Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya danna kofar ya bita ciki ya maida kofar ya rufe. Rabi'a ta ce a uzubillahi minashaidanir rajim. Muhamd ya kyalkyale da dariya ya ce yarinya yau kin zo hannuna tunda kika zo gidan nan nake fama da muguwar sha'awar ki a zuciyata. Wannan fitinannan mijin naki ya kasa ya tsare to yau dai baya nan ko ki yarda in biya bukatata dake ko in miki sharrin da ba za ki iya fita ba ta hanyar cewa ke kika kasie hajiya yaya. . . . . . . Allahamdu lillah Allah ya bani ikon kammala littafi na farko sai kuma Allah ya hadamu a littafi na 2 kukasance dani danjin yanda zata kaya Zaharaddeen Shoma Whatsapp 08168575100 LAUNIN FATA Kashi na biyu 2 Rabi'atu Abubakar Nasidi Creat by:- Shuraih 99% @http://fb.com/hausaebooks Launin Fata 2-01 Posted by ANaM Dorayi on 11:20 AM, 20-Oct-15 Under: Launin Fata Kan Rabi'a na kasa gabanta na faduwa kamar zai tsage ya fito tana jin dariyar da muhmd ke kyalkyalawa yana fadin ko dai ki bani hadin kai ko in kulla miki sharrin da ba zaki iya fita ba. Muryarta na rawa ta ce ka ji tsoron Allah ka tuna ranar da zaka hadu da shi, ni matar dan uwanka ne bai dace ka nemi yin alfasha da ni ba. . . Ya ce ke kin san kuwa kyakkyawar surar da kike da ita? Ko mutum bai niyyar kallanki ba sai ya kalle kin sha'awarki ta dade tana wahalar da ni ba zan iya hakuri da ke ba. Na baki minti 2 ina zuwa ki yi tunani bance dole sai kin yarda ba amma abin da zai biyo bayan rashin yardar taki ba zai miki dadi ba. A hankali ya sulale ya fice daga dakin yayin da Rabi'a ta sulale itama ta zauna ta kama kai da hannu 2 2 tana fadin innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wace irin rayuwa na fado haka? Tunanin abinda ya faru rana ita yau makamancin na jiya ya fado mata. Fitowa tayi daga daki ta tsuguna gaban tahir ta ce me zan fada maka mai gida? Kan ya yi magana sai ga Dije ta daga labulan ko sallama babu ta tsaya a kansu ta ce to munafuka uwar kinibibi me bin miji da rana ko kizo hura wutar tuwo. Tahir ya manna mata harara ya ce bata zuwa. Da jin haka Ali dan dije ya ruga daki gayawa kawu ga tahir can zagin innarsa dan ta ce Rabi'a tazo ta hura wuta. Haka shima kawun ya fado dakin yana huci kamar wani kumurci dije na ganinsa ta fashe da kuka ta ce yawwa gara da ka shigo malam ni na gaji da wulakancin da tahir yake wa kowa a gidan nan a kan matarsa. Kawu ya ce dama baka da mutunci ko tahir? Akan matarka kake zagar mini mata haka? Tahir ya ce nifa ba zaginta nayi ba kawu yarinyar nan ba lafiya gareta ba ya dace a dinga sata aikin da yafi karfinta, amana ce a guna dole ne in kare mutuncinta daga dukkan abinda zai cutar da rayuwarta .Kawu tanimu yace af nima zagin nawa za ka yi to zageni ko ka dakeni karewar zagi sannan ne nasan ka isa marar mutunci. Tahir ya zauna kan kujera bai kuma magana ba Dije da kawu suka kare mai cin mutunci tas a gaban yayansu yara da manyan kawu ya ce kuma tilas ne ya bar matarsa ta ci gaba da ayyukan gida kamar kowace mace dan ba fin matar kowa tayi a gidan ba har suka gama bala'insu suka fice tahir bai motsa ba sai hawaye ke zubo mai, Rabi'a na daki tana nata kukan tabbas zaman gidan yawa fitina ne, ta mike ta fito falo ta zauna kusa da tahir ta kamo hannunsa ta ce ka yi hakuri komi na Allah yana da iyaka watarana duk wanan lbr zai zama. Ya mike ya barta zaune dan bai son ta ci gaba da ganin hawayansa, dakin hajiya yaya ya shiga tana kwance kan gadonta na karfe tana fama da zazzabi ya zauna kan kujera ya yi tagumi ta mike zaune da kyar ta ce dan an yi ma fadan kan abinda kake kake yin kuka, shi kenan dai kai ba za a fadi gaskiya a kan matarka ba ya marairaice fuska ya ce don Allah hajiya kada ki goyi bayan wannan rashin gaskiya a hannunki na tashi a cikin gidan nan mutanan nan babu kiyayyar da basu nuna mini ba har Allah ya rayani ke ma kin san ba kaunata suke ba zasu ci gaba da yin duk abin da zasu yi ne dan ganin sun ga bayan zaman lafiyata da kwanciyar hankalina shi yasa. Shi yasa tun farko ban yi tunanin zama a gidan nan ba saboda na san abinda zai faru kenan. Batan fatan ki gaya mini wata maganan ya kasance ban yi aiki da ita ba shi yasa na zo na zauna. Duk wanda zai samu sausuce a gunsa a gidan nan bayanki zan bi, idan ban samu sa'ida ta bangaranki ba a gunwa zan samu? In har kin goyi bayan wulakancin da kawu da matarsa suka yi mini nasan kin yi haka ne dan kece kika haife shi ni kuwa maraya ne bani da uwa bani da uba bani da mai goya mini baya kan gaskiyata. Hankalin hajiya yaya ya tashi da jin kalaman bakin tahir, ta kama kuka ta ce tahir yau bakinka ke fadar wadannan kalaman marasa dadi gareni abinda baka taba yi ba. Ya ce hajiya gaskiya dama haka take bata taba yiwa wanda ake fadawa ita dadi ba ki yi hakuri ko da bake kika haifeni ba ke kika haifi mahaifina. Shima ya kifa kai a kujera ya shiga kuka, hajiya ta ce ka yi hakuri tahir nima na san ba a kyauta maka a gidan nan babu yadda zanyi da tanimu ne nuna yafi karfina shi da matarsa dije sune kan jagorancin duk wani rashin gaskiya da son zuciya da ake yi a gidan nan. Ya mike ya fice a ranar bakin ciki bai bar shi ya ci abinci ba, Rabi'a tayi lallashin ta gaji ta sa mai ido.Haka aka ci gaba da zaman ba dadi kullum cikin bacin rai, damuwar har tafi ga tahir ita Rabi'a tana dannewa saboda dai tasan babu inda zata kai karar halin da take ciki sai gurin Allah, ko ummi dake goyon bayan auranta da tahir bata sö gaya mata irin wannan matsalar dan bata son ita dinma ta tsani auran ta da tahir saukin da take samu ta bangaranta itama ta rasa. Haka take ta yiwa matan gidan nan biyayya kan jiki kan karfi amma basu gani sun hada kai kullum cikin neman abin da zasu mata wulakanci suke, wai dan kawai mijinta na sonta yana kula da ita. Duk abinda tayi bata yi daidai ba aikin tuwan dare kullum mutum biyu ke yi amma ita bata da ranar hutu kullum sai ta fita anyi aiki da ita in bta yi ba bala'i. Tahir yayi yayi ta daina fitowa tana aikin da yafi karfinta duk abinda zasu fada su yi ta fada ta ce ita dai yayi hahuri ya kyaleta zaman lafiya yafi zama dan sarki wata rana sai lbr. Sai da cikinta ya yi wata biyar ta samu saukin laulayi ta fara samun lafiya ta daina zuwa gidansu saboda kowa ya kalleta ya san bata cikin kwanciyar hankali, a dalilin ramewar da tayi, sai umminta ke zuwa lokaci lokaci duk sanda tazo da takaici take fita yadda rayuwar diyarta ta koma dan bata son nunawa Rabi damuwarta ne da tuni ta fahimtar da ita itama auran tahir ya fara fita daga ranta. Da kuma yawan tausayin da tahir din ke bata, ya gama kallafa rayuwarsa kan soyayyar Rabi'a rabasu ba karamin tashin hankali ba ne. Yau juma'a bayan an sakko daga masallaci tahir na kwance a falo yana kallon wani nigerian film, Rabi'a na waje tana fama da fitinar wuta wake da shinkafa take dafawa na sayarwar dije da take dora ma yayanta ita dijen zata unguwa ne da safe har da lekawa dakin Rabi'a ta ce Rabi zani unguwa hansai zata dora wake dan Allah ki tayata ki dafa kafin in dawo.Ta ce adawo lfy. Ta gaji da fifita ice jikakke ne kanta har ciwo yake saboda hayaki ta dawo daki ta dauki wata roba tata ta fasa taje ta danna a wuta ta kama ta dawo ta kwanta tana nishi tausayi mai tsanani ya kama tahir ya mike yaje gabanta ya tsuguna ya ce wlh rabi'a ina matukar tausayawa halin da kike ciki a gidan nan, dole ne in nema mana mafita zaman gidan nan ba zan ci gaba da ganinki cikin wahala da damuwa haka ba. Ta ce ka daina damuwa da yawa na sha gaya maka cewa ni ina daukar rayuwa ne yadda ta zo mini. Komi lokaci gare shi, ba 9an ce maka ba ni damuwa da halin da nake ciki a gidan nan ba yes na damu amma na san akwai ranar da zai zama tarihi, idan mutum ya daga hankalinsa kan abin da lokacin yankewarsa bai yi ba wahala kawai zan sha a banza. Tahir ya girgiza kai ya ce kai Rabi'a samun mace irinki sai an tona, na gode Allah da ya bani ke da ace haka sauran mata suke kasancewa masu tattalin mazajansu da ba a samu matsaloli a gidajan aure ba. Ta yi murmushi ta ce kai ma haka abin yake gareka maza da yawa da sun kasance masu halayyarka da mata da yawa ba su dinga kuka da mazajansu ba. Ya ce Rabi na sha gaya miki ba zan gaji kuma da gaya miki ba cewar ina sonki son da da ban taba yiwa wani mahaluki ba ina bakin cikin abinda zai rabani dake ko na rana daya ne. Ina kishin in mutu ki auri wani ni kadai na san ni'ima da gamsuwar da nake samu a tare da ke ta bata rai ta ce kai sai ana magana mai dadi ka dinga sako maganar mutuwa, insha Allahu za mu yi doguwar rayuwa. Ya ce Rayuwa kam ta Allah ce. . . . Dogon tunanin Rabi'a ya katse anna sai yanzu idanunta suka cika da kwalla tabbas ta fada cikin fitina babu mai fitar da ita sai Allah tana rokon Allah ya tsarer da ita daga sarrin dan ladi (muhamd kenan) yawancin mutanan gidan da dan ladi suke kiransa.A hankali ya turo kofar ya dawo dakin tana mamakin yadda yake iya shigowa gida irin wannan cike da mutane ba a ganin shiwarsa ne ko kuwa ana kallonsa son zuciya ne ya sa aka kyaleshi, an san dai ba dakin matarsa ba ne kuma yana da mata a gidan me zai kaishi dakinta alhali mijinta baya nan. Ya tsaya a gabanta ya ce na baki dogon lokaci da ya isa ki yi tunanin duk da za ki yi nazo jin amsa. Ta durkusa a gabansa ta ce ka ji tsoron Allah, ka sani dan mijina baya nan Allah yana nan kuma yana kallonka ni matar aure ce duk abin da kayi da ni sai anyi da matarka. Ya buga mata tsawa ya ce ke dakata ni zaki yiwa wa'azi. Ya kai hannu da karfi ya damumi wuyanta tana fadin innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Kamar daga sama sai suka ji muryar kawu yana fadin danladi. Da sauri ya saketa kafin ya fita kawu ya shigo falon ya ce kai lafiya? Tahir din ya dawo ne? Mahmud da ce bai dawo ba nima shigowa nayi in tambayeta ko ya dawo ta ce bai dawo ba. Kawu ya ce to kuma zaman me kayi tun dazu fa naga shigowarka dakin. Ya jinjina kai muje waje in baka lbr da zai baka mamaki kawun ko da yaushe takamar tahir matarsa shi bai san wace irin mace yake zaune da ita ba. Zaunn fa ake jugum jugum a gidan ana jimamin mutuwar hajiya yaya amma kawu tanimu kamar ba mahaifiyarshi ta rasu ba, yana can gun danladi suna kulle kullen sharrin su a kan baiwar Allah Rabi'a zafi 2 ne ya haduwa Rbi'a a wannan dare koma 3 ga dai tashin hakali bacewar mijinta ga mutuwar hajiya yaya wadda a gunta kadai take samun sauki a gidan ga wata sabuwar fitinar da muhamd ya bullo mata da ita. Ta kasa zaune ta kasa tsaye duk iya kwarewa da sata irin na barci a wannan rana hakuri yayi ya tafi ba tare da ya sace Rabi'a ba dan bata runtsa ba har gari ya waye. Bayan ta idar da sallar asuba ta fito sanye da hijabinta zuwa dakin hajiya yaya inda matan gidan suke zaune ana shirye shiryen jana'izar hajiya yaya gaba dayansu kallon banza suke mata kadan ne suka amsa gaisuwarta, tun a daran jiya dije da ladidi sun yada cewa Rabi'a mayya ce ta lashe hajiya yaya. Wasu daga cikinsu suka fara cewa mu ma idan ba mu bi a hankali ba sai ta lashe mu mu da yayan mu idan muka ba hali sai mu bar mata gidan.Duk da mutuwar ba a fasa wannan gutsiri tsoma ba a cikin gidan, lamarin da ya sa zaman gidan ya dinga yiwa Rabi tsanani, da kunci dama dai tana sumun sauki ne idan an kuntata mata zata kalli mijinta mai sonta da tausayinta ta ji sanyi a ranta ta maida komi ba komai ba to gashi yanzu babu shi babu mai lallashinta, mutanan gidan basu kaunarta ba tare da ta yi musu komi ba masu kaunarta dinma tsoron kawu tanimu da dije ba zai bari su jata a jiki ba. Bayan an kai hajiya yaya an rufe ta dawo daki ta kwanta tana hawaye ta dauko waya ta kira umminta ta sanar mata mutuwar hajiya yaya da bacewar tahir tun safiyar yau. Ummi ta ce to ki yi shuru ki daina kuka zan zo an jima. Ta tsara Abba da cewa zata dubo kawarta a asbiti, fatima ta nace zata rakata bashir ya tukosu a mota da yake yazo gida hutu. Daga bashir har fatima babu wanda ya taba zuwa gidan tunda rabi ta zo ummi ce kadai ke zuwa itama daga baya ta daina zuwan saboda bata jin dadin yanayi da take iske diyar ta in tazo. Basìr ya yi parking a nesa da gidan kadan ya dubi ummi lokacin da take fita daga motar ya ce yanzu wannan ne gidan da Rabi'a take? Ta tsuke fuska ta ce to menene ba rayuwa ba ce. Fatima ta tabe baki ta ce auran soyayya kenan ya yi amfani. Ummi ta ce kwarai kuwa yayi amfani dan tana cikin kwanciyar hankali da mijinta. Suka yi ta'aziya ga mazan dake zaune a kofar gida tana cikin . Suka yi ta'aziya ga mazan dake zaune a kofar gida ana zaman makoki suka shigo cikin gidan wadda ke cike da mata wasu sunyi jugum jugum wasu kuwa hirasu suke.Rabi'a tana daki ita kadai jin sallamarsu ta fito ta fito ta rakasu daki daki suka yi gaisuwa sai wani irin kallo ake musu sun haska gidan gaba daya, lokaci guda kamshin jikinsu ya cika gidan suka dawo dakin Rabi'a tana kokarin danne damuwarta amma ina kallo daya kayi mata zaka shaida muguwar damuwar da ke damunta. Fatima ta ce anti Rabi dan Allah tunda tahir baya nan gashi mutanan gidan nan ba kaunarki suke ba ki dawo gida ki yi zamanki ki haihu ka da ki zo haihuwa su illataki. Ta girgiza kai ta ce fatima aure na da tahir bai zamo auran nadama ba a guna, har yau babu namijin da nake so sai mijina tahir soyayyar da nake masa yanzu ta ninka wadda kika san ina yi masa kafin mu yi aure. Babu wata wahala da zata sa in gudu in bar ladana, wannan wahalar insha Allahu dadi ce a gaba dan ance bayan wuya sai dadi. Ina so ku ci gaba da tayani addu'a Allah ya bayyana mini tahir, ba zan iya barin dakina da nake da yanci in tafi in da bani da yanci ba. Ummi ta ce kina da gaskiya Rabi'a insha Allahu tahir zai dawo ku ci gaba da kyakkyawan zamanku. Bashir dai tagumi yayi ya kasa cewa komi. Har aka share makikin hajiya yaya tahir bai dawo ba kana danladi bai daina yiwa Rabi'a barazanar ko ta yarda da shi ko kuma ya shirya mata sharrin da ba zata iya fita ba. Yau da ya lallabo ya shigo dakin tsakiyar dare dama ba wani barci take ba tana zaune kan abin salla ta idar da nafilfilnta tana adu'o'i ya zuba mata harara ya ce ke in dai fa kina cikin gidan nan sai na cimma bukata a kanki. Ta yarfa mai itama hararar ta ce to wai waye ya hanaka yin abin da kake so? Na sai dai tunda kai baka jin tsoron Allah ka iya fyade? Kuma kasan ba fin karfinka zanyi ba, mene ne na zama neman yarda ta? Ba sai ka yi min fyade ba. Haka kika ce ko? Ta ce eh haka na ce. Ya kyalkyale da dariya ya ce yaro dai yaro ne tabbas kuma na iya fyade yau za ki ga fyade yau zaki gane kuranki tausayinki nake ji shi yasa nake lallabaki. Ta ce karya kake kace kana jin tausayina. Babu rashin tausayi da yafi abinda kake nuna mini ka ki ka barni inji da bakin cikin bacewar mijina babu wanda ya damu a cikinku saboda ba kaunarsa kuke ba. Kullum sai ka zo ka daga mini hankali to ka sani ban hanaka aikata abinda ka so da ni ba sai dai wlh ba zan yi kaffarar wannan rantsuwa ba in har ka isa gareni ka keta mini mutuncina sai na luma maka wuka a ciki, sharrin da kace zaka yi mini na kashe hajiya yaya kisan ya tabbata a kanka in yaso nima a kasheni. Abin mamaki sai taga jikinsa ya yi sanyi baice da ita komi ba ya juya ya bar dakin. Ta fada kan gado ta runtse ido tana mai godiya ga Allah da ya bata karfin halin da ta yi maganin iskancinsa. Duk abinda take fada karfin hali ne da karfin adu'ar da take ba abin da zata iya. Tabbas in banda karfin addu'a da tuni danladi ya samu kaiwa gareta a yadda yake nuna zalamarsa karara a kanta ko kunyar mutannan gidan baya ji su kuma da yake munafukai ne ana jin tsoronsa babu wanda ya tba magana akan haka sai abinda bai dace a yi magana a kansa ba sai suka iya. Tun da aka gama zaman makokin hajiya yaya aka sake sabon babin yiwa Rabi'a wukanci a gidan ganin ba idon tahir dama dai dije da ladidi na raga mata ne saboda shi tun tasowar tahir a gidan duk abinda na ke masa yana kauda kansa a kan Rabi ne kawai bai da hakuri. Ita kuma ta kudiri niyyar babu inda zataje tana nan tana adu'ar duk inda mijinta ya shiga Allah ya dawo mata da shi su ci gaba da zaman soyayyarsu. Duk bacin ran da take sha a gidan dai dai da rana daya tahir bai taba fita daga ranta ba, kullum ta zo kwanciya barci sai ta yi kukan rashin sa a kusa. Sai ta tuna wani abu wanda ta yi ya tsaye mata a rai na faranta wa a iya zamansu da tahir ba za ta iya fadar wani lokaci da wanda ya bata mata rai da gangan ba. Sai dai cikin rashin sani da sabani na zaman yau da gobe, wanda soyayya komi karfinta ba ta iya maganinsa. Ko ta yini da karfin hali in dare yayi sai ta yi kukan zuciyarta na son tahir saboda kyawawan dabi'unsa da hakurinsa da soyayyar da yake mata da uwa uba addini. Ta daukarwa kanta alkawarin ba zata nuna gazawarta a gun abbanta ba ya samu abin yi mata dariya, ummi ta aiko mata da kudi masu yawa da kayan abinci a boye ta ce duk abinda take so tayo mata waya. Itama ba ta son Abban ya gane karayarta ta gargadi fatima da bashir..... Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Launin Fata 2-02 Posted by ANaM Dorayi on 11:21 AM, 20-Oct-15 Under: Launin Fata Kada wanda ya gayawa abban bacewar tahir. Dan haka Abba bai san abinda ake yi ba, tun tana bakin cikin abinda ake mata a gidan nasu har ta fara sabawa matsalarsu ta daina damunta, aiki ne in an sa ta wanda ta ga zata iya tayi wanda ba zata iya ba sai ta shige dakinta ta kullo, Dije tayi masifar ta ta gama wanda taji ta ji wanda ba ta ji ba oho. Abincin da take dafawa kansa ba ci take ba yadda ya kama ta ballantana nasu. Abinda ta fahinta shi ne suna so ta bar gidan, hakan ya bata kwarin gwiwar ci gaba da zama a gidan ko da yaushe haka za a yi tayi mata habaici da cin fuska iri iri bata taba tankawa wani ba. A haka har cikinta ya shiga watanni haihuwa a lokacin nan watannin tahir hudu da bacewa, duk abinda za a bukata ummi a kawo mata ta shaida mata da taji nakuda ta yo mata waya zata taho da nurse. Sai da ta shafe wata na goma kana a wata safiyar juma'a ta tashi da ciwon haihuwa. Tun tana karama Rabi tana da dauriyar ciwo, haka ta yini ita daya a daki tana fama sai daf da la'asar ta kira umminta awaya ta gaya mata halin da take ciki. A kai rashi sa'a Abba yana gida ta ce zata je gaida kawar babarta ya ce sai dai gobe yau yana da baki baya son su zo basa nan, hankalin ummi ya tashi ta san ba yadda za a yi abba ya bari taje gun Rabi'a in ta gaya mai gaskiyar lamarin, ta kira fatima ta gaya mata ta ce to ummi duk ba ita ta jawo kanta ba.Ta ja tsaki ta mike ta rasa a bin yi ta kira Rabi'a Rabi'a ta kasa daga waya saboda tana cikin mawuyacin hali ga haihuwa shima. Ta gaji taje ta samu Abba a falo ta fito ta gaya mai gaskiya. Ya mike zaune ya galla mata harara ya ce amma ke baki da da tunani yarinyar da ta nuna mijinta ya fimu ita zan bawa wani taimako a gidana. Ummi ta marairaice murya ta ce Abba Rabi'a bata nuna mijinta ya fimu ba ka yi hakuri ka barni in je. Ya ce to ina mijin nata ta kasa magana ya ce to ba inda zaki je. Ya mike ya ficewarsa ya bar ummi kamar ta hadiyi zuciya dan takaici sai tayi alwala ta yi sallah la'asar tana adu'a Allah ya sauki yarta lafiya ta ce ko naje ko banje ba babu abin da zai sauya.Rabi'a na daki ita kaidai duk da mawuyacin halin da take ciki bakinta bai daina furta salati ba, karfe 5 na yamma ta haifo santaleliyar diyarta mai kama da tahir sak har fatar. Ga dai Rabi'a fara kal amma yarta baka sai dai hasken fuska irin na jarirai, da yar da mahaifar haka suka fado gaba dayan Rabi'a ta godewa Allah jikinta sai rawa yake bata san yanda ake komi na haihuwa c ga ya na kwance a tayal tana ta tsala ihu. A tsakar gida su dije na zaune a na ta shewa hansai ta ce kai ku dakata ni fa kukan jariri nake ji. Ladidi a ce kar dai waccan munafukar yar ce ta haihu. Dije ta ce anya kuwa zata iya haihuwa ita kadai haihuwar fari saratu ta ce tabdijan Rabin mugun abin da ke cikinta yayi yawa sai ta haihu mana. Bata gama rufe baki c suka ga rabi'a ta fito daga daki duk jikinta jini ta iso gabansu ta ce dan Allah ku taimaka mini ana haihu. Dije ta yi mata wani matsayacin kallo ta ce aikin banza sai yanzu kika san da neman taimakon namu? Saratu ta ce to yaya za mu yi dole a yankewa ya cibiya dan kar a samu a bakin duniya. Dije ta ce tabdijan sai kije ki yanke ni dai ba ruwana tunda ta iya haihuwa da kanta har yanke cibiyar ma sai ta yi. Saratu ta jima tana tausayin Rabi'a bala'in dije take gudu, ita da hadiza suka shiga dakin Rabi'a suka yi mata duk abin da ya da ce.Har kwana bakwai ta cika abba bai bar su ummi sun zo ganin Rabi'a ba ran ummi gaba daya ya gama baci, hatta fatima na son ganin yar uwarta sai dai waya duk hakurin ummi sai da suka yi rigima da abba ta yi kuka mai yawan gaske shi kuwa ko a jikinsa ya ce ai tunda rabi'a ta auri bakin mutum talaka ba shiga lamarinta sai dai bai hanata zuwa gidansa ba amma shi da iyalansa ba zasu je inda take ba. A waya ummi suna magana da rabi'a tana kuka ta ce Rabi abbanku ya hanamu zuwa mu ganki ta ce subhanallahi shi ya kike kuku ummi? Ta ce to ya ba zanyi kuka ba rabi'atu ko a gidan da ake kaunarki kike zan so in ganki in ga lafiyarki da abinda kika haifa ballantana a gida irin wannan ko mutum shiga ya yi ya fita a wannan gida ya san ba a kaunarki, haihuwa ko ta nawa zaki yi kina bukatar kulawarmu ballantana haihuwar fari da baki san komi ba akai ba? Rabi'a ta ce dan Allah ummi ki daina kuka, wannan kukan naki shi zai tayar mini da hankali fiye da rashin zuwanku.tun da Allah ya saukeni lafiya Allah ya sa tausayina a zuciyar wata baiwar Allah a gidan nan sunanta saratu matar wan mahaifin tahir ce tana kula dani yanda ya dace. ummi tace Alhamdulillah dama haka sha'anin ubangiji yake, ki kara hakuri kan wnda kike yi insha Allahu alheri zai zame miki, Allah yana tare da masu hakuri kamar yada ya fada a cikin alkur'ani maigirm. bayansuyi salama rabi'a ta ajiye waya jikinta a sanyaye ta dauki bebi ta wanda ke cikin kayaan sanyi yana ta kamshin turare, hawaye ya dunga zuba a idon rabi tunda ta haihu sai yau tayi kukan bakincikin gorin da ake mata a gidan nan ya isheta, su dije sun sami nayi har waka ake mata atsakar gida wai bata da kowa tun da ta haihu ba wanda yaxo daga gidansu gidan nasu ma bakaunarta ake ba. maganar bata taba damunta ba sai yau takai idanunta ga yar bebin ta maikama da mahaifinta tahir sak, ta tuna wa tarana da tahir ya sameta kwance tana shan ice cream yace haba rabi'a yaya kina da ciki kike shan kayan sanyi?Saratu ta shigo tare da baffa ibrahim babban wan mahaifinsu tahir ta ajiye baby da sauri tasauko kasa ta gaida shi ya ce kiyi hakuri ki daina kuka yar nan insha Allahu Allah zai bayyanar da mijinki muna ta adu'a. Saratu ta miko mai yar yace akwai wani suna da tahir ya taba nuna miki yana sha'awar sawa idan ya haifi mace? Ta girgiza kai ya ce to ke kina da zabi? Nanma girgiza kai tayi. Ya ce

Chapter 7 of 12