Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kwance ……Ya fada masu a rude…… Cikin maganar da bata fita Hajiya tace "Hate ka kaishi a dubashi ……"Aunty Fatee ta mike Ta bi bayanshi ……yayin da Aunty Zuby ta bisu da harara ……fadila kuma kwashewa tayi da dariya…… Sample na gabanshi suka dauka tare sa dinbar jininshi ……da result ya fito HIV/AID kadae ne positive ……sannan nurse din tace basu gano,wata cuta ba game da gaban nashi illa iyaka suna tunanin yawan bin matane yasa gaban nashi yayi haka ……magunguna suka rubuta masu…… 《》《》《》《》 Da kyar maryam ta samu Safeena ta yarda suka je gidan granny wajen hudu na marece …… Fira suka sha sossae da ita…… Anan ne ma maryam ke fada mata abunda su Aunty Fatee sukawa Abban Safeena …… Hajiyar batayi wani mamaki ba don tasan zasuyi abunda yafi haka…… 【】 JB kam tunda ya koma gida ya kasa zaune bare tsaye ,yawo kawae yake tsakanin falo da dakinshi ,ko da mum ta mashi magana ……tsawar da ya sake mata dole ta koma daki kamar wata diyarshi …… Kiran wayar Safeena yayi amma har ta katse bata dauka ba ,wani abu ya tokare mashi lumfashi ,ya koma ya zube saman gado tare da dafe kanshi …… Uban duka aka sake mashi a bayanshi da karfi ,gantsarewa yayi sannan ya mike yana kalle kalle ……Zuciyarshi ta buga da karfi ganin labulen window na dagewa wani iska na fita daga dakin …… Cike da bacin rai ya yaye bargon dake shimfide saman gadonshi yabi iskar da duka yana fadin "Ni zaa wa iskanci ……to wallahi nima ba karamin dan iska bane ,duk shegen da ya kara dukana ya raina uwarshi……" Bai rufe baki ba aka daukeshi da mari ……kamar sabon kamu ya kaiwa iska duka cike da rashin tsoro "Na lura wani salom iskanci zaa kawo man na dukana ,to wallahi bana tsoron ko wane dan Iskan aljani……" Kofar toilet dinshi ta bude da karfi ,ya bi da gudu ya kamota ya rufe yana fadin "Baza'a barta bude ta ba yan iska a rufe nayi raayin ganinta ……" Kamar mahauci ya dinga surutu shi kadae cike da jarumta ……Sae da komae ya tsaya sannan ya mike ya fita daga dakin ……Har aka gama magrin bai bar surutu ba…… Tunaninshi daya inda zai samu safeena suyi magana yanzu ……"Dutsin safe……" ya fada da karfi tare da daukar mota ya fita …… Tun kafin ya shiga gidan yake kwala mata kira kamar zaya tashi sama ……Suna zaune da granny ya fado falon yana haki …… Cikin hargowa yake fadin "Amma Safeena Abdul maleek ya cika babban shege mara alkawari……" Kallonshi sukayi su duka ba tare da wani ya amsa mashi ba …… "Kin tsaya kina kallona ki fito muje ki karbo takardarki ……" "A gurin wa?Granny ta fada har lokacin tana kallonshi …… Fizgo Safeenar yayi da karfi ya mikar da ita ya hadeta da jikinshi …… lafiyayyen mari ta sakar mashi tare da fincike jikinta daga rikon da ya mata …… Cikin mamaki ya ke kallonta dafe da gurin da ta mara "Abunda kika aitaka yanzu ya nuna man kina bayan Abdulmaleek Safeena……?ya fada cikin konar rai "Akwae jahilar macen da zata kwarewa mijinta baya dama ……? ta fada tare da tsareshi da ido Dauketa yayi da mari yana fadin "Ni zaki ciwa amana?wallahi baki isa ba…… ke tawa ce kuma dole ki dawo hannuna ……" Bai rufe baki ba Maryam ta daukeshi da mari tana fadin "Akwae Ubanda ya haifawa Abba ita a family dinku……? Ya daga hannu da niyar ya rama yaji an rike hannun "Karka kuskura ka taba ta wallahi domin shine kuskure mafi muni da zakayi a rayuwarka ……"cewar Abdul maleek da ya shigo yanzu Kamar wani mahaukaci ya shakereshi "Abdul maleek karka tabashi ……"granny ta fada tare zuwa kusa dasu ta nuna jabir "Jabir fita ka bar man gida dan girman Allah……" "Wannan ne gida?ya fada yana watsa mata kallo "Ko ma menene nace ka fita Jabir ……" "Zan fita amma wallahi Sae dai mu duka mu rasata indae har na bar Safeena kowa ma ya barta ……" "Naji ikon Allah jabir kasan kana sonta me yasa ka saketa?Tunda baa maka dole ba ka saketa cewa akayi ta dawo gida a sama mata magani ta koma ,kai kuma kace mamarka tace ka saketa ,to me kake so a maka yanzu jabir.……? Banza ya mata Kamar guguwa ya bar gidan Zama Abdul maleek yayi suka gaisa da granny …… Safeena da maryam suka shige daki abunsu …… Nan yake fada mata da yayi niyar shigar da Aunty fatee kara sae dae rashin shedu ya hanashi saboda Abban bai riga ya ci abincin ba bare a ce an kaishi asibiti an tabbatar da poison suka saka a ciki…… Sae da ya fadawa granny gaskiyar bai boye mata komae ba hatta aikin da yake sannan ya kara da fadin zai tafi da Safeena yanzu …… Cewa tayi,"Ba komae Abdul maleeku fatan mu Allah ya sanya alkhairi cikin zaman ku ……" Sannan ta mike ta samu Safeena da Maryam zaune ,Sossae ta ma Safeenar fada sannan tace ta tashi ta bi mijinta su tafi …… Turo baki tayi tana fadin "Wallahi granny baran bi sa ba ……" Juyar da kai granny tayi tana fadin "Tunda kika taso nake lallashinki Safeena amma wannan karan kaniyarki zanci wallahi ……" Maryam ta amshe "Wannan karan bana bayanki besty ,ki tashi kawae ku tafi ……" Ganin da gaske suke ya sata daukar hijab dinta tana turo baki ta fita ,maryam ta bita har bakin mota tana mata magana amma sam bata kulata ba .…… Bayan motar ta bude ta shiga ,bai ce mata komae ba yama maryam bankwana suka tafi …… *ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. [4:07AM, 11/15/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*: *💧💧 ZAN RAYU 🌹*🌹*🌹* 🌹*🌹* 🌹* © *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. ( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* ) *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha👌🏻**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Bestowed to Aunty Sis💕**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..49 to 50*ZAN RAYU DAKE.. DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. Tsayawa yayi ya sayar masu abinci sannan suka tafi ,koda suka iso gidan cewa tayi bara ta fito ba wallahi …… Cikin lallashi yace "kiyi hakuri ki fito kinji Twee kinga dare yayi har 10 fa ……wallahi banyi dan na sakaki kuka ba i want to examine wther you love me or not……" Banza ta mashi tana kallon gefe guda …… Wata mota da yaga anyi yayi parking nesa dasu…… yasa ya waiga yana kallon motar na yan mintuna wadda dama ya lura tunda suka taho ake binsu…… Kallonta yayi sannan ya fita ya bude gate din ya shigar da motar yayi parking…… "Ki zauna anan karki Fito kinji ko?……idan ba ni nazo na bude ba……"ya fada yana kokarin fita daga motar …… Tabe baki tayi ba tare da tace komae ba…… juyowa yayi yana kallonta sannan yayi Kissing dinta motar ya fita yana kallonta …… a kumatu tare da bude Binshi tayi da kallo har ya bude kofae falon gidan ya shiga……Sannan ta lumshe ido a hankali ta kwantar da kanta baya Mutane suka fara dirowa cikin gidan su kusan 12 Ko wane rike da makami…… Tana dagowa gidan ya gauraye da haske A rude ta fara binsu da kallo daya bayan daya…… JB ta hango rike da katuwar bindiga yana nuna masu kofar gidan ……Ganin sun shige cikin falon yasa ta fara kokarin balle kofar ta fito…… Duk iya kokarinta ta kasa ashe ya rigaya ya rufeta ta waje ……Wani irin ihu ta saki da karfi tana dukan glass din motar tare da kwala Abdul maleek kira…… Abdul maleek da tunda ya shiga gidan ya zauna falon hankalinshi bai kwanta da motar da ya gani ba ……Yana jin lokacin da suka diro ya kira wani police officer yana fada mashi…… Uban bugun da aka kai mashi da kasan bindiga ya sashi sakin wayar kasa ……kallo ya bisu dashi har ya tsayar da idonshi kan JB dake harde saman kujera tun zuwansu…… "Ina take ……?JB ya fada da idanunshi kamar garwashi…… "Wacece ……? ya tambaya yana watsa mashi wani fitinanen kallo "Ku fada mashi ko wacece……"Ya fada tare da kallon yaran da suka zo tare…… Su duka suka rufeshi da duka…… duk da yana kokarin ramawa amma sae da suka mashi laga laga …… "Where's she……?JB ya fada cikin tsawa "Yanzu na tabbatar Kai ba namijii bane Jabir !macece cikin kayan maza…… tun da har ka dauka wadannan karnuka aka mace ……"Ya fada a galabaice Yar dariya yayi yana fadin "Kae da kake namiji yanzu sae ka gwada taka jamurtar……" Kafin su ankara ya saka kafa ya farde jabir din har sae da kanshi ya daki tiles da karfi ……Bugu sauran yaran suka rufeshi dashi wasu kuma na yankarshi har sae da suka barshi kwance …… Sannan yasa Yaranshi suka bincike kaf gidan amma babu ita……Har karkashin bed da cikin drawers suka bincika amma babu ita duk wani lungu da sako na gidan sae da suka bincike amma babu ita……Suka dawo suka fada mashi …… Bakin bindiga ya buga mashi yana fadin "Tana Ina……? "Ban sani ba……"ya fada yana dafe da inda aka dakeshi…… Safeena kam wayarta ta lalubo cikin kuka ta fara kiranshi…… Ganin haske ya sa JB ya kai hannu ya dauki wayar "TWEE……" Ya gani bisa screen din …… "Tana kiranka……"JB ya fada yana murmushin mugunta…… Da sauri Abdul maleek ya kai kafarshi ya hankade wayar ta fadi kasa ta tarwatse…… Wani daga cikinsu ya kai mashi yanka a gefen hannunshi na dama ……Dafe gurin yayi tare da sakin karamar kara ya duke don har bone dinshi sae da ya fito …… jini kam kamar an bude famfo …… Wayar JB ya dauka tare da hadewa ya kunna ……tana kawo haske Safeena ta sake kira ……dauka yayi tare da sakata speaker…… "Ki fito daga inda kika boye…" Cikin kuka ta ke kiran sunan Abdul maleek …… Tsawa JB ya daka mata yana fadin "Kina ina nace wallahi idan baki fito ba na zo na nemoki da kaina sae na kasheki sannan na kashe Abdul maleek idan kunso ya RAYU DAKE a lahira……" Kamar ana fizgar lumfashinta take fadin "Kar ka mashi komae Jabir zan fada maka inda nake yanzu ……" Da karfi Abdul maleek yace "No Safeena karki sake ki fada masu……" Yana jin lokacin da ta saki kuka tana fadin "Ina cikin……" Kukan kura yayi ya warce wayar tare da bugata a jikin bango ta yarda barata sake amfani ba …… "Mu tafi dashi oga Zata kawo kanta ……"Wani daga cikinsu ya fada Mikar dashi sukayi da tsiya suka fito dashi harabar gidan jini na fita sosae daga jikinshi…… Tana kokarin kiran wayar JB taga sun janyoshi kayan dake jikinshi kansu sun canza kala …… Uwar kara ta saki tana buga glass din motar da karfi ta yarda zasuji…… Su duka hankalinsu ya dawo gurin tare da sakin Abdulmaleek din sukayo kanta …… Tambayarshi keys din sukayi yace bara ya bayar ba ……Kara yankarshi sukayi……ya tafi kamar zai fadi yayi saurin dafe kofar …… Buga kofar take cikin kuka take fadin "Ka basu Abdul maleek dan Allah……" Girgiza mata kai yayi yana fadin "I Wld'nt Safeena……" "Kuyi ta dukanshi har ya fito dashi ……"JB ya fada tare da juya baya …… Kamar ranta zai fita take fadin "Ka daina Jabir…… na roke dan Allah ka daina dukanshi it griefs JB ……" Jin yarda take kukan ya sa Jabir din juyo wa yana masu alamar dasu dakata sannan yace "Kina sonshi ne? Bata san lokacin da ta dinga daga mashi kai ba tana fadin "Ina Sonshi jabir…… dan Allah karka cutar dashi……" Da sauri Abdul maleek din ya daga kai yana kallonta …… Kallonta JB d yayi da idanuwanshi kamar garwashi sannan ya kalli Abdul maleek din tare da gyara bindigarshi yana fadin "KO WA YA RASA……" Tare da saita Safeenar ya harba……ta cikin glass bullet ya huda tare da nutsewa a kafadarta ta haggu…… Kara ta saki da karfi tayi baya ta daki dayan glass din motar ……zaya kara harbinta Abdulmaleek din ya saka kafa tare da tadiyeshi ya fadi yana dukanshi da karfi …… A hankali yake fadin "You'll pay for this JB ……" Karan motar yan sanda ta su suka bi ta katanga suka dire su dukansu …… Da gudu ya fara laluben flowers din dake gefen motar har ya fito da keys din ya bude ya shiga tare da rungumota yana girgiza fuskarta ……cikin kuka yake fadin "Dan Allah ki tashi Safeena despite the fact you're the light that brighter my heart,you're are everything to me i'm lost without you……" Shigowar yan sandan ya sashi koma driver sit …… kwantar da ita cikin motar tare da fitowa ya Da sauri police ya matso yana fadin "Sorry……Bamu da petrol lokacin da ka kira……" Tsawa ya daka masu yana fadin "If any one of you step one hnds here I'll chop his legs wallahi ……Me zaka man yanzu ?meye amfanin ku?baku da wani amfani a rayuwar yan adam ……aikin kawae sae criminals sun tafi sannan ku zo da uzurinku na banza……Kar wanda ya matso kusa damu bama bukatar komae daga gareku……" Kunna motar yayi ya fita daga gidan ya barsu tsaye cirko cirko…… Tuki yake amma hankalinshi naga Safeenar ……duk bayan seconds sae ya juyo ya kalleta ,har yayi parking cikin asibitin sannan ya fito da sauri tare da balle marfin motar ya daukota ……Sae da ya shiga asibitin sannan ya lura da police din da ya biyoshi ……kallon daya ya mashi ya watsar tare da sakin tsaki da karfi…… Nurses suka karbeta aka shiga da adjoin …… Kamashi wani nurse yayi don ganin ciwon dake cikinji ……da sauri ya dakatar dashi yana fadin "Karka damu dani kaje ku dubata……" Sae da wata nurse ta fito tace mashi an cire bullet din sannan ya yarda sukayi treating dinshi …… Ana fitowa da ita ya bi bayansu har aka shigar da ita wani daki da ke da duhu ……Cewa akayi kar ya shiga amma bai kula kowa ba ya shige tare da zama gefen gadon yana shafa fuskarta …… Kamar karamin yaro ya dinga kuka yana surutai…… 《》《》《》《》 Su JB kam suna barin gidan guest house na babanshi suka nufa ……Kudinsu ya basu suka tafi sannan ya zauna dafe da kai kamar zuciyarshi zata fito saboda masifar bugawa…… Fitilon dakin suka dauke lokaci guda Sannan lalubayen dakin suka fara yayewa yayin da kara ta cika dukka dakin ……Ko gizau baiyi ba ya mayar da kai ya kwantar yana dafe da gefen zuciyarshi …… Wani farin abu kamar gawa yaga ya fara nufo inda yake …… Wayarshi ya fara laluba yana kokarin kunna flash din ……kifar da wayar akayi kasa tare da kifa mashi mari ……dafe gurin yayi yana fadin "Yanzune zaa sha banban don bana daukar duka daga ko wane shege……" "Ko zaka rama yanzu ma……" Yaji maganar na fitowa daga bayanshi …… Murya na sarkewa yace "Fito idan kai babban shege ne kaga idan ban rama ba ,don wallahi bana daukar rainin duka ninan namijin dan iska ne wallahi……" Haske ya gauraye dakin ta ko'ina ……tare da kida kamar ana dukan ganga…… Ta bayanshi aka taboshi…… A hankali ya fara waigowa yana fadin "Yanzu kau zan gwada maku nima shegen kaina ne ……" Dafe wandonshi yayi yana fadin "RABBANA ATINA FID DUNIYA……"Ganin wata mummunar bakar halitta sanye da korayen kaya ……duk hakorinta daya yafi karfin bakin mutun daya ……idanuwanta na fitar da wani irin jini yayin da gashin kanta ke jan kasa…… Cikin wata hargitsartsar murya take fadin "Gani ka rama namijin dan iska……" Jan numfashi yake da karfi ya kasa furta ko da kalma daya har lokacin yana rike da wandonshi da ke kama da an wankeshi…… Matsowa ta fara yi jikinshi yana jan baya har ya kai jikin bango …… Cikin tsawa tace "Ka rama babban shege ko sae na kara maka wani zaka hada ka rama……" Lokaci guda tayi girgiza ta dawo sak Raliya da suka hadu india ……kafin ta sake juyewa ta zama raliyar da yakai Fadama ……sannan ta zame masa yarinyar da ya kora shekaranjiya…… Kallonta kawae yake yana fitar da numfashi yayin da zufa ta wanke mashi jikinshi ,fitsari kam yayi ya kai sau biyar nan take …… Dariyar ta saki da karfi sannan ta kai hannunta zata sake marinshi …… "QUL HUWALLAHU……"Ya fada tare da sulalewa jikin bango yana fizge fizge kamar mai farfadiya…… Dariya ta saki tana fadin "Ka dade kana wa yaudarar yan mata ta hanyar yi masu alkawarin aure amma da zaran bukatarka ta biya sae ka wulakanta ……nima na maka alkawarin aure kuma bama sabawa Jabir……" Wani abu ta hura mashi sannan ta bace bat kamar walkiya…… 《》《》《》《》 Kwana Abdul maleek yayi kusa da Safeena ko nan da can bai je ba ……Haka ya hana idonshi bacci gudun kada ta farka yana bacci …… Bai kuma kira kowa ba har garin Allah ya waye ……haka ya wuni ko abinci baici ba ……yan sanda kuwa sunyi shigowa yafi 10 wae sunzo investigation ne……ko kallon inda suke bayayi don baiga amfanin yan sandan nigeria ba da sae an gama mugun abu sannan ka gansu…… Wajen karfe 6 na marece sannan ta fara bude idonta a hankali,…… A rude yasa hannun ya ida bude mata su yana kiran sunanta "Safeena …… "Kalleni dan Allah kinji Safeena Abdul maleek ……"ya fada lokacin da ya gama bude mata idanun da hannunshi …… *ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. [2:31PM, 11/17/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*: *💧💧 ZAN RAYU 🌹*🌹*🌹* 🌹*🌹* 🌹* © *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. ( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* ) DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha👌🏻**ZAN RAYU DAKE.. *ZAN RAYU DAKE..Bestowed to Aunty Sis💕**ZAN RAYU DAKE.. , *ZAN RAYU DAKE..51 to 52*ZAN RAYU DAKE.. "Bude idonki ki Kalleni kinji Safeena Abdul maleek ……"ya fada lokacin da ya gama bude mata idanun da hannunshi …… Sae da ta maida idon ta rufe da sauri sannan ya tuna abunda yayi bai dace ba "Sorry ……"ya fada a hankali Bude idon tayi tana kallon gefen hannunshi dake nannade da bandage sannan ta saki kuka a hankali tana fadin "JB ne Abdul maleek……Shine ya yankeka ,bayya da imani sae da nace mashi karka yayi amma yayi Allah bara ya barsa ba wallahi mugune……" Lumshe idonshi yayi yana jin kukan nata har cikin ranshi ……Rungumeta yayi sossae yana fadin "Ki bar kuka kin ji Insha Allahu muna cikin kariyar Allah kuma,nima bazan kyalesa ba ……" A Hankali tace "Yana so na mutune Abdul maleek……? Da sauri yace "Ko yana so ko bayya so nothing will happen to you ……" Sae da kalleshi sannan tace "Zai sake zuwa nan Abdul maleek ……Mun tafi gurin Abbana……" "Bara ya zo ba kinji ko……"ya fada cikin sigar lallashi tare da kara rungumeta sossae…… Sun dade a haka sannan ta dago idonta tana kallonshi ……Shima kallon nata yake kafin ya sa hannun ya rufe idonta yana murmushi …… "Menene……?ya fada cikin kunnenta har lokacin hannunsa na saman idonta …… A Hankali ta sa hannunta saman nashi tare da cirewa tana aika mashi da wani irin tsadadden kallo na musamman …… Sannan ta Lumshe ido a hankali tana fadin "Last tima i asked you Abdulmaleek How did you bear when i insulted you so badly without understand you amma baka bani amsa ba am appolozed……" Rungumeta yayi yana fadin "I see your love on me behind every word you say……I love you" Shiru tayi tare da zagaye hannunta da baya da ciwo a jikinshi ……likitan ya shigo yana fadin "Patient dinka ta tashi amma bakayi reporting ba kana nan cikin lovers trcts ko?Ga magunguna nan ya kamata ku samu abu liquit kuci sannan ku sha ku duka sannan kaima ka kwanta ka huta saboda yanayin jikinka……" Langwabe kai yayi yana fadin "Help,me doctor ga kudi ka bada a sawo mata ni bana bukata ……" Sannan ya maida hankalinshi kanta yana fadin "Da na tashi kuka zakiyi ko Twee……?ya karashe maganar yana kallon fuskarta Kadan ta murmusa cike da kunyar likitan …… "Ba wani kai dae ne zakayi kukan idan ka tashi……ya kamata ka kwanta ka huta tunda ta tashi ko……"likitan ya fada tare yin gaba yana fadin "zaa kawo,maku abinci ka tabbata ta ci kaima ka ci dan Allah sannan kusha magani……" "Okey……"ya fada a hankali tare da bin likitan da kallo har ya bar dakin…… Wani Police ya shigo ya zauna yana fadin "Sir ya mai jikin……" Kallon zanci gidanku ya mashi sannan yace "lafiya……" "Zaka iya fada mana cikakken sunan wadda aka harba……" "A'a ……"ya fada kai tsaye "Me yasa?ya kamata ka bamu hadin kai domin gano wadanda suka maka wannan aikin……"ya fada yana kallonshi Wani kallo ya watsa mashi yana fadin " Bana tunanin nan da Shekara goma zaku iya gano su ……please Get out……! "Amma……" Katse shi yayi yana fadin "Baka san kofar da ka shigo bane?alright ka juya lefthand side dinka zaka ga door akwae dan karfe a jiki sae kayi clicking ,idan ya bude sae ka fita ka bani guri……" "Kayi hakuri lokacin da ka kiramu motar mu babu petrol sae da aka kira commissioner ya aiko da kudin sannan……" "Shi yasa nace baku da amfani yanzu……Dan Allah ka fita……" A sanyaye ya fita…… bai damu da abunda Abdul maleek ya mashi ba tunda yasan laifinsu ne da basu zuwa cikin gaggawa …… Nurse ta shigo rike da katon flask dauke da ruwan zafi sae kamar Cler a hannunta da Plates…… "Thank you……"Abdul maleek ya fada bayan ya karba sannan ta juya ta fita …… Chips ne a cikin Cler din ……ya juye yana cije bakinshi saboda hannunshi da ya rike yanzu …… Kallonshi tayi tare da karban Plate din da hannunta mai lafiya ta aje gefe guda …… Zaiyi magana ta daura hannunta saman lips dinshi tana jefa mashi wani fitinannen kallon da yasa shi dauke idonshi da sauri …… "Go nd brush……"ta fada ba tare da ta kalleshi ba …… A Hankali ya mike yana tafiya har ya isa toilet din …… Brush yayo ya dawo yana mika mata hannu alamun ta taso itama tayi …… Hannun nata mai lafiya ta bashi ,ya jata har toilet din tayo brush tare da alwala sannan suka dawo ,suka zauna saman gadon…… Tea din ta ta hada a cup sannan ta kai bakinta ta sha kadan tare da janyewa ta daura saman nashi …… Lumshe ido yayi a hankali sannan ya bude yana kallonta ,cikin sanyin murya tace "Ko da zafi ne……? Murmushi yayi ya hade cup din da hannunta ya rike yana kallon kyakykyawar Fuskarta …… " Kullun kai ke Feeding dina Abdulmaleek……don Allah yau ka barni nayi naka……"ta fada muryarta rawa Sakin hannun yayi a hankali yana kallonta tare da lumshe ido …… Chips din ta debo ta saka mashi a baki ……sae da ya hadiye sannan ya bude ido tare da kama hannunta ya debo wani ya kai bakinta ……Janye idonta tayi daga kanshi tare da bude bakin ta saka tana murmushi mai fitar da ainahin kyawunta…… A haka suka ci abincin har suka koshi sannan ta janyo magani suka sha tare da kwantar da kanshi saman cinyarta tana fadin "Sleep……"kusa da kunnenshi …… Lumshe ido yayi yana shakar kamshinta farinciki na ratsa dukkan zuciyarshi …… Bai san lokaci da bacci yayi gaba dashi ba …… Murmushi tayi lokacin da ta fahimci yayi baccin tare da saka hannunta tana zagaye dukkan fuskarshi a hankali ……Sannan ta cusa yatsunta cikin sumar shi…… "I Love you……"ta fada tare da pecking goshin shi…… Wayarta ta janyo tayi dialing number Abbanta cikin saa ya dauka ,bata fada mashi abunda ya faru ba sae dae tambayarshi da tayi yaushe zai dawo…… "Nan da sati daya Safeena……"ya fada kai tsaye Daga haka suka cigaba da firansu …… Sunfi awa daya sannan ta aje wayar tana kallon Abdul maleek da har lokacin bacci take cikin natsuwa …… Hannu ta kai ta Shafi wuyanshi ,da Sauri ta janye jin jikin nashi kamar wuta …… haka nan taji kwalla na neman zubo mata …… Kwanto da kanta tayi bisa kanshi tana fadin …… "Sorry……Allah sae ya saka maka wallahi……" 【】 Tun suna Asibitin Hajiya tace a zubar da cikin amma likitan yace idan aka kuskura aka zubar dashi to wallahi zata iya mutuwa saboda ciwon dake tare da ita …… Duk da hakan bata yarda ba Aunty Fatee ta aika wani asibitin ta karbo mata wasu taps ta dawo …… Ranar da ta shasu kamar zata mutu amma cikin yaki fita …… Satinsu biyu asibiti sannan aka sallamesu wanda har lokacin barin jikin hajiyar baya amfani…… Aunty Zuby kam keken guragu aka bata ta dinga amfani dashi idan taji sauki …… kuka sosaae tayi da ta tabbata da ta riga ta zama gurguwa……Babban tashin hankalinta da akace hajiya nada HIV ita ma ta san bata rasata tunda kamar yarda boka ke kusantar hajiyar ita ma haka yake kusantarta ……tayi kuka kamar ranta zai fita tare da nadamar rayuwarta ta baya…… Gashi tunda aka kawota asibitin sau daya dadyn su Fadila ya leko ……yanzuma da Aunty fatee ta kirashi tana tambayarshi ko gidanshi zaa maido Aunty zubyn cewa yayi aa ta zauna gidan hajiyar ba sae ta dawo ba…… Fadila ma jini sae abunda ya cigaba tun tana sa ran daukewarshi har ta fitar da rai domin har kananan Tsutsa ke fita wani sani …… Set na gold din Aunty fatee ta sace taje ta sayar dashi dubu dari da hamsin ba tare da kowa ya sani ba taje asibitin zaria aka hado mata magunguna ta dawo …… Sauran kudin kuwa taci gaba da kashewa abunta…… Uncle Abbah ma duk da magungunan da yake sha amma abun yaki sauki ……wani irin jini ke fita daga cikin kurajen sossae ta yarda baya da damar saka wando sae ya baci ga tsutsa da yanzu sae uku ta fito lokaci guda…… Kullun yana zaune da yar shara sae ya daura zani a ciki ta yarda rigar barata baci ba …… Tunda suka koma gida Aunty Fatee ke hidima dasu don dawowa tayi gaba daya gidan da zama kwanansu biyu ta fara gajiya da hidimarsu komae ita ke masu hatta kashi nan hajiyar ke yinshi sae dae ita zata wanke mata …… Saukinta ma da

Chapter 13 of 16