Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dan ba dana bane da babu abin da zai sa in zo a wulakantani a banza. Kowa ya ci gaba da fadin albarkacin bakinsa cikin dacin rai tahir yana tukin mota ya rasa abin da ke mai dadi a duniya ya rasa da me zaiji da takaicin gidan su Rabi'a ko takaicin maganganunsu da ba zasu barshi ya ji da abu daya ba, haka a gidansu aka dinga yamadidin maganar ana dada zuzuta lamarin har da masu cewa uban Rabi'a ya zazzagesu, kai maganganu dai iri iri marasa dadi. Tahir ya shiga daki ya fidda kayan jikinsa ya yi wanka ya kwanta kan katifa zuciyarsa ba dadi ya dau waya ya kira Rabi'a wai ya ji muryarta ko ya ji sanyi a ransa, amma tana dagawa sai ya ji ta tana kuka ya rasa abin da zaice sai ya kashe wayar ya ci gaba da kwanciya yana son yin barci ya kasa sai juyi. Sai karfe hudu saura kwata ya fito yana sanye da farar jallabiya ya festo furaran yayi alwala ya shiga masallaci ya yi sallar la'asar cikin jam'i ya shiga cikin gidansu dakin yaya tana zaune kan abin salla itama sallar ta idar ta zuba mai ido ta ce yanzu za ka je dauko amaryar ya ce Eh. Ta ce uhum ni ban taba ganin aure irin wannan ba Allah dai ya kyauta an gama share gidan. Ya ce Eh cikin kudin da mahaifiyar Rabi'an ta ban na sai duk abubuwan da gida ke bukata an gyara gidan gaba daya. Ta ce shi kenan Allah ya sa an yi a sa'a. Sallama suka ji ta mahmud yana fadin kai tahir ai an hutar da kai ga amaryar nan ubanta ya sawota a mota ya biyoka da ita. Ya dafe kirji ya ce suna ina? Ya ce suna kofar gida shi ya ce in ma iso da kai. Hajiya yaya ta mike tana fadin iko sai Allah. Abba yana tsaye jikin mota yana hura hanci, rabi'a na tsaye kusa da shi tana kuka kamar ranta zai fita. Tahir ya durkusa har kasa ya gaida abba, abba ya ce kai da Allah mike munafukin banza da wofi an gaya ma nazo ne dan ina bukatar gaisuwarka, matarka ce na kawo maka naga kayi nawar zuwa daukar ta bana son ci gaba da zamanta a gidana. Ya finciki Rabi'a ya ankadata jikin tahir ya shiga mota ya ja da karfi ya bada musu kura ya bar gun. Wani irin gumi ya dinga ketowa tahir, musamman ganin yadda lokaci guda labarin gidansu abu ga babban gida, nan da nan aka firfito matan gidan da yaran aka shiga surutu iri iri kowa da abin da zaice har sai tahir da Rabi'a suka rasa me kwakwalensu zasu dauka a ciki ya kama hannu rabi'a suka shiga dakin hajiya yaya ta dunkule kanta a hijabi tana kuka na fitar hankali. Hajiya yaya ta ce ki daina kuka yar nan kin zo gidan mai sonki ........ Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Launin Fata 1-06 Posted by ANaM Dorayi on 04:49 PM, 06-Oct-15 Under: Launin Fata Insha Allahu zaki ji dadin zama da tahir ba wai dan ya kasance nawa ba nake yabon shi sai dan halinsa na amitance, ballantana ke da yake so. Yanda tahir ya zauna ya zuba tagumi bai iya cewa komai ba dan haushi kallon Rabi yake tana kuka a matsayinsa na namiji bai dace ya yi kuka ba shima da yayi kukan.A dakin hajiya yaya Rabi'a ta kwana kuka ta tashi da shi ga kunyar mutanan gidan da suke lekowa gaisuwar gulma suna yada mata habaici duk da haka su dinma tun a ranar suka gano abinda ya sa tahir ya mannewa Rabi'a matar muhmd zarah ta ce kaga yarinya kamar aljana dan kyau, tabdijan ai dole tahir ya kasa sukuni a kan ta. Wata a cikinsu matar kawu tanimu mai suna dije ta ce nifa tsoro ta dinga bani ganinta nake kamar ba mutum ba, cikin dare firgita na dinga yi sai da nayi ta karanta ayatul kursiyyu naji daidai. Washegari tun da sassafe tahir ya dau matarsa suka bar gidan bisa rakiyar hajiya yaya ita kadai gidansu ya yi kyau sosai ba wani girma gareshi ba amma anyi mai tsari mai kyau. Hajiya yaya ta yi musu nasihar zaman lafiya da hakuri da juna ya daukota a motarshi ya dawo da ita gida ya koma gun amarya tana kwance bisa gado zazzabi ya rufeta jikinta yayi zafi zau zau, ya zauna ya kamo hannunta ya ce nasan daman wannan kukan sai ya sa miki zazzabi, bari in siyo miki magani. Bayan ya dawo daga siyan maganin ya shiga kicin ya dafa mata shayi ya soya kwan ya hado da bread ya zo ya dagata ya shiga bata a baki da kyar ta sha kadan ta sha maganin ta koma ta kwanta, shi kuma ya fita ya sayo mata kayan sawa kasancewar Abban ta bai kawota da komi ba. Abin mamaki yana dawowa gida ya iske ummi da asiya sunzo ya zauna cikin fara'a da girmamawa ya gaidasu ya dora da godiya bisa karamcin da aka yi masa. Ummi ta ce ba komi ai duk yiwa kai ne bata da bukatar komi a gareshi illa ya ba mara da kunya ya riki amanar Rabi'a. Ya ce haba ummi wlh idan naci amanar Rabi'a sai amana ta cini, ai ni tsakanina da rabi'a sai Allah ki ci gaba da yi mana adu'a.Rabi'a na kwance kusa da ummi har lokaci idanunta basu daina hawaye ba bakin cikin abin da abbanta ya yi mata ya tsaye mata a zuci. Asiya ta matsa daf da ita tana share mata hawayen ta ce ki yi hakuri Rabi'a bai dace ki dinga kuka haka ba. Ta ce bari in yi kuka anti asiya abin kukan ne ya saman, kina kallon tozartawar da Abba ya yi min. Asiya ta ce wannan yawan kukan da kike tamkar butulci ne ga Allah da ya azurtaki da nagartacciyar uwa mai tsoron Allah wadda babu son zuciya a cikin dukkan al'amuranta. Idan kin kalli Abab kin kalli abinda yayi miki ranki ya baci to kada ki tsananta damuwa har damuwar ta shiga rayuwarki ki yi sauri ki kalli gata da kaunar da ummi ta nuna miki, kiyi farin ciki ki godewa Allah da ya sa kina da rabon auran wanda ranki ke so sai ki zauna lafiya. Shima Abba wata rana zai gane kan kuskure yake ya dawo kan hanya. Da kyar rabi'a ta dakatar da hawayanta ummi tayi musu alkawarin tana tare da su in sha Allahu ko yaushe suke bukatar wani abu su sanar da ita cikin sirri zatayi musu kuma duk sanda ta samu lokaci zata dinga zuwa tana ganinsu, su ma su dinga zuwa suna gaida Abba ko da zai musu wulakanci kar su damu watarana sai lbr. Rabi'a ta marairaice fuska ta ce dan Allah ummi ku bari sai da yamma. Ta ce yini yanzu ma asibiti na ce zamu da kyar abba ya bari muka fito dan ya yi zargin nan za mu zo. Tahir ya rakosu inda suka yi parking yana godiya da fatan Allah ya sa a gama da duniya lfy. A bisa hanya ummi na jan mota asiya na zaune gefenta ummi ta ce, asiya kinga sirikin mutunci wanda ya san mutuncin mutane ya san abin da yake. Ba irinsu kabir kaduna ba kn kin san karshan wancan watan da naje ni kadai din nan a gaban nafisa lokacin da tayi rashin lafiya na shiga gidan yana kwance a falo daga shi sai singileti da gajeran wando, yadda na yi sallama haka ya amsa min shekeke ko kallon arziki bai mini ba, na zauna ina zaton ya sha giyar ne tayi mai karo sai ni nace mai ina kwana, yana wani mitsitsike ido ya ce lafiya, na ce ina nafisan ya ce tana ciki, ni dai na shiga ciki na iske ta kwance tana faman kuka na ce lfy ta ce wai kwananta 2 a asibiti tun da kabir ya kaita baije ya duba ta ba da aka sallamota ma sai makociyarta ma waya ta zo ta daukota da ta zo gida ta mai magana sai cewa ya yi bai ajiye mata kudin da zasu isa a yi komi ba me zaije ya yi, ko in yaje shi zai cire mata ciwon? Na yi murmushi na ce to mene na damuwa har kina zubda hawayenki a banza. Ta ce ummi dole in damu ace kana auran miji bai damu da kai da rayuwarka ba da ka yi magana sai ya turo ma kudi, kudi su ne maganin damuwa? Na ce ah su ne mana nafisa. Na yi mamakin jin wannan maganar ma a bakinki, ke da abbanki kika ce ni har da kudi ba matsala dama kin daina kuka kin ci gaba da zaman kudin da kike tunda fari kin nuna wa kb ku bayin kudi ne shi yasa ya takaku ya zageku ke da abba ya biya kudin zagin kuma a zauna lafiya, ni dai ba zan iya maganin damuwarki ba abba kuma ba zai kalli matsalarki ba saboda duk wata kb zai jefi bakinsa da damin kudi. Da na tashi dawowa wai marar kunyar kb din nan sai ya dauko kudi ya biyoni da su a gaban direba mannir ya mika mini na kalle shi a lalace na ce an gaya ma nima kwadayin kudinka ya kawo ni? Sai ya ce oh haka ne ashe fa ance ke bakya da son kudi to ki sauka lafiya ki dinga yiwa mijinki nasihar ya rage son kudi. Kiji dan girman Allah har yau maganar nan ciwo take mini da na dawo gida na gayawa abba yadda muka yi da kb ko a jikinsa sai ma ya nuna nice mai laifi ni naje gidan kb na gaya mai magana shi yasa ya samu damar fadar haka. Wlh asiya ina mamakin abbanku a rayuwata ban ta ganin mutum mai tsananin son kudin Abba ba ina tausaya mai randa son kudinshi zai ja mai fitina ba dai mugun baki nake mai ba. Asiya ta ce ai ba a zancen mugun baki a magana ta gaskiya ko yanzu irinsu kb fitina ne a gareshi dan ba wulakancin da ba sa mishi, ni rannan wani abu da akayi ya ban kunya shi ne muna hira da nazir kafin komawarsu london abba ya shigo falo ya zauna yace nazir dan Allah ka taimaken ka shawo mini kan sultan ya amince ya auri fatima ban son ya kubuce daga gidan nan ina son hada jini da su, nazir ya ce abba dan Allah ka daina zubda girmanka gun sultan kana rokonshi fatima ba girman da ta isa aure tayi ba karamar yarinya ce ko secondary bata gama ba ina ga lokacin auranta baiyi ba sultan bai son auran karamar yarinya. Abba dai yamatsawa nazir kan ya nemo mai sultan a waya su kara magana abin haushi da nazir ya nemoshi suka gaisa ya ce Abba ke sö magana da shi sai ya yi tsaki ya ce gaskiya ba ni son magana da wannan kwadayayyan tsohon, kudi yake nema duk abinda zaka kai na neman auranka da asiya ka ninka biyu ka bashi a madadin wanda yake tunani ya rasa na neman aurena da Rabi'a ko fatiman da yake nacin na aura. Daga haka sai ya kashe wayar sai nazir ya ce kaji ko abba. Anan ne kuma ya tashi jiki ba nauyi ya fita.Ummi ta ce bakin ciki kamani yake in ina jin wadannan abubuwan ko talaka futuk da bai da komi ba zai abin da abba yake a kan kudi ba, ballantana shi da ya mallaki kudi kamar wanda zai yi guzurinsu zuwa lahira.sanda suka isa gida Abba na tare da su nafisa a falo, abba ya ce har kun dawo? Ummi ta ce eh. Ya tabe baki ya ce jikina na bani ba asibitin kukaje ba gidan waccan marar kunyar kuka je? Ummi ta ce hankalinka ne kan ta shi ya sa kake tunaanin can muka je. Ya ce ko baki gaya mini ba na san kina tare da yarki kuma kece kika taimaka mana ta samu kwarin gwiwar guje mini. Nafisa ta ce Abba ka daina damun kanka tunda dai ka bata wanda take so kuma ka barta da shi in tayi ruwa rijiya in ba tayi ba ma sai. Ya ce kina da gaskiya nafisa na dai gaya muku kada wani a cikinku ya hada kai da Rabi'a ya saurareta, duk wanda na samu yayi haka ba ni ba shi. Asiya ta mike ta bar falon. Yini guda hirar Rabi'a ake gida suna kalubalantar auranta da tahir suna ganin ba zai haifar mata da da mai ido ba. A can kuma sai yamma zazzabin jikin Rabi ya sauka mai gida tahir na ta fama da ayyukan gida ya wanke ko ina tas tas ya goge komi na kyalli ya kunna turaran wuta gida ya dau kamshi da ya gama ya shirya masu lafiyayyar jalop din shinkafa da taji kayan hadi da dankalin turawa da curry sai kamshin girki da kamshin turare ya hadu. Da ya gama ya hada mata ruwan wanka duk tana kwance falo tana kallonsa, ya zo gabanta ya tsaya daga shi sai farar best da dogon wandon shadda ya ce gimbiya za ki iya yin wankan ko in yi miki har yanzu jikinki ba kwari, duk da na ji zazzabin ya sauka. Ta yi murmushi cikin tausayawa ta ce haba gara ka yi wanka ka huta tunda safe da muka zo gidan nan baka huta ba. Yace kar ki damu in dai a kan hìdimarki ne ba zan gaji ba ko zan kwana in yini a tsaye tashi in miki wanka nafi son ki ji dadin jikinki ki san kin zo gidan masoyinki wanda ya sadaukar da dukkan farin cikinsa a kanki da lokacinsa. Zuciyarta tayi mata dadi sosai tayi mai murmushin da yake so ta ce to na gode zan iya yi da kaina amma dan Allah kaima kaje kayi wanka ka huta haka kayi min adon angwanci. Ya yi dariya ya kama hannunta suka shiga bandaki ya rufo mata ya fito ya zuwa nashi dakin ya yi wanka ya zabo ado da fararan kananan kaya ya zuba turaran net work yana fitowa falo itama tana fitowa falon tana cikin atamfar super wax cikin sabbin kayan da ummi suka kawo mata a dazun duk da cewa akwai rama sosai fuskarta da jikinta amma ta yi kyau. Jiri ne yake damunta kawai yanzu ta zube kan kujera ya tsuguna gabanta ya ce ki daure ki ci abinci yunwa ce ke saki jiri nasan kin kwana kin wuni ba ki ci abinci ba Daran jiya dake na kwana na kasa barci yadda naga rana haka daga dare,ban taba ganin dogon dare irin na jiya ba saboda Allah Allah nake gari ya waye in daukoki in dawo da ke gidan nan in samu damar lallashinki in baki abinci ki ci na miki tausa tunda a can babu damar da zan miki. Wlh rabi'a daran jiya kin bani tausayi mai tsanani wannan kukan da kike ya tayar mini da hankali, ko da yaushe adu'a ta Allah ya taimakeni ya bani ikon rike miki amana kin mini halarci mai yawa yaya zanyi in rike amanarki ne in sauke nauyin amanar da na dauka. Ta lumshe ido a ranta tana jin wai waye yafi wani tausayin wani tsakanin ita da tahir. Hawaye ya taru a idöta ta godewa Allah da ya bata namijin da yake sonta so na tsakani ga Allah itama take sonsa don Allah suka yi aure dan Allah. Ta kamo hannunsa ta ce tahir ina kaunarka ina sonka. Ya girgiza kai ya ce Allah sarki Rabi'atul Badawiyya Allah yasa mi ki da Alherin duniya da lahira. Ta ce amin summa amin. Abincinma a a baki ya bata, tun tana jin kunya har ta gaji ta saki jikinta suna hira suna cin abinci. zama mai dadin gaske suke yi tahir ya zama kamar bawa a gun rabi'a duk abinda take so shi yake mata tausayin da yake ji nata har ya yi yawa, yana ji da ita kamar kwai. Haka itama take ji da shi ba su da wata matsala da ke damunsu komi suke so suna mallakawa junansu shi. Ranar da suka yi wata 2 da aure da yamma tahir na kwance a kan gado yana shan lemon gwangwani Rabi'a ta shigo tana sanye da yallow din shadda riga da zani kanta ba dankwali gashin kanta ya sauka a kafadarta ta ajiye tray din abinci gabansa ta ce yayana ta so ka ci abinci. Ya kafa mata ido lokacin da ya tashi zaune ya jawo hannunta ya dorata kan cinyarsa ya ce kin kara kyau kyanki har ya yi yawa, bana gajiya da kallon kyakkyawar fuskarki. Ta ce na gode da son da kake mini. Ya ce ba ki da bukatar yi mini godiya ni ne da hakkin godiya a gareki babu abin da ba ki yi mini ba Rabi'atu na kasance ina burin in yi doguwar rayuwa don in rayu dake rayuwa mai tsawo, amma ban san dalili ba sai zuciyata ta dina zartar da ni wasu abubuwa marasa dadi tana kusanto mini da nesa kusa tana kusanto mini da rabuwarmu a kwana kusa ko ta dalilin mutuwa ko ta wani dalili da ban san shi ba.Ta marairaice fuska ta ce dan Allah ka daina wadannan zantukan basu da dadi, so da shauki ke sa kake jin haka insha Allahu za muyi doguwar rayuwa ni da kai. Ya yi murmushi rayuwa ta Allah ce mu na tare da kayan aro Rabi'atu. Ta bude abinci ta ce taso ni in baka, kana bani tausayi da yawa. Ya ce kin fi ni zama abin tausayi so da tausayinki har sunyiwa zuciyata yawa ban san inda zansa rayuwa ta ba, saukkina daya kina da hankali Rabi kin san abin da kike yi da wata ce ta samu dama aa kaina haka ta fahimci sonta yayi mini yawa haka har bani da katabus sai abinda ta ce da ni da shikenan sai ta yi ta gasani tana wahalar da rayuwata. Rabi'a ta ce to wannan ai shirme ne miji ai shi ne suturar ya mace yana da daraja mai karfi a gunta, babu dalilin da zata wahalar da shi in yana sonta. Ya ce gaskiya ne yau ne zamu je gaida Abba ko. Ta dan bata rai ta ce mu bari sai gobe duk nishadin da muke ciki in muka je gidan nan sai mun fito da bacin rai gashi kai sai ka yi ta cewa sai munje, bana jin dadin yadda in munje abba ke ma wulakanci. Ya ce ba komi matata bana jin haushin abba saboda darajar ya haifeki duk abin da zai mini na hakura wata rana sai labari. Ba a son ranta ba bayan sallar isha'i suka shirya a cikin kaya iri daya dukansu sun yi kiba sun goge sunyi kyau da gani suna cikin morar amarci da kwanciyar hankali. Kowanne gwani ne gun farantawa dan uwansa sai, ita ke tuka motar yayin da tahir ke zaune gefenta suna hirarsu gwanin ban sha'awa. Tahir ya ce asiya sun tafi london din ne? Ta ce eh wannan satin ta tashi dama sai mijin yana can ko bikin bai zo ba an yi bikin anan da daurin aure akaa tura mai ita can yadda abba ke son kenan. Ta yi parking dai dai lokacin da abba ya ke fitowa daga cikin gidan' dariya yake yana ganinsu ya murtuke fuska kamar dama can bai taba dariya ba.Tahir ya isa gabansa ya durkusa yana gaida shi ya ce tashi ka sani bana son wannan durkuson munafuncin idan kana yi ne dan ka burgeni babu abin da zaka burge ni da shi, sau nawa ma zan gaya maka ku daina zuwa gidan nan? Tahir ya ce dan Allah ka yi hakuri. Abba ya ja tsaki ya yi tafiyarsa ya barsu nan tsugune, Rabi'a ta ce dama na gaya ma, kace sai mun zo, mun zo an wulakantamu sai mu koma ko? Ya ce ba wani abu ummi zata faranta mana rai a cikin. Ta ce ita din ma a tsorace take hira damu dan kar Abba ya yi mata fadan dan ya raba yan gidan nan da mu. Ummi ta nuna farin cikinta sosai da ganinsu ta sa musu albarka ta ce kin san kuwa matar Rufa'i tana gidansu? Ta ce subuhanallahi yaya akayi haka? Ta tabe baki ta ce wai ke duk abinda ba a yi shi dan Allah ba akwai inda zaije? Wai wancan satin ne shi Rufa'i ya dawo daga portharcourt ya iske babu abinci a gidan kin san Rufa'i bai da hakuri in yana jin yunwa ko a gidan nan ba a fada dashi sai in ba a gama abinci da wuri ba, ya ce garin yaya aka bar gida babu abinci? Ta ce masu aikin dafa abincin da ka basu nan daya ta tafi ganin gida daya bata da lafiya itama tana gidansu. Haushi ya sa ya kwanta a falo yana tunanin abincin da yake ci ma cikin lalura yanzu babu? Sai gata ta fito daga daki ta ci uwar kwalliya wai ya tashi ya kaita unguwa. Kin san zuciyar mai tsumma a kusa take ya ce gidan ubanwa zata? Daga fadin haka sai ta sa kuka wai ya zagi ubanta, shi kuwa ya ce ya zaga din iyayan nata da basu koya mata tarbiyyar komi ba sai abinda taga dama take? Abinci wannan ba zata iya dafawa miji ba sai dai ya ci na yan aiki, ba za ta iya kula da gidan ta ba komi sai dai ayi mata? Shi kam bai taba ganin irin wannan tsari ba. Ta fashe da kuka ta ce wai dama so yake ya ci mata mutunci kuma ya yi da yar halak, iyaye kuma ba nata ya zaga ba nasa ya zaga dama can ya san bata da tarbiyar ai ya auro ta, ya ce ta kama bakinta in ta sake ta zage shi sai ya tattakata ai da budar bakinta sai cewa tayi an zage ka kai din banza kai din wofi har me ka isa ka yi in an zageka? ,Sai kuwa ya zage karfinsa ya nada mata duka, ta nufi gidansu a lokacin babanta ya zo gidan nan nan da kansa in kinji cin mutuncin da ya karewa Abbanku da shi Rufa'in kya rike baki. Rabi'a ta ce kash abin bai yi dadi ba to yanzu me ake ciki? Ta ce ina ai bai fita daga gidan nan ba baban nata sai da Rufa'i ya bashi takardar yar maza Rufa'i ya je ya kwashe duk abinda ya sani nasa ne ko su watso mai waje, ya isa ya wulakanta musu ya ya ci arzikin yar tana sonshi ta ce kar a kulle shi yau da yaga wulakanci in sun kulle shi a bursin sai kamanninsa sun sauya an mantada shi, ke ranar nayi kallo, bai bani haushi ba saboda na san duk wanda ya hau motar kwadayi tashar wulakanci zata kaishi suka ce Allah ya kyauta. Ta ce amin ku tashi ku tafi kar Abban ya dawo ya same ku. A gurin nura Abba ya samu lbr ummi ce ta sayawa tahir gida da mota da kudin da ya yi ìdimar auran rabi'a ai kuwa ya tada tashin hankalin sai ya kwace ai duk kudin da fa ummin ke samu nasa ne, dama yana jin takaicin yaea suke zaune lfy. Ason ransa ana kai Rabi'a ta gamu da matsalar da dole ta rabu da auran ta dawo gida ya bata wanda yafi so sai gashi duk tafi ya yan da ya aurar inda yake so kwanciyar hankali da samun zaman lafiya. Ballantana a bangaran soyayya, samun namijin arziki wanda ya san hakkin aure irin tahir za a jima. Yana tattalin zuciyarta kamar kwai, duk inda yake hankalinsa na kanta. Duk sonsa da abu in har Rabi'a ta nuna bata so ko da wasa ne ya bashi har abada, in kuwa ta ce wasa to shi kenan ya shiga rudani bai samu nutsuwa sai yaga ta dawo normal, sanin hakan ya sa ko bata da lafiya bata yarda ya gane dan bata jin dadin yadda yake daga hankalinsan a kan dukkan abin da ya shafeta. Abba bai nunawa ummi komi ba ya sa idris ya rakashi gidansu Ribi'a a safiyar wata lahhadi. Bai shiga ba ya aika aka kira mai tahir ya fito cikin rawar jiki ya fadi ya gaida shi ya ce lfy Abba baka aika na zo c ka zo da kanka. Ya buga mai harara ya ce mike tsaye ka karkade kunnuwanka da kyau ka ji abinda ke tafe da ni. Lfy ba zata sa nazo gidan ka ba kamar yadda ka dade da sanin ba zan kaunace ka ba. Nazo ne dan in tabbatar baka manta da zuwa na ba kuma ba zaka yi wasa da abinda na gaya maka ba. Tahir ya ce ba wani abu Abba ai dama kai ba abokin wasa na ba ne. Ya ja........ Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Launin Fata 1-07 Posted by ANaM Dorayi on 11:10 AM, 20-Oct-15 Under: Launin Fata Ya ja tsaki ya ce wannan gidan da kake ciki bana wadda tayi muku kyautarsa ba ne gidana ne motar da ta ba ka ma ba tata ba ce tawa ce kudin da ta tara ma su ne nata suma da na wane sai ka biyani. Wannan ita ya shafa, abinda nake so da kai ka shiga ka fito mini da takardun gidana da mukullin motata ga idris zaija na baku wata 2 ku nemi gida ku tashi nan ba gidan zamanku bane, idan wata 2 suka cika baku tashi ba zaku sha mamaki. Dama can na barku kun dana ne dan ku mori amarci sai ku san abin yi. Yadda Tahir ke tsaye gumi ne kawai ke tsiyayo mai tun daga goshi har sassan jikinsa, bai taba jin fin karfi irin wannan ba, Abba ya buga mai tsawa ya ce zaka shiga ka fito mini da kayana ko kuwa? Ya juya jikinsa ba kwari yaje ya dauko takardun gida da makullin mota har kasa ya durkusa ya ba Abba ya ce A sauka lafiya Abba na gode. Harara ya galla mai ya mikawa idris mukullin mota ya ce jamin ita mu tafi. Hatta idris din duk yadda ya tsani tahir sai da yaji jikinsa ya yi sanyi saboda tausayin da tahir din ya bashi, Abba ya shiga mota ya ja, idris shi ma ya ja motar da da take maunin ta tahir. Tahir ya dawo cikin gida ya iske Rabi'a a zaune a falo tayi tagumi bata san me ke faruwa ba, amma tunda idris ya shigo ya ce mata Abba ne ya zo da kansa gidansu ta san wani tashin hankali ne ya tunkarosu. Tana ganinshi ta mike ta rungumeshi tana kuka ta ce cin mutuncin abba ne yau ya biyoka hir gida? Nasan dai alheri ba zai kawo Abba gidan mu ba. In banda ina sonka bani son rabuwa da kai da na hakura da kai na

Chapter 5 of 12