Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wayarshi ba ,kiyi hakuri kiyi sallah zuwa safe sai na kira maki shi kin ji ko……" Kallonshi tayi na yan mintina sannan ta sauke kafufuwanta daga gadon tana kokarin mikewa ……kamar an jehota ta dawo tare da sakin kuka tana fadin "Kafana Abdul Maleek ……" Saurin duba kafar yayi amma bai ga komae ba ,ya dago yana kallon yarda ta dage tana kuka bil hakki da gaskia ,Dan murmushi ya sake sannan ya cire jallabiyar da yayi da sallah da ita ya aje tare da daukarta ya kaita toilet din ya aje …… ,,Kamar wasa yaga kafafunta na rawa bayan ya ajeta zai juya ,Saurin tallabota yayi jikinshi yana binta da kallon mamaki "Twee me ke faruwa ne……" Dukar da kai tayi tana share hawayen da suka cika mata ido tare da fadin "Sorry for disrupting……" Saurin kamo hannunta yayi yana kallon cikin idonta "Look Twee karki kuma fadin haka kinji , ko kin manta har kudi aka bani don inyi jinyarki ……? Saurin kallonshi tayi ,ya gyada mata kai yana fadin "Yeah 10m ya bani ,ni kuma zan mayar masa da 20m ya barni na kare rayuwata ina jinyarki ……" Bata san lokacin da murmushi ya subuce mata ba ,jan hancinta yayi yana fadin "Me kike so yanzu ……? Shiru ta masa tana rufe ido "Baki iya wankan ne Twee……"ya fada a hankali "Zan iya ……"ta fada da sauri "Nima bance zan maki ba ai Twee don ban shirya hakan da JB ba……"ya karashe maganar kamar an mashi dole ,Sae yanzu ma yake kara jin takaicin JB da yake neman,ya miyar dashi kamar wani wawa ,wae ya mashi jinya sannan ya sakar mashi ita …… "Ka bude man zip din sae ka fita ,Zan san yarda zanyi ……"ta fada a hankali Lakuce mata hanci yayi sannan ya saka hannu ya juyo da ita jikinshi ya zuge mata zip din ,yana kallon fuskarta …… Dan murmushi yayi tare da shafar digon bakin dake tsakiyar bayanta sannan ya fita daga toilet din …… Da kyar ta samu tayi wankan tana kuka ,Sae da ta daura towel ta sa Pad sannan ta kwala mashi kira cikin muryar kuka don yanzu ba laifi jinin ya rage zuba sosae ,kawae idan ta kwanta baccine take bata jikinta …… "Kuka kikayi ko Twee……"ya fada yana kallon kwayar idonta Shiru ta masa tana turo baki ,Bisa Abun sallah ya ajeta ya dauko mata jallabiyar da ya cire ya saka mata tare da hijab sannan tayi sallan daga zaune don kafafunta basa tsayuwa sosae…… 《》《》《》《》 "Wae kawae sae naga 'ta kwaso na maguzawa ta tankara' _Haske Writer's Association_*Aunty Sanah matazu ta hanani zagi_Haske Writer's Association_* yana motsa hannu ……"cewar Aunty Fatee dake tsaye phydiartric tana waya da Hajiya…… "Sae akae ya kuma ……"hajiyar ta fada cikin,zakuwa A sanyaye tace "Sae na kaishi asibiti……" "Anyi Asararki Fateema wallahi,Na Zubaida dan a gida na haifeki da sai ince musayarki aka man asibiti,Banda kila doluwa bara ki ida karashi ba a dakin……" "Hajiya sae da ba na tattaro masu aiki sannan ya fara motsa hannun ,taya zan karasa shi gaban mutane ……" "Ke ai ya karasaki dan ubanki ……" ta fada tare da kashe wayar tana sababi ita kadae Fadila dake zaune ta kalleta tana fadin "Shi Abdul Maleek din bara ya dawo ba tunda boka yace jiya zata rasu……" A Fusace tace "Sae ki kirashi kiji dan ubanki ,kina ganin wannan banzar uwar taki tana neman ja man asara kina kira man wani Abdul maleek can ……" Tabe baki Fadilan tayi tare da fadin "Ko tashi asarar yake gani ……" hadi da mikewa tabar mata falon Abban kam Yana kwance sanye da Oxygen likitan ya shigo zaya debi jininshi ,wanda kusan sau uku kenan ana shigowa ana dibar saliva dinshi tare da jini …… Bude ido yayi tare da rike hannun Likitan yana mashi alama ya cire Oxygen din ,Da mamaki likitan ya shire yana kallonshi ,Mutumin da aka kawo ake kiran ya mutu amma ya bude idonshi tar yana kallonshi…… A sanyaye Abban yace "Ka fita ka fada masu na rasu……" "A kan me ……? ya tambaya a razane "Haka suke so Doctor……Dan Allah ka fada masu zakaga farinciki kwance a fuskar wadda ta kawoni ……" "Me yasa Kake so ace ka rasu Alhaji " "Karka damu ……"Ya fada a sanyaye "To idan suka bukaci gawarka fa ……"ya jeho mashi tambaya "Sae ku basu wadda a ka nemi mai ita aka rasa……"ya fada kai tsaye Yar dariya likitan yayi yace "Alhaji basu sanka bane da zamu basu gawar wani ,sannan ba abu bane mai yiyuwa ……" Shima dariyar yayi mai cin rai sannan yace "Akan abun duniya suke neman halakani ,abunda ni na tare da gumina ba wani ya bani ba ,matar da ta kawoni ni da kaina naji tana waya da mahaifiyarta akan zasu zuba man magani a abinci na mutu ,shine banci abincin ba sae nayi pretending kamar naci ,sae da ta tara mutane sannan na fara motsi har aka kawoni nan ,Akwae aibu don nace ka fa masu na rasu……" ya karashe maganar murya na rawa Cikin tausayawa yace "I'll prepare anything Alhaji ,Zan basu gawar da aka riga aka nade da likafani ta yarda rufewa kadae zasuyi ……sannan wannan criminal act ne dole a shigar dasu court ……" "Na riga na shigar da kara likita ……" "Good Alhaji ,amma yaushe har kayi reporting ko ka saka wani ya maka hope ka bayar da evidence naka……" Yar dariyar yake ya saki yace "Court dina bata bukatar wani Evidence ,gaban Alkalin akayi komae ,kawae mu jira lokaci ,lokacin da zasu karbi hukuncinsu ……" Girgiza kai likitan yayi cike da tausayi ,sannan ya fita ya sanar da su Aunty Fatee cewa wanda suka kawo ya rasu ,Sannan zasu shirya gawar zasu basu zuwa anjima kadan …… Kafin lokaci kadan Asibiti ta cike da mutane ,masu kuka nayi masu dariya nayi , Ciki har da mutanen JB da family na maryam ,Granny kadae ce bata sani ba …… Idan akace Maryam ba diyarshi bace babu wanda zai yarda a gurin yarda take kuka na fitar hankali ,Mum dinta ce ta fizge wayarta ganin tana neman kiran Safeena gurin tare da fadin "Maryam ba kya son Safeena ne ……" Cikin kuka tace "Ina Sonta Mummy Abbanta ne fa ya rasu ,shine bara a barni na fada mata ba ……" "Idan har kika fada mata a haka Maryam ba kya sonta ,sannan bara ta taba mancewa da Kece kika fada mata rasuwar Abbanta ba……" "To Mummy bani na fadawa Abdul Maleek ko addu'a su mashi dan Allah ……" A sanyaye ta mika mata wayar ,ringing daya ya dauka yana fadin "Munyi fushi tunda sae yau kika kiramu ……" "Abba Abdul Maleek ……"ta fada cikin kuka A rude yace "Me ya sameshi Maryam ……" Kai tsaye tace "Ya rasu……" A Razane ya kalli Safeena dake zaune tsakiyar gado tana game ,Suna hada ido yayi saurin barin dakin ya fita waje tare da yanke wayar …… "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un " ya dinga maimatawa har ya dawo da natsuwarshi Kamar yaro ya tsugunna bakin kofar dakin yana kuka ……Sae da yayi mai isarshi sannan ya goge fuskarshi ya koma dakin …… Turo baki tayi tana fadin "Da waye kake waya……? Murmushin Yake yayi yace "Da sweetheart dita……" Tabe baki tayi ba tare da tace komae ba ,A Hankali ya matso ya zauna saman gadon tare da janyota jikinshi "Sorry……" ya furta da zance biyu …… "Twee Gobe mu koma gida ko……" ya fada a hankali Murmushi tayi tace "Kaima din ka gaji ko ……" Juyo da ita yayi yana fadin "Kalleni Safeena ……Karki kuma fadin kalmar na gaji a bakinki kin ji ko……" Gyada kai tayi a hankali tana kallon fuskarshi …… Wayarta tayi kara ganin sunan JB ya Sashi saurin kai hannu ya dauka ……ba tace mashi komae ba sae binshi tayi da kallo …… *ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. [4:05PM, 11/11/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU 🌹*🌹*🌹* 🌹*🌹* 🌹* © *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. ( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* ) *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha👌🏻**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Bestowed to Aunty Sis💕**ZAN RAYU DAKE.. 4⃣3⃣ Wayarta tayi kara ganin sunan JB ya Sashi saurin kai hannu ya dauka ……ba tace mashi komae ba sae binshi tayi da kallo tana murmushi …… Kamar jira yake a dauka ya ce "Baby Sorry ……Abba ya riga mu gidan gaskia ki dawo gida gobe……" "To ……" Abdul maleek din ya fada a takaice tare da datse wayar ,yana girgiza kai ……lallae jahilci mugun ciwone da tare suke a haka zai fada mata rasuwar mahaifinta kamar yana fada mata rasuwar mai shagon unguwarsu ……lallae JB Dom ne ya fada a hankali "Me ya fada ……"ta katse mashi tunani "Cewa yayi na dawo mashi da matarshi "ya fada yana murmushin yake "Sae kace mashi me……?ta fada a hankali "To nace masa Twee……"Ya karashe maganar yana yake Itama murmushin tayi a hankali ba tare da tace komae ba …… 《》《》《》《》 Cikin mintina kadan aka hada masu gawar da zaa basu suka tafi ,likitan ya koma yana fadawa Abban cewa akwae wata yarinya dake kuka kamar ranta zai fita a waje …… Yana fadin haka Abban ya gane Maryam ce ,Ce ma likitan yayi ya kira mashi ita a sirrance Family din maryam likitan ya tsaida har sae sa su Aunty Fatee suka tafi sannan ya shiga da Maryam din office dinshi inda Abban ke aje …… Dafe kirji tayi tare da waro ido tana fadin "Abba ko fatalwarshi ……" "Abban dai Maryama ……" ya fada dauke da murmushi tare da mika mata hannu ,Likitan ta kalla taga ita yake kallo dauke da murmushi sannan ta tabbatar da Abban ne zaune …… Da gudu ta matsa kusa dashi tare da tsugunnawa gabanshi ,cikin kuka take fadin "Abba suka ce ka rasu wae ……" "Ban rasu ba Maryam kinji ,amma a gurinki ……"ya fada cikin sigar lallashi "Abba Aunty fatee ma ta dauka ka rasu sae kuka take ,bara na kirata na fada mata ta daina kuka……" "Kul Maryam a gurinki kadae nake a raye kinji ko ba ……" ……Karki fadawa kowa ban rasu "To me yasa Abba" "So suke na rasu Maryam ,shi yasa na basu guri su ci abunda ke cikin duniyar ……" Kamar yarda ya dauki Safeena haka ya dauketa bai boye mata komae ba Kuka ta dinga yi tana "Allah ya isa Aunty Fatee,Me Abba da Besty suka maki ……" Rasuwar ta tara mutane yarda baa tunani ,wasu na bakinciki wasu na farinciki …… Abba kam daga asibitin tasha ya nufa ya shiga motar kaduna…… 《》《》《》《》 《》 Takardun da Uncle Abba ya kai hajiya ta zubesu saman gado tana dubawa…… "Zuby duba man wadannan takardun na uban meye wannan yarinyar ta dauko……"ta fada lokacin da ta daga wata takarda dake kumshe da kudin da companyn ya bayar bashi …… "Wannan ai takardar bashi ce da Alhajin ya bayar……"cewar Aunty Zuby tana hararan takardun…… "Tab ……zo ki gani Hajiyarmu babu ta gida a nan don duk irinsu nake gani ……" Watse takardun sukayi kasa ,amma babu takardar ko da fili a ciki ,daga ta kudin da ya bayar bashi sae ta kudin da aka biyashi ,Ciki har dae da takardun safeena na primary school…… 《》《》《》《》《》 Cikin bacci yaji ana kissing lips dinshi na kasa,kai hannu yayi ya buge bakinshi tare da gyara kwanciya……ji yayi an dallah mashi mari da karfin tsiya ,ya mike a zabure yana waigege rike da kumci …… "Uban waye ya mareni……"ya fada cikin jarumta amma zuciyarshi harbawa take da karfi ,Jin anyi shiru ya sashi mikewa yana waigege ya fita daga dakin …… A falo ya iske mum dinshi tana kallo ,ganin yana waigege ya sata kallonshi da sauri tana fadin "Lafiyarka Son…… " Kai tsaye yace "Ina fa lafiya wani shege ya mareni ina bacci……" Yar dariya tayi tana fadin "Mari kuma JB? to gaskia babu wanda ya shiga dakinka yanzu ……ko dae mafarki kayi……" Tsaki yaja yana fadin "Da Allah ni mum bansan jikina bane?to ba wani mafarki ……mari na akayi kuma wallahi sae na mari kowa na gidan nan yau……" "Allah ya baka hakuri……"ta fada kamar tana tsoronshi Mikewa yayi ya tattaro duka yan aikin gida daga tsofaffi har yara ya dawo falo…… Babu laifin zaune babu na tsaye ya bisu da maruka bibiyu ,bai dagawa kowa kafa ba…… Sannan suka mike suka tafi cike da takaicinshi ,dama kuma idan da sabo sun saba da halinshi…… 《》《》《》《》 "Da gaske gobe zamu tafi gida……"ta fada a hankali tana kallon gefenshi "Eh Twee kiyi hakuri kinji ko ……"ya fada tare da kwantota a jikinshi…… A hankali tace "To me yasa AbdulMaleek……" "Kirana akayi baffa baya lafiya……Ko bakya son komawa mu zauna anan Twee?……" ya fada cikin sigar lallashi…… Girgiza kai tayi a hankali ba tare da tace komae ba ,Wayarshi ta hau ringing ya sa hannu ya dauko ganin sunan Abba a jiki ya sa ya mike a hankali tare da zareta jikinshi ya sauka saman gadon …… Binshi tayi da kallo a sanyaye idanunta suka ciko da kwallah ,Ta saba gabanta yake waya amma daga jiya zuwa yau ya canza gaba daya sae ya fita yake daukar wayar ……Hawaye suka ciko mata a ido ta saka bayan hannu ta share ,wani gefen na zuciyarta ke fada mata ko dae shima ya gaji ne ……Sunan Allah ta furta a hankali kamar yarda taji yanayi tare da kifa kanta a filo ta saki kuka mara sauti …… Yana Dauka yaji muryar Abba ,a kidime yake tambayarshi shi dinne koko wani ne…… "Nine Abdul maleeku……"Abban ya fada cikin sanyin murya "Abba kuma maryam ……" Datse mashi maganar yayi yana fadin "Tace maka na rasu ko Abdul maleeku……? Gyada mashi kai yake kamar yana kallonshi …… Shi kanshi Abban yasan mamaki ne ya hada Abdul maleek din magana …… A hankali ya warware mashi komae,tare da fadin "Ina Maharaja hotel yanzu haka a kaduna……" Sun dade suna magana sannan Abban ya kashe wayar …… Cikin Farinciki ya koma dakin ,Shi kanshi ya godewa Allah da bai fada mata ba ,to da yanzu sae yace mata me kuma ?ya tabbata ko gabas da kudu zata hadu barata yarda ba …… Cikin shauki ya kira sunanta"Safeenah……" Banza ta mashi tana kukanta kasa kasa…… Shima bai tsammaci zata amsa mashi ba ,ya matsa jikin socket ya saka charge sannan ya shige toilet yayo wanka…… ya fito yana yar waka a hankali…… Tsaki ta saki da karfi tare da kara sautin kukan nata ……Ido ya waro cike da mamakinta ya matsa yana fadin "Twee kukan me kike ……" Dago fuskarta yayi ya tsaya yana kallonta ……ganin bilhakki da gaskia kukan take kuma da alama ba yanzu ta fara ba ……don daga yanayin idonta zaka gane ta dade tana yinshi …… "Ya salam Tweena me aka maki……Sorry ki bar kukan ki fada man me ke faruwa?ko na maki laifine……?ya karashe maganar cikin sigar lallashi…… Rungumeta yayi sosae yana lallashinta…… amma taki danka mashi ,lokaci guda duk ya rude idanuwanshi sukayi jawur "Twee bakya lafiya ne " Banza ta mashi ta cigaba da kukanta ahankali…… "Look dan Allah ki man magana kinji Safeena……Me ke faruwa?wani guri ke maki ciwone Twee……? Ganin yana niyyar yi mata kuka ya sakata bude baki a hankali tace "Ka gaji Abdul Maleek……" *ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. [2:20PM, 11/12/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU 🌹*🌹*🌹* 🌹*🌹* 🌹* © *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. ( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* ) *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha👌🏻**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Bestowed to Aunty Sis💕**ZAN RAYU DAKE.. 4⃣4⃣ Ganin yana niyar yi mata kuka ya sata bude baki a hankali tace "Ka gaji Abdul Maleek……" A rude yace "Dame na gaji Twee? Da hannu ta nuna mashi kanta tana kallon kasa…… Kafadarta ya riko da sauri yana kallonta sannan yace a sanyaye "Ni na fada maki na gaji Twee……?har ga Allah baya son wannan kalmar ta gajiya tana fitowa da ga bakinta "Look Safeena ……Wallahi Billahillazi kinji na rantse maki da Allah ban taba gajiya da ke ba……"ya fada a hankali A hankali tace "Ka gaji mana……" Rumtse idonshi yayi da sauri sannan ya bude yana fadin "Kalleni Safeena…… har rantse maki fa nayi ……" Shiru ta masa tana kallon kasa ……dago Fuskarta yayi ya hade da tashi yana kallon cikin idonta ……a hankali yace "Kin yarda ban gaji ba Twee……? Girgiza kai tayi alamun aa ……A sanyaye ya saketa tare da mikewa yana kallonta …… Kayanshi ya fiddo ya saka ba tare da yace mata komae ba ya dauki wayarshi ya bar dakin…… Jikinta yayi bala'in sanyi ta bi bayanshi da kallo…… Bayan mintina kadan ya dawo rike da leda a hannunshi ,ajewa yayi ya dauko plate sannan ya dawo ya juye kebabs din ciki ya mika mata ba tare da yace komae ba …… Kin karba tayi ta mayar da kanta kasa ……ko baa fada mata ba ta san fushi yake da ita tunda bai taba mata haka ba …… Gabanta ya aje mata plate din ya juya da niyar tafiya yaji ta riko hannunshi tare da sakin kuka a hankali tana fadin "Sorry………" A sanyaye ya dawo ya zauna tare da rike kafadunta yana kallon fuskarta ,hannu ya saka ya share mata hawayen sannan yace "Ya isa hakanan kinji ko ,Wallahi bana kaunar wannan kalmar na fitowa daga bakinki ,Dan Allah ki daina Safeena……" Gyada kai tayi tare da kwantar da kanta jikinshi tayi lamo …… "Tashi ki ci abinci kinji ko……"ya fada tare da dago kanta Wayarshi ta fara ringing ya mike yana fadin "Bari na dawo kinji Twee……" Hannunshi ta rike gam tayi rau rau da ido "Dawa kake waya tun dazu kake fita ……?ta fada har da dan guntun hawaye Haka kawae ya samu kanshi da farincikin tambayar da ta mashi ……Shirun da yayi yana kallonta ya sata sakin hannun nashi tare da komawa ta kwanta …… "Abba ne Twee……" ya fada tare da dagota Ba ta kalleshi ba tace "Shine kuma sae ka fita……" "Bude idonki ki kalleni Safeena ,dama shi yasa kike kuka dazu ……?ya fada yana aika mata da sanyayyan kallo…… Bude idon tayi tana kallonshi da fararen idanuwanta wanda ko da tayi kuka mintina kadan zasu juye su koma fararensu …… Tun daga farkon wayarshi da Maryam har zuwa Wayar da sukayi da Abban ya fada mata cikin natsuwa da sigar lallashi …… Abunda yake gudu shi ya faru don kuka ta sake mashi bata yarda ba Abbanta na raye ……Ita bata yarda ba…… "Baki yarda dani bane Safeena?ya fada kamar zaiyi kuka Fuskarshi ta rike da hannayenta tana girgiza mashi kai "Abbana Abdul maleek……"ta ke fadi kamar numfashinta zai bar jikinta "Wallahi Allah yana raye Safeena ……bai ci abinci da ta bashi ba……" "Ni dae ban yarda ba ka kaini gurin Abbana shi kadae nake dashi Abdul maleek dan Allah……" Wayarshi ya dauko ya kira Abban akayi rashi saa,wayar tashi a katse ……Abincin ma kin ci tayi ,Dole ya tafi ya nema masu private jet da zai maidasu gida da safe …… Ko da ya dawo kukan take kamar ranta zai fita ,Kasan carpet ya zauna tare da kura mata ido ,kamar wasa yaji hawaye na bin kumatunshi…… ……A hankali ta sauko daga saman gadon tare da dawowa kusa dashi ta rungumeshi sosae tana fadin "Ina Son Abbana Abdul maleek Shi kadae nake dashi sae granny …… Mamina ta rasu sannan Hassanata ma ta rasu ta barni…… dan Allah ka kira manshi Abdul maleek……" Rungumeta yayi sosae yana kara trying number Abban ,ji da yayi ta shiga ya sashi dagota tare da kanga mata wayar a kunne …… Sun kusa awa biyu suna magana Da Abban,banda lallashinta babu abunda yake …… Dakyar ta yarda ta aje wayar sannan ta kalli Abdul maleek din tace "Anya Abbana ne Abdul maleek ……? Kuka ko dariya ya rasa abunda ya dace yayi ,Ita da ta gama waya Da Shi amma take tambaya ko shine da gaske ……Harara ya sakar mata yace "Bansani ba……" Hawaye ya gani sun taru a idonta ,yayi saurin rungomota yana fadin "Allah ya baki hakuri Twee ,wallahi shine ko anayin muryar mutun sak ne……? Girgiza kai tayi a hankali …… Duk da hakan bai sa hankalinta ya kwanta ba ta mike ta fara hada masu kaya …… "sluggish girl……da cewa nayi Twee tashi kije can ki dawo…… kuka zaki man kice kafarki zai kare……"ya fada yana kashe mata ido Littafin dake hannunta ta wurgo mashi cike da kunya tana fadin "Ai kaine ke cewa bana iyawa ko nace na warke……"ta karashe maganar tana turo baki "Ba wani nan ……Ke dae kawae slothful lady ce……"ya fada yana kwaikwayon muryarta Hararanshi tayi cikin salo da jan hankali sannan ta dan cije lips dinta na kasa ta cigaba da abunda take…… 《》《》《》 "Wallahi zuciyata ke masifar tashi kwana biyun nan……"cewar hajiya tana yatsina fuska "Kisha magani mana Hajiyarmu……"Cewar Aunty zuby tana kokarin daukar gyalenta da ke saman gadon hajiyar ……sannan tta kara da fadin "Bara mu je mu dawo don na lura fadila bara ta barni na zauna lafiya ba indae ba ganin yaron nan ya dawo tayi ba……" Bata fuska tayi tana toshe hanci sannan tace "A dawo lafiya……" 【】 "Boka ka tabbata ta rasu ,kuma yaronnan har yanzu bai dawo ba……"Aunty zuby ta fada dake durkushe gaban boka…… Dariya yayi yana fadin "Ta dade da mutuwa ……don aljanun da muka tura mata ba kanana bane suna tafiya ne da wuta ,duk wanda suka raba sae sun konashi …… Maganar dawowarshi kuma Yarinyar ta shigo mu dubata yau dinnan zai dawo in dae bukatarmu ta biya ……" ya karashe maganar yana kallom kirjin Fadila Su duka biyun suka mike daga tsugunnin da suke suna kallonshi cike da tsaro …… Aunty zuby kam bata tunanin zata yarda boka ya sadu da diyarta ,haka ita fadilar ke ji bara ta yarda wannan kazamin ya rike ko da hannunta…… "Ki jiramu daga waje……"Cewar bokan yana nuna Aunty Zuby Kallon uku saura kwata fadila ta mashi cike da jarumta tace "Idan ta jiramu kayi uwar me dani……" Kafin ta rufe baki Aunty Zuby ta amshe "Fice mu tafi fadila wallahi baran taba yarda wannan mummunar halittar ya kusanceki ba,Har yanzu ina sonki ban shirya kwasar takaici ba ……" Dariya ya saki da karfi yace "Ita Uwar taki da ta yarda na kusanceki bata kaunarki ne ……" Fadila ta bashi amsa cike da tsiwa "Uban me ya shafeka da uwarta ,wannan ita taji zata yarda amma ni tawa uwar bara ta yarda ba ……Dama sae da na fadawa hajiya wannan tsinannen bokan babu abunda zai iya amma ta nace tace ya iya aiki ……Mummy dallah mu tafi tun kafin na kifar da shegun tukwananshi……" Tunda Boka yayi maganar jikin Aunty Zuby yayi sanyi har sae da fadilan ta jata zasu fita sannan ta dawo hankalinta …… Duka dakin ya dauki ihu kamar zaya tsage cikin wata irin murya bokan yace "Jeki yarinya ku tafi ke da uwar taki muga me zaki amfana mata……JELILI ka sakar mata mafi munin cuta har tsawon rayuwarta ……" A fusace Aunty Zuby ta juyo tana fadin "Ta Allah ba taka ba tsinanne……" "Kin san da Allah kika zo nan ……"ya fada cikin karaji…… Dan karamin tulun dake gefen hannun Fadila ,ta juya tare da takeshi da takalminta tana fadin "Na fi karfin ka tsinanne ……" Fashewar tulun yayi dae dae da karar da bokan ya saki tare da yanke jiki ya fadi kasa ……Wani jinine ya fara fitowa daga jikin tulun yana nufar gurin da bokan yake kwance …… Sannu sannu har ya fara mamaye dakin ……Da sauri Aunty Zuby ta fizgi fadila suka bar dakin suka fada mota …… A motar maganar bokan ke ta yawo a kanta ,Kenan hajiya ba santa take ba tunda har ta bari boka ya kusanceta …… Wawan birki Aunty Zubyn ta taka ganin guguwa tayo kan motarsu ……Addu'a ta fara nema amma duka sun bace mata tunda dama ba iyawa tayi ba ……da kyar ta kakaro "INNA NAKAFU MIN RABBANA YAU MAN ABU SANKAM DARIRI……" Cikin dakewa Fadilan tace "Mum karki jira ki tada motar mu tafi kawae aikin wannan shegen bokan ne……" Bata rufe baki ba taji kamar ruwa na fita daga karkashinta da sauri sauri…… A Rude ta saka hannu ta laluba pant dinta lokaci guda tana kallon Mum din a kidime "Muje mum karkk tsaya ……"ta fada cikin tsawa …… Kunna motar tayi zata bi ta cikin guguwar ta wuce ,Kamar an fizge motar daga hannunta haka taji sannan tayi ta juyi dasu cikin daji …… Cikin kidima Fadila ke fadin "Mum kiyi Addu'a mana sannan ki rike motar kin tsaya kina kwalalo ido ……" "ALLAHUMMA INNI A'UZUBIKA MINAL KUBSI WAL KABA'ISI……"Abunda ta fada kenan tare da balle marfin motar zata fita…… *ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. [12:40AM, 11/13/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. 🌹*🌹*🌹* 🌹*🌹* 🌹* © *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. ( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* ) *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha👌🏻**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Bestowed to Aunty Sis💕**ZAN RAYU DAKE.. 4⃣5⃣ ALLAHUMMA INNI A'UZUBIKA MINAL KUBSI WAL KABA'ISI……"Abunda ta fada kenan tare da balle marfin motar zata fita Bala'in da suke ciki bai hana fadilan cewa "Amma mumy kinji kunya duk da bana zuwa islamiyya amma Umman Safeena ta taba fada man addu'ar shiga toilet ce wannan……" Kafin ta rufe baki Aunty Zubyn ta bude motar ta fita ……Har lokacin motar bata daina juyi ba don haka ta bi ta kafar Aunty zubyn ta cigaba da juyi a sama…… Kusan minti Talatin fadila na ciki tana ihu Aunty Zuby kuma kafarta tayi daga daga …… Motar ta tsaya cak don kanta ……sannan fadilan ta samu ta fito tana tangyadi tare da kwarara amai …… Bata lura da Kafar Aunty Zubyn ba ta zauna tare da dafa kafar tana rike da ciki …… Ihu Aunty Zubyn ta saki tare da janye kafar da sauri…… Kallon

Chapter 11 of 16