Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kin zo da babban al'amari. Rabi ta ce ki taimakeni dan Allah ummi. Ummi ta ce duk wannan ba zai gagare ni ba tunda ina da halin yi tsoro nake ji kin sani Abba bai son bakin mutum ko yana da kudi da wahala ya bashi ke bana son fitina. Rabi ta ce sai mu yi tayin addu'a Allah ya taimakemu a kansa. Ta ce to shi kenan zan yi tunani. Gida mai kyan gaske ummi ta sayawa tahir da mota yar ubansu ta yayi ta dora mai da kudi har naira miliyan biyu ta ce ya zo kai tsaye neman auran Rabi'a. Lokacin da ta kirashi take mai wannan bayanin tahir rudewa yayi ya zauna sharaf a gabanta yana hawaye ya kasa magana. Wannan rana ya tabbatar rabi'a da mahaifiyarta suna kaunarsa ne saboda Allah. Shi kam bai san da abin da zai saka musu ba. Ummi ta ce kar ka damu na yi ma haka ne dan kana son Rabi'a itama tana sonka in dai wadannan abubuwa ne zasu hana yiwuwar auranka to ko ba zan bari ku yi asarar junanku ba. Saboda haka kar ka damu kanka da komai. Tahir kuka ya ke yana godiya ga ummi ta mike ta shige gida ta barsu shi da Rabi'a, ta ce tahir mun zama daya ni da kai zuciyoyinmu sun zama daya. . . Shigowar motar Abba ya katsewa rabi'a magana direban Abba ya yi parking ya fito aguje ya bude musu kofa shi da nura suka fito cikin isa da takama nura ya ce Abba wai baka raba waccen yarinyar da wancan bakin yaron ba. Cikin takaici ya ce laifin umminku ne ita ke bata damar ta yi duk abin da taga dama, yau fa da safe nake gaya musu cewa a yammacin nan sultan da nazir zasu zo gidan nan amma dan wulakanci ta jawo shi yazo in sultan ya ganta da wannan me zai daukeni? Nura ya kwala mata kira taho da sauri ta durkusa, ya buga mata tsawa ya ce munafuka mike tsaye ba Abba ya rabaki da wancan bakin yaron ba? Ta waiwaya taga tahir na tahowa ta ce dan Allah ka yi hakuri wata magana ce ta kawo shi gunka Abba.To naji magana ce ta kawoshi gurina wa ya ce ki fito gunsa ke da aka yi miki miji? Abinda tahir ya fara ji kenan da sassarfa ya karaso gaban abba ya durkusa ya gaida shi, ba wanda ya amsa nura ya nuna mai hanyar fita ya ce dan Allah malam kama gabanka ko kana ganin iri irinka na shugo mana gida? Tahir ya ce zan fita dan Allah ka taimaka ko minti 2 ka bani in ma bayanin abin da ke tafe da ni. Abba ya wuce yana fadin ka jirani a nan zan ma gargadin karshe a kan zuwa gidan nan in baka ji ba zaka gaya musu. Nura ya bugawa Rabi tsawa ya wuce ciki kar mijinki ya sameki a nan. Mike ta shiga suka bar tahir tsaye cikin takaici. Wai shin me mutane suka dauki dukiya ne. Ya kwashe minti ashirin kafin a aiko ya shigo falon Abba, yana zaune kan kujera ya dora kafa daya kan daya yana ma tahir wulakantancen kallo ya ce to sarkin naci gaya mini abinda ke tafe da kai kafin ka ji nawa bayanin. Tahir ya dukar da kai ya ce Abba ka taimakeni ka bani Rabi ina sonta. Abba ya buga mai tsawa ya ce baka da hankali ne ina ga kana da matsala a kwakwalwarka duk abubuwan da nake gayama ba shiga kunnanka suka yi ba shi yasa ka kara zuwa guna da batun neman aure ko? Tahir ya ce abba ka gafarceni in dai kudi ne nima ina da su a yanzu. Ya ce ina dasu abba. Yayi murmushi in kana da kudi ai baka sauya launin fata daga bakin mutum zuwa farar fata ba ko? Ko ban gaya ma bana bawa bakar fata yaya na ba, to tashi ka bani guri, baka da tagomashin da zaka zama surukina, kuma idan ka sake zuwa ko kofar gidan nan sai na kulleka na manta da kai ballantana har ka shigo mini gida ba da izinina ba kana magana da yata. Tahir ya shiga magiya abba ya yi mai banza daga bisani ya danna kararrawa mai gadi ya shigo aguje ya ce maza ka fice mini da wannan yaron daga gida, duk ranar da ka kuma barinshi ya shigo gidan nan a bakin aikinka. Maigadi ya tusa tahir a gaba ya fitar da shi, kafin tahir ya isa gida zazzabi da ciwoo kai har sun kamashi, yana shiga dakinsa ya fada kan katifarsa yana cizon yatsa, yau yaga wulakanci ganin idonsa, ga soyayyar Rabi na cinsa a zuci kamar zuciyar zata fashe. Ya dau waya ya kirata ta daga da sauri ya gaya mata yanda suka yi da abba ya ce Rabi'a ki gayawa ummi na gode da kaunar da ta nuna mini na maido mata gidanta da motarta da kudinta aure tsakaninmu sai hakuri abba ba zai bani ke ba.Rabi'a ta ce wli tahir in dai muna raye ni da kai aure ba fashi, ba zan auri wanda yake so din ba nima. Zai magana ta ce na fa gama magana ka zuba ido ka ga abin da zai biyo baya kawai. Ta kashe wayar ta shiga falon ummi ta gaya mata yadda tahir suka yi da abba. Ummi ta ce ai dama na san haka ne zai faru nayi yadda kike so ne dan kar ranki ya baci amma na san da wahala a cimma nasara. Fatima ta shigo da sauri ta ce anti rabi ga sultan da nazar sun iso. Ta ja tsaki ta ce idan kika kara yi mini maganarsu sai ranki ya baci. Fatima ta ce kin san Allah da kin hada ido da sultan za ki fatattaki tunanin kowane da namiji a zuciyarki, wlh sultan yadda kika san ba mutum ba don kyau Taja tsaki ta ce na bar miki ni fa wannan bakin da ba a so shi nake so. Daukar dala da gammo kenan. Inji fatima ta fada tana murmushi. Rabi ta shiga dakinsu ta tsala ado da wasu shegun riga da wando da anti nafisa ta sayo musu a indiya sunbi jikinta sun lafe sun bayyanar da surorin jikinta, gashin nan baki sidik ya sha gyara ya kwanta a kafadarta ta zuba turare ta dubi asiya wadda ke nata shirin ta ce yaya nayi? Asiya ta ce yanzu a haka za ki je gaban sultan? Ta ce ai ko tahir din da kike so kullum da hijabi kike zuwa gabansa....... Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Launin Fata 1-05 Posted by ANaM Dorayi on 04:45 PM, 06-Oct-15 Under: Launin Fata Ta ce wata sabuwar soyayya yau zan jewa sultan da ita amma fa mai ciwo a zuci. Asiya ta gyada kai tana dariya ta zuba nata kayan irin na rabi'a amma ita brown ne mai duhu, ban san wadda ta fi cinyewa ba a ciki. Fatima na can nata hidimar sanya musu abinci sultan da Nazir na falon abba na cikin gida kowanne yayi bala'in haduwa, kananan kaya ne suma a jikinsu iyakar burgewa da cinyewar da namiji sunyi. Nazir ya fi sultan son magana da raha sultan na da jan kai da miskilanci tunda suka gaisa da fatima bai kara yin magana ba ya dau jarida yana dubawa, nazir ke janta da wasa itama da yake tana da surutu sai ta biye mai suka tayi hausa kadan kadan suke jefota yawanci maganar larabci suke yi. Abba da nura da rufa'i suka shigo yadda sultan da nazir ke zaune kan kujera a kasaice shigowar abba baisa sun motsa ba, shi ne yayi musu sannu da zuwa cikin fara'a gara ma nazir ya amsa cikin sakin fuska ya gaida abba ya baiwa rufa'i da nura hannu sun gaisa, sultan kuwa duk su ne suka gaida shi. Wai dan kawai yana da farar fata kuma yana da dukiya ba abin da ya damu abba da tsananin jin kan sultan sai dai kawai alfahari yake irin mutanan da yake so sunzo neman auran yayansa, (ALLAH KARABAMU DA IRIN WAYANNAN IYAYEN) fatima kanta duk yadda take yabö kyan sultan da dacewarsa da ajinsa sai da taji haushin yadda ya yiwa su abba har hasko yadda tahir ke zubewa kasa yana gaidasu nura kansu yake balantana Abba da yake yi kamar ya kwanta su taka ruwan cikinsa. Ta koma ciki ta barsu suna hira cikin harshen larabci, sama sama sultan yake magana ba laifi sun danci abinci kana abba ya mike da kansa ya shigo cikin gida ya sike rabi'a da asiya a falon ummin ya ji dadin adon da ya gansu a ciki.Ya ce asiya bani da matsala ta fanninki ke kuwa Rabi ina sane da abin da ke zuciyarki, ko da yake nasan kin ci gaba da son wancan bakin yaron ne dan idanunki basu yi arba da sultan ba. Na sani daga lokacin da kika ganshi kin yi bankwana da kowane da namiji sai shi isarsa da kwarjininsa sun isa su gamsar da mace tun kan ya kai ga yi mata magana. Amma duk da haka ina jan kunannki da kakkausar murya a kan sultan. Kada ki yarda bakinki ya furta wata magana marar dadi a gareshi ba wulakantaccen mutum ba ne baki isa ki wulakantashi ba. Ku taso ku zo suna son ganin ku. Ya juya Rabi ta bishi da ido tana murmushi. Ummi ta ce ki yi abin da ya ce ki yi. Ba ta ce ko mai ba ta yi gaba asiya ta bita da sultan da nazir ne kadai a falon rabi'a ta yi sallama nazir ya amsa cikin fara'a ya ce barka da shigowarku gimbiyoyi. Ta ce yawwa barkanku kuma da zuwa manyan baki muna murna da zuwanku Nigeria musamman kuma gidanmu. Nazir ya ce mun gode Rabi'a ke asiya baki mana barka da zuwa ba. Ta ce kanwata ta wakilceni. Suka yi dariya banda sultan wanda yake musu wani irin kallo da ya kara fusatar da Rabi'a. Tabbas in kyau ne abin kallo da isa da kasaita da dukiya sultan ya isa a dube shi, to amma wannan daban so daban har wannan lokaci da rabi'a tayi ido hudu da sultan zuciyarta na tare da tahir ba ta jin kuma zata sauya ra'ayinta saboda kyaun sultan. Wata kila da tausayi da kaunar tahir bata shiga zuciyarta ba da ta so sultan dan abin so ne abin haushin dai shi ne ya cika jin kai da yauki tun a lokacin ta fara tunanin anya sai yace yana sonta ba tallanta akai mai ba? Dama haka ake zuwa neman aure? Namiji ne mai jin kai da isa magana ma tsada take mai? Nazir ya ja hannun Asiya suka fice waje, suka yi tsit, sultan ya kafawa rabi'a ido bai san ma me zaice da ita ba. Saboda wannan shi ne karo na farko da ya taba zuwa gun wata budurwa da kansa sunan neman aure ya yi yammata kala kala a kasarsu da kasashen da yake zuwa musamman london inda rayuwarsa tafi yawa duk wata mace ko sultan yaje inda take ba sai dai ita ta zo inda yake. Babu abinda iyayansa suka fi so sai ya yi aure, baiga matar da zata da ce da rayuwarsa ba ne sai sanda yaga Rabi a hoto, ta burge shi sosai, sai dai ya yi ta jinjina yanda zaizo gaban mace ya yadda ajinsa yana mata hirar soyayya. Zuwa can ya budi baki da kyar ya ce Rabi'atu abbanku ya miki bayanina da dalilin zuwana ko? Ta dubi kwayar idanunsa masu kyan gaske ta ce Eh, ya yi mini sai dai ban amince ba. Sultan ya fiddo ido cikin mamaki ya ce kamar yaya? Ta ce eh kwarai kuwa ban amince ba. Saboda ban miki ba? Ya yi tambayar cikin lallon raini da wulakanci. Ta ce ba wai ba ka yi mini ba ne ba yadda za a yi mace ta dubi kamarka ta ce bai mata ba, sai dai kafin kai na mallaka zuciyata ga wani nayi mai alkawarin kaina ba zan iya janyewa in saba mai alkawari ba. Cikin takaici sultan ya ce amma Abbanku ya san da wannan bai gaya min ba, ya bari na baro ayyukana tun daga london na zo nan? Ta ce Eh to lokacin da ya yi ma alkawarin zai baka aurena a china bai san na tsaida zuciyata ga wani ba amma lokacin da ya dawo ya kawo mini lbr ka na gabatar mai da wanda nake so. Ka yi hakuri ba wai bani sonka bane ina duba girman da darajar alkawari kuma na gode da ka ce kana sona Allah ya baka wadda ta fini. Daga haka bata jira komai ba ta mike ta fice ta shige dakinsu ta kulle ba tare da wani ya ganta ba. Sultan kuwa bin bayanta ya yi da ido zuciyarsa ta yi bakikkirin ransa ya baci ainun. Tunda yake bai taba ganin wulakanci irin wannan ba, kamar shi mace karamar yarinya zata yiwa haka kawai dan ya ce yana sonta? Ya mike hannayensa zube a aljihun wandonsa ya fito ya tsaya a kofar falon, abba yashigo daga get ya hangoshi gabansa ya fadi jikinsa ya bashi ko yarinyar nan ta batawa sultan rai, da sauri ya karaso ya ce sultan lfy? Wani irin mununan kallo ya yi ma Abba ya ce mene ne yasa ka sani na zo gidanka alhali yarka tana da wanda take so. Abban ya zaro ido ya ce haka ta gaya maka? Ya ce da haka ta tabbatar mini da bakinta, ban ji haushinta ba dan nafi son a gaya mini gaskiya fiye da a yaudareni, kai ne ka bani haushi da ka bata mini lokaci. Abba ya ce dan Allah dan annabi ka yi hakuri sultan yarinya ce mai taurin kan tsiya amma zanyi maganinta bata isa ta yi ma wulakanci ta zauna lafiya ba. Sultan ya ce hakan ba zai amfani ba dan na hakura da ita har abada ka bata wanda take so kawai. Ya wuce ya bar Abba tsaye sororo don takaici sai ya wuce cikin gida yana kwalama Rabi'a kira, ummi fito tana fadin lfy. Abba ya ce ina munafukar yarinyar nan kin daure mata gindi ta wulakanta mani mutane to yau sai ta gane kuranta. Rabi na fitowa daga daki Abba ya rufeta da duka yana bambani sai da yayi mata lilis ya fice ya barta tana kuka. Rigima ta yi rigima a gidansu Rabi, babu yadda Abba bai yi da sultan ba kan ya karbi fatima ya ce bai so ya hakura da neman aure sam shi ba zai juri wulakanci ba dama haka mata suke in akace ana sonsu? Nazir ma ya yi kokarin nuna mai cewa ba haka abin yake ba ya ce sam ina shi yayi ya gama, nazir bai ji dadin lamarin ba yadda asiya ta amince da shi suke shimfida soyayya har ansa ranar aure sati 3 kacal haka ya so a yi bikin gaba daya da amininsa abin zaifi armashi. Rabi ta ci zagi a gun Abbansu fadi yake taja mai asara, ko da ace baya neman kudi yayi abinda zai samu a gun sultan da nazir ya isheshi rayuwa amma da yake ita mai kashin tsiya ce tayi mai abin da ya sa har fatiman ma yace bai so in banda ummi da Asiya ba mai goyawa Rabi'a baya duk yan gidansu haushinta suke ji da ganin wautarta, ba kamar yaya nura da yake j kamar ya shake Rabi ta mutu ya huta da ganinta haka nafisa gara gara ma bashar ya ce a kyaleta ta auri wanda take so ai jiki magayi ne. Da haushi ya ishi Abba sai ya ce Rabi'a ta turo mai bakin yaron da ta nacewa, ta kira tahir a waya ta ce ya zo babanta zai ganshi.A guje za zo ya iske shi a harabar gidansa ya fadi kasa kamar zai kwanta mai ya gaidashi abban yayi mai wani matsiyacin kallo wai a kan wannan aka wulakanta sultan ya ce. Kai anya ba asiri ka yiwa Rabi ba ta fifita soyayyarka a kan kowa? Tahir ya ce wlh ba haka ba ne Abba soyayya ce kawai daga Allah. Ya ja tsaki ya ce kai rufe mini baki munafukin banza da wofi ban yarda ba da abinda ka yiwa yata. Abinda zan gaya ma shi ne tunda Rabi ta manne bata da mijin aure sai kai na baka ita goben nan in Allah ya kaimu kazo da waliyyinka da sadaki a daura muku aure ka dauketa ku tafi bana bukatar ci gaba da zaman ta a gidana tunda ba za ta yi abinda nake so ba. Ta hir yana mutuwar son Rabi'a fiye da yadda yake son kansa a duniya yana jin babu abinda zai fi mai dadi kamar a ce an bashi auran Rabi'a to amma ba a irin wannan yanayin ba. Duk auran da aka yi ba bisa son ran iyaye ba akwai matsala. Jiki a sanyaye ya ce ka yi hakuri abba albarkar da muke nema a auran ba zata samu ba matukar babu son ku a ciki na hakura da rabi ka bata wanda kafi so. Abba ya buga mai tsawa ya ce tashi ka bani guri bana son munafunci har ni zaka yiwa dadin baki, bayan ka gama kangarar mata da kunne bata jin maganar kowa sai taka, ni dai babu ruwana da ita da auran ta da kai duk wani hali da rayuwarta zata shiga ba abinda yayi min zafi. Ya mike ya shige cikin gida ya bar tahir zube a kasa har lokacin da Rabi ta ji shuru yayi yawa ta fito ganin zaman da yayi ya fadar mata da gaba, muryarta na rawa ta ce lafiya tahir. Ya runtse ido hawaye na zuba idonsa ya bayyana mata yadda suka yi da abba ya kare da fadin wlh Rabi'a zuciyata bata da karfi kan dukkan abin da ya shafe ki da ace zan iya hakuri da ke da. . . . Ta sa hannu ta toshe mai baki ta ce mene ne dan abba ya fadi haka, ciki da gaskiya wuka bata huda shi ka kwantar da hankalinnka tunda muna son juna ne dan Allah, kuma zamu auri juna don Allah, babu abin da zai faru da auranmu sai alheri. Hajiya yaya ta dubi tahir bayan ya gama kora mata jawabi ta ce tun farko sai da na gaya ma yarinyar nan ba matar talaka ba ce ka hakura ka ki, tunda ya ce haka zan ma kawunanka da Alhaji isa magana kuje tare da su a daura auran Allah ya kyauta. Kwanan farin ciki da damuwa tahir ya yi yana farin cikin auran masoyiyarsa wai gobe ya war haka in isuna raye rabi ta zama matarsa yana jin abin ne kamar a mafarki kamar zai farka yaga ba haka ba a gefe guda yana jin damuwar yadda lamarin ya kasance. Har gari ya waye bai gasgata kansa ba sai da Rabi'a ta kirashi a waya tana kuka ta ce babanta ya matsa mata da zagi da duka har ya fasa mata jiki ya ce ta gaya mai kada ya bari karfe taran safiyar ta wuce bai zo ba an daura auran ya tafi da ita ba. Zuciyarsa ta yi mai kunci ya ce ki yi hakuri Rabi'a ko mai mai wucewa ne komi yayi farko zai yi karshe, wata rana lbr zai zama ni dai babu abin da zance muku ke da ummi sai godiya. Kun nuna mini kauna ta hakika kuma ta gaskiya insha Allahu za ki yi alfahari da aure na. Kyakkyawan zaton da kike mini na zan rike ki amana har kika sadaukar da rayuwarki gareni ba zan baki kunya ba. Ta ce Allah ya sa taìr mahaifina baya son auranmu saboda hujjarsa marar tushe ballantana makama, Allah ya sa in kasance mai farin ciki da auranka, Allah yasa in karyata maganar nan da ake cewa da namiji ba dan goyo bane. Ya ce kada wani tunani marar dadi ya shiga zuciyarki a kan auran mu ki ci gaba da kyautata mini zato kamar yadda kika saba insha Allahu za ki samu farin ciki fiye da yadda kike zato a kaina. Suna aje wayar ya tashi ya shiga gidan kawunsa tanimu ya yi mai tuni kan zuwan dauri daurin auransu, kawu ya ja tsaki ya ce ni bana son inje in da za a wulakantani.Tun kana karami kake da wannan dabi'ar duk abin da za ka yi sai ka zo da fitina da iya yi kamar kai din wani na daban ne. Yammata babu irin wanda babu a gidan nan da unguwar nan dan iya yi ka ce ba su yi maka ba katafi inda za a wukantamu muce ba zamu ba a ce kai maraya ne mun ki kula da kai don iyayanka basu gidan duniya. Zuciyar tahir ta kara baci abin ya yi mai yawa, sai da ya tuno matar da zai aura kana ya ji sanyi a ransa ya ga wannan duk ba komi ba ne. Da zarar an daura auran na ba shi matarsa an gama. A can gidansu Rabi ma dai rigimar ce a kwance tun da gari ya waye Abba yakewa rabi'a bambamin masifa da ma kwana tayi ba ta yi barci ba tana fargabar yaddalamarin zai kasance duk irin zumudin son da takewa tahir da burin auransa da take hankalin ta gagara kwanciya yayi saboda yadda lamarin ya kasance, bai wa kowa dadi ba a gidan. Wayewar gari wannan rana tun da sassafe ya kira duka yayansa a waya har da nafisa da ke kaduna da bashar da ke zariya makaranta ya ce lallai yana son ganinsu kafin karfe tara, duk sun san rigimar mahaifinsu karfe bakwai da rabi basar ya iso nafisa kuwa takwas da rabi ta zo. Abba na zaune kan kujerar zaman mutum 3, ummi na gefensa ta yi tagumi rufa'i na gefen Abba, nura ya harde a gefe daya bashir na kusa da Rabi'a wanda ke ta kure a gefe ta hada kai da gwiwa idanunta sun kumbura sun yi jawur kamar ta shekara tana kuka. Nafisa ta fi kowa jin haushin Rabi'a dan bata ga dalilin da zata jefa kanta a wahala ba ga dadi hutu na kiranta bayan kudi ga sarauta. Asiya ce ke taya rabi'a kuka yayin da fatima dan haushi tayi kwanciyarta a gefe, idris kuwa da yafi kowa tsanar rabi'a kan maganar bai zauna ba a falon. Abba ya ce dukanku kowa ya san abin da ke faruwa kan maganar auran Rabi da tahir ko? Gaba daya suka amsa eh mun sani abba. Ya ce to Alhamdulillahi gaskiyar magana ita ce bana son auranta da tahir kamar yadda kowa a cikinku ya dade da sanin ra'ayina, ban taba tsammanin akwai wata ya da zata yi mini gaddamar da rabi tayi mini ba na yi iya kokarina in nuna mata illar da nake hango mata kan lamarin amma taki. To na taraku ne dan ku shaida na bawa tahir Rabi'a duniya da lahira kuma na fidda hannu a kanta, bance ba ta cikin yayana ba yata ce, amma babu hannuna cikin duk wata matsala da zata same ta idan auransu ya yi dadi ita dadin ya shafa. Bana bukatar in ji ko mi in san komi a kai, idan matsala ce ta taso nan ma kada ta nufo gidan nan, farin cikinta nata ne ita kadai matsalarta ma tata ce. Basar ya ce Abba ka yi hakuri ka sassauta wannan hukuncin na ka, duk lokacin da iyaye suka ce sunfidda hannunsu kan matsalar dan su fushi suke da shi kenan. Fushin iyaye masifa ne ga dansu saboda girman darajar da suke da ita a kansa fushin ba zaisa ya gyaru ba sai dai ya kara shiga wa matsalar kenan. Abba ya ce kai rufe mini baki ba kiranku na yi don in nemi shawararku kan lamarin ba na kiraku ne don ku zama shaida saboda gaba. Bana son wani cikinku ya kara bani hakuri a kai, yadda ita bata hakura ta yi biyaýa ga umarnina ba ta dage kan ra'ayinta sai ni na janye nawa ra'ayin nabi yadda take so haka nima babu wanda zai sa in yi abinda ban yi niyya ba. Asiya ta duka ta ce duk haka abba ka gafarcen mu ci gaba da tayata adu'ar Allah ya sa haka shi yafi alheri, babu wanda ya san abin da zai faru gobe sai Allah. Nafisa ta zabga mata harara ta ce wai ku da kuke fadin haka me yasa ita baku tursasata ta yi biyaýa ga Abba ba a matsayinsa na mahaifinta sai shine zai mata biyayya a matsayinta na yar da ya haifa? Duk ummi na jinsu ko tari bata yi ba, idanunta kan Rabi'a wadda tun tana kuka har ta goge hawayen ta a ranta ta ce ko mi na Allah ne insha Allah komi zaizo mata da sauki. Karfe tara minti biyar tahir ya zo tare da kawu tanimu da alhaji isa abokin mahaifinsa da abokinsa ibrahim sai dan wan babansa muhamd, tahir dama ya san ba zasu samu tarbar arziki a gidan ba, har falo aka shigar da su, ummi da Rabi'a da asiya da fatima da nafisa suka shige cikin gida suka barsu a falo nan take aka daura aure bisa sadaki naira dubu dari, in banda limamin unguwar da makotansu abokan abba Alhaji garba babu wanda abba ya gayyato su ma rufa'i ne ya matsa mai ya kira su dan su shaida auran.Abba na bambami ya ce ni bana son kiran kowa in sha kunya harka ta matsiyata wa zai gayyato masu arziki ya sha kunya a banza. Motar da ummi ta ba tahir suka zo sai ya jawosu a motar mota ce mai kyan gaske da tsada amma duk da haka kallon banza Abba ya yiwa motar lokacin da aka gama daurin auran suka fito ya ce dube su da Allah, kayan da ango tahir ya sa sun isa a dubeshi a matsayin rayuwar da yake kai amma a gun Abba a talauce ya zo ransa a bace yake sosai ko ganin tahir bai son yi. Sadakima da Alhaji isa ya mikawa liman ya amsa ya mikawa abba cewa ya yi ba zai karba ba a kira Rabi a bata abin ta kuma su tafi yanzu yanzu ba zata yini a gidan sa ba. Anan ne liman ya ce ko kadan haka ba zai yiwu ba ya bari tahir ya kai mutanansa ya dawo da yamma ya dau matarsa. Abba dole ya yarda da haka tahir yaga cin fuska a wannan rana yaga wulakanci na karshe suka baro gidansu ran su ya baci sosai a hanyarsu ta komawa gida mahmud yake ta bambami ya ce wlh da wannan wulakancin yarinyar nan ko yar gold ce na hakura da ita sai dai santa ya kasheni, mutane kawai dan suna da kudi sai su dau kansu a wata tsiya. Kawu tanimu ya yi tsaki ya ce ai wlh dan kar a ce mini naki zuwa ne

Chapter 4 of 12