Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ko 3 ba aikin ga da sauki ko Amal tace sosai ma yanzu dai gobe kushirya mu shiga kasuwa kowa ya siyo abinda akace musiyo naji kunyi shiru ko ba a ce Ku siya bane Binta tace tafada mana yanzu na keso na fadawa mommy Hajiya tace Amal idan kudin gurinki baze kaiba ki fada min na kara muku Abu Binta kuje kuyi karatu gobe jara bawa Abu tace hakane bari muje Amal tace kujirani muje kunayi ina jinku Taho to suka tafi suna wasa da dariya hajiya ta kalle su tayi murmushi "Allah ya raya minku Abu da Binta suka jera sati1 suna zuwa zana jara bawa sai su raba dare suna karatu Amal dakinsu ta dawo da kwana tana temaka musu saboda ita jami'a take zuwa hankan yasa su Abu da binta suke fahintar abinda suke karan tawa hakan besa sun dena zuwa koyan KWALLIYA da girkiba sun bawa komai lokacin shi jiran ranar da za a basu hutu da saka makonsu suke jira duk sunbi sun hana Amal sakat daga sun tuno saisu ce mata na nawa zamuzo sai tace musu na 1 Binta tace Amal ni saina ga kamar ba gaskiya kike fada manaba Amal tace ban fa himtaba kodai duk irin karatun da mukeyi yatashi abanza Abu tace kamarya yatashi a banza bam fahim taba Kin fahimta hankali kawai zaku raina min woto idan munyi karatu idan kunje makaranta sai kuyi wasa ko Binta tace injiwa bakiga yanda muke cika paper ba To idan hakane karku sake damuna kusa a ranku cewa zaku fito da saka mako me kyau kunga ne ko To munji Yau zamu gama namu jara bawar natafi Saikin dawo Allah ya bada Sa a Ameen nagode muku Tashirya ta fita Amal na fita suka shirya zasu tafi makaranta dakin hajiya suka je suka sanar da ita tai musu addu'a Suka wuce makaranta Suna shiga aji yan ajin suka Sa dariya Abu da Binta suka kule suka basar suka samu guri suka zauna duk wanda ya juyo ya kalle su saiyasa dariya abinya ishi Abu me kuke nufi da mune dazaku kalle mu kusa dariya ko kungamu da wata makusa ne hannune daku muma muna dashi kuna da kafafu muma muna dashi to meye na dariya Binta tace Rabi dasu DA alama sai mun dagargaza bakin su tukunna zasu gane naga dan rainin hankalin da ze kuma dariya Anan inbamu koya mishi hanka liba Tana gama fada suka Sa dariya A zuciye Abu da Binta suka yi Kansu zasu daka Malamin su yace karku fara kutsaya tukun na Binta tace amma malam tinda muka shigo suke ta mana dariya dube mufa kaga meye abin dariya a jikin mu Yace kume yasa kuke musu dariya Yan ajin basu ce komai ba sai dariya da sukeyi Hakan ya kara konawa Abu da Binta rai Malam matsa kar jini ya tabaka dan cikin ajin nan yau ba wanda ze fita cewar Abu Yace meyasa kukeda saurin fishi ya fada yana dariya Binta tace harda Wannan abin a kara bata mana rai Abu me muke jirane Yace A'a ku Tsaya ni da kaina zan fada muku da lili an hada dika aji 2 a nan ne saboda wani abu Meye shi ayi a fada mana hannuna na kai kayi wlh zan fasa baki cewar Abu Yace Bakinwa dafatan dai ba nawaba a ss1A zainab kece kika dauki na1 A ss1B kuma Fatima kece ta 1 Yana gama fada yan haji suka tafa musu "suka ce Wannan shine abinda yasa muke muku dariya murna muke tayaku Abu da Binta baki harkeya suka koma suka zauna Yace ga result dinku kukai gida Suka ansa suna murna baki yaki rufuwa Ana tashi me mota ya daukesu ya maida su gida yana a jiyesu suka fella da gudu suka shiga gida suna shiga suka samu hajiya da Amal a falo sai kuma suka canza fuskar jiki a mace suka zauna Amal tace meya faru kardai kuce min kunfadi a jara bawa Hajiya tace Ku kwantar min da hankali mana Abu Binta Ku fada min meya faru Abu tace gaskiya mun tabbata marasa kokari mune mukazo na karshe a aji shine kawai Amal tace karya ne duk irin karatun da kukayi magudine Wannan anyi cuta wlh naga saka makon naku Suka mika mata Amal na budewa ta fashe da dariya ta run gumesu "nidai nasani cewa kuzakuzo na 1 indai ba ayi magudiba Hajiya cikin farin ciki tace Allah ya temaka kukara dagewa wajan karatu yanzu ss2 zaku idan ankoma hutu ko Eh Hajiya tace Da kyau Alhaji ya dawo daga tafiya fitayayi ba dadewa zedawo yana dawo wa nizan fara fada mishi Zeji dadi sosai na sani Abu da binta suka ce Muzamu shiga ciki sai anjimanku Amal tace kujirani ina zuwa mutafi tare Tabisu suka tafi koda dare yayi hajiya taje dakin Alhaji a zaune ta same shi Tai sallama Ya amsa Tasamu guri ta zauna " Alhaji wata magana na keso muyi da kai Ina jinki fada min Alhaji bansan yanda zaka dauki maganar ba amma ya dace na fada Ba komai koma meye ki fada min ina jinki Alhaji cewa nayi meyasa baza mu hada Abu Binta da Aqeel Arif aure ba kaga su Arif haryanzu basu fitar da matan da zasu auraba su Binta kuma yanzu ss2 zasu shiga za a iya daura aure idan sun gama makaranta saisu tare yaran Nada kokari sosai saboda karatun da ake musu a gida suna zuwa makaranta a kasasu a ss1 susu kazo na 1 a aji Murmushi Alhaji yayi "naji dadin maganar da kika fada nima nayi Wannan tinanin saidai amincewar yaran shine Zasu amince Wannan ba matsala bane Alhaji basa kula samari koda sun musu maga shiyasa nakeda tabbacin cewa bazasu kiba Alhamdulillah Wannan ba matsala bane Sunyi hutufa Alhaji shine nace kar a Ja abin meze hana muje DARAUDAU mu sanar dasu a dauro auren daga can mudawo Kemafa kin kawo shawara bakomai dama kuma zanjima kafin na koma jiya nayi wayada mahaifin Abu yadawo yana gida yanzu haka ki sanar dasu hajiya kisa rana sai muje Aini ko gobe idan mukaje ba komai Alhaji bakasan yanda na damuda Wannan hadinba dama sunjima basu jeba bari naje na sanar dasu su shirya gobe muje Hajiya kina maganar shirya wa su Aqeel Arif kin sanar dasu ne Zan sanar dasu kuma koda anyi musu aure baza suyi maganaba Allah yasani munbasu dama amma haryanzu ba lbr To shikenan Allah ya basu zaman lpy Ameen Bari naje gurin su Tana fita taje ta samesu suna ta hira basuda niyar yin bacci Sannun Ku da hutawa Mommy yaushe kika shigo bamuga shigowar kibafa cewar Amal Hakane kuna hira baza Ku saniba Abu Binta kushirya gobe muna *DARAUDAU* A tare Abu da Binta sukace muyi me a *DARAUDAU* Hajiya cikin mamaki tace mekuke nufi inna Nura da Umma kum manta dasu kenan ko yaya Abu ta zumbura baki tace badan na ajiye su a canba ba abinda ze kaini *DARAUDAU* Lallai Abu ma haifar taki cewar Amal Binta tace itafa bazaku gane bane mu baza mu iya zama a canba yanzu tinda muka saba da nan Allah dai yasa muna zuwa zamu dawo New writer's Hakan Take *husba'ahfama* 🌹🌹💋 👠👠👠👠👠👠 👝👝👝👝👝 👠👠👠👠👠 👝👝👝 👠👠 👝 💄💅 *'YAR KWALLIYA* 💅💄 👝 👠👠 👝👝👝 👠👠👠👠👠 👝👝👝👝👝 👠👠👠👠👠👠 Written by *husba'ahfama* 47-48 Idan munje a can zamu zauna ba dawowa cewar hajiya Saikun dawo mudai ba inda zamu cewar Abu da Binta Amal dariya take ta yi "bantaba ganin mutum yaki komawa inda ya fitoba zuwa kamar anje Ehhhe nima inaso naje *DARAUDAU* Girgiza kai binta tayi "Kita zuwa mudai ba inda zamu saidai idan ta karfi za a mana bazaki ganeba Amal nagode Allah cewa dake zasuje zakika komai da idanki idan kin dawo kya bamu lbr Kun isa kafata kafar Ku zamuje *DARAUDAU* Abu tafashe da kuka " Nifa idan aka kira sunan garin tahin zuciya yake sani idan aka kuma fada kuma zan iya amai Hajiya tace Kyama dena dan idan muje zamu dan jima kafin mudawo Binta tace mommy kinga Ku musu kudin mota su suzo badai mu muje ba Nifa na gama magana kushirya gobe muna *DARAUDAU* cewar hajiya Tana gama fada tayi fice warta Amal tace hartsawan sati2 zamu zauna a gida ba inda zamu zamu iya zuwa idan mun dawo kuma sai muyi bikin gama koyan dinki KWALLIYA girki natafi yara kuyi murna saida safen Ku Bintasu kayi da kallo rai a bace Itafa waccan murna kawai takeyi cewar Abu Binta tace tinda naji ance *DARAUDAU* yanda kika san karna kwanta bacci dankar safiya tayi a ce mu fito mutafi Ya muka iya kayan aro baya rufe katara dole mu hakura muyi addu'a kar Allah yasa idan munje su baromu Binta tace bazasu baro muba idan suka baromu karatun mu fa Waze mana Hakane kuma hakuri kwai zamuyi mu kwanta bacci saida safe Allah ya kaimu Kwanciya sukayi badan suna jin bacci ba a kunne su aka kira sallar Asiba suka tashi sukayi sallah saiga Amal ta shigo Tinjiya na gama shirya kayana yan mata sai tafiya kufa Binta ta kalle ta "tsirara zamu Amal tayi dariya "Allah ya Baku hakuri daddy ya tafi masallaci yana dawowa sai tafiya shine nazo na fada muku Abu tayi tsaki "shine me ko kuka zamuyi saboda kin fada mana haka Bazan so kuyi kukaba kuyi farin ciki kuda zaku DARAUDAU kuga wayanda kuka jima Baku ganiba kuje dandali kokum mantane Abu ta kalli binta Suka kama hannun Amal suka fitar da ita daga dakin suka rufe Bakomai dai zamu hado a motar zuwa DARAUDAU Kinsan meyasa take mana haka saboda ta gane cewa ba masan zuwa daga yanzu mununa cewa munaso aje cewar Binta Bazan iyaba wlh saidai tai tayi ko a jikina Ai shi kenan sai kishiga Kiyi wanka kifito nima nayi cewar Binta Wai yanzu da gaske dai za a je Cewar Abu Gashi kuwa waccan kwandar tace tashirya harda hada Kaya ma Bakomai Allah gamu gareka Tashiga wanka ta fito Binta tayi ta fito Suka saka Kaya iri1 Sai ga Amal ta dawo Nazo naga wana irin KWALLIYA zakuyi Abu tace Ya akai kika shigo Makullin dakin ku yana gurina shiyasa bansha wahalaba kai kayama iri1 mukasa kai abin mamaki Ita kadai taita magana basu kulataba harsuka gama shiryawa ita ta daukar musu kayan da zasu tafi dashi dakin hajiya sukaje suka gaidata suna fitowa suka ga Alhaji shima suka gaida shi suka zauna a falo suna jiran fito warsu bajimawa suka fito suna karyawa suka shiga mota suka dauki hanyar tafiya DARAUDAU sunyi tafiya me tsawo kafin suka isa garin suna zuwa yara suka zagaye motar a kofar gidan su abu suka yi parking din mota koya ya fito banda Abu da Binta Saida hajiya tayi dagaske kafin suka fito dan cewa sukayi a kirasu suzo su gaisa sai su koma basai sun shiga ba suna fitowa Amal tace yara Baku gane su bane Abu da binta ne yaran suka shiga kiran sunan Abu da Binta sukuma suka hade rai Amal dariya take tayi cikin gidan suka shiga inna ta shimfida musu tabar ma Suka zauna Abu da binta na tsaye sunki zu zauna Inna tace Abu Binta Wannan wana sabon salone kuma haka Abu tace inna karki damu yanzu zamu koma base mun zauna ba Abu da Binta suka gaida inna Ta amsa cikin mamaki "lallai yaran nan sun shiryu yau kune kuka gaisheni mariya nagode naji yanzu ba kanshin gado sundena KWALLIYAR haukan nan amma naji dadi Binta tace inna ina yaya Nura ban ganshiba Dashi da baban Ku suna can wajan daurin aure yanzu zasu dawo Abu tace umma fa Tace gatanan zuwa dan nasan lbr yasameta cewa kunzo yanzu zata shigo Koda suka gaji da tsayuwa suka samu guri suka zauna Nan fa inna ta shiga gaisawa da Alhaji hajiya da Amal bayan sun gama gaisawa A tare malam munzali Nura da umma suka shigo Abu da binta sukasa ihu da tsalle Suka Tsaya a gaban Nura Yace na sani ai baza Ku taba gyaruwa ba ko ina kukaje yanzu Wannan ihun na me Nene kuma Farin ciki mana Tsaya ma tukun na baka farin cike da ka ganmu ne ko yaya kaga dama ba dadewa zamuyiba yanzu zamu koma kwantar da hanka linka cewar Binta Yace yazance bana farin ciki da ganin Ku babu wanda ya kaini farin ciki nayi kewarku sosai da kyar na iya jure rashinku wlh Sukace Allah sarki yayan mu Umma suka gani a gefe tana kallon su tana dariya Suka Sa ihu sukayi ganta cikin farin ciki da so da qauna ta rungumeso Amal na ganin haka tagane cewa mahaifiyar Binta ce Umma harda hawayan farin ciki ganin yarta tayi fari tayi kyau tana cikin koshin lpy Amal ta taso ta sunkuya a gabanta ta gaidata umma ta amsa gaisuwar tareda dago Amal umma ta samu guri ta zauna suka gaisa dasu hajiya tai musu godiya malam munzali ma gaisawa sukayi Abu da Binta sukace munganku kuna lpy mu zamu tafi daddy mommy Amal kutaso mu tafi Kudai kutafi mukuma muna nan bazamu koma gida ba cewar Amal Abu tace to ai shi kenan mu zamu shiga gari bazamu dadeba zamu dawo Amal taho muje kiga DARAUDAU Amal tace To muntafi Nura yace Ku Tsaya mu tafi tare dan yaran nan ba nutsuwa sukaiba suna iya zuwa wani ya tsokanesu sukuma su daka tatashi suhau fada Yaya nura we are not a kid's she kararmu 17 mun wuce yara ko Hakane bakiyi karyaba Amal mutafi Suka fita gaba 1 su wato sun hakura sun yarda suna karatu a can kenan Amal tace Eh yanzu ss2 zasu shiga Ss2 kuma dawana kanzasu shiga amma sunyi sauri yaranda basu iya karatu ba Sanin da kamusu yanzu ba haka suke ba susukazo na1 a ajinsu Tab amma kunyi babban yaki kafin su fara zuwa makaranta ko Wannan yazama lbr yanzu dan Gashi suna jin dadin makarantar tasu Koda yaran suka fita ya rage saura iyayan Alhaji Nasir yayi gyara murya "wata maganace take tafe damu nanya sanar dasu abinda suka yanke akan yaran nasu Malam munzali yace Wannan ba matsala bace kunfi karfin haka a wajan mu saidai ga mahaifiyar Binta bari muji daga bakinta Umma tace bakomai wlh ni banida matsala idan yaran sun yarda shi kenan Allah ya musu Albarka ya basu zaman lpy Alhamdulillah tinda munfahimci juna yaushe kuka zaba dan a daura auren nasu cewar munzali Alhaji Nasir yace munfi so a daura auren nasu Anan sai kusa rana munana har a gama komai na bikin a musu komai kamar yanda a keyi Bakomai Wannan ba matsala bane yau laraba mu bari ranar juma'a sai a daura musu aure Wannan ba matsala bane cewar munzali Inna tace ni kuma zanyi magana da su Abu da Binta nasan zasu a min ce To Bakomai Allah ya kaimu da rai da lpy Su Abu na cikin tafiya wani ya Tsaya a gaban su da redio irin nada yana jin waka Abu tace Wannan rashin hanka linfa zaka wani zo gaban mutane ahaka Yace kuyi min uziri san kune ya makantar dani tin kafin Ku tafi birni nake dawai niya da sanku banaci bana sha koda na samu lbr zuwanku nayi murna sosai shine nazo na sanar daku kafin kumin nisa Abu da Binta suka kalli juna suka tafa Binta tace a haka kake sonmu dubi kayan jikin ka Riga daban wando daban hula a yahe kuma dan idonka da kwalli shine zakace kana sonmu Abu tace maza wayanda suka fika a birni saudubo ko kulasu bama yi shine dan munzo nan zamu kulaka kabace a gaban mu komu gyara maka zama New writer's Hakan Take *husba'ahfama* 🌹🌹💋 👠👠👠👠👠👠 👝👝👝👝👝 👠👠👠👠👠 👝👝👝 👠👠 👝 💄💅 *'YAR KWALLIYA* 💅💄 👝 👠👠 👝👝👝 👠👠👠👠👠 👝👝👝👝👝 👠👠👠👠👠👠 Written by *husba'ahfama* 49-50 Nura yace kina ganin suko Amal daga haka zakiga ga sun rufesu da duka Amal tayi datiya Nura ya karasa inda suke "kai katafi ka basu guri tinkan sununa maka cewa basu nutsu ba Ka fahim tar dasu cewa ina sonsu zuciyata ta kasa daurewa bazan iya rayuwa inba busuba Abu tayi kwafa "waiba iro bane dan gidan mati Godiya ta tabbata ga Allah madau kakin sarki shine mahaifina kinga komai yazo da sauki Binta takare mishi kallo " kura tayi lpy har yaushe tsoho ya dena yankan Aljihu kai kuma kadena kama kaza da a gwagi Ke nizaki gayawa magana dan ina sata hakan baze hana ni aureba ko Ya isa shiyasa nace katafi nasan su sarai cewar Nura Natafi da soyayyar Ku a zuciya ta sai wata rana Banza gaja kucaki dashi dan qauye cewar Abu da Binta Amal tayi dariya "Mudai muyi sauri muje mu dawo na fara gajiya da tafiya garinku da girma sosai Binta tace tin ba aje ko inaba kingaji mukoma daga nan to anjima muje dandali musha rawa Abu da binta Suka fara rawa da waka harda juyi Kinga halin nasu ko wai suna muku haka a can koda yake za suyi na sani kwabar rawar haka sai kunje dandali ko yaya Munbari muko ma gida cewar abu da binta suna komawa gida inna ta kirasu ta sanar dasu maganar da sukayi a Kansu Abu da binta suka tibire waisu baza suyi aureba koda zasuyi banda su nunar rana Inna tace meye aibinsu da zakuce bakwa son su yanzu Ku dan bakuda kunya zaku iya fadar maganar nan a gaban Alhaji nasiru da hajiya mariya da Amal Abu ta girgiza kai "mommy daddy da Amal sunfi karfin haka a gurina su nunar rana ne inna bakiga yanda suke takura mana ba wlh Hajiya tace Amal binta da abu zasuyi aure fa Aure mommy baza a barsu su gama karatu ba za a musu aure susunce suna sone gaskiya baze yiyu ba Murmusawa hajiya tayi " seki tsaya kiji wayanda zasu aura kafin kice haka Bazan jiba baruwana dasu bari naje gurin inna da kaina tinda Ku bazaku hana faruwar haka ba Aqeel da Arif zasu aura za a daura auren ranar juma'a Amal tayi murmushi ta dawo kusa da ita ta zauna "yaya Aqeel da Arif namu Eh su kina iya zuwa ki hana meyasa kika dawo Murmushi tayi " baki fada min da wuriba shiyasa naji dadin haka bari naje gurin su Dagudu ta tafi Binta tace gaskiya inna sai munyi shawara da Amal tukun na jiramu muna zuba Suna fita sukayi karo da Amal tana murmushi " ya kun amince Kinsan da maganar kenan meyasa zamu a mince kinsan komai fa base na fada miki ba cewar Binta Amal ta kamo Hanna yansu "karku damu da komai yanzu zaku rama abinda suke muku lokacin kune yanzu amma karku tsauwala musu saboda ni Abu tace insha Allahu hakan baze faruba Nifa nunar rana me KWALLIYAR Aljanu yake cemin fa Shine nace miki kuma kununa musu kunwaye yanzu kindena KWALLIYAR Aljanu kinkoma yi normal kamar kowa koda yake karku damu nida kaina zan biya muku karatun ku amince kawai Sukace ba komai kuje Ku fada mata kun amince cewar Amal Sukace muje tare suka shiga suka sanar da ita inna taji dadin jin haka sosai Ranar juma'a aka daura auren su Aqeel da Abu Arif da Binta A kan sadaki dubu dari ko waccen su Washe gari ranar asabar Alhaji hajiya Amal Abu da Binta suka kamo hanya suka dawo gida kano Abu da Binta sunsha nasiya a gurin inna da umma Alhaji ya kira su Arif ya sanar dasu batun auren saidai be fada musu kosu waye ba hanka linsu ya tashi sosai saidai baza su iya yiwa mahaifinsu musuba haka Suka hakura Bayan dawo warsu Abu da binta da sati1 akayi bikin gama koyan KWALLIYA girki da dinki da suke koya bayan shekara daya kuma su Abu da Binta suka sauke Al-Qur'ani me girma lokacin yakama suna ss3 suna daf da zana neco da waec ranar Asabar yakama dawowar su Aqeel Arif daga America inda suka dawo da aikin su Nigeria gida ya hargi tseda kanshi dan Binta ce a kitchen tana musu girki Amal na dinka musu kayan da zasu Sa Abu Asibi da kande kuma suna gyara gida gida yayi kyau sosai bayan sun gama komai suka je sukayi wanka Abu ta musu KWALLIYA na azo a gani suka saka kayan da Amal ta dinka musu sunyi yau sosai lokanin suka kira hajiya sukace mata gasunan zuwa gida jirginsu ya sauko Alhaji Nasir ya turo direba yadauko su ya kaisu gida motarsu na shigowa hajiya tayi waje cikin farin ciki take musu Sannu da zuwa koda suka gaida hajiya tace suje suyi wanka su fito basu jimaba wajan yin wanka suka fito a dining suka zauna suka samu hajiya a zaune tana jiran fito warsu Aqeel yace mommy gidan ba kowa ne ina Amal da kucakan "ya'yan ki Bazaku tam bayi matan kuba sai kucakan yarana Mommy rabu da matan nan nina tabbata ko mun gansu baza mu so suba saboda bamu mukace muna soba cewar Aqeel Mommy burina naji abincin nan a cikina zanfi kowa farin ciki jiwani kanshi da yake tashi cewar Arif Aqeel ya bubude komai ya gani "bakarya zeyi dadi sosai bari na zuba mana yazuba musu suka fara ci Takun tahowar mutane sukaji takalmi na kara suka dena cin abinci suka Tsaya suga waye Aqeel a zuciye yace momi waye Wannan yake cika mana kunne da karar takalmi A'a waidame kuka dawo gidan nan ne dagajin karar takalmi sai masifa har yanzu baka canza ba Aqeel Mommy karnayi magana idan andameni kenan cewar Aqeel Arif yace Naji dadi da kauyawan nan basa gidan nan harna fara jin iska na shigata ta ko ina wlh Kai koni ai duk wanda yayi farin ciki bekai ya nawaba nida yaran nan suka kusa hauka tani cewar Aqeel Natau sayawa mazan da zasu aure

Chapter 10 of 12