Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
koma gidanmu ko dan ka huta da wulakancin Abba. Ya toshe mata baki a sanyaye ya ce ki daina damuwa na gaya miki lamarin abba bai taba damuna ba na san komi lokaci gareshi, kada in kara jin kin yi batun rabuwar mu a kan lamarin Abba. Ta sake shi ta koma ta kwanta lamo ya wuce cikin dakinsa ya zauna yayi tagumi bai son Rabi ta dameshi da tambayoyin da bai son amsar su ba. Baya son gaya mata gaskiyar lamarin ne saboda daga hankalinta za ta yi duk abinda zai daga mata hakali kuwa baya sonshi. Haka ya yini sukuku ba kuzari abinci ma kasa ci ya yi da yamma Rabi'a ta gaji ta saka mai kuka ta ce wlh da abin da Abba ya gaya ma wanda ya dameka ka boye mini idan ka boye mini dan in damu damuwa ba zata bar zuciyata ba tunda kana tare da damuwa garama ka fito fili ka gaya mini mu san abin yi. Babu mafita na yin haka dan haka ya gaya mata yadda suka yi da Abba. Ta dafe kirji ta ce innalillahi wa inna ilaihi raji'un garin yaya ka bashi takardun gidan? Ya ce to Rabi'a idan ban bashi ba ya ya zanyi? Ko kinga ina da karfin da zanja da Abba ne? Ta ce idan Abba ya fi karfinka ai baifi karfin hukuma ba ko? Ya ce haba Rabi Allah ya sauwake in kai Abba ga hukuma idan nayi haka ai na bar abin fadi har ga jikokin mu, akan gida da mota in kai wanda ya haifi matata kara? Ta lankwasas da kai ta ce kana da hujjoji masu karfi da hukuma zata maido ma gidan nan da motarka hannunka. Ya ce ki bar wannan maganar Rabi'a abu ne da ba zai yiwu ba kina darajar da zanwa Abba komi saboda ke. Ta ce to yanzu ina zamu zauna? Ya ce ba komi kafin wata 2 da ya dibar mana Allah zai bamu inda zamu zauna din. Ta mike tsaye ta shiga kai komo a dakin zuciyarta ta gama baci in ranta yayi dubu ya baci sai yau ta tabbatar da kiyayyar da Abbansu ke wa auranta da tahir ba kiyayyar wasa ba ce. Duk abinda zai yi yaga bayansu shi yake nema, ta yaya za ai bashi ya sai gida da mota ba ba da kudinsa aka saya ba ya kwace? Kwana tahir ya yi a ranar yana lallashinta tana kukan bakin ciki.Yayin da ita kuma ummi ta fada cikin bala'in Abba domin yana shiga gidan ya hauta da masifa ya ce dama ni na san duk munafuncin yana gunki kika dau gida kika ba ma wannan matsiyacin yaron to na kwace kuma wlh idan na kara jin kin basu wani a bakin auranki. Ummi ta saki baki tana kallon Abba tana mamakin yadda ya ji wannan sirrin takaici yasa ta rasa abinda za ta yi ma wace irin rigima ce wannan. Kwana 2 da yin haka Rabi'a tana cikin matsananciyar damuwa ko abinci bata iya ci sosai har tahir ya fara gajiya da lalalshi ya shiga yi mata fada ya ce yaya kike so in yi da raina ne? Menene dan an karbi gida da mota da can nasan da su ne? Ran da yake jikinmu wata rana rasa shi zamu yi ballantana abin duniya Allah shi ya san yadda zai yi da mu. Ta kwanta lamo tana hawaye ya yi ficewarsa ya barta nan' zuciyarta ta dinga tashi ta amayar da dan shayin da ta sha nan da nan sai zazzabi. Tun tahir bai kulata ba har zuciyasa ta kasa juriyi ya daukota suka je asibiti a can ne likita ya tabbatar musu tana da shigar ciki wata daya amma ta rage damuwa cikin baida kwari zai iya faduwa. Labarin samuwar wannan ciki ya tafi da damuwar dake zuciyar tahir farin ciki ya kama shi zai yi da dama shi haka yake bai cika sa abin duniya a ranshi ya dameshi, duk lokacin da wata damuwa ta yi mai yawa sai ya shiga adu'a. Ya ci gaba da tattalinta kamar kwai bai da magana sai ta cikin nata, ala dole ta rage damuwa, ya gargadeta a kan kada ta gayawa kowa abin da Abba yayi musu baya son wani ya ce zai baiwa Abba hakuri shi ma zai yi kokari samun nasa. Kar ummi tazo gidan Rabi'a Abba ya hanata zuwa ko ina sai ita Rabi'a ta saci jiki ta zo ta gaya mata yadda Abba ya yi musu kukan da Rabin ke yi ya ba ummi tausayi da yawa itama sai da ta yi hawaye ta ce Ba komi rabi'a ki ci gaba da zama lafiya da mijinki da yi mai biyayya Allah yana tare da masu hakuri. Allah ya baki miji nutsatse mai mutunci in shi kadai ke mutunta Abba da ni duk wulakancin da abba ke mai bai dubawa.Tunda Abba ya wulakantashi a kan dukiya insha Allahu sai ya ci moriyar dukiyarsa wata rana Abbba ya ce a bakin aure na in na sake baku wani gidan, dana siya muku wani. Rabi'a ta firgita sosai da jin wannan maganar har ta dawo gida kuka take yi. Hajiya yaya kadai tahir ya gayawa abinda surukinsa ya yi masa ya ce ya samu madaidaicin gida a nan kasan layinsu zai kama haya. Ta rike baki ta ce haba dai haya har me kake samu a wata da zaka dinga iya biyan kudin haya ga dawainiyar matarka wadda ko yaushe kake karewa kan hidimarta, ka dauko yar masu kudi da bata cin abinci irin namu sai mai tsada, bata da sutura irin tamu sai mai tsada ubanta bai kaunarka. Duk zuri'ar gidan nan wanda ya tashi aure daidai dashi yake nemowa gashi kowa yana zaune lafiya banda kai kaima da dai dai kai ka dauko da baka ga wanan takaicin ba.Saboda haka zancan kama haya bai taso ba ga dakin mahaifinka ciki da falo har da bandaki a ciki yafi kowanne sashe kyau a gidan nan ka kara gyarawa ka zauna, in kuma matarka tafi karfin zama da mu ne shi kenan. Ana wata ga wata, maganar hajiya yaya tafi karfin musu a gun tahir ita ce ta haifi mahaifinsa, lokacin da mahaifinsa zai rasu wasiyya 2 ya bar masa. Na farko ya ce ya guji duniya da kwadayin abinda ke cikinta da son zuciya ya ji tsoron Allah duk abinda zai yi ya tuna zai mutu ya hadu da Allah. Na 2 shi ne lallai duk abinda zai yi ya yi shawara da hajiya yaya in ya saba mata shi ya sabawa. Gumi ya dinga tsayayowa taìr yana mumfashi da kyar bai kaunar kawo matarsa gidan nan saboda shi ma ba kaunarsa mutan gidan ke yi ba suna cewa ya fiye sanabe da iyayi ga jin kan to ina ga matarsa, duk abin da zai takura rayuwar matarsa baya so. Haka ya amsawa hajiya yaya taso ya nufo gida ya saidawa Rabi'a yadda sukayi ta ce c komi ai kowa da halin sa zai zauna, da muje gidan haya ai gara can din. A ransa ya ce tabdijan baki san matsalar dake kwance a gidan mu ba ne. A kai akai Abba ya dinga kiran tahir a waya yana shaida mai wa'adinsu ya kusa ciki ya ce ina sane Abba zamu tashi. Abba ya zubo ido yaga Rabi'a ta dawo gida ya ji shiru, ya gaji yaje gidan da kansa lokacin tahir baya nan yana makaranta, tunda ta ganshi ta san ba alheri ne ya kawo shi ba, bata amrheshi da walwala ba ya shiga har falonta ya zauna bayan sun gaisa ya ce dubeki dubi yadda kika koma kin yi fari fat kamar aljana sai dogon hanci kamar talakan bature kin lalatar da kanki a kan wannan matsiyacin yaron da bai da komi ki kwashe kayanki ki koma gida. Ta ce nifa Abba ina son mijina ko ba shi da ko mi ina sonshi haka kuma zanci gaba da zama da shi a haka? Ya ja tsaki ya ce sai ki yi ta zama wahala ce bata isheki ba na tabbatar kwadayi ne ya kai tahir ga auranki yanzu da na toshe mai hanyar da zai samu abin da yake samu ba abinda zai saka miki da shi sai saki. Ta yi tsit ya karaci kame kamen fadansa marar dalili ya tashi ya tafi yana mamakin halin Rabi'a.Bata gayawa tahir zuwan Abba ba dan abin kunya ne a gareta a ce babu wanda ya zama fitina ga auranta sai mahaifinta. Bayan kwana biyu suka tattara kayansu suka koma gidansu tahir, dakin ya gyarashi sosai ya fashe simintin kasa ya yi mai tayar silif ma mai tsada ya sa ya sa har da bandakin ya sa AC da duk wani abin kawata daki, sauran kayansu ya sa a dakinshi na zaure da ya tashi ya rufe, falon da dakin baæin nasu ya yi kyau sosai amma duk da haka da ummi ta saci jiki ta zo sai tausayinsu ya kamata ta hango ita daular da ta ke ciki a gidansu kamar Aljannar duniya kullum dada kayatar da shi ake amma ji muhallin da yarta ke ciki wani tsukakken falo da daki daya kawai da toilet ko kicin babu. Bata yarda Rabi'a ta gane damuwar ta ba dan kar ta karyar mata da zuciya amma tana fitowa kuka ta kama yi a mota musamman da ta tuna da kallon banzan da mutanan gidan ke yi mata suna yada kananan maganganu a tsakar gida. Bata ga alamar za a zauna lafiya a wannan gida ba. Tun a washegarin ranar da suka tare da safe Rabi'a ta shiga dakin hajiya yaya dan gaida ita hajiya ta ce Rabi'a zaman duniya iyawa ne matan aure sun kai goma sha 2 a cikin gidan nan kce ta sha 3 dole sai kin iya da kanki duk wanda ya ce zo mu zauna kamar ya ce zo mu saba ne, duk kusancin harshe da hakori wata rana sabawa suke ballantana mutum da mutum. Da safe da rana kowa girkinsa yake amma da daddare tare ake yin tuwo gaba daya gidan, zaki shiga cikin wannan tsarin kuma. Rabi ta dawo daki ta zuba tagumi, bakin cikin Abbansu ya kara dawo ma a sabo fil haka kawai suna zansu lfy ya kwace musu gidansu ya jefosu a wahala da bacin rai. Ba wai dan zai amfana da gidan ba sai dan ya kunsa musu bakin ciki da damuwa, to tabbas sai ta bashi kunya babu wata wahala da zata sa ta koma gidansu ta rabu da mijinta dan yana sonta yana tattalin farin cikinta itama shi kadai take so. Tunanin da ya dauke hankalinta shi ya ja har tahir ya shigo bata ji ba sai ji tayi ya rumgumota ta baya ya ce wannan tagumi fa na meye? Ta yi ajiyar zuciya ta ce ba komai.Yace haba mutum ya zuba tagumi irin wannan kuma ya ce ba komi matsalolin gidan nan sun fara damun ki ko? Ta ce a a. Ya ce ki yi hakuri in sha Allahu ba zamu dade a gidan nan ba ni dai ina godiya da kaunar da kike mini ba dan na isa ki soni ba ina godiya da juriyar da kike da duk wani hali da ke riskarki a dalikin aure na. Ta mike tana fadin godiyar ta isa haka. Ya damko ha6unta ya ce me kike söci in dafa miki? Ta ce um um ni zan dafa kada ka manta gidan nan ba irin can ba ne akwai idanuwan mutune sosai a kanmu dole mu hakura da rayuwar da muka saba. Kamar amsa ga abinda take fada kawai sai ganin yarinya suka yi budurwa katuwa ta daga musu labule babu ko sallama ballantana neman izinin shigowa, a kalla zata kai shekara goma sha 7 ransa ya yi mugun baci ya saki Rabi'a ya buga mata tsawa ya ce ke lfy za ki shigowa mutane daki babu sallama? Ta turbune fuska ta ce hajiya ce ta ce in kirawoka. Ya ja tsaki ya ce je ki ce ina zuwa. Rabi'a ta shige daki ta kwanta tana tambayar kanta irin rayuwar da zasu yi a gidan nan kenan. Tahir ya shiga dakin hajiya yaya ransa a bace ya zauna ya gaida ita, ta bata rai ta ce dan na aika kiranka shi ne kake mata bambamin masifa, kai ko kunya baka ji da safiyar nan ka kulle da mace a daki, wa kaga yana wanna tabarar a gidan nan? Kunya tasa ya sunkuyar da kansa ya rasa abinda zai ce, tabdijan komi sa ido ne kenan a gidan nan, ta tura mai kwanan sha cike da kunun tsamiya da kosai mai zafi ta ce gashi nan ku je ku karya dan naga alama matar taka dan kosa ce ga alama girkinma kai ke yi mata. Ya dauko ya dawo daki Rabi'a ke kokarin janshi da hira shi kuwa damuwa ta hanashi sakat. laulayi ya sa Rabi'a a gaba ga takaicin da take kunsa a zaman gidansu tahir, da takura tana fama da barci da kasala ga yawan aikin matan gidan sun debi ido sun sa mata komi tayi a kyara da hantara take. Lokaci guda ta rame tayi wani irin hankalin tahir duk ya tashi wani lokacin in ya zauna a gabanta har kuka yake mata abinda ita kuma bata so. Yau satinsu hudu daidai da dawowa gidan, taliya ta dafa jalup da rana ta ji attaruhu da albasa saboda bakinta ba dadi tana cikin ci yaron Dje salhu ya shigo dakin yana gatsine gatsine na rashin kunya ya ce Rabi wai ki zo in ji ummanmu. Ta ce to je ka ce ina zuwa. Ba ta je c sai da ta gama cin abincinta tana shiga dakin jije ta zabga mata harara ta ce aikin banza da wofi dan kina cin taliya zaki ma salihu tsawa kice ya fita daga dakinki, taliyar banza da wofi. Ta rike baki tana kallon salihu wanda ya yi kicin kicin da fuska tana harararta yara kanana suna mata wulakanci da rashin kunya kawai dan iyayansu sun daure musu gindi. Ta ce salihu yaushe na maka tsawa? Dje ta ce ya miki karya marar kunya kawai. Kishiyar ta ladidi tana zaune a gefe ta tabe baki ta ce zaki daina ganin laifinta tahir ne da yake nuna mata kamar tafi kowa a gidan nan dan yana auran yar masu kudi sai kace baki ga wani irin kallo da yakewa mutane, baka isa tahir ya gaida kai ba kamar ba mu ne muka ci kashinsa da fitsarinsa ba. Dije ta ce to ai aikin banza yake surukin nasa ba wulakantashi yake ba, ina ce ba shi ne ya korosu ba suka dawo tahir din, baya da kuma yake yafi karfin ya zauna da mu a gidan nan. Wannan surukin nasa har wani abin takama ne a gunsa? Suka yi tsaki. Dije ta ce ni tashi wanke wanke na ne sumaýa bata yi ba ta tafi unguwa ki yi mini kuma kin san ke ce zaki yi tankadan tuwo amma kika nade a daki ke ga yar gata. Ladidi ta ce anya kya sa ta wanke wanke kuwa? Shekaran jiya fa dan kawai na sata iza wuta tahir ya shigo ya sameta a gaban murhu tana fifita makirar yarinyar nan tana gani mijinta sai ta fara matsar ido wai ita hayaki ya dameta. Da yake ba shi da kunya sai ya zo gabanta ya tsaya ina hangoshi daga daki ya amsì maficin ya fifita wutar ya janye ta suka yi daki har da turo kofa a ranar sai ni nayi towon gaba daya bai bari ta tayani ba. Da takaici ya isheni na kasa hakuri da safe na yi mai magana na nuna mai bai dace ya dinga nuna wa matarsa tafi kowa a gidan nan ba yadda ake ya haka mu ma muke yaya daukar cikiou aka yi yadda aka dau nata haihuwarmu akai yadda aka haifeta muma ba daga sama muka fadoba ,ba daga bola aka tsintomu ba kowa fa yana son hutun nan. Da budar ckin marar kunya sai ya ce gaskiya sai dai mu yi hakuri matarshi yarinya ce bata saba da wahala ba zata iya aikace aikacen gidan nan ba sa6an juna 2 gareta tana bukatar hutu. Dije ta tare ta wai sai kikace mishi me? Ko kuwa ido kika sa mai ya ke rashin kunya. Ta ce to mai zance mai dije fadan da yafi karfinka wasa kake mai da shi ni dai na ce to ba zan kara sa matar shi aiki ba kada wata rana wani abu ya sameta a ce nice' dan naga kamar kwai haka yake ji da ita. Dije ta ce tabdijan ashe lallai za a yi ta wlh bai yiwuwa dan mu ma c cyi cne haka iyayanmu ba bayi ba ne. Ga hadiza nan shekarar ta sha 5 kacal aka kawo ta gidan nan amma tas take zama tayi tuwon gidan nan mijinta bai taba cewa tana da ciki ko bata sa ba whala ba kuma itama yar gta ce haka hansai sai ita yar gwal in iar tana gidan nan sai tayi abin da kowa ke yi. Rabi'a ta mike ta fita jiri na dibarta sama sama ga wani azababban bacci tana ji ta shiga wanke wanke, ga manyan tukwane bakikkirin Dije ta ce a wanke mata su tas saboda rashin sabo kusan awa 2 tayi tana wanke waken tana nishi ta share tsakar gidan kana ta dauko tankaden garin masara amai ya dinga taso mata, jiri na daukar ta ta ajiye gari ta tashi da gudu ta shige daki ta fada toilet ta dinga kwarara amai kamar yayan hanjinta zasu fito. Tahir ya shigo tun daga falo ya jiyo kakari ya shiga da gudu ya iske rabi'a cikin mawuyacin hali sai da ta gama ya daukota ya rungume kamar zai yi kuka ya fito da ita falo ganin tana gumi ya tayar da inji da sauri ya kunna mata fanka. A tsakar gida Dije ta fito daga daki ta iske tumaki na cin garin nan da nan idanunta suka rine da bala'i dama mai neman kuka ballantana anjefata da kashin awaki.. Ta fusata ta nufi dakin Rabi'a tana fadin dan wulakanci da rainin hankali in baki tankadan ki ajiye tumaki su cinye mini ai gara ki ce ba za ki yi ba,ta hankada kofar ta shiga tahir na zaune dirshan ya dora Rabi'a a cinyarsa ya fitar mata da riga daga ita sai bra. Wai duk da wannan abin da dije ta gani bata fasa zazzaga masifa ba fadi take ai dama nasan kai ka hana ta yin abinda na sata. Bakin ciki da kunya suka kama su Rabi'a ta mike tana duddukawa ta shige cikin daki yayin da tahir ya mike cikin matsanancin haushi ya ce baki ga bata da lafiya ba ne. Ta ce karya take dan ta ganka ne tun safe take harkokinta. Ya ce to ni dai gaskiya ban yarda da wannan tsarin ba. Dije ta fidda dankwalinta ta ci damara tana fadin tunda baka yarda ba sai ka zo ka dakeni sanan ne zan san ka isa marar kunya. . . . Yara ne suka ruga waje suka fadawa kawu tanimu ana fada dije da tahir. Ya taso da sauri ya shigo gidan cikin matsanancin haushi yadda dije ta shigo cikin dakin shima haka ya danna kai ya riski tahir yana fadin ni dai bance zan dake ki ba ina dai so in gaya miki ne daga yau matata ta daina bautar dafa ma yayanku abinci ana yi mata wulakanci.Kawu tanimu ya ce sannu me mata? Kai yanzu har ka yi girman da kasan dadin mace zaka zagi iyayanka a kan mace? Wuce muje gun hajiya in ita ta baka damar......... Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Launin Fata 1-08 Posted by ANaM Dorayi on 11:14 AM, 20-Oct-15 Under: Launin Fata Wuce muje gun hajiya in ita ta baka damar ka wulakantamu a kan matarka sai mu tashi mu bar muku gidan ka zauna kai da matar taka in nine na haifeka ka yiwa matata haka, kai ka iya duka binda a kai maka ka ce an nuna ma bambanci dan kai maraya ne kai kuma ka iya yin duk abin da ka ga dama. Tahir ya mitsittsike idanunsa ya wuce gaba suka shiga dakin hajiya yaya tana zaune kan gado har yanzu bata da lfy amma dai jikin da sauki. Kawu tanimu ya ce dije gayawa hajiya abin da ya faru. Ta karkace ko tsoro Allah bata ji ba ta sharo karya tana matsar ido ta ce hajiya ni daman tun randa uban yar nan ya sawota a gaba dan abin kunya ya kawota gidan nan jikina ya bani in har a gidan nan zata zauna sai an samu matsala gaskiya ni ba za zauna yarinya tana mini kallon banza mijinta ya nuna mata bamu da kima ba, ba mu isa mu sata ko hanata mijinta sai ya zagi mutum, zamu bar ma tahir da matarsa gidan. Hajiya ta ce ya isa Dije duk abin bai kai zafin haka ba, kai tahir abin da zan gaya ma shine ba a kanka aka fara aure ba kuma ba kanka za a kare ba, a ciki gidan nan ka girma tunda ka taso baka ga wanda yake wa iyayansa rashin kunya a kan matarsa ba. Kawu tanimu ya ce yawwa gara a gaya masa dan naga alama watarana sai ya kamani da kokawa a kan matarsa. Hajiya ta ce ya wuce ke kuma dije ki ji tsoron Allah kin kusa yin jika da rabi'a banga dalilin da zaisa ta tsole miki ido kina damuwa da ita ba ki rike ta amana kuma kin haifi yayan nan gasu nan a gabanki sai kuma Allah ya kai naki yayan inda za a rike amanarsu a kula dasu kana taimakon dan wani ne dan gyara rayuwar naka. Saboda baka san inda Allah zai kai naka ba kaima a gaban ko baka mutu ba imma kana rayan.Tunda tahir ya fita a ranar bai dawo ba sai sha dayan dare, Rabi'a tana zaune a falonta ta zuba kwalliya da shadda maroon colour, abinka da farar mace sai kalar tayi amta kyau ainun duk bacin ran da tahir yake ciki sai da ya neme shi ya rasa ya ajiye ledar da ya siyo mata gashasshan nama ya jawota da karfi ya rungumeta yana shafa cikinta ya ce cikin nan girma yake Rabi'a sai kyau yake kara miki wata matar in tana da ciki sai tayi muni ke kuwa kyau kike karawa. Ta lumshe ido ta narke a jikinsa ta ce nayi fushi. Ya ce me na yi gimbiya ki rufawa rayuwata asiri komi zai iya faruwa da ni in kika juya mini baya. Ta yi murmushi me yasa kaje ka dade a waje? Yana shafa gashin kanta ya ce ki yi hakuri Rabi'a tuna takaicin abin da ke faruwa a gidan nan ya yi mini yawa, ina bakin cikin yadda kika fada wahala a dalilin aure na. Nasan Abba da yan uwanki na can na fadin dama ga abinda suke jiye miki nan. Gaba daya sai in dinga ganin ban kyautawa rayuwarki ba. Ta rufe mai baki ta ce haba mijina duk wanda yaga laifinka a kan wannan ya kasance mai tsananin son zuciya.Ko kadan ban dau wannan lamarin a matsayin abin da zai zama matsala ga auran mu ba ni dai abinda nake so da kai ka dinga dauke idonka a kan duk abinda zaka ga an yi mini a gidan nan wanda baya yi maka kadi. Saboda yin maganarka ba zai kawo masalaha a cikin lamarin ba sai dai ya kara lalata al'amarin. Su gani suke ma asiri nayi maka kake mini irin wannan son kasan yanzu an daina ganin namiji na son matarsa irin haka. Ya ja tsaki ya ce yi shuru Rabi'a duk wadannan hujjojin da kike zana mini basu da tushe ballantana makama, babu wani dalilin da wani zai sa ma ido danshi bai kula da matarsa ya ce kai ba zaka kula da taka matar ba, ko kuma wata dan mijinta bai kula da ita ta ce ke mijinki ba zai kula da ke ba. Soyayyar da nake miki Rabi'a tafi karfin in boye a cikin kasan goman ban fito miki da kashi biyar ba kashi uku ce idan na fito da ita gaba daya sai ki yi tsammanin na haukace ni kuma duk abinda zai faru da ni sai dai ya faru wallahi ba zan fasa kulawa da ke ba.Rabi'a ta rasa abinda zata gaya mai ya fahimce ta dole ta sa mai ido ya ci gaba da baýana mata matsayin ta a zuciyarsa abin har ya kaishi ga kwalla. Tun abin yana ba Rabi'a tausayi da sha'awa har abin ya koma bata tsoro. A wannaan dare ta ga wata irin soyayya mai wahalar sha'ani a gun tahir kukan da ya yi mata na soyayya daga daran zuwa wayewar gari ya yi matukar firgitata jikinta rawa ya dinga yi ta dinga ganin ko dai ya zautu ne. Tunda ya aure ta take ganin soyayya iri iri agunsa, amma bata taba ganin yayi mata abin da ya yi mata yau ba kuma ya tashi jikinsa a sanyaye kamar an mai mutuwa. Wajan karfe bakwai na safe yana kwance kan doguwar kujera da carbi a hannunsa yana ja farar jallabiyya ce a jikinsa duk inda Rabi'a tayi sai ya bita da kallo, ta gaji ta zo gabansa ta zauna ta ce dan Allah ka gaya mini abinda ke damunka wanan kallon naka yana firgita ni da yawa. Ya mike ya fice ya ce mata ina zuwa. Shuru shuru tahir bai dawo ba mamaki ya isheta ta ta ci gaba da ayyukanta, dan har sha 2 rana tahir bai dawo ba, azahar tayi la'asar ma shiru. Ta shiga dakin hajiya yaya ta isketa jikinta ya tsananta ta kasa gaya mata ta dawo daki ta yi ta gumi duk gidan ba wanda zata tinkara da maganar tahir sai hajiya gashi ita kuma ba lafiya. Hankalinta bai gama tashi ba sai da dare ya yi tahir bai dawo ba ta kira wayarsa taji ta a daki kan mudubi tun tana dauriya har takama kuka ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta shiga dakin hajiya yaya ta zauna tana kuka hajiya ta bude ido ta ce Rabi'a matso ki min adu'a kirjina ya yi min nauyi da yawa. Jikinta na rawa ta matsa daf da ita ta hadu da muhamd dan wan tahir ya ce ke lfy? Ta ce shigo dan Allah kaga hajiya. Ya bita yana fadin me hajiya ta yi ita da na barta tana magana sosai. Yana taba hajiya ya ce innalillaì wa inna ilaihi raji'un. Ke din nan mayya ce kashe hajiya kikayi dan dana fita na barta tana hira a zaune na barta kin shigo kin kashe ta. Kafafun Rabi'a da suka kama rawa sai ta zube a gun tuni mutanan gidan suka hallara a dakin. Rab'a ta sulale ta bar dakin ana ta koke koke ta shige dakinta zata rufe kofa kenan muhmd

Chapter 6 of 12