Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sukayi tafiya me tsawo sukayi nisa da gidan sosai Duk wanda ya gansu mamaki yakeyi ganin KWALLIYAR dake fusko kinsu duk wanda ya kallesu baya karawa Abu ta jabe a kasa tace daga nan babu inda zani Meyasa Saboda yunwa nakeji indan banciba bazan iya tafi yaba To bari naga ko zamuga abin siyar wa Wata yarinya ta wuce ta ga bansu tace zaku sai waina Binta tace waina Abu kinji waina tab shegu yan birni nasani ai duk abinku saikun hada da qauye sauke mu gani Yarin yar ta sauke sukace na nawa ne a ciki Tace dubu1 Abu tace Yarinya kingama ciniki yidari Yarinya tayi dariya Abuda binta suka Sa hannu a robar waina suna ci Can gida kuwa ne mansu kaiwai a keyi suzo suci a binci gashi kuma malamin da ze koyar dasu yazo Amal tace yaya Aqeel bangan subafa Baki gansuba kamarya ina zasuto cewar Arif Amal tace nima ban saniba Hajiya ta daga hannu sama tana cewa Allah kasa muga yaran nan Allah kakaresu a duk inda suke Aqeel yace mommy dan Allah karki damu zamu nemo su duk inda suke bari mu tam bayi me gadi koyaga fitar su Dukan su suka je gurin megadi Arif yace kaga fitar kannen mu guda2nan da sukazo Eh nagani sunce min suntafi bude ido Alhaji yace Bude ido kai Arif Aqeel kuzo muje Neman su Aqeel rai a bace yacewa megadi tin yaushe kake aiki a gidan nan dasuka ce maka haka saika zo ka tam baye mu kafin ka barsu su fita Ayi min Afuwa insha Allahu hakan baze sake faruwaba Arif yace daddy karka damu kukoma ciki zamu nemosu da kanmu mu kawo su Amal tace yaya zan biku Arif yace taho mu tafi Hajiya tace saikun dawo Ku kula da kanku idan kun gansu Ku kira Ku fada mana To mommy Me gadi ya bude musu suka fita Neman su abu Saida su kaci suka koshi sukace taje ta siyo musu ruwa da kudinta tajeta siyo ta kawo musu suka sha Alhamdulillah Allah na gode maka yanzu naji dai_dai dauki wai narki ki tafi Allah ya kawo ka zuwa Yarin yar tace kubani kudina saina tafi Binta ta kaiwa yarin yar duka tace rashin kunya zaki mana bazamu biya ba Kiyi abinda zakiyi New writer's Hakan Take *husba'ahfama* 🌹🌹💋 👠👠👠👠👠👠 👝👝👝👝👝 👠👠👠👠👠 👝👝👝 👠👠 👝 💄💅 *'YAR KWALLIYA* 💅💄 👝 👠👠 👝👝👝 👠👠👠👠👠 👝👝👝👝👝 👠👠👠👠👠👠 Written by *husba'ahfama* 31-32 Yarin yar tace hakama zakice wlh Baku isaba duk abinda kuke takama dashi Nina fiku bala'i yanzu zan dakeku na daki kudina na kaiku gurin yan sanda Binta tace Ko to bisimillah mafashi keda kinsan komu suwaye tsayawa ma baza Kiyi a nan ba Yarin yar ta kai wa Abu duka Abu rai a bace takai mata wani mugun naushi saigata a kasa Abu da binta suka rufar wa yarin yar sukai mata duka Abu tace Banza a banza kemu zaki nunawa taurin kai hmm Allah ya temakeki mu kara haduwa saina zubar da hakwaran bakin ki Yarin yar kuka kawai takeyi danta daku bakadan ba Allah ya isa kuma saina turo muku yayana ainaga gidan da kuke Shegiya wato binmuma kikeyi ko kufa yan birni kunada matsala Yasin sa ido ya muku yawa Wannan KWALLIYAR ne Baku taba ganiba Niba KWALLIYAR Ku nake ganiba a bayan layin Ku gidan mu yake zakuga gatana cewar yarin yar Binta tace kafin muga gatanki bari mubaki ladan gida sukai mata dukan tsiya ko tashi ma ta kasa Abu tace barta haka mu koma gida sai anjima kuma zamu kara fitowa To mutafi Arif yana tuki yana waige ko ze gansu duk sun baza ido suna duba hanya ko zasu gansu Abu da binta sukazo zasu tsallaka titi Abu kaitsaye ta tafi ko hanya bata duba ba motar su Arif ya taho da gudu ganin Abu da yayi yasa shi taka birki cikin sauri ya Tsaya Aqeel ya Bude ya fiyo ya kaimata mari Abu ta gigice ta rasa inda zatasa kanta Binta kura batama san anayiba me karas tagani yazo wucewa hanka linta ya koma gare shi Arif Azuciye ya fusgota ya kaimata mari Gigi cewa tayi Tana cewa gatan naki kenan badai kince abayan layi kikeba har gidanku zamu Yasin mudake ki Jin haushin Abinda take fada yasa Arif ya kara marinta sai lokacin tagane wanda ya daketa Ta fashe da kuka Abu ma kukan takeyi dan itama saida ta sake shan mari Amal takasa cewa komai kallon su kawai ta keyi tana kuka Arif rai a bace yace Bakida hankali waya gaya miki haka ake tsallaka titi da kuka fito me kuka fito yi wakuka fadawa da zaku fito ke kuma kura daga ganin A binci hankalinki yatafi dayanzu bamu bane wani dabanne yabita kanta ya wuce kiceme baki ganiba ko bakya gurin Aqeel yadaka musu tsawa yace su shiga mota Da sauri suka shiga suka zauna har lokacin basuce komaiba kuka kawai sukeyi Arif ya kira hajiya ya sanar mata sunga Abu da Binta hajiya taji dadin jin hakan Arif fada kawai yake musu har suka isa gida Amal da gudu ta tafi ta fada jikin hajiya tana kuka Hajiya tace me kuka mata take kuka Aqeel yace meze sata kuka inban da taba yaran nan da mukayi saboda ita kenan kar a musu fada idan sun yi laifi Mommy dana sani ban bisu ba suna sane suka tafi dani dan su dakesu a ga bana nima tsoran su sukeso naji kuma naji tsoran naku Amal ta fada tana kuka Hajiya tace Amal dolene Amusu fada idan sunyi laifi basuba harda ke kema yaiyan naki suna so su Abu su dena abinda sukeyi shiya Sa Amal ta goge hawa yan fuskarta tace hakane to shikenan nina dauki nauyin gyara su Binta zasu dena duk abinda sukeyi insha Allah Tana gama fada ta wuce dakin ta Arif yace Lallai indan baki gyara suba su Sa koya miki hada sallah da rashin wanka wayan nan yaran kuma hmm Hajiya taiwa su Abu fada sosai fadan yashige su sukai mata Alkawarin cewa bazasu sake ba 🤔 bari muga ko Abu da binta zasu iya cika Alkawarin da suka dauka🙄 Hajiya tace kuje kuci Abinci kuyi wanka malamin Ku yazo Atare sukace to Suna tafiya suna hararar nunar rana Kwafa Aqeel yayi yace mommy duk sanda me KWALLIYAR Aljanu ta fado hannu na hmm ina tausaya mata Hajiya tace yara ne sai hakuri Amal na dakin Abu da Binta rai a hade sai Kada kafa takeyi Sukazo zasu wuceta Amal tace Ku Tsaya a koda yaushe ina zuwar muku da sauki saboda Ku ba kine amma kun kasa ganewa ko to shikenan daga yau Anan tafiya ta daku ta canza salo muguwace ni banida kyau idan raina ya baci Binta tace tomu ina ruwan mu canta matse miki Amal ta daka musu tsawa tace haka kuka ce ko naji dadi kushiga kuyi wanka ko kuma ta zira hannun ta karkashin Gado ta Ciro wani shar beben kara tace idan na fara zaneku dashi saiya karye zan barku Abu ta matsa kusa da binta take rada mata tace gaba daya yan gidan nan hawai niya ne kinga itama ta canza Binta tace ya za muyi yanzu Abu tace muyi abinda tace dankuwa bada wasa take ba Amal tace kun gama shawara Suka daga mata kai tace dakyau waze fara shiga Abu tace binta Binta tace Abu Amal tace ya isa nida kaina zan zaba Abu shiga ki fara yi kuma ki tabbatar kin goge baki Tsaya nafasa bari nakira Asibi ta Tsaya a kanku Abu tace A'a karki kirata zamuyi tin rikon da tamin rannan haryau gurin zafi yake min To shiga ki fito Abu ta shiga tayi wanka ta goge baki tafito Binta ta shiga tayi ta fito dariya na kokarin kwacewa Amal ganin yanda suke tsoran ta saidai Ta dake taki dariya Tabasu mai su shafa suka shafa suka dauki kayan da suka cire zasu maida Amal tace mezan gani haka kayan zaku mayar sunyi datti gawasu kusa wayan can kuma za a kaisu wanki Tab gaskiya a'a jiyafa muka sasu mudai kar a wanke mana muna sansu a haka to ko kayan mu se sunyi wata kafin mu wanke balle sabin Kaya hikuma saiya hekara Ya isa Wannan a qauye kenan nan kuma birni ne dan haka kuyi abinda nace kafin raina ya baci Haka suka dauki wanda ta basu suka Sa badan ransu yaso ba Tace muje kuci abinci Munkoshi baridai muyi KWALLIYA Eh banyarda ba haka nake son ganin ku kuwuce muje malam kabiru na jirani mu Abu zatai magana amal ta kafeta da idanu ganin haka yasa tai shiru har suka karasa gurin malam a waje suka ajiye mishi kujera sukuma suka zauna a tabar ma Malam kabiru ya Bude Qur'ani yafara karan tawa Amal ce kawai take jinshi Abu da Binta hankalin su na wani gurin ji sukai garin ba dadi Arif da Aqeel suka fito suka zauna gaba dasu kadan suna ganin su Abu da Binta ganin su Aqeel yasa suka maida han kalin su gurin malam Haya niyar me gadi da wasu mutane da basu san kosu wayeba Arif da Aqeel suka jiyo Arif yace malam karka damu zamuji da komai kucigaba da karatu Lokacin mutanen suka tunkude me gadi suka shigo Arif yace lpy kuka shigo mana gida Tan gadi yakeyi hannun shi rike da taba Yan ra konsa na mai busa da kirari Kanshi sai fasuwa ya keyi Yana tangadi yace ina suke Aqeel yace qaura meya kawoka gidan mu qaura yace daliline ya kawo ni kubanisu na fidesu harni qaura za a samu wayanda zasu budewa qanwata idon da raina da lpy ta yakarashe maganar yana layi Dan koranshi yamishi kirari qaura ya zaro wuka yana gogawa a jikin shi Aqeel yace qaura ban gane abinda kake nufi ba fa qaura yace qanwata ce ta tafi talla wasu daga gidan nan suka mata A kuya kotashi bata yi Haya niyarda hajiya da Alhaji sukaji yasa su fitowa Hajiya tace ba a gidan nan ba kasake tam bayan ta qaura yace Na tam bayeta saboda me bayan qanwata bata karya Alhaji yace idan a nanne to waye qaura yace yeeeehu harni za a kawowa rainin hankali aiya maza jada baya ga rago ba tsoro bane yanzu zanyi fata fata da mutum na kwana lpy Abu da Binta suka taho gurin Suna kallon qaura yana yiwa kanshi kirari Abu tace qaryar banza kaje an disashe kaifin wukar kazo kana mana burga dashi mune nan muka daketa me zakayi qaura yabude ido yana kallon Abu da Binta yace gaskiya bintu ta badani wayan nan dabefi ta murde musu kaiba amma ba komai Ya sun kuya yana saita wukar ya saito gurin su Abu da Binta Arif ya Tsaya a gabanshi yace qaura a'a karmuyi haka dakai wayan nan bakine fa Ina ruwa na kabarni na fedesu Susan wadda suka taba Alhaji yace qaura kayi hakuri muje naga yarin yar na kaita Asibiti Abu tace Kawu tsimina na tahi dan'uwar makocin kishiyar kakan su binta qaurane ya jika ya bamu mu bama rike wuka ko gora namu salon na da banne matsa ka gani Nanfa Alhaji hajiya Aqeel Arif da Amal suka shiga ba qaura hakuri qaura yaki hakura Arif yace shi kenan gasu nan na bar ka dasu Binta ta Ja da baya tace kawu matsa karma ya hakura abinda nake jira kenan Suka sun kuya Suka debo kana nan duwatsunda aka baza a filin gidan suka fara jifan qaura da muta nansa tako ina daga me fashashan baki saime goshi a fashe Koda qaura da mutanan Sa suka ga Abu da Binta na ji musu jiwo nan fa suka Sa gudu kofar ma ta musu kadan qaura da yake a bige nanfa ya watsa ke yana gudu har waje Abu da binta Suka rakasu da jifa New writer's Hakan Take *husba'ahfama* 🌹🌹💋 👠👠👠👠👠👠 👝👝👝👝👝 👠👠👠👠👠 👝👝👝 👠👠 👝 💄💅 *'YAR KWALLIYA* 💅💄 👝 👠👠 👝👝👝 👠👠👠👠👠 👝👝👝👝👝 👠👠👠👠👠👠 Written by *husba'ahfama* 33-34 Ko da Abu taga sun tafi tasa ihu Hankalin kowa ya dawo kanta Tace saini Abu yar gidan Inna karwar yaya Nura saini Abu me qanhin da babu irin hi saini Abu kawar Binta gagare sarkin kwadayi kura kyaci da gahi Kai Abu cin fuskar naki harda ni nice ma kura Abu tace karkiga lai fina tsimi nane ya motsa kome nayi bana cikin hankalina yeeeehu saini qadan garen bakin tulu akarni akar tulu abarni na bata ruwan tulu Binta tace wayace damu bamuba muma muce dashi bashiba Aqeel yace daddy mata kenan fa kalli wana jahilin ne ze kwashi Wannan qaura fa suka kora Alhaji yayi murmushi yace Zasu de na insha Allah Amal tace yaya kune kuka yiwa qaura wata fassara ta daban kuma abin ba haka bane qaura ragone na bugawa a jarida yan Koran sane masu karfi kuma suma bakoda yaushe ba dankuwa dasunga anfi qarfin su sai gudu basa tsayawa Hajiya taceTab amma anfadi ba nauyi qaura yayita birga a unguwa Ashe duk bogine dan iskan karya ne Arif yadaka musu tsawa yace su rufe mishi baki suwuce suje su cigaba da karatu Suka tafi fuska ba walqala Alhaji yace Nina kasa cewa komai Arif zoka rakani gidansu qaura Eh Alhaji me nake ji kana kallon abinda Abu da Binta suka musu shi ne zaka gidan ka bari dai sai gobe shima idan qaura baya nan To shi kenan Allah ya kaimu SU WAYE Aqeel da Arif Abdussamad Aqeel Abdulmalik Arif Yarane nutsatsu kamu lallu sunyi karatu a America a yanzu haka suna Aiki a America hutu suka zoyi gida miskilaine su basosai suka fiya dariyaba kuma basa son raini basa son haya niya sunada saurin fishi Aqeel baya iya boye fishin shi Arif kuma yana boye fishin shi Arif da Aqeel sun yanke shawarar cewa matan da zasu aura dole su zama yan2 masu irin halin su basa son mace me surutu da rashin kamun kai shiyasa basa shiri dasu binta A yanzu haka basuda matar aure suna dai dubawa sune na nafari a gurin Alhaji Nasir sai Amal autar su Malam kabiru na karatu Abu ta daga hannu Tace malam inada tam baya Yace Allah yasa na SANI Tace kama sani cewa nayi a ajiye karatun a kama wani kawani zaunar damu kana mana karatu kamar munje masallaci Binta tace kema dai kya fada sukinsan An kwankwadi karatu bakiga ko hutawa baya yiba Amal ta kalle su sukayi shiru Malam yace to mun Ajiye karatun Qur'ani sai gobe idan kuka kawo na yau sai a kara wani Malam ya shiga yi musu wa'azi Abu da binta sukayi shiru kamar ruwa ya cinye su wa'azi yake musu akan sallah da tsafta suka nutsu sunaji harya gama Yace antashi yau sai kuma gobe Abu da Binta jiki a mace suka kasa cewa komai Amal ce tace Allah ya kaimu suka tashi suka shiga gida dakinsu suka wuce Abu tace na kasa hakura Binta ni nunar rana ya mara saboda wani Abu da be taka kara ya karya ba tace naki kika gani bakiga irin Marin dana shaba dan kawai nabi me karas da kallo Abu tace haka zamu barsu Tace injiwa ramuwa ya zama dole ai tsaka ninmu da nunar rana ba yafiya Abu tace naji dadin jin haka nadauka zakice mu hakura wa'azin malam ya shigeni saidai bazan iya yafewa nunar rana ba Binta tace yanzu za a kira sallar juma a idan suka fito zasu tafi kizuba ido Kiyi kallo Allah Binta Nice fa kema kinsan komai basena fada ba Hakane sekinyi kai Abu komai naki yayi matsalar ki1 rak kwadayi shine kawai matsalar ki Au dama saboda ki zageni kika kodani to shi kenan nafasa Kiyi da kanki Haba Binta ni dake ba yar haka taso muje naga Abinda kika shir ya Binta ta mike Suka fita kitchen su kaje Binta tace natab bata yau manyan Kaya zasu Sa dan haka muna bukatar manja Allah qawata ko Anan kika Tsaya na gane inda kika do Sa saidai ina tsoran shan mari Kinji ai tsoro ya miki yawa Abu kinga ki faki idon Sa ki shiga ki zuba mai a kaya nikuma nasan yanda zanyi nawa Gaskiya hakan be kwanta minba Binta ki sake min wani To shikenan biyoni Binta da manja a hannu Suka fito Amal suka gani ta nufi Sa shan su Arif Da sauri Abu tatsaya a gaban ta Amal tace lpy Lpy bana son ganin ki kina aiki Amal Wannan na waye Lemo ne yaya Aqeel ne yace na kai mishi yasha kanya tafi masallaci Abu da Binta suka kalli juna sukace da kyau Amal tace da kyau kamar ya ban ganeba Abu tace gurin su za mu basu hakuri akan abinda mukeyi ko zaki bani na kai mishi Amal tayi dariya tace meze hana gashi kukai Nina koma ciki To suka ce Amal na tafiya Suka sheke da dariya suka tafa hm baki san Meyeke faruwaba Binta tace kinga nizan Tsaya Anan keki shiga To Abu tace harda sallah Marta ta shiga Tace ga shi inji Amal Kallon banza ya mata yace ana aiken mutane tana aikomun wata halitta ita ba mutum ba itaba Aljanba Shigo ki ajiya Bazan iya shigowa ba Azuciye ya taho ze ansa itama ta taho tana kara sowa ta juyar da kofin lemon ya zube a kayan shi daya gama shiryawa Abu ta fara kukan karya tace Yazube yanzu me zanje na cewa Amal Cikin takaici Aqeel yace nida kika batawa kaya bakya tani sai wata Amal Batace komai ba ta fita tana kukan karya Aqeel takaici ya ishe shi Zuwa tai gurin binta tana dariya Binta tace yi shiru karya jiyomu muje daki Suka tafi Binta tace nasan zasu kawowa hajiya kara lokacin zanyi nawa zokiji Binta ta radawa Abu yanda zatayi a kunne Sukayi dariya suka Tafa bajimawa Arif ya rako Aqeel gurin Hajiya Lokacin Abu ta biyo Binta da gudu suna tsere tana karasowa gurin Arif tayi kamar zata fadi ta juye mai manjan hannun ta a Kaya Abu kinga laifin kiko meyasa kika biyoni da gudu yanzu kinga abinda yafaru Ni laifi nane kenan karyar banza bawani kece da laifi Binta tace Kece ba niba Abu tace Kece baniba Binta tace Lai fin kine Abu tace Nakidai Arif ya daka musu tsawa yace karku sake magana laifin kine ko nata be sha feniba kinsan me yanzu zanje na cire na kawo muku kuwan ke Abu ta kalli Binta tace wanki Bakomai kawo zamu wanke Abu tace haka bari na bika na anso Aqeel Yace Arif wayan nan zakaba wankin riga kafella musu mari kamusu dukan tsiya a wuce gurin dan gaskiya ban yarda da yaran nan ba Binta tace karka damuda nunar rana dan bakin cikine idan katashi kawowa ka taho da nashi Arif yayi dariyar mugunta yace zanbaku bari na Ciro kuwanke ya fita tas Yakarasa magana yana kallon Aqeel Aqeel yace duk Abinda ya biyo baya ba ruwana karka nemeni To naji Arif ya tafi Aqeel yabi bayan shi Abu da binta dariya kawai su keyi Binta tace Abu yakika gano rigar nan a hannunmu Kibari kawai harna kasa jure wa nakagu sukawo hmm Allah yasomu dan hana ruwa gudun nan be rinjaye shiba Arif ya taho yana dariya yace Gashi harda na Aqeel kuwanke Ku goge mun tafi masallaci A dawo lpy suka ce gaba dayan su Suna fita Abu da Binta Suka ajiye kayan a kasa suna tsalle akai saida suka gaji suka zauna Abu tace hifa nunar rana jiyake da kanhi jihi fari tas koda yake yan gidan ma haka suke Tace jankosai zakice duk abinshi munzama ciwan ido mu i na ruwanmu ma yanzudai yaza muyi da kayan nan New writer's Hakan Take *husba'ahfama*🌹🌹💋 👠👠👠👠👠👠 👝👝👝👝👝 👠👠👠👠👠 👝👝👝 👠👠 👝 💄💅 *'YAR KWALLIYA* 💅💄 👝 👠👠 👝👝👝 👠👠👠👠👠 👝👝👝👝👝 👠👠👠👠👠👠 Written by *husba'ahfama* 35-36 Abinyi shine muwanke kamar yanda suka ce amma karya fita Ko to shikenan mu tafi Suka tafi suna Jan kayan a kasa har suka karasa dakin su ban daki suka wuce suka zube kayan a kasa Abu tace Nifa banga sabulun wankiba gadai bokiti Anan Binta ta yamitse fuska tace Nifa dadina dake qauyan ci su basa amfani da sabulu ga abinda suke wanki dashi ta nuna hypo da bula Haba tab sufa yan gidan nan badai karyaba yanzu meye aibin sabulu da basa amfani dashi Binta tace waya sani kila suna son su bambanta kansu da mu yan qauye miko bokitin Abu ta miko suka Sa kayan a ciki Binta ta dau hypo Abu ta dau bula Binta gaba1robar hypo ta juye a kayan Abu ma kwalin gaba1 ta juye na bula a kayan gashi kayan Ja

Chapter 7 of 12