Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Waige ta fara canta gano wukarda ya mata bara zana dashi ta dauko Kaya sunyi kyau ba karya nikaina Abu na yaba saidai yanzu zan lalatasu tayanda bazasu sawuba Tasa wukar ta yanka bayan rigar shaddar daga sama har kasa ta maida wukar ta ajiye taninke rigar yanda tagani zata fita taga takalmi da alama ya ajiyene ze hada da kayan tayi gaba da takalman Abu tatafi boye takalmin ta dawo gun Arif wani ta gani yana tahowa da Kaya a hannun shi Abu tace Sannu ina wuni Yace lpy Arif yana nan Tace Eh yana nan Yace yauwa ga kayan shi kibashi sauri nake yi shiyasa bazan samu damar kara sawa gurin shiba ki kaimai da wuri dan tin dazu yake kirana a waya Abu tace to yace ma idan na ganka na fada maka ka kashe wayarka tinda kakawo mai dinki To zanyi Agabanta ya kashe wayar ya tafi Abu tace Waiyi wancan abin yine waya niai idan aka bani madubi zanyi dahi waiwaya abin dariya Abu ta komai tariko hannun binta suka wuce dakinda Amal ta nuna musu tace na sune A kan gado tazube kayan da takalmin Binta tace me zamuyi da wannan Abu tace bazamu kai mihi ba a ina zamu boye Binta tace daga katifa kisa a kasa Suka daga katifa suka Sa kayan a kasa Abu tace binni ba abinda babu kalli gadonsu gari guda ta daka tsalle ta tima akai tace hegen lauhi Bintama tsalle tayi tafada kan gadon Abu tace kadan kenan ai munkulla daku Yasin Arif saikiran wanda ze kawomai Kaya yake wayar shi a kashe gashi lokaci da sukasa zasu fita ya kusa Aqeel hankali kwance yazo gurin kayanshi ya waiga bega takalmiba beda muba ya kalli kayan yasa hannu ya dauko rigar New writer's Taku *husba'ahfama*πŸŒΉπŸŒΉπŸ’‹ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  πŸ‘πŸ‘πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  πŸ‘ πŸ’„πŸ’… 'YAR KWALLIYA πŸ’…πŸ’„ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  πŸ‘πŸ‘πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  Written by *husba'ahfama* 21-22 Aqeel ya ajiye rigar ya dauki wando yasa Yatafi dakin Arif yabude yashiga yasamu Arif na kai kawo a dakin Aqeel yace lpy naga baka shiryaba lokaci yana kurewa fa Kabari kawai tindazu nakira me dinki yace min yataho kawo min dikina nazauna jiranshi Amma haryanzu be zoba nakira wayarshi kuma a kashe Nikuma ya kawo min nawa kuma naso naga kamar harda naka ya kawo Eh yakawo min tsawo rigar yamin na Bashi yaje ya rage min shine haka ya faru Kasake kiranshi muga yanzu koze dauka Nahakura Aqeel kona kira baze shigaba nakira kusan saunawa amma haryanzu Bari na Sa rigata nazo muje gurin shi Yauwa Sa kazo muje Ok to jirani inazuwa Aqeel with full confidence ya daga rigar zesa mamakiyayi ganin rigar a yage What!!! mezan gani haka ya akayi rigar nan ya yage ba haka yakawo minba Arif Na'am meye haka Aqeel dawayon ka da komai ka yaga kaya idan bakaso saika bayar Haba Arif yazakace haka kasan yanda nake son kayan nan kuwa nazo sawa ina dagawa na ganshi a yake kuma Abu aka Sa aka yaga min Banganeba kana nufin wani ne ya yaga maka kenan Eh mana Ikon Allah sai kallo Aqeel tinda muke a gidan nan haka be taba faruwa saiyau kuma a kan kayanka to waya yagarigar kenan Abinda nake tinani kenan natabbata kowaye yana sane dacewa ina son kayan shiyasa yamin haka waye zemin haka Shine abin Gashi lokaci na kurewa fa kai kowaye Wannan yana sane da cewa zamu fita inda zamu yanada mahim manci sosai Wait ooh Meyarin yarnan tace minma Wa Me KWALLIYAR aljanu mana tace karna bari tafara dani Eh haka tace Waiyoo Idan narike ta bazaji dadi ba yatake dasuna matsa Tsaya karkace zakaje ka gwada zuciya ya agurinta yarinyar ko ido bata bari kuhada yanzu idan kaje kabata tsoro zatace zata tafi gidan su kome takeyi tanayine cikin karfin hali kuma Amal bazataji dadi ba wlh gaskiyama kenan Aqeel yajefarda rigar yace shikenan nabarta taci bulus kenan A'a bahaka nake nufiba nidai kwai karka bata tsoro danna sanka da zuciya Aqeel Naji shi kenan I will try too control myself kaiii yarin yarnan ta sham maceni To shi kenan dai Aqeel sai hakuri inagafa gurin nan saidai mu hakura kawai dan bahalin zuwa yau Aqeel yayi shiru da Alama hakankalinshi na wani gurin Arif ya tabashi Na'am Aqeel karka ce zaka tattaro damuwa kasawa kanka akan dan karamin abin nan kanada kudinda zaka sai dubunshi dan haka banga abin damuwa ba To shi kenan bari naga Amal Muje tare nima inason ganinta Bawani abune zekai ni gurinta bafa Nasani shiyasa zan rakaka Dakin hajiya suka shiga suka samu hajiya na tambayan Amal abinda yasa ta shigo takasa cewa komai sai kaiwa da dawowa takeyi Alhamdulilah naji dadin ganinku gatanan dai kullum a Abu 1 zanga randa zaki zauna kina wasa da dariya Amal Aqeel yace Amal meya faru kika kasa zama Daddy dai tacika Alkawari yakawo miki kawaye har2 masu hankali Gashi nikuma tayagamin Riga duk a cikin hankalin nata Amal tace wacece tayaga maka Riga Wacece in banda me KWALLIYAR Aljanunnan itace kadai zatayi haka nasani Amal tace gaskiya ba ita bace dan tinda suka shiga daki basu fito ba Mommy ba Wannan ba ma wainace suyi wanka Abu tace bazasuyiba kar tiraren jikin su yafita Arif da Aqeel sukayi dariya Suka tafa Arif yace sabon salo sukuma Wanka ne basayi Hajiya tace inji Abu haba koda nace tindazu nakejin wani wari yana fitowa Ashe sune rabu dasu bari naje zasuyi yanzuma kuwa Mommy bazasuyiba babu yanda banyi dasuba amma ina sunki gane wa danayi magana saisuce saisuce kanshin jikinsu zaifita Aqeel yace mommy ki barni dasu zasuyi wanka yanzuma kuwa yayi dariyar keta Arif yace sukuma haka suke nasu gayun ba wanka Amal tace bawanka ba kwanke baki haka sukace min Abu nata ma yafi tace rabonta da wanka harta manta Aqeel yace Eh baliga irinta yabaza tayi wariba zan samesu idan zasuyi da Kansu shikenan idan baza suyiba zan Sa a musu Hajiya tace yauwa dadai yafi yaza suce zasu zauna ba wanka idan mu mundaure wasu bazasu daureba ga gidanmu gidan mutane Aqeel yace ni zasu kunyata nida abokaina dasunzo zasuce sesun gaisa dake mommy suzo suji wari mezan ce musu Duk Abinda sukeyi Arif jinsu yake yi yana dariya Amal tace yaya Aqeel ba Wannan ba muje kasa suyi wankan Muje to Suka tafi Arif da Hajiya suka rufa musu baya Dakinsu Abu sukaje suka same su suna bacci Aqeel yace kut bacci hmm Amal samo min ruwa me sanyi Hajiya tace kar ka fara bance ba Abu Binta Aqeel yace dan Allah Mommy ji yanda dakin nan yake bugawa duk irin tiraren da akasa a dakin Hajiya tace Bakomai haka maza zasu gansu suce sunaso daidan wani karkataccen wani Aqeel yace tab dako yacika mara wayo duk irin matan dake fadi duniya yarasa wayanda zeso sai wayan nan Yanuna Binta da Abu dake bacci harda munshari Arif yace Aqeel mommy fa tayi gaskiya meye laifin yaran nan kaida muke shirin baka Me KWALLIYAR Aljanu tsabar sofa nunar rana take ce maka Hajiya da Amal dariya sukeyi Aqeel yace ni Allah ya kiyaye banaso akai kasuwa Amal bazaki tashe subako bari Nina tashe su Yadaga hannu ya kaiwa Abu duka Agigice ta tashi tana dukan Binta tana Cewa πŸ—£barayi nasani mune da laifi gidan Ku mukazo Allah ya Baku hakuri barayi Amal Mommy kinga irin hankalin nata ko daga tashinta sai ihon barayi basalati ba komai cewar Aqeel Yaya Aqeel wlh dukan ya shigeta kalli yanda ta gigice cewar Amal Hajiya tace banason Wannan saurin hannun naka Aqeel Abu ba barayi bane Bude idonki kiga mune Aqeel yace mommy muyi abinda ya kawo mu mubar dakin nan daki nabugawa kamar ba mutane bane aciki Hajiya tace Abu Binta kutashi kuyi wanka Abu tace tab harna wastsake Nifa nafada muku bazanyi wankaba nafada muku baze yiyu nabaro inna a qauye saboda fadan da take min akan Wanka nazo nan na sameki duk kinbi kindameni akan wanka Ke meya kawoki dakina dazu harkika yaga min Riga cewar Aqeel Ni a'a badai niba inama nasan dakinka dahar zanzo namaka me waina yaga Riga banda dukana da kayi harda yimin sharri Nidai nasani Abu bazata taba yaga maka rigaba cewar Amal Arif ya kalli inda suke kwance yaga gurin yayi tudu da kwari yace ya haka kutashi na gyara muku baza kuji dadin kwanciya a hakaba tashi muga Abu da binta sukai dare dare kan gado sukaki tashi Binta tace Kabari mun gode zamu kwanta a haka Tinda Aqeel ya kalli yanda Suka birkice akan za'a daga gadon ya matso kusa da gadon ya daga katifa saiga binta da Abu a kasa Tim Nasani nasan wani Abu kamar haka ze faro Wannan shine ramawar da kikace zakuyi Gashi kinyi kinji dadi cewar Aqeel Cikin mamaki Arif yace Kaya nane Wannan tareda takal minka Aqeel yace zaku tashi kuyi wanka ko baza kuyiba Maganar gaskiya shine baza muyiba kaifa dama na riga na baroka bakin ciki kawai ka keyi damu cewar Binta Amal jeki kiramin kande da Asibi Aqeel yafada rai a hade Amal tace to yaya Tatafi ta kirasu Yaya gasu cewar Amal Asibi kande wanka zaku yiwa wayan nan yaran komai na ciki duk wanda yaki Ku sanar dani Yaciro wuka a aljihun shi Abu ta tashi tsaye kan gado tace nunar rana karkamin haka bazan yi wankaba kuma karka kasheni Aqeel yace sauko kutafi yafada rai a hade ganin fuskarshi ba alamar wasa yasa ta sauka ta buya bayan Amal Yazauna a bakin Gado yana goga wukar a kasa wukar na kara kamar ze yanka sa New writer's Hakan take *husba'ahfama*πŸŒΉπŸŒΉπŸ’‹ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  πŸ‘πŸ‘πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  πŸ‘ πŸ’„πŸ’… *'YAR KWALLIYA* πŸ’…πŸ’„ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  πŸ‘πŸ‘πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  *NA SADAUKAR DA WANNAN* *SHAFIN GADUK* *WANI MASOYIN NOVEL DIN* *'YAR KWALLIYA A DUK INDA SUKE A FADIN DUNIYA* *BAZAN MANTA DA KUBA YAN 'YAR KWALLIYA* *FANS GROUP NAGODE ALLAH* *YABAR ZUMUNCI* *MUSAM MAN* πŸ‘‰fulani πŸ‘‰Hany πŸ‘‰Aysha Hamza πŸ‘‰Hassana lawal Naji dadin comments din da kukayi jiya akan *'YAR KWALLIYA* kunkaramin kwarin gwiwa sosai nagode Allah yabar qauna 🀝 Written by *husba'ahfama* 23-24 Ya wasa wukar yadaga yana kalla Aqeel yace Amal matsa muga Na matsa naje ina yaya kamata ahankali mana cewar Amal Binta tace gaskiya Akwai matsala nayarda da komai amma banda wanka bazan yiba Abu tace balle ni Abu Wanka Sam ka ajiye wukar ka agefe muyi magana ta fatar baki Yace bazan ajiyeba kamar yanda baza Kiyi wankaba hakanima bazan ajiye wukaba Arif yace ina bayanka sushiga suyi wanka saika ajiye idan sunki hmm kasanar dani Binta tayi wuf tace madoki zaka dauko dama kace dukanka yana kisa ko Arif ya hade rai bece komai ba Aqeel rai a hade ya nufo inna Abu take da wuka tana kalli Waitoo amal kina gani ze kashe ni waiyoo inna Abu ta fada tana niyar yin kuka Hajiya tace Aqeel Tsaya Abu Binta kushiga kuyi wanka kona barku dasu kuma Abu karki sake abinda kikayi Almubazzaran cine kina jiko Kai kawai Abu ta daga tace hajiya kece kawai zaki gane Nifa banason Wanka Yasin Hajiya tace kishi ga Kiyi yau idan kikayi zakiji dadin jikin ki gobe ma dakanki zakiyi Abu tace tab banga ranar ba ni nabari tirarena ya fita ba amana kenan gaskiya nunar rana Kaine kadai kake cin sa'a ta Yasin amma Bakomai Wukar Aqeel ya sun kuya ya wasa kanar washin ya cika dakin Hajiya tace Abu Binta kunga fitata tinda baza kuyi abinda nace ba kunga kuwa banga abinda zan zauna nayi mukuba tai fice warta daga dakin Abu ta fasa kara tana kuka tana cewa waiyoo inna ze rabani da tirarena waiyoo baba nakawo kaina Keee Rufe mana baki Aqeel yafada cikin tsawa mai raza narwa Abu tai shiru kamar ruwa ya cinyeta Arif yace shiga kishiga nace yafada cikin tsawa yanuna Binta yace kema zoki wuce Abu da binta suka shiga Asibi da kande suka rufa musu baya Asibi ta rufe bandaki suka shiga wanke Binta da Abu tin Asibi da kande najin kanshin sabulun harsuka dena ji Asibi da kande basu wani sufaba da karfin su su irin matan nane masu kirar karfi dukda sunfara sufa da karfinsu Kowan nan su yarike mutum daya yana wanka iya karfin shi suka tsefe musu kai suka wanke musu suka debo kayan aski suka aske inda ya dace Asibi da kande sunsha kanshi suna musu wanka abuda binta na zagin su Aqeel rai fes beso yasa musu baki ba yaga mishi rigar da Abu tayine yasa dariya kawai yakeyi shida Ari Amal kuwa ido ya ciko da kwalla Saida suka shafe tsawan lokaci suna Wankar abu da binta saida suka tabbatar sun fita tas sannan Asibi da kande suka fito Daga bandaki Abu take cewa mugayan tsofi tinda ta danneni da kafarta na kasa motsi dadin tadai muna tare zakisan ni kika yiwa haka Arif yace abinda zaki saka musu dashi kenan Amal je dakina zakiga abinda nake duka dashi ki dauko min A'a karka dauko cewar Binta To ku gyara maganarku Ku yanzu Abu tace mun gode takarasa fada tana gunguni Aqeel yace Asibi karku tafi da saura basu goge baki ba Asibi tace hakane muma bamu goge musu ba Abu tace Yasin yanda kasa suka rabani da tirarena basu isa su rabani da almiskin bakinaba hikenan kuma danku mugayene shine zakumin babun badilahu Arif yace Asibi kushiga Ku Tsaya a Kansu idan basuyiba kuyi musu ninace Binta tace nunar rana kwai mugu kamar mu ze raba da tiraren jikin mu damu dakai zaman lpy ya kare Yasin Buruhi zasu mana wai ni Yasin tsoran mannan nake lokacinda tajo yadawo daga binni shiya tahowa dayan gidan su tashin farku da fanteka tayi saiga hakwaranta a kasa sun zube gaba1 Abu ta gigice tarasa inda zatasa kanta Duk hirar da suke Arif da Aqeel najinsu dariya ya hanasu magana Yaran nan zasu kashe mutum da dariya Arif ya radawa Aqeel Amal barin dakin tayi dan bazata juri jin ihon binta da Abu ba Kande da Asibi suka koma bandaki Asibi ta dauko brush ta Sa musu man goge baki ta basu Binta tace ya akeyi to kinwani bamu matajin kai ni yanzu jin kaina nake kamar baya jikina tinda akawanke nauyin da yake dama yanzu babu Asibi tace kusa abaki kuyi kamar yanda zanyi Asibi na goge baki suna kallon ta Abu tace a sharama harda baki nidai bakina beyi datiba kalli wani kunfa dayake fitowa yana gama fita sai mutuwa Binta bakiji tana kakarin mutuwa ba Kande tace kunfar bana mutuwa bane dadtine yake fita zaku wanke komu wanke muku πŸ—£Waiyoo zasu kashe mu Amal abinda Abu da Binta suka fada kenan Arif yace Kande komatse su kuwanke bakin Kande tace to Suka kama su sukawanke musu bakin suna kuka suna dukan su amma ko a jikin su jinin da yafita daga bakinsu kuwa ba a magana saida bakin ya fita tas sannan Asibi da kande suka fito Kande tace mungama muna iya tafi Aqeel yace Eh mun gode ga Wannan kusai magani kusha dan Wannan ba karamin aikibane Dubu 10 ya basu Bakomai mune da godiya cewar Asibi Abu da Binta babu abinda sukeyi sai kuka suna zagin Asibi da kande Arif yaje dakin hajiya yakira Amal Hajiya tace ammusu wanka Eh hajiya naso ace kina gurin saikinyi dariya iya san ranki Hajiya tace yanzun ma nayi dariya ga kayan da zasu Sa Arif ya dauka yace Amal kekika zabo amma yayi kyau Tafita batace komai ba Arif yayi dariya yabi bayanta Abu Binta Ku fito Abu cikin muryar kuka tace muyi me bayan kun kaheni kun rabani da kanhina da Almiskina gaba1 Amal ta Bude bandakin ta shiga ta rar rashe su dakyar suka yarda zasu fito Amal ta basu hijabi suka Sa suka fito Tinda suka fito Arif da Aqeel suke binsu da kallo harsanda Amal ta gane haka Tace yaya Ari yaya Aqeel kallon yayi yawa Aqeel yace Amal suma yan biyune A'a meka gani ta juya tana kallon Abu da Binta Kai ikon Allah Abu kodai kuma yanbiyu ne cewar Amal Abu tace yan2 nemu kuma takan nunar rana zamu fara Kofi Arif da Aqeel sukayi dariya Arif yace to muna jira saida kusani koda Ku ba yan2 bane to kuna kama sosai saida safe Yafita daga dakin Aqeel ya wasa wuka yace ina jiran wata mara kunya takawomin wani rashin hankali yankar rago zan mata Yana gama fada yabar dakin Abu da Binta rai ahade idan kagansu bazakace sun tabayin dariya ba Amal tace ga man shafawa ga tiraren mekanshin dana fada muku Nina tafi saida safe Binta sukayi da kallo Arif da Aqeel dakin hajiya suka wuce Arif na shiga yace mommy qazanta bakyau kinga yanda yaranki suka fita fes bawannan bama kinga yanda suke mugun kama su2 Hajiya tace haba dai suna kama Sosaima kibari gobe kya gansu yanzu sunyi bacci cewar Amal Allah ya kaimu harna kagu na gansu cewar hajiya Su Aqeel sukayi wa hajiya saida safe suka tafi Bangaren yan qanshi Abu da Binta ba abinda sukeyi sai gunguni koda kande takawo musu abinda sukasa agirka musu kinci sukayi Abu tace Binta duba ni da kyau Anya ban hujeba kuwa Binta tace hujewa kamar ya gakinan yanda kike saima wani haske da kikayi Binta bazaki ganeba iskace take shigana ta ko ina shine na dauka ko hujewa nayi ta wani gurin Ashe dai bani kadai naji hakaba shiru kwai nayi nunar rana Allah ya kaimu gobe damu kake magana cewar binta Yihiru Binta ba a cewa komai gobe sai wanda ya gani Abuta baje musu kayan KWALLIYA sukayi suka kwanta bacci harda munshari New writer's Hakan Take *husba'ahfama* πŸŒΉπŸŒΉπŸ’‹ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  πŸ‘πŸ‘πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  πŸ‘ πŸ’„πŸ’… *'YAR KWALLIYA* πŸ’…πŸ’„ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  πŸ‘πŸ‘πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  Written by *husba'ahfama* 25-26 WASHE GARI Hajiya tayi samma kon zuwa dakin Abu da Binta tasamu suna bacci Tata she su Abu cin magagin bacci tace waiyoo waye Wannan ko ince dan bakin ciki baccin ma baza a barmu muyi cikin kwanciyar hankali Hajiya tace nice Abu Bude idonki kiganni safiya tayi kuma banji motsinku da Asiba ba Binta tace zamu tashi amma sai anjima Sallar fa Binta Hajiya zamuyi idan mun tashi cewar Abu Ban yardaba kutashi kuyi yanzu kona kira Arif da Aqeel kuma kunsan sauran Zumbir suka tashi Suka shiga bandaki sukai zaman su ganin basuda niyar fitowa yasa hajiya ta fita ta turo musu Amal Amal tazo bata gansu adakin ba duk ta tada hanka linta tana nemansu taduba ko ina banda ban daki tasakarfi ta Bude ban dakin tiris tayi tana kallon abin mamaki Akwance ta samesu a ciki suna bacci ko a kansu Abu kutashi wayace muku ana kwanciya a bandaki Waiyoo ko ina ba sauki nan dinma ba za a bar muba cewar Abu Binta tace kema fada kike wayan nan yanda kikasan sun hada jini da mayu naci agurinsu kudama nan ya gansu ya barsu Amal tace Bakomai kutashi suka tashi suka zauna amal tace ya kuka ji jikinku jiya Abu tace harna wassake ba dadi nida iska ya hanani bacci sai higata yakeyi kuma kaikayin da jikina yakeyi jiya beyiba Gahi munyi bacci medadi ko binta binta tace eh mana Yanzudai kuzo muje muci abinci kowa na can Ku ake jira naceko kunyi sallah Abu da binta suka kalli juna sukace Eh munyi To shikenan mu tafi Amal na gaba suna binta a baya harsuka karasa Amal tanuna musu inda zasu zauna Suka zauna itama ta zauna Abu da Binta Suka gaida Alhaji da hajiya Arif da Aqeel kuwa hararane ya shiga tsaka nin su Amal ta zuba musu komai ta basu Arif ya zuba musu lemo ya basu Yana dariyar keta A yamutse sukeci dan basu saba da shiba hasalima ko dadi be musu ba Abu ta kasa daurewa tace kawu wai gidan nan ba abin dadi sai wayan nan Abu ba dadi abani Koko da kosai hine nasan naci abinci Alhaji yace Abu kudaure kusaba da wayan nan cimar yanada dadi shima amma ba komai bari nasa amuku abinda zaku iya ci Arif yace kusha lemone me dadi Abu ta dauki kofin lemon ta kai baki ta kasa rike lemon saboda gas din shi saiga lemo ya dawo ta hanci Abu ta mike tana tsalle tana cewa Arif ze kasheta Aqeel ya daka mata tsawa yace malama kinutsu kinjiko karkizo nan kijuye mana guntun haukar ki idan kinsan baki taba shaba meyasa zaki sha Abu ta fara hada hanya tace juwa ce take dibana Anya ba giya ka baniba kai dan Allah tana gama fada ta zibe a kasa Alhaji yace Abu lemone ba giyaba mema ze kawo giya gidan nan Aqeel yace kafin yaran nan su waye sai Ansha wuya daddy lemo wai giya badan kunga abinda ya bataba

Chapter 5 of 12