Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ne yazo ze tafi damu baki gan hiba tahin farko dubu1 yabani Binta tace jirani na hado kayana mu tafi dubu1 tab kice tin yanzu mufara canza tafi Abu tace Yasin kuwa muje na zabar miki kayanda zaki tafi dashi saboda canba qauyen *DARAUDAU* bane sonake mu haukatasu da sakaya da KWALLIYA Binta tace hakane muje Suka shiga suka hada kaya sukafito Binta tace umma mun tafi binni sai nadawo kikula da kanki idan na tashi dawo wa zantaho miki da kayan dadi Umma tace Binta banganeba Waze kaiki birni niban sani ba Abu tace umma idan kinaso kiji gaskiyar magana dauko maya finki kizo muje kiji Haka ko akayi umma ta bisu suka tafi Abu tace kinga abinda zamu hau mutafi binni tanuna motarda Alhaji nasir yazo dashi Umma ta gaidasu suka amma tashiga cikin gida gurin inna inna tai mata baya nin komai umma ta amince Takuma yi musu addu'a tayiwa Alhaji nasir godiya data fito Abu gaba daya kayanta ta kwaso Innata an she ta zaba mata wanda yadace ta tafi dashi suka fito zasu tafi Abu ta jefa kayanta saman mota ta anshi na Binta ta jefa sama Abu tace kinsan su yan binni mutum 1ne aciki sannan duk wanda ze hau shikuma yana sama kicici bani na fara hawa shi kuma saiya cici boki au ga Inna nanma zata cici boki Binta ta ta ciciba Abu saiga Abu a saman mota Binta tace umma zoki cici bani nima Abu ta hau saura ni Kamar daga sama Alhaji nasir yaji maganar Binta yace acici bani Abu ta hau saura ni Dasauri yajuya yaga Abu a saman mota ta hakim ce Yan gari kowa yafito yana kallon su Abu sai wani yasina take tana shankan shi Alhaji nasir yace Abu sauko waya gaya miki nan ake hawa sauko Abu tace nasauko kace kafasa zuwa dani nafa San komai gameda jirgin nan Alhaji nasir yace zantafi dake sauko kiga Abu tace mezan gani Alhaji nasir yabude mota yace da Binta tashiga binta cikin tsoro ta shiga ta zauna sai taji ta lume da sauri ta fito Binta tace gaskiya a canza min mazauni ina zama yabude baki ze hadiyeni Abu tace nasani ai hi yasa nai zamana Anan kinga Wannan baze taba fada miki gaskiya ba miko hannun ki na janyoki muyi zaman mu Anan Binta ta mikawa Abu hannun abuna janyota Alhaji nasir yace malam munzali da alama sai kasa bakifa Munzali yace yar baba sauko kiga nan ake shiga ba saman mota ba Abu tace baba nayarda dakai barina sauko amma kanaji Binta tace yabude baki ze hadiyetafa Yace ba hadi yeta zeyeba kasa yayi saboda tazaun zoki shiga ki gani Abu ta sauko da kayan su itama ta sauko Abu tashiga tazauna tace baba hakane nazauna Binta shigo Binta tashiga ta zauna tace kawata yakika ji gurin dadi ko danma bamuje canba Abu tace hakane dole idan munje mu nuna musu munsan komai dan karsu raina mu Binta tace to Sanyi sukaji yana shigarsu tako ina suka hau kerma abin bemusuba sukasa ihu suka fito Alhaji nasir da malam munzali dasuke sallama hankalinsu yadawo gurin Abu da binta Alhaji Nasir yace lpy kuka fito Abu tace baba nagane hidai Wannan mutumin bakin ciki yakeyi damu yasan munfi yan matansu na binni haduwa hine ya turo mana jaura dan muce mun fasa Munzali ya kalli Alhaji nasir Alhaji nasir dariya yayi yace AC ne a kunne bari na kashe tinda bakwa so amma ni ban turo muku jauraba hasalima ni ina so kuje birni Ku wayar dasu Alhaji nasir yakashe AC yace kushiga nakori jaura ta bakin naku Alhaji nasir yayi sallama dasu yashiga mota yaja suka tafi Yan gari murna ya cikasu ganin Abu da binta zasubar gari har motar su Abu ya bace yan gari basu dena daga musu hannu ba Kome Abu da binta suka gani sai suyi ihu su buga mota harsuka karasa gidan megadi ya bude musu gate Alhaji nasir yashiga da mota yafaka ya bude musu mota yace su fito Koma gana Abu da binta sun kasa Tsaya wa sukayi suna kallon gidan babban gidane tsayawa fadan haduwar gidanma qauyan cine Amal da hajiya mariya matar Alhaji nasir da gudu suka fito Amal da gudunta ta taho zata rungume su tana zuwa taji kanhin tiraren jikin binta da Abu a haka ta rungu mesu tana murna Amal tace sannunku da zuwa tinda nasamu lbr zuwanku na sa aka gama komai da wuri kuzo mushiga ciki kuyi Wanka kuci abinci Abu tace Wanka tab bakiji kanhin tirarena bane Amal tace banjiba saidai naji wari Abu ta dunkule hannu zata kaima amal duka binta tarike hannun Tace Abu gidansu kika zofa kiganar da ita idan taki ganewa saiki ragargaji bakinta nida kaina zan tayaki Abu tace kinci sa a kufa yan bin tsiyata daku hirme warin da kikaji ba wari bane qanhine zokiji Amal ta matso Abu tace rabona da wanka harna manta Hancin Amal ha toshe har Abu ta gama magana Amal tace naji kuma na gane kuzo mu shiga ciki New writer's Taku *husba'ahfama*🌹🌹💋 👠👠👠👠👠👠 👝👝👝👝👝 👠👠👠👠👠 👝👝👝 👠👠 👝 💄💅 *'YAR KWALLIYA* 💅💄 👝 👠👠 👝👝👝 👠👠👠👠👠 👝👝👝👝👝 👠👠👠👠👠👠 Written by *husba'ahfama* 17-18 Abu da binta suka kalli hajiya mariya suka ce ina wuni Hajiya mariya tace lpy kalau Abu tace naka gu naga cikin gidan nan yasin binta gani nake kamar na higa haljan na Yasin Wannan yayan Inna dan bakin cikine yasan da Wannan gidan a duniya yaki yazo ya daukeni sai yanzu dana Riga na girma a qauye datini bansan kiba Binta Binta tace nikuma naji dadi dabe zo ya daukeki da kina karamaba daya daukeki da kinmin bakin cikin zuwa binni dubafa kiga girman gidan nan bantaba Tina nin zanzo hiba yausaiga Binta a ciki Abu da binta na tafiya suna hirar gidan Hajiya da Alhaji suka shiga Amal na bayan Abu da Binta Amal tace kushiga mana Abu da binta suka kalli juna tiles ne baje a falon gidan Binta tasa kafa Abu matasa suna tafiya santsi na jansu suka zube kasa Abu tace daga nan bazan dara ko inaba Binta tace nima haka muna tafiya yana janmu dan hihigi Abu tace gaya mata dai Binta kalli kiga hoton ki a nan tanuna mata tiles din dake kusa da ita Binta tace hi Wannan banda tafiya da mutane har hoto yana dauka laaaaaa kalli kiga kema gaki a nan Amal tace dan Allah Ku bari tiles ne baya tafiya da mutane kutashi kuga Abu tace Yasin daga nan bani zuwa ko ina bayan a gabanki yatafi damu bakice komai ba Amal tace to shi kenan zan mishi magana yanzu kutashi Binta tace kai Nifa jinake kamar nakawo kaina inda zan sha wuya daga zuwa naci karoda Wannan abin ze tafi dani gaba kuma mezan gani Amal tace ba abinda zaki gani kuma nadau Alkawarin yiwa komai na gidan nan fada Abu tace dagaske Amal tace dagaske mana nidaku yanzu kawaye ne kutashi Abu da binta suka tashi suka tsaya Cak ganin basuda niyar tafiya yasa Amal ta shiga tsakiyar su ta rike Hanna yen su tafi dasu ta zaunar dasu a kan kujera ta kunna musu kallo Amal tace ga kallo na kuna muku kuyi ina zuwa bari nakai muku kayanku dakin ku yanzu zan dawo Binta sukayi da kallo basu ce komai Ba suka maida hanka linsu kan kujera suna daddan nawa suka shafo tiles din Binta tace Abu kinsan me Wannan shine Aljan nar duniya da malam rabi'u yake fada mana kintuno Natuno mana saidai kinsan me yanzu kanhin titaren jikin mu zeyi Amfani sosai ma cewar Abu Binta ta kalli TV tasa ihu tana nuna shi da dan yatsa Abu ma ihu tayi hajiya, Amal, da yan aikin gidan Asibi da kande suka taho gurin su da gudu hajiya tace Abu Binta lpy meya faru Abu tace hajiya Aljanune suka Bude mana ido muna kalla mukaga wani gabjejen kato ya kaiwa wani nauhi sai dukansu yake daga karshe ya dunkule hannu zekai mana nauhi kamar haka Abu ta dunkule hannuta tayo saitin hajiya hajiya ta sunkuya Abu ta samu kaiwa Asibi naushi a baki Amal tace Abu kinfasa mata bakifa Hajiya tace nashiga3 alhaji kakawo mana aiki Binta tace ba laifinmu bane laifin Aljanun canne susuka Ja komai harmu har doke doken mu munga wayanda suka fimu Amal tace Asibi muje ciki yi hakuri Hajiya tace ku bata hakuri Sukace yi hakuri Hajiya tace ba aljanu bane kuje Ku zauna Binta tace tab babu inda zani sun dunkule hannu zasu nau hemu mun kauce kice mu koma Abu tace fada mata dai ga hican yana kallon mu da alama mu yake jira muna zuwa hi kenan ba lbr Hajiya taje ta kashe TV tace kuzo kuzauna nakoresu sun tafi Binta tace gaskiya a canza mana gurin zama sabo aljanunnan zasu dawo inada tabba cinhaka Amal tazo tace kuzo muje Amal ta kaisu dining Abu tace ina ne nan kuma nasaba ganin idan za ayi tafiya sai anhau mahin Ku kuma da kafa a ke zuwa nan Amal tayi dariya tace bawani tafiya bane me tsawo shiyasa kika ga haka Binta tace Abu Yasin idan Akazo rabani da Wannan Aljannar za a shawuya dan nahigo kenan ba inda zani nida *DARAUDAU* sai ziyara Abu tace ke kenan ni ko ziyara bazan jeba duk wanda ya matsu yazo ya ganni damuwata 1 yaya Nura,inna da baba Amal tace Ku zauna muci abinci bayan mungama na zagaya daku kuga dakin Ku da gidan gaba 1 Abu tace bayan nan akwai wani unguwar da zamu tab ba inda zani idan bada jirgin yan binni ba Amal tace shikenan dai Ku zauna zansan abinyi Amal ta zuba musu taliya da miya da na man kaza Tinkan Amal ta gama zubawa Binta take hadiyan yawu tana gamawa Binta ta danki naman kaza tana ci Amal kallon su kawai takeyi tana dariya Abu taliyar take kalla fuska a yamitse tace yan binni da kwada yintsiya tsutsar ma cikuke Abu ta kalli binta dake danbe da naman kaza Amal tace Abu ba tsutsa bane taliyane yanada dadi sosai cikiji Kai bada niba ko a qauyan mu daga akuya sai kaji zabo tantabara agwagwa sune Abinda nasan Anaci banda tsutsa kikawo min tuwo danmalele ko dan bagalaji waiyoo dadi saikin bani lbr cewar Abu Amal tace kici Wannan yanzu kafin nasa a dafa miki abinda kika lissafo To bari na gwada Tasa hannu ta debo taliya takai baki ta fara tauna ta furzar da shi Tace tab Yasin bazan iyaba kibani tsutsa da ranhi da komai inaci yana motsi gaskiya yan binni bakuda tausayi Abu Wannan fa ba tsutsa bane kamar yanda kike Tina ni amma Bakomai muje kisami Asibi kifada mata abinda kike so a dafa miki Sai lokaci binta ta dawo cin hanka linta bayan ta cinye kaf kajin gurin tana gyatsa tace dadi binni wai bani komawa ko ina zama dis saita fashe dakuka waiyoo umma tana can tana fama da tuwo tafada da muryar kuka Ta kalli abincin da kyau ta fasa kara ta koma bayan Amal Binta tace gaskiya bazan iya cin tsutsa ba nadai ci kaza zan iya zama daku amma abinda nake ci kubakwa ci shine kawai matsala Amal tace karki damu shima zaki saba dashi zo muje Takaisu gurin Asibi suka fada mata abinda zasuci tace su bata lokaci kadan zata dafa ta kawo musu suna fitowa daga kitchen Amal tace kujirani Anan karkuje ko ina ina zuwa nazo na za gaya daku Amal ta tafi Abu tace mutsaya kar muje ko ina karya ma kenan binta biyoni Suka fara tafiya suna Kalle kalle Abu kinsan me fasa har kawunki a dakuna ta kare kalli kiga irin dakunan dake gidan nan nasani mutanan garin nan gaba1 Anan suke kwana sun fita Neman abinci anjima zakiga gidan nan yacika da mutane Abu tace Yasin be birgeniba dayabar su Anan daya musu a wani guri daban sukuma su zauna Anan Binta tace Abu kinji abinda nake ji kuwa Abu tace naji wakar daga daku nan nan2 suke fitowa saidai ba irin wakarda mukeyi a dandali bane Wannan yafi dadi Yasin Tana fada tana rawa Binta tace sosai ma bazaki hadaba binni yafi qauye kalli gidan nan kamar gidan sarki hiko me gari gidan muma yafi nahi kyau Abu tace nidai zan higa dakin nan naga waye a ciki ke kuma ki duba dakin nan To hi kenan Abu ta Bude tana lekawa da bataga kowaba saita shiga sautin wakar nashigarta tafara rawa Binta kaitsaye data Bude ta shiga lemo ta gani a ajiye a cikin Kofi ta dauka Tace giyar yan binni barina sha abina meyafi raina ba yaya Nura balle yamin fada cewar Binta takafa kai tana sha tace dadi gaba daya zan shanye takai baki tana sha Me zan gani haka yadaka mata tsawa yace me kikeyi Anan cewar Arif Binta najuyowa saboda tsoro ta fesa mai lemon bakinta Kai keee ni kika fesawa lemo wacce ke tukun nama dahar zaki fesa min lemo kinsan koni waye kuwa cewar Arif Binta tace kokai waye be dame niba wa yace ka tsora tani Arif yace haka zakice ko Binta tace kwarai da gaske Arif ya nufo inda take yace ke warin me kikeyi Binta tace kut Yasin yanzu bakinka zeyi jini indai kasake cewa wari kudama yan binni kwai rainin han Kali Arif cikin tsawa yace fita kona dakeki kowaye ya kawoki gidan nan ma oooho Abu rawarta kawai takeyi tsabar dadin wakar yasa ta danne danne harta kara sautin wakar Waye waye a nan Yaji ba a amsaba yace sister ba a amsaba yace Amal shiru saiya fito da kanshi MaMaki yakeyi yanda akaita shigo yaje ya kashe wakar yace me kikeyi Anan fuska kamar Aljana kifadamin Aqeel ya fada cikin tsawa Abu tana rawa dukda ya kashe wakar take cewa duk inda ake kida da waqa kirana ake dan haka wakar kace ta kirani Aqeel ya toshe hanci kinga dadawar cikin gida zaki kai sune masu amfani dashi ba niba Abu tace a ina kaga dadawa kuma kanhi dai gaskiya kanada babban sa'a tinda kaji kanhin tirarena Aqeel yace tirare karkice daga jikinki warin nan yake fitowa Wari Yasin karka bari na fara dakai karka sake cewa wari kanhidai Wari ko kanshi beda meniba fita daga dakina kokuma na yankaki Eh yankani zaka aikata dantinda naganka naji tsoronka Ashe kisa kake Aqeel ya dauko wukarda ya yanka lemo dashi ya rike a hannu Arif yace bazaki fitaba ko duka nakeyi kuma dukana yana karya mutum koma ya mutum Eh karka kasheni zanfita Arif yace fita cikin sauki kona dauko abinda nake duka yanzu na fasa miki jiki Abu tace kakasheni a kasheka amma dai kabarni darai zan fita Aqeel ya biyo abu da gudu Abuta fito Arif yabiyo Binta da gudu Binta ta fito Abu ta kalli Arif Binta ta kalli Aqeel Atare suka kurma ihu mai kara suka rungume juna Abu na nuna Arif Binta na nuna Aqeel New writer's Taku *husba'ahfama*🌹🌹💋 👠👠👠👠👠👠 👝👝👝👝👝 👠👠👠👠👠 👝👝👝 👠👠 👝 💄💅 *'YAR KWALLIYA* 💅💄 👝 👠👠 👝👝👝 👠👠👠👠👠 👝👝👝👝👝 👠👠👠👠👠👠 Written by *husba'ahfama* 19-20 Gaba daya yangidan suka fito sukazo gurin Amal tace Abu Binta lpy Abu cikin muryar tsoro tace kalli kiga Amal tace nagani yaya Arif ne Binta tace gaskiya bazan iya zama a gidan nan ba gida ya cikada Aljanu biyoni yayi yakoro ni ina fitowa na ganhi a Wannan daki Harlokacin suna kankame da juna Amal tayi dariya tace laifinane daban gaba tar muku da suba kutashi kugansu dakyau Abu tace kinga bazan iya hada ido da nunar rana ba kinsan meya cemin kuwa Amal tace kome yace miki yafada ne kawai ba da gaske yakeba kutashi mana Aqeel yace karma su tashi beda meniba Aljanu mutane duk yanda suka dauka dai daine Arif yace yarin ya bakai lemo na ajiye naji wayata tana ringing naje dau kowa nasamu ta dauki lemon tana sha Amal tace yaya dan Allah kubari ya wuce Gashi yanzu kun tsora tasu Aqeel yace Dama atsorace suke inba hakaba meye abin tsoro dan Arif yafito daga dakin nan Nina fito a Wannan daki Hajiya tace amma saiku duba cewa basu sanku yan2 bane yaba zasu tsorata ba kamar ku1 kayanku iri1 sannan kuce meye abin tsoro Amal tace Abu Binta wayan nan yayyu nane su yan2ne Yaya Aqeel da yaya Arif kuma yanzu sun zama yayyinku Abu tace tab bahi kuka dauka tinda kuka tsorata mu saina rama yasin Aqeel yace aikin gama ramawa Wannan kwalliyar taki kadaima abin tsorone dana ganta fa sanda na tsorata saina dake kwai nai mata magana Amal tace haba yaya Aqeel meye abin tsoro a Wannan kwalliyar kuma Arif yace bazaki ganiba ai tinda ancika miki burinki ankawo miki qawaye ko saida kawayan naki wari sukeyi dan haka Akwai aiki a gabanki Binta tace kut da alama yanzu baki zeyi jini suwaye suke wari Abu tace barsu dani nice nan daidai kai nunan rana dani kake magana bawai kai makahiba ko a kaina dakai zan rife ido namaka abinda nakewa maza a qauyen mu Yasin Aqeel yace Amal kinyarda cewa kinada aiki wacce macace zata Tsaya yin fada da namiji inba kucakaba dawani fuskarki dayaci wuwar kwalliya kamar wata Aljana Arif yace maza kuce zakuyi abinda kukeyi a qauye ne idan kukayima dariya zasu muku masu fada da maza Anan abuhu ake sasu a kulle aba kura Abu tace Amal kike kowa sudai wayan nan nunar ranar babu wata magana me dadi a bakinsu inaso ki fada musu cewa karsu bari nafara dasu banida kyau Aqeel ya hade rai yace kifara damu kigani kucaka qazama kawai kika kara ce mana nunar rana saina zubar miku da hakori Yana gama fada suka shiga daki suka rufe Abu tazube kasa tana tumami tana dukan dakin Aqeel tana cewa Yasin zan samu lokacin ka tinda kace min kucaka mun kullada kai Yasin Amal tace yi hakuri Abu baze sakeba daso kiji Binta tace haba Abu kinbani kunya wayan nan zaki Tsaya kinawa haka sekace bakece Abu ba Abu tace hakane kuma natahi Amal tace kokefa kuzo muje dakin Ku Suna tafe suna hira harsuka karasa qanhin jikinsu na dukan hancin ta tin tana daurewa harta kasa ta koma toshe hanci Amal tace ga dakin Kunan amma gaskiya kusamu kuyi wanka kanshin tiraren naku yana damun mutane kusamu kuyi wanka koda ya ragu Binta tace tab waikinji Abu Abu tace munfiso kanhin yafi hakama tinda mun higo binni baraini tsaka ninmu daku Amal ta zauna akan kujera tace kuyi wanka nikuma zan kawo muku tirare ma kanshi wanda idan kunfesa kunje guri kanku karasa tiraren yarigaku karasawa Binta tace bar abinki bama so kanhin tiraren mu basemun fesaba kukuma kince saikun fesa na mune na gaskiya naku kuma jabine Yanzudai Ku zauna Ku huta ina zuwa cewar Amal To sukace gaba dayan su Binta ta tashi tana kalle kalle ta Bude bandaki ta shiga tana kalla wanda ya mata kyau kuma ta taba Binta tace Abu kinsan me su yan binni basa kahi Abu Tataso tazo gurinta tace meyasa kika ce haka Binta tace kalli kiga daga randar yan binni sai madubi da baho ba gurin kahi muma daga yau munde na kahi Tace tab gayu hikenan dai binta kinga Binta tace bakin gurin ne kina tabawa ze fara magana hiyanzu Ankulle bakin hi bazeyi maganaba Abu tace Niko zanso naji abinda zece ta danna gurin Ruwa ya fara zubowa daga sama binta tasa kara Amal ta taho da gudu Tace lpy Abu tace kinga bada munaba amma ana ruwan sama Amal tace tabawa kukayi Wannan da kuke gani idan zakuyi wanka zaku kunna shi Tanan ruwan ze Zibo Wannan kuma abin goge bakine ga man da ake tsawa zakaga bakinki ya fita yayi kyau sosai Abu da binta Suka kalli juna Binta tace hifa dan binni kwai kakale banda gawayi da gihiri har Akwai wani abin wanke baki bayan hi Amal tace gawayi da gishiri a qauye kenan nan kuma birni da wayan nan da kuke gani dasu ake amfani Abu tace nikoda gawayi bana wanke baki balle Wannan daganin hi bamam arziki bane ina sahi a bakina hakori na zezibe Amal tace injiwa kina nanfa na gama fadan amfanin shi gaskiya bazaku zauna bakwa wanka ba kwa wanke bakiba namuku ta sauki amma kunkiji shi kenan ni inada wayanda zasu saku kuyi kokuna so ko bakwaso idan baza kuyiba inada masu muku Abu tace tashin duni banga me rabani da tirarena ba Yasin duk wanda yace zesa nayi wanka hmm zamu kwashi yan kallo Binta tace jeki ki turo duk wanda zaki turo baza muyi wankaba jeki bacci za muyi Amal ta fita rai a bace Abu tace bacci fa kikace Binta muda zamuje dandali Yasin na hiryawa duk wanda yace ze tsokane mu Binta yanzu haka zamu bar wayancan 2 kinga abinda suka mana fa Abu tace karki samu da muwa dani yake magana nice kucaka qazama hmm Binta tace ba haka yakeso yace ba gannin mutane a gurin ne yasa yace haka amma ni naga ne komai Binta zo muje Binta tace to suka fita Akofar dakin Arif da Aqeel suka tsaya Abu tayi murmushi tace gamu munzo nice dai Aljana yanzu Anan zan fara aikin Aljanu Tatura kofar dakin Aqeel ta shiga Tana shigowa taci karo da wata bugaggiyar shadda ruwan kasa a kan kujera Dakin ciki da falo ne daga ciki taji yana cewa gani nan zuwa yanzu aka kawo min kayan daga gurin dinki ina sonsu sosai Abu tace hikuma nunar rana dawa yake magana koda yake ba abin mamaki bane da Alama kanhi ya kwance naji dadi karage min aiki makahi yanzu zan kahe kayanka

Chapter 4 of 12