Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
saratu wani suna ya dace a sawa yarnan? Ta ce na taba jin tahir yana son suna nabila. Yace shikenan angama magana sunan wanan yarinyar nabila, Allah ya rayata Allah ya sa mata albarka. Saratu tace amin. Ya mika mata ita zai fita sai ga ummin Rabi'a tare da fatema da bashir da nafisa. Rabi'a ta mike ta rumgume ummi tana kuka, itama ummi kukan ta kama yi Bashir yace to meye abin kuka kamar wada akayi muku mutuwa.Nafisa ma haka tace, fateema ce mai tayasu kukan, ummi tace an yi yanka ne? Rabi ta ce a a. Tace to akwai rago a mota saboda haka na ce bashir sayo wa za a yiwa magana a yanka. Tace bari na kira saratu a tambayeta. Matan gida suka fito tsakar gida ana shewa da yada magana a wulakance suka masa gaisuwar su ummi, nafisa tace gaskiya ummi tafiya zanyi bana son harka tatsiya wannan ba xan iya zama a gidan nan ba inna cigaba da zama ina ganin wadannan abubuwan rigima za'ayi dani. Ummi tace muma tafiya zamuyi kinsan abba yana nan banda kinxo ma da ba zai barmu mu zo ba. Baba ibrahim ne ya yanka ragon shida bashir sukayi komaidole su ummi suka tsaya har akayi azahar ta ba rabi'a kudi masu yawa ta duk abinda bata dashi ta siya kada ta yarda ta bar gidan nan abba yaga gaxawarta suyi mata dariya shida su nura da nafisa. Da sukayi waya da asiya daga london ma haka ta gaya mata tace kin burgeni Rabi'a hakurin da kikayi ba xai fadi kasa a banxa ba isha'allahu sai kinga sakamakon hakuri domin Alla (s w a) shi yayi alkawarin yana tare da masu hakuri. Tace anty asiya kina zaune lfy da nazir ko? Tace eh muna xaune lfy da nazir don yana sona ma iyaka abba ya yi min illar da yasaba yimana a gun surikansa ma'ana ya nuna kwadayinsa a fili ga nazir, ko haka wani dan sabani ya hadamu dashi sai ya nuna mini kwadayin ubana, wanda hakan ba karamin ciwo yake yimun ba. Ko da yaushe sai na tunaki tare da jin jina maki da kika tsaya kan ra'ayinki kin samu soyayya mai tsarki a gun mijinki wanda babu al'gus a cikinta.Lokacin da tahir ya cika shekara daya cif bai dawo ba mutanen gida suka fara yan tsegumgumi akan xamar matar shi cikin gida. Wasu suna cewa a sallameta ta tafi gidansu wasu suna cewa a kai kara kotu a raba auran harda masu cewa idan anraba auran su suna so kowa dai yana kawo nasa son zuciyar, wani abun in rabi'a taji tayi kuka wani abun tayi dariya. Takan raba dare akullum tana adu'ar in har mijinta yana raye Allah ya dawo mata dashi.Don har yanxu babu namijin da take so take kauna sai shi, tayi kuka tayi kuka kamar kwayan idonta zai zazzago, saboda rashin mijinta abin alfaharinta. Wani lokacin idan nabila tana kuka sai ta dinga ganin kamar kukan maraicin rashin uba take. Sai itama ta kama kuka ta dau yar ta rungume tana fadin yi hakuri nabila ba ke kadai zakiyi kuka ba tare zamuyi kukan rashin mahaifinki jarumin namiji daya tamkar da dubu mai tausayi da kulawa. Sai tayi mai isarta take hakura tashare hawayenta tunda babu mai lallashinta. Sau daya taje gidansu ta kai ma abbanta yar ya karbeta yace dubi sanadin auran bakin mutum kin haifo bakar ya saboda taurin kai irin naki duk zuri'ar mu ba baki sai wanan yar. Ya jefa mata abinta kan cinyarta ya mike yana tsaki zai fita ummi tayi murmushi tace wannan yar tazamo abin alfahari a gidan nan tunda ita ce jika ta farko a gidan nan kuma insha Allahu sai anyi alfahari da ita har kai kanka. Domin ka ba Rufa'i diyar fararan mutane ita da iyayenta sun ce ba zata haihu ba, Rufa' bai ajiye mana jika a gidan nan ba, nafisa ka aurar da ita ga mai kudi (half case) ya ce bai yarda da haihuwa ba bai son yaya bata ajiye mana jika a gidan nanba, ga asiya can a london a gaba na a gabanka yace ba zai rufe mana ko mai ba zai mata allurar hana haihuwa saboda bai shirya haihuwa yanxu ba. Abba yaja tsaki yace shine me? Dan rufa'i da nafisa da asiya ba su haihu ba har wani abu ne? Tace wani abune mana. Kai yanzu da me kake takama in ba da yayanka ba. Kamayar dasu hannun jari da kake samun kudi shiga da su in har haihuwa ba wani abu bace ba xakayi takama dasu ba. Yayi mata wani lalatacen kallo ya wuce bai kuma cewa komi ba lamarin baiwa rabi'a dadi ba ta kama sharar kwalla. Ummi tace ki daina bata hawayenki a banza, in sha Allahu sai abba ya ci gajiyar wannan yar da ubanta sai ya gano kuskuren da yake tafkawa. Har rabi'a ta baro gidansu a ranar bata daina kuka ba shine dalilin da yasa bata kara zuwa ba.Sai ummi ke zuwa ganinsu tana kawo musu duk abin da suke bukata ita da fateema bashir in yaxo hutu shima rufa'i yazo musu sau daya, nura ko ko hanyar gidan bai taba yowa ba, halaiyarsu daya da abba ta kyamar bakin mutum da talaka kamar su sukayi kansu a fararan kuma su ne suka baiwa kansu arzikin. * nabila na da wata 5 ta iya xama sosai, rabi'a ta gaji da zaman da take yi haka ta fara zuwa islamiyar matan aure dake bayan gidansu ta asabar da lahadi. Ranar wata laraba wuraren karfe 8 na dare, danladi ya shigo dakin ta yana salama a hankali babu mahalukin da ta tsana irin daladi ta ajiye littafi arba'una hadis da take dubawa ta kwantar da nabila cikin net dinta ta kura mai ido lokaci daya yake zama kujera tace lafiya? Yayi wani munafikin murmushi yace ita ta kawo haka. Tace to tashi kafitan min daga daki ko nayi maka ihu. Ya bushe da dariya yace idan kinyi mini ihu abin kanki zai kare gara na kirufa wa kanki asiri ki tsaya kiji abinda nazo na fada maki. Ta saki baki tana kallon shi tace to koma me zaka fada mini ban ga dalilin da zaka shigo min daki awanan lokacin kanka tsaye haka ba. Kada ka manta nanfa dakin matar aure ne, idan akayi ma haka dakin matarka ranka ba zai so ba, akwai hadisin manzon rahama (s a w) da yake cewa imanin dayanku baya cika har sai ya sowa dan uwansa abinda ya ke sowa kansa. Ina nasiha gareka mhmd kaji tsoron Allah ka dinga tuna gamuwarka da Allah. Ka daina barin shaidan na wasa da hankalinka da zuciyarka, kasani duk abinda kayi sai anyi maka shi. Alokacin ne ta tabbatar jikinsa yayi sanyi tasan inda ba a kaunar tahir a gidan nan ba ya xa ayi manyan gidan nan susawa danladi ido yana haike mata haka. Ko a tsakar gida yasameta ta ayyukan da ta saba sai ya dinga yi mata maganganun da basu kamata ba ko matarsa tana gurin ba abin da ya dameshi, amma duk cikin gidan ba bu wanda ya taba ko da kalubalantarsa kan haka balantana a samu wanda zai tsawatar masa. Batasan wane irin tunani yayi ba sai yatashi ya fice, tabishi da ido daga bisani tayi tagumi hawaye nazuba a idonta ta dauki nabila ta kamkameta tana fadin tahir ina kashiga ne ka barni cikin fitinar yan uwanka? Tatashi tasawa kofarta key dan kada ya dawo * tunda tahaihu tayi 40 ayyukan gidan suka ninka na da ta daina sa lamuransu a ranta tana damuwa, damuwar rashin sanin inda yake kadai ya isheta ta kan goya yarta tayi ta fama da ayyuka tun safe har yamma, in badare yayi ba bata samun hutu. Sukance mai kankanba da iyayin tsiya bai nan tayi aiki a kan dole. Tana tsugunne tana tatar koko da hantsi daladi ya shigo ya tsaya a kanta sai dije nagefe har matarshi lubabatu suna hira yace oh malama rabi tata ake ne? Ko daga kai batayi ba ta dubeshi tama ci gaba da aikinta, yayi magana tayi mai banza. Sai kawai lubabatu matar tasa ta fashe da kuka. ta tashi tashiga dakin mahaifiyar danladi shi kuma ya kada kansa yayi waje, yayin da duka matan gidan sukabi bayan lubabatu tana gaban innar danladi tana kuka tace inna nikam nagaji da wulakancin da danladi yake yi mun a kan wanan kodadiyar yarinyar da watakila ma mayyace. Idan so yake ya aure ta ya fito fili mana ya fada? Nanfa matan gidan kowa ya ta fadin albarkacin bakinsa wasu na fadin ba laifin daladi bane laifin Rabi'a ne ita ke masa kisisina har taja ra'ayinsa yarinya sai shegen feleken tsiya, yanda ta mallake tahir haka takeso tayiwa danladi shima in ya aureta a nemesa a rasa. Innarsa tace Allah ya sauwake ki share hawayenki zai gamu dani. Yini guda ranar maganar da akeyi kenan mamakin yanda aka lankayawa rabi sheri ya isheta tana fadin wannan rashin tsoron Allah da yawa yake, mutane sun san gaskiya kiri kiri amma dan son zuciya da tsoro su take. Danladi bai dawo gidan sai dare bai nufi dakin kowa ba sai dakin Rabi'a sai ya tsaya a bakin kofa ya kwankwasa mata kofa tace waye? Yace nine danladi. Tace kakoma ba zan bude ba. Yace kidubi girman Allah ki bude da kanki idan kinki budewa zan karya kofar. Ta taso ta bude tana sanye da doguwar riga ta dora dogon hijabi akan fiskarta murtuk kamar bata taba yin dariya ba, ta jingina da kofa tace lfy. Sai tayi mai kwarjinin da bata taba yi mai ba ya shiga inda inda sai taja tsaki tace idan har wanan inda indar ce tasaka bugun kofa ka kama gabanka dan bani da lokacin sauraranka. Yace ah ba haka bane kin gane Rabi dan Allah ki tausaya min ki bani hadin kai na rasa yanda zanyi da sha'awarki da ke damuna in ma kin yarda zamuyi aure zanyi muki duk abinda kike so tunda kinga har yanzu tahir bai dawo ba. Tayi masa wani wulakantacen kallo tace an dai sha haushi an kuma fadi ba nauyi. Ni ba yar iska bace na tabbatar da haka, auran tahir dake kaina yana nan bangaji dashi ba ko zai kai shekara goma bai dawo ba ina nan ina jiransa, in har da yardata xakayi fasikanci dani to ba ka isaba in kuma fyade zakayi mun kafili ga mai doki. Tuni dai kana sane da sharadin da na gindaya ma duk sanda kasake kayi mini fyade kuma wlh da gaske nake karka dauka barazana ce in kuma ba kayarda ba kana ganin wasa ne ka gwada kasha mamaki. Ta maida kofar ta rufe da karfi ta barshi nan tsaye ransa gaba daya ya baci ya shige dakin dije yana banbami ya fada mata wulakancin da rabi take masa dan yanuna yana sonta. Ta ce rabu da shasha ta tsaya jiran mijin da babu tabbacin rayuwarsa idan gari ya waye zansa a rubuta takarda ka ba babanta kace tahir ne ya aiko da ita daga inda yatafi yace a ba matarsa ka nuna mai cewa zatafi daukar sakon da muhinmanci idan shi ya bata da kansa saboda shi tafi ganin darajarsa. Ta kadar xata kumshi sako ne daga tahir yana bada umurni daga matarshi rabi'a idan ta sami muji tayi aure ya sauwake mata saboda bai san ranar da zai dawo ba. Ihu daladi yayi da tafi yana yiwa dije jinjina yana fadin shike nan kinga an huta ta hakura dan dole ta tafi gidansu daga can dan dole ta aureni ko dan yarta. (kaji wauta). Irin wuraren karfe taran safiya rabi'a na falonta tana wa nabila wanka baba ibirahim yayi sallama rabi na ganin mutuncin dattajon sosai da girmansa saboda yana tausaya mata da kaunarta, ta lullube jinta da mayafi ta leko rumgume da nabila ya amshe ta........ Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Launin Fata 2-03 Posted by ANaM Dorayi on 07:08 PM, 22-Oct-15 Under: Launin Fata Ya rungume, Rabi rabi ta durkusa har kasa ta gaidashi ya amsa. Yace rabi'a yau Allah ya amsa adu'ar mu ina zaune da safiyar nan wani matashi yazo yace mini sun hadu da tahir can wanigari cikin mali ya bashi takarda yace a kawo miki ina ganin ta gaisuwace dan muna yace a gaidamu yana nan tafe. Shiyasa nace ba zan baiwa kowa ya kawo miki da kaina zan kawota in miki wannan albishi da kaina. Hannun rabi'a narawa gabanta na faduwa ta amshi takardar da hannu bib biyu tayiwa baba ibrahim godiya mai yawa, yace ba ko mai rabi Allah yayi maki albarka. Ya mika mata nabila ya juya tana rawan jiki ta yage ambulan abun da tagani anrubuta ne yasa ta yanke jiki ta fadi kasa maga shiyan. Ga abin da takardar ta kunsa. BAYAN SALAMA IRIN TA ADDININ MUSULINCI, DAGA MIJINKI TAHIR ZUWAGA MATATA RABI'A NA BARKI GIDA CIKIN KUNCI GA TAFIYA TA TSAWAITA INA GUDUN CUTAR DA RAYUWARKI A MATSAYINKI NA KARAMAR YARINYA DAN HAKA NA YANKE IGIYAR AURENA DAYA DAKE NA BAKI DAMA IN KIN SAMI MIJI KIYI AURE. Rufe idon da rabi tayi adu'a take Allah ya karbi rayuwarta ta huta da wanan tashin hankalin da take ciki tajima kwance dif nabila nata bugun kirjinta tana cewa ma ma ma. Da yake ta dan fara iya magana a lokacin watanninta bakwai da haihuwa. Zuwa can ta mike ta kara karanta takardar ta nemi hawaye a idonta ta rasa sai dai kanta dake sarawa kamar zai fashe, idanunta sunyi jawur zuciyarta na faman turiri. Ta dunga karanta adu'ar. Allahumma ajirni fiy masibatiy wa akh lufniy khairan minha. Ta daga hannuwanta biyu sama tace Allah na tuba kayafe mini, Allah banyi bakin ciki da duk abin da ka kaddara zai saman ba dan na kasance butulu gareka da baiwar salihin miji na gari wanda yake tsoronka sai dan zuciyata bata da karfin kan duk abinda ya shafe shi, bani da juriyar da zan iya shanye damuwar rabuwa da mijina ban zubar da hawaye ba. Da bazanyi kuka ba saboda nasan Allah ne ya azurtani dashi alokacin da basanshi ba. Allah na gode maka Allah kasa haka shi yafi zama alkhairi garayuwata. Ta mike tayo alwala tayi sallah raka'a 2 alokacin karfe goma dai dai na safiya ta bude alkur'ani mai girma ta dinga rero kira'a cikin suratul bakara. Sai alokacin hawaye ya dinga zubo mata idan tayi kamar tayi shuru in ta kalli nabila sai zuciyarta ta kara karaya, tausayin yarinyar ya kara kamata hankalinta ya tashi ta kamota ta rumgume ta ce wanan yarinya kin shigo duniya cikin garari bansan yadda rayuwarki zata kasance ba, nan gidan ba a kaunarmu gidan mu mahaifina baya kaunar babanki nasan ba zai bari ki zauna a gidanshi ba. Nan kuma ba zaki rayu cikin farinciki ba, amma akwai Allah yana sane damu shi yasan yanda zaiyi damu.Su dije da danladi suka zuba ido kwana daya biyu uku har saty basu ga rabi'a ta kwashe kayan ta ta bar gidan ba, kuma bata nuna wata damuwa ba a fuskarta, ta ci gaba da ayyukanta na yau da kullum yadda ta saba. Ranar da saty biyun ta cika har daki dije ta isketa da yamma tace wai ke wace irin bakar mayya ce? Mijin nan naki ya gaji da tsotseshin da kike yi ya gudu ya barki baki tafi gidanku ba, ya aiko maki da takarda nanma dan naci baki tafi ba sai yaushe? Tace zan tafi ne umma sai nagama idda. Taja tsaki ta fice tana fadin aikin banza mayya kawai. Lokacin ne rabi ta fara sabon tunani akan takardar da aka kawo mata ta saki daga mijinta masoyi nagaskiya tahir. Shi kansa babfa ibrahim lullube mai maganar akayi, baisan abin da maganar ta kunsa ba, ya yadda ya kawo wa rabi yana murna anfara samun lbr tahir haka yake tsanman gaskiyar lamarin harcikin xuciyarsa. Sai da maganar ta yadu a cikin gidan kunya ta ishesa yaxo har dakin rabi yana hawaye da idonsa yace nayi bakin ciki ace nine na kawo takarda da hannuna. Itama ta kama kuka tace dan Allah kayi hakuri kadaina kuka baffa aure rai gareshi zaman lfy da soyaya basa mutuwar aure idan wa'adinsa ya cika haka rashin zaman lfy da kiyaya basa kashe aure idan lokacinsa bayyi ba. Rabi'a ta mike ta dauko takardar wadda ta adana can kasan kayanta tasake karantawa tana nazarin rubutun duk da cewa zuciyarta na tsananin yi mats kunci. Rubutm kam yana mata kama da na mijinta ta mayar ta ninke takarda. Ta kwanta tana tunani watarana da tahir yasameta a kicin tana girki da tsakiyar rana ya dawo daga makaranta yace gimbiyata me ake dafa mana gaba daya unguwa ta kama da kamshi haka. Tace ah ni fa bani son zolaya. Yace karkiyi zaton haka zolaya nake sauri ki zubo mini yawu na sai tsinkewa yake. Suna cin abinci suna fira yace mata Rabi'a anya macen da ta kware a girki mijinta zai iya fushi da ita. Ta tun tsire da dariya tace in nace santy kake yi fushi me zai hana in tayi laifi yayi fushi kuwa? Yace kai koyayi sai ya huce kuma ina tabbatar maki iya girki gamace yana ja mata wata daraja ta musamman a gun mijinta yana kara dankon soyaya tsananin mace da mijinta yana kara kankame igiyar auransu. Tace gaskiya santi kake. Yace idan ma santy nayi banyi laifi ba Rabi'atu kin cancanci ayi santi a kanki ta kowanne fanni, dukkan mutun 9 yake bai cika goma ba, amma ke din nan banga ta inda kika raga ba, igiyoyin aure da ana daura goma ko dari zan daurata a tsakanin nida ke bama ukun ba. Auran mu da ni dake mutu karaba takalmin kaza.. Mutu karaba takalmin kaza. Kalmar da ta maimaitawa kenan to amma me yakawo takardar saki? Kaddara mana. Ta ba kanta amsa. watanni ukun da shari'a ta aje a matsayin idda suka cika Rabi'a na dakinta a lokacin watannin nabila goma da haihuwa. Tana cikin tsananin fitina da zalamar mahmud a lokacin ne ta yanke shawarar komawa gidansu duk abinda Abbanta zai mata ya mata idan ta ci gaba da zama a gidan mahmud zai yi galaba a kanta wataran kuma ma meye amfanin zaman natan?Rabi'a tayi ajiyar zuciya ta tashi tayo alwala ta dau alkur'ani mai tsarki tafara karatun suratul an'am, batasan taci gaba da kuka dan kuka bai da an fani a gareta ba zai mata magani matsalartar da take fuskanta ba a rayuwarta....... A falo Rufai tausayin yar labubuwar yarinyar nan Nabila ya cikashi shi kansa ya rasa abinda zai yi yarinya yar wata goma a rabata uwarta, yatsaya cak kowa ya kasa magana ko nura duk yanda yake bin ra'ayin abbansu sai da ransa ya baci kan wanan rashin tausayin da ya nunawa diyar rabi'a. (KAR KU MANTA AN KOMA KAN ZARAN LABARIN DA MUKA BARI TUN FARKO). Ummi tace rufa'i katafi ka kaita in abbanku ya dawo baka kaitaba wata sabuwar fitinarce ba barinta zaiyi gidan nan ba. Bashar yace to dolene Rabin sai ta zauna a gidan nan. Gidan wa zata zauna in bata zauna a nan ba, zata cigaba da rayuwa cikin fushin mahaifinta ne saboda yarta? Hakuri xatayi Allah ne yasan yanda zaiyi da rayuwar yar. Fatima tamike ta amshi nabila ta rumgume har yanzu bacci take ta dauki kayanta dake cikin laida poly bag tace muje mu kaita yaya. Bai ce ko mai ba ya wuce suka shiga mota zuwa gidan su tahir. Baffa ibrahim suka samu a kofar gidan suna fira suka gaisa Rufa'i ya gabatar da abinda ke tafe dasu duk son zuciyar danladi sai da yaga wautar mahaifin rabi'a ya sa hannu ya amshi nabila daga hannun fatima yace kace mun gode zamu rike ta in sha Allahu. Baffa ibrahim bakin cikine yasa ma yarasa abinda ma zaice har su rufa'i suka wuce baice komai ba. Sai mahmud ne yace zan rike yarinyar nan baffa. Baffa ya girgida kai yana kallon nabila wadda ta kwanta lamo jikin mahmud kamar tasan abinda ke faruwa a kanta yace ba ruko ne masalar ba kasan halin matan nan gidan nan. Yace ba komai baffa tunda sukayi haka insha Allahu wannan yarinya tana cikin kulawata da amanata. Baffa yace Allah ya tayaka riko Allah yayi ma jagoranci kan kyakyawan aniyarka. Ya shige gida rungume da nabila da kayanta ba kowa a tsakar gidan matar tasama bata nan ya zauna a daki ya dauko alawa ya dinga lasa mata a baki zuciyar mahmud ta karaya tausayin yarinyar ya dameshi da yawa. Ya tuna sandasuka sa aka rubuta ta kardar saki akan baiwar Allah rabi'a dan kawai ynason ya aureta lokaci daya zuciyarsa ta sauya gumi ya dinga keto masa ya fara tunanin meye makomarsa kan wanan lamarin da ya aikata? BAYAN SHEKARA GOMA SHA BIYAR. Yadda Allah yaso haka rayuwa ke tafiya maka haka mutane keso ko akasin haka. Abubuwan da suka auku cikin shekaru goma shabiyar suna cike da tarihin Rabi'a da diyarta nabila da mahaifin nabila wato tahir. Watanni shida bayan kai nabila gidansu tahir lokaci guda abban rabi'a ya gudiri niyar komawa garinsu yamen da xama sakamakon wata gagarumar harka da ta fado hannunsa daga manyan masu fada aji a kasar tasu, lokacin da ta tara iyalansu ya saida musu bako zaiyi halinsa, kowane ya girgiza amma ba kamar Rabi'a wadda kukan da take na rabuwa da yarta ne. Nan tasan muddin suka koma yemen da zama sunyi bankwana da yarta da mijinta wadda har wannan lokacin bata fidda ran rabuwarsu ba tunda komi na Allah ne tun lokacin da aka rabata da nabila watanni shida da suka shude ta tsananta da adu'ar Allah ya bata hakuri da juriyar kan jarabawar da yayi mata. Cikin ikon Allah tana samun saukin damuwarta kuma tundaga wanan lokacin ne suka shirya sosai da abbanta kusan yanzu yafi nuna kulawarsa akanta fiye da kowane dansa. Yayin da ita bata damu da hakan ba har abada tasan ba zata daina ganin bakinsa ba akan bakincikin da ya kullawa rayuwarta. Daga baya ma tunanin da ya dinga shiga zucuyarta shine anya ba damuwa ce tasa tahir ya bar gida ya buya awani gurin ba. Kuma ba kowane ya haddasa musu wannan damuwar ba sai mahaifinta wanda yanuna ma tahir zahirin kiyaya ko kunya baiji. Bayan an gama shrye shiryen barin kano ana yagobe zasu tashi ajirgi zuwa yemen tana zaune a dakin ummi ta fahimci kukan da take, ummi tace kiyi hakuri Rabi'a kije kiga nabila tafiya ba mutuwa ba ce komawar mu yemen bashine rabuwar mu da nabila har har abada ba. Cikin kukan tace nabila ba ina gudun yanayin da zan ganta a ciki, hankalina zai dada tashi ne fiye da yan zu na hakura da nabila na san mun rabu kenan Allah ne ya kaddara auranmu da tahir dan in haifi nabila na gode masa. Ta mike tafice tashiga cikin dakinsu ta kwanta fatyma tashigo tace anty in baki so kitafi ki bar nabila a kano me zai hana kiyi zamanki a kano? In zauna a kano gidan wa? Hakuri in biku yemen shi yafiye min alkairi, haduwa ta nabila na san yadda Allah yayi. Washegari da sassafe suka bar kano da zazzabi mai zafi a jikin rabi wani abin ta kaici har da abba a lallashinta kamar bashi ne ya ja mata duk wata damuwa da take ciki ba. Suka bar kano nabila na hannun inna mahaifiyar mahmud babu abin da ta nema ta rasa duk abin da takeso mahmud ke mata sai ya zamo kamar mahaifinta ba ya yarda kowa ya taba ta a gidan, saboda tsoron matarsa babu mai taba ta mutanen gidan har mamakin son da mahmud ke ma nabila suke. Lokaci guda mahmud ya maida kansa dan kirki ya daina tunanin auran Rabi'a balantana sha'awarta da aikata fasikanci. Lokacin da damuwarsa kan abin da ya aikata ya dameshi sai ya yanke shawarar yaje gidansu Rabi'a ya roki gafarta ya bayyana mata gaskiyar lamari cewa wannan takarda fa ba tahir ne ya aiko da ita ba. Yana zuwa gidan ya iske mumunan labari cewa su rabi'a sunyi kaura sun koma kasar mahaifinsu ta haihuwa wato yemen. Makocinsu aminin abba ne wanda aka daura auran rabi'a a gabansa yayi wa mahmud wannan bayanin lokacin da yaje gidan. Tunda mahmud ya sunkuyar da kai zuface kawai ke tsatsafo mai yana tunanin inda zaiga rabi'a ya sauke nauyin hakkin da ya dauka, sai da alhaji garba ya gama bayani kana ya dago kai ya tambaye shi ko yasan inda suke a yemen din? Ya jin jina kai yace wlh ban taba zuwa kasar yemen ba sai dai yayi min kwatancen garinsu da unguwarsu kuma ina da number wayarsa, nanda karshen shekara zani in kana bukatar zuwa sai muje. Mahmud ya dawo gida cikin ma tsananciyar damuwa tun tuni gidansu a ke tsegumin cewa makauniyar soyayar da ta kama tahir ta kama mahmud tunda gashi ta bar gidan amma gaba daya ya rasa sukuni sai ramewa yake yana fama da tunani gaba daya yanayinsa ya sauya. Ya dauko yarta ya manta a zuciyarsa babu dan gata duk fadin gidan agunsa sai ita, yayansa ma 2 gasu nan bai damu da su ba yanda ya damu da yar Rabi'a wato nabila, lubabatu matarsa tayi masifar tayi bala'in har sakinta yayi akan maganar nabila ta tsani nabila yadda ta tsani mutuwarta amma ina mahmud yafi karfinta babu yadda ta iya dashi. Dole ta hakura ta dawo ta zauna ta hadiye kin da takewa nabila dan in har yana gida to yana manne da nabila itama tasaba dashi bata iya bacci sai a jikinsa, kullun da safe in zai fita da wayo suke rabuwa shi ke mata komai in bai nan kuma tana hannun innarsa. Itama tana son yarinyar tana yi mata gata, nabila ta zamo yar gata fiye da kowane yaro a gidan nan a gidan ba bu wanda ya taba zaton faruwarsa. Dama haka sha'anin ubangiji yake shi ke jujjuya lamuransa yadda yaso a lokacin da ya so, yawan kudin da aka kiyasta masa zai kashe yayin tafiya yemen bai firgitashi ta fasa zuwa ba.Yayi alkawarin zaije ko da zai dawo baya da ko kwandala sai dai ya neme gafarar rabi'a kan abin da yayi mata. Mafarkan da yake yi da ita suna dada firgita shi har kuka yake wani lokacin lamarin dake kara tada hankalin matarsa kullum gidansu surutun kenan Rabi'a mayya ce ta lashe mahmud kullun yana tunaninta yana son yarta fiye da kowa. Sai dai yana jinsu yana ta shirin tafiya yemen kawai sai anawata sai ga watagaf da shekarar da zata kare yaje ya tambayi Alhaji garba batun tafiya ya tarar Allah yayi masa rasuwa, a dalilin hadarin mota da ya rutsa dashi a kan hanyar dutse zuwa kano kuma shima ta aziya yaje suna dawowa matarsu ta fadi sai gawarsu aka kawo gida. Alokacin da aka korowa mahmud wanan bayani zubewa yayi a gun yayi zaman dirshan ya daga hannunsa sama yace ya Allah dukan dan adam ajizi ne mai kuskure nasan ina aikata kuskure a rayuwata na gano kuskure na na nemi hanyar da zannemibaiwarka Rabi in roketa gafara ban samu ba Allah ka yafe mini ka kaddara saduwar mu in nemi gafararta. A takaice nabila bata taso cikin maraicin iyaye ta sha wahala amma gatan da mahmud ke nuna mata yafi gaban a bayyana, mahassada na ci gaba da hassadar su hassada naci gaba da zama taki ga mai rabo. Har wanan lokacin ba a samu labarin tahir ba shekaru goma sha biyar kenan...... Zaharaddeen shomar Whatsapp 08168575100 Launin Fata 2-04 Posted by ANaM Dorayi on 07:05 PM, 22-Oct-15 Under: Launin Fata Da bacewarsa yayin da har wanan lokacin mahmud bai daina fatan

Chapter 8 of 12