Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ne Abu tace ni abin wankin nasu Amai yake niyar sani Nikuma bacci nake ji Zomuje muyi bacci indan muntashi sai muyi KWALLIYA To muje su Abu suka kwanta bacci Kaya kuma na jike harsu Aqeel suka dawo suna bacci koda suka tashi kayan KWALLIYA Abu ta dauko musu sukayi Wannan karan KWALLIYAR tafi muni dan a fukar nan babu inda suka bari ko ina sunsa Jan baki da kwalli da Eye shadow saida suka gama sannan Suka je gurin kayan da suka bari a cikin ruwa Abu ta shiga mamakin ganin ruwan ya canza kala daga Fari ya koma Blue tasa hannu ta dauko rigar Tace hege iro lokacin da nakai mihi kayana ya Rina min yace hibaze rinaba saina bahi kudi waya mutu waya tahi yanzu Gahi munkoyi rini cikin sauki jan kaya ya koma haka shagali Binta tace kece kika wani damu da wani iro bantaba kaimai riniba yanzudai mu matse kayan Abu tace to suka matse kayan binta ta Bude rigar taga tana kallon Abu ta cikin rigar Abu na kallon ta Kayan ya huhuje ya canja kala I hu Binta tasa ta saki rigar a kasa sosai ta gigice ganin yanda rigar ta koma ita kanta bata san dalilin rude warta ba Abu tarike ta tace Binta ki dawo cikin hanka linki mana meye abin damuwa Anan sukai aimusu faci sukansu zasu so kayan Allah Abu ni harna shiga damuwa bawani Abu nake tsoroba illa nunar rana tinda muka zo gidan nan yake jin haushin mu Rabu dahi Wannan na mihi uziri kanshi baya aiki zo muje gasu can suna hira Abu ta rike hannun Binta da bokitin da kyan a ciki suka wuce falo Suna shiga Abu tayi ido4 da Aqeel ta fashe da kuka Binta na ganin haka itama tasa kuka Hajiya tace lpy kuke kuka wannan bokitin na meye Amal tace tinda kika ga suna kuka wata tsiyar suka shuka Nina sani Nidai nace bada yawuna ba amma ka dauka ka basu duk abinda yasamu Kaya na bazan hakura ba wlh zaku gane kuran Ku Abu da Binta najin haka suka kara sautin kukan da suke yi Aqeel ya daka musu tsawa yace kuyi wa mutane shiru me kuka yiwa kayan Suka kara fashewa da kuka Hajiya tace Aqeel ka musu a hankali Abu meya faru Ku saki jiki kuyi magana ina nan ba abinda ze faru duk kun daga min hankali Abu tace hakane kuma mune dai aka bamu wanki muka yi kuma ta fashe da kuka Binta tace yi shiru Abu abin hine masu rini a za ma ninnan sunyi karanci mu samman a birni mun yi muku wanki kamar yanda kuka ce harda rini muka muku Aqeel cikin kaguwa Yaji abinda ya samu kayan yace Ke Me KWALLIYAR Aljanu kifada mana abinda kuka yiwa kayan mana idan kuka bari na sake magana hmm kunsan sauran Abu da Binta suka goge hawa yan fuskar su suka sunkuya kowa ya dauko riga1 Abu ta saita Aqeel ta Bude rigar tana kallon Aqeel yana kallon ta tawani wawa keken yaga ta tsakiyar rigar Binta ma Arif ta saita da rigar yana kallon ta tana kallon shi Aqeel a zuciye ya mike ya nufu Binta da gudu ta koma bayan Amal Hajiya tace Aqeel zoka zauna barni dasu tukun na Abu garin ya haka ya faru Binta tace in banda nunar rana da abinhi meye a ciki dan kayan ya yage Gashi kamar an kwato daga bakin kura nidai bana cin Kaya balle ace nice ni da naga rigar nan harya tunomin da wani ma haukaci a *DARAUDAU* hima haka kayansa suke muyi ta tsokanar hi Abu tace Allah sarki koyayi aure ma ban saniba kaga yanzu kudauki kayan kukai a muku faci idan akayi muku faci hmm ba a cewa komai dan kyanda kayan nan zasuyi sai yan garin nan sun koka da kayan kuma zaku biya kudin rini dan ba a banza muka Rina ba Ehhhe Hajiya tace Abu kayan za a kai faci kuma ASA a jiki dan hauka Arif yace ina Wannan mahau kacin da kuke fada shiya dace daku beyi aureba kuyake jira dankuma bakuda hankali kamar ku kila maya fiku hankali Amal tace me kuka yi amfa nida shi wajan wanke kayan Binta tace jita dan Allah da wata ma gana sai kace Baku kuka ajiye dan wanki ba na roba munjuye hi gaba1 na kwalima haka Gaba dayansu salati kawai sukeyi Hajiya tace Dole Kayan ya yage ya canza kala kuma dai bakwa son kayan shiyasa kuka basu su wanke muku se kuyi hakuri Ku anshi kayan a haka kukai faci ta bakin nasu Abu tace hine magana hajiya hiyasa nake sanki yasin kina saurin gane wa banda su nunar rana Aqeel yace a haka baze yiyuba mommy ya mike yazo kusa da Amal yadaga hannun ya kaiwa Abu duka Hajiya kina ganin nunar rana ko duka yakumakai mata a baki Yace daga yau nadena raga miki duk sanda kika ce nunar rana saina cire miki hakori kucaca kawai Hajiya tace banga amfanin fadan da kuke musuba alhalin kune da laifi idan Baku basu kayan ba haka ze faru Arif ya kayi shiru Mommy mezan ce tsautsayine ko Abu da binta sukace Eh Arif yayi dariyar mugun ta Karar shigowar mota sukaji kafin motar ta tsaya suka sauko Da gudu suka shigo falon Abu da Binta na ganin su jiki ya fara rawa idoya ciko da hawaye Sojojine sukazo gidan Abokan su Arif ne Arif yasan da zuwan su Agaban hajiya suka tsaya suna gaidata1bayan1 hajiya na Amsawa Abu da Binta ba bakin magana kiris kwai suke jira su fashe da kuka Amal ta gaida su jin Abu da Binta sunyi shiru Arif yace Ku gaida su abo kan mune Aqeel yace Ahmad dama ana ganin Ku Ahmad yace Eh wlh yanzuma wucewa muka zoyi ta unguwar ku Aisha tace min kundawo saidai kun kusa komawa shine nace bari nazo mu gaisa Arif yace tin dazu ya sanar dani cewa yayi nayi shiru yanaso ya baku mamaki ne Ahmad yace wayan nan fa kai kalli wani KWALLIYA kamar an hako su daga rami nibadan da mutane a nanba sai nace gamo nayi kalli yanda ta kafeni da idanu Harlokacin Abu da binta basu dena kallon suba Ahman yace Ke lpy kodai wani laifin kukayi Allah ya baku hakuri karku tafi damu bazamu sake ba tam bayi hajiya ita kanta tasan bama laifi tinda mukazo bamu taba laifin ba Aqeel yace karya sukeyi Ahmad tinda sukazo suke samu suru to kalli yanda sukayi da kayan nan daga basu su wanke idan barrack zaku kutafi dasu Ku kaisu kudakesu karkuma kudawo dasu munbaku A'a hajiya kisa baki kinga suna kyauta damu waiyoo inna yaya Nura gasoja ze kasheni waiyoo inna nadena Arif yace karya ta keyi karku yarda bazasu dena halin suba kutafi dasu kawai Binta tasa iho tana kiran umma kite makeni zasu kashe mu Cika gidan da suka yi dakuka yasa 1 daga cikin sojojin ya daka musu tsawa Abu da Binta suka rude saiga fitsari na zubowa kamar yara kafana rawa Amal dariya kawai takeyi ta kasa cewa komai Aqeel da Arif suka hade rai David yace daku zamu tafi Ku wuce mu tafi Koda Abu da Binta suka ga bindigar hannun shi suka kara gigi cewa Hajiya tace sun dena Ahmad kar a tafi dasu David yace maman mu yan2 sun gama magana mu zamu tafi dasu kuyi magana da ita Abu da Binta suka kafe hajiya da jajayan ida nunsu suka ce hajiya mundena baza musake ba idan kika bari suka tafi damu ta matsa kusa da hajiya tace me Jan idoncan da bindiga a hannu kashe mu zeyi Hajiya ta kalli Arif Ahmad ya hade rai yace mekika ce mata koma dai me kikace be da meniba Ku wuce mu tafi Abu ta rude tace hajiya kiyafemin idan kinga inna kice taya femin Allah yayi nizan rigata mutuwa lokacina yayi kicewa yaya Nura ina qaunar shi kuma nayi kewar shi kinga Wannan mezibin mugayan tinda yasa baki nasan komai ya baci New writer's Hakan Take *husba'ahfama* πŸŒΉπŸŒΉπŸ’‹ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  πŸ‘πŸ‘πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  πŸ‘ πŸ’„πŸ’… *'YAR KWALLIYA* πŸ’…πŸ’„ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  πŸ‘πŸ‘πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  Written by *husba'ahfama* 37-38 Ahmad ya daka mata tsawa yace nine me zibin mugaye naji na yarda David kutafi dasu Binta da Abu ciki ya murda suka fara tsalle suna ihu harda kuka Aqeel yace meye haka kuma Ahmad kana gani ko kokun tafi dasu kumusu dukan tsiya Ku karya kafa finsu da hannaye Abu tace hajiya kina jiko karya mu zasuyi kiba su haku waiyoo Allah na Hajiya tace ba inda zaku Ahmad kuyi hakuri indan sun sake nida kaina zan kira Ku Arif yace to mommy saidai ki bari David ya dakesu tukun na jikin su ya gaya musu Aqeel yace kayi musu dukan kawo wuka nikuma zan kira motar Asibiti Abu da Binta Suka zube kasa suna kuka suna cewa ba inda zasu David yace su tashi Abu da Binta Suka ki tashi Ahmad na daka musu tsawa Suka tashi suna tashi David ya daukesu da mari saida suka ga taurari Ahmad yace mu zamu tafi kukuma mu tafi Abu da binta ido yayi Ja sai kallon hajiya sukeyi Aqeel da Arif namusu dariya ganin yanda Abu da Binta Suka rude Hajiya tace Ku tsaya kusha koda lemone mana mun Tsaya muna magana ba a kawo muku komai ba Amal dauko musu lemo Hajiya ki barshi akan hanya muke zamu ware rana muzo mu yinar muku Tab Saikun sha lemo zaku tafi inbaku shaba Ku tafi dashi ze muku amfani tinda akan hanya kuke Taje ta dauko ta kawo musu Suka musu rakiya zuwa waje Abu da Binta na ganin su a jikin mota sojoji suka fara kyarma jikinsu yai zafi Amal tace Abu Binta lpy Abu da binta sukayi shiru Amal ta tabasu zafi taji da sauri da dauke hannun ta a jikin su Mommy jikinsu zafi basuda lpy Aqeel yace Ahmad karya ne basa so Ku tafi dasu ne kawai Hajiya bata ce komai ba ta kama Hannun su zasu shiga gida Ahmad yace mommy zaki tafi dasu basu yi Alkawarin dena abinda sukeyiba Abu da Binta sukayi caraf sukace mundena bazamu karaba Ahmad yace kuma kara kira kawai yan2 zasu mana muzo mu tafi daku shi kenan kuma baza a kara jin labarin kuba Hajiya tai musu sallama ta shiga ciki dasu Abu da Amal Arif dariya kawai yakeyi Ahmad ma haka Ahmad yace yan2 ba wasaba dana gansu na dauka matan kune dan nasan Wannan dogon burin naku dawuya ya ciki dan Kun Ja dayawa Haba dai Allah ya kiyaye ba dai muba kaga idan kana ciki sai kayi magana tin kafin mu bada su cewar Aqeel Ahmad yace yaran abin dariyar su yayi yawa irin Wannan tsoran haka Arif yace shir mensu kuma saiya kusa saka kuka kaga dai yanda suka yiwa kayan mu Kaya na2 kenan Ahmad yace kace yabi jiki to gaskiya zan gaya muku wayan nan bazasu nutsuba saidai su rage wani Abin koda sun waye Aqeel yace Allah Ahmad Da gaske nake fada maka yana yinsu zaka gani bana Tina nin Wannan abin zesa su nutsu mu zamu tafi Kace da sauran aiki Ahmad yayi dariya Suka shiga mota suka tafi Abu da binta naciki jiki zafi yaki sauki in banda karuwa ba abinda yakeyi Suna dakinsu a kwance sai rawar sanyi sukeyi Arif da Aqeel dakin suka je Aqeel ya daka musu tsawa yace Waze muku aikin fitsa rinku da kukazo kuka kwanta Zazzabine a jikinmu shiyasa muka kasa gyarawa Ko to Ku tashi Ku wuce manya da kudai Asibi da kande baza su muku aikin fitsari ba To gamu nan zuwa Da dai yafi kutashi yanzu da rashin jine dakunyi kun gama dake yanzu fitsarin kune shine zakuce bakuda lpy ko cewar Arif Aqeel yace yaran unguwa zan fita na tara muku su muku wakar fitsari Abu tace Kut Allah ya basu sa'a naji wani yace fitsari hmm Yasin bakin shi zanfasa na zubar da hakorin bakin kirasu kaga Aqeel yace Wani kinga Nifa nariga na baro jirgin ki Abu kanki baya aiki kinfi gane fasawa da duka da danbe inajiye miki randa zaki samu dai dai ke Arif ya kalli Binta da tayi shiru tana jinsu yace ke lpy Tace jinake kamar jikina ba ya tare dani ga kaina namin ciwo ga soja ya mareni ga saitin gurin ciwo kawai yakeyi Arif yace kefa dama kin iya kan kara Naganoki da cin abincine baza Kiyi Lissa fin nanba kuje Ku gyara fitsarin na kaiku Asibiti To suka ce suka fita gurin me gadi Suka je sukasa ya Bude musu kofa Megadi yace gaskiya bazan bude ba bakusan matsalar da kuka sani ciki bane Abu tace Kaga nan wajene ba inda zamu kasa zamu Ehbo Megadi yace yanzu naji magana kuje ina kallon Ku Suka fita Abu ta baza maya fin jikinta Binta ta zuba mata kasa da kyar suka samu suka kulle mayafin sukayi kama kama suka dawo cikin gida inda sukai fitsarin sukaje suka ajiye kullin kasa Arif da Aqeel na zaune suna kallo A tashar AREWA24 suna kallon mai mai cin gari ya waye Abu ta kwance kullin suka juye kasar a gurin da sukayi fitsari Binta ta baza kasar Aqeel da Arif tashin kasa kawai suka ji suna juyowa suka ga inda kasar yake Abu ta bige maya finta ta maida gwullin da tayi dashi a kugunta Arif yace ma su KWALLIYAR Aljanu anya kanku 1 kuwa meye na zuba kasa Anan kuduba fadin falon nan a ina kuka ga kasa da zaku zo kuzuba Binta tace kaga nunar rana karkusake kuce bamuyi dai_dai ba danku kun iya ciki baki mu a *DARAUDAU* da kasa muke rufe fitsari tam bayi abu Abu tace ina nan bame karyataki ko dandali indan munje fitsari ya kama mu saimu samu guri muyi mu rufe da kasa ta fada tana dariya Aqeel tsabar haushi ya kasa cewa komai komawa yayi ya zauna bazaku hauka taniba wlh nagode Allah hutum mu yakusa karewa dabansan yanda zan yiba Wannan ai rashin hankaline Abu tace Banga abin rashin hankali a nan ba mun gama kuzo ku kaimu inda kukace zaku kaimu Yasin muna jin jiki Aqeel a kufula yace Ku mutu Yasin yaran nan kozasu waye sai anshawuya Yasin Kunji ko kunfara samin qauyan cinku a baki Haya niyarsu hajiya da Amal suka jiyo suka fito Amal baki ta saki tana kallon kasar cikin mamaki ta tambaya tace waye da Wannan aiki ko ince tinanin waye a cikin Ku Binta tace namune nan da magana ne ke nafa Riga na gane take taken ki abamu fili yau mu kece raini tsaka ninmu ki gani inbam miki dukan tsayaba Abu tace nakine ya fito fili nima inada cikinta kiris nake jira jikin wata ze gaya mata Bayan Hajiya Amal takoma tace wato kun shirya yanda zaku zaneni tsabar mukunta ko to shi kenan yaya Ahmad beyi nisaba sena Kirashi yadawo Binta tace Mudai hajiya bamuda lpy kice sukaimu gurin magani ko sassakene a bamu musha Arif Ku kaisu Asibiti karku damu da nan zansa kande ta share Abu binta Allah ya kara sauki Aqeel yace mommy kice musu karwanda ta sake tayi magana harmu karasa dan yanda nake jin haushin nan nasu tsaf zan dakesu wlh Hajiya ta masu Abu fada sukace sunji baza suce komai ba Aqeel yace Amal taho muje tare Amal ta zaro ido tace niii yaya bada niba saikun dawo kanajin abin da suka gamacewa shine zan rakaku kalan su toshemin baki su dakeni Bame tabaki kizo muje Amal tace zanbikune kadai idan kunce zaku dinga juyowa akai_kai saboda tsaro badan tsoroba Eh munji taho muje cewar Arif Hajiya tasasu suka canzo kayan jikin su amma basu goge KWALLIYA ba Abu tace fita zasuyi su sumar da samarin birni dan su Aqeel ma gani gani suke musu da alama suma zasu suma akan KWALLIYAR Aqeel idan ban sumaba na sumar dake kucaka me kamada Aljanu Amal a tsorace tabisu Kai tsaye Asibiti sukaje Likita ya duba binta da Abu ya rubuta musu magani da Allura Arif yaje ya siyo komai ya dawo suka wuce dasu inda za a musu Allura New writer's Hakan Take *husba'ahfama*πŸŒΉπŸŒΉπŸ’‹ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  πŸ‘πŸ‘πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  πŸ‘ πŸ’„πŸ’… *'YAR KWALLIYA* πŸ’…πŸ’„ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  πŸ‘πŸ‘πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  Written by *husba'ahfama* 39-40 Abu da Binta suka karewa gurin kallon Abu a tsorace take yiwa Binta rada tace anya ba gurin kashe mutane suka kawo muba Nima dai haka nake Tina ni kalli guri shiru ba mutane ni dai a tsorace nake Kinga Binta karmu saki jiki dasu munaganin abin da bamu yarda dashiba mu gudu Kawai shine magana Wata mace ce tafito Aqeel ya mika mata Allura Abu taradawa binta tace ga makashiyar ta fito Tabare allura ta zuko ruwan tace kuzo namuku sauri nakeyi Binta tace kut muda zaki kashe zaki gayawa sauri kije kidawo bamu shirya mutuwaba mu kinga tafiyar mu Aqeel ya kalle su cikin fishi da jin haushin maganar da suka fada yace wai Ku meyasa a ko ina saikun nuna haukan Ku Kiyi musu kawai karki damuda dabinda suke cewa Abu ta dunkule hannu tace taho idan ban hada miki jini da majinaba mace dake kizabi kidinga kisa ko tsoran Allah babu Ku Nifa ba kisa nakeba allura nakeyi kuma za a muku ne sabida samun lpy kodai ba sune marasa lpy ba Amal tace sune nan yaya kurikesu kawai da alamu zasu bada wuya Gaskiya a rikesu kinyi gaskiya saboda idan suka goce Akwai matsala To ba damuwa semu rikesu cewar Arif Aqeel yace zaka rikesu dai danni ba wanda zan rike manya dasu ida na rikesu Sabolu nawa zan karar a jikina kafin na dawo yanda nake fitsari sukayi kana gani suyi wanka kafin Susa Kaya sunki shine zan rikesu Arif yace kana kallo dai lokaci zasu bata mana babu wata hanya inba Wannan ba Aqeel ya rike Abu badan yasoba Arif ya rike Binta a ka musu allura suka cika gurin da kuka ana gamawa suka zube a kasa suna kuka Abu cikin muryar kuka take cewa muguwa yar iska kirasa a ina zaki biga kusa a jikina sai duwawo dan bakin mugunta Gashi gurin ciwo kawai yakemin Binta tace kitam bayeta kwana nawa kusar zeyi ajikin mu kafin mu mutu kinsan hine zesa baza mumutuba yanzu amma yana fita shikenan mun mutu suka kara fashewa da kuka Wadda tai musu allura tace kuyi hakuri nadan lokacine zaku dena jin zafi kunji karku damu Binta tace Muguwa yar iska kingama watanda da damu kinshirya randa zamu mutu dole kice haka mudai shikenan munkawo kammu daga Wannan sai wancan Aqeel yace Dan Allah Arif kayiwa yaran nan magana sutaso mu tafi tinda sun gama jizgamu Arif yace kutaso abinda Baku saniba shine idan kuka cigaba da surutu kusar zefita kuma kunsan abinda zefaru idan ya fita zabi ya rage naku Abu tace munyi shiru mutafi Abu da Binta suka karaso gurin su da rarrafe Aqeel yadaka musu tsawa yace meye haka kuma dallah kutashi kuyi tafiya da kafa finku malamai Abu ta marai raice bazamu iya tashiba tazira kusar canciki bata yanda zamu iya tafiya hakan shine kadai mafita Amal dariya harda hawaye Binta tace Allah yabaki sa'a Amal zamu hadu sata gidan barawo rancene Kiyi ta dariya lokacin kine yanzu namu na zuwa muma Yanzu ya zamuyi da yaran nan haka zamu barsu su rarrafa har waje kenan Arif yake tambayan Aqeel Kabarsu meye a ciki susuka ga zasu iya ni kaga tafiya ta Abu Binta kutashi ku gwada tafiya zakuji kusar ta fita kunga shikenan saiko taka da kafarku Allah ko naji dadi shawararki ke dama sokike mu mutu shiya sa kikace haka ta Allah ba takiba muna nan darai kece dai zaki mutu ki barmu Amal tace Kutafi a haka Kukuka sani tinda Ku bakwa daukar shawara Amal da Arif sukayi gaba Binta da Abu na rarrafe insunyi su tsaya duk wanda ya gansu saiyayi mamaki ga kafarsu garau amma suna rarrafe Arif dan takaici yadaka musu tsawa yace kosu mike koya kira Ahmad soja nanfa suka mike tafiyar abin dariya gaba daya hannun su sukasa suka rike kugunsu suka ware kafa finsu idan suka jefa daya saisu huta sukara jefa dayar ma Arif da Amal sun manta da sun fita kafin Abu da Binta suka fito gaba1 dai abin dariya suka Zama Abu tashiga mota dakyar tanashiga ta kwanta ta daga duwawunta sama Binta ma yanda Abu tayi haka tayi Suka cike guri Amal tagir_giza kai ni ina zan zauna yanzu kuduba fa kuga yanda kuka cike gurin Aqeel afusace yajuyo zaku matsa mata kosaina yi kwallo daku yanzu yan qauye kawai Allah ya dawo da daddy lpy saikun koma qauye ko kunaso ko bakwaso Abu tace tab banga me maida ni *DARAUDAU* ba nazo kenan kai gwanda ma kusaba da halinmu dan munzo kenan kekuma uwar masifa shigo ki zauna ko yaya kikaga gurin karkice komai Guri kadan suka matsa mata ta shigo ta zauna a takure Aqeel yace ga tirare Amal ki dinga shaka dan zakisha kanshi Binta tace kanshi a ina fito fili kafadi abinda ke cikin ka munan da kake jida gani munfiku tsafta damma kunrabamu da tiraren jikin mu aidaba hakaba Abu tace fada mihi kuma in karya ne atashi ayi yar hin-hine Aqeel yace dani banshirya jiyowa kaina abinda yafi karfin kaina ba kuji da kanku Arif idan kayi gaba kadan zakaga super market ka Tsaya zan sai Abu Arif yace to haka ko akayi suna karasa wa ya Tsaya Arif da Aqeel harda Amal Suka shiga ciki sukabar Abu da Binta a mota Suna zuwa gurin takalmi amal ta daukarwa Abu da binta wani takalmi me tsiniπŸ‘  Arif yace Amal zaki karya 'ya'yan muta Nene dazaki ce a siya musu Wannan Yaya Kaine kake raina wa yaran nan hankali yaya idan suka tashi wayewa sai kayi mamaki Aqeel yace badai wayan canba gatakalmi dai ansiya musu kishirya kaisu gurin gyaran kashi Suka gama siyaiya suka fito suka koma gida Suna shiga Abu da binta da rarrafe suka je dakin hajiya suka fada mata abinda ya faru hajiya tayi dariya ta rarrashi su Abu *KWANAKI NATA SHUDEWA* akwana a tashi abu da Binta suka fara gyaruwa kadan sukafara sallah

Chapter 8 of 12