Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
rai ai duk abinda ya sameni kaine sila saida nace ba fadan da zanwa Binta da Abu kace kaisam saina musu gashi abin daya jamin dagir mana da komai na yanko ta cikin unguwa da gudu kowa na kallona Yanzu binta da Abune sukai maka haka a garin nan cewar me gari Liman yace hmmm ni nasan su sarai shiyasa tin farko naki kadage kace sainayi yanzu gurin saukarma ba halin zuwa ta kona babban rigar sukuma wayan nan kaga dai yanda tai musu harda manja a jiki kamar za a Kada miya gashi badamar na koma gida yanda ranta yake a bace Kai kutashi kuje Ku ne mo min su A'a kudawo Ku zauna Allah ya baka yawan rai nayafe Abarsu kawai nidai goggo me tuwo itace kadai damuwata ita taimin hakafa Nan yakwashe duk abinda ya faru yafada wa megari Shine zakace a barsu gwara mu koya musu hankali cewar megari Eh Bakomai a barsu cewar liman To shi kenan zansa a kiramin gogo me tuwo zan mata bayani karka samu damuwa To shikenan godiya nake Allah ya baka yawan rai Kai tsaye suka shiga gidan ba sallama Yaushe zaku girma abin naku kara lala cewa yakeyi ko Abu da Binta cewar Inna Saida suka samu guri suka zauna sannan sukace salama Alaikum Inna tace Allah nagode maka binta da Abu Nura yatafi maka rantar boko Yinme inna cewar Binta Inna tace Yaje saku a maka rantar boko daga nan yamai daku isilamiya dan harda rashin ilimi a abinda kukeyi Abu tace Boko tab ba inda zani Inna bokoko awuta kike nunfin zamu toko su yan bokokon Awuta tsoron bokon sukeyi ba inda zani saidai ko binta gata nan Waaaaniii tab namutu Allah yasani awuta ba bokon da zani cewar Binta New writer's Taku *husba'ahfama*🌹🌹💋 👠👠👠👠👠👠 👝👝👝👝👝 👠👠👠👠👠 👝👝👝 👠👠 👝 💄💅 *'YAR KWALLIYA* 💅💄 👝 👠👠 👝👝👝 👠👠👠👠👠 👝👝👝👝👝 👠👠👠👠👠👠 Written by *husba'ahfama* 11-12 Wlh baku isaba haka kuke so mu zauna daku a jahirce cewar Inna Yasin bazani ba wuta tsilim cikin sauki bokoko Awuta bada niba cewar Abu Binta ta tashi daga inda take ta koma kusa da Inna Tace Inna kisa baki akahe maganar nan dan baze taba yiyuba Yasin haka kawai ze Kaimu lahira da kanhi Kanshi kanshi inna taji yana tashi A jikin Binta Tato she hanci tace Binta warin me nake ji haka kardai kema kinhau layin rashin yinwanka Dariya Abu tayi tace Inna nice nan nadorata alayi tam bayeta kiji ita kanta tafijin dadin jikinta yanzu fiye da da Rufemin baki sakarai qazama nayi dake *'YAR KWALLIYA* Binta kiyiwa Allah karki bari Abu ta koya miki rashin Wanka da Wannan maya taccen KWALLIYAR nata Inna saidai kar a kuma dankuwa karatu yamin qanhi yabi jiki bakiga irin kallon da megari yake minba nikadai nagane meyake nufi cewar Binta Abu tace Nagani rabu dahi binta ze fado hannu banda hima ya tema kawa kanhi besa bakiba aida tuni munkoya mihi hankali kamar yanda muka koyawa liman Oohni Inna ina zansa kaina nan nasamu lbr anga liman yana zuba gudu a gari har ana zaton ya Hauka ce ashe ba Hauka cewa yayiba gamo yayi da 'ya'yan Aljanu binta da Abu babban gamo yai cewar Inna Abu kwaso kayan KWALLIYAR muyi muje gidan Amaryar da aka kawo nan bayan layin ku cewar Binta Abu tace Hakane fa banjeba kuwa Tashiga ta dauko ta ajiya a gaban binta Inna tace shiyasa tin farko banso qawan cen kuba wlh nasani sarai cewa abinda kuke da NA yanzu saiya fishi kuma gashi na gani Suka kafe inna da idanu Inna tace bance komai ba ni badaku nakeba Allah yabaku hakuri Suka juya suka cigaba da KWALLIYA Salama Alaikum inna nadawo Wa'alaikumus salam gonda da Allah ya kawo ka Yi shiru Inna nasamu lbr komai inaji nasan sune zasu aika tawa liman haka komai yazo karshe na sasu amaka rantar boko hakama isilamiya ga kayan maka rantar nasu Alhamdulillah shikenan kurinkus kandan bera boko Saikun je kokuna so ko ba kwaso cewar Inna Abu tace Boko Boko dai hikenan naji duk abinda ake fada akan boko ance yan wutane hine mu za a kaimu saboda ba a sonmu Ba a San naku gobe zaku fara zuwa daga nan idan kuntaso saiku wuce isilamiyar malam rabi'u Binta ta tashi ta daka tsalle tace rabi'u Yasin ba inda zani Wannan bakin mugun baki da Wannan kan nahi dayake kyalli kamar an cirohi A tandun mai Malamin naku kinga binta nasan irin takun sakar da kukeyi da malam rabi'u idan kika bari yakawo min karar ki kikuka da kanki irin dokan dazan miki baze faduba harda ke Abu cewar Nura Abu tace hikenan dai zamu leka wutar bakomai amma idan mukaji da zafi bazamu sake koma waba Tsaki Nura yayi yatafi ya basu guri Sukaci uwar KWALLIYA suka fice basu cewa Inna komai ba WASHE GARI Abu tana tashi tasa kayan maka ranta ta janyo kayan KWALLIYA zata yi Nura yace karki sake kiyi KWALLIYA makaranta zaki ba dandaliba Abu tace Tab yaya Nura gaskiya bazan iya fita banyi KWALLIYA ba ga kanhin tirare i nayi Amma ba KWALLIYA a fuska ta Nura yace Eh ba a KWALLIYA idan za aje makaranta Abu dole kidena wasu abubuwan yanzu tinda kinfara zuwa makaranta Binta ta shigo ba sallama agaban kayan KWALLIYA ta zauna zatayi KWALLIYA Nura yace ke Binta ba sallama Bakomai kiwani zo gaban kayan KWALLIYA Binta tace yaya Nura tinda nafito banyi magana da kowaba Gahi yanzu kasa nayi magana Almiskin bakina yafita Hanci yatoshe yace naji Almiskin kice kema kinbi layin qazantar Abu ko makaranta zaku zakuje kuga yanda Ake safta Binta tace *'YAR KWALLIYA* mezan gani haka meyasa bakiyi KWALLIYA ba Abu tace Binta kibarni kibarni kwai ni Abu *'YAR KWALLIYA* ni za a hana yin KWALLIYA badole kiga haka ba Binta tace shine kike daga hanka linki ina Inna Abu tace tana ciki Binta tace yaya I na bayanka gwanda daka hanata bani kayan KWALLIYAR NA shiga dasu au baza kibaniba bari na dauka da kaina Binta na shiga ta juye kayan KWALLIYAR a Jakarta tafito Binta tace bata cikifa Abu tace hakane yanzu ta fita zomuci Abinci bayan sun gama cin Abinci Nura ya kaisu maka ranta Duk wanda yaga fuskar Abu ba KWALLIYA sai yayi mamaki dan bata taba fita ba KWALLIYA ba Suka shiga Aji Binta tace Abu Albishirin ki Abu rai a hade tace goro Binta ta bude Jakarta tace kalli Abu cikin mamaki tafasa kara ta rungume binta ta tsalle a aji Hankalin daliban ya koma Kansu Abu tace muna fukai me kuke kallo da sannu duk zanyi maga ninku Daliban Suka dena kallon su Suka baje kayan KWALLIYA sunayi malami ya shigo aji akatashi ana gaisuwa banda Abu da Binta KWALLIYA kawai suke yi Malamin ya karaso gurin su yace Ku meye haka kwalliya a cikin aji me kukeyi a nan aji bantaba ganin kuba Abu tana shafa Jan baki tace baza kasan muba hime maka rantar be sanar dakai komu suwaye bako hege wato ya cinye kudin ko to hikenan Yace bagane me kuke nufiba fa Binta tace kaga waimu sa babbin dali baine kuma nanne ajin mu kana jiko jeka to Yace kee Nifa malamin kune kibani girma bakowana magana zaki dinga fada minba Abu tace inji kaba girma idan karike girmanka mutayaka rikewa idankuma kaki rikewa mubi takai mu wuce Malamin yayi murmushin keta yace kugoge fuskarku sannan kubani kayan KWALLIYAN Abu tace tab ba abinda zamu baka kuma ni Abu bazan goge KWALLIYA ta ba Binta tace nimadai bazan gege ba malam kabar daliban naka a tsaye fa Yace kuzauna yayi murmushin yaje gaban Allo yafara koyar dasu kamar yanda ya saba Abu tace gaskiya nagaji baza a yi wani abin bane bayan Wannan kazo ka I hemu da surutu Binta tace a he kekina jin hi tinda yafara har I yanzu banji komai ba ni yunwa ma nakeji Yace Anya karatu kuka zoyi kuwa Abu tace waya sani Abu a duhu Nifa karatun higa wutan nan beda meniba dahi da bahi duk1ne bokoko Awuta Binta tace gaya mihi kadai koyarda su dan naga kamar suna gane wa Yace anya Ku muta Nene kuwa ke dawani fuskarki kamar aljana waya gaya miki karatun shiga wuta nake koyawa Binta tace baka jiba bokoko a wuta hine zakace bakaratun higa wuta bane Yace kutashi Ku fita daga ajin nan kufita kuyi shir menku a waje Abu tace seme danka koremu kahiga wutar kaika dai kacike gurin karkabari asa wani Yace keni zaki fadawa haka Tamurguda baki Yadauko bulala ya zuba mata Tasaki kara Binta tace meyasa ka daketa kai ko a qauyen mu mune muke yiwa maza duka hmmm Yace me kike nufi nima dukana zakuyi kenan Abu tace meze hana tinda ka dakeni saina rama Yace waya gaya miki idan malami yadaki daliba tana ramawa Binta taja hannun abu Tace Abu rabu dahi zomu fita ze fito ya same mu damu yake maga mekoya karatun higawuta dole mukoya mihi hankali Suka fita Abu kinga ya aika a siyomai abinci Abu tace waye ya aika asiyo mihi abinci mekoya karatun higa wuta Binta tace Eh hine zomuje Yaron ya siyo abincin zekai wa malam binta da Abu suka tsare shi Abu tace Kai bamu abinci kaje kadebo min ruwa zansha kagani ba quwace Yace malam ya aikeni bari nakai mishi nadawo saina debo miki Binta tace harna hadiyi yawu banga abin dake cikiba amma nasan zeyi dadi tafada tana dariya New writer's Taku *husba'ahfama* 🌹🌹💋 👠👠👠👠👠👠 👝👝👝👝👝 👠👠👠👠👠 👝👝👝 👠👠 👝 💄💅 *'YAR KWALLIYA* 💅💄 👝 👠👠 👝👝👝 👠👠👠👠👠 👝👝👝👝👝 👠👠👠👠👠👠 *GODIYA GA DUK WANI* *MASOYIN NOVEL DIN 'YAR* *KWALLIYA INA GANIN SAKON* *NIN KU NAGODE* *ALLAH YA BAR ZUMUNCI* 😍😘 Written by *husba'ahfama* 13-14 Abu tace Kura kyaci da Gashi tobaci zakiyiba na me koya karatun higa wuta ne Yaron yace Gashi barina debo miki Abu tace yauwa na gode ga abincin me koya karatun higa wuta a hannun Binta zomuje Binta ba labari idonta nakan kwano baki a Bude Abu tace Binta kinga halin naki ko to cika dan Kibar sauran akwai abinda zanyi kafin yaron ya dawo Kan Abu ta gama magana harbinta tasa hannu tayiwa abincin wawan diba saida yayi rabi takai baki Abu tace kaiiii Binta kincinye ai bakomai zodai muje Binta tace nidai da zaki temaka kibani na cinye abincin yayi hegen dadi Abu tace Bazan baki badain sarkin kwadayi dake Binta tace Bakomai kome zakice kice kinsan idan naga abinci wani shaukine yake kamani sai naji hannuna yana rauwa Abu tace hannun yafadi kasa inyaso cine dai bazan baki kiyiba Abu tayi gaba wajan me abinci tabar binta da side hannun Abu tace me abinci kinada gihiri Eh Gashi Abu tayi murmushin tace nagode Tabude ledar gishirin ta zuba gishirin a cikin abincin tajuya dafa dikan shin kafa ne Ta mikawa me abincin sauran gishirin Tace Gashi nagode Garuwan na debo miki Abu tace na gode ga abincin kakai mihi To yace yatafi kaiwa me koya karatun higa wuta Malam ga abincin Yace to jeka zauna kuyi sauri kugama nasa hannu To malam yaran suka ce Malam ya wanke hannu yabude abinci ya ganshi kadan be damuba ya sa hannu yadebo a abincin yakai baki cikin bacin rai yafurzar da abincin Kai a wurin wa kasiyo min abinci Abu tace Agurin me abinci nikuma na kyara maka abincin yanda zeyi dadi yakaji to Yace Keee nizakiyiwa haka kinsan nawa nasa nasiya kuwa Binta tace konawa kasa be da me muba badai ka daki Abu bako hmmm Me koya karatun higa wuta ya dauko bulala ya nufi gurin su Binta taimaza ta watsa run a hanyar da ze taka rai a bace ko gabanshi baya kalla sai Abu yana sa kafarshi santsi yajashi ya fadi kasa daliban aji suka sa dariya Cikin muryar tsawa yace kuyi shiru nace inba haka ba duk kanku sai kunyi kuka Abu tace mekoya karatun higa wuta a kasa yara kuyi dariya iya san ranku ba abinda ya isa yamuku Yace saikunbar makarantarnan yau din nan nake gaya muku Binta tace idan mubamu bar makarantar ba kaika bari Yace ko haka kuka ce Abu tace kwaraida aniya kaga tafiyar mu Binta tace Abu ina zamu Abu tace gurin shugaban makaranta mana wanda yaya Nura yakaimu gurin hi dazu Binta tace hakane muje kafin ya rigamu Salama Alaikum Wa'alaikumus salam Fatima zainab yaba kwacikin aji yanzu bayan kowana malami na cikin aji Abu ta fashe da kuka Yace zainab meye na kuka kuma wani malamin ne ya da keki Sai Binta tafashe da kukan karya tace damu aka daka ai abin da sauki amma kamar kai wai za a wayi gari wani yana zaginka Yace ni waye kuma ya zageni Fatima Abu tace me koya karatun higa wuta ne yace hiwai ya gaji da aiki a karka hinka ba abinda kake bahi wahalar banza kawai yake maka nibama Wannan bane ya dameni tafashe da kuka Binta tace waikai baki ka ajiye katon ciki kana zaune kana sheniska sukuma kabarsu da yara suna henwuya idan yasamu dama saiya sace maka katon cikin ka dan mun masa maga munce mekai masa yake zaginka hine yace mufita mubar mihi aji Rai a bace yace ban gane malamin da kuke nufiba amma muje ajin naku na gan shi Binta da Abu na gaba yana binsu a baya harsuka isa aji Yanzu kai lawan abinda zaka min kenan duk irin abinda namaka da Wannan zaka saka min Me nayi kuma Baka ma san kome kayiba ko meka fadawa yaran nan Ni lawan mezan fada musu babu wata magana da mukayi hasalima bakaga irin abinda suka minba yakamata akoresu daga makaranta karsu koyawa sauran yaran halinsu Idan ban Kore suba kaina koreka daga aiki irin wadan nan mugayen kalaman zaka jefeni dasu kaje na koreka Dan Allah karka min haka da aikin nan na dogara dashi nake ciyarda kanne na da mahaifiyata idan kakoreni inazani nashawuya kafin ka daukeni aiki Abu da binda sukayi dariya Abu tace su gaban maka ranta ayi mihi hakuri idan ya sake sai kadauki mataki To shikenan na dawo dakai Amma kar hakan yasake mai maita kanshi To nagode sosai insha Allahu hakan baze sake faruwa ba Shikenan nizan koma Fatima zainab kuje kuzauna To suka ce Yana fita suka kalli malam lawan Ya kaga aikin mu kayarda cewa mu zamu iya sawa a koreka cewar Abu Yace kuje Ku zauna Bayan antashe su daga makaranta hanyanzu na komawa gida suka wuce kasuwa wasu maza suka tsaya a gaban su Abu tace lpy kuwa 1 daga cikin samarin yace Lpyar kenan shine kuka sa aka kori yayan mu sannan kukasa aka dawo dashi yanzu abinda kukeyi mukeji a gari ya fado gidan mu Binta tace ba abin mamaki bane dan kana jin lbr yanzu kuma yafado gidan Ku mu ai ruwan darene gama duniya Yace yanzun nan zamu koya muku hankali tinda Ku bakuda kunya Abu tace Allah ko sannu me kunya saika koya mana muna jira Binta tace 🗣jama'a ga barayin da suke muku sata dan munce zamu fada muku hine suka ce zasu dake mu Nanfa mutanan kasuwar suka zageye samarin suna cewa dama kuwa ansaba mana sata gashi yau Allah yatoni a sirin Ku Samarin sukace wlh muba barayi bane Dama zakuce haka mekuke jira da sune cewar Abu Nanfa mutanan suka rufesu da duka Abu da binta cikin farin ciki suke Binta tatafi gidan su Abu ma haka Abu na shiga gida taga baban ta ya dawo Naji dadi daka dawo sannu da zuwa baba kaga yaya Nura yasani a bokoko awuta yauna fara zuwa amma sanda me koya karatun higa wuta ya dakeni cewar Abu Yace yi hakuri yar baba shikenan komai ya zo karshe ke bari na zokarshen zancen bazaki sake koma waba daga yau Abu tace Yasin naji dadi hiyasa banaso kana tafiya baba idan kana nan bame min fada komai nayi daidaine a gurin ka kuma nafi sakewa Saiki bishi kutafi tinda haka kikace cewar Inna Yace abin harda kishi yar baba shiga ki cire kaya kici abinci dan nasan wanka ba a yi danga qanshi naji zanyi magana da Babarki Tayi dariya Tatashi ta shiga daki Yace ina kike jiya mukayi wata magana da yayanki Alhaji nasiru Shine yasa meni yace meze hana nabashi Abu tayi karatu a birni kinga Amal tasamu kawa kenan shine nace ya bari nayi magana dake tukunna Inna tace Ehhhto birni a kwai karatu nasani nasan kewa na damun Amal kasan cewar ita kadai ce mace a gidan su abin shine yardar Abu shine matsala dayanda zasu jure hala yanta a can dantani ba matsala wlh saidai yanzu Abu tayi qawa duk inda zata tare suke zuwa komaka ranta da Nura yatashi Atare yasa su Yace To wacece qawar tata dan nasan dole ya kasan ce kucakace irin ta Inna tace au dakanka kake ce mata kuca ka Ashe kasan kuca karce bari na kirata taji da kunnen ta Abu Yace bari mana yar baba yi zaman ki Inna tace daka bari nakirata ai bawata bace illa 'yar gidan malam murtala me rasuwa Binta Yace Auzubillahi karki cemin binta gagare Sarkin kwadayi Inna tace ita dai Yace babu inda za aje da ita idan taje birni ai saita sawa yangidan hawanjini konida ba mazauniba nasan halin Binta amma kinyi kokari tab ya Abu take ita kadai balle an hadata da binta gagare Inna tace gaskiya baze yiyu kazo ka raba suba bacci ne yake raba Abu da Binta wani lokacin binta Anan take kwana abu ma tana kwana a gidan su shine zaka ce haka nasan yaya nasiru sarai bazeki karbarsuba yarike nawasuma balle Binta data zama yargida Yace to shi kenan Allah ya kaimu gobe muga yanda za ayi dan gobe yace zezo amma dan tani babu inda za a da Binta gagare Inna tace ya zaka dinga take halin 'yarka kana hango na wata idan har gaskiya za a fada Abu ma da halin ta dan harwanka tahana Binta Yace ina ruwan ki qawance baya yiyuwa sai hali yazo 1 yanzu kekinsan irin halinda Abu ta koya a gurin ta Inna tace A'a bansani ba Yace to gingani mubar komai dai se gobe in Allah ya kaimu New writer's Taku *husba'ahfama*🌹🌹💋 👠👠👠👠👠👠 👝👝👝👝👝 👠👠👠👠👠 👝👝👝 👠👠 👝 💄💅 *'YAR KWALLIYA* 💅💄 👝 👠👠 👝👝👝 👠👠👠👠👠 👝👝👝👝👝 👠👠👠👠👠👠 Written by *husba'ahfama* 15-16 WASHE GARI Alhaji Nasir yazo tafiya da Abu Tin a kofar gida da Abu taga mota ta Tsaya tana shafa motar Abu tace I nama ace na higa cikin jirgin yan binni mu Anan daga amalanke sai keke sai jaki suko yan binni suna jin dadi Ta shiga leka cikin motar tana dariya Baban taya fito ne manta Yar baba aike nake nema zo kiga Kerere ta Tsaya a gaban su ta Ciro hudarda ke soke a kugunta tana shafawa Munzali yace Yar baba ga Alhaji nasiru yazone danya tafi dake birni Zabira tayi ta saki hodarda yake hannunta tace da gaske zani Binni barina kira Binta tazo mu tafi Kaiiii Yasin bazan yardaba hodata ta fahe yanzu mezan dinga sha fawa idan naje birni tafada tana kuka Alhaji nasir yace Yi shiru Abu ni zan siya miki wani idan munje birni akwai wanda yafi wannan a can sosaima Abu tace nidai gaskiya bazan yardaba bayan Ance Ku yan binni bakuda cika Alkawari nidai kawai kabani kudi naje na siyo wani Munzali yace Yar baba yazakice haka yan birni suna cika alkawari Wannan da kike gani shima mahai finkine yayan mahaifiyar kine kuma Amini nane sosai kodan lokacin dayake zuwa kina yarin ya shiyasa baki sanshiba Abu tace nidai ba ruwana abi yani huda ta kuma guda2 nake so daya ni daya Binta Alhaji Nasir ya Ciro 1k ya bata Waiyoo dadi dolema naje binni tahin farko nera dubu me yafi raina Bari naje na hado sa babbin kayan KWALLIYA ta yanda idan nayi KWALLIYA zan sumarda samarin binni da yan mata Munzali yace yar baba bari nafada miki idan kikayi Wannan KWALLIYAR taki a birni sai maza dubu sun suma hamsin sun mutu hamsin kuma suna gadon Asibiti inada tabbacin haka Abu ta gyara tsayiwa tana juyi Baba bari na fadawa binta tashirya mu tafi Yace yar baba wai Wannan Binta dakike fada kanwa tace kota Inna kekadai zaki tafi kina jiko Abu tace baba Nifa idan ba binta babu inda zani ehhhe Alhaji Nasir yace wai wacece binta nan ne da Abu take nagana a kai Abu tace kawa tace baban ta ya mutu ita kadai ce a gurin ummanta Alhaji nasir yace Bakomai indan mahaifiyarta zata yarda sai mutafi da ita Bakomai Abu tace hine magana Nina tafi Gidan su binta Abu taje ko sallama babu ta shiga gidan tana kiran binta Binta tace gani lpy kike min irin Wannan kiran Abu tace jeki hado kayanki kizo mu tafi binni Binta tace anya Abu lafiyan ki kalau kuwa dasafen nan kiwani tasoda maganar zuwa birni nidai bazan kaiki ba kinji na fada miki Abu tace kinga bake zaki kainiba yayan Inna

Chapter 3 of 12