Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yasan nabila tayi mujin nunawa agari mijin takama ko me yasa yarinyar nan take da yawan sa'a a rayuwa ne. Tunanin su kenan, hankalinsu bai gama tashi ba sai da amir ya fiddo damin kudi ya ajiye a gabansu ya ce su rabama yara suka fice suka barsu nan zaune babu mai iya magana. Inna tashige daki gun nabila tace tabbijan wanan shine mijin naki, wanan ai ba bahaushe bane. Nabila ta ce eh ba bahaushe bane balarabe ne. Tace masu gari sai kifita kada su gaji da jiranki. Tuni ta tsala kwalliyarta tafito tana takun kwas kwas ta wuce su lalididi duk an rude ginin kudi ga matsanancin bakinciki dake damun zuciyoyinsu. Dije tace uhm da can anyi mana yanga da jin kai balantana yanzu? Naji baban nata na cewa in an gama bukin kasar waje zasu tafi ta ci gaba da karatu. Lubabatu tace ku raba muna kudin nan nasan inda zani wanan kudin dasu za a tarwatsa wanan auran ba zai yuwu muna zaune wanan matsiyaciyar yarinyar ta samu cigaba haka ba. (KUJI WATA WAUTAR KUMA) Nabila ta iske mujahid da amir kishingide a bayan mota yau direba ne ya jawosu, ta rusuna ta gaidasu, mujahid ya gabatar mata da amir a matsayin baban amininsa, itama ya gabatar da ita a matsayin matar da zai aura ga amir din. Yace to muwuce ko amir. Amir ya gallamai harara ya ce wane irin zance ne haka daga zuwan mu zakace mutafi har an gama hirar. Ya yatsina fuska kaima kasan ba wani iya hira nayi irin wannan ba tunda mun gaisa ba shi kenan sai mu tafi ba.Ranta ya baci har kunyar amir taji tace to sai anjimaku. Kansuyi magana ta koma cikin gida, amir yace wai dan Allah wane irin mutun ne kai? Matar da za ka aura din ma baka iya zama ka lallasheta ku shaku da juna ku fahinci juna wane irin zama ne za ayi irin wannan tsarin naka? Mujahid ya tsuke fuska yace amir kafin kowa ya san dalilin wanan neman auran nawa? Lifiya kalau kasan yanzu ina 25 ba zancen zan yi aure ba babu yanda zanyi in nemi auran karamar yarinya kamar wannan ko da auran zanyi, baban ta fa ya ce mun duka duka shekararta goma sha shida to me zan tsinta a jikinta. Amir yace kai mujahid kada ka auri yarinyar nan dan ka cutar da ita, nasani ba zata iya tsallake fadawa cikin kogin soyayarka ba lokaci daya zata kamu da sonka alhalin ka yadda ka dauketa a cikin zuciyarka.Ina tausayin yarinyar nan da wahala ta jurewa tantirancinka da budewar idonka.. Mujahid yace wai kai meye ka daukeni ne, abinda nakeso ka gane ina sha'awar sufofin jikin yarinyar sosai amma ba zan iya anfani da ita a yanzu ba saboda bata gama cika mace ba. Shekarunta na da rauni ba za ta iya daukar rigimata a fannin saduwa ba kaima kasan irin matan da nake ma'amala dasu ba irin wadannan matan bane na garinnan, kuma ba yarinya kamar nabila ba. Amma nasan in tana gidana akwai lokacin da zatayi cikar da zan kwanta inyi sadu da ita yadda nake so. Amir yayi tsaki yace nifa duka wannan ba shine damuwa ta ba ina nufin kada ka tafi da yarinyar nan ka cutar da rayuwarta ta hanyar kin kulawa da rayuwarta ta yan da ta dace. Yace a a wannan kar ya dameka duk abin da nasani na bukatar rayuwa wanda kudi ke iya saya zan mata, a bin da nasani yanzu ba zan iya ba shine zancen soyaya kasan ni bana son raini daga diya mace,sukuma mata raini garesu da zarar kafito ka nuna kana sonsu shi ke nan sai su raina ka, ban saba zuwa ince ina son mace duk macen da ka ganni da ita ita ta nuna bukatarta a kaina idan naga tayi mun in amsa tayinta in bata yi mun ba in fito in gaya mata ta kama gabanta. Amir yace ni kaina ina ganin bai dace ka auri yarinyar nan ba kana da wannan tsarin ba. Yace mutafi dan Allah na gaji da wannan maganar. Bakincikin nabila na yau yafi na jiya, inna lilliahi wa inna iliaihir rajun, ta shigo gidan tana karantawa ta wuce matan gidan anata kasafin kudi ta shige daki ta zauna ganin inna bata dakin yasa tayi tagumi, babu yadda za ayi ta kubucewa auran mutumin da baya sonta tunda babanta ne ya kawo shi ya ce ta aureshi, ko zai dinga yankan naman jikinta ne in an kaita gidanshi ta amince ya yanka in har ran babanta mahamud zaiyi fari ta ci gaba, mahmud ko shine ya haifeta ya ci tayi mai biyaya balantana ba shi ya haifeta ba yake nuna mata soyayar da bai nunawa yayan da ya haifa da cikinsa. Sannan tana matukar son mujahid son da bata taba tunanin zatayiwa wani da namiji ba a duniya. Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Launin Fata 2-06 Posted by ANaM Dorayi on 07:13 PM, 22-Oct-15 Under: Launin Fata Wadannan dalilai 2 suka sa ta amince zata auri mujahid zata amince da duk wata fitina da zata gani a gunsa kuma bazata bari wani ya gane a kwai matsala tsakaninta da mujahid ba. karfe goma sha 2 dare mujahid ya mike daga kan gadonsa ya dubi amir wanda yaketa bacci yayi murmushi yace, da raina da lafiya ban iya ina kwanciya ina barci nikadai a kan gado. Ya shige toilet yayi wanka ya tsuke cikin kananan kaya ya baza turare ya dau key din mota, mai gadi ya daga mai get ya finciki motarshi ya bar gidan. Gidan budurwarshi ilham yaje cikin unity road, yayi fakin a kofar gidan ya kira ta waya. Yace ke da waye yanzu?Tace ba kowa sai kanwata zeenat . Yace to fito ki bude mun get inan kofar gidanku. Ta buga tsalle tace dan Allah in zolayata kake kabari kada kasa zuciyata ta buga, babu wata macen da take da tagomashin kaje gunta da kanka sai dai kai aje a sameka. Yace ke ni bani son surutunki ki zo ki bude mun get.ta watsar da wayar ta fito sai da ta ganshi ta yarda shi din ne, aka fara watsewa. Daya daga cikin abin da yasa mata suke son mujahid da sha'awarsa ya mugun iya soyaya duk bacin ran da mace ke ciki idan tazo hannun mujahid yanzun nan so yayayr sa zai sa ta manta a duniyar ma da take balantana ta tuna wata damuwa. Idan mujahid ta tashi farkon abinda zaiyiwa mace shine yayi mata wata runguma kamkam wace zatasa taji kamar numfashinta zai dauke,kana zai dinga bata hot kis ta ko ina yana mata wata irin busa a kunne, lokaci guda zakaga mace ta fita daga haiyyacinta, kuma a tsaye zai mata haka sai ya gama gala baitar da ita a haka kana ya kwantar da ita. . . . . . . . . . Abin da bai amince ya bata lokaci a kai ba shine zancen soyaya. Sai yaga mace bata da tagomashin da zai zauna yana rokonta ta soshi ko wacece ita din kuwa idan ma ya lura tana da rawan kai ko yanga da jan aji sai ya san yanda ya rumgumeta ya hadata da wannan salon nashi kawai sai kaga mace ta ajiye yangar nan da dukkan jin kan ta rusunar da kanta gareshi tana rokon suyi soyaya kawai.Idan mujahid yayi anfani da mace sau daya shi kenan ya rabata da duk wani jin dadi a gun wani namiji, bata iya tunanin wani sai shi, shi yasa duk inda yake zakaga mata na binshi kamar jela. Wanna ne ya zamo sanadiyar da bai iya bin mata mace da kansa ya ce yana son ya saba sai dai a zo gareshi asamu ya kula matsayi ne, domin a gun mace a ganta da matashi wanda ya isa matakin rayuwa kamar mujahid ba karamin cinyewar bane ba karamin daukaka darajarta da ajin ta na rayuwa bane,kuma duk inda mace ta kai da dajarabarta mujahid yasan yadda zai kosar da bukatarta taji ta gamsu, mujahid jarumin namiji ne shiyasa yake ji da kansa, dan shima yasan ya gama haduwa. Dan gatane sosai a gun iyayensa ba su son damuwarsa shine dalilin da yasa suka hakura ya nemo matar da yake ra'ayi da kansa ba su bashi zabin su ba.Lokacin da yake kasarsu bai sa fitinar mata a ransa ba, sai da yaje maleshiya karatu matan da kansu suka bude mai ido har ya kware da neman mata, sabo da dai sun ganshi yaro matashi mai jini a jika gashi ko a ido yana da sifar jarumin maza, dan haka ko mace bata dan danashi ba in ta kalleshi ta san za a huta a jikinsa, ga uwa uba naira. Matan wannan zamanin babu abinda suke so a tare da namiji sai kyau da naira idan namiji ya mallaki wadannan abubuwan sun amince yayi musu ko wane irin wulakanci za su bishi a haka (amma wasu fa hakane ?) Saboda mujahid bai san zafin naiman kudi ba ajiye mai su kawai ake shi yasa bai jin zafin yin kyauta ko da na wace. Zai baiwa mace in dai zai ji dadi a jikinsa zai cika mata jaka da naira, tayaya ba za a dinga binsa ba. Tun baifi shekara daya a malesiya ba ya zama kwarare a harkar mata da kora barasa, amma yasan yanda yake tafiyar da rayuwarsa yanda yake mu'amala da mata da barasa ba kowanne zai gane hakan ba. In ka ganshi ba zaka taba cewa yana wannan halaiyar ba in gaya maka akayi ka iya cewa shairi ne wannen ne ma yasa hankalin iyayansa yake kwance da zamansa a malesiya basu girgiza hankalinsu ya tashi ba sai watarana da abbansa ya kai mai ziyarar bazata a gidan da yake a malesiya ya iske mujahid din kwance a falonsa daga shi sai wani mi tsitsin pant wata budurwa tana mai tausa yayin da wata take dakin baccinsa itama tsirara tana jira a gama da ta falo a dawo kanta, ga kwalbar barasa birjik ya sha ta isheshi. Lokacin da suka hada ido da mahaifin nasa zatonsa mafarki yake dan haka ya ture hannun budurwar tasa mai suna laila ya mike zaune yana mitsitsike idanunsa, abba nashi na tsaye ya rumgume hannuwa yana kallon dan sa mujahid. Duk fitinar mujahid da taurin kansa yana tsoran iyayansa bai son abin da zai bata musu rai. Laila ta shiga tambayarsa waye wannan, ya buga mata tsawa cikin harshen turanci ya ce mata maza ta bar gidan babanshi ne ya zo. Ta barmar kunya da hauka ake nadeta abin da yayi kenan, abban nashi ya zare mai ido ya ce kai shiga hankalinka kada ka wulakanta yar mutane a banza da me yasa a kirawota, ba ni ya dace kaji tsoro ba Allah da ya halicceka ya dace kaji tsoro wanda shine ya haramta abinda kake aikatawa. Abin mamaki da takaici ga aban shine yadda ya ga wata macen ne tafito daga dakin barcin mujahid tsirara daga ita sai dan pant da bra tana wata irin karairaya tazo ta dafa shi tace lfy? Ya hankadata itama ta fadi kasa. Abban ya buga mai tsawa yace kai kada ka karya yar mutane a banza ni kaga tafiyata ka ci gaba da abinda niyya tunda shi ya dace da rayuwar musulmi kamar kai. Yafice daga gidan alokacin yasa aka shirya jirgi ya bar kasar hankalinsa a tashe game da halin da ya iske danshi. Ya dawo da mahaifiyar mujahid labari mara dadi tace alhaji babu abinyi illa ayiwa yaron nan aure a kai mai mata can shine zai rabashi da bin matan banza. Yace nima tunanin da nake kenan sai dai kinsan mujahid da taurin kai ya iya cewa baya so? Sai dai mu bashi damar lallai ya kawo matar da yake so da kanshi a aura masa ita ko a bashi duk wacce ta samu. Mujahid a wannan rana ya kwana ne cikin matsananciyar damuwa duk yada ya tsani kwana shi kadai a kangadonsa ba tare da mace ba haka ya kwana a ranar yana juyi ya tsani abinda zai bata ran iyayansa. Duk in da ya dace ya ga mahaifinsa sai da yaje bai sameshi ba ya tabbatar juyawa yayi ya bar kasar ya kasa kiranshi a waya dan yana jin tsoron abin da za a ce da shi. Gaba daya jikinsa yayi sanyi yasan tilas sai wani abu mara dadi ya biyo bayan wannan ziyara ta bazata da aka kawo mai tundaga ranar ya dan ja baya da mata da barasa ya rage bai dai daina gaba daya ba. Aka shafe sati daya bai naimi abba da umminsa a waya ba shima babu wanda ya nemeshi alhalin da kullum sunyi magana, in shi bai nemesu ba su zasu nemeshi suji ko yanada wata matsala. Yayin da kullun abbanshi sai ya kirashi da asuba yace ya tashi yayi salla. Shi yasa duk yanayin da yake ciki da mace idan asuba ta doso zai koma cikin natsuwarsa abu a muryarsa tundaga wannan rana da abba ya ganshi bai kara kiransa ba, dama amir ya sha gaya mai idan bai daina abin da yake ba iyayanshi zasu kamashi watarana. Yayi dariya a lokacin yace haba kamar wani yaro? Amir yace iyayene fa sunfika wayo da iya zaman duniya duk budewar idanuwannan naka a tafin hannunsu kake. Bai dauki maganar amir da wani muhimmanci ba sannin cewa abin da yake fada ba me wani muhimmanci ba ne, bai tashi tunawa da haka ba sai ran da abbanshi ya kamashi dumu dumu, kuma yayi mai abinda ya tsana wato ashareshi ba a ce mai komai ba har gara ayi mai fada, ko a dakeshi ma da wannan shurun da akayi mai bai san matsayinsa a gunsu ba bai san hukuncin da aka yanke mai ba. Ranar da sati biyu ya cika hankalinsa ya gama tashi abisa dole ya ajiye komai ya nufi kasarsu a can ya iske amir yayi mamakin hakan zuwansa bai ba iyayensa mamaki ba shima bai mamakin kin sakar mai fuska da ummi da Abba sukayi ba a ranar da ya sauka yana gidansa shi da amir yayi tagumi gaba daya ransa abace yake, amer me abba yace maka game dani? Amir yayi dariya ai kiran da yayi min nakane saboda kai din yace in ajiye komai inzo yana son ganina. Gabanshi ya fadi ya matso kusa da amir yace me yace maka? Amir yace abinda nake ma fada a kai baka daina ba shi ya kirani ya tambayeni dama can halaiyarka haka take ko daga baya ka fara. Idanuwan mujahid suka fito waje yace sai kace me amir? Ya tamke fuska. To me zaince inbanda in gaya mai gaskiya, kokuwa kana ganin zan iya yiwa abba karya ne? Ya girgiza kai. A irin fahimtar da abba yayi mun ba zai yuwu in boye mai gaskiya ba dan ya hadanine da girman Allah da darajar manzonsa in gaya mai gaskiyar abin da nasani na halaiyarka matsayina na amininka wanda yafi kowa sanin sirrinka ciki har su da suka haifeka. Na rasa amsar da zan bashi a lokacin yace amir kaji tsoron Allah ka gaya min gaskiya ka ci amanata. Nantake na gaya mai yadda ka koma tun komawarka malaisiya ban taba ganin damuwarsa irin wannan rana ba. Ya jima zaune tsit daga bisani yace amir tunda kake tare da mujahid kataba jin macen da yace yanaso? Nace gaskiya ban taba jiba dan nasan yammatan dake rububin sonsa, yace akwai wacce ya taba nuna sha'awar zai aura? Anan ma nace ban taba gani ba shi da yake cewa sai ya kai shekaru arba'in zaiyi aure. Abba yace wannanan karon zan fuskanci abinda bai so zan masa aure ko yanaso ko baya so ba zan zuba mai ido dan ina da kudi ba na sakar mai kudi ya dinga sabon ubangiji da su. Annan na shiga lallashin abba da yayi hakuri ya barka ka kawo mata da kanka kada ya ce zai baka mace da kaanshi, saboda idan yabaka mace da kanshi abin da zai faru shine matar tana ganinka zata kamu da sonka kai kuma bai zamo dole kasota ba zata sha wahalane kawai a kanka azo a bata goma daya bata gyaru ba, har gara in kai kanemoi ko baka sonta sosai da sauki a akan wadanda bakaso kwata kwata. Abba dai ya amince da hujjata yace zai baka zabi cikin kankanin lokaci, yace zai aikeni in gaya ma hakan sai gashi Allah ya kawoka. Innalillahi wanna ilaihi'raju'un. Mujahidke fadi yana fadin na shiga uku ni nura ina ni ina aure yanzu? Amir yace nura aure lokaci gareshi lokacinka ne yazo sai dai kayi hakuri. Kwana sukayi yana nanata maganar da gari ya waye ya shiga gidansu a dakin mahaifiyarsa ya iskesu tare da abba yana mata bayani yadda sukayi da amir a jiya. Ya zauna a kasa yana gaidasu, abba yace dole kaji kunya mana, kowa ya gyara ai ya sani haka in sabanin haka, hakika nayi mamakin haka saboda ban taba zato ba, bamu kasabawa ba Allah da ya halicceka ka sabawa ka roke shi gafara, mu dai hukuncinmu a nan zakayi aure abokinka amir ya bukaci mu baka zabi to mun baka watanni uku to kaka wo mana matar da kake so kuma ka tabbatar kakawo wadda zamu amince da ita da iyayenta ita ce wadda zata dace da rayuwarka. Mujahid ya baro kasarsu ya dawo malesiya da muguwar damuwa da tunanin yadda zaiyi, zahiri da badini baya son yin aure a wannan lokacin dan a ganinsa ba karamin takura zai zamo mai ba da sa ido. Bayan wata biyu da yin haka yasa mu hutu baije kasarsu hutun ba saboda fargabar abinda zaije ya taras, gashi saura wata daya cikar wa'adin da abbansa ya dibarmasa baiga ko alamar matar da zai aura ba shine dalilin da yasa ya nufo kano hutu. Aranar da ya sauka kano airport ya hadu da laila ta dawo daga lagos suka mannewa juna bai nemi gidansu amir ba inda yake sauka in yazo kano sai da yayi kwana uku suna lalacewarsu da laila da kyar ta amince suka rabu kamar zatayi hauka a kansa ga iya soyayya ga kudi. Lokacin da ya dora idonsa a kan nabila kai tsaye ya amincewa zuciyarshi zai aureta, amma fa ba soyayya ta sosai a ransa dan shi bai iya soyaya ba zallar sha'awa da fitina a kan mace na tashan samartaka da naira kadai ne a kansa. Sai karfe hudun asuba ya saki laila tana nunfarfashi shikam bacci mai dadi ya shiga yi, laila na kallonshi kamar zata lasheshi dan masifar so da sha'awa Laila shaidaniya ce idonta ya bude sosai da bariki tana harka da alhazawan birni masu ji da kansu amma babu wanda ya taba gamsar da ita kamar mujahid, gata dai yarinya duka bata fi shekara ashirinba amma ta iya salo salon da wadda ta haifeta a bariki bata iya shi ba. Duk wannan shai dancin nata mujahid ya kere mata gudu ya sha gabanta ta ko ina. Tana zaune tayi tagumi tana kallon mujahid taji wayarsa tayi ringing ta dauka taga ansa abbana, ta girgiza kafadar mujahid da karfi ta tashi da sauri jin ringing din da yasa a kan wayan mahaifinsa yasa ya mitsitsike idonsa ya nutsu ya amsa da sallama. Abban nasa yace nura katashi kayi sallah kokuwa kana nan kana ta barcin? Yace abba bansan na makara ba yanzu zanyi. Cikin taushin murya yace nura ka rinka rage son duniya ba ko mai a cikinta sai rudani na rashin tabbas. Kayi kokari ka rike addininka da gujewa sabon Allah, ka tuna komin dadewa..... Zaharaddeen shomar Whatsapp 08168575100 Launin Fata 2-07 Posted by ANaM Dorayi on 09:37 AM, 23-Oct-15 Under: Launin Fata Katuna komin dadewa zamu hadu da Allah kowa sai yayi bayanin abinda ya aikata da kansa ranar gaskiya da gaskiya. Mujahid yayi tsit tana sauraran abbansa jikinsa gaba daya yayi sanyi har bayan sunyi sallama ya ajiye wayar bai iya tashi daga gun ba, sai da laila ta kwanto kan ciyarsa ta bayansa a zaune, yayi ajiyar zuciya ya mike yayo sallah yayi tagumi laila tazo gabansa itama tasha kwalliya ta zauna ta meke kafa tace nura me abbanka ya gaya ma da ya sauya ka cikin gaugawa haka? Cikin sanyin murya yace laila abbana yayi mun nasiha ne na inji tsoran Allah in rike addinina in daina aikata sabon Allah, kana in dunga tunanin ranar da zan hadu da Allah. Zamuyi sallama dake yau dan aure zanyi iyayena basa son abin da nake.Ta dafe kirji ta kankameshi tace dan Allah mujahid kada karabu dani ina sonka fiye da yanda nake son kainama ka taimaka ka aureni ka cece rayuwata zan bar wannan harka.Ya mike ya ajiye mata makudan kudi yace laila kada kisawa zuciyarki zaki sameni dan ba zaki sameni dinba kiyi hakuri Allah ya dubi niyarki ta barin sabon Allah ya baki mijin da ya fini ko mi a rayuwa. Yafice da ga gidan ya bar laila tana faman kuka Afalon sashin amir na farko ya iske amir don kwance yana bacci ya girgiza mai kafada ya mike zaune cikin magagi yace daman mafarki nake baka nan? Yace kai da Alla can sarkin magagi dawo cikin natsuwarka.Amir ya mitsitsike ido yace nasan da gaske bakakwa kana gidan nan ba Allah yasa nabila na da juriya bata da fitinar sha'awarka. Ya yi tsaki ya shige daki ya fada kan gado sai bacci. kanin mahaifin mujahid dake zaune da iyalansa a nan kano shi ne suka gabatar da komi tare da Alhaji mukutar na neman aure bisa al'adar kanawa kenan mahaifin mujahid yaji dadin yanda kaninsa alhaji muhammadu mustapha ke bayyana mai nagartar gidan da mujahid ke neman aure, haka nan mata sun shai da masa yarinyar kyakyawar gaske ce kamar larabawar ce suma ko da yake anshaida musu mahaifiyar yarinyar balarabiyar kasar yemen ce gaba da baya.Har suka tura masa hotunanta ta wayar mahaifiyar mujahid tayi farin cikin hakan sosai haka nan taji tun a hoto tana kaunar yarinyar basu da fargabar ko mi a kan batun soyayar dansu a zuciyarta dan sun amince da dansu abin so ne a duk inda yaje kyawun hali shine abun ji, sun amince ta hada jini da ita. Duk shirye shiryen da ake na auran amir ke gabatar da ko mi ga amarya da kawayenta babu abin da ya damu ango iyaka yaxo su gaisa yayi tafiyarsa.Abu biyu ya hadawa nabila soyayya da damuwa. Son mujahid na cin zuciyarta tana fama kullun dare darana da wahalar ciwon sansa, damuwar rashin kalawarsa da ita ta hanata sukuni.Kawayenta irinsu fauziya fadi sukeyi masha Allahu har innice na dace da miji irin mujahid koda yankan naman jikina ma shi zaiyi din dan rashin kulawa ai zan zauna dashi.idan damuwar rashin kulawarsi ta dameka sai ka tuno kyan kyawun idanunsa su kadai sun isa su mantar da mace duk wata damuwa da ta shafeta,balantana in ya budi baki yayi magana tautausar muryarsa ta ratsa sassan jikin mace.wannan shine tunanin mafi yawa a cikin kawayenta, wasu kadan ne da suke ganin jin kan mujahid yayi yawa.Nabila tana da kyan da namiji dole ya kalleta ko da bai son mata amma shi ina kudi dai gasu nan ba matsala. Ko wayar hannu irin mai masifar tsadan nan ya aiko mata musanman ya bada oda aka kawo maiita ya ba amir ya kai mata dan in yana son magana da ita ya kirata waya ce wadda duk wanda ya ganta yasan ta hadu. Lokacin da aka kawo kayan lefen nabila mutanen gidansu cewa sukayi wata kila mujahid dan yankan kaine saboda uwar dukiyar da aka kashe a kayan, sai kace ba asan ciwon kudi ba. Akwatuna ne set biyu kowanne sai guda shida ba yawan akwatunan bane abin kallo a a kayan da aka danno a ciki atamfofin da leshi leshi da shaddodi kamar suyi magana, gold kuwa wani karamin kit aka ciko da si abin ya wuce ayi magana ga hassada sai dai shuru kawai ana gyada kai. Lubabatu tayi tagumi tana ta kaicin kudin da ta kashe a gun bokaye ana ce mata ba za ayi auren nabila da mujahid ba ko yaushe sai ci gaba magana take. Su kansu yan kawo kayan sun fahimci mutanen gidan ba kaunar nabila suke sosai ba, saboda basuyi masu tarba da ta dace ba. Aranar mahassada irinsu Dije kamarsu hadiyi zuciyarsu su mutu.Washegari aka fara buki aranar ne iyayen mujahid da manyan abokansa suka iso kano duk dacewa anyi abubuwan ne a kuraran lokaci duk da hakan abubuwan suntafi cikin burgewa da ban sha'awa. Masu bakin ciki sai dai rusa kuka kawai duk duk yanda suke zaton daukakar nabila ta samu ya wuce nan, mutum ba zai gama fahimtar hakan ba sai aranar alhamis din nan da aka shiga gaggarumin fatin manyan baki da kowa da kowa ya halarta su dije sunce ba inda zasu basu saba ganin irin wannan watsewarba, yaya da iyaye sai tafiya wai party daga baya kuma suka gagara dai basu iya zama ayi babu su suka shiga wata jibgegiyar mota mai numfashi sanyin AC na ratsasu aka kaisu wani kayatacen hotel a nan kano inda akayi party. Anan sukaga mahaifiyar mujahid da mahaifinsa da wasu daga cikin yan uwansa, fararan kaya ango da amarya suka sa babu walwala sosai a tare da mujahid saboda bai sami gayyato yan matanshi ba a dalilin zuwan iyayensa wanda baiyi zaton zai gansu sun zo ba,da yake auren da matar duka ba damunsa sukayi ba sai ya sa bai yi wani shiri ga bikin ba duk da haka duk wanda yaje bukin nan yasan ana kashe naira kuma an burge iyakar burgewa ango da amarya sunyi kyau har sun gaji yanda ango bai da walwala haka amarya zuciyarta ke cike da damuwa, amma bata bari damuwar ta bayyana a fiskarta ba dan kar babanta muhmud ya fahimci cewa bata son auran ya shiga damuwa, duk abin da zai bata ran bawan Allah nan bata sonshi saboda darajarsa da kimarsa a gunta shida mahaifiyarsa shiyasa ta sadaukar da rayuwarta kun faranta musu kamar yadda suka ji tausayinta lokacin da take neman taimako.Duk lokacin da tuno iyayenta sai tayi kuka, tunaninta a kansu ba mai kyau bane, gani take sun watsar da ita ne kowanne ya kama gabansa ko ta rayu ko ta mutu oho bata taba furtawa inna wannan tunanin nata ba dan kar ta sauyata daga haka a haka take son ta tafi tana musu addu'a ne saboda arzikin haihuwa kawai kauna da soyaya sai baba muhmud da inna. Tunanin da kenan fati har aka tashi zuciyarta babu dadi, da suka dawo gidansu fauziya inda suke zaman amarci da kawayensu ta kwanta lamo bisa gado gobe ne juma'a za a daura musu aure da mujahid na mijin da bai damu da ita ba zai aure ne dan wani dalili nashi nakanshi ba dan soyaya ba.A daidai lokacin da zuciyarta takeyi kamar ta fashe dan tsananin soyaya.. Yanmata kawayenta sha'aninsu kawai suke biki yana musu dadi saboda iyayen kudin da aka sakar musu wautarta suke gani yadda bata da walwala da gani kasan tana tare da damuwa, fauziyya har ta gaji da yi mata nasiha ta sa mata ido.washegari da safe aka daura auren nabila da muhmud nuraddin (mujahid) bisa sadaki naira dubu dari biyar wanda ango yabiya da kansa kamar yadda shari'a tazo dashi, sauran hidindimun auren kaf iyayensa da alhaji mukatar suka yi mai. Tuni sun shaida wa iyayen amarya da ko tsinke komi suna da shi amarya kawai suke bukata. Da yanmacin ranar mafatin suka tafi launchin ne na cin abincin rana harda yaya a sani abacha stadiym, makada da mawaka sun sha kudi

Chapter 10 of 12