Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
lokaci ba suka tafi sae da suka fita gari sossae sannan suka yanke daji ……sunyi kusan tafiyar Awa daya sannan suka isa bakin wani burtu dake gefen wata katuwar kuka…… Tun daga waje suke jiyo ihun mace ……hajiyar ta kalli Fadila tana fadin "Ki kiyayi bakinki Fadila idan mun shiga ,ina sane sarae baki da kunya to wallahi wannan mutumin keras yake jira ya wulakanta mutun ……" Turo baki tayi tana fadin "To ni hajiyarmu ina ruwana dashi ……" "Na dae gaya maki ki kiyaye sosae……" Fitowar matar dake ciki ya sasu tsaida maganar da suke ……Sae da suka bar hango matar sannan suka shiga tare da aje takalmansu a bakin burtun ba tare da sallama ba ……Dan tsamurmurin tsohone fuska cike da furfura gashi bakikkirin sae Uban wari yake …… Yafi minti Talatin yana kallon fadilan sannan ya hade miyau ya juya ga hajiya dake zaune tana kallonshi ……katon bakinshi dake cike da algae ya washe yana fadin " Shegen yaro ya hanaku sakat Shafa'u……" Gyada kai tayi tana fadin "Kwarae kam boka……" Wata katuwar tukunya ya fito daga bayanshi ya aje gabanshi yana yan surutai har tsawon minti goma sannan ya dago yana fadin "Shegen yarone mai tsabar riko da addini ba'a zaune yake ba, uwa uba ruwan ganyen magarya shi ya zame ruwan wankanshi ba lalle bane asiri ya kamashi ba ……" "Haba boka akwae wanda ya gagareka a duniyar nan ……"hajiyar ta fada tare da hade hannunta guri guda Dariya ya sake yana fadin "Ai Allah baya bamu sa'a akan muminan bayanshi sae dae idan yana cikin kaddararsu shine sae ya ara mana dan lokaci kadan akansu amma shi wannan shegen yaro ko kadan baya sakaci da addininshi ……Hajiya Shafa'u yarinyarki ta fitar man daga burtu……" A Rude ta kalli Fadilan,saboda sanin halinshi da tayi sam baya da imani ko kadan duka ta kai mata da karfi tana fadin "Boka ka yafe mata ,ke kuma dan ubanki tashi ki koma mota mara kunya……" Tabe baki tayi ta mike ta bar Burtun, Boka kam tun da ta mike ya raka kugunta da kallo sannan ya juyo yana kallon hajiyar da har yanzu tana rude "Ki shigo daga ciki bukatarki zata biya ……"ya fada yana matse kafafuwa Babu musu ta mike ta shiga inda ya sa jan labule ya katange ,shima ya bi bayanta ……Sae da ya gama lalata da ita sannan ya dauko wani karamin zobe ya mika mata yana fadin "Komae yayi Shafa'u, ki bawa diyar taki wannan zoben ta aje sae tsakar dare ta tashi ta kalli yamma ta daura zoben saman hannunta na haggu sannan tace Zoben zalleni jeka zuciyar Abdulmaleek ka hana mashi sukuni har sae yazo gareni ……idan har taga zoben ya bace to tabbas zaizo gareta a ranar idan kuma zoben bai bace ba to aikin baiyi ba sae ku sake dawowa a canza wani salon … amma a zahiri akwae yarinyar dake cikin zuciyar tashi wadda kuka kawo kwanaki aka ma wannan aikin…… to ita yake so sossae idan asirin shi bai kamashi ba, to ita zamu sakawa hauka ta shiga duniyar ta yarda bazai iya rayuwa da ita ba…" *ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. [5:10AM, 11/4/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. 🌹*🌹*🌹* 🌹*🌹* 🌹* © *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. ( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* ) *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha👌🏻**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Bestowed to Aunty Sis💕**ZAN RAYU DAKE.. 3⃣3⃣ _Haske Writer's Association_*I love you din banza ki daina astrayed kanki baby rapidly da na bar novel din kin barni……_🌹* Dan jinjina kai tayi sannan ta karba ta fita a mota ta iske fadilan tana chat abunta sae da ta zauna sannan ta harareta tana fadin "Ba kyajin magana ko ,idan da kin ja mana bala'i fa……? "Yo hajiya mayan kallo ne ya wani kurawa kirjina ido sae kallo yake sakaran bai ma san duk ciko bane……"ta karashe maganar tana rufe baki "Mtsew shine sae ki hararashi kuma to wallahi ki kiyayi wancan mutumin ya wuce duk yarda kike tunani……" Ko da suka koma gida zoben ta bata tace tayi amfani dashi kamar yarda boka ya mata bayani…… 《》《》《》《》《》 Dan karamin tsoki ya sake ganin turawan da yan mata yan kasar nigeria dake yawo a harabar hotel din wani uban Feelings ya taso mashi ……Ga mace har mace amma babu amfani "Wallahi na gaji ……"ya fada tare da dunkule hannunshi guri guda A hankali ya sauka harabar Hotel din gurin wata da ke ta zaune kusa da ruwa da alama yar nigeria ce ……kusa da ita ya zauna tare da mika mata hannu …… Kallon uku saura kwata ta mashi sannan ta yatsina fuska tana wasa da ruwan dake gabanta …… Da yake dan duniyane bai bar gurin ba sae da ta saki jiki dashi sossae har tana fada mashi sunanta raliya ita yar kaduna ce karatu ya kawota india ……sossae suka hau fira har ta kaisu da shiga room din da take zaune ……Sae da suka shege ayarsu sannan ya fito ya shiga asibitin gurin Safeena …… Lokacin ta har fito daga dakin da ake treating dinta tana zaune tana jiranshi ……Da sauri ya karasa kusa da ita tare da rungumota yana fadin "Sorry baby wallahi chocolate naje samo maki kuma babu masu dadi……" Dan murmushi tayi tare da mikewa tana fadin "Is Okey ……" Shafu fuskarta yayi yana fadin "Ya jikin naki baby? ya rage sossae……" Dan girgiza kai tayi a hankali idonta ya ciko da kwallah ta kasa magana ……deep kiss ya mata a lips yana fadin "Sorry karki yi kuka kin ji ko ……Very soon zaki samu sauki……" Yana rungume da ita har cikin dakinsu sae da tayi wanka sannan ya kawo mata abinci ya aje ya fita yana fadin "Make sure kin ci sossae baby yanzu zan dawo nima ……" Dan girgiza kai tayi tare da daukar wayarta ta kira granny lokacin suna zaune da Maleek din yana mata bayanin wani magani daya karbo ……Maleek din ta kalla tana fadin "Safeena ce bara na dauka……"dan girgiza kai yayi tare da maida hankalinshi gaba daya ga granny din…… "Menene Safeena daga daukar waya sai kuka koma……"Granny ta fada cikin sanyin jikin Wani irin kuka mai tsuma zuciya ta sake tana fadin "Granny harda tsutsa yau da naje asibiti……"ta karashe maganar cikin wani irin kuka kamar ranta zai fita Shiru granny tayi tana maimata addu'a a ranta bata so ta karyawa Safeenar guiwa ita kanta idonta ya ciko da kwallah a hankali ta mikawa Abdul Maleek din wayar don ta tabbata bara ya rasa abunda zai ce mata ba ……ita kam da ta kuskura ta furta kalma daya to ta tabbata da kuka zata fito…… A sanyaye ya karbi wayar tare da kangawa a kunne ……har lokacin kuka take kamar ranta zai fita lokaci guda yaji zuciyarshi na bugawa da karfi da ace zai iya dauke ciwon ya dawo jikinshi babu abunda zai hanashi yin haka …… "Safeena……" ya kira sunanta karo na farko a rayuwarshi ……Dan sassautawa tayi da kukan jin muryar Abdul Maleek din "Safeena ko wane bawa da yarda Allah ke tsara mashi rayuwarshi wani ya kanyi rayuwa cikin jin dadi daga farko sae a karshe Allah ya sauya mashi da wahala ,wani kam yana tashi cikin tsanin rayuwa daga karshe Allah ya sauya mashi da farinciki ……Safeena ki dauka wannan itace kaddararki ba kuma dan Allah baya sonki ya daura maki ba sae don ya jaraba imaninki ……"Shiru yayi yana sauraren yarda take fitar da wani irin kuka "Dan girman batayi shirun irin haka,Zan yarda bara ki Allah ki bar wannan kukan Madam……"ya fada muryarshi na rawa , jin ba ya sashi fadin "Wae meye amfanin jabir da zai barki kina kuka zo Madam wallahi baran juri kukanki ba ni zanzo na kula dake ta samu lokacin da zakiyi kuka ba……" Cikin kuka tace "No Maleek muma sauran kwana biyu mu dawo ……"daga haka ta yanke wayar Shigowar JB ce ta sata juyowa a hankali tana kallonshi ……Zaro ido yayi da sauri yana fadin "Meye haka nake gani Baby……? Inda taga yana kallo nan ta kalla……irin tsutsotsin dake fitowa daga kasanta ne suka gangaro kasan kafafuwanta ……azababben kuka ta sake tare da kifa kanta saman gadon …… "Kai wallahi baran iya……Tsutsa fa Safeena ke fitowa daga jikinshi ……Kai Bata yiyuwa wallahi Ina Sonki Safeena amma har ga Allah baran iya rayuwa dake ba da wannan abun a jikinki ……zan bayar da ko nawane idan mun koma wani yazo yayi jinyarki amma bani ba……" Da sauri ta dago tana kallonshi da rinannun idanuwanta ……kafada ya daga yana fadin "Yeah Safeena ina sonki amma baran iya rayuwa dake ba a haka ……ni zan biya kudi wani yazo yayi jinyarki harki warke baby ……Sorry……" Bata ga laifinshi ba har ga Allah sannan ta san granny kadae ke iya jinyarta a haka ……Wasu hawaye suka zubo mata data tuna cewa yanzu tsofa ya zowa granny ba komae zata iya mata ba a rayuwa ita kanta granny tana bukatar Kulawa a yanzu …… Maryam fa ……Runtse ido tayi gam tana girgiza kai …… 《》《》《》《》 Karfe biyu Hajiya ta tada Fadila tare da bata zoben ……a hannun haggunta ta daura sannan ta kalli yamman tayi kamar yarda boka ya fada amman zoben still na hannunta bai bace ba …… Kallon hajiyan tayi tace "Hajiyarmu kinga bai bace ba fa……" "Ki sake gwada wa mana kila ba yi daya yake bace wa ba……"hajiyar ta fada kamar bata so wani yaji abunda take fada Cikin sanyin jiki ta sake maimaitawa amma still zobe be bace ba ……kusan kwana sukayi suna abu daya amma zobe na nan daram ……kusan asuba fadilan ta kalli hajiya a hasale tana fadin "Wannan munafukin bokan karya yake babu wani abunda zai iya……" ,"Uban wa yace maki bara ya iya komae ba kaji mara kunyar yarinya fada man,uban,wa ya hada auren duka iyayenki idan bashi ba?wallahi ki kiyayi bakinki ……"itama ta fada a hasale don ko kadan bata kaunar ace bokanta bai iya aiki ba…… Tsaki fadilan ta sake sannan ta bar dakin gaba daya ……Falo ta koma ta kwanta cikin mintuna kadan wahallen bacci ya saceta ……ko sallar asuba ba tayi ba har kusan karfe 11 sannan ta mike ta koma dakin hajiyar tayo wanka ta fito tayi breakfast…… 《》《》《》《》《》 Tunda JB ya gane raliya bai kara kwana daki daya da Safeena ba ……sannan ko ya shigo dakin ya dinga dode hanci kenan wae wari dakin keyi ……Tun bata jin haushin abun har ta fara ……Saboda dae dae gwargwado tana kokarin gyara jikinta duk da abunda ke fita …… Sam ita bama taga amfanin shigowar tashi ba tunda ba wani abu yake tsinana mata ba komae ita zata tashi da kyar tayi abunta bata jiranshi…… Tana kwance kalabar da Maryam ta mata kafin so zo ya shigo rike da leda a hannunshi daga bakin dakin ya tsaya yana kallonta "Baby ki shirya gobe zamu wuce……" *ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. [9:05PM, 11/4/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU 🌹*🌹*🌹* 🌹*🌹* 🌹* © *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. ( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* ) DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha👌🏻**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Bestowed to Aunty Sis💕**ZAN RAYU DAKE.. 3⃣4⃣ Dan kallonshi tayi ta cikin mirrow ta watsar sannan ta cigaba da abunda take ba tare da ta amsa ba "Wae baby sae wani sha man kunu kike ko nayi laifine?ya fada tare da langwabe kai yana kallonta ,Tabe baki tayi tana girgiza kai a hankali sannan ta mike tsam ta koma gefen gado ta zauna tana latsa wayarta……karasa shigowa dakin yayi ya tsugunna gefenta yana bata fuska kamar yaga kashi "Sorry baby wallahi ina sonki matsalar daya ce baran iya zama dake ba a haka ,dan Allah ki gafarceni idan munje gida zan samu wani na biyashi kudi yayi jinyarki har ki warke na tabbata granny barata iya jinyarki ba tunda tsofa yazo haka Abba shima namijine zan samu wanda na aminta dashi sae na maki saki daya na bashi kudi ya aureki yayi jinyarki harki warke sae ya sakeki mu mayar da aurenmu ……" Binshi tayi da ido lallae JB wawa ne na karshe a tunaninshi wane sakarae zai aureta a haka har ma yayi jinyarta ta warke sannan ya saketa kamar wani wawa…… Hannunta ya kamo duka biyun "Kiyi hakuri baby wallahi ba yarda na iya ne bana kaunar jini bare wanda ke fita da tsutsa,Na yarda zan kashe ko nawane don ayi jiyarki baby ki dawo gareni……" Har lokacin kallonshi take cike da mamakin maganganunshi a yarda ta fahimta sam JB ba karamin wawa bane a tunaninshi ita zata yarda idan ta warke ta dawo gurinshi ……nadamar aureshi ta,zo mata ……Cikin dakewa ta gyada kai alamun ta yarda da zancenshi "Amma Jabir wa kake tunanin zai aureni a haka? Yar dariya yayi "Gasunan da yawa baby ,babu abunda kudi bara suyi ba……Ko wannan,driver naki ai na tabbata zai yarda yadda naga ya damu da rashin lafiyarki sannan uwa uba ga kudin da zan bashi ……amma dan Allah karki fadawa Abbanki ni nasan yarda zan ce mashi ……" "Abdul Maleek kake nufi?……ta tambaya tana gyada kai tare da kura mashi ido "Eh shi mana ,na tabbata zai iya jinyarki yarda ya kamata na yaba da kulawarshi……beside ma 10m zan bashi yayi jinyarki sannan nan na kara mashi 10m tare da gidana dake GRA ya sakeki bayan kin warke……yayi ko? Juyar da kai tayi sau biyu bata da tabbacin Abdul Maleek zai yarda ……koda ya yarda ya aureta ta tabbata bara ya saketa ba don ta warke ……Gyada mashi kai tayi alamun ta gamsu 《》 《》《》《》 11:46am Dae dae suka gashi cikin garin katsina gida Abba yace a wuce da ita amma sam tace gidan granny take so , Abban cewa yayi a wuce da ita gidan granny gashinan zai zo a bakin kofar gidan suka iske maryam har ta rigasu zuwa ,da murnata ta bude motar ta kamo Safeena tana tambayarta ya jikin Tabe baki tayi tana fadin "Ke ba sauki……" Ahankali ta gyada kai jikinta a sanyaye sannan ta kamata JB na bayansh har cikin gidan ,A falo suka iske granny kwance saman doguwar kujera bata jin dadi tana ganinsu ta mike da fara'a tana taba hannu "Maraba da yan tafiya,ai ban dauka da wuri zaku iso ba……" Zama tayi kasan carpet tana fadin "Maryam taikaman da ruwa please……" babu musu ta mike da sauri ta bude fridge ta dauko masu bottle biyu tare da cup ta aje daya gaban JB sannan ta dawo ta zauna kusa da Safeena tare da tsiyaya mata ta mika mata tana fadin "Sannu besty……" Suna gaisawa da granny Abba ya shigo Abdul Maleek ya kawoshi ……Hannu ya mikawa JB din suka gaisa sannan ya juya ya gaida hajiya tare da mata ya jiki Sannan ya juya gurin Safeena "Safeena ya jikin……" Bata fuska tayi tana fadin "Abba wallahi ba sauki kamar kara man ciwon akayi da naje can……"ta karashe maganar murya na rawa "To yi hakuri Allah zai baki sauki kin ji ko "ya fada cikin sigar lallashi ,sannan ya juya gurin JB yana fadin "Jabir ya hanya? "Lafiya lau Abba mun sameku lafiya……"ya fada yana kallon Maleek da ya shigo lokacin Hannu Maleek din ya mika mashi suka gaisa sannan ya matsa gurin granny tare da dukawa yace "Hajiya ya karfin jikin……" "Baka da kunya Abdul Maleeku jiya ya mukai da kai da safe ……"ta fada tana hararanshi ,Satar kallon Safeena yayi sannan yace "Ayi hakuri tsohuwa……" "Haba wallahi zaka sameni ne ……"ta fada tana gyada kai ,maryam tayi dariya tana fadin "Haba granny dan kinga mutane zaki dinga daga mashi murya Abdul Maleekun ki fane ……" dariya Abba yayi sannan yace "Ka dauko man wayana ……?gyada kai yayi sannan ya mika mashi tare da zama kasan carpet ya lankwashe kafa …… Cikin Sanyin murya JB yace "Abba dama akwae maganar da nake so muyi da kai ……"ya karashe maganar yana satar kallon safeena wadda itama shi take kallo tana son taji me zai fada "A a ba komae Jabir ina jinka……" Maleek ne da Maryam suka mike zasu fita Abba ya dakatar dasu "ku zo nan Abdul Maleek damu da ku duk dayane……" Babu musu suka dawo suka zauna Cikin ladabi da sanyin jiki yace " Abba dan Allah ka gafarce akan abunda zan fada……" Sosae jikin Abban yayi sanyi yace "Bakomae Jabir ina saurarenka……" "Abban tun lokacin da Mummyna ta samu labarin Safeena bata lafiya ta kafe dole sae na rabu da ita a cewarta baran iya kula da macen dake dauke da wannan ciwon ba ……Abba yanzu maganar da nake jiya ta kirani tace idan ban saki Safeena ba zata tsineman Albarka ,wallahi na rasa yarda zanyi da rayuwata har ga Allah ina son Safeena amma mummyta ta dage akan sae na rabu da ita ……Babban abunda nake tsoro tsinuwar da tace zata man na tabbata zatayi ……" Sanyaye Abba yace "Uwa ta wuce yarda kake tunani Jabir tun ,lokacin da ta nuna rashin amincewarta da auren ya kamata kazo ka fada man ,Jabir tsinuwar Uwa ba abun wasa bace ka kiyayeta ,Duk abunda mahaifiyarka bata so ka kiyayeshi domin samun albarkar rayuwa……har ga Allah bazan zargeka ba kayi man halacci sossae na aurenta da kayi ,Ni kaina mahaifin Safeena na yarje maka daka saketa yanzu Idan matarka ce bayan ta warke zan sake baka ita Jabir ,Allah yasa hakan ya zama Alkhairi sannan Allah ya albarka ce ku baki daya……" A sanyaye ya fito da takarda ya aje gaban Abban sannan ya fita falon da sauri yana dafe kai kamar mai shirin faduwa "Jabir kabi a hankali karka fadi ……"Cewar Abban ganin zai fadi ,sannan ya kalli Abdul Maleek yana fadin "Taimaka Abdul Maleeku ka maidashi gida kada yaje wani abu ya sameshi a hanya ……"Mikewa yayi a sanyaye ya bi bayanshi Abban ya juyo yana kallon Safeena sam babu damuwa a tare da ita hakan ba karamin dadi ya mashi ba "Safeena kinga yarda Allah ya kadarta maki ko,karki dauki wannan a,bakin komae insha Allahu zaki samu lafiya sannan,ba kasar da zaa maidaki ni da kaina zanyi jinyarki kinji ko ki ci gaba da addu'a ……" Gyada kai tayi a hankali tana jinjina munafunci irin na JB wae mum dinshi tace zata tsine mashi saboda masifar karya ,Sannan ta kalli Granny da ta rafka uban tagumi duk abun duniya ya dameta……Ji tayi maryam ta kama hannunta tana fadin "Sorry besty……" *ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. [3:44AM, 11/5/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU 🌹*🌹*🌹* 🌹*🌹* 🌹* © *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. ( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* ) DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha👌🏻**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Bestowed to Aunty Sis💕**ZAN RAYU DAKE.. 3⃣5⃣ Abdul Maleek kam a bakin mota ya iske JB jingine kamar yana jiran wani ,Kallo daya ya mashi ya watsar sannan yace "Alhaji yace na maidaka gida……" "To nagode"ya fada tare da bude frnt sit ya zauna zagayawa Maleek din yayi ya zauna sannan ya kunna motar suka juya ……Sae da suka fita unguwar sannan JB ya kalleshi fuska daure yace "Abdul Maleek ina son ka auri Safeena yanzu……" Wani wawan burki ya taka su duka sukayi gaba tare da dawowa baya suka daki kujerun da suke zaune ……Wani irin kallo yake watsawa JB din kafin yace "Out of sense……" ya kunna motar ya ci gaba da tafiya "Seriously Abdul Maleek zan baka 20m da gida ,ka auri Safeeena har ta warke sannan ka sakar man ita na aureta……" wannan karon birkin da ya taka yafi na dazu don har sae da suka sauka saman hanya,Gaba daya ya juyo yana kallon JB din …… Dafa kafadarshi JB yayi yace "Ka natsu sosae Abdul Maleek na tabbata kudinne suka rudaka haka ,Zan baka fiye da haka in dae kan Safeena ……Abunda nake so ka yarda ka aureta kayi jinyarta yarda ya kamata bayan ta warke sae ka saketa ba tare da ka bari Abbanta ya san ni na saka aurenta ba,Abunda yasa nake son ka aureta Saki uku na mata na tabbata idan dad dina yaji na saketa cewa zaiyi dole na mayar da ita saboda akwae kyakykyawar alaka tsakaninsu da Abbanta ni kuma baran iya zama da ita a haka ba kaga kenan ko yace in maidata auren bara ya yiyu ba ,kai kuma auren kisan wutane zakayi har ta warke saboda idan ta warke nazo nace ka aureta zaa dauki lokaci kafin ta fito kila ma har ka fara jin wani abu game da ita ,dan zaman da zakuyi idan bata lafiya babu abunda zaka ji, aikin kudi kawae zakayi ……" Girgiza kai yayi tare da jinjina jahilci irin na JB a tunaninshi kudi sayeshi ne wae 20m ko yanzu ya tabbata kudin dake accnt dinshi sun lika yake kokarin bashi ,lallae ya yarda komae ilminka na boko indae babu na to da kai da jahili duk daya kuke ……ai ko duniya zata hade baya tunanin gangancin sakin Madam ba,bayan ya sameta …… zasu abunda addini zaiyi A jahilce ya kalli JB din yace "taya kake tunanin zata yarda na aureta……" "Kar ka damu ni zan shirya duk yarda zaayi sae dae ban yarda ka rike ko da hannunta bane da sunan ta birgeka sannan ban yarda tayi kuka ……" Gyada kai yayi sosae yana kallonshi ……a cikin manyan jahilae ya yankarwa JB katon fili ya ajeshi, ji yayi yana fadin "karanto man account numberka na tura maka 10m yanzu zuwa lokacin da zata warke zan baka sauran ,idan kuma baka da account din gobe zanje na bude maka a bank……" Murmushi ya saki mai sauti sannan yakaranto mashi accnt number din "Wane bank ne "Jb ya tambaya……"UBA" ya bashi amsa a takaice…… idan yaki karbar kudin zai iya fahimtar wani abu…… Mintuna kadan Alert ya shigo mashi Sae da ya duba sannan ya tashi motar suka karasa gidansu JB din ,a bakin gate yayi parking JB ya fito da card dake dauke da numbershi ya mikawa Maleek din "Ka kirani anjima by 9:30 zanyi saving numberka ……"daga haka ya wuce abunshi Bayanshi ya bi da kallo tare da tribted dinshi yana fadin "Shugaban wawaye……" A hankali …… Juya kan motar yayi wani farinciki na ratsa shi wani bangare na zuciyarshi kuwa tsoro yake kar Abban ya ki yarda da wannan zancen bogin ba…… 《》《》《》《》 Cup ta mika mashi tana fadin "Alhaji Safeena ta dawo amma bara ta zauna nan gidan ba fisabilillahi, Me yasa baku daukeni a matsayin mahaifiyarta ba…… kusan kwana biyu fa kenan duk tunanina zata dawo nan amma shiru……" "Ba haka bane ba Fateema Safeenarce ta matsa dole sae gidan hajiyarta zata zauna ,kuma naga da nan da can duk daya ne kawae fatanmu Allah ya bata lafiya……" "Ameen amma ya mijin nata yace ,nayi tunanin ko gidanshi zata zauna ma……"ta fada cike da son sanin halin da ake ciki Bai kawo komae ba a ranshi ya fada mata yarda sukayi da jabir din ya kara da fadin "Ni kaina nayi mamakin saki ukun dake cikin takardar don duk tunanina bai wuce saki daya ba sae daga baya nayi tunanin kila mahaifiyar tashi tace ya mata haka ……fatana Allah ya sa hakan ya zama alkhairi garemu baki daya……" Hannu ta daura bisa kai tare da sakin kuka tana fadin "Amma dai wannan dan iskan yarone shikenan don bata lafiya sae ya kama ya mata saki har uku Alhaji ……" Ganin abun nata ya koma hauka ya sashi shareta …… Wayarshi ta hau ringing ya kalleta "Dan Allah kiyi shiru zan amsa waya " Tare da daukar wayar ya kanga a kunne …… Daga dayan bangaren JB ke fadin "Abba naje office dinka an fada man kana gida yanzu haka ina bisa hanya zan iya karasowa gidan koko sae kadawo na sameka office din……" *ZAN RAYU DAKE.."Ka karaso mana jabir ……" "to Abba" Falo ya sauko ya zauna Aunty Fatee ta biyoshi baya ,Cikin yan mintina Jabir din ya iso har kasa ya gaidashi sannan ya gaida Aunty fatee ya zauna "Ya Abban naka Jabir……" "Lafiya lau Abba yace ma a gaidaku ……" "Muna Amsawa ai jiya munyi magana dashi na fada mashi ba laifinka bane jabir……" Dukar da kai JB din yayi sannan ya saka hannu ya fito da ticket guda biyu tare da mikawa Abban "Abba gashi visa ne na nemawa Safeena zuwa asibitin Madina a dubata to da tare dani na zamu tafi sae Mum dita tace baran je ba ,to Abba kawae sae na maida Sunan Abdul Maleek don na tabbata zai kula da ita sosae ……" "Wane irin abune Jabir taya zaka daurawa mutun wahala ba tare da saninshi ba ,duk da Abdul Maleeku karkashina yake baran iya take hakkinshi ba sannan Abdul Maleeku ba muharramin Safeena bane da zaiyi jinyarta kaje a soke wannan Visar ba mai yiyuwa bace Jabir……" ya fada cikin daga murya Kwantar da murya yayi yana fadin "Abba tun ina can na kira Abdul maleek din na fada mashi kuma ya yarda sosae ,bara ma na kira maka shi……" "Dama ta ya zaiki yarda ,Ban taba sa Abdulmaleek wani abu ba yaki yi man ,wannan karan baran shiga hakkinshi ba ……" "Wallahi Abba ya yarda ,da sunanka zan saka sae yace na sa nashi zai tafi da ita,……"ya fada cikin kwantar da murya "Idan ya yarda shi Muharramintane da zasu tafi a tare har yayi jinyarta? "Abba Safeena bata da aure yanzu , Kana iya ba Maleek din aurenta kafin sun tafi tunda sae sati mai zuwa tafiyar ,Ni kaina na yaba da hankalinshi wallahi babu wanda zai iya kula da Safeena kamar shi ,dole Wanda zai kula da safeena ya zama mai rikon Addini

Chapter 8 of 16