Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kafar tayi tana fadin "Mumy ai ke kika ja kanki da kin tsaya da kafarki bata ji ciwo haka ba……Amma shine kika fito ki ka baroni wato duk abunda zai faru dani ya faru ko?Allah ya kara ai……"ta fada har lokacin tana amai Juyar da kai Aunty Zubyn tayi tana hawaye ba tare da tace komae ba …… Dakyar Fadila ta mike ta je bakin titi ta samo wani mai mota aka dawo aka saka Aunty Zubyn sannan suka tafi gida …… Tsaki mai motar yayi lokacin da fadila ta fita yana fadin "Haba hajiya kin san kina da matsala kuma sae ki zauna man gaban mota ……" Kallon gurin tayi sannan ta kalli bayan rigarta tare da sakin tsaki " Sae ka aje motar kaga idan ba'a wanke maka ba banza jarababbe sae kace ba cikin jini uwarshi ta haifeshi ba……" Cike da mamaki yace "Daga taimako ……? Bata jira shi ba tayi cikin gida ta bar Aunty Zuby da mai motar ya fiddo ya juya ya tafi yana yaba rashin kunya na fadilan…… Asibiti aka kaita Cewa akai kafar barata ta gyaru ba sae dae a yanketa gaba daya ……A sanyaye hajiyar tace a yanke …… 《》《》《》《》 A kaduna suka sauka …… Sannan suka kira Number Abban ya fada masu room number da yake …… Safeena na ganinshi ta kwace hannunta daga na Abdul maleek ta nufeshi da gudu ta rungume tana kuka …… Shima kanshi Abban kuka yake kamar karamin yaro …… Abdul maleek dinne yayi jarumtar lallashinsu har sukayi shiru ……sannan Abban yace su tafi Katsina su sauka gidanshi …… Ya fada mata inda ya jefa keys din da inda takardun suke yace ta dauke…… shima yana nan zuwa nan da dan lokaci kadan …… Mota daya suka dauka daga ita sae shi a baya …… Hancinta yaja da karfi ganin tunda suka baro gurin Abban bata mashi magana ba …… Yar kara ta saki cike da shagwaba sannan ta kwantar da kanta a kafadarshi tana hararanshi kasa kasa …… "Twee nayi laifine ……? Banza ta mashi ta lumshe ido kamar tana bacci ……Hannu ya saka ya shafi gefen wuyanta a hankali tare da mintsinawa …… "Biyu kenan ……"ta fada bayan ta saki yar kara "Ke ce Twee kinki kulani ……"ya fada tare da kwantar da kanshi saman kanta "Shine sae ka mintsine ni ……"ta fada a hankali "To yi hakuri……" Shiru ta masa ganin driver ya maido hankalinshi kansu…… 【】 Kamar yarda Abban ya fada gidanshi suka sauka harda Abdul maleek ……da yake darene babu koma kofar gidan yana rike da hannunta har tsakiyar falon …… Hannunta ya saki ganin Aunty fatee tana saukowa daga saman benen tana waya ……,Kallonshi Safeena tayi tare da matsawa sosae jikinshi …… Aunty Fateen bata lura dasu ba har sae da ta sauko falon sannan ta lura da safeenar…… tayi saurin datse wayar tana kallon Safeenar cike da tsoro …… "Ke Safeena ke ce ……"ta fada arude tare da nunata da hannu …… Kwantar da kai tayi tana jefa mata kallo sannan tace "Na canza maki ne……" Kuka Aunty Fatee ta saki tana fadin "Baki canza ba Safeena ……" Tabe baki tayi tana kallon Abdul maleek …… Kusa da Ita Aunty Fatee ta matso cikin kuka tana fadin "Safeena Asirin mu ya tonu Allah ya dauke mana Alhaji Safeena kaiconmu Diyata……" "Kaiconki dai Aunty Fatee ……Ubanki ya rasu ……to meye a ciki idan Abbana ya rasu?Allah ya ji kanshi ……"ta fada tare da jan hannun Abdul maleek suka shiga dakin Abba dake bude …… "Shiga ki gani wallahi da gaske nake Safeena ya rasu ……"Cewar Aunty fatee tana jan majina …… Rufe kofar sukayi ……Wani bakin ciki ya tare mata makoshi ganin an watsa komae na dakin da alama takardun ake nema …… Girgiza kai tayi a hankali hawaye suka biyo mata a kumata "Shiiii ……"ya fada tare da daura hannunshi saman lips dinta Hadiye kukan tayi ta koma ta zauna tana kallon Abdul maleek dake kokarin janyo Mirrow …… Aunty Fatee kam suna shiga dakinta tashiga ta kira Hajiyarsu amma har ta kare ringing bata dauka ba ……JB ta kira cikin saa yana kusa da wayar ya dauka "Safeena ta dawo kuma ta warke Jabir ……"Abunda ta fada kenan ta datse wayar sannan ta fito waje …… Fitowa sukayi dauke da jikka A hannun Abdul maleek ……da sauri Aunty Fatee ta tare tana fadin "Ina Zaki da ita Safeena meye kika kwaso ……? "Kudinsa ne da takardunsa ……"ta fada kai tsaye Cikin rudu tace "taya zaki kwashe kudin bayan bake kadae ke da gadonsa ba……"ita kanta Aunty fatee ji tayi kamar an fizgo maganar daga bakinta …… "BARRISTER ABDULMALEEK AHMED……Lauyan Alhaji ina da hurumin da zan kwashe duk wasu kaddarorinshi tare da sa hannun kuto har zuwa lokacin da zaa raba maku gadon……" Abdul maleek ya fada tare da fito ID card dinshi dake dauke da kyakykyawan hotonshi cikin rigar lauyoyi…… Amsar ID card din tayi ta buda ,bata yi mamaki ba tunda dama tasan Barrister ne tun da dadewa ……mika mashi tayi ta juya a sukwane ta koma daki …… Kallon Safeena yayi da ta bude ido da baki tana kallonshi ……kunnenta ya kamo ya rada mata "Duk burga ce Baby ……" Dariya tayi don ta yarda burgarce sae dae ID card din da ya nuna fa? Dakinta ta shiga ta dauko makullin motarta don tun lokacin da maigadi ya batashi tare da takardar da yace Abdulmaleek ya bashi bata kuma bi ta kanshi ba…… Mika mashi keys din tayi suka bar falon …… A Mota ta kalleshi a hankali tace "Ina ……" Katse ta yayi yana fadin '"Ina na samo ID card ko……? A hankali ta gyada mashi kai tana kallonshi …… "Copy ne jiya da muka sauka nasa aka man printing tare da lamination ……"Sannan ya kalleta yana fadin "Muje gidanmu mu kwana ko? Dan murmushi tayi tana gyada kai …… Bayan yayi Parking kofar gidansu ya juyo da murmushi a fuskarshi yace "Kinga gidanmu Madam ……zaki iya kwana kuwa? Hararanshi tayi tare da bude marfin motar ta fita ……bin bayanta yayi har ta shiga zauren ya riko hannunta yana fadin "Sae ki baroni Twee……" Banza ta mashi tana kokarin zame hannunta daga cikin nashi ……a kunnenta ya matsa yace "Sorry……" Fuska a daure tace "Ka gyara maganar da kayi sannan ……" …… Lumshe ido yayi sannan yace " Safeenata zata kwana gidan Baffana ……"ya fada cikin wata irin murya …… Kallon juna sukayi tare da murmushi lokaci guda wanda su kadae suka san fassararshi…… Inna sahu ta karbeta hannu bibiyu ……sae da suka zauna sannan yace bara yaje ya dawo ,Jikkar gaba daya ya aje bayan dakin Baffa cikin kejin kaji sannan ya daura buhunnan taki a sama tare da tsummuna…… Ya Tabbata tuwon dawa inna sahu tayi ……Fita yayi ya sawo mata Chips da Tabouleh gefe guda …… Sannan ya dawo ya iske har Inna sahu ta kawo mata tuwon da miyar kuka tsanwa shar da ita bata fara ci ba ……Suna fira da Nana da tunda ta dawo ta gane Safeenar ta makale mata …… Gabanta ya aje sannan ya zauna yana kallon yarda ta sha kunu tare da janyo langar tuwon ta fara ci ……Bai ga fuskar cewa taci abunda ya sawo mata ba Har taci tuwon ta koshi ba tare da ta kalleshi…… 【】 JB yana kwance da sabuwar yarinyarshi Aunty fatee ta kirashi …… Mikewa yayi zumbur yana kokarin mayar da rigarshi ……Yarinyar da ta riga tayi nisa a bukace take dashi tayi saurin riko hannunshi…… "Baby ina zaka please……?ta fada idonta a lumshe "Sorry baby…… Feenata ce ta dawo yau zanje na ganta ……"ya fada yana kokarin daukar wayarshi "Karka man haka Jabir wallahi a bukace nake kaima ka sani ……"ta fada idonta cike da kwallah …… Hannunshi ya fizge yana hararanta "Meye nawa a ciki ……" "Da kasan zaka man haka da baka tado man da feelings ba ,dan Allah ka taimaka man karka barni haka JB……"ta fada hawaye cike da idonta Kallon uku saura kwata ya mata tare da fiddo kudi cikin wallet dinshi ya aje mata "Duk yarda zakiyi kiyi ki samu natsuwa ……dama na fada maki inada wadda nake so kuma ta dawo …I wishes you all the best baby………" Girgiza kai tayi a hankali tana kallonshi har ya bar dakin sannan ta mike tsaye saman gadon tana girgiza ……Maciji ta koma bakikkirin tare da silalewa ta window ta fita …… *ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. [4:52AM, 11/13/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU 🌹*🌹*🌹* 🌹*🌹* 🌹* © *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. ( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* ) DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha👌🏻**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Bestowed to Aunty Sis💕**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..SISTER SAWWAMA HERE'S YOUR CHPPY DEAR ENJOY❣**ZAN RAYU DAKE.. 4⃣6⃣ Gurin Aunty Fatee ya wuce a tunaninshi Safeena tana gidan ,Ko gaisawa basuyi ba ya tambayeta "Ina Feena din ……? Tabe baki tayi tana fadin "Sun fita amma na tabbata gidan hajiyarsu ta tafi ……" Mikewa yayi yana fadin "Bara naje can na samesu ……" bata ce mashi komae ta sae binshi da kallo da tayi …… A gidan Granny ma wayam ya iske don cewa tayi bata san ma sun zo ba …… Wayar Safeenar ya kira amma a kulle…… Ta Abdul maleek din ma a kulle ,karamin tsoki ya ja sannan,ya mike ya fita ba tare da bankwana ba …… Da kallon Mamaki granny ta bishi a ranta take fadin ……Meye ruwanshi da dawowarsu zai rude haka …… A Bakin motarshi yaga budurwar da ya baro ……tsaye tana jiranshi karasa yana fadin "Uban me kika biyoni na maki anan……? a fusace ya Shiru ta masa tana kallonshi …… "Nonsense ……"ya fada tare da bude motar zai shiga …… Rike hannunshi tayi tana fadin "Kaine mutumin da ka fara kusantata Jabir …kuma dole ka aureni…" Dariya ya sake yana fadin "Amma baby baki da hankali taya zan iya auren macem da na kusanta a titi? "Amma kasan kaine mutumin da ka kauda man budurci ko……? "Wannan ba abunda ya shafeni bane Baby na maki dole ne……ko ba ke kika kawo kanki ba……"bai jirata ba ya shige mota ya barta …… 《》《》《》《》 Sae da yayi wanka ya shirya cikin riga da wando sannan ya shigo gidan ……duk tunaninshi bata tashi ba yanzu amma yana kutsa kai ya ganta tana wanke wanke Nana na mata dauraya Bata fuska yayi sosae sannan ya karasa gurin yana hararan Nana ……babu shiri ta mike ta bar gurin …… Kafarshi kawae ta kalla ta cigaba da abunda take ……Ganin tsakar gidan ba kowa ya sa ya Dagota karfi yana hararanta …… Turo baki tayi tana hararanshi kasa kasa tace "Meye haka ……? "Ki wuce ki koma daki ……"ya fada babu alamun wasa a fuskarshi Kallonshi tayi sannan ta dauke kai tare da komawa ta cigaba da wanke wankenta …… Daki ya shiga ya dauko mata hijab dinta tare da jikkar kayansu sannan ya fito yana fadin "Inna mun tafi zan maidata gida ……" Inna Sahu ta fito tana fadin "Da safe haka Abdul maleek ka tsaya a kawo mata koko mana wallahi tun dazu na aika a sawo mata basu dawo ba……" "Hajiyarta ta kirani yanzu idan munje can tayi kalacin ……"ya fada tare da daura mata hijab din saman kafadarta yayi gaba …… A sanyaye ta bi bayanshi ,inna sahu ta biyota tana mata addu'ar a sauka lafiya …… Bayan motar ta bude ta shiga tana turo baki ……Bai ce mata komae ba ya tada motar……Har sae da yayi parking Layout gaban wani katon gida ……Sannan ya juyo yana kallonta na yan mintina "Twee Fito muje ……" Ba ta dago kai ba haka bata tanka ba ……Bude motar yayi ya fito ya dawo bayan ya zauna tare da kamo hannunta …… "Twee Dan nace ki bar wanke wanken shine kike fushi ……"ya fada a hankali Banza ta mashi tana kallon kasa…… "Kin taba yin wanke wanke a rayuwarki safeena ……? Kallonshi tayi a hankali sannan tace "Idan ban taba yi ba sae aka ce maka ban iya ba kuma……? "Allah ya baki hakuri ……mu shiga ciki, Tunda Asuba JB ke kirana ……Na fada mashi yazo nan ya iskeni ……" Kallonshi tayi tare da fadin " Gidan waye nan ? "Gidan da JB ya bani ne Safeena ……"ya fada yana kallonta "Kenan zaka sakeni……? ta karashe maganar kasan makoshi Kallonta yayi na yan mintina sannan ya bude motar tare da jan hannunta suka fita ……Kamar yarinya take binshi tare da kallonshi har suka shiga wani katon falo sannan ya zaunar da ita yana lumshe ido …… Kujeran kusa da ita ya zauna ……Ya fito d a Envelop guda biyu daga cikin aljihunshi ya aje saman hannun kujeran tare da mayar da kanshi ya kwantar …… A Sanyaye take binshi da kallo tare da karewa ilahirin falon kallo……Sam hankalinta baya ga tsaruwar falon yana ga Envelop din da Abdulmaleek ya aje …… Wayarshi tayi kara ya dauka tare da fadin "Kashigo……"a takaice ……Sannan ya juya ya kalleta tare da mikewa ya koma saman hannun kujeran da take …… "Ko kina sona Safeena……? ya fada kamar yana mata rada …… Duk da faduwar da gabanta yayi hakan bai hanata sake mashi harara ba tana fadin "Bana sonka ,idan ka tashi kaman saki dari …Hakan ba zai sa na koma hannun JB ba" Yar dariya yayi tare sa kissing goshinta don ya gano tsatsar kaunarshi a idonta "Sha kuruminki Twee uku kadae zan maki ,amma ki daure ki koma gurin JB kinga kudin da ya bani fa suna da yawa sannan ga katon gida……Dan Allah madam bai burgeki ba…… sae dae ban sani ba ko bakin ciki kike man ……" Karamin tsaki ta saki tare da mikewa tsaye tana fadin "Idan na san wannan abun zakayi da ban biyoka ba ……bani takardar na tafi……"ta fada tana mika mashi hannu Dariya yayi yana fadin "Twee ki bari ya zo man na damka mashi amanarshi a hannu mana……" Bata saurareshi ba ta nufi kofar fita…… bin bayanta yayi yana dariya da envelop din yana fadin "Allah ya baki hakuri Twee ga takardar taki……" A fusace ta fizge envelop din subuce mata …… tayi gaba tana kokarin danne kukan dake niyar Aharabar Gidan sukayi karo da JB ……kamar sakarai ya saki baki yana kallonta tayi wani fresh da ita "Beaut……"ya fada yana shafar sumarshi…… Ganinn hawaye a idonta ya sashi fadin "Meye na kuka Fennat?Ke da ya kamata kiyi farinciki *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU DAKE*ZAN RAYU DAKE.. yanzu baby……" Kallon da ta watsa mashi ya makale sauran maganar……sae da ta fito titi sannan ta samu abun hawa …… Gidansu Maryam ta nufa kai tsaye…… 【】 "Good Job……"JB ya fada tare da mika mashi hannu…… Murmushi yayi mai sauti sannan yace "Ka ganta ne ……" "Yeah na ganta da takardarta a hannunta yanzu da zan shigo ……Naji dadi sossae Abdul maleek kayi man abunda banyi tunani ba …… " "Eyeh ……Karka damu " ya fada tare da daukar wayarshi yana latsawa "Ina Copy na takardar da ka bata? Envelop din dake aje ya mika mashi hankalinshi naga wayarshi …… Karba yayi ya aje sannan yace "Sae dae kayi hakuri Abdul maleek wallahi kudin da nace zan baka basu samu ba……dama companyn mu na sayar to har yanzu ba'a bamu kudin ba sae zuwa karshen month dinnan zan turo maka ……" Yar dariya ya saki yana fadin "Karka damu" Dariyar mugunta yayi sannan ya bude envelop din ya fito da takarda guda biyu ta sama an yi rubutu dan gutun :【NI ABDULMALEEK AHMED BAWA BAN TABA TUNANIN ZAN IYA SAKIN MATATA SAFEENA BA ……INA MATUKAR KAUNARTA TA YARDA BAZAN IYA RAYUWA BABU ITA BA ……MALAN JABIR GA CHEQUE DIN NAIRA MILLION 20 NAN NA LINKA MAKA KUDINKA…… KA BARMAN SAFEENA MU KARE RAYUWA DA ITA……】 Wata wawar shakara ya wa Abdul maleek din yana fadin "Wallahi baka isa! sae ka sake man Matata ……" Tunkude JB din yayi yana fadin "A tunaninka kowa wawane kamar ka Jabir?Tun ina shekara biyu nake zuwa islamiyya kuma har yanzu ban daina zuwa neman ilmin ba ……Malan jabir ko da na auri Safeena banyi niyar sakar maka ita ba saboda ina mata son da kai baka mata…… kasan meye AUREN KISHIN WUTA?na tabbata amsar bata wuce aa ……to Abdul maleeku yasan me ake nufi AUREN KISHIN WUTA sannan yasan meye makomarsa ……Kana fadin *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU DAKE*ZAN RAYU DAKE.. amma ka kasa jinyarta na dan lokaci ……a hankan zaka rayu da ita Jabir?Sannan saboda batan basira ka rasa wanda zaka ce ya auri Safeena sae Ni Abdulmaleek ?har ma na maka jinyarta ta warke sannan na sakar maka ita kamar wani sakarai?………Kasan tsawon shekaru nawa na dauka ina lallashin soyayyarta Jabir?Sannan na sameta cikin sauki na saketa kamar wani mahaukaci sabon kamu?zauna kayi tunani da kyau JB……" Kara shakareshi yayi yana nushinshi da karfi…… "Wallahi sae dae mu duka mu rasata……" abunda yake fada kenan …… Tun Abdul maleek yana kokarin kauce dukan da JB ke mashi har ya fara ramawa ganin abun ba mai karewa bane …… Dambe sukayi sossae kamar bara su rayu ba ……sae da suka daku dan kansu sannan suka rabu kowane ido kamar garwashi…… JB ya nunashi a harzuke yana fadin "Wallahi sae ka sake……" "Wallahi baran saketa ba……" *ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. [5:35PM, 11/13/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. 🌹*🌹*🌹* 🌹*🌹* 🌹* © *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. ( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* ) *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha👌🏻**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Bestowed to Aunty Sis💕**ZAN RAYU DAKE.. 4⃣7⃣ "Mu zuba mu gani ……Waye ubanka a garinnan?me kake takama dashi……?cewar JB din "Ba wanda nake takama dashi sae kaina ……Uba kuma bandashi ,kai kuma da kake takama da ubanka ,zamu gani idan ya isa ya sani sakin Safeenah……" "Safeena tawa ce ,idan ba haka ba kowae zai rasa……" "Kaine ka rasata JB……" A fusace JB ya bar Gidan yana fadin "Kowa zaya rasa wallahi babu wanda ZAI RAYU DAKE SAFEENAH……" Banza yayi dashi ya zube saman rug yana mayar da numfashi ,tun tasowarshi bai taba dambe irin haka ba ……Dan karamin tsaki yaja sannan ya mike ya shiga dakin dake kallon falon …… Toilet din ta bude ya sakarwa kanshi ruwan zafi na tsawon awa saya sannan ya fito ……Allah ya taimakeshi ya aje kaya a gidan ya dauka ya saka sannan ya shigowa da Safeena motarta ya fita da tashi …… Gidansu ya koma ya dauko jikkar da ya aje bayan dakin Baffa sannan,ya kaita bank ya aje ya wuce office dinsu …… 《》《》《》《》 Fadila ta kalli Aunty Fatee tana fadin "ni fa Aunty fati ba lokacin period dina bane amma sae bleeding nake ……" Kallonta tayi tace " Ko dae kin manta lissafine……" Tabe baki tayi tana ware kafada sannan ta kalli hajiya dake zaune gaban,gadon Aunty Zuby tace "Hajiya har kin karbo test din……? Girgiza kai tayi tana fadin "Sunce idan idan,sun fito da result din sister baraka zata kawo mana ……" Da sauri Aunty Fatee tace " Wae hajiyarmu tun yaushe baki jin dadin ni ban sani ba……" Hararanta tayi tace "Dama yaushe zaki sani tunda rabon da na ganki tun bayan rasuwar mijinki kina can kin saki baki ,takardun ma kinki ki nema……" Ta bude baki zatayi magana Sister baraka ta shigo rike da result din ……Aunty fatee ta karba tana dubawa ……lokaci guda ta saki kara tana fadin "CIKI HAJIYA……"Uban kuka ta saki tana cigaba da fadin HIV/AID :Positive HEPATATIS:Positive Shikenan mun shiga uku Hajiya mun lalace …… Yanke jiki hajiyar tayi ta fadi a sume …… A Yashe aka dauketa aka bata gado …… Kusan awa daya ta farka sae dae barin jikinta baya amfani ,a rude Aunty Fatee ta je ta fadawa Nurse din suka shigo tare …… Duk Wani test da zasu mata su kayi suka tabbatar da paralysis ya kama hajiyar …… Ko da ta farka da "Na shiga uku ni Shafa ……Ina na samu Ciki" ta bude ido "Gurin Boka" Aunty zuby da ta farka lokacin ta fada tana kuka …… Aunty Fatee ta saki kuka tana fadin "Muke da shiga uku Hajiyar ace uwarmu da cikin shege……" Fadila kam mikewa tayi ta shiga toilet tare da cire dankwalinta ta linka ta sa sannan ta yarda pad din ganin pad din bata mata wani amfani sannan ta fito ta zuba masu ido suna koke kokensu…… 【】 Safeena kam tana isa gidansu maryam ta iske Mum dinsu a falo…… Da sauri ta tare ta rungumeta tana mata ya hanya cike da tausayi Kuka ya kwace mata ,Mum din ta fara lallashinta tare da bata baki ,don duk a tunaninta Rasuwar Abban nata takewa kuka…… Kwala maryam kira tayi ta fito ……ai kuwa makalkale Safeenar tayi kamar zata kadata ……sannan ta jata dakinta ta rufe kofa tana fadin "Besty karya suke maki Abba na raye na wallahi ……"ta fada lokacin da ta zaunar da Safeenar saman gado Cikin kuka tace "Na sani besty……" Idon maryam din ya ciko da kwallah ganin Safeenar na kuka tace "Baki warke ba besty? *ZAN RAYU DAKE.."Na warke"ta fada cikin kuka "Besty so kike nima nayi kukan ,Dan Allah kiyi shiru kin ji menene to? "Abdul maleek ne besty……" Da sauri maryam din tace "Wani abu ya sameshi ……" Takardar ta mika mata tare da komawa baya ta kwanta …… Sae da ta gama karantawa sannan ta kalleta tana fadin "Ashe baki da wayau besty……" Da sauri ta mike tana kallon maryam din …… Daure Fuska maryam ta kuma yi tana fadin "Yeah ban taba sanin baki da hankali ba sae yau Safeena ,da mutuncin Abbanki kike neman ki zubar mashi dashi a idon Abdulmaleek……meye ribarki idan kinyi auren kisan wuta kin koma hannun jabir? Abun kunya ma Safeena har da yardarki ……ya kike tunanin idan Abbanki yaji kinyi aurene idan kika warke ki koma gidan jabir saboda shi,bara ya iya jinyarki ba sae Abdul maleek ko besty ?drivernki dake karkashin Mahaifinki ……to bara kiji wallahi Abdul maleek babban barister ne hakanan ya cigaba da kaiki makaranta …… kuma wallahi Safeena indae har Abdul maleek ya sakeki ki manta da ni maryam a rayuwarki……" Kuka take tana fadin "Wallahi maryam bance ya sakeni ba shi ya bani takardar yanzu ,kuma wallahi banyi niyar na rabu dashi ba haka banyi niyar na aureshi bayan na warke na ya sakeni ba ,Shin banda wayau ne besty koko ban san banbancin SO da SHA'AWA ba Besty ……Abdul maleek ke Sona kuma ina ina sonshi ……jabir kuma sha'awata yake ni kuma sha'awarshi ki fahimceni mana ……" Duk yarda maryam din takai ga daurewa amma ta kasa ,rungume Safeenar tayi tare da sakin kukan itama ,don ko kadan bata son abunda zai shafi kawartata ……duk wani farinciki na Safeena tana fata su rabashi biyu ……haka duk wani bakin ciki,nata tana fatan a rabashi uku ita ta dauki biyu …… Sae da suka ci kukansu sannan Maryam din ta koma tana lallashi Safeena "Dan Allah kiyi shiru wallahi wasa nake baran iya rabuwa da ke ba kinji ……" Shirun tayi tare da kallon maryam din tana fadin "Na sani besty kawae ina kukan,na batawa kawar da tayi Shekara biyar tana raba duk wani,bakincikina ta dauka ,sannan kawar da ta man abunda babu wani mahalunkin da ya kwatanta man shi a rayuwa……Dan Allah ki yafe " Dariya maryam din tayi sannan ta janyo takardar tana karantawa da karfi 【Safeena ko da yarda na aureki banyi niyar na sakeki ba bayan kin warke ,Wallahi na aurekine don na RAYU DAKE Har abada ……Dan Allah Madam ki karbeni a matsayin miji ko da baki son haka wallahi nafi dacewa dake a rayu nafi Jabir Kaunarki nesa ba kusa ……ki yarda dani Safeena ina maki wani irin So mai wuyar fassara na maki alkawarin bara ki taba kuka dani ba……Tun lokacin da na fara ganinki a bikin beeba na fara sonki dabi'unki da komae naki abun burgewa ne gareni safeena……nayi farinciki sosaae da mahaifinki ya daukeni a matsayin driverki sannan nayi bakinciki lokacin da naji zakiyi aure ……Dan Allah KI YARDA DANI Ina matukar kaunar ki Safeena…… ……by 8:00pm zan zo na daukeki mu dawo gida kinji ko ……Much love 】 Fizge takardar tayi ta fara yagawa tana fadin "Wallahi sae na rama……" Dariya maryam din tayi sannan ta mike da debo mata abinci ta kawo mata …… 《》《》《》《》《》 Sae da harka tayi nisa sannan Uncle Abbah ya fara kokarin wando …… Wata uwar zabura yarinyar tayi tare da mikewa tsaye tana kallon PPart dinshi "Kutmar can a hakan da kake kokarin shigata……" *ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. [4:53AM, 11/14/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU 🌹*🌹*🌹* 🌹*🌹* 🌹* © *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. ( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* ) *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha👌🏻**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Bestowed to Aunty Sis💕**ZAN RAYU DAKE.. 4⃣8⃣ Wata uwar zabura yarinyar tayi tare da mikewa tsaye tana kallon PPart dinshi "Kutmar can a hakan da kake kokarin shigata……" Janyota yayi jikinshi yana fadin "Haba Baby kamar wata yarinya da Allah ki tsaya mana wallahi yau set na gold zan baki……" "Uwar Gold zaka bani Abbah ……ka mayar dani yar iska da wannan kazantar zan tsaya ka shigeni lallae baka da hankali……" PPart din ya kallah tare da mikewa zumbur yana kallon gurin ……wasu kurajene suka feso jawur dasu ga gurin ya tsatstsage yana fitar da jini kadan kadan …… Kallon gurin yake a tsorace ,duk da ya san akwae kuraje amma basu kai girman haka ba ……wani farin abu yaga yana kokarin fitowa …… Su duka suka kurawa gurin ido ……Lokaci guda suka mike tsaye ganin karamar tsotsa fara daga tsakiyar gurin ta fito tana yawo saman kuraje …… Gyalenta ta dauka ta fice da gudu tana fadin "Allah ya isa shege ……" Shikam maida wandonshi yayi ya nufi asibiti inda su hajiya ke

Chapter 12 of 16