Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ BOOK 2 🅿️➖1️⃣ ______________ *_Assalamualaikum. Barkanku da wannan lokaci, fatan ansha ruwa lafiya? Anyi salla lafiya?. UBANGIJI ya karɓi ibadunmu, ya yafe mana kurakuranmu, yasa muna a cikin ƴantattun bayi. Ina mana Barka da dawowa filin daga, ya rabbi ka bani ikon rubuta abinda bazai cutar dani da ku ba. Ka tsarkake min alƙalamina domin rahamarka. Ka gafarta ma iyayenmu da malamamu damu baki ɗaya. Ka ɗauramu a bisa tafarki madaidaici da bazamuyi dana sani ba. ALLAH ka hanamu cutar da junanmu koda da kalma mara daɗi ce.🙏_* _Ayi mana afuwa da jinkirinmu yau da gobe sai ALLAH 🥰🥰❤️._ *Ƴan ƙungiyar Bati ku matso nan munada meeting 😂. Kun san dai AZUMI aka gama ko, goman ƙarshen nan hummmm 😂 karki yarda ki zama a cikin wanda na ɗaga hannu nace ya ALLAH gasu nan....* _Bazan dai ƙarasa ba amma gaskiya kada ki yarda sister dan in dai an amsa akwai cakwakiya gaskiya 😂😂😂😂🏃_ 500 kacal ne 😘 _____________ ........Sosai ciwon kai yay ma Maanal rijib a wannan yinin isowarsu Abuja, shima kuma AA ɗin zuwa yamma dole aka saka masa drip ma, dan sam baya jin wani ƙarfin jikinsa. Har cikin dare ba'a gama saka masa ruwan ba dan kusan leda uku ne. Dole Fawzan ya kwana tare da shi bisa umarnin Abah. Oum taso yin magana amma tai shiru, dan ita so tai ta kawo Maanal a daren sashen AA ɗin, amma ta fahimci take-taken Abah so yake ya kawo wani sharaɗin hora AA ɗin, dan dama shine ya bata umarnin wucewa da Maanal sashenta sanda suka iso.       Bayan sun baro sashen AA bin bayan Abah tai nasa sashen ta masa magana, amma sai ya nuna mata shi barci yake ji ta barsa dan ALLAH. Haushi ne sosai ya kamata, dan haka fuuu ta baro sashen. Da kallo ya bita ganin yanda ta wuce, sai kuma ya shiga girgiza kansa a fili ya furta, “Fateema son yaranki yayi miki yawa, in dai fushi ne ƙyama sakko dan sai na hora Ajwaad a gidan nan”. Daga haka ya shige toilet yana murmushi... ___________★      Zuciyar Babban Yaya cike da wasi-wasi ya nufi sashen Oum ganin har goma saura na dare yau ma Maanal bata koma sashenta ba, ga AA ɗin kuma ma jikin nasa ya dawo dan yanzu haka wani ƙarin ruwa aka cire masa. Ganin bata a falo ya nufi bedroom ɗinta. Sai da yay sallama ta amsa tare da bashi izinin shiga sannan ya shigan. Yanayin yanda take a zaune da fiskarta dake cike da damuwa yasa gabansa faɗuwa, duk da yasan akwai damuwar yanayin da Auta ke ciki dai.        “Oum baƙya jin daɗi ne?”.    Ya faɗa cike da damuwa matuƙa yana kaiwa kusa da ita zaune. Idanu ta zuba masa kawai, dan duk yanda taso yin murmushi ko sassauta damuwar tata hakan ya gagara sam. Sai ma ƙwalla kaɗan da suka taru mata a idon. Ai sai babban Yaya ya sake rikicewa matuƙa.    Hannunsa ta riƙo tana girgiza masa kai, “Kaga kwantar da hankalinka bafa wani abu bane ba.”         “Haba Oum yazan yarda da hakan, kalla fa yanda damuwa ta bayyana a fuskarki sosai. Dan ALLAH in ma dan ciwon Auta ne ki daina tada hankalinki komai zai wuce kamar ba'ayi ba in sha ALLAHU. Dan yanzu hakama barci yake yi na cire masa drip ɗin dan ya ƙare. Jikinsa sam kuma babu zafi da ganin yanda yake barci ma kasan Alhamdullah babu wani damuwa ba kamar jiya da yinin yau ba. Yanzu haka ma nazo ne akan batun Maanal, nazata zata kwana a can ne yau ai tunda jikin da sauƙin itama?”.           Sosai ɓacin ran Oum ya ƙara bayyana akan fuskarta, ta ce, “Akan hakanne ai Abanku ya ɓata min rai Fadeel, yace wai bazata koma can ba yanzu sai bayan salla ya koyama Ajwaad hankali. Wane hankali kuma ake buƙatar koyama yaron nan bayan wanda ya koya. Kama ajiye batun wahalar ciwo da yasha a shekarun baya, a kwanakin nan kawai kaga hanlin daya shiga fa da wanda yake a ciki yanzu. Kowa fa a rayuwa da irin yanayinsa da kuma ƙaddararsa, amma Abanku ya kasa fahimtar hakan, ya kasa fahimtar Ajwaad nada zurfin ciki ne. Yanda Maanal keda muhimmanci a garesa bana tunanin dole sai ya buɗe baki yace wani abu za'a yarda dashi. Shin so yake na rasa yarona ne saboda wannan tsaurin nasa?”. Ta ƙare maganar muryarta na rawa kamar zata saki kuka.       Cikin sake rikicewa sosai Babban Yaya ya shiga girgiza mata kai nasa idanun na kaɗawa sosai shima. “Dan ALLAH Oum ki kwantar da hankalinki, ni bara naje na samesa yanzu. Ko kuma ki kira Baba ko Abba ki haɗashi da su.....”           “Saboda ban isa da gidana ba kenan ko mai uwa?”. Atare babban Yaya da Oum suka juya da sauri suna kallonsa, ƙarasa shigowa cikin ɗakin Abah yayi, cikin nuna ɓacin rai sosai ya cigaba da faɗin, “Saboda biyan buƙatar taka uwar ni a kira nawa iyayen a haɗani da su. Lallai Fadeel sannu, nace sannu kaji ko!”.        “Kayi haƙuri Abah ni ba haka nake nufi ba, amma Oum fa......”     “Malam tashi ka wuce sai da safe.” Abah ya sake katseshi cikin sake nuna ɓacin rai. Kallon Oum Babban yaya yayi idanunsa na sake kaɗewa, kanta ta jinjina masa alamar yaje ɗin. Dan haka ya miƙe kawai ya nufi ƙofa. Da kallo Abah ya bisa, sai kuma ya girgiza kai a zuciyarsa yana ayyana (su dai akan uwarsu kowa ma ya mutu har liman babu ruwansu). A fili kam dubansa ya maida kan Oum data ɗauke kanta gefe tamkar ma bata san da shi ba a ɗakin. Sai kuma ta yunƙura zata miƙe. Yasan mi zatayi, dan haka cike da bada umarni ya ce, “Koma ki zauna”.        Komawar tayi ta zauna, kafin ta ɗago idanunta da suka sake kaɗewa a karo na farko ta kallesa, aiko ya sake yin kicin-kicin da fuska harda ɗan willa mata hararar data sakata janye idanun nata a kansa sannan ya furta, “Oh ke yanzu saboda na yanke hukuncin daya dace akan ɗanki shine kika ɗauki fushi da ni kin kira babban ɗanki kina sanar masa kuyi min taron dangi saboda ban isa nace ga yanda za'ai ba”.       Idanu Oum ta ɗan rumtse kaɗan, sai kuma ta buɗe a kansa. Baki ta buɗe kamar zatai magana sai kuma ta fasa saboda ƙwallar da suka cika mata idanu. Ɗauke nasa yay dan yasan yanzu sai ta karya masa zuciya, shi kuma a wannan karon ya ɗauka aniyar tauna tsakuwa dan aya taji tsoro, dolene ya hukunta Ajwaad kodan ya sake sanin muhimmancin Maanal. Bazai yiwu ya samu aurenta a ɓagas ba su kuma bashi ita a ɓagas. Ƙoƙarin barin ɗakin yayi, sai Oum kawai ta saki hawayen da take riƙewa cikin muryar kuka ta ce, “So kuke sai kun kashe min shi hankalinku zai kwanta ko Gadanga, yanzu horon da ƙaninka yay masa kawai bai wadatar a yafe masa ba”.          Murmushi Abah daya tsaya cak tun fara maganarta ya saki a hankali, sai kuma ya maida fuskarsa ya haɗe kafin ya juyo yana kallonta daga inda yake tsayen. “Rafeeq bai hora ɗanki ba, takarar nema sukai yay muku adalci ya sadaukar saboda ƙyaƙyƙyawar zuciyarsa, da kuma nasan zai yi hakan sai na hana masa”.  Ya ƙare maganar yana mai juyawa ya fice abinsa. Wani irin ƙululun abu ne ya sake tokare wuyan Oum, har zuciyarta na tunzurata akan takai Maanal sashen Ajwaad koma miza'ayi ayin mana....... ___________★          Alamun shigowarsa ya sata dakatawa daga kai-kawon da takeyi, zama tai kamar ba ita ba ta nutsu a bakin gadonsa tare da ɗaukar littafin addu'oin sa dake a bed side drawer ta fara karantawa. Da farko Abah daya shigo ransa a ɓace sam bai ganta ba. Sai da ta ɗago ta kallesa cikin tausasa harshe matuƙa ta furta, “Sannu da shigowa”. Sannan ya kalleta. Ciki-ciki ya amsa mata, dan haka ta taso da ƴar sassarfa tana faɗin, “Lafiya kuwa? Naga kamar ranka a ɓace?”. Tsaki yaja mai ƙarfi, sai kuma ya wullar da wayarsa a saman gadon nasa shima yana kaiwa zaune hannunsa akan goshinsa yana murzawa. “Fateema ce ke neman ɓatan rai Kamila”.       Ɓoyayyan murmushi Mamy ta saki, a zahiri kam cike da damuwa ta ce, “A haba kodai baka fahimta bane, amma nasan bazata ɓata maka rai da son ranta ba yallanɓai.”          “Mtsoww!! Bazaki gane ba Kamila, ita dai sam bata gajiya da rikici akan ƴaƴanta, dokar dana kafa jiya akan komawar Maanal sashen Ajwaad shine taketa faman fushi, yanzu naje mata sai da safe na samu ta tasa babban ɗanta gaba tana faɗa masa, shiko yana bada shawarar a haɗani da iyayena.”      Sosai Mamy takai zaune yanzu kam, hannunsa ta kamo cikin nata cike da kulawa. “Kayi haƙuri, zan sameta muyi nagana ta yanda zata fahimta. Dan tabbas Ajwaad ya cancanci a fara horashi kafin a bashi yarinyar nan kodan halaccin iyayenta da basu duba abinda ya faru a baya ba suka sake bashi batare da ko tada magana ba. Taurin kan yaron nan ne yayi yawa, ya kamata ya fahimci ba komai akema taurin kai ba a rayuwa....”        “Abinda nake son ta fahimta kenan ai nima Kamila. Amma tamaƙi ta nutsu ta saurareni, ni kuma so nake mu rabashi da halin kodan bambancin dake a tsakanin jiyansa da yau ɗinsa”.        “Karka damu zata fahimta in sha ALLAHU. Ka bata lokaci ta huce yanzu sai mu haɗu muyi magana. Idan ma ta kama Maanal ɗin ta dawo sashena da zama to, dan in ba hakaba bazai damu ba”      Ɗan jim Abah yayi, sai kuma ya jinjina kansa cike da gamsuwa ya ce, “Kumafa kinzo da shawara Kamila, dan in har Maanal na a sashen Fateema ba'a rabu da bukar bane an haifi habu za'ai. Dan ɗan nata dai can zai koma ya tare abinsa, kinga kuwa bazai damu ba.”         “Tabbas hakan ce zata kasance”. Cewar Mamy wani farin ciki na ratsa mata zuciya na nasara. Abah kuwa da bai san dawan garin ba ya sake furta, “To ai zanyi maganin abun, bari dai ya samu lafiya”. “ALLAH ya bada iko, ina goyon bayanka kuma ɗari bisa ɗari a wannan gaɓar. Dan in aka biye ta Mamansu haka za'a mika masa ita kaga ya samu damar cigaba da mana abinda yaso tunda ta shagwaɓa shi daga ita har ƴan uwan nasa. Sun nuna masa komai ya nema sai ya samu komai girman sa”. Sosai kalaman Mamy ke shigar Abah, yana kuma jin gamsuwa da su da tasirinsu ƙwarai da gaske a zuciyarsa fiye da yanda take ma fatan ya fahimta ɗin.........✍️ *(Mamy😏. Mamy☹️. Mamy😮‍💨. Matar nan ko🤔. Hummmm😥.)* _Amin afuwa dan wlhy mura nake mai zafi, idan na samu sauƙi za'afi ganin page ɗin da tsaho..._ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖2️⃣ ______________ ........A safiyar washe gari har kusan sha biyu Abah baiga idon Oum ba a gidan. Dan haka ya fahimci fushin nata fa na gaske ne. Shi dariya ma ta bashi, dan haka shima ya shareta. Har yamma dai bai ganta ɗin ba, ya dai daure har akai sallar magrib da isha'i sannan ya nufi sashenta. Ko'ina tsaff yake da ƙamshi, sai masu aikinta daya samu a falon ƙasa suna hira. Suka gaisheshi da girmamawa ya amsa musu da kulawa ya wuce.        Oum na zaune a doguwar kujera Maanal kwance ta ɗora kanta a cinyarta su duka idanunsu a tv. Sallamar Abahn ta saka Maanal ta shi zaune, kanta a ƙasa tai masa sannu da gaida shi. Shima fuska ɗauke da murmushi ya amsa mata tare da tambayarta ciwon kanta. A tausashe ta ce, “Ya daina Abah Alhamdullah”.      “Masha ALLAH ai haka ake so ɗiyar Abanta ƴar albarka.”     Murmushi Maanal tayi mai faɗi, sai kuma ta miƙe tsam, dining area ta nufa ta ɗakko ruwa a freight tazo ta ajiye gabansa, cike da dabara ta shige bedroom ɗin Oum. Shi ko Abah cike da mamaki sosai ya ke kallon Oum ganin tunda ya shigo falon bata ko ɗaga ido ta kallesa ba. Sai ma wani sake ciccin magani take. Ji yay kamar ya juya ya fita ya bar mata sashen. Har yay kamar zai juyan sai kuma ya dakata, ruwan da Maanal ta ajiye masa ya ɗauka ya sha kafin ya dubeta da ƙyau. A ɗan kausashe yace, “Har yanzu fushin ne kenan? Dan na hana ki bama ɗanki matarsa shine nima kika ɓiye min ganinki yini guda Fateema? Ni kenan ban isa sharɗanta doka a fahimceni ba ashe dai?. Miyasa kike da son kanki da yawa akan ƴaƴanki ne wai?”.       Karo na farko ta ɗago ta kallesa, idannunta cike da hawaye. Muryata na ɗan rawa ta ce, “Miye abun son kai anan Abahn su?. Yaron nan kodan halin daya shiga ai ya cancanci a yafe masa a kuma fahimcesa. Eh naji shi mai kuskure ne, amma koda bai fito yace yana son Maanal ba halin daya shiga kawai amsa ce. Amma sai ace baza'a bashi matarsa ba har sai bayan salla. Haba Gadanga ka fahimta mana, baifa da lafiya, yana buƙatar mai kulawa da shi.....” hawaye suka shiga ziraro mata batare data kai ƙarshen zancen ba. Shi Abah sai abun ma ya fara bashi dariya. Yanzu dan kawai yace Maanal bazata tare ba sai bayan salla shine abin kuskure har ta zauna tana kuka. Oh ya rabba, Fateemansa sarkin daru kenan. Kansa kawai ya girgiza, batare da yace komai ba ya juya zai bar mata ɗakin, dan dole ya turza sosai ta yanda ita da ɗan nata zasu san ba wasa yake akan al'amarin ba. Da sauri ta ce, “Gadanga!”. Tsayawa yay, tare da ɗan waiwayowa ya kalleta. Sai kawai ta sake sakar masa kuka. Da sauri ya fice abinsa, dan in tana irin wannan darun nata yafi buƙatar yin nesa da ita, idan ba haka ba sai ta karya masa zuciya ta sakashi yin abinda bai niyyar ba.        Kai tsaye daga sashen Oum ɗin sashen AA ya nufa, dan son sake duba jikinsa, saboda yau ma a kwance ya yini ko salla bai fita ba sakamakon rashin ƙwarin jiki da yake fama da shi har yanzu. A sashen ya samu babban Yaya da Fawzan a tare da shi, sai dai shi barci ma yake AA ɗin, su kuma suna ƴar hirarsu. Cike da girmamawa suka gaisheshi, ya amsa musu da kulawa yana taɓa goshin AA dake barci. Jikinsa babu zafi kamar jiya, dan da ganin ma yanda yake barcin zaka san Alhmdllh. A hankali ya sauke ajiyar zuciya, sai kuma ya ɗago idonsa akan su Babban Yaya ya ce, “Alhamdullah yanzu kam babu zazzaɓin ai. Ya kamata kuje ku kwanta ku huta kuma ni bara na zauna da shi yau”.            Idanu Fawzan ya ɗan waro waje da faɗin, “Haba Abah da kanka. Ai sai Oum ta zane mu.”     Dariya Abah yayi, hakama babban Yaya ya murmusa tare da faɗin, “A'a Abah mun yafe maka kaje abinka. Dan gaskiyar Fawzan Oum zata iya zane mu ne”.     Nan ma murmushi kawai Abah yayi, sai kuma ya zauna suka ɗan tattauna akan jikin AA ɗin da tun shekaran jiya da suka iso daga Kano sai a hankali, dan duk dauriyarsa sai da ya sake kaiwa kwance. Gashi ya kuma kafe bazai je asibiti ba, sai nan doctor yazo yake duba shi. Bayan Abah ya musu sallama ya fito babban Yaya ya biyosa da sauri. Dakatawa yayi yana kallonsa harya ƙaraso.       “Lafiya dai ko Fadeel?”.    Cike da ladabi babban Yaya ya ce, “Eh Abah, kawai dai akan batun tarewar Maanal ɗin ne dai, dan ALLAH kayi haƙuri a bashi matarsa, ALLAH bana jin daɗin yanda nake ganin Oum a cikin damuwa. Abubuwan sun mata yawa, ga ciwon Ajwaad ɗin ga kuma wannan batun. Abah harfa rama naga tamun yau ALLAH ”. Babban yaya ya ƙare maganar kamar zai yi kuka.       Murmushi Abah yayi, sai kuma ya ɗan furzar da iska tare da faɗin, “Wato Fadeel ya kamata muma kammu adalci muyima yarinyar da iyayenta suma. Dan tabbas da nasan Rafeeq zai zagaye yay wannan aikin sai na hanashi, saboda nifa har yanzu ina akan bakana sai Ajwaad ya sauke kansa ƙasa yazo da bakinsa ya nema na bashi Maanal bayan ya nema afuwarta, idan ma ta kama ya faɗa mana dalilinsa na wannan dagewar”.      Kai sosai Babban Yaya ya jinjina, ya ce, “Na fahimceka Abah, kuma nima ina bayanka. Sai dai hakan bazai hana na baka haƙuri ba na kuma nemawa Auta afuwa. Kasanshi da zurfin ciki, maybe akwai abinda bamu sani ba game da al'amarin, amma wlhy mu shaida ne Ajwaad na son Maanal matuƙa. Kuma sai nake ga mata da miji sai ALLAH, kamar barinsu su kasance a taren zai sa su sasanta kansu kodan soyayyar da suke ma juna su duka”         “Humm wace soyayya kuma Fadeel, yana sonta zai watsar da al'amarinta ya zauna jan jiki a sanda ya sake ganinta, to Miye na girman kan, aure abin wasa ne? Barshi dai a bata tare ɗin ba, zai fi jin zafin wannan bulalar fiye da wadda kake hangen. Ina son hakan ya zama izina a garesa ya canja wannan halin nashi kodan yanzu shi mai iyali ne nanda wani lokaci haihuwa za'a fara masa”.     “Tabbas aure ba abin wasa bane Abah, mu kuma masu biyayya ne ga kowanne irin hukunci daga gareku. Amma idan mukai dubi da halin kawai daya shiga akan tsoron rasata abun muyi nazari ne. Ta wani ɓangaren ina tsoron kar dangin mahaifinta ne fa sukai masa wani abun tun wancan lokaci tunda dama kakarsu ta nuna bata son aurenmu da su Shaheedeh. Abah kasan zata iya bin kowacce hanya domin cin nasara, sannan shi kansa asiri gaskiya ne fa”.      Sosai Abah ke kallon babban Yaya. Zuciyarsa nata faman kai-kawo akan kalamansa. Sai dai kuma baice komai ba akan hakan illa nufar hanyar fita da faɗin, “Zanyi nazari, amma ina akan bakana na bazata tare ba yanzu ku cigaba da jiyyarsa ALLAH ya tashi kafaɗunsa”. Daga haka ya fice abinsa. Da kallo kawai Babban Yaya ya bishi, shi kansa al'amarin Autan nasu na damunsa, da rikita shi, amma dai koma miye ai ta ƙare tunda an ɗaura, komai mizai biyo baya mai sauƙi ne insha ALLAHU......         Murmushi mai faɗi da yalwa Mamy ta saki, dan dukan tattaunawar Abah da su Babban Yaya a cikin kunnenta ta kasance. Tayi matuƙar yin farin cikin yanda shirinta yay tasiri akan Abah cikin sauƙi haka, dan sam batayi zaton zai amshi batun da muhimmanci ba duba da sanda take tsara masa yin hakan yi yay kamar maganar tata bata tasirantu a gareshi ba. Shiyyasa taga ƴar gwal ɗin tashi har yanzu babu fara'a ashe an sake wargaza mata shiri ne. Wani murmushin ta sake saki haƙoranta na bayyana sosai, sai kuma ta gimtse fuska da gyara yanayinta ta ƙarasa shigowa falon sosai tana sallama.         A tare Fawzan da Babban Yaya suka ɗago suna kallonta tare da amsa sallamar. Cikin yanayin da take nuna musu na kawaici ta amsa gaisuwar da suke mata, tare da tambayarsu yaya mai jikin. Suma cikin girmamawar da suke bata suka tabbatar mata da sauƙi, yanama yin barci ne. Kai kawai ta jinjina musu, batare data sake cewa komai ba ta nufi bedroom ɗin AA ɗin. Barcin kuwa yake har yanzu, fuskarsa tayi fayau. Guntun murmushi ta saki a hankali, dan tasan tabbas ƙaunar da takemasa dabance a cikinsu, tun daga ɗaukar cikinsa har haihuwarsa duk da wahalar data sha shi ɗin na musamman ne a gare ta. A karo na biyu ta sake sakin murmushin, sai kuma ta kai zaune kusa da shi gab tare da kai hannun ta shafa yalwatacciyar sumar kansa dake a hargitse. Addu'ar samun lafiya tai masa mai ɗorewa tsahon mintuna kafin ta tashi ta fita....         A hankali AA da tun tsaiwar Mamyn a kansa ya farka ya buɗe idanunsa ya bita da kallo, sai da ta maida ƙofar ta rufe ya sake maidasu ya lumshe luuuu. Ya jima kafin ya sake buɗesu, sai dai sun masa nauyi sosai alamar barci bai gama sakinsa ba. So yake ya tashi zaune, sai dai kansa juya masa yake yi, dan haka dole ya sake maida idanun ya rufe barcin ya ƙara yin awan gaba da shi cike da mafarkin Mamy da haka kawai ganinta a kansa tsaye ya tsaya masa a rai duk da yasan ba wani abu mara ƙyau tazo tayi a garesa

Chapter 1 of 15