Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tayi a sanyaye tana kallonshi har ya fita sannan ya dawo dauke da ruwan ,shi da kanshi ya dinga zuba mata tana alwalan har ta gama ya kamata suka fito ,sannan ya shinfida mata abun sallah ……Har ta kabbara sallah sannan ya koma toilet din ya wanke kayan Tare da wanke toilet din sannan ya fito …… Lokacin ta gama Sallan ta daga hannu tana addu'a ,Gefenta ya zauna tare da daga hannun shima har ta shafa sannan ya shafa yana fadin "Ameen……"Tare da janyo ledar daya shigo da ita ya fara budewa …… Duk abunda ta fada shi ya sawo mata sae chocolate da ya hado dashi Pistachio ya bude tare da debo kadan a hannu yana fadin "Oya open,your mouth……" Bata fuska tayi tana fadin "Zan ci da kaina……" "Ban yarda ba bude na baki da kaina……" "Maleek ……"ta fada hankali "Na'am Twee……"ya kwaikwayi muryarta Hararanshi tayi sannan tace "Stop calling me wani Twee baka san sunana ba……" Kashe mata ido yayi yana fadin "Na fi kowa sanin sunanki Twee amma baran iya fadi ba……" "Me yasa? ta fada tare da waro ido "Baran iya kiran matata kamar ina kiran wata cousin dina ba……" "To ni bana so……ka kirani Safeena ……" Bae ce mata komae sae wani sanyayyan kallo da ya bita dashi tare da kara mika mata pistachio din a bakinta ,wannan karon bude baki tayi a hankali tare da runtse ido …… Sae da ya gama bata ta koshi sannan tace bacci zatayi ,daukarta yayi ya daurata saman gado sannan ya dawo ya tattara gurin ya komo ya zauna bisa stool din dake gefen gadon tare da langwabe kai "Twee ina zan kwanta……" Shiru ta masa har sae da ya kara maimatawa sannan tace "Ga kujera a can mana ……" Marairaicewa yayi yana fadin "Wallahi Twee fadowa zanyi ……" A Zahiri ta yarda da fadowar zaiyi don itama,idan bacci ya dauketa saman kujeran dakinta sae dae ta farka ta ganta kasa …… "Ka dauki blanket ka shifida a kasan carpet to……" ta fada ba tare da ta kalleshi ba Kara marairaicewa yayi yana fadin "Twee Allahu ,So kike mura ya kamani ko ,don ba JB bane ko ……" Kallonshi tayi tana turo baki sannan ta matsa can karshen gadon ta kwanta tare da juya baya ……tsadaddan murmushi yayi sannan ya canza kaya ya dawo ya kwanta bayanta …… "Maleek duk can filin ba isheka ba sae ka dawo kusa dani ……"ta fada tare da mikewa tana fadin "Ba matsala bara na koma kasan ni……" Saurin rike bargon yayi yana fadin "Allah ya baki hakurI Twee dan Allah karki koma kasan wallahi zan matsa sosae kin ji ko ……" Da sauri ya matsa can karshen gadon ya kwanta sannnan itama ta kwanta …… 《》《》《》《》 ,Cikin kwantar da Murya hajiyarsu ke fadin "Boka mun nemi zoben mun rasa bayan an ajeshi da asuba ……" "Wannan sakacinku ne Shafa……"ya fada cikin budaddiyar muryarshi Aunty zuby tace "Ba yarda za'ai a taimaka mana boka…Daga baya sae mu nemi zoben ,don wallahi Diyata na can banda kuka babu abunda take tun jiya da ta samu labarin sun bar kasar………" "Za'a taimaka maku idan kun kawo zoben ……ku tashi ku tafi "ya fada cikin daga,murya "A taimaka boka……" Kallon da ya jefa masu ne yasa hajiya mikewa tare da jan hannun Aunty Zubyn zasu fita ,har sun kai kofa yace "Ku dawo……" Cikin kyarma suka dawo suka tsugunna , Aunty Zubyn ya kurawa ido yace "Za'a taimaka bayan kin biya man tawa bukatar……" Hajiya ta kalla ,tayi saurin daga mata kai alamun ta yarda kawae ……Sannan ta kalleshi tace "Na yarda ……" ta karashe maganar kamar zatayi kuka ,da ta tuna warin da ta shaka farkon da ya fara saduwa da ita ……Wanda daga lokacinne bata kuma yarda tazo gurin ba sae yau da fadilan ta takura mata da kuka …… Dariya yayi da karfi yana fadin "Jeki waje ki jirata Hajiya……" Mikewa tayi ta fita babu alamun damuwa a fuskarta ……Kusan minti goma da fitowar tata ta fara jiyo ihun Aunty Zubyn ……Mota ta koma ta zauna tare da lumshe ido har Aunty zubyn ta dawo da idanuwanta jawur …… "Allah ya isa ……"ta fada lokacin da take kokarin shiga motar Dariya hajiyar tayi sannan Aunty zubyn ta tada mota suka bar gurin …… Suna shiga harabar Gidansu suka ga wata yar tsamurmurar budurwa ta fito daga part din Uncle Abba……Tabe baki Aunty Zubyn tayi tana fadin "Ina Amfanin fiddawa saurayi part a harabar gida ……" Kallonta hajiyar tayi sannan tace "Ke ma kya fada in dae Abbah ne ,ya dinga kwaso mata kala kala kenan har garin Allah ya waye,wallahi na fara gajiya kada yaje ya dauko mana wata cuta ……" Kwala mashi kira Aunty Zuby tayi ganin ya biyo budurwar yana bata wani abu da alama kudine ……Sae da ya sallameta sannan ya matso yana fadin "Aunty zuby daga ina haka keda hajiyarmu……" Hararanshi tayi tana fadin "Ina ka samo waccen shegiyar kuma……" Dariya yayi yana fadin "Oh Aunty zuby wallahi ba shegiya bace, Baby ce …… Ziyara ta kawo man yanzunnan ……" Hararanshi ta kuma yi tana fadin "Ka dae kiyayi kanka wallahi ,idan ba haka ba kana zaune cuta zata kasheka ……" Dariya yayi yana fadin "Haba Aunty zuby cuta bata kasheki sae ni ……" Banza ta masa suka shige ciki suka barshi 《》《》《》《》 Tafiya yake amma sam hankalinshi ba a gurin kidan dake tashi cikin motar yake ba …… Solution yake nema ta yarda zai rama rashin kirkin da Maleek ya mashi jiya …… Decision kawae ya yanke bara ya cika mashi kudin shi ba zai mashi wayau ne yace yana jiran wasu kudi ne ,Sai bayan ya saketa shi kuma ya aura sannan ya fada mashi gaskia rungumar da yayi mata ce ta sauran kudinshi ……sannan ko gidan da yake niyar bashi ,takardun fake zai bashi yarda bara su mashi amfani ba ……Wani murmushi ya saki tare da dukan sitiyarin ya ci gaba da bin wakar …… Wasu tsadaddun yan mata suka tsayar dashi ,tun kafin ya tsaya ya kare masu kallo ,dukansu ba na yarwa …… Parking yayi tare da rage glass yana fadin "Yane ……" *ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. [7:35PM, 11/8/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU 🌹*🌹*🌹* 🌹*🌹* 🌹* © *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. ( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* ) *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha👌🏻**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Bestowed to Aunty Sis💕**ZAN RAYU DAKE.. 4⃣0⃣ DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. Wata daga cikinsu tace "Can Fadama zamu ko zaka taimaka ka saukemu……? "Ku shigo ba matsala……" ya fada yana spreading arms dinshi ……tunda suka shiga motar ba wanda ya sake magana har yayi parking sannan suka bude zasu fita …… Wacce ta fara magana ya kalla yana fadin "Excuse……"Dawowa tayi ta zauna tare da dagawa sauran hannu alamun tana zuwa Cikin sigar yaudara yace "Har zaki tafi baki fada man sunanki ba baby……" "Raliyah……"ta fada dauke da murmushi Duk da gabanshi ya fadi na jin sunan hakan bai hanashi sakin murmushi ba tare da fadin "Wow nice name ……Bani digit dinki mana……" Karanto mashi tayi yayi saving da Baby R sannan yace "Me zakuyi anan ? Yar dariya ta saki sannan tace "Munzo mu huta ,ko zakayi joining ne ……" "Wow baby dama kinsan am incomplete wallahi ,Muje kawae ……"ya fada cike da zakuwa…… Bude motar sukayi suka fito tare sannan ta matsa kusa da yan matan ta masu magana ……yanajin suka dauki dariya a tare sannan ta dawo gurinshi ……Receiption suka shiga suka karbi keys guda biyu sannan suka fito …… Room daya yan matan ne ,Sae gudan room din shida Raliyah…… Shafin badala suka bude shi da ita ,kusan Awa Uku suna abu guda sae da hankalinshi ya dawo jikinshi sannan ya duba ya ga bata kusa dashi ……"Baby ……"ya dan kira sunanta ,amma shiru Lekawa toilet yayi yaga wayam babu ita sannan inda ta aje kayanta nan ba babu komae ,bai damu ba dan ya saba da harkar yan mata ……ya tabe baki tare da watso ruwa sannan ya dawo ya dauki kayanshi ya mayar ya leka dakin da yan matan suka sauka ko can ta tafi …… A kulle ya iske dakin shima ,Fitowa yayi waje amma ko alamunsu babu ……Mamaki kwance a fuskarshi don tun da yake harkar da yan mata bai taba samun wacce ta tafi ba tare da ta karbi kudi ba ……"Ke kika sani nonsense ……dama kin tsaya ko kudi kin karba da kin huce takaici ,don ba kara ganina zakiyi ba nonsense ……" ya fada tare da fiddo phone dinshi yayi deleting numbertah …… 《》《》《》《》 "Me ke faruwa Twee ko sun fada maki wani abune da kika shiga ……" Ya karashe maganar tare da rungumota jikinshi Lumshe ido tayi tana fadin "Sunyi duk wani test amma basu gano komae ba Abdul Maleek sae dae sun bani wani magani sunce nayi amfani dashi zuwa one week a gani …… "ta karashe maganar idonta cike da hawaye …… "To Sorry karki yi kuka kin ji ko ……" Gyada kai tayi a hankali tare da kara kwantar da kanta jikinshi "Daki zamu koma ko mu fita ki ga garin……" Girgiza kai tayi alamun aa sannan ta duka tana fadin "Ka yarda ID card ……" Kafin ta kai ga dauka har ya dauke ya mayar aljihu yana murmushin yake …… Ta dade tana kallonshi sannan tace "Bakka da gaskia ne? Waro ido yayi yana fadin "Me nayi Twee? "Babu……" ta fada a takaice Hannunta ya kama suka koma cikin dakinsu ,sannan ya hada mata ruwan wanka tayi ,ya wanke kayan da ta fitar sannan ya dawo ya zauna yana yarfe hannu tare da fadin "Twee ko sannu ko ……" Cikin wasa ta harareshi tare da fadin "Sannunka na account dinka……" "Haka kika fada Twee……? Gyada kai tayi tana tsuke baki "Zakiyi man bayani Twee……" "Kai ma din zakayi bayani ne……" Ta fada dauke da murmushi Tallabe kai yayi yana fadin " What is the screat of your beauty and glamour Twee……" Banza ta mashi ta janyo wayarta tana kokarin kunnawa ……ganin taki kamawa ya sa ta kalleshi a shagwabe tana fadin "Help me wit your Phone Abdul Maleek ……" Damka mata wayar yayi a hannunta sannan ya mike ya kunna Tv ya dawo …… Abba ta kira suka gaisa sossae yana tambayarta ina Abdul Maleeku …… Sae da ta kalleshi sannan ta kawar da kai tana fadin "Baya nan Abba……" "Idan ya dawo ki ce ina gaidashi kin ji Safeena ,sannan dan Allah ki natsu yanzu ke ke kasanshi ba shine kasanki ba ,ki tausasa halshenki kin ji ko ……"Gyada kai tayi a hankali tana kallonshi kasa kasa …… "Zaki gama wayan Twee sae kin fada man dalilinki na man karya……" ya fada yana watsa mata kallo …… Sae da ta gama wayar sannan ta kira Maryam ,itama sun dade suna fira cikin jin dadi ,Cikin Wasa maryam ta dinga zaro mata magana mai cike da hikima tare da kwatanta mata meye asalin so sannan meye shaawa …… Sae da sukayi kusan One houe suna waya sannan ta juya zata mika mashi wayar …… Murmushi tayi ganin bacci ya daukeshi ,sannan ta matsa da kyar ta cire mashi takalminshi tare da safar dake kafarshi ta mayar da kafafuwan saman kujera…… Ta dade tana kallonshi tare da yaba kyawun halinshi ,Ko kadan baya kyamarta shine ke wanke duk kayan da ta bata harta pant shike wankewa duk da tsotsar da ke makalewa jiki amma bai taba cewa a yarda ba ko da ita tace ,Sannan baya jin komae ya kwanta kusa da ita tare da rungumeta har safe haka zai tashi jikinshi kaca kaca kamar shi ke jinin …… Lumshe ido tayi tare da bashi wani matsayi na musamman a ranta ……Sannan a yarda ta fahimta JB ya rainawa hankali ba sakinta zaiyi ba…… *ZAN RAYU DAKE..Lemme See su waye a team dina*ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..TEAM JB……ni dae💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. Drop your comment amma yan ™JB kadae 08066598868 ……kar naga ™ ABDULMALEEK Don kun man yawa 😡😡 *ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. [9:08AM, 11/10/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU 🌹*🌹*🌹* 🌹*🌹* 🌹* © *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. ( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* ) *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha👌🏻**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Bestowed to Aunty Sis💕**ZAN RAYU DAKE.. DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. 4⃣1⃣ s*ZAN RAYU DAKE..Gaisuwarku ta dabance Sisters👄 Sawwama,Pherty,Faxy fashion,Maman Sawwama,Pherty,Faxy fashion,Maman khadija,Hafsat mai shariff,Billy galadanci,Safiya huguma,Hajjace,Khaleesat haydar,Asmy b,Maryam kaumi ,Muneera,Sanah Matazu,Mrs splendid,,Parrot,Meela Adeel,Jiddah Aliyu……🌹**ZAN RAYU DAKE.. Hannunta dake saman kafarshi taji ya kamo tare da bude ido a hankali yace "Why're staring me……" "Me zan Kallah a nan ……"ta fada tana kawar da kai Janyota yayi da karfi jikin tare da kwanto da kanta saman kujeran yana fadin "Zo na gwada maki abunda kike kallo ……" Turo baki tayi tare da mikewa tana hararanshi……Lokaci guda ta dafe kai tare da sakin gigitacciyar kara sannan ta fado jikinshi …… A rude ya mike zaune ya rike dukkan kafadunta "Menene Safeena ,Fada man,kinji meke faruwa ,Bude idonki ki ganni kin ji ko……" ya fada a gigice …… Ganin ta cigaba da yin karan ne ya sashi rungumeta sossae tare da tofa mata addu'a ……Jiyayi dukkan jikinta ya saki tana fitar da lumfashi da karfi…… Duk ya gigice yana kiran sunanta "Safeena…… Rungumeta yayi sossae yana tofa mata addu'a har sae da Lumfashinta ya koma dae dae …… A sanyaye ya dago fuskarta "Menene Safeena……are you Ok?ya fada tare da kura mata ido Still Razanannar kara ta saki sannan ta hankadashi gefe guda da dukka karfinta tare da mikewa daga jikinshi ……Kujeran da suke zaune tayi baya ta fadi dashi baya…… Kafin ya yunkura ta fice daga dakin da gudun tsiya ……Shima binta yayi har sae da ta kusa fita harabar Hotel din sannan ya samu ya riketa da kyar …… Duka take kai mashi ta ko ina amma bai saketa ba……Mutanen dake gurin babu wanda yayi niyar taimakonshi don kowa harkar gabanshi yake …… Dakyar ya samu ya sabata a kafada ya komar da ita dakin tare da saka keys sannan ya direta ……Birgima ta fara a kasa tana wani irin kuka mai cin rai …… Dafe kanshi yayi ya koma ya jingina da bango idanuwanshi jawur ,shi kanshi da zai samu yayi kukan da yafi samun sauki ……Tunaninshi ya tsaya cak lokacin da wani bakin hayaki ke fita daga jikinta …… Kara ya saki yana fito da idanu waje ,Tundaga inda yake tsaye ya kai guiwarshi kasa har zuwa kusa da ita tare da tallabota jikinshi yana girgizata "Nothing will happen to you Safeena ……"ya fada tare da sakin kuka ……Addu'a ya fara tofa mata duk wacce ta fito bakinshi ……Kamar wuta haka jikinta yake saboda masifar zafin da ya dauka amma hakan bai sakashi sassauta rikon da ya mata ba …… Ganin hayakin bai daina fita ba ya sashi rarrafawa yana rungume da ita ya fito da zam zam din da Malam ya bashi yana shafa mata a dukka jikinta …… Kusan Minti biyar sannan hayakin ya daina fita daga jikinta sae wani uban duhu da fuskarta tayi kamar an shafa mata charcoal…… ,Lumshe ido yayi hawayen dake makale suka gangaro saman goshinta ……Ta dan jan lumfashi da karfi …… "Safeena……" A hankali ta fara bude idonta da suka kada sukayi jawur har ta sauke saman fuskarshi …… Hannunshi ya daura yana zagaye fuskar tata da tayi duhu ,a hankali ya furta "Are you Ok ……"can kasan makoshi…… Girgiza mashi kai tayi a hankali tana nuna shi da hannu tare da kwace jikinta ta koma ta makure jikin bango……A Sanyaye ya bita har jikin bango ,Matsawa ta fara yi tare da sakin kuka tana girgiza mashi kai da hannu …… "Kiyi Magana mana Safeena……"ya fada kamar zaiyi kuka , Kasa magana tayi sae dae kukan da ta sake da karfi tana girgiza kai , "Nine ba kya so nazo gunki Safeena? Ya fada don ya fahimci kar ya matso take nufi Da sauri ta gyada mashi kai tana kuka ……Lumshe ido yayi yana fadin "To yi hakuri ki bude baki ki man magana, sae na tafi kinji ko……" Juyawa tayi ta hade kanta da bango tana kuka ,Asanyaye ya matsa tare da dafa bayanta yana kiran sunanta …… Juyowa tayi ta fara dukanshi da karfi tana turashi ……A sanyaye ya mike ya fara tafiya da baya har ya kai bakin kofa ,sannan ya bude ya fita tare da rufe kofar a hankali ya jingina da ita …… ,Kanshi yayi bala'in daurewa ,Tambayoyine ke zagaye a kwalwarshi wanda ya rasa wacce zai amsa a ciki ,fito da wayarshi yayi ya fada dialing number granny ,Da sauri ya datse kiran yana girgiza kai "No ……" Ganin tsayuwar bara ta mashi ba ya sashi zaunawa bakin kofar har tsawon awa daya ,sannan ya mike kamar an tsikareshi ya fita harabar hotel din yayo alwala ya dawo ,Sae da ya kunna karatun kur'ani sannan ya bude kofar dakin ya shiga kamar barawo …… Karkashin gado ya hangota kwance da alama bacci takeyi ,Tausayinta sossae ya darsu a zuciyarshi ya karasa gurin tare da tsugunnawa ya janyota a hankali ,Har ya fito da ita bata farka ba ,Daukarta yayi ya kwantar da ita saman gado ,sannan ya zauna yana kallon fuskarta da tayi kamar an shafa mata charcoal …… Cikin jikkarsu ya dauko cotton da zam zam yazo yana goge mata fuskar a hankali ,Cikin sa'a duka bakin ya fita ta koma fresh da ita ,Addu'a sosae ya tofa mata sannan ya mike ya rufe dakin ya dawo ya kwanta gefenta ,har lokacin kira'ar sheikh sudais ke fita daga wayarshi …… Rungumeta yayi sosae sannan ya kashe light ya rufesu da bargo…… 《》《》《》《》《》 Uncle Abbah ya shigo falon rike da bakar leda ,Ganin Abban Safeena zaune ya sashi komawa baya ya boye ledar a aljihu sannan ya shigo da sallama …… "Alhaji barka da wuni……" Ya fada harda dukawa Cikin Fara'a ya amsa "Barka kadae Abbah ya gurin su hajiyar ……" "Suna lafiya lau Alhaji sun ma ce a gaidaka……" Mikewa yayi yana fadin "Madallah " sannan ya bar falon ……Mintina kadan Aunty Fatee ta fito tana hararanshi "Kai shine tun dazu hajiya tace ta aikoka amma dan iskanci sae yanzu kaga damar zuwa……" "Ance maku ni banda aikin yi ne……Malama dallah ki karba sannan ki kirata ta maki bayani ……"ya fada yana mazurai Fizge ledar tayi ta juya tana surutai …… "Ke nufinki bara ki bani kudin petrol ba ……" Karamin tsoki ta sake ta wuce ta barsa a gurin ,Shima kwafa yayi ya fita yana fadin "Zamu hade ne wallahi ai kar ta san kar ce……" Sae da ta rufe dakin sannan ta bude ledar ta zazzageta saman gadonta ……Kullin maganine guda biyu a cikin daure cikin takardar nama …… Tabe baki tayi sannan ta dauko wayarta dake jone a jikin socket ta kira Hajiyar …… "Ya kawo hajiya……"ta fada jin hajiya ta dauka "Yayi kyau ,kina ina yanzu ……"hajiyar ta fada "Ina dakina mana ……" "Yauwa magani na karbo maki don na gaji da zaman banza Fatee ,ina amfanin zaman da kike babu da babu jika a gidan ……" Yatsina fuska tayi tana fadin "Kema kya fada……" "Yanzu ga magani nan kulli biyu ki zuba mashi dukansu a abinci ,Ki tabbatar yaci yau dinnan ……" "To na meye hajiya……"ta fada a hankali "Gidanshi na gaskia zai koma……"ta fada kai tsaye A razane tace "Mutuwa hajiya? "Kanin ubankine da bazai mutu ba ……" ta bata amsa kai tsaye ,A sanyaye tace "amma hajiya ko ya mutu fa hakkin takaba kawae nake dashi, meye amfanin hakan ?ba kara na zauna ba ko sato mana na dinga yi ……" "Rufe man baki sakarai ,ai da yake yarda kike banza haka kowa yake ,to bara kinji kina saka mashi yaci ya shure ko motsi bara ya kara ba sannan zaki tattara komae Uncle Abbah yazo ya karba kafin mutane su taro ……" "Safeena fa Hajiya……" "Ta mutu……" ta fada a takaice Yar dariya Aunty Fatee ta saki tana fadin "Yanzu naji batu Hajiyarmu ……"Sannan ta yanke wayar ta shiga wanka ,Mintina kadan ta fito tare da tsantsara kwalliyarta sannan ta dauki ledar ta shiga kitchen da ita …… Da sallama ta shiga dakinshi yana zaune da computer gabanshi ta duka tana fadin "Abban Safeena baka gajiya da aiki……" Dan murmushi yayi yana kallonta sannan yace "Ke kuma bakya gajiya da yawo ko……? Share maganar tayi tana fadin "ka sauko kaci abinci gaskia ……" "Kin hado man da ruwan zafi ko ……?ya fada yana karewa abincin kallo "Kaga na manta wallahi ,Amma bara ns zuba maka abincin sannan na tafi na daura ruwan zafin ……" Da murmushi yace "Thank you ……" Zuba mashi abincin tayi tana fadin "Ka sauko kaci kafin na dawo dan Allah ,wallahi bana son kana zama da yunwa……" Rufe computer yayi ya sauko yana fadin " Na sauko hajiyata ……"Sae da taga ya dauko spoon ya saka a cikin abincin sannan ta fita tana waigenshi da murmushi kwance a fuskarta…… *ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. [2:17PM, 11/10/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU 🌹*🌹*🌹* 🌹*🌹* 🌹* © *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. ( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* ) *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha👌🏻**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Bestowed to Aunty Sis💕**ZAN RAYU DAKE.. 4⃣2⃣ DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. Aje Spoon din yayi ya mike a sanyaye ya rufo dakin ,sannan ya dawo ya dauke duk wani takardunshi masu mahimmanci da kudinshi dake aje ya kai toilet ya rufo da keys ,sannan ya wurga keys din bayan mirrow …… Abincin ya debi rabi ya zuba a leda sannan ya bude glass din window ya jefa bayan gida ,Wayarshi ya fito yana dialing number Safeena amma a rufe ,ta Abdul maleek ya gwada har tayi ringing ta katse bai dauka ba……Rufe wayar yayi ya sakata a pocket na wandonshi sannan ya dube dakin ya dawo gaban abinci ya kwanta kamar matacce …… Turo kofa tayi harda yar wakarta ,ganinshi a kwance ya saka ta tako har gabanshi tana wank girgiza tare da tabe baki "Bikin sallah ……"ta fada tana hambare hannunshi dake cikin abincin Drawer ta bude ta fito da tilin takardu tana fadin "Idan sunje can sun fitar ……"yana ji ta kira Uncle Abbah tace zata bar takardun a falo idan yazo ya dauka …… Sannan ta fita da gudu tana ihu kamar mahaukaciya ……Hawayen da yake dannewane suka gangaro mashi na tausayin kanshi da diyarshi ……Hannun riga ya saka ya goge jin tana taho da masu gadin gidan tana fada masu Alhaji ya rasu…… Kukane kwance a fuskarta kai da gani zakayi tunanin hakan ne a ranta ……"Shikenan Alhajina ,Asirina ya tonu na shiga uku ni,Fateema ……"Abunda take fada kenan tana kallon masu aikin dake tsaye cirko cirko …… A hankali ya fara motsa hannunshi ta yarda zasu gani sossae ,Bala sabon driver tun bayan tafiyar Abdul maleek ne ya zabura yana fadin "Yana motsi wallahi ……" "Ku kamashi akaishi asibiti dan Allah ……"cewar mai gadi tare da nufoshi ya dagashi , Aunty Fatee kam tsaye tayi ta kasa motsi yayin da kukan da take shima ya tsaya cak ,Har sae da su Bala suka fita dashi sannan ta dawo hayyacinta tabi bayansu …… Da yake balan shi ke driving cikin mintina biyar suka kaishi FMC…… Yarda suka shiga asibitin a rude suna ihu yasa akayi saurim shiga dashi emergency…… 《》《》《》《》《》 A wahale ta fara bude idanunta da har lokacin suke jawur ……Daga kai tayi tana kallon Abdul Maleek da idanuwanshi ke lumshe sae dae ba bacci yake ba sae dae karatun Alkur'ani da yake bi a hankali …… "Abdul Maleek……"ta fada kasan makoshi Da sauri ya bude idon yana fadin "Twee are you ok……" A hankali ta gyada kai tare da fadin "Ruwa……" kallon bakinta da ya bushe yayi sannan ya zura hannu cikin dan karamin fridge din dake gefen gadon ya dauko mata bottle din faro ……Yana budewa ta karbi da sauri tare da kallon sama tana shan ruwan …… Sae da ta kusa shanyewa sannan ta saki hannunta kasan gadon tare da sakin sauran ruwan tana fadin "Abdul Maleek……" Kallonta yake cikin tausayawa sannan yace "Na'am Twee ya akai ……? "Headache……"ta fada tana runtse idanu Gefen kanta ya kama yana fadin "To yi hakuri Sannu kinji ko ……" Kuka ta saki a hankali tana fadin "Dukan man shi ake Abdul Maleek da karfi ,kace su daina ……" Rike kan yayi yana tofa mata addu'a har sae da ta fara lumshe ido sannan ya saki yana fadin "Sorry Twee ……" Tabe baki take tana juyar da kan tare da kiran sunanshi bayan duk wani fitar numfashinta ……Bai gaza ba gurin amsa kiranta ,har sae da ta bari don kanta sannan ta koma baccinta ……Kara gyara mata kwanciyar yayi saman kirjinshi yana bin karatun kur'anin cikin natsuwa …… Tunda asuba ya mike ya cire da kayanshi da suka baci yayi wanka sannan yayi sallah ,Yana addu'a ta fara motsi da kai a hankali tana kiran sunanshi ……"Abdul maleek……" Da sauri ya matsa tare da rike mata hannu yana kallon fuskarta da bakinta da ya bushe yayi fari fat ……A hankali yace "Twee menene?ina ke maki ciwo……" Lumshe ido take tana budewa a hankali tare da kiran sunanshi,Kusan minti biyar sannan ta budesu tar saman fuskarshi tana kallonshi ……"Inna lillahi wa inna ilaihirraju'una……" ya maimata mata a hankali Ganin ta amsa ya sashi talloba ya zaunar da ita jikinshi "Kiyi wanka kiyi sallah ko Twee……"ya fada a hankali Noke kafada tayi tana fadin "Abbana Abdul maleek……" "Na kira maki shi……"ya fada cikin sigar lallashi Juyar da kai tayi tana kallon bango ba tare da tace komae ba……Wayarshi ya janyo ya kashe karatun kur'anin sannan ya fara kiran Abban amma wayarshi a kashe …… Kamo Hannunta yayi yace "Twee kinga asuba ce Abba bai bude

Chapter 10 of 16