Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ZAN RAYU DAKE Na Feedohm Ebook creat by Shuraih Usman Ebook Publish by www.hausaebooks.cf Ga masu bukatar su sanya littatafansu cikin wepsite namu sai su turo mana da littafin ta Emai namu hausaebooks@gmail.com Domin samun sababbin ebooks namu sai ku ziyarci shafinmu akan adireshi www.hausaebooks.cf [11:03PM, 10/21/2017] Feedohm 馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU DAKE..馃尮*ZAN RAYU DAKE.. 馃尮馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 馃尮 漏 *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. ( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* ) *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM 馃挒_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. 1 鈨� Gurin dinner ya cika makil da dunbin jamaa kae da gani kasan bikine na masu naira .yan mata top class ke juyi tsakiyar gurin ....yayin da hall din ke fitar da wani azababben kamshi ..Daga gefe kuwa wasu yan mata ne su biyu ko wace zaune take hankalinta naga wayarta kirar Iphone6 sam hankalinsu baga cikin hall din yake ba ... .... Mc ....ya bukaci babbar aminiyar Amarya yar uwa ga amarya ta fito ... Fitowarta tata ita da Aminiyarta ta saka hall din karadewa da ihu tare da sowa .... Tana karbar abun maganar gurin yayi tsittt kamar daukewar ruwan sama ... daga gefe kuwa wasu dandazon samarine ke ihu...banda suke fada ..... "Feenah" ...babu abunda "Sunana Safeenat Khalid Mudassir" .....ta fada kallon kaf mutanen dake cikin hall din ....kafin ta cigaba da fadin ... "Duk cikin ku nan babu shegen da bai san Engineer Khalid Mudassir ba ...! Hall dinne ya sake karadewa da ihun mutane ...tayi tsit ..kafin ta daure fuska tace ... "na dauka bikine na masu naira sai naga abun ya banbanta ga dangin ango ..dan banga alamun akwae arziki a tare da su ba.. kaf dinsu sanye suke da yadin da bai wuce 20 thousand ba ..kuma a haka dan tsabar rainin hankali aka gayyaci Feena? .... Kanwar ango ta taso a fusace da niyar wulakancin ta ..... dauketa da mari don ta gama kuluwa da Aminiyarta dake kusa da ita tayi saurin rike mata hannu tana hararanta ... wani Ja'irin murmushi Feena ta sake kafin ta aika mata da wani irin kallon tana fadin ..."Barta Maryam ...ki bar shegiya ubanta ya mutu yana nadamar haihuwarta ....! Wurgar da ab din tayi sannan tayi gaba abunta ....ishak abokin ango ya tare da murmushi don tunda ta shigo ta tafi da hankalinshi ..... " Excuse me Feenat .!....ya sha gabanta tare da harde hannayensa ... Wani kallo ta zabga mashi kafin tace ..."what " " Just Few mints Swky ...ina son contact dinki please"..ya hade hannayenshi guri guda dauke da murmushi .... itama murmushin ta sake ...tare da zabga mashi mari ...tayi gaba tana fadin ..."take it boy .". Hall din ya dauki ihu .....har ta fice bai saki inda ta mareshi ba ...!!! Bayanshi yaji an dafa tare da fadin ...."Weldon ...maganinka kenan .. banga amfanin kula macen da bata san darajar bil'adam ba ...next time idan zaka kula wata ka fara duba dressing dinta before ..." Bai jira amsar sa ba ya zagayeshi tare da barin hall din... Amarya kam banda hawaye babu abunda take ....tayi nadamar gayyatar Feenah gurin taronta duk da ita ce babbar aminiyarta amma batayi tunanin zata mata haka ba ...ko ba komae ya kamata ta duba alakar dake tsakaninsu ta yan'uwantaka ....... "Excuse me, ko ma ciki inda na zauna zaka ga hanky ka dauko man trappr dinta a kasa" ..ta fada tare da dalloshi da flash din wayarta ... Yarda motarta bata amsa mata ba haka bai ko kalli inda take ba ya da niyar bude motar ... saka hannu Ji yayi ta fizge keys din tare wurgar dashi kasa ...." Har ka isa ina maka magana ka wuceni ...!! Dan gidan uban waye kae ? ..me kake takama dashi ? ... A fizge ya kalleta ya girgiza kai yana murmushi ...ba tare da yace mata komae ba ya dauki keys din ya shige motar ya barta tsaye rike da mamaki ... Har ya tada motar yaji tana fadin "Wawan banza bakauye "... Da sauri ya ja motarshi ya bar gurin gudun matsala ... A falo ta iske grandmah dinta ta wajen dad ...gaidata tayi fuska Murtuk sannan ta bude fridge ta fito da robar swan ta balle marfin tana sha .... "Safeena manya..ke dae haka halinki yake " ...kakar ta fads tare kallonta tana girgiza kai ... Aunty Fati ta fito daga kitchen rike da katon tray a hannunta ta ajiye kusa da kakar tare da tsiyaya mata lemo a cikin cup ta mika mata... Kakar tace "sannu Fatima Allah ya biyaki kinji ko ..Allah ya jikan Habiba ....!! "Ameen" ta fada dauke da fara'a sannan ta kalli feena tana fadin ... "Safeena har an dawo ? Ba tare da ta kalleta ba tace ..."baki so dawowata ba ko ? ..saboda na tsare maki gidan uba ko ? ..ta dago tare da zuba mata ido tana aika mata da kallon da ke kunshe da tsabar raini .. Kakar tace ..".kaniyarki Safeena ashe baki da mutunci ...matar ubanki kike fadawa wannan maganar ....? "Uwata ce ? ....ta fada ta Fada a hasale..... "Ai kanwar uwarki ce mara mutunci ...matar da tun kina cikin tsumma ta raineki?.ta goyaki ...,ta baki abinci ..ta baki tarbiya ...haba safeena ..! "Ince abincin ubana ke kawowa ? ko daga gidan kaka ta zo dashi ? ..ina jin tun da ya hada mata garan biki bai kuma aiko mata da ko tiyar shinkafa ba ? *ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM 馃挒*ZAN RAYU DAKE.. [11:03PM, 10/21/2017] Feedohm 馃挒: [8/24, 8:27 PM] Feedohm 馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU DAKE...馃尮*ZAN RAYU DAKE.. 馃尮馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 馃尮 漏 *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. ( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* ) *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM 馃挒_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..this page goings to ...Fa'izahbarwa, Safiyya galadanci , Meela Adeel & It'z Ruky....Allah ya barku da Lanto mai dinki ....馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀*ZAN RAYU DAKE.. 2 鈨� Rike baki tayi tana fadin ...Safeena!!! "Kinga grandy ...idan gulma ta kawoki gaskia ki tafi ...abinci dai na ubanane ...Goyo kuma da kike magana ..ta dauko zani taga idan ban goyata ba ...tarbiyya kuma ai ba da kudinta ta biya man kudin islamiyya ba ...!!ta jefar da robar ruwan tare da shigewa daki abunta ... "Uwaki nace ...kaji man ja'iran yarinya to dan ubanki ki zo na balle maki zanina ki goyatan mu gani mara kirki !! Aunty Fati tace..."kiyi hakuri sae dae Allah ya shirya ....!! Kaka ta amsa da "Ameen Fatima kina kokari ..." � Da sauri tayo baya tare da nuna shi da hannu ..."Kaine dan Iskan nan da na aikeka last gurin dinner beebarh kika zuwa ko ? Da mamaki ya kalleta tare da kauda kai gefe guda yaci gaba da tafiyarshi zai shige cikin falon ... "Wane dan iska ne ya bar wannan abun ya shigo nan gidan" ....ta fada cikin tsawa tare da nuna Abdulmaleek da hannu ... Cak ya tsaya tare da juyowa yana kallonta ...kar dae ace wannan yarinyar diyar oga ce ...tab Albasa ba tayi halin ruwa ba ..... Wani yaji yana fada mata ..."wae Alhaji yace a shigo dashi ..". Cigaba yayi da tafiyarshi ya shige falon da sauri ....itama dawowa tayi cikin sauri ta komo cikin gidan ...tana bala'i ita kadae ... A babban falo ya iske Alhajin zaune saman kujera ...har kasa ya zube yana gaidashi cikin girmamawa .... Cikin faraa ya amsa mashi yana fadin ya zauna da kyau ...girgiza kai yayi tare da dukar da kanshi kasa ... "Abdulmaleek"....Alhajin ya kira sunanshi cikin natsuwa .... "Naam .".. "So nake ka baro office ka dawo gidana ...Driver dake kai Safeeena unguwa shine ta kora ..ni kuma bana so na ta dinga fita ita kaidai ...tunda aikin nan da office din duk dayane ...anan ma kafi samun sauki ..tunda akwae boys quarters da zaka zauna wanda zai fi maka sauki ...amma sae kayi hakuri da halinta ..na yaba da hankalinka shi yasa ma na nemoka ...ina fatan ba matsala ....? : Zufa ta fara keto mashi ta ko'ina ...duk da Ac dake gauraye da. Falon ....a iya saninshi sam yarinyar bata da mutunci duk da sau daya ya taba ganinta ....sannan ko kadan baiyi tunanin itace tayi wannan rashin mutuncin ba .....sannan sam albasa batayi halin ruwa ba saboda mahaifinta mutumin kirki ne ...muryar Alhaji ta katse mashi da tunani da yaji yana fadin ... "Kayi Shiru Abdulmaleek ko kafi son zama can ne? Dagowa yayi a wahale yana fadin " Ba matsala Alhaji nagode sosse" ...shi kanshi bai san abunda yake fada ba Cikin jin dadi yace "Ameen Abdulmaleek Allah ya maka albarka yaji kan mahaifinka ..." A hankali Alhajin ya juya ga Safeena dake tsaye bakin kofa tare da mika mata hannu .... Dan takowa tayi har gabanshi ta zauna bisa hannun kujeran da yake zaune ....tana bata fuska *ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM 馃挒*ZAN RAYU DAKE.. [11:03PM, 10/21/2017] Feedohm 馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU DAKE...馃尮*ZAN RAYU DAKE.. 馃尮馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 馃尮 漏 *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. ( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* ) *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM 馃挒_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha 馃憣馃徎*ZAN RAYU DAKE.. 3 鈨� Hannunta ya kamo yana karantar yanayin fuskarta sannan yace "Safeena ga sabon driver nan kullun zai dinga kaiki inda kike bukata Bana son matsala wannan karan Safeena" "Abbah da wannan abun zanyi yawo?...ta fada a dakile "Kwarae don na gaji da shashancinki Safeena ki kiyaye ni wallahi bara ta yiyu ki dinga wulakanta duk wanda aka kawo aiki karkashinki ba ...AbdulMaleek ba wae yaro kadae na daukeshi ba aa amintaccenane ...!! Mikewa tayi tana bubbuga kafa tare da turo baki .... "Mene matsalar Safeena? ...Abbah ya tambaya tare da mika mata hannu ... "Bana sonshine kawae Abbah last week fa bikin berbah ya raina man hankali ashe ma da motar Abbah na yake tutiya ni dae ...... Katseta yayi yana fadin ..."Wuce Safeenah ..." Da Sauri ta fara hawan stair tana gunguni ....Bakin part dinta tayi karo da Aunty Fatee wani sakaran kallo ta watsa mata tare da shigewa daki abunta .... � Bayan ya bar Gida direct gidansu ya nufa ...Nana kanwarshi ya iske tsakar gida tana wanke wanke .... "Subhanallah Nana waya baki wannan aikin bayan bakya lafiya? ...ya tambaya a rude tare da matsawa kusa da ita ... "Ni ce nan dan Ubanka ko zaka dakeni ne mara mutunci " ....Inna Sahu ta fito daga dakinta tana fada ... "Me ya kawo na duka kuma Inna? Kawae naga bai dace ba tunda bata lafiya a bata aiki irin haka ..Tashi Nana jeki bara na ida kinji ko !! "Da kyau Uwarta to bana son nakan banza na mata" ....ta fada a harzuke tare da matsowa kusa da Nana... Nana tace "Bandee ka barsa na ida kaji ....Allah na warke " A harzuke ya juya zaya fita wayarshi ta dau ringing har ta yanke ba dauka ba ....Sae da ya zauna saman dakalin gidan sannan wayar ta sake kara karo na biyu ....Sunan Oga da ya gani ya sa shi ya dae dae ta natsuwarshi tare da daukar wayar ... Oga yaji yana fadin "Abdulmaleek kana lafiya kuwa tun dazo Safeena ke kiranka kazo ka kaita saloon baka dauka ba ? "Wallahi Alhaji ban lura da kiran bane amma gani nan zuwa " ...ya fada tare da mikewa ... "Ayyah nima abunda na fada mata kenan amma kasan Safeena da rigima " ....Alhajin ya fada a hankali Dan murmushi yayi yana fadin ..."Afuwan Alhaji gani nan a hanya " " Ok" ...ya fada tare da yanke wayar ... Missed call din ya buda a tunaninshi zai ga irin kira uku ko biyu amma sae yaga sau daya ta kirashi shine har ta fadawa Abbanta ...."huh" ...ya fada tare da gyara mirrow din left hand dinshi ....Cikin mintina 10 ya isa gidan ...ga mamakinshi sae ya ganta zaune ita da wani saurayi bisa carpet a harabar gidan don duk tunaninshi zaya iskeshi tana jiranshi amma sai yaga zancenta take hankali kwance ..... Ba wani dalili kawae yaji gabanshi ya fadi ....a sulale ya idasa gurin da suke zaune tare da fadin "Madam gani" a hankali ... Bata kalleshi ba sae dae saurayin ne ya kalleshi ya dauke kai ....yayi tsawon mintina goma kafin ya sake fadin "Madam Gani fa" "Uwar me zan maka ....". ...ta fada a fusace Yaji ciwo amma ya daure tare da dai daita fushinshi yana fadin "Oga yace kina kirana ..Sorry ni sam banga lokacin da kika kira wayata ba " "Dama taya zaka gani? ..Kwalwa ta tunkushe da tuwan dawa !! .. Shiru ya mata ba tare da ya kalleta ba ...saurayin nata yace "Feenah please ki sallameshi ya zo ya mana tsaye a kai ya bata mana iskar guri !! "JB Barsa yayi ta tsayuwa idan ya gaji ya tafi don banga uwar da zai man ba yanzu lokacin da na kirashi ai bai zo ba ...kawae Abbah ya ja man raini !!! A hankali ya ja kafafuwanshi zaya fita ...sae da ya kai bakin kofa yaji tana fadin " Maleek " ... Duk da yana cikin bacin rai hakan bai hanashi jin dadin sunan daga bakinta ba ...cak ya tsaya ba tare da ya juyo ba ... "Ka jira a waje idan na gama zan duba idan da lokaci sae ka kaishi ...." *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM 馃挒_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. [11:03PM, 10/21/2017] Feedohm 馃挒: *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU DAKE...馃尮*ZAN RAYU DAKE.. 馃尮馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 馃尮 漏 *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. ( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* ) *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM 馃挒_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha 馃憣馃徎*ZAN RAYU DAKE.. 4 鈨� Abdul Maleek bai bar gurin ba sae da aka kira sallar magrib sannan ya mike yayi alwala tare da sallah a masallacin gidan ...yana fitowa masallaci yaga ta fito raka JB dan kallonshi tayi kafin ta kauda kai tana dagawa JB hannu da wani blwng smile a fuskarta ....Sae da yaja motarshi sannan ta juyo gurin Maleek din ta kafa mashi ido .. "Zaman me kake mana anan ? Ba karamin kona mashi rai tambayar tayi ba ya danne tare da fadin "Ke kika ce na jiraki Madam Zan kaiki saloon ko" "Gidan Uwarka zan tafi da darennan ...kai baka da tunani baka san darajar mace ba ? Common dallah matsa na wuce !! Ta fada kamar idanuwanta zasu fito saboda tsabar harara Shiru ya mata tare da matsawa ya bata hanya ...sae da ta kusa shiga gidan sannan ta dan daga murya tana fada "Gobe by 7:30 ina jiranka karka bata man lokaci sannan ba kiranka zanyi ba idan kaso ka kai 3pm baka zo ba Bllshit .....!! Ko saurarenta bai idasa parking tare da kwantar da azabar karfi ....kanshi ya kamar kara watsa mashi gas ba ya shige motar ya bar unguwar ....bakin titi yayi kanshi saman sitiyarin motar zuciyarshi na bugawa da dinga bugawa a jikin sitiyarin ko ya samu sauki amma ake a zuciyar ...... Sae da yaji ana kiran isha'i sannan ya fita daga motar ya gangara masallacin dake kusa yayi sallah ......Gurin mai sayar da abinci ya nufa ya sayi shinkafa da wake da miya take away biyu sannan ya nufi gida ....Garejin da yake aje motar ya kaita sannan ya taka ya shiga shagon da yake kwana ya watsa ruwa tare da sanyo bakar jallabiya ya dauki take away din guda ya nufo gidansu dashi ... Tsakar gidan yayi duhu Nana kadaece a bakin dan karamin iccen magoron dake a gefe ta kudundune sai rawar sanyi take .... "Nana " ...ya fada a rude tare da dagota ya hadeta da jikinshi ..."Menene Nana? ..ya akai kika fito ke kadae tsakar gidan duk wannan uban sanyi ? ...ya fada tare da dago fuskarta ... Kuka ta sake a hankali tare da kwantar da kanta a jikinshi .."Baddee inna tace wae baran kwana ba a dakinta saboda dazu ka mata rashi kunya " ...ta fada cikin kuka Duk ya rude yana bubbuga bayanta ....Bakinciki biyu suka taran mashi ...."To yi Shiru kinji ko ? Kinci abinci ? ...ya tambaya a hankali Girgiza kai tayi tare da dago kanta ... Ba tare da yace mata komae ba ya zaunar da ita bakin dakin Baffa ya bude mata abinci ...da sauri da sauri ta dinga ci kamar wani zai kwace mata sae da ta cinye sannan ya debo mata ruwa a randa ya mika mata ..... "Kin ko shi ko? ...ya fada a hankali ... Daga kai tayi tana sauke ajiyar zuciya .. "Baffa ya dawone? Zata bashi amsa suka ji sallamarshi ....Tare suka amsa mashi sannan nana tayi saurin karbo buhun dake hannunshi ...Fuska sake yace "Nana ba'ayi bacci ba? "Uhmm " ...kawae tace tare da murmushi ...Maleek ma gaisawa sukayi sannan ya masu sae da safe ya tafi ...Baffa ya bude dakinshi suka shiga tare ...dama ya saba indae yaga Nana tsakar gida to a dakinshi zata kwana ranar saboda bakin Halin Inna Sahu ...... Yar katifarshi ya gyara mata yace ta kwanta sannan ya shinfida buhu yayi sallah tare da kwanciya gurin ko kan ta Inna Sahu baibi ba ... 《《》》 Tunda Safe yayi Wanka ya shirya cikin kananan kaya wando blue sae rigarshi red ...duk da kayan ba masu tsada bane amma sunyi bala'in karbarshi dan turarenshi ya shafa mai saukin kudi tare da kamshi maidadi .. Karfe 7:00 ya isa gidan lokacin masu aikin gidan kowa ya kama aikin gabanshi. ...... Har harabar gidan ya shiga da mota sannan ya zauna saman fararar kujeru yana jiranta .... Wajen karfe 8:15am ta fito sanye da kayan sport zata shiga gym dake kusa da garden din gidan .... Cikin mamaki ya bita da kallo kafin ya mike tsaye ya bi bayanta .... *ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM 馃挒*ZAN RAYU DAKE.. [8/27, 1:25 P [11:03PM, 10/21/2017] Feedohm 馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU DAKE..馃尮*ZAN RAYU DAKE.. 馃尮馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 馃尮 漏 *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. ( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* ) *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM 馃挒_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha 馃憣馃徎*ZAN RAYU DAKE.. 5 鈨� "Madam"...ya kira sunan a hankali ganin zata shige gym ta barshi tsaye ... Dan juyowa tayi tana kallonshi a murtuke ba tare da tace komae ba ... "Kince karfe 8:00am nazo ko ? ...ya fada yana kallon fuskarta "Da yaushe nace kazo ? "7:30 madam kuma yanzu har pass 8 ....!! "Sae 12:00pm zanyi lecture din sorry ka jirani " ....bata saurareshi ba ta shige abunta .... Ji yayi hawaye na neman zubo mashi da yasan haka wannan shegiyar tace da bai yarda da aikin ba .... yarinyar Babban abunda yafi daga mashi hankali 12:00pm ake tado su nana makaranta ...sam inna sahu bata ba ta kudin mashi sae dae ta bawa yayanta biyu ita kuma indae baije daukarta ba sae dae duk uwar tafiyar dake akwae ta taho kasa ...... A jiyar zuciya ya sake tare da jan kafarshi ya fita ....cikin mota ya koma ya fito da time table dinshi ya duba ...ganin yana da lecture karfe 10 to 12:00pm ya sashi jin dan sanyi sanyi Yana Shiga yar'adua Unversity ya fara ganin course mate dinshi suna shigowa tsayawa yayi ya ragewa mazan hanya sannan suka shiga faculty of law .... Lecture ake masu amma sam hankalinshi baa gurin yake ba ganin 11:15 tayi gashi lecturer din baya da niyar fita tunda dama sae 12....Ishak ya kalla yaga shima danna wayarshi yake abunshi ..... Dan taboshi yayi yana magana a hankali .."Zan tafi please idan zaa yi attendance ka man !! Daga mashi kai yayi ba tare da ya kalleshi ba .....Sulalewa yayi ta kofar baya cikin sauri ya fita ba tare da lecturer din ya ganshi ba ..... Cikin saa kafin 12 din ya isa .....sae da yayi kusan 30mint sannan ta fito sanye da wani farin less mai stone blue sae dan karamin mayafinta blue da karamar jikka a hannunta ..... Duk da bata cika fara'a ba amma hakan ba karamin kyau tayi ba ...... Baya ya bude mata tashiga sannan ya zagaya shima ya shiga ya ja su ....cikin natsuwa yake tukun ta glass din gefenshi yake hango kyakykyawar fuskarta tana latsa waya tare da sakin wani blwng smile dake fito da side dimples dinta ...... Bai lura ba sae dae yaji tana magana cikin fada "back nace maka ...!! Wani uban burki ya taka tare da yin baya a hankali .... "Yauwa yayi nan ..." ta fada tare da balle kofar motar ta fita .... Shima da sauri ya bita ganin abunda zata fitar mawa ....Gabanshi yayi muguwar bugawa ganin Safeena duke gaban Nana tana rike da hannunta tare da sake mata murmushi .... Duk da ba jin abunda suke fada yake ba amma yana ganin bakin nana na motsawa tare da saka bayan hannunta tana share hawaye Bai gama mamaki ba sae da yaga Safeena ta daga Nana cak tare da mannata jikinta tana bubbuga bayanta alamun lallashi sannan ta nufo mota da ita ... Cikin sauri ya koma motar tare da kife kanshi ...wani irin dadi ke ratsashi ta ko'ina ya rasa dalili .... Har sae da ta zauna sossae ta daura nana saman cinyarta sannan ya tada motar ba tare da ya bari Nana ta ganshi ba .... Ta madubi yake kallonsu "Meye sunanki ? ...Safeena ta fada tare da gyarawa nana wuyan hijab dinta daya keshe .... Cikin Muryar Kuka tace "Nana" "Shiii ba nace ki daina kuka ba ....yi shiru kinji ..." ...ta fada dauke da fara'a .... "Oya Nana ba suna bane na gaskia ...meye asalin sunanki !! "Nana Aisha" ...ta fada hankali "Yauwa daga yau idan yayanki bai zo daukarki ba karki kuma masa kuka kinji ko , Ni zanzo na daukeki kullun zan biyo tanan kinji ko...dama duk haka suke !!! Ta fada tare da kauda kanta gefe guda .....da sauri ya kalleta ga mamaki sae gani yayi ta goge idanuwanta da hankyn dake hannunta .... "Wane Unguwa kuke ?....ta fada a hankali "Kofar Marusa!! ..Nanar ta fada tare da kallon Safeena ... "Maleek kofar marusa zamu kai Aisha " ...ta fada har lokacin tana kallon waje .... Baiyi magana ba sae dae canza akalar motar yayi tare da kura mata ido ta madubi ... Dae dae primary suka tsaya da yake motar barata shiga ciki ba ..... Su duka biyun suka fita tana rike da hannun Nana ....fitowa yayi ya zuba masu ido tare da harde hannayenshi guri guda...yana sakin murmushi mai fitar da sauti ... *ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM 馃挒*ZAN RAYU DAKE.. [11:03PM, 10/21/2017] Feedohm 馃挒: [8/27, 9:25 PM] Yar Lukuta 馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU DAKE...馃尮*ZAN RAYU DAKE.. 馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 馃尮 *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association 馃挕_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. ( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* ) *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM 馃挒_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha 馃憣馃徎*ZAN RAYU DAKE.. _Haske Writer's Association_*Gaisuwa mai yawa tare da fatan alkhairi ga duk masoya da ma wadanda basa karantawa ...nagode sossae da kauna ....Ummy Aysha Mrs Maleek ko kuma nace snatcher ....Safeena tace na fada maki

Chapter 1 of 16