Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
aibaza Ku yardaba kalli abinda takeyi kamar tasha giyar da gaske Hajiya dariya kawai takeyi Tace zasu sabane ahankali Amal tace Abu zo kici koda kadan ne kinga Binta na ci Binta tinda aka bata ta fara ci saida ta cinye tas ta side hannun tayi gyatsa Tace wahala Abuba dadi da anyi magana suce birni Arif yace ko duk cikin badadin kika side hannu harda gyatsa Komai ai sai an daure nima daurewa nayi ni amai nema yake taso min Amal dasauri ta mika mata lemo tace sha abincin baze dawo ba Binta tace to na gode kece kadai ta kirki a gidan nan saikuma mugaye a gefena ta kalli su Arif Aqeel yace Bakomai sha lemo Abu na gefe a zaune tayi zaman yan bori sai shafa ciki takeyi ta fasa uwar kara Tace waiyoo cikina ana gobara kayan cikina na konewa waiyoo inna yaya Nura zanmutu waiyoo waiyoo Hankalin hajiya Alhaji da amal ya tashi sosai Arif da Aqeel ko a Kansu kukanta da ihuntane ya Dame su Aqeel yace daddy ba wani gobara yunwace kawai jiya tayi zuciya taki cin abinci Amal dagudu ta tafi gurin Asibi Tana zuwa ta samu Asibi tayi Koko da kosai zata kawo musu Cikin fara a Amal tace Wannan nawanene Asibi tace na Binta da Abu nasan sunkasa cin abincin Ku ko Eh bani na kai musu To Gashi barina cigaba da aiki Amal takaiwa Abu Abu na gani ta fara hannu baka hannu kwarya saida taci ta koshi ta ture Hajiya tace Abu ya cikin da sauki goba rar ta mutum Ya bazata mutuba dawani KWALLIYAR ki kamar Aljana indai a gidan nan zaki zauna ina tabbatar miki da cewa saikin dena Wannan KWALLIYAR *'YAR KWALLIYA* kawai cewar Aqeel Abu ta mike ta dunkune hannu tace kawu da alama nunar rana karfi yakeso mu gwada burinka ya cika taho idan ban fasa maka bakiba Arif yace mommy mace kenan fa waida Aqeel zatai danbe tsabar kanta ya kwance Alhaji yace Abu Anan ba a fada da namiji koda wasa karki kuma kinaji ko Takoma tai za manta Aqeel yace mommy yau ki shirya kinada babban baki usman ne zezo tareda kannen Sa maza Kai kace na shirya yaushe rabonsa da gidan nan harna manta Arif yace bakiga yanda ya komaba yan zu America ta an she shi sosai Barinaje gurin Asibi da kaina na musu ba yanin abinda zasu girka Kowa ya watse daga Binta sai Abu a gurin suka kalli juna sukai dariya Suka koma dakin su Abu sai kai kawo ta keyi Binta tace Abu meye wai haka Ki bari kawai shirya abinda za muyi wa bakin nunar rana nakeyi Binta ta tashi ta dafota tace karki damu na shirya komai kixuba ido Kiyi kallo Allah Binta Yasin kowasa babu a maganata Abu ta daka tsalle ta rungumeta tace hiyasa nake alfahari dake Binta ga kayan KWALLIYA muyi kafin bakin su raina mana hankali suka fesa uwar KWALLIYA wanda sukayi yafi wanda sukeyi a qauye suka sa kayanda Amal ta kawo musu jiya suka fito suna tafiya 1 bayan 1amma in akakalli fuskar kamar aljanu Abu tace Binta Tsaya ina zamuje yanzu Binta tace madafa muga abinda aka girkawa bakin Hakane kuma mujeto Suka tafi suna shiga sukaji kitchen din yadau kanshi Su Binta harda hadiyar yawu karar Hadiyar yawun kande taji yasa ta waigowa Abu tace sannunku da aiki komai na tafiya yanda ya dace duk kanhin girkinne haka dankari zasuci dadi Asibi tace Abu Ku Tsaya Anan bari muje mu gyara inda zasu zauna Tana gama fada suka fita To ba komai saikun dawo cewar Abu Sun gama giriki sunzuba sun rufe Binta ta bude 1 takaimai wawa Abu tace ci iya cinki binta kibar sauran kyauta zanyi dashi Binta saida ta Bude kowanne taci iya cinta tazube a kasa cikinta yayi kato tace Abu anya zan iya tafiya daga nan kuwa Meyasa kikace haka Cikin yamin nauyi Karki damu na hutar dake zanyi komai da kaina Abu ta fito ta duba taga bakowa a falo ta fita waje ta tara yara masu yawa acikin su ta samu wani yaro da bokiti ta ansa ta dawo ciki ta juye musu komai a bokitin ta kai musu tace suje su raba yaran nata murna suna ihu megadi na kallon su Abu tace kaima ga naka Megadi Ya ansa yayi godiya Abu ta koma ciki ta rike Binta ta kai ta daki ta kwantar Ta fito Keeee ina zaki cewar Aqeel Nunar rana wasa zanje nayi Dawan nan fuskar naki kalan ki tsorata yara koma daki kije ki zauna karna sake na ganki a waje idan bakina suka zo To duk yanda kace haka za ayi nunar rana na koma ke ina wasa dake bance karki kara fadamin sunannanba ko ajikinta abu tashigeshi tai tafiyar ta yace him lallai ya rannan semun koyamusu hankali a gidan nan Kande da Asibi Suka zo gurin Aqeel Kande tace Aqeel mun gama komai yana kitchen zamu fita yanzu zamu dawo To nagode bakomai saikun dawo Karar parking din mota Yaji yafita da sauri Usmane yazo Aqeel fuska cikeda farin ciki ya rungume shi yana murna Yace sannun ku da zuwa mu shiga ciki To yayi musu jagora zuwa ciki New writer's Hakan Take *husba'ahfama* 🌹🌹💋 👠👠👠👠👠👠 👝👝👝👝👝 👠👠👠👠👠 👝👝👝 👠👠 👝 💄💅 *'YAR KWALLIYA* 💅💄 👝 👠👠 👝👝👝 👠👠👠👠👠 👝👝👝👝👝 👠👠👠👠👠👠 Written by *husba'ahfama* 27-28 Usman kuzauna bari na kira mommy Usman yace To Usman Sannu da zuwa ko nace ba maraba ba kawani kawo katon kanka shikuma harda shirya maka abinci hmm kaci mugani Abu ta fada ta wuce dakin ta Aqeel yaje dakin hajiya yasanar da ita zuwan su Usman Hajiya da saurinta ta fito Manyan baki magana tatabbata Arif yace min ka zama kato Usman yace mommy karki yarda bawani kato dana zama ina nan yanda nake shine kawai Hajiya tace fada kake yi Usman duk wanda ya sanka da ya ganka yanzu yasan ka canza sosai ma kuwa Hakane to mommy ina wuni ya gida yasu Amal Lpy kalau ya karatu ya kowa da kowa Lpy kalau ina Amal din ko tana maka ranta A'a tana ciki zata zo yanzu Kannen usman suka hada baki suka gaida hajiya Ta amsa tace Aqeel ka kaisu dining bari na turo Abu da Amal su zo su jera komai Aqeel yace to mommy ina zuwa ya zauna kusada Usman yace inda nine kai ba abinda zan dawo yi nan zamana kawai zanyi Ko kai meyasa baka zauna ba ina ka rigani zuwa cewar Usman Aini be karbeni yanda ya karbe kaba kuma ni gaskiya bazan iya zaman canba Hmm shine ni kake so na zauna Sukayi dariya Kuzo muje dining Aqeel wai ina Arif tinda nazo ban ganshiba Fita yayi bajimawa ze dawo Ku zauna Aqeel ya wuce kitchen Hajiya dakin su Abu ta wuce ta Bude ta shiga Bacci Abu lpy Binta kalau kuwa Hajiya lpyan ta kalau wlh tsabar jindadi ne Gashi kuma taci ta koshi abinka da kura Abu meye haka bintarce kura Hajiya kenan tinda kikaji nace mata kura kiyarda kwai kurarce inkuma baki yardaba anatare zaki gani da idonki Abu KWALLIYAR nan tayi yawa kirage ta kuje kitchen kudauko abinci Ku jera a dining Su Asibi sun fita Tab harkinsa na tahi narage KWALLIYAR fuskata tab anrabani da tiraren jikina yanzu kuma KWALLIYAR ma hanani za ayi daga ragewa za kuma ace na dena yi A'a Abu ni bazan hanaki KWALLIYA ba saidai yanda kike naki yana yawa hasalima yana canza kaman ninki shiyasa nace ki rage Hajiya ina ganin girmanki gaskiya bazan rageba To shikenan kuje Ku dauko abinci kina fita Za kiga Amal a waje To hajiya natafi Abu na fita ta ga Amal suka wuce gurin su Usman Amal ta gaida Usman Abu ma ta gaida su Kannen Usman satar kallon Abu sukeyi damagana abakin su amma sukayi shiru Usman ma haka azuciyarshi tanbaya yake wacece wannan kai tsaye kitchen Abu da Amal suka wuce Abu ta Tsaya daga gefe tana kallon Aqeel dake waya tana dariya Amal tace bari nadauki Wannan yafi girma kekuma ki dauko Wannan To Abu tace Amal na dauka taji banauyi da sauri ta ajiye ta bude taga ba komai aciki Yaya Ina abincin yake ko ankai dining Bece mata komaiba yadaga mata hannu alamar yana zuwa Ya kashe wayar Yace me kikace Yaya Bakomai a cikifa Yace A cikin me Amal ta nuna mishi da sauri yazo yabude yaga bakomai yabude sauran ma yaga ba komai Ya haka nida kaina naga sun girka abincin amma yanzu babu kuma kansu fitama sunfadamin sungama yanzu ya zanyi da Usman Abu tace Amal waihi waye Usman din Amal tace babban Abokin yayane tare sukayi karatu a America Abu tace hm kekika sanhi sunan garin da kika fada nida bansa ko inaba sai *DARAUDAU* Ran Aqeel ya baci sosai dariya na niyar kwacewa Abu taita dannewa dan karya gano ta Naji dadin ganin ranka a bace nunar rana tukun na ma Abu ta fada a cikin zuciyar ta Amal tace yaya ya za ayi yanzu Aqeel ya kasa cewa komai sai huci yake Abu tace susha ruwa su tafi tinda abincin ba dole bane dama duk Wannan aboki akayi wa girkegirke haka Nina dauka sarkine ze kawo muku ziyara ruwanma karku baso tinda gidan bana gyatimi bane A fusace Aqeel ya juyo yana huci shi tinda yazo gun bekula da itaba se yanzu mur yarta Yaji sai lokacin yasan tana gurin ya zari shar bebiyar wuka tana kyalli yabi Abu dashi Dagudu suka wuce su Usman Amal na binsu a baya sukayi dakin hajiya Gudun da taji yasata saurin mikewa tace lpy Aqeel mezan gani haka Yace hajiya matsa ki bani ita ina abincin da aka dafawa su Usman babu shi ita kadai tasan inda ta kai shi Abu tace hajiya karki yarda da abinda zece wana tabbaci yake dashi na cewa nina boye abinci Inni naboye abincin ina nakaihi Yace mommy ita kadai ce zata aikata haka Nina sani Abu ta fito daga bayan hajiya tana murguda baki zatayi magana Aqeel ya dauketa da mari Abu ta gigice takurma ihu ta zube kasa tana birgima Yaya meyasa meyasa ka mareta kome ta maka ka dinga hakuri mana cewar Amal Yimin shiru yadaka wa amal tsawa kema yanzu nahada dake nakula tinda sukazo kike goyan bayansu bakyaso aimusu fada kuma kina ganin irin abin da sukeyi bedaceba Hajiya tace Aqeel karka sake dukanta kome ta maka ka sanar dani ni nasan mezan mata Amma mommy Tadaga mishi hannu tace ya isa bana son jinkomai kanta karasa maganar ta tuno maganar da Abu tace mata Binta kurace taci ta koshi Waiyoo Aqeel temako zoka temaka ka dauko Binta mukaita asibiti Abu karkicemin duk yawan abincin nan ita ta cinye Hajiya Nifa ba tsoran nunar rana na keyiba maganar gaskiya hine Binta taci iya cinta sauran kuma na rabawa mabu kata Mommy kina jiko kinajin abinda take cewa Wlh zan karkarya yarinyarnan Nidai Aqeel yar mutane katemaka mu kaita asibiti To naso ace ke kikaci ba ita ba saidai dani kike magana Yafita daga dakin rai abace Arif ya shigo hannun shi dauke da leda guda2 Aqeel dasauri ya karasa gurin shi yasanar dashi abinda Abu tayi seyai murmushi yace Nasan wani Abu me kamar haka ze faro tinda na gane cewa indai ta fadi Abu saitayi yasa na ke fadada tina Nina karka damu ga Wannan nabi ya na siyo abincine masu dadin gaske Kai naji dadi Amma hakan baya nufin na hakura dan yau raina ya baci sosai Yace karka damu muma zamu hukunta su Su kayi dariyar mugunta Arif yaje suka gaisa da Usman Aqeel ya jera abincin da Arif ya siyo Aqeel ya fita kunyar Abokin shi dan Abincinda Arif ya siyo kamar a gidansu akayi Saida yamma Usman da kannan Sa suka tafi Lokacin ne Aqeel ya maida hankalin Sa ga Abu hukuncin da ze mata kawai yake Tina ni Aqeel Tina ninme kakeyi haka Kabari kawai Arif zo muje Arif yabi bayan shi suka tafi kitchen sukaje Arif yace me za muyi Anan Zuba ido ka gani Aqeel ya Dora ruwa yana ta fasa yasa taliya yana laushi kadan ya sauke ya kwashe yasa miya Aqeel yace nagama mu tafi To amma ka hada mata da giyarta ta dazu Haka ne jeka dauko ka sameni a kofar dakin su Arif yace to yaje ya nauko lema yanufi dakinsu Binta Atsaye a kofar dakin yaga Aqeel Aqeel na ganin Arif yazo yabude dakin ya shiga bacci kawai Abu da Binta sukeyi han kali kwance Arif da Aqeel sukayi dariyar mugunta Arif ya tsaya a bangaren da binta take Aqeel ya Tsaya a bangaren Abu Atare suka daga hannu suka Kai musu duka me shiga jiki a gigice suka mike suna ihu Aqeel ya daka musu tsawa Suka yi shiru suna kallon su Arif Arif yace kun kyauta a binta kukayi kunbirgeni sosai Ku zonan Binta tace nan ina muyi me kuma banda Wannan cin zalin da kuka mana Aqeel rai ahade yace cinzali ko to bari namuku dukan kawo wuka muga abin da zaku kira Wannan kuma Abu tace nuna karmuyi haka mana bari muzo Agabanshi so ka Tsaya Aqeel yace ku zauna a gaban kwanan dana kawo To sukace sukayi kamar yanda yace Arif yace Ku Bude kuci Binta tace dandai ci gidan kazo ta Bude kwanon tana ganin abinda ke ciki tasa kara Aqeel ya zaro wuka yace kokiyi shiru kona caka miki ba ina nufin hakan zan farayiba saina fara gunduwa gunduwa daku tukun na Binta ta rufe baki Abu tace nunar rana bama cin sutsa fa kukawo mana wani abin banda Wannan yai dariyar mugunta Arif yace Ko lokacin da kuka rabar da abincin kunyi shawara dani Abu ta girgiza kai alamar a'a Aqeel yace Yauwa dan haka Ku cinye sutsar nan gaba1 banaso naga komai a cikin kwanan nan Baza mu iyaba harni har kwada yina ban taba cin sutsa ba yasin cewar Binta Balle ni Abu bazan iyaba dan Allah kuyi hakuri Aqeel yace Hakuri Sam bazamu hakuraba har sai kun cinye sutsar nan gaba1 ya daga wukarshi yana sha fawa To za muci Abu ta juya kai tasa hannu ta debo taliya jitayi yana mata motsi a hannu ta zubar dashi Aqeel ya hade rai yace 'YAR KWALLIYA kinjawa kanki bayan kuncinye taliya ga lemo kushanye shi tas shima Giya dan Allah kayi hakuri malam Rabi'u yace ba kyau shan giya fa Tinda kika kirashi giya kekadai zaki shanye cewar Arif Lokacinku ya fara daga yanzu inba Ku cinyeba ga Aqeel a kusa dani Aqeel ya daga wuka ya nuna musu To shi kenan zamuci haka Abu da Binta suka rufe ido suna cin sutsa ta bakin nasu Suna hawaye serige ciki suke kamar zasuyi amai New writer's Hakan Take *husba'ahfama* 🌹🌹💋 👠👠👠👠👠👠 👝👝👝👝👝 👠👠👠👠👠 👝👝👝 👠👠 👝 💄💅 *'YAR KWALLIYA* 💅💄 👝 👠👠 👝👝👝 👠👠👠👠👠 👝👝👝👝👝 👠👠👠👠👠👠 Written by *husba'ahfama* 29-30 Harsuka cinye Abu da Binta sai rike wuya sukeyi Arif yace kun gama da Wannan saura lemo Gaskiya Ku barmu haka Aqeel ya wasa wuka Binta tace Abu yi shiru bamu Arif ya zuba ya basu Suka ansa suna sha Binta Kura kyaci da Gashi tana sha taji dadi ta kafa kai ta shanye ta mika mishi Kofi Arif yace Me zanyi dashi Tace Wani zaka zuba min Arif ya zuba mata takuma shanyewa ta miko mishi Kofi shikuma yabata gaba daya ta ansa tashanye Binta tace bawani Ku karo min Yasin giyar badai dadi ba wai kaf qauyen mu idan za a zagaye bana tinanin za a samu ya Wannan Arif da Aqeel suka kalli juna Aqeel yace ke harkin shanye Abu tace Eh na gama tafada tana hawaye Aqeel yace Yauwa ita dai waccan wani hanyar zamu sake dan na kula Wannan kura ce yanuna Binta Kiran salla sukaji suka mike zasu tafi masallaci Aqeel yaga su Abu ba a daniyar tashi kwanciya ma suke shirin yi a gurin ya daka musu tsawa yace meye haka bakuji kiran sallabane kuke shirin kwanciya Abu tace munyi tin a *DARAUDAU* ba a binmu bahin salla zaro ido sukayi atare suka hada baki sukace mekukace sukace mun shiga UKU Akwai bamban aiki Arif cikin mamaki ya dawo ya zauna yana fukan tarta yace ban ganeba Binta tace sallar sati1 muke hadawa muyi a rana1 kaga sauran ranakun mun huta Ku kuna salla mukuma muna hutu ta fada tana dariya Aqeel yace hauka zalla bana tinanin kan yaran nan a kwai kwakwalwa wlh kai kaji wani Abu ko yaro bazeyi shir mannan ba Arif yace kuna zuwa islamiya a qauye Abu tace muna zuwa malam rabi'un ne dan rainin han Kali Abu kadan duka hine muka dena zuwa ban fada makaba har bokoko a wuta munyi sau1 mukaje shima ya raina mana hankali muka hukuntashi bamu sake komawaba sai gamu a barni tafada tana dariya harda tafawa Aqeel kaji magana gangariya nakula jahilcine kawai yake dawai niya dasu amma komai yazo karshe Aqeel yace shi malam rabi'un ne ya ce Ku dinga hada sallah A'a mune mukaga hakan yafi dacewa saboda bamuda lokaci zama muyi akan lokaci saboda dasafe mu debo ruwa darana naraka Binta tallar gurjiya da yamma muje dandali tafada tana rawa Aqeel ya kalli Arif yace a kwai matsala ke dena mana rawa ko kinji kidane nibana tinanin kawunan yaran nan zasu dau karatu Arif yace koma meye sunan Ku ban damu na saniba kutashi kuyi Alwala kuyi sallah yanzu sannan Ku sani ba a hada sallah kowacce ana yinta akan lokacinta kunaji Allahu'akubar kaji malamai munji kuma mun gane zamu gyara wai bazaku kaimu dandali bane natara rawa masu yawa Ku kaini na juye yanbirni su gani su sani mu yan qauye hmm tatashi tana rawa Aqeel yace yarin yarnan a bace take bata gane komai zomuje masallaci kaga har an tada sallah Suka tafi sukabar Abu na rawa binta na zaune tana shafa ciki Binta tace Abu zoki rakani gona nayi kahi sunan basuda shadda Gashi a matse nake waiyoo Abu ta dena rawar da take cikin mamaki tace binta kefa ki kace yan birni basa kahi ya haka kuma keza kice na rakaki gona Kinga su wayanda aka Haifa a birni nake nufi banda mu kinga aimu zuwa mukayi ko eh hakane kinga yanzu yamma tayi kihiga inda aka yi mana wanka ina randar nan ta ruwa Wannan farin Binta tace Eh na ganeta Kije Kiyi a ciki Abu ba komai bakomai jeki na Tsaya miki Binta ta shiga tayi ta fito tana rike ciki tana yamitse fuska Abu hanci a toshe tace Binta duk warin kahin kine haka kamar mushe Bana son wula kanci lafiyace da bani dashi bazan yiba Amal ta Bude ta shugo tana shigowa warin ya daki hancin ta tace meye haka warin meye Wannan Binta tace ji wani Abu da takeyi kamar bata taba yin kashi ba wayasanima ko naki yafi nawa wari Amal tace a ina kikeyi Binta tace shiga nan ta nuna ban daki zakiga randar ruwan nan a ciki nayi karki damu sanda na Debi ruwan tsarki a randar tukunna nayi Randa Amal ta mai maita cikin ban dakin tashi ga tasamu binta batayi shirmeba korawane kawai bata yiba ta kirata ta nuna mata yanda akeyi Abu tace Tab saura kiris mu fita waje Neman Gona da zatayi a can Ashe Gwanda da bamu fitaba da munsha wa halar Banza Shiyasa nace kome kuke so Ku tam bayeni To ai mun gane yanzu kuma Bari naje gurin mommy ina zuwa Tabude ta fita su Aqeel ta samu a dakin Aqeel yace mommy gaskiya a nemawa yaran nan malamin da ze dinga koya musu karatu a gida idan suka fara hankali a kai su makaranta Arif yace mommy yaran nan naki da girman su hada sallah sukeyi Hajiya tace Eh hada sallah bangane ba Aqeel yace hmm dazu suka fada mana waisu sallar sati1 sukeyi a tare rana kunda zezo kuma sun huta Hajiya tace tab Allah ya rufa asiri yakamata musamo musu malami yanzudai malamin da ze dinga koya musu Qur'ani da sauran littattafai na addini shine malam kabiru dama shiya ke koyawa Amal Arif yace hakan ma yayi idan suka ga amal kila su zauna mommy boko fa Eh to Wannan dinma kabiru ze iya koya musu tinda tsohun malin makaranta ne Arif yace to mommy zan Kirashi na sanar dashi daga gobe zasu fara inba hakaba abin nasu lalacewa ze karayi Hajiya tace yauwa Aqeel idan malamin yazo kuja musu kunne karsu yiwa malamin halin nan nasu dan naga suna tsoron ku sosai Niko yakayi da Usman duk kunya ta hanani fitowa koda muke Salama Akunyace nake wlh Aqeel yayi dariya yace mommy Arif ya findake kunya shiya siyo abinci ya kawo bazama kice a waje aka yiba kannen Usman sunce suna godiya da yautar da kika musu Alhamdulillah amma naji dadi Allah ya muku Albarka Ameen mommy tafiyar mu zuwa America na kara matsowa fa Hakane fa harna fara kewar Ku Mommy karki damu ga *'YAR KWALLIYA* da *KURA* za su debe miki kewa suka fada suna dariya Hajiya tace yaran nawane kuraye lallai inajiye muku wlh ranar jinkunya musammanma Aqeel kafi kushe su Tab indai wayan nan ne ranar bazata zoba nida zan dauko miki sirika a America me zanyi da wata yar qauye Allah yaya to shi kenan zamu gani cewar Amal Mommy saida safe mu zamu tafi Allah yatashe mu lpy Washe gari da safe Abu ko karyawa basu yiba suka fice daga gidan Abu na tafiya tana mita Kai dan Allah ki Tsaya Abu mitar me kikeyi Binta tinda mukazo basu kaimu sun nuna mana gariba sun barmu a guri1 sannan gasu nunar rana gidan ma ba dadi ko dandali basu kai muba Binta tace shine abin damuwa to ba Gashi mun fitoba muga gari iya san ranmu daga nan muje muga dan dali Hakane kuma saida

Chapter 6 of 12