi tare da ɗan duƙowa ya sumbata. A hankali ta lumshe nata idanun tare da jan ajiyar zuciya.
Su dai ma'aikatan jirgi sun shagala suna kallon ikon rabbu, wannan al'amari kamar a film, dama a baƙaƙenmu akwai masu irin wannan shagaltacciyar ƙaunar, dan wannan ta wuce soyayya sai tsantsar ƙauna mai zafin gaske da sam bata ɓoyuwa a idanun masoyan. Da ƙyar ɗaya tai ƙarfin halin miƙama Manaal plaster ɗin data yanko tare da ƴar audiga. Maanal ɗin ta amsa ta sanya masa sannan tasa plaster ɗin a sama. Tattarwa sukai suka wuce suna waigensu..........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖2️⃣8️⃣
______________
.......Matuƙar saka rayuwar Huznah gaba Sageer yayi a wannan tsakanin da buƙatunsa. Tabi kowacce irin hanya na bijirewa amma ya nuna mata namiji yake. Sai dai taci kukanta da zaginsa a zuciya dan tsoronsa ALLAH ya dasa mata. Ko fita yay da zarar taji motsin dawowarsa zuciyarta ke fara dukan uku-uku. Gashi yanzu ya hana kowa shigowa gidan dan kullesu yake ta ciki, mutum ya ƙaraci bugunsa dole ya haƙura. Wayarta ya amshe ya kashe tun ranar da sukai waya da Hajiya Basariyya. Girki kam tunda tayi sau ɗaya ta ƙwaɓa musu hauka ya koma yi da kansa. A rana ta uku yasata shiga kitchen ɗin ya fara koya mata. Dan ya tabbatar mata yana da mata bazai dinga zuwa gidansu cin abinci ko saye ba. Idan zata zage ta zage babu abinda za'a fasa. Tako tabbatar da babu abinda za'a fasa ɗin kuwa. Dan tako ina baya raga mata yanzu. Hatta da gyaran gidan tsaye yake mata akai sai tayi komai yanda yake so.
Sau biyu tana satar wayarsa ta gwada kiran Hajiya Basariyya sai taji tata wayar a kashe itama. Ba ƙaramin tashi hankalinta yay ba da rashin jin uwar tata. Shiko sarai yana sane da ita, abinda bata sani ba yaji komai akan abinda ya faru da Hajiya Basariyyar a kwanakin nan Daddynsu na faɗa ma Babanshi saboda haƙurin daya bashi akan ya barsu su koma ɗakinsu suyi azumi. Shine yake sanar masa abinda Hajiya Basariyya ta aikata, da idonsa ya ganta shi da ƴaƴanta a wani ƙauye bin malamai, su kuma sunje cinikin gona ne a kusa da ƙauyen. Amma yay masa alƙawarin maida Hajiya Yaya idan tayi azumi koda goma ne a gidansu.
Sosai Huznah tai ramar dole a wannan gaɓar, ga shi kota kulle ƙofar ɗakin ma yanzu a banza ama wofi zai buɗe da wani key ɗin ne. Gida kuma in zai fita ta baya yake kulleta. Tun tana masa girman kai harta fara tunanin saukewa ta bashi haƙuri kozai taimaka ya bincika mata Umminta, dan tana son sanin wane hali take. Kamar kullum yau ƙarfe biyar ya dawo kasuwa. Tana falo zaune idonta a tv sai dai bata fahimtar komai kallon kawai take yi. Shigowarsa ta sata zabura tana masa sannu da zuwa. Sosai ya zuba mata ido dan mamaki. Amma sai baice komai ba ya gyaɗa mata kai kawai. Kitchen tai saurin nufa, a wani mamakin nasa bata jimaba sai gata ta fito da ruwa ta ajiye gabansa. Badan ruwan leda bane ALLAH sai ya tsargu wani abun mutuwar ta zuba masa. Amma yasan bazai yiwu ba tunda fure water ne....
“A kawo abinci?”.
Ta faɗa cikin katse masa tunani. Sai ya samu kansa da sakin murmushi. “Kina lafiya kuwa Huznah?”. Ya faɗa yana tsatstsareta da idanu.
Kanta ta jinjina masa alamar eh.
Iska ya ɗan furzar, sai kuma ya gyaɗa kansa da miƙewa yana faɗin, “Okay bara na watsa ruwa to, kibar abincin sai nayi sallar magrib tukkunna.”
Murya a ƙasa ta ce, “To”.
Nan ma sai da ya sake kallonta kafin ya wuce ciki abinsa yana kwasar dariya a zuciyarsa.....
Ni kaina dai abin ya bani dariyar Man Sageer 🤣😜
_________★
Gaba ɗaya Oum kewar yaranta take ji, dan ma babban Yaya da Fawzan sun ɗauke mata kewarsu. Nibras ma da farko ta shigo, amma jin hirar da su Fawzan keyi akan tafiyar su AA ɗin saita miƙe tsam kamar ma wadda jikinta ke rawa. Sallama tai musu cikin danne kukan dake neman zuwa mata tace zataje ta kwanta ta gaji. Da kallo kawai Oum ta bita. Hakama babban Yaya da tuni shima ya fahimci take-takenta. Amma a mamakinsu shi Fawzan ɗin da suka ji tausayinsa ya kama su shi hankalinsa ma nakan waya abinsa sai zabga murmushi yake dan charting yake da Najma.
Sai sukai tunanin ai bai fahimci matar tasa bane saboda sonta ya rufe idonsa. Sai dai abinda basu sani ba Fawzan ya riga kowa fara fahimtar matar tasa da inda haukanta ke ɗawainiya wajen kaita. Ya barta ne kawai bisa wasu dalilai dan yasan wane Autansu. Sannan yafi son kowa ta fahimta da kansa musamman Mamy data haɗa auren nasu. Dan yayi alƙawarin in sha ALLAHU da bakinsa dai bazai cema kowa a gidan ga halin da yake zaune da Nibras ba, har sai idan sune suka gani sukai magana....
Kuka sosai Nibras ta shiga yi a sashenta, ba komai ya kawo hakan ba sai jin matsanancin kishin AA akan Maanal. Yanzu ita har rashin muhimmancinta a gidan nan yakai AA ya shirya tafiya da wannan ƴar iskar yarinyar amma bata sani ba har sai bayan tafiyarsu. AA ɗinta, sanyin idaniyarta. Aiko har abada bazata yafe ma Maanal ɗin wannan tafiyar ba, sai ta mata hukunci dai-dai da hakan....
A ɓangaren Mamy ma dai ranta a jagule yake ita da muƙarrabanta su Nuratu. Dan Nuratu ma tun bayan tafiyar su Maanal data shige bedroom bata sake fitowa ba. Ita kanta Mamy sai da Abah ya fahimci bata cikin walwalarta. Koda ya tambayeta sai ta nuna masa kawai yanayi ne sannan kamar kanta zai mata ciwo take ji tasan kuma zafin gari ne dake sirkawa.
Sannu yay mata tare da bata magani yace tasha ta kwanta yau yama yafe mata zuwa sashen nasa kawai. Aiko wannan freedom ɗin data samu kusan raba dare sukai suna waya da yayarta da maman su Saheeba. Sun tsara yanda zasu tarwatsa Oum da Maanal sosai a gidan. Daga ƙarshe suka birkice zuciyar Mamy musamman akan AA. Tare da tunzurata akan batun ƙara auren Fawzan wai dan a tantance waye baya haihuwa shi da matar tasa tunda idan sunje asibiti sai ace musu duk ƙalau suke lokacine kawai baiyi ba. Su dai sam basu aminta da hakan ba dole akwai lauje cikin naɗi.
Tsaf kuwa zuciyar Mamy duk ta hau akan shawarwarin nasu. Duk da ita dai Aunty Babba har cikin ranta tana yaƙine da kishin ƴar uwarta wato Mamy, yayinda Maman Saheeba ke komai da zuciya biyu, dan itafa fatanta ƴaƴanta su kasance a gidan su mamaye komai na dukiyar su Babban Yaya ta hanyar baza ƴaƴa. Kunga ko komai ai ya dawo tafin hannunsu. Dan ita kanta Saheebar ido a rufe maganin haihuwa ake neman mata tunda tun daga cikin Anum shiru kake ji bata sake ko ɓatan wata ba ga Anum na neman cika 5years.
Ita ko Mamy ɗauka take duk sonta suke yi musamman ma Maman Saheeba, dan wasu lokutan ita Aunty Babba kan ɗan faɗa mata gaskiya shiyyasa tasu bata tsaho a tare.....
_________★
Bayan sallar magriba da isha'i da su Maanal suka gabatar ita da AA da har yanzu bai sake ba wajen zamansu suka koma. Ganin ya buɗe laptop itama sai ta ciro novel a bag ɗinta kawai ta hau karatu. Koda aka kawo musu abinci daga ita har shi babu wanda yabi takai duk da shine da kansa ya bada umarnin a kawo ɗin. Ɗan ɗagowa yay ya kalla Maanal jin kamar ta daina motse-motse, aiko dai gyangyaɗi take. Shi sai ma taso bashi dariya, yo tun ba'aje ko ina da tafiya ba, Chaina fa suka nufa tafiya mai nisan awanni.
Wani ɗan bottom ya danna a gefen kujerar a take ta wani kalar buɗewa ta zama gado, abinda ya raba tsakkiyarsu mai kama da hannun kujera ya naɗe kansa wajen shima ya zama flat. Laptop ɗin ya matsar gefe ya kwantota a jikinsa tare da zare novel ɗin hannun nata ya ajiye. Fuskarta data fito so cute a zagayen rolling ɗin veil ɗinta ya zubama ido, sai kuma ya janye cikin lumshewa ya kuma buɗe a lokaci guda. Veil ɗin ya shiga warware mata a hankali bayan ta cire pin ɗin data riƙe da shi. Yana ko gamawa ta gyara kwanciya tana sauke ajiyar zuciya. Shima sai ya samu kansa da sauke ajiyar zuciyar acan ƙasan maƙoshi. Ɗan takurewar da tai waje guda ya sashi ɗaukar lallausan farin mayafin dake gefensu kaɗan ya lulluɓa mata har a kafaɗa, sai kuma ya zare ribbons ɗin data kama kanta da su a tsakkiya gashinta ya tarwatse masa a hannu, kamawa yay ya tattaresa cikin hannun nasa ya shiga tufkewa a hankali ta yanda bai tsamke tushen ba balle taji zafi. Veil ɗin ya ɗauka ya ɗaura mata a kan kamar ɗan kwali cike da dabara, daga haka ya ɗan ranƙwafa ya sumbaci kan nata sannan ya ɗauka laptop ɗinsa ya cigaba da aiki duk da kuwa wani ɓangare na jikinta yana a jikinsa ne...
Sosai ya raba hankalinsa biyu a kallon fiskarta da aikin, dan yanda ta ɗam tsuke baki zaka fahimci kamar tayi barcin ne da faɗa a zuciyarta. Yasan halin mutuniyar tasa ba rabo take da masifa ba har a cikin barci tanayi faɗa. Kawai dai kura ce tai lafiyar dole. Eh lafiyar dole mana tunda dai risinar ta dole ce ai....
★Barci sosai Maanal tasha, dan bata tashi farkawa ba sai kusan 9:30, zuwa sannan awa ɗaya da rabi ce ta rage musu su sauka cikin ƙasar Qatar domin yin canjin jirgi. A hankali ta shiga motsawa, sai kuma tai juyin daya bata damar komawa tana fuskantar lafefen cikin AA, rashin nauyin rigarsa da yanda ta kwanta masa a jiki har yana jin saukar nunfashinta a kan fatar cikin nasa. Sosai tsigar jikinsa ta fara tashi. Cikin wani irin motsawar zuciya ya lumshe idanunsa a slowly sakamakon sake motsawa da tai ta kife ƙirjinta da ƙyau a cikin nasa tare da zagayo hannayenta ta bayansa. Daga ganin yanda tai ɗin ka tabbatar ta ɗauka filo ne ta rungume. Cigaba da saukar numfashin nata mai ɗumi a jikinsa ya sashi jin ina bafa zai iya ba. Da ƙyar ya iya jawo busashen yawun da ke neman suɓucemasa a baki ya haɗiye, maƙoshinsa yay wani irin yin sama da ƙasa a lokaci guda cikin wuyansa. Idanun da yake faman rumtsewa ya buɗe, sai kuma a hankali ya ture laptop ɗinsa gefe can ƙuryar maƙoshi ya shiga kiran sunanta cikin taushi da sauƙin sauti dake fita cike da kasala da ƙyar..........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 15