Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
,hakuri,kyautatawa da juriya Abba ,kuma duka Abdul Maleek yana dasu ,shin Abba kana da wanda zaka tura mai irin wadannan halin yanzu,idan kana dashi lokaci bai kure ba zanje na sake masu wata Visa ,fatana ta samu sauki……" Aunty Fatee dake zaune ta zaburo tana fadin Abdul maleek kuma?kai jabir wannan ba zancen uwa sae a dauki aurenta a ba driver ,don yayi Uncle Abbah sae su tafi da ita,ko ni da kaina "Wane irin Safeena ta auri da kamawa bane kamar dae bata da yan jinyarta kawae ,Kaga Alhaji ko nayi jinyar ta……" *ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. [5:38AM, 11/5/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU 🌹*🌹*🌹* 🌹*🌹* 🌹* © *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. ( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* ) *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha👌🏻**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Bestowed to Aunty Sis💕**ZAN RAYU DAKE.. 3⃣6⃣ Cikin Sanyin jiki Abban yace " Fateema AbdulMaleeku yana da duk abunda jabir ya fada kuma nima zanso na bashi amanar diyata matsalar kawae shin idan na hadashi aure da Safeena suka tafi ban cuceshi ba? Karaf tayi tace "Ai ko ka cuceshi Alhaji, ae sae duniya ta zagemu mun dauki diya da cuta mun lakaba mashi don kawae yana karkashin mu……" Daga mata hannu yayi yana fadin "Fateema dan Allah idan bara kiyi shiru ba ki koma daki tunda babu wanda ya kiraki ……" Mikewa tayi tana fadin "Wannan ai son kaine ,Kuma wallahi bara ta yiyu ba……" Binta sukayi da kallo har ta shige daki tana gunguni sannan JB yace "Abba ba cuta, har kudi nace zan bashi yayi jinyarta amma yace bara ya karba ba sannan na fada mashi indae aka sa sunanshi to zai aureta kafin su tafi yace ya yarda ,Wallahi Abba yaron yana kaunarku yarda baku tunani ……" "Duk da haka jabir sae naji ta bakinshi sannan……ka kira manshi yanzu yazo……" Ko da Abdulmaleek din yazo Abba ya mashi magana cewa yayi ya amince, dama me neman kuka ne aka jefeshi da tsakuwa , Sai dai baiyi tunanin Abban zai amince da wuri ba haka …… Farinciki Sosae Abba yake da Maleek din ya amince gidan granny yaje ya fada mata ,itama kasa boye murnarta tayi ta fara guda tare da hamdala tana kwarara mashi addu'a ……Safeena kam tabe baki tayi da Abba ya fada mata don ta riga ta san dawon garin sannan ta dauki alwashin ko ta Warke Abdul maleek din ya saketa bara ta koma hannun JB ba……Maryam ta janyo hannunta tana fadin "Ke bama zakiyi farinciki ba Allah ya baki wanda yafi Jabir din " Yatsina fuska tayi tace "ke kina farincikine……" Cikin fara'a ta gyada kai"Sosae besty samun kamar Maleek sae an tona kinga dae drivernki ne amma yana da wadatar zuciya gashi dan gayu ga kyau ga ilimi wallahi ba wanda zai ce baya da kudi ……" Kallonta tayi tace "Yana burgeki ne besty" Yar dariya maryam ta sake tace "duk wanda yace Abdulmaleek baya burgeshi yana bakin cikine ……" Yan mintuna ta dauka tana kallonta sannan tace "Za ki iya aurenshi……" Harara ta watsa mata tana fadin "Besty akwae shirme wa yace maki zan iya aure maki miji……" Hannayenta kamo sannan tace "Besty ba shirme bane Indae kina son Maleek na maki alkawarin da mun dawo zaki aureshi……" Duka maryam din ta kai mata a cinya tana fadin "Sae inyi ya da Ahmad……" Dariya Safeenar ta sake tana tsuke baki "Oh na dauka an ture gwamnatin Ahmadi……" Granny ta shigo tana fadin "Mara kunya ana fada maki kina yatsinawa mutane fuska amma kin shigo daki har da kashewa, dama ni nasan a rina ana son dan yaro ana kaiwa kasuwa……" Harara ta sakar mata tana turo baki tace "Ai duk abunda ba dan Allah akayi shi ba watsewa yake da wuri……"ta karashe maganar tare da murguda baki "Ke dae kika sani ……"cewar granny sannan tayi gaba tana Fadin "Ke kuma Mayyarta sae ki tashi ki je gida ki gaido mamanki ga Abdul Maleek nan zaizo ya tafi dake ……" "Kai granny ina ruwanki ……"cewar Safeena "Kyaleta besty ba komae naji ni mayyarki ce ita kam ko Tayya bata da ita bare mayya ……" Langwabe kai Safeenar tayi "Nima ai mayyar taki ce besty you done much to me……" Granny suka jiyo tana fadin "Haba yarinya biye mata, zata tafi ta barki ki zo nan kina man mashau mashau da ido wae ke Safeena bata nan lokacin zanci kaniyarki wallahi ,kuma ki fito ya ajeki gida tunda baku da hankali ku duka……" Tare suka fito tana rike da hannun Safeenar sannan ta zaunar da ita bisa kujera , Abdul Maleek maryam ta kalla dauke da fara'a "Ompo besty……" ta fada cike da zolaya Dan murmushi yayi yana kallon safeena ta gefen ido ……ta wani hade rai kamar NADIYA DA AHMADI…… "Rabu da su Abdul maleeku za suyi bayani ne gaba kadan ……ka biya gidan Malam ka karbo abunda yace zai baka "Granny ta fada sannan ta mike ta koma daki ,Itama Maryam din fita tayi ta bar falon ,Cikin sanyin jiki ya dawo gabanta tare da zama kasa "Madam kinga ikon Allah ko……" Yar dariya tayi tana fadin "Ikon naira dae Maleek ……" Shima murmushin yayi "Kin san komae kenan " Tabe baki tayi tare da juyar da kai "Zuwa gobe zaa daura mana aure kin yarda da hakan ……"ya fada yana kallon fuskarta "Duk cikin aikin kudinne ka tambayi yardata?Bestyna na jiraka a waje da gurinta ka tafi da ka fi burgeni Maleek ,lastly banyi tunanin kudi zasu saye ka ba har ka yarda da irin wannan wahalar ……" Murmushi yayi mai sauti " In dae kece bana tunanin zanyi wahala Madam, zan iya komae a rayuwata akanki……" "Gyara kalamunka Maleek cewa zakayi indae akan kudine zaka iya komae a rayuwa……" Mikewa yayi yana leken fuskarta "A yarda ku ka tsara kenan Safeena ,amma a sannu zaku san waye Maleek da yarda na tsara nawa labarin Madam ,ba irin karen da kuke tunani bane daga ke har Jabir din ……" ya karashe maganar tare da kashe mata ido ……Saurin janye idonta tayi tana kallon kafafuwanshi…… 《》《》《》《》 A hasale hajiyarsu tace " Uban meye amfaninki da har zaki bari ya yarda ,sannan dan kina banza sae ana gobe daurin auren zaki zo ki fada man, Yanzu uwarki kike so inyi……" Shiru tayi tana kallon fadila dake kwance bisa cinyar Aunty zuby tana kuka, Sannan tace "Wallahi hajiyarmu ba yarda banyi ba amma ya amince mashi ……" Aunty Zuby ta harziko tana fadin " Dallah rufe man baki ,ke ba mace bace dan ubanki ,Wallahi bayan a gida hajiyarmu ta haifeki da sai ince masanya aka mata a asibiti,Ke fadila ta fara fadawa matsalarta amma gabanki aka rushe duk wani plan dinmu ,sannan dan kina wawiya ki kwaso shegiyar kafarki kozai kozai kizo kina fada mana ……" Kuka ta saki tana fadin "To ni Aunty Zuby ya kuke so nayi maku ……" "Ubanki muke so ki mana"cewar Hajiya Cikin gunguni Aunty fatee tace "Sae dae kuyi hakuri tunda lokaci ya kure" "Sae dae Uban kowa ya rasa wallahi Aunty fatee" Fadila ta fada cikin kuka hade da daga hannunwa sama…… "Dallah rufe man baki dan ubanki ,Ina kika kai zoben da boka ya baki……"cewar hajiya "Yo ni nasan inda yake" Fadila ta fada Aunty Zuby ta dago kanta a fusace tana fadin "Tashi ki nemoshi dan bura ubanki yanzu mu koma gurinshi……" Sannan ta mikawa Aunty Fatee hannun "Ke kuma ina kudin da nace ki tahowa da hajiya dasu……" Jikkarta ta bude tana gungune ta fito da rapper ta dubu ta mika mata ,Fizgewa tayi sannan ta ciri kusan rabi ta mikawa Hajiyar sauran ta bi fadila daki "Kin ganshi koko" Turo baki Fadila tayi "Yo banganshi ba mummy,ni fa wannan shegen bokan ba abunda ya iya……" Duka ta kai mata a baki "Dallah rufewa mutane baki sakaran banza uban wa ya hada aurena da ubanki idan bashi ba……" *ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. [5:25AM, 11/7/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU 🌹*🌹*🌹* 🌹*🌹* 🌹* © *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. ( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* ) *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha👌🏻**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Bestowed to Aunty Sis💕**ZAN RAYU DAKE.. DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. 3⃣7⃣ 『 *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*MEENARH PARROT♣ Wannan page din naki ne kyauta 🌹*Don na tabbata ni da ke kadae ne muke_Haske Writer's Association_* ™JB💃🏻*💃🏻*……*ZAN RAYU DAKE.. 』 Neman duniya sukawa zobe amma sam babu alamunshi a cikin dakin, Hajiya tace su bari zuwa gobe sae a fitar da kayan dakin kila wani guri ya makale …… 『』『』『』『』 Abdul maleek kam ko da ya fadawa Baffanshi abunda ke faruwa fatan alkhairi ya mashi ,Wanda dama ya riga ya sani Baffan nashi baya da matsala ,Nana ma kasa rufe baki tayi don murna har ya fita waje ta bishi da gudu tare da riko mashi hannu ta baya ……"Baddi na zaiyi aure" ta fada tana washe baki Dan juyowa yayi yana kallonta sannan yace "Ko bakya so ne Nana" Saurin girgiza kai tayi tana fadin "Ahh baddi ina so mana ,kaga sai in koma gidanka ko? Murmushi ya mata yana fadin "Jeki ki wa inna aiki kinji ko ……" 《》《》《》《》 *ZAN RAYU DAKE..Friday……*ZAN RAYU DAKE.. Bayan an gama sallar juma'a a cikin masallacin liman ya daura auren *ZAN RAYU DAKE..ABDULMALEEK DA SAFEENA*ZAN RAYU DAKE.. Duk da ba wani gayya Abba yayi ba amma daurin auren ya tara dumbin jama'a wanda ko bikin farko bai tara su ba ,yawancin mutanen duk abokan arzikin Abdulmaleek din wanda harda Justice Ahmed kabir tare da VC na yar adua ……Jabir ma baa barshi a baya ba don har dad dinshi sae da yazo gurin …… Yar walima Dad ya hada aka ci aka sha daga abunda ya sawwaka sannan kowa ya watse dob baiyi tunanin daurin auren zai tara mutane haka ba……JB ne yabi bayan Maleek din ganin zai shiga mota ya barshi ,janyo kafadarshi yayi yana fadin "Ba ka ji ana kiranka ba ne" Lumshe ido yayi yana fadin "Oh JB banji ba wallahi ,ina saurine zan gano jikin madam ne duk yau banje ba……" Wani tukukun bakin ciki ya tokare mashi wuya ,ya dage kafada yana wulla mashi wani mahaukacin kallo "Ban yarda ka dinga shishshige mata ba Maleek ……"ya fada a hankali Murmushi yayi mai sauti "Baka san hakkin mace bane akan mijinta?alright bara na fada maka don bana tunanin unguwarku akwae islamiyya ,Madam tana karkashina yanzu dole na kula da ita yarda ya dace ba tare da na gaji ba ……" bai saurare shi ba ya fada mota tare da bata wuta ya barshi tsaye Kallo ya bishi dashi tare da dunkule hannu yana naushin iska ,Dafa bayanshi da akayi ya sashi juyowa da sauri tare da dukar da kai "Abba ina wuni" "Lafiya lau jabir ,ga Dad dinka can baya yana nemanka kaje ka sameshi ……" Abban ya fada tare sa shigewa motar dake kusa da JB din suka tafi da wasu mutane …… Da kyar ya ja kafafuwanshi ya isa gurin Dad din nashi suka koma gida ,A falo ya suka iske Mum dinshi zaune ita kadae ,Dad din shigewa part dinshi yayi ,shi kuma JB din ya zauna falon tare da sake uban tsoki Da sauri Mum din ta kalleshi tana fadin "Kae da wa Son" Tsakin ya kara saki tare da fadin "Mum wannan bakauyen ne man " Tasowa tayi tare da zama hannun kujeran da yake "Me kuma ya maka? "Mum magana ya fada man ,Don nace kar ya shishige mata ,kuma wallahi sae na dauki mataki bai shani banza ba…… " ya fada cikin daga murya "To ai Jabir dole sae ka kauda idonka zuwa lokacin da zai sakar maka matarka ,ka daure kaji ko,karka damu da ta warke zai saketa…… "ta karasa maganar cikin sigar lallashi Yatsina fuska yayi "Mum yunwa na ke ji fa "……Mikewa tayi ta nufi Darea ta dauko mashi trnks na abincinshi sannan ta dawo ta zuba mashi ,Sae da ya fara ci sannan ta nufi gurin dad dinshi…… 《》《》《》《》 Da sallama ya shiga falon amma shiru babu motsin kowa a ciki ,yayi minti goma a tsaye amma ba wanda ya amsa sallamar ,Dakin da Safeena ke ciki ya leka tare da sallama, idonta na kan wayarta ta dago a hankali tana mashi kallon kasa kasa ,sannan ta mayar da hankalinta ga abunda take …… Da murmushi yake fadin "Madam sallamar ma bara ki amsa ba ko?to ai sallama dolene a amsata indae anyita ……" Harara ta sakar mashi ganin yana kokarin shigowa har da su tura dakin tana fadin "Idan a azuciya na amsa fa?ka bude man daki zafi nake ji maleek ……" Murmushi ya sakar mata yana kashe mata idanu "Yi hakuri sai na kunna maki fanka madam ……"ya karashe maganar tare da kunna fankar sannan ya karaso bakin gadon ya tsaya saitinta fuskarta yana kallonta "Wae meye ne kulle Daki kuma ……"ta fada tana bata fuska ba tare da ta dago ba Hade hannayenshi yayi yana fadin "Allah ya baki hakuri don kada kofar ya dinga kara ne naga ana iska ……" Banza ta mashi tana latsar wayarta ,Ganin ba kulashi zatayi ba ya saka shi zama gefen gadon tare da zare wayar a hankali "Meye haka Maleek "ta fada cikin daga murya Yatsanshi ya daura saman lips dinta "Shiii meye na daga murya Safeena ,ko kema baki san matsayin miji a gun matarsa ba ne?ya karashe maganar a hankali tare da langwabe kai gefe guda Dariya ta subuce mata hadi da watsa mashi harara "Fada man matsayin da kake dashi bayan auren kishin wuta kayi ……" Tabe baki yayi yana kashe mata ido "ko……" Gyada kai tayi still tana hararanshi ,Katse maganar yayi ta hanyar tambayarta "kinci Abinci……? "Shafa kaji ……" ta fada tare da sakin karamin tsoki "Wow ina zan shafa Madam……" ya fada yana kanne ido Hararanshi tayi tare da sauko da kafafuwanta kasa ta mike tsaye tana fadin "Idan ka gaji da zaman dakin ka fito ……" bata rufe baki ba ya dagata cak ya nufi hanyar fita da ita yana fadin " Ina zamu koma to madam ……" Mutso mutso ta fara tana fadin "Ka saukeni Maleek dan Allah ……"Wani wahallen kallo ya watsa mata har sae da ya direta falo sannan …… A sanyaye ta bishi da kallo ganin farar Shaddar dake jikinshi tayi staining sossae daukotan da yayi ……A hankali ta dukar da kanta kasa tana kallon carpet , Ganin yanayinta ya sashi dago habarta yana murmushi "Zan samu clean a ciki madam ……?ya fada saitin fuskarta A Sanyaye ta gyada mashi kai "Sorry Abdul Maleek ,sae da nace ka saukeni amma kaki ……"ta fada idanunta cike da kwallah "Kin sani na daukeki ne dole Madam?karki damu kinji ko zan wanke gurin yanzu,Idan naje gida zan canza kayan dama……"ya fada yana sake mata lallausan murmushi …… Mintina kadan ya fito ya wanke gurin, yana fadin "Ina Maryam da Hajiya ne ? "Sun fita" ta fada a takaice "Ok ,ke kin ci abinci ne……?ya fada babu alamun wasa Dagowa tayi da niyar hararanshi amma ya mata kwarjini tayi saurin mayar da kanta tana girgizawa a hankali "Ok kina cin Kebabs na dauko maki a mota ko akwae abinci a kitchen na dauko maki ……" Yatsina fuska tayi tana girgiza kai a hankali "Wane kike so Safeena "ya fada cikin sigar lallashi ……Saurin kallonshi tayi, Yarda yake magana cikin natsuwa da lallashi kamar ba Maleek ba ,Duk da tasan mai ajine amma yau ya sauya sosaae …… "Safeena……" "A kwae a kitchen" ta fada a takaice Da ya ke ya san kitchen din ya shiga ya zubo mata sakwarane da Miyar egusi da taji danyen kifi sosae a ciki ,Dawowa yayi ya daura mata plate din saman stool din dake gefe sannan ya matsar mata dashi gabanta shi kuma ya zauna a kasan carpet tare da harde kafafuwa yana kallonta…… Ji tayi ta takura ,duk yarda taso ta daure kar tayi mashi magana kasawa tayi "Meye kake kallona haka ……"ta fada lokacin da ta kai lomar sakwaran kusa da bakinta "Yi hakuri ……"ya fada a sanyaye bata kuma cewa komae ba har ta gama cin abincin sannan ya dauke komae ya mayar ya dawo "Na taimaka maki kiyi wanka ……? Dakyar ta taushi bakinta daga bakar maganar da take niyar kwabo mashi…… "Kinyi shiru madam ……" "Nagode idan Maryam ta dawo zanyi ……"ta fada fuska a daure Murmushi yayi mai sauti sannan yace "Ba matsala ,ni zan tafi idan Hajiyar ta dawo kice ina gaidata ……" kafin ta bashi amsa ya bata kiss a gefen kumatunta sannan ya fita da sauri don ya tabbata bara ta iya hakuri ba Dariya yayi lokacin da yaji tana fadin " Da ka tsaya mana wallahi duk da bana lafiya sae kasha mari …… *ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. [9:01PM, 11/7/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU 🌹*🌹*🌹* 🌹*🌹* 🌹* DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. © *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. ( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* ) *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha👌🏻**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Bestowed to Aunty Sis💕**ZAN RAYU DAKE.. 3⃣8⃣ 『 💜💜💜💜💜💜』 *ZAN RAYU DAKE..Wannan page din kyautane ga dukka mosayan wannan book din ,nagode da kaunarki gareni*💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* Cikin bacci JB yaji wayarshi na ringing kai hannu yayi ya dauka ba tare da ya bude ido ba "To karamin dan iska shine tun da ka tafi ka gagara kirana ko ,Ga raliyar banzaye ta gama maka amfani ……" Waro ido yayi tare da mikewa zaune tsakiyar gadon yana fadin "Wallahi raliya ba haka bane na dawo gida na iske Dad baya lafiya so hankalina ba kwance yake ba……" Dariya mai sauti ta saki tana fadin "Kar ka gwada man karya JB ……" Cikin kwantar da murya yace "Ba Karya na maki ba raliya ……" ket yaji ta katse wayar ba tare da ya karasa maganar ba ,Tabe baki yayi yana fadin "Wawuyan yarinya zaki tada mutun yana bacci ……" Sannan ya gyara kwanciyarshi ,cikin mintina kadan bacci yayi gaba dashi ……A cikin baccin ne yayi mafarkin Raliyar ta zo mashi cikin wata irin Mummunar siffa tana fada mashi zatayi tafiyar Shekara dari amma da ta dawo zata nemeshi ……Firgigi ya farka yana lalubar wayarshi tare da sake kiran numberta amma switch off ,Yanayin yarda ya ganta tayi bala'in tsoratashi ,A sanyaye ya mike ya fita daga dakin ya koma dakin Mum dinshi ya kwanta sae dae babu alamun baccin da ke tare dashi…… 《》《》《》《》 Ranar da zata su tafi tun da safe Maleek yaje daura gidan Malam ibrahim bayan sun gaisa ne yake fadawa malamin cewa harda tsotsa ke fita yanzu …… A jiyar zuciya malam ibrahim yayi yana fadin _Haske Writer's Association_*"SIHIRIL NAZEEF kenan Abdul Maleek Shi kalar Wannan Sihiri yana aikine kawai Ga Mata ……Bokane Zai turo Aljani zuwa ga matar Ya kuma umurceshi da ya rika Fitar mata da jini ta gabanta, Shi kuma Aljanin nan take zai shiga jikinta a cen cikin Jijiyar jininta (veins)." _Haske Writer's Association_*Manzon Allah (Saww) yace:……"LALLAI SHAIDAN (ALJANI) YANA GUDANA A JIKIN DAN ADAM AKAMAR YADDA JINI YAKE GUDANA".……Ma'ana: Yana iya shiga duk inda jinni zai shiga, saboda bashi da gangan jiki da zai hana shi yin hakan. Imamu Bukhari da Muslim suka ruwaito shi (An-Nawaawi, 14/155).……A wani Hadisin Kuma na Imamu Bukhari; Lokacin da Hamma bint Jaash ta tambayi Manzon Allah (saww) game da tsawaitar zubar Jinin (prolonged bleeding) a lokacin haila, Sai Annabi (saww) YaCe, "WANNAN YANA DAGA CIKIN MAKIRCIN SHAIDANUN ALJANNU"……(Imamu At-Tirmidi, da Imamu Bukhari suka Ruwaito Shi).……Imam Ahmad Ya fitar da wani hadisi Cewa, Annabi (saww) YaCe, "FITAR JININ HAILA WANDA YA WUCE QIMA YANA DAGA CIKIN SHAIRIN SHAIDANUN ALJANNU".……(Imam Ahamd da An-Nasa’i suka ruwaito shi).…… Duka wayannan hadisan suna nuna mana Cewa duk fitar jinin da ya wuce Qima na haila to akwai sharrin aljannu a ciki Don haka Zan baka Ruwan Zam-Zam dana karanta ayoyin Rukiya a ciki abawa Safeenar ta rika yin alwala da su tsawon kwana 3……Haka kuma ta rika shan wayannan ruwan sau 3 a rana tsawon kwana 3, In shaa Allahu za'a dace.……Sannan idan ka fita ta nemi *ZAN RAYU DAKE..HABBUR RASHAD,FIJIL,KUSTUL HINDI ,HABBATUS SAUDA ,GARIN FUREN ALBABUNAJ*ZAN RAYU DAKE.. Sai a debi cokali uku na kowane a hada da zuma ta dinga sha kullun ……_Haske Writer's Association_* "To ina zan samesu malam……?ya tambaya cikin kwantar da kai "Da kaje islamic chemist Abdul Maleeku zaka samesu duka insha Allahu ……" Godiya yayi sannan ya mike suka fita tare har gurin motar Malamin ya rakashi tare da mashi fatan Alkhairi sannan ya dawo …… Sae da ya biya gidansu yawa Baffa bankwana sannan ya biya islamic chemist ya hado duk abunda Malam ya fada mashi sannan ya dawo gidan Granny din, a can ya iske Abba Suna magana da ita …… Bai samu ya mata bayanin ba ……ya tsaya suna magana da maryam tana zolayanshi wae tunda aka ta bashi bestynta bai kuma zuwa ba …… Dariya yayi yana kallon Safeena yace "Ki tambayi bestyn taki idan banzo ba……" Juyawa tayi tana kallonta "Wae besty yazo? Harara ta sake mata tana fadin "Ban sani ba……" "Allah ya baki hakuri besty yau fa zaki tafi ki barni amma shine kike man haka ……"ta fada cikin sanyin murya Dan kallonta tayi taga ta mata kallar tausayi tace "Yazo fa besty mantawa nayi ban fada maki ba sorry……" Shima hararan Safeena yayi "Madam bara ki man ne ……"ya fada cikin zolaya magana ba ko? ,ko sae munje can Banza ta mashi tana fadin "Besty dan Allah ki saka man wancen littafin a jikkana dashi zan tafi ……" Abba yace su fito a tafi ,kuka sosae suke ita da Maryam da Abban yace bara a tafi da maryam din ba ta rakata ……Dakyar aka fidda safeenar daga jikin maryam din sannan suka tafi daga Su sae Abban ……ko A Airport din ma Ko bankwana Abba baiyi da safeenar ba ya juya ya tafi…… Rungumeta Maleek yayi a jikinshi yana lallashinta……Daga bayansu suka ji Muryar JB na fadin " Wane irin iskancine haka Abdul Maleek……" Su duka suka juya cike da mamakinshi ashe har nan ya ya biyosu ,Dan waro ido Maleek din yayi yana fadin "Me ke faruwa Jabir ……? Cikin daga murya yace " Baka san abunda ke faruwa ba kenan ,to saketa karamin mara kunya……" Dafe kai yayi yana leken fuskarta "Oh Sorry madam ,Sorry Jabir ,na manta cewa kayi na kula da ita sossae ,na fahimci laifina bai kamata na barta tana tafiya ba ……" yana rufe baki ya dagata ya daura saman kafadarshi ya nufi Wroom da ita …… "To the hell of you thug fox……"JB ya fada cikin daga murya yana nunashi Duk da yaji zafin zagin amma bai juyo ba sae da ya ajeta sannan ya zauna gefenta tare da dafe kanshi da duka hannayenshi …… Hakanan ta ji bata ji dadi ba ,Ahankali ta dafa bayanshi tare da fadin "Sorry……" Kallonta yayi yana murmushi sannan ya zagaya da hannunshi saman kafadarta tare da daura kanshi bisa dayar kafadar ya lumshe ido …… Suna a haka har a ka kirasu suka mike yana rungume da ita har suka shiga…… A cikin jirgin ma duk wani motsinta a idonshi takeyi har bacci ya dauketa ta kwanto saman kafadarshi …… *ZAN RAYU DAKE..MILLENIUM AL AQEEQ MEDINA HOTEL*ZAN RAYU DAKE.. Anan suka sauka anan gab da fara sallar Magrib ,room 12 floor 2 …… Zaunar da ita saman kujera yayi sannan ya duka yana cire mata takalman kafarta ……Sannan ya dago yana sakar mata wani irin sassanyan kallo , Dole yasa ta saki murmushi tare da kawar da kanta gefe …… Peck ya mata a goshi "Zanje sallah ,I'ld be back soon……" Murmushi kawae tayi ba tare da tace komae ba ,shi kanshi bai damu ba ,godiya ma yake da murmushin da ya samu ,Har ya kai bakin kofa ya juyo yana fadin "Tsara ban me kike so ……" "Addu'a"ta fada a takaice "Wannan dole ce ,banda ita ……abinda zaki ci……"ya fada yana kokarin gyara ID card dinshi dake kokarin tona mashi asiri Dan Waro ido tayi "A mosque din" Gyada kai yayi yana fadin "Yeah ke dae fada" "Nothing……" ta fada tana tabe baki "Sae kin fada " ya karashe maganar tare da dawowa kusa da ita "Fadaman please……" "Bana bukata fa……" ta fada tana bata fuska "Dan Allah ……" Banza ta masa tare da jinginar da kai gefe guda "Tunda bakyaso lemme kiss your lips sae na tafi ……" harara ta sake mashi ,ganin ya zauna saman cinyarta tare da dago kanta ya sata fadin " Pistachio……"da sauri tana runtse ido "And ……? ya fada yana kashe mata ido "Ice cream ……" "Sae me……" "Shikenan ……" ta fada tana murmushi "Good……" ™ *ZAN RAYU DAKE..JB😛😛*ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. [5:10PM, 11/8/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU 🌹*🌹*🌹* 🌹*🌹* 🌹* © *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. ( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* ) *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha👌🏻**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Bestowed to Aunty Sis💕**ZAN RAYU DAKE.. 3⃣9⃣ Yana fita ta mike da kyar ta shiga toilet ,Sae da tayi wanka sannan ta tsaya tana wanke kayanta da su ka baci ,Muryarshi taji yana fadin "Twee……" Tabe baki tayi tana fadin "Sabon salo ……" Jin karar ruwa ya sashi shiga binta toilet din ,Waro ido yayi tare da karbar kayan da ke hannunta yana fadin "Twee meye kike haka……? Kallonshi tayi tana fadin "Me ka gani……" Kamo hannunta yayi yana fadin "Kar ki sake kin ji ko I'ld do anything for you…… Bara na kawo maki wasu ruwan kiyi alwala kin ji ko ……" Gyada kai

Chapter 9 of 16