Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
haduwa da Rabi'a ba ya roki gafararta. Nabila ta tashi a gidan tamkar wata tauraruwa zarah cikin taurari saboda tsabar kyanta. Ba fara bace kalkal wankan tarwadace mai haske, tana da matukar kyan fuska da kyan diri ga wayo da iya magana. Tun tasowarta abin da ta dauka shine mahaifiyarta ta rasu tasan inna itace kakarta mahmud shi ta dauka mahaifinta, tun kan ta mallaki hankalin kanta mahmud ya gargadi kowa a gidan kada wanda ya sake ya bayyana wa nabila ainihin lbr ta, duk wanda yayi haka zai fuskanci bacin rai kusan a rayuwa irin tasu babu abinda ta nema ta rasa tana da kokari sosai a makaranta. Rayuwar mahmud ta sami cigaba yana daga cikin masu fada aji a cikin family dinsu, ya gina baban gidansa a nan kano ya maida matarsa can har ya kara auran wata matar sunanta ummulkhairi, amma dai ita nabila tana gun inna har yanxu nabila tana da tsiwa sosai ba ta fiye barin ta kwana ba da yawa suna sonta ne saboda kyanta da tsiwarta matan gidansu irinsu dije da ladidi sun tsaneta ainun ganin yadda take da farin jini dun tsiwar nan tata bata hana mutane su sota ba. Su kansu din tsoranta suke ji basa iya taka ta da sun gaya mata zata mayar saboda gaba daya sun gama nuna mata basu kaunarta ita kuma ba tsoron kowa take ji ba a gidan tana abin da ta gadama ne. Shekaranta goma sha daya kacal ta gama primary a ta sha biyun tana secondary wanan shekara ta sha shida ga watan haihuwarta tayi candy tana zaman jiran sakamako jarrabawar tawanda zai bata damar shiga jami'a kamar yadda take ta buri. Tun tana yar mitsitsiyarta take da son karatu duk jarabawarta ta daya take zuwa duk sanda tayi na biyu da kuka da ciwon kai har da zazzabi take kwana. A da kamarsu daya da mahaifinta tahir daga baya ta juye kamanin mahaifiyarta sak. Tun tana da shekaru goma sha biyu a duniya tayi saukar karatun alkur'ani mai tsarki, rayuwar nabila tana da ban sha'awa sosai duk tsiwarta bata da raina na gaba da ita sai in fa na gaba da ita ne ya yadda girmanshi ya neni nuna mata san zuciya da fin karfi to anan fa babu ragowa tsakaninsu. Yau satin su biyu da yin candy da yammacin lahadi tana kwance a kan gadon inna ta sha kwalliya da wani dan ubansun matereal ruwan powder yayi mata kyau iya kyau, tana ta zuba kamshin turare ta da tafeso. Alhaji mahmud ya shugo dakin ganinta a kwance ya bata rai wai ke me yasa naxo gidan nan a kwance zan ganki, kamar wata mara lfy. Ta mike zaune cikin shagwaba tace to me zanyi abba? Yace bazaki je kina tayasu aikin girki ba kema ki dinga koya. Ta bata rai tace nifa baba ba sai na koya wani girki ba tunda ba aure zanyi yanxu ba. Inna ta harareta tace ba aure zakiyi ba to me zakiyi? Ki kina nufin duk makarantar da kikayi bata isa ba sai kinyi wata. Tace inna ni fa karatu yanzu na fara yinshiduka shekaru goma sha shida a dinga maganar aure. Baba mahmud yace ke nabila shiga hankalinki ki saurara kiji abin da zan gaya miki. Tunda take bata taba ganin ya bata ranshi a kanta haka ba, duk lokacin da zai mata magana zai matane cikin lallashi, lallai yau tasan maganar ta gaske ce ta sauko daga gado ta lankwashe kafafu a gabansa. Yace ke nabila ada nayi niyar na barki kiyi karatunki iya yadda kike so amma yanzu lamari ya sauya. Akwai kanin abokina mai suna mujahid yana karatune a malaisiya yazo hutu nan kano zai koma nan da sati biyu a jiya da suka zo gidan nan ya ganki yace yanaso, abokij yayansa alhaji mukutar shine ya nema mai auranki a guna kai tsaye nace na bashi. A razane ta dago kai suka hada ido tace eh? Ya amsa yace eh nace na baiwa mujahid ke kuma za a daura auranku nan da sati daya, wani satin in ya zagayo insha Allahu za ayi biki ku tafi malesiya inda zai ci gaba da karatunsa na likitanci ke kuma xai nema miki makarantar da tadace da ke kema ki ci gaba da naki karatun kan fannin duk da kike so kuma kika zaba, na amsa na bashi ke saboda dalilai uku na farko nasan na isa dake kina mini kaunar da zakiyi mini biyaya kan duk abinda na umurceki, nabiyu nasan tun kina karama baki da burin da ya wuce karatu. Sai na uku na amince da mijahid saboda yaron arziki ne mai mutunci dan masu mutunci, kuma mai ilimi, wanda yake da ilimi shi yasan darajar ilimi. Ki tashi ki shirya anjima zai zo ku gaisa. Ya mike ya fice ya barta zaune ga badaya gwiwowinta sunyi sanyi, ta waiwayo ga inna tace inna kinji wani hukunci da baba ya yanke min kai tsaye. Inna tayi murmushi irin tasu ta manya tace uhum nabila yasan ya isa ne wanda bai isa ba ai ba zaiyi haka ba. Tace inna da ma haka ake bada mutum aure batare da anji ra ayinsa ba yana so ko bai so ba? Ba tare da an bada dama ya ga mijin da za a bashi ba? Nan ma murmushi tayi ta ce eh haka ne kuma da ba haka ba ne? Me kike nufi inna?Nabila ina nufin eh ana haka abawa mace miji batare da ta ganshi tana son shi ko a a ba. Kuma ana bawa mace dama ta zabi duk mijin da take so a aura mata musanman a zamani irin wannan da ake kiranshi wayayen zamani wanda aka ci gaba ma alokacinmu idan za ayi auran yarinya ba ruwan iyaye da batun soyaya ya rinya ba zata ga mijin auranta ba sai tayi kwana uku ko ma bakwai a gidan mijin ta. Haka shima mijin ba zai ga matarshi ba sai anyi wadan nan kwanakin. Tace inna to tunda zamani ya sauya ba a wancen zamanin muke ba ya dace baba ya tambaye ni ko? Tace eh ya dace yayi hakan amma tunda baiyi ba yana da hakkin kiyi mai biyyayya. Wai shin ma in tambayeki nabila. Cikin sanyin murya tace ina jinki inna. Kinsan wacece mahaifiyarki? Girgiza kai tayi tace bansantaba inna, ba zan santaba tunda kince tun ina yar karama tarasu. Ta girgiza kai cike da tausayi ta dafa kafadarta ta ce nabila ba zai yiwu muci gaba da boye maki abinda ya dace ki sani ba game da rayuwarki, dan haka ba gaba da boyuwa zaiyi din ba, dakiji a wani gun inda zakiyi muna mumunan fahimta gara kiji daga bakina a ta kaice dai nabila mahaifiyarki nanan a raye bata mutuba. Afirgice ta ce inna karki razanar da zuciyata.... Ta katseta tace ba razanar dake zanyi ba nabila gaskiya zan gaya miki duk abinda zakiji daga bakina ki dauka gaskiya ne ba wanda zai gaya miki fin hakan sai dai daidai da haka ko ma kasa da shi. Inna tas duk la barin iyayan nabila na gaskiya ta gaya mata. Babu abin da ta boye mata, nabila ta daskare a gurin tana mamakin kasancewarta ba diyar babanta mahmud wanda ya haifa a cikinsa ba kai amma ya cika masoyi a gareta na gaskiya. Ta mike bata ce da inna ko mai ba ta dau hijabinta ta fice a kofar gida ta iske baba mahmud tare da mutane suna hira ba abin da ya dameta da mutane ta fada jikinsa tana wani irin kuka mai firgitarwa, yariketa jikinsa na rawa yace lafiya nabila? Ganin ta kasa magana yasa ya jata cikin gida dakin inna me ya samu nabila ko dai dan na mata maganar aure ne?Inna ta ce ba haka bane na gaya mata lbr iyayanta na asali ne. Ya ce haba inna me yasa kikayi haka, bayan kinsan zai jefata tunanin da zai din ga wahalar da rayuwarta ne? Tace yin haka ya zama wajibi a wannan sirri ne da ba zai iya cigaba da boyuwa ba. Jinsa daga bakinmu yafi ta jiyoshi a wani guri. Ya zauna kan kujera har lokacin nabila na manne jikinsa tana kuka ya share mata hawaye ya ce nabila ki daina kuka kasancewata ba ni na haifeki ba ba zai zamo illa ga rayuwarki ba, zakici gaba darayuwa dai dai da yadda kike yi, in har mahaifinki na raye zaki gansu insha Allahu. Nabila kuka take tana karawa ta kara magana, inna bata kuma cewa kmi ba sai aikin lallashin tunanin nabila shine duk soyayar nan ta baba mahmud gunta bashi ya haifeta ba. Ita kuwa mai tayiwa mahaifiyarta da ta tafi ta barta tsawon wanan shekaru ko sau daya bata zo ta ganta ba. Har bayan sallar isha i kuka take tana zaune kan sallaya, Aliyu ya shigo yace ance tana da bako a waje tace ya tambayo sunansa ya ce ance mujhid ne. Gabanta na faduwa ta mike ta kara gyara jikinta ta daura kallabi da a tamfa super tayi kyau iyaka, ta yafa karamin mayafinta iya kafada ta sako takalmi mai tsini tafito zure tana takun kwas kwas kai kace wata kasaitaciyar liyafa zata. Wata yar ubansun mota ta hango irin new modern din jeep din nan lafiyaya tana zuba kyalli tundaga nesa take juyo wani tautausan kamshi mai ratsa zuciya na tashi. Ta isa gun jikinta ba kwari ta tsaya daidai saitin da mai motar zai hangota, mujahid na kwance a mazaunin direba ya kwantar da kujera music ne mai taushi ke tashi, yana sanye ne da baki da farin kananan kaya duk duk yanda naso kwatanta mujahid a kyau da komi abin ba zai taba yuwuwa ba. Ko wanda bai san duniya da abinda ta kunsa ba yasan mujahid ya hadu dogo ne sosai mai jiki madaidaici ma'ana shi ba mai kiba ba kuma ba shi da rama. Inda kyanshi ya tattara shine a fuskarsa, ya mallaki fuskar da duk namijin da ya mallaki irinta ya isa yayi yanga kowane mutum akwai inda ya cika akwai ya tauye, a iya gane gane nabila na maza a kanobata taba ganin namijin da ya kama kafar mujahid a kyau ba.Komi nashi yayi mata nantake taji nunfashinta na neman daukewa lokacin da ya warware mata kwala kwalan idanunsa yana mata wani irin kallo wanda bata taba gani a gun wani da namiji ba. Itama shi take kallo har ta gaza ta mai da idanunta kasa ta cikin sanyin murya tace sannu da zuwa. Wato tunda tafito tasan yau tayi arba da kyakyawan namiji amma ba ta gama tabbatar da haduwarsa ba sai da ya budi baki ya amsa mata sallama da sannu da zuwan da ta yi mishi. Ya buda mata mota kusa dashi yace ta zagayo ta zauna. Tashiga tana sa kanta a motar wani sansanyan kamshi da sanyin Ac suka ratsata tayi ajiyar zuciya har saida mujahid ya kalleta. Ta gaida shi ya amsa bata yi mamaki ba da taji hausar sa bata fita sosai yafi kama da larabawa. Yace nabila ko? Tayi karfin halin amsawa eh haka sunana yake. Kiran sunan ta da yayi ya shigo da sabuwar faduwar gaba da sanyi a jikinta ta ce, subhanallahi wane irin mutum ne yau na hadu dashi kuma. Yace nabila menene burinki na rayuwa a yanzu? Ba tambayar da ya dace ya fara yi mata kenan ba a ganinta, kumababu wani namiji da zai yi mata irin wannan tambayar bata gwasileshi ba kai a ganinta shisshige ne yazo mata da shi amma ina mujahid ya wuce haka a gunta. Shi kadai ne da bakinta ya fara mutuwa a gabansa, ta kasa katabus kanta na kasa kamar ba ita ba. Da kyar ta tattaro natsuwarta tace bani da burin da ya wuce karatu mai zurfi. Murmushi yayi wanda yayi masifar kara mai kyau, ya lumshe ido yace haka babanki ya fada mana a jiya lokacin da na shaida mai ina sonki. A lokacin mu munganki ke baki ganmuba muna tsaye mu da babanki da abokin yaya Alhaji mukutar wanda nake sauka a gidanshi idan nazo hutu nan kano. To sai dai bai fada mini mai kike son karantawa ba, ina son ji daga bakinki. Tace to ina son zama lauya ina son zama likita ina son zama malamar makaranta masana koyarwa. Yace na yaba ma zaben ki duka din da kika zaba zasu dace dake duk da haka nafi maki sha'awar likita. Tayi murmushi ta ce ko? Yace yes. Tace dalili fa? Yace sai nan gaba zakiji. Ta ce ba damuwa. Yace nabila. Sunana mahmad nuraddin ana kirana da mujahid saboda suna daya da mahaifina, mu larabawar kasar egypt ne, ina da iyaye a nan kano shine abinda yake kawoni kano lokaci lokaci yin hutu. Shekaruna na haihuwa duka ashirin da biyar bansan da lilin da yasa iyayena keso inyi aure ba. Ko da yake suna burin mu cika musu gida da jikoki ne inaga shi yasa suka damu da aure na inaso ki bani hadinkai muyi aure ko mai zan maki iyayena ma zasuyi maki, amma karki damu da soyaya ta dan gaskiya na ce ina sonki ne zan aureki dan in huta da fadan da iyayena ke mini kan maganar aure ba wai dan lokacin auren yayi gareni ba. Bani so su bani matar da bani ra ayinta shi yasa nace ina sonki. Gaba daya sanyin Ac din dake motar sai ya zamewa nabila hucin wuta sabo da gumin da ya jikata. Wane irin al'amari ne kuma wannan mai kama da almara, cikin sarkewar murya tace kana nufin ba sona kake da gaske baza ka aureni dan gudun kar iyayenka su baka macen da baka ra'ayi? Ya kara kashe murya yace no karki damu kanki da batun soyaya aguna ina da wani irin hali game da mu'amala da mata sai nan gaba zaki fahinci hakan ke dai in kin amince da aure na shikenan. Ta maida kanta kasa tana tunani saboda al'amarin da yazo rayuwarta, ya duba agogo yace ni zan koma dan ina so inyi asubanci tafiya maiduguri ina ga wani abokina. Ya dora mata rafar dubu dai dai sababi yace ki sha lemo na shiga wani super market da niyar inyi maki tsaraba bansan me kike so ba. Muryarta na rawa tace dan Allah ka bar kudinnan sunmin yawa. Dan Allah karki damu dauka ai ba rokana kikayi ba nine nayi niyya yaron gidan ma zan iya yimai kyautar da tafi haka ballanta na yarinyar da zan aura.Lokacin da nabila ta shugo gida tunaninta ta gayawa innarta cin fuskar da mujahid yayi mata, wai kamarta yau da take ji da kanta mujahid dan yana ganin ya isa a soshi ya budi baki yace kar ta damu da neman soyayarsa ya nemi auranta ne dan iyayanshi sun damu suna son yayi aure bai son a hada shi da wanda bai ra'ayi. Sai kuma tayi tunanin inna fa mahaifiya ce ga mahmud bawan Allah da ya riketa tsakani da Allah ya ke kaunarta dan Allah har bata iya sanin ba shi ne ya haifeta ba saboda tsantsar kauna da soyayar da yake mata, sai a wanan rana da hali yayi aka fada mata. In banda taji daga majiya mai tushe bakin da ba zai yi mata karya ba da ba zata taba yarda cewa ba mahmud ya haifeta, kaunar da yake nuna mata ko yayan cikinsa ba a ga yana musu haka ba. Wanan tunani ya sa jikin nabila ya dada sanyi, ta ajiyewa inna kudinin da mujahid ya bata ta koma gefe ta yi tagumi. Inna tace yaya na ganki cikin damuwa baki sonshi ne? Nanda nan ta saki fuska tace ina sonshi mana inna nidai ina tunanin rabuwa dake ne zuwa rayuwar da baka saba da ita ba, a gidan da baka saba dashi ba cikin mutanen da baka saba dasu ba. Inna tayi murmushi tace nabila tun kina da watanni goma kike hannuna babu wani abu naki da zai buya gareni ko motsi kikayi nasan abinda kike nufi idan har wannan yaro bai maki ba.Ko wane motsi kikayi nasan abinda kike nufi idan har wannan yaron bai maki ba kina da damar ki ce baki so ba zan bari ayi maki auran dole ba duniya na iya zagin mu a ce dan ba iyayenki ya sa muka tilastaki yin abinda ba ki so. Nabila tace dan Allah inna daina wannan maganar karki sani kuka, wannan mujahid din da baba ya ban namiji ne wanda babu macen da ta isa tace bata son shi. Duk yadda ake son namiji ya wuce nan zancen ince bana sonshi ma bai taso ba ni ban ni ban taba kallon wani namiji da sunan soyayya ba. Saboda ba soyayar ce a gaba na ba, ban san yadda ake soyaya ba tun da ban taba kamuwa da son wani ba amma wallahi inna ina hada ido da mujahid na ji gaba daya yanayi na ya sauya na tsinci kaina a tunanin da ban taba shiga ba. Ko da ban san meye so ba na san na kamu da son mujahid ta farat daya. To wlh inna ba mujahid ba ko wane irin mutum baba ya kawo ya ce na aura zan aureshi na gode wa Allah da ya nu feki da bayyana mini gaskiya lamari a kan rayuwata, hakan ba zai sauya matsayin baba a guna ba illa ya kara daukaka darajarshi a zuciyata ta yadda zan sadaukar da zuciyata inyi mai biyya bakin rai bakin fama. Saboda haka dan Allah inna ko da wasa kada kinunawa baba bana son mujahid don ina sonshi din. Ko da bai kai matsayin da za a soshi ba zai ci darajar baba in soshi in aure shi in zauna dashi, balantana kuma mutum ne shi din mai daraja namba daya cikin maza. Inna ta ce to Alhamdulillahi ina jin dadin yadda kike da wayo da hankali nabila, Allah ya yi miki albarka amma me ya sa kika karbar mai kudi masu yawa haka? Tace shi ya bani inna na ce ya barshi ya ce sai na amsa. Alwala tayi shafa'i da wutiri ta hau katifarta ta rufe idonta kamar tayi baci, tayi haka ne dan bata son hirarsu da inna yau tunani ne kawai a gabanta ta fado wata sabuwar rayuwa da bata taba shiga cikinta ba. Lallai mujahid ya isa namiji duniya da za a soshi illar daya ya fito ya fada mata baya soyaya a gabansa zai aureta ne kawai dan ta zame mai garkuwa daga auran dolen da iyayensa zasu iya mai in bai kawo matar aure ba. Shin ina makomar rayuwarta a gaba lokacin da mujahid zai gaji da ita tunda baso na hakika yake mata ba. Tana jin inna na fadin ho yar nema yau ba za a karanta mini lattafi ba a kai barci?ba ta ko motsa ba tana ji ta gama tata hidimar ita ma ta kwanta. Tam bayoyi ne barkatai ta kema zuciyarta babu amsa, da gari ya waye haka ta tashi sukuku jiki ba kwari, gashi ba makaranta balantana aje a shiga kawaye dauke mata kewa da rage damuwa. Inna na kallonta da yake bata son matsa mata ba tace da ita ko mai ba wuraren karfe goman safe baba mahmud ya iso gidan bayan sun gama gaisawa da ragowar matan ya shigo dakin inna, nabila ta gaidashi zata tashi ya janyo hannunta yace haba yar lele na ya naga duk kinyi sanyi yau? Ko baki son mujahid din ne?nikuwa gani nake kamar zai dace da rayuwarki zai kula min dake. Tace baba ina sonshi ba abin da yake damuna. Yace alhadulillah nasan dama ba zaki bani kunya ba nabila ta sai a fara shirin rabuwa da inna dan in an jima zasu kawo kudin aure da kayan lefe. Inna ta ce da wurwuri haka? Yace eh ai na gaya muku ba ma zauni bane kasar zasu bari nan da sati biyu. Gaban nabila na faduwa ta tashi ta shiga daki ta kwanta tana jin yadda baban ta yake bayyanawa inna kirkin mujahid da kyakyawan dabi'unsa. Bayan tafiyar baban nata ta shaidawa inna zata gidan miniyarta fauziya da sukayi candy tare bata da aminiyar da ta wuce fauziya gidansu na karshen layinsu inna tace adawo lafiya amarsu ta ango. Ta zunburi baki ta fice. Fauziya na ganinta tace yanzu fa nake shirin zuwa gidanku.... Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Launin Fata 2-05 Posted by ANaM Dorayi on 07:06 PM, 22-Oct-15 Under: Launin Fata Nabila ta wuce suka gaisa da ummansu fauziya suka shige dakin su fauzeeya tazu ba mata ido tace ke yaya na ganki haka duk idonki yayi ja lfy? Nabila tace fauzeeya ina fa lafiya yau saura kwana shida a daura mini aure. Fuzeeya tace da B.U.K ko A.B.U zaria ko?in ba dasu za a daura maki aure ki tafi can ba wane irin aure ne haka bashiri kamar auran baby wasan yara. Tace kinsan Allah aure za a daura mini fuzeeya baba ne ya badani kai tsaye ni kuma na amince. Fauzeeya ta fido ido tace dan Allah in gaske kike bani lbr yadda akayi in zolaya ta kike ki bari kawai muyi wata hirar. Nabila ta bata rai tace kin taba ganin nayi maki irin wanan wasan? Ta zaiyana mata duk abubuwan da suka faru. Fauzeeya ta kasa magana dan mamaki sai da nabila tace fauzeeya bansan yadda soyayya take ba amma ko shakka babu nasan na kamu da son mujahid ta farat daya. Sai dai abin takaici mujahid ba sona yake ba, kuma da ganin idontasa kinga tantirin wayayen mutum budewar idonsa sunyi yawa ina gudun shiga wata rayuwa da ban saba shiga ba. Fauzeeya tace tabdijan ai wlh tun wuri ki fitar da batun damuwa a zuciyarki ki natsu kisan yadda zaki cunkusa mashi soyayyarki a cikin zuciyarsa ya soki.Tayaya zanyi haka fauzeeya? Na gaya maki yace yana sonane ba dan wai yana sona din ba sai dan ya kubutar da kansa daga auran dolen da iyayensa zasu iya yi masa. Fauziya tace baki da wayo nabila shi mujahid yana gudun iyayensa suyi masa auren dole, kenan yana nufin kema dole yayi ma kansa zai aure ki.idan wacen yarinyar da iyayensa zasu iya bashi dole ce ke din wayasa yace yana sonki, ai idan hakane da yayiwa kansa auran dole gara iyayensa su mai. Tunda har ya kai idanunsa kanki in dai zuciyarsa ce ta kawata masa wani abu naki har yaji zai iya zaman aure dake. Zai iya yiwa soyayyar bata gama ratsashi ba kamar yadda ya gaya miki, dama wata soyayar tana shiga zuciyar mutum ne a hankali yayin da wata zatashiga da karfinta. to shi nashi salon soyayar kenan na tabbatar idan babu rami babu abinda zai kawo magaar rami, idan babu so ko kaka babu abin da zai kawo maganar aure. Baya sonki zai sha'awar zama dake, zama kuma na aure, zaman da ba asan iya kacinsa ba sai Allah. Wata kila shi irin mazannan ne da basu son raini, yana ganin ke karamar yarinya ce idan ya fito maki da soyaya fili kya iya rainashi. Saboda haka ki kwantar da hankalinki nasan tunda kika ce mujahid na da kyau ya hadu lallai ya hadun saboda ban taba jin kince wane ya hadun ba.Mujahid zai soki in dai har kincika mace zaki iya samowa kanki soyaya a zuciyarsa. Ko waye mujahid ko wane irin kyau gareshi wlh nasan ba zai fi karfinki ba, ba zaifiki kyau ba sai dai yafiki gogewar fata na jin dadi da yanayin gurin da yake rayuwa da ilimi da wayewa da budewar ido Nabila tayi gauran numfashi tace fauzeeya dan bakiga mujahid din bane shiyasa kikecewa ba zai fini kyau ba ke na gaya maki tunda nake fa ni ban taba ganin kyakyawan namiji irinsa ba duk yanda naso kwatanta shi ba zai kwatantu ba. Ni dai nasan na gamu da gamo natun da na dora idona a kan mujahid ban kara samun kwanciyar hankali da natsuwa ba gashi abin mamaki bai ji nauyin ya fito ya nuna min ba matsuwa yayi da sona ba.Fauzeeya tace na gaya maki kada ki bari wanan ya dameki namiji ne fa, tunda ya amince zai aureki ai an gama magana kuma sai ya furta da kanshi tunda ba wanine yayi masa tallarki ba ba wani ya tursasa shi ba. Duk abubuwan da fauzeeya ke so nabila ta gane jinta kawai take bata gamsu ba ta dawo gida cikin sanyin jiki lokaci guda kowa a gidan ta sauya duk wanan surutun da tsiwar sukai ta koma ta koma zama shuru har bata so ayi mata magana tafi son tayi zamanta ita daya tana tunanin mujahid. Tunani mai dadi kuma mara dadi idan ta tuno kyanshi da haduwarshi taji dadi in ta tuno yace ba dan yana sonta zai aureta ba sai dan wani dalili gaba daya sai taji hankalinta ya kuma tashi tana tunanin makomarta a irin soyayar da ta damki zuciyarta kai tsaye. baba mahmud ya shaidawa duk mutanen gidansu cewa nabila tasamu mijin aure za ayi aure ne nan da sati 2 kuma anjima zai zo ya gaisa dasu. Abinka da gidan yawa nan da nan aka shiga tsegumin wane irin aure ne haka kamar auren yartsana yau she mijin samu babu wanda yasani har aka yanke lokacin aure. Ladidi tace duk kinibibin mahmud ne da ya dau son duniya ya daura a kan wanan mara kunyar da bata ganin kan kowa da gashi, shi zai nemo miji ya kawo mata. Dije ta ja tsaki tace ai mu rabi ta tafi ta barmu da irin jaraba, yarinya tasa ba mai kallon yayan mu, duk wanda zai magana sai dai yayi a kanta. Ta dunka yanga tana yauki kamar kilaki. Lubabatu tace uhum an gama feleken karatu ne da ba cewa sai anyi digirin da girgir ba? Mu yayan mu ba yaya bane sai ita? Dije tace wai ke haka aka bar mahmud, tun uwarta tana gidan ta gama dashi da ta tashi tafiya ta hada jinin sa da na yarta ta yadda ta fidda son kowa a zuciyarsa sai na yarta yake mata son da bayawa ya yansa da ya haifa kila har uwarsa da ta kawoshi duniya. Lubabatu tafi kowa jin haushi al'amarin shi yasa ta kasa zama tunda aka kawo maganar auran nabila.Tun safiya ake ta ya madidin maganar nan har yamma lokacin da baba mahmud yazo yasa yara keta share gidan ana gyarawa, ta kai ci ya kara isar matan gidan sai dai babu yadda suka iya babu wanda ya isa ya kawo wa mahmud raini, basu isa yace za ayi suce a a ba. Kar fe biyar dai dai na yamma Mujahid da abokinsa amir suka iso gidan dan gaida surukansu a cikin motar da yazo jiya suka zo, tuni yara sukayi dafifi suna kallon motar da masu motar wasu suka ruga suka gayawa iyayansu ai mijin nabila bature ne ba bahaushe ba, nanfa suka shiga rarraba idanu manyan kaya su mujahid suka sa tun suna kofar gida kamshin turaransu ya bay baye gidan, baba mahmud ya yo masu jagora suka shigo cikin takun isa da kasaita, gaba daya matan gidan na tsakar gidan, da yayan su nabila ce kawai kwance a dakin tana shakar kamshin mujahid ta lumshe ido wata zazzafar soyaya ta kara kwarara a cikin zuciyarta tamike ta leko ta window.Sai a yau ta kara tantance waye mujahid da ta ganshi a cikin haske kai subhanallahi wannan mutum da kyau yake. Dije da ladidi da lubabatu sai share zufa kawai suke dan tsananin bakin ciki ko gaisuwar da su mujahid ke musu basu iya amsawa ba, iyakar burgewa kam duk hassadar mutum

Chapter 9 of 12