Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sun wake ango da amarya yadda ya kamata har tsigar nabila yadinga tashi yadda suke manna sunanta da na mujahid suna fadin auran soyaya mai dadi a ranta take cewa kukuke ganin auran soyaya ne. Duk wannda yaje gun fatin ba wai tsabar kudin da ake kashewa bane yafi daukan hankalinsa illa dacewar ango da amarya wato idan ka kalli mazaunin ango da amarya ka kalli ango ka kalli amarya sai kaga kamar irin greeting cards dinnan na turawa wato kyaune da kyau suka hadu abin har ba'a magana, dole ne dan bakinciki ya rasa inda zaisa kansa da damuwa dan na gaba kan yayi gaba.Washegari asabar akayi dinner party ta tsakar daretsakanin angwaye da amare su kadai a nanne mujahid yasa mu gaiyyato yanmatanshi na holewa na nan kano da na mako a ka cashe, sai a wanan fatin akaga walwalarshi sosai, yadda yanmata ke manne ai ya dagawa amarya hankali ta dinga tambayar kanta menene na sawa zuciyarta kishin wanda bai damu da ita ba ne. Soyaya ke kawo kishi. Duk wani so kuwa tana yiwa mujahid indai akwaishi a duniya sai dai in babu da asuba party tashi ga barci a idon nabila ga damuwa da masifar kishi kamar zuciyarta ta fashe.da zasu dawo gida yana kwance a kan wata jibgegiyar jeep ta hadu yana ta dan ne dan nen a hadset dinsa nabila na zaune gefensa, amir ne zai ja motar abokinsu salman ne zaune kusa da amir din a gidan gaba har ya fada mota wata budurwar mujahid da suka zo tare da salman daga malesiya ta leko saitin mujahid ta juya baki cikin harshen larabci ta ce my dear za kazo din ko.Wani irrin kallo yayi mata yayi murmushi ya ce duk cikar wayanda suka halarci gun dinner din ba wacce tafiki daraja bakin dai da na gayyata kinyi kokari da kika zo dole ne inyi maki abinda zai faranta ranki kema,tayi dariya ta ce na gode duk da cewa auran da kayi zai takurawa rayuwarmu sosai amma ina taya ka murna auran kyakyawar yarinya da ta dace da kai sosai ka iya zabe. Yace ko? Tace karkayi shakkar hakan. Yace na gode sai mun hadu. Tace ok. Ta zagaya gun salman tace fito mutafi a motar zainab ba zan gane ba kasar. Yace shikenan amir na biyoku. Kai kawai ya gyada mai ya fice shi shi amir takaicin mujahid ne ya hanashi yin magana. Har salman suka gama yin magana da mujahid ya tafi bai ja motar ba, mujahid yace me kake jira ne amir nagaji da yawo so nake inje inyi bacci fa?Amir yace kaje kayi bacci ko kaje kayi wanka katafi gun karuwai? Mujahid yace to meye? Amir yaja tsaki ya fisgi mota da karfi suka bar gun suna tafe yana bambami, mujahid bai sake cewa komai ba, sai da suka zo kofar gidansu nabila ta bude kofa zata fita mujahid ya gallamata harara yace ke wa ya baki izinin fita? Amir yace bata bukatar neman izininka saboda baka bata fuskar da zatayi hakan ba, nabila wuce gidanki ki huta kinji ko? Tayi murmushi tace nagode amir Allah ya huta gajiya. Bayan fitarta mujahid ya tabe baki yace amir so kake karfi da yaji kasa yarinyar nan ta rainani ko. Amir yace bani nake son in sa ta raina ka ba kaine zakasa ta rainaka daga lokacin da ta gaji da cin kashin da kake mata. To wai me nake mata amir? Ya galla masa hararayace haka ake mu'amala da macen da za'a aura? Dan kana shawa karuwarka kamshi suna binka kamar jela itama haka ya dace kayi mata? Sanin kankane ita tana da banbanci da karuwa ya dace ka lura da haka ka dinga tausasa mata banaso kasa ta tsaneka dan kawai randa reshe zai juye da mujiya. Kakamu da sonta a lokacin ita kuma zata rama abinda kayi mata shiyasa nake so ka dinga abubuwan a hankali... Mujahid yace nifa na gaya maka ban iya yar murya a gun mace ba, yadda na saba tafiyar da mata itama haka zantafiyar da ita. Amir yace in tagaji tana iya cewa ba zata zauna ba. Kasandai su abba bazasu kara barinka ka zauna babu mace ba alokacin bazasuce ka kawo mace da kanka ba duk wadda tasamu baka zasuyi ba yadda ka iya kuma.A nan nr jikinsa yayi sanyi ya ce mu bar gun nan dan Allah amir ina da binyi fa. Ya bude motar ya dawo gaba, amir ya ja mota yana fafadin basan abinda kake hange ba da kake cewa nabila tayi ma kankanta. Bai ce ko mai ba ya dauke kansa yana lumshe ido.aranar da zazzabi nabila ta wuni babu party a washegarin lahadi sai da daddare ne akayi walima ta maza zalla a gidan su amir, wuni su inna sukayi da rana amarya na kwance kawayenta sai kaiwa da dawowa anci ansha anyi hani'an babu abinda bai wadata ba a gidan bakin nan , mutane ba abun da suke bada labari irin facakar likin da ake da naira agun party da kudin da ake kashewa gun ga abubuwan ci nan da nasha. Ranar litinin bayan la'asar akayi sisters day, a gidan dan hausa washegari talata aka rufe biki da picnic na zallar yanmata da samari da yamma daf da magariba suka dawo dare nayi aka tafi gala night wanda shima yanmata ne da samari kadai. Washegari karfe goma shabiyun dare suka dawo, bikin nabila da mujahid yazamo abin bada labari sati guda ana shagali ana kashe kudi sai ranar laraba da safe aka kai nabila gidan dangin mijinta da sukayi masauki a gidan alhaji muktar alokacin mujahid na can dakin amir yana ta bacci shi kadai ya kullo kofa ya kashe dukkan wayoyinshi dan baison kowa ya dameshi. Iyayan nabila suka danka amanarta a hannun iyayan ango suka amsa da adu'ar Allah ya taimaka musu su sauke amanar aka basu suka yi godiya mai yawa da karamci da akayi musu aka basu ya. Inna tace mune da godiya da aka nemi diyar tamu duk wanda yazo yace yana son yar ka da aure ko shakka babu ya isa masoyinka, domin shi aure idan akayishi anzama jini daya ne. Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Launin Fata 2-08 Posted by ANaM Dorayi on 09:39 AM, 23-Oct-15 Under: Launin Fata Jini daya kuwa ba wasa bane, idan mutun baisonka ba zai so ya kusanceka ba ma balantana haryace zai hada jini da kai, ba bakaramar soyayya da girmama mutum akai ba in akace ana son nashi da aure, mata nawa aka tsallake aka ce ana son taka.Hajiyar su amir ta ce gskiya ne inna amma dukda haka mu ne da godiya ka nema abaka shine darajar da girmamawar mutum nawa suke nema basu samu ba mu muka nema aka bamu, duk wanda ka nema yarsa da aure yabaka lallai ba karamar soyayya yake maka ba. Wanda bai kaunar ganinka ma bai son yi balantana yaso hada jini dakai. Gaba daya aka ce wannan maganar gaskiya ce.Aka yi addu'a aka ci gaba da barkwanci kana wata mata ta fito da wasu madaidaitan farantai guda uku daya ancikashi da kayan marmari masu kyau irinsu tuffa da kankana da abarba da lemon zaki lafiyayu suna ta kamshi, dayan kuma turarukane masu tsananin kamshi da tsada, dayan kuma turaren wutane nadaki masu kamshin gaske, a dan kananun kwalabe masu kyau suma guda goma gyafe guda an zuba dabino da kwakwa, ta mikawa dangin amarya tace munsiya bakin amarya Allah yasa kada tayiwa ango gaddama.Aka tuntsire da dariya gaba daya suka dawo da nabila gidansu sai gari ya waye zasuyi asubanci tafi malesia da angonta. Tun aranar nabila ke kuka bayan sallar azahar baba mahmud ya kirata zaure shi kadai ta isa gabansa, ta durkusa tana sharar kwalla ya ce ki daina kuka nabila aure gata ne da rahama ba ukuba bane balantana kiyita kuka haka ni dai abinda nake so da ke shine kiji tsoron Allah kiyi wa mijinki biyya dukkan hakkinsa da ya rataya a wuyanki kibashi idan kinyi haka Allah zai samiki Albarka da rayuwarki, ki dage kiyi hakuri sosai gaba daya rayuwar aure hakuri ce rayuwace zakiyita da mutumin da baki saba dashi ba, kuma zakiyi abubuwan da baki saba dasu ba a gidan da baki saba dashi ba, to annan ma hakurine zaiyi aikinsa har kisaba din. Na gode sosai da biyayyar da kika yi mun in sha Allahu zakiga alkairi arayuwarki. Kukan da take ya bashi tausayi sosai ya kamo hannunta ya shiga da ita cikin gidan matan gidan na zaune na kallon ikon Allah gashi basu isa su hana komi ba. * nabila ta gama sallama da kowa a kano a kano ta dau abin da ta fi bukata sun bar gida Nigeria zuwa malesia ranar alhamis da yamma, tunkafin aje a mori amarci da jin dadin nabila ta kara kyau sai dai rama na damuwar da mujahid ke kunsa mata da azabar sonsa dake zuciyarta. Shi da ita da amir suka isa gidan iyayansa da kannansa mata biyu kamanninsu daya su suka koma egypt yayin da amir zai dada kwana biyu kan ya koma Nigeria gida kano dabo jalla babbar hausa ko da me kazo anfika. Yayi hakan ne dan ya kara kwantar wa nabila da hankali ganin irin damuwar da take ciki.. . Kafin iyayen mujahid yatafi sai da sukayi mai gargadi sosai a kan ya kula da hakkin yarinyar nan. Shi yace yana so ba wani ya cusa mai ita ba, iyayanta kuma suka bashi bawani dalili da zai sa su wula kanta masu ya. Abba ya ce idan naji wani labari marar dadi akan zamanku zaka faskanci fushi na. Takaicin da ya hanashi sukuni kenan bayan tafiyarsu ya rasa abinda ke mai dadi a duniya, daga yin auransu har za a fara ta kura mai kan yarinyar da ba wani damuwa yayi da ita ba. Ya tashi yayi wanka ya sanya kaya zuwa kanana ya tsuke sosai ya baza turare ya fito falo yasami amir kwance yana kallon wani film yace zan fita zakaje? Amir ya bishi da kallo ya ce haba lokacin yawo ai baiyi ba yana da kyau ka koyi zama a gida tunda kasan da da yanzu ba daya bane . Da baka da mace ba nauyin kowa a kanka, yanzu kuwa kana da aure yana cikin hakkin ka da da ya rataya a wuyanka ka dinga zama a gida kana kana debe wa matarka kewa, musanman a kasa irin wannan da bata san kowa ba sai kai. Ya rausayar da kai yana murmushi yace amma dai kasan ni dalibine har kokin karatu ba zasu barni in dinga zama ba, ita din ma makaranta zata rinka xuwa nan da dan lokaci. Bai jira wani bayanin amir dake bata mai rai ba ya wuce ya bar gidan, nabila na kicin tana da dafawa amir abinci yace yunwa yake ji ta gama ta kawo mai ya dubeta cike da tausayawa yace kinci naki ne. Ta ce banci ba. A daki zaki ci? Yace a a ki daure ki ci alamunki sun nuna kina jin yunwa, idan baki ciba nima ba zan ciba, nasan ina jin yunwa amma sabodake na tayar da dake yin girkin yanzu. Ta zame ta zauna a gunta ta dora kanta a cinyoyinta ta kama sharar kwalla. Tace idan kasani naci abinci yau gobe da jibi da sauran ranaku wa zai lallasheni in ci? Banaso in saba da abin da ba zai dore ba gareni. Nafiso inci gaba da tafiya yadda mai gidan yatafi da rayuwarmu a hankali zansaba. Amir yace nabila nasan dole ki damu kan abinda mujahid yake miki amma dan Allah ina so ki ci gaba da ba mara da kunya kiyi hakuri, duk wadannan abubuwan da mujahid ke maki watarana sai kin tausaya mai idan yazo hannunki. Tace amir hakuri yazama dole ga zuciyar da ta kamu da son wanda bai damu da ita ba, ba zan ce maka ina bakin ciki da haduwata da mujahid ba saboda bansan abun da zai faru gobe ba sai Allah, amma duk da haka ina takaicin kasancewata a wannan halin ban taba son wani ba sai shi.Amir ya gyara zama ya ce nabila babu inda aka taba cin nasara a rayuwa batare da an hada da hakuri ba, ita nasara ne tana tafiya ki ci gaba da hakuri ki fidda duk wata da damuwa a kan mujahid watarana zakiyi mamakinsa. Ke ba matar da za a iya ci gaba da daukewa kai ba ce musanmam ga mujahid da yake da fitinar sha'awa, zan gaya miki sirrin mujahid wanda indai kina mashi shi ya shiga hannunki ko baya so. Nafarko mujahid mutum ne mai son tsafta baya son kazanta ko yaushe cikin kamshi yake yana son duk wanda zai rabeshi ya zama mai tsafta, ki dage a wannan zaki ja ra'ayinsa. Na biyu mujahid mutum ne wanda baya son raini idan har zaki rinka girmamashi kina nunawa ke ba ko mai bace a gunsa to kin gama dashi. Sannan mujahid mutum ne mai son wayayyar mace shiyasa bai son karamar yarinya, dan kada ta zo mai da raini da duhun kai, ko da yaushe ki rinka tsukewa cikin kananan kayan da muka jubgo maki a lefe in zaki lura hoogs sunfi yawa a lefenki da kaina na saye su saboda kija ra'ayinsa da su. Ko mujahid bai niyyar kula mace ba in taja ra'ayinsa da waddanan kayan sai kiga ya saurareta. * kamkam ta rike hudubar da amir yayi mata, kwananta uku ya koma kano ya bar nabila cikin kewar hira debe kewa da yake mata da shawarwarin da yake bata. Dk safiya mujahid zai fice bai dawowa sai yamma, zai bar gidan kalkal ya dawo ya sa mai kalkal, ko ina na kamshi turaran kamshi turaran wutar da ta taho da shi da na ruwa dare da rana yinsa take a gidan, wannan ne abu na farko da ya fara daukar hankalin mujahid game da nabila, yana son tsafta da kamshi in ya shigo kuma zata tareshi a falo a cikin kwalliya ta jan hankali ta gaidashi ta karbi jakar hannunsa ta rakashi daki ta fito ta barshi yayi wankansa ya shirya kaya.. Duk abinda take takan ajiye ta zauna a falo hanyar da zaifita takan ce mai an shirya mai abinci randa yaga dama ya ci kadan ya tashi randa bai da ra'ayi ya ce ya gode ya koashi abincin da take bata lokaci sosai gun dafashi ta sha wahala amma wanda akayi danshi in ya zo sai yace ya koshi, idan ya fita da yamman nan bai dawowa gida sai tsakar dare yana dan lekawa dakinta kana yawuce nasa dakin ya yi bacci. Kusan kullun abbansa ko umman sa sun kirashi a waya suna tambayar lafiyar nabila ya yace kalau take itama in sun kirata sun tambayeta haka take gaya musu har ta shafe wata uku a gidan bata taba nuna musu tana da matsala da mujinta ba, haka shima baba mahmud daga gida kano ko yaushe yana mata waya su gaisa haka amir shi da yake yasan komai shi yake dada yi mata nasiha da ban hakuri.Ta kance dashi amir ka dai na bani hakuri hakuri yazama dole ina hakuri da mujahid hakurin da ban taba tunanin zan yishi da da namiji saboda son da nake mashi. Amma nasan da cewa gaskiyane da hausawa kance mai hakuri zai dafa dutse har yasha romansa. Ni na dora nawa dutsen a wuta ina ta dafa shi watarana in har muna raye zai dahu nasani. Tana yawan baiwa amir tausayi. Idan ya ma mujahid magana sai ya rufeshi da fada sai yace wai me kake so in mata ne goya ta zanyi, sanin kanka ne ba zan zauna inlalace gun yar karamar yarinya haka ba mai zan tsinta a jikin nata? Aure ne aka ce sai nayi kuma nayi ina gargadinka da ka kama bakinka kada kasake ka gayawa abbanmu abinda kasan zaimin fada. Amir yayi murmushi in har ba kan gaskiya kake tafiya ba abba da kansa zai gano haka ba sai na fadi mai ba. Hatta abinci da abinsha din da mujahid ke so amir ke gayawa nabila yana cewa ta daure tana yi mashi in yau baiciba gobe zaici in har yana yin dadi zai daina cin abincin kowa sai nata. Ranar da ta cika wata uku cif a gidan tana zaune da sassafe ta fito da wasu rantsantsun body hoogs haduwa rigane da wando sun matse jikinta kam kam Duka surorinta sun bayyana ta saki gashin kanta a kafada, duk da ba wani jin dadin kasan mujahid ya mallaka mata ta fannin soyayya ba amma jikinta ba karamin kyau yayi ba, fatarta ta kara gogewa da haske sosai irin kalar nan mai tsada. Jikinta da falon na wani irin bacci mai dadin gaske, wani yaron mujahid mai hidimar gidan ya kwankwasa kofa ta mike ta bude yagaida ita ya miko mata wasu takardu yace wanine ya kawo yace abawa mai gida. Ta karbi ta juyo ne suka hada ido da oga mujahid yana tsaye kofar dakin baccinsa ya zuba mata ido zuciya ta gama kule shi ganin irin kallon da yaron yake mata na zalam, ta iso gabansa ta tsuguna ta gaida shi ta mike mai takardun, ya danna mata harara ya ce dama haka kikeyi da ma'aikatan gidan nan? Ta ce me nayi kuma? Yace me kikayi me yasa ya kwankwasa kofar baki lullube jikinki ba kika fita a haka ya gama ganinki. Cikin sanyin murya ta ce ka yi hakuri zan kiyaye a gaba. A nan ne jikin mujahid ya yi sanyi har yanzu idonsa a kan ta yake, wannan itace rana ta farko da ya kare mata kallo da bai taba yi mata ba. Ya fara fahimtar abinda bai fahimta tana da shi ba, ya kasa dauke idonsa a kanta ko ranar da ya fara ganinta har yace yana sonta bai mata irin wannan kallon ba. Ya gyada kai yace tashi ki zauna. Ta mike ko ina na jikinta rawa yake, yarinya danya sharaf tana kan gabar budurci komi na jikinta ya bude ta cika taf ya haramtawa kansa halal dinsa wai dan kawai ta raina shi. Har ya kai bakin kofa yaji tace ga abincinka ka daure dan Allah ka ci. Ya waigo suka hada ido tayi shirin maida nata idon kasa yayi ajiyar zuciya ya koma kan tebur yace to zo ki zuba mini. Ta taso tayi sauri ta zuba mai, yana mamakin yadda ta haddace abincikan da yafi so ta iya dafasu yadda yake bukata, yaci sosai yana yi yana satar kallonta idan sun hada ido sai yasha mur ya dauke kanshi, har abin ya fara bata dariya tsammaninsa bata wayo ne saboda yana daukarta yarinya mai karancin wayewa a wannan fannin. Bai san tana da nata wayon ba duk yadda yake tunaninta ba haka take ba, a kansa ta zama mai hakuri da kauda kai, saboda babu wani tsari da zuciyarta zata iya a kansa a dalilin tsananin son da take masa. A gabansa ne bakinta ke mutuwa tsiwarta ba zatayi tasiri a kansa ba da zarar taganshi jikinta mutuwa yake shi kadai ne namijin da ya isa tayi mai komai yana so da baya so dan zuciyarsa tayi haske. Bayan ya gama cin abinci ya mike ta amshi jakarshi zata rakashi waje, ya manna mata harara yace a hakan zaki kara fita ko Ta dubi jikinta kana tashiga daki ta dauko zani ta lullube jikinta tayi ajiyar zuciya haka kawai yau yasamu kansa da son kallonta. Jikinsa yayi sanyi da ya shiga mota ta mika mai jakar ta rusuna tace adawo lfy Allah ya kiyaye hanya. Rana ta farko da taga yayi mata murmushi ya ce amin yi maza ki koma ciki bana so ana kallonki. Itama murmushi tayi masa ta ce to. Murmushin da ya tsaya mai a zuciya har ya shiga makaranta yana tunanin fiskarta yadda murmushin yai bala'in yi mata kyau tunaninsa shine dama yarinyar nan tana da kyau haka. Gaskiya za a huta a jikinta sai da muwarsa ita ce kada tazo ta raina shi, ko da yake ya fahimci tana da ladabi da hakuri duk dauke mata kan da yake dare da safe in dai zai shigo gidan sai tayi mai adu'ar Allah ya bada sa'a bai taba mata kallon rahama ba sai yau duk da haka bata fasa ba. Yana shirin fitowa daga motar sa wata budurwarsa mimi ta iso da sauri ta karbi jakarsa ta bude hannu suka rumgumi juna yace nayi mising dinki mimi kamar nabiki kasarku yaushe kika dawo? Ta lankasar da kanta a kirjinsa tace nasan ban isa ka bini ba shiyasa bansa ran zaka bini din ba, yau da asuba na dawo gidanka nayi niyar zuwa fatyz ta ce mun kayi aure kuma ka gargadi dukan yanmatanka kada wadda ta kara zuwa gidanka yanzu kana da mata, bakincikin hakan yasa na nufo makarantar nan yanzu saboda na baro gida cike da kewarka, ina kishin ruwan kirjinka da soyayyarka, ka taimake ni. Mujahid ya lumshe ido ya maida ta cikin mota ya shige ya suka nufi inda zasu huta, soyaya ta fitar hankali sukayi a wannan rana suka sha giya yadda suke so tun safiya sai tsakiyar dare suka rabu, mujahid yayi bacinsa ya isheshi ya tashi yayi wanka, ya fiddo wasu kayan a motarsa ya bazo turare ya dawo gida yana wani shan kamshi kamar ba shi ba. A falo ya iske nabila tana zaune tayi tagumi lokaci baiyi ba ta sani da zata gaji da zaman hakuri da take a gidan mujahid amma yau hankalinta ya fara tashi. Tun safe yayi mata murmushi jikinta ya sauya zuciyarta ta tsumu da son ya rinka kasancewa da ita kamar kowanne mata da mijin ta wuni cikin wannan halin, da yamma ta sauko harabar cikin gidan ta zauna tana karanta wani littafi na hausa da tayo guzirin abinta daga gida sanin irin zaman da zatayi kadaici da kewa suna damunta na rashin abokin hira. Wata sisi ta shigo gidan tana takun kwas kwas kamar zata karye, ta tambayi yaron gidan ima ko mai gidan na nan, ya ce baya nan amma ga matarsa can, ya nuna mata nabila ta iso gabanta tana wani irin kallo cikinharshen turanci tace tana son zama ta jira mujahid a nan. Cikin takaici nabila tace ba zai yuwu ba nan gidan matar aure ne ba gidan karuwa ba, ta yi sauri ta fice ranta ya baci, haushi ya kamata ta ce koda yaushe nan fa take zuwa ta jirashi nabila ta buga mata tsawa ta ce idan bata fita ba sai tasa an mata duka, ta fice tana fadin sai ta gayawa mujahid din. Nabila ta mike ta koma cikin daki ta kwanta a gado ta matse idonta yaushe ne lokacin da mujahid zai saurareta duk da cewa bata taba aure ba amma ta san ba haka ake zaman aure ba ta dafa abinci ba a ranar saboda tsabar sanyin da jikinta yayi tun bata fi sati a gidan ba ta san mujahid mayan mata ne ita da take zaman halal din sa bai kula ta ba. Riga da zani na atanfa ne a jikinta ba wani make up a fuskarta sai dai daddadan kanshin nan na kullum wanda mujahid ke matukar so. Daga zaunan da take ta ce mai sannu da zuwa..... Zanaraddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Launin Fata 2-09 Posted by ANaM Dorayi on 09:40 AM, 23-Oct-15 Under: Launin Fata Tausayinta ya kama shi ya matso daf da ita ya ce baki da lafiya ne yau? Lafiyata kalau. Ta bashi amsa a takaice. Bai ce komai ba ya wuce dakinsa baccine har yanzu a idonsa ko kayan jikinsa bai cire ba takalminsa ma na kafarsa,cikin karuwansa na makarantarsu tana juriyar shanye fitinar sa batsaa raki in zai kwana yana takarta ba zata kosa ba, irin wadan nan matan sun fi burge shi. Nabila ta kasa juriya ga halin da take ciki ta dubi a gogo ta jawo waya ta kirawo numbar amir. Bayan sun gaisa ta ce Dan Allah kazo ka tafi dani gida ban iya ci gaba da zama a garin nan ban san kowa ba sai mujahid shi kuma bai da lokacina duk lokacinsa na makarantunsa ne da holewa da karuwansa, na yi iya kokari na in shawo kansa in jawo hankalinsa da duk abinda ka nuna mini da wanda nimaa na sani banyi na sara ba. Na hakura dashi izawa wannan lokacin na san ba zan sami nasara a kansa ba na hakura in sha Allahu hakuri zai zame mun maganin ciwon sasa da ke damun zuciya ta. Amir yayi murmushi yace na yarda ke yarinyace nabila kuruciya na damunki yanda na fahimci kina son mujahid ko shekara goma ina zaton zaki kina jiran lokacin da zai shigo hannunki ba zaki kosa ba. Sai gashi watanni uku kacal kina fadin kin hakura? Nasha gaya maki ba a cin nasara sai anyi hakuri, shi kuma hakuri da kike ganinsa shine abinda yafi komai wahala kafin ayishi sai ansha wahala, wannan hakurin shine zai mallaka maki mujahid kuma shine zai rike maki zuciyarsa a gaba duk inda ya shiga yana tare da tunaninki. Nabila nasan nura tun shi bai gama sanin kansa ba, na san abinda yake so da wanda baya so, da ace nasan ba zaki iya jan hankalinsa ya shigo hannunki ba da ba zan bari ki zauna da shi ba har yanzu ko anyi auran naku sai na san yanda nayi kika dawo gida. Amma da yake nasan ke irin matar da yake matukar so ne kuma nasan shi mayan mata ne shine dalilin da yasa iyayansa suka takura yayi aure bai da hakuri a kan mace macen kuma irinki. Kada kiyi gajen hakuri ki maida aikinki baya kada ki bari ki rasa masoyinki wanda zuciyarki take so daga baya kizo kiyi nadama. Kici gaba da hakuri wata rana zaki ci riba. Kuma duk yanda kike shan damuwa ta bangaren shi kada ki sake ki kai karan mujahid baya so a hadashi da iyayensa, ni kadai ne zan kai kararsa ga iyayensa, ya hakura dan ni babu yanda zaiyi dani. Bayan sun ajiye wayar ta mike ta shiga dakin nasa ta durkusa dai dai kansa tana kallonsa ko mai kyau yakewa mujahid hatta bacci inyanayi kamar karya tashi, ta shafi sajen fuskarsa sai taji yayi ajiyar zuciya ta matsa da sauri a zatonta farkawa zaiyi ya mareta ya ce ta raina shi. Lallai fauzeeya tayi gaskiya da tace babu wanda zata so bayan mujahid sabo da shine wanda zuciyarta ta fara so, rabuwa dashi zai haifar da damuwa mai tsanani a zuciyarta. Yazama wajibi taci gaba da hakuri dashi har zuwa lokacin da zata samu zuciyarsa. Idan bata bar gidanshi dan damuwar shi damuwar da zata shiga a gidansu inda bata ganinsa sai ta ninka wadda take ciki a yanzu. Saboda nandin gidansa da take yana kwashe mata rabin damuwar da duk damuwar da take ciki idan mujahid ya shigo zuciyarta sai tayi haske taji dadi ta dinga tunanin wanne irin so take wa gayen nan ne? da gari ya waye ta shirya mai abinci mai rai da lafiya yau ma sai ta sanya a tamfa riga da zani ta kulle kanta tsam batayi wata kwalliya ta a zo a gani ba.. Mujahid ya fito daga dakinsa cikin kananan kaya (giant sosai) ya fidda space din idonsa ya dubeta a yatsune ya amsa gaisuwarta yace daman wadannan kayan kika saba sawa? Ta sunkuyar da kanta kasa tace naji kace in daina sawa ma aikatan gidannan na kallo na. Yayi murmushi yace ai ba ina nufin ki daina sawa gaba

Chapter 11 of 12