Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta ba kallon su kawai take suna hidimarsu. Akayi biki na kece raini, abba na alfahari yayanshi na da sa'a ya kance shiyasa ya kashe musu kudi dan a kalle su da daraja, ina talaka ina gidana? Ummi ta yi murmushi kawai tana kallonshi kamar bai san abinda yake yi ba. Ya dau rayuwar duniya ya sa a gaba kamar ba za a mutu ba, aka kai nafisa kaduna cikin gata da daula kb kamar ya hadiye ta don so, ta kwashi fiye da watanni tare ta kb ana shan soyayya ba matsalar ko mai, lokacin da tayi shekara daya nafisa ta fara fuskantar matsala daga gun kabir. Matsalar farko ita ce yawon dare kabir sai ya kai karfe 2 na dare bai dawo gida ba, in tayi magana ya ce shi fa daman bai iya zama a gida ba kamar mace, tayi fushin ta gaji ta dawo lallashi bai daina ba sai ta kai ta kawo ya fara kwana a waje. Wata rana ya fita tun sassaè bai dawo ba sai da ya kwana 2 bakinciki ya damu nafisa gashi ya hanata aiki ballantana ta dinga fita ya ce bai amince da aiki ba, tana kwance a daki taji tsiwar motarsa ta mike ta fito suka hadu a baban falonta ya fadi kan kujera da kwalabar giya a hannunsa ko minti 2 baiyi ba sai barci nafisa na tsaye ta zuba mai ido ta dauko kwalbar giya tana juyawa dan giya ta aura?Ta jefar da kwalbar ta fashe ta koma daki ta kwanta tana kuka ta fara tunanin makomarta a gun KB, kudi dai shi suke so ita da mahaifinta akwasu babu matsala, duk abin da take son in dai kudi na siya kabir zai mance da su akasan matashi. Tun tana da watanni 2 a gidan sa kb ya fito karara ya ce mata shi baya son haihuwa dole ne ta yarda a juya mata mahaifa c zata samu ciki ya rusa mai tsari ba. Duk da cewa itama ba damuwar ta ta hauhu ba, amma taji tsarin be mata ba, da ta nuna mai haka sai cewa ya yi shi fa mace ba ackin komai take a gunsa ba yana da damar auran 3 irin ta lokaci guda ya ajiye su yi mai duk abin da yake so ba ta isa ta sauya mai tsari. In har tana son zaman lfy ta yi yanda yake so kawai. Sai ta bishi a haka ya dauketa ya kaita asibiti dan ajuya mata mahaifa, likitan da zai yi aikin ya dubi kabir ya ce to bamu guri ko? Kabir ya galla mai harara ya ce in baku guri kamar yaya? Matata ce fa me zaka yi mata wanda ya haramta in gani? Likita ya ce aikin za ayi kuma aiki ne da yake bukatar nutsuwa ba a son motsi. Da kyar ya amince ya fita din dan dai yana son a yi aikin. Likita ya dubi nafisa ya ce da amincewarki za a yi miki wannan aikin? Alhalin da kuruciyarki da komi? KB namiji ne a yanzu duniya da kudi da tashan da yake ji na lafiya da karfi a matsayinsa na matashi ya sa yake ganin bai dace ya haihu ba. Haihuwa zata bata mai tsarinsa, daga lokacin da ya gama duk wadannan abubuwan hankali ya dawo jikinsa ya faìmci inda rayuwa ta sa gaba to zai auro matar da zata haihu ne ke kuma ya cuce ki kenan har abada. Nafisa na sharar kwalla ta ce Dan Allah likita ka taimake ni ka ce da KB ka yi aikin nan ka yi mini allurar da zan shekara 5 ban haihu c idan yaga cn samu ciki ba shi kenan ko nawa kake so zan baka. Haka aka yi likita ya dannawa nafisa allura ya ce da kabir an gama aikin... Nafisa tayi doguwar ajiyar zuciya ta mike ta dawo fal ohar yanzu barci kb yake ta dau jakarsa da yake fita da ita ta hannu ta bude ta fiddo matsayacin hoto mace ce tsirara haihuwar uwarta kyakyawar gaske, jikin nafisa ya kama rawa, ganin badalar ta yi yawa ta sake danna wani gun sai ga filin sosai yana juyawa mijinta ne kb da waccan yarinyar da ta fara ganin hotonta tsirara haihuwar uwarta suna aikata masha'ar yarinyar. . . Yana wani irin. . . Da. . . Ya rike mata. . . . Alamun yana cikin wani hali. Jikin nafisa ya hau rawa hankalinta ya yi mugun tashi, a rayuwar da tayi gwargwadon wayewarta da budewar idanunwanta ta ga masha'a iri iri amma bata taba ganin rabin wannan ba. Ta yi sauri ta kashe wayar gaba daya, ta zauna sharaf gaba dayan jikinta ya saki a kan kujera kanta ya yi mata dumm ta rasa tunanin da zata yi.Shin mene ne kb ya rasa a gunta da yake neman mata? Tamike ta shige dakin ta ta tsaya gaban makeken gadonta tana kallon kanta, ita dai ta sani duk wani abu da namiji yake nema a jikin mace tana da shi kuma iya kokarinta na farantawa kabir a fannin sha'awa tana yi saboda tun randa ta shigo gidansa ta fahimci shi mutum ne makalin mace, yana da masifar sha'awa bai iya hakuri akan mace, dole take amfani a bubuwan da zasu kara mata kuzari da ni'ima dan ta samu juriyar da zata iya shanye fitina kabir duk dan kada ya nemi matan banza ashe duk a banza tayi. Tun tana A.B.U zaria ta tsani namiji mai neman mata duk burinta bai wuce ta auri namiji mai kudi wanda zata fantama ta huta ba. Amma ba ta son dan giya mai neman mata ashe shi zata fado hannunsa. Kome ya hanata fahimtar haka tun a da (RABI'ATU NASIDI TA CE KUDI NE) hakane yan uwa? Kb ya boye mata halinsa a zaman da suka yi na shekara daya bata taba ganinshi da giya ba kuma bata taba ganinshi da mace ba haka kam ya aure ta bai taba nuna mata wani iskanci ba. Ashe kura ce lullube da fatar akuya, ta dawo falo ta kara bude jakar kb sai kuma ta ci karo da pant da bra wadanda ba na ta ba, da ace su ta fara gani sai ta rufe tunda ta ga waccen badala me zai firgitata cikin pant da bra kuma? Tabbas wannan aike ne a kayo mata dan ta gani, yarinyar da kb ya kasance da ita a jiya ita ta aiko mata da wannan sakon, ita ta hana kb dawowa gida a daran jiya. Ta maida idonta kan kb yana ta faman barcinsa bai san abin da take ba ta daddage ta girgizashi da karfi ya farka nan take cikin matsanancin haushi. Dama abinda ake bata mai rai kenan a tashe shi yana barci, ya buga mata tsawa ya ce ubanwa ya ce ki tasheni ina barci? Ashe baki da hankali?Ta zuba mai wata uwar harara ta dauko wayarsa ta kunna mai film din sa ta haska mai ai yana gani ya mika fuskarsa ta rine da bala'i ya ce ubanwa ya ce ki daukar mini waya? Sau nawa nake gaya miki ki daina taba mini waya? Ta ce an taba din sanin baka da gaskiya ne ya sa kake tsoron in taba ma waya, ashe kai dan iska ne ban sani ba? Mazinaci, mashayin giya! Kb ya fincikota ya shake mata wuya ya shiga lodarta yana fadin ni kike zagi? Ke har kin isa ki zageni? Kin isa ki hanani abin da na yi niyya? Ina ce kudi na kashe na auro ki? Ubanki bai baiwa kowa dansa sai mai kudi dan na aureki sai in zauna dake ke daya. Ya yi mata lilis ya dau motarsa ya bar mata gidan, itama ta nufo kano gidan iyayenta cikin tashin hankali, Abbansu baya nan sai ummi ta fada mata abinda ya faru. Ummi ta ce ai auran mai kudin kenan ga ribarsa nan kin gani sai ki jira mai daure muku gindi ya zo. Abba ya zo ya ji cin mutuncin da Kb ya yi ma yar lelensa a ranar ya nufi kaduna ya taki sa'a ya iske kabir a gida, ko kallon arziki baiwa Abba ba ya ce kaga ni fa dan na auri nafisa bata isa ta hanani abin da na ga dama ba. Dan me yasa za ta yi mini bincike dama mai bincike yana cike da ganin bacin rai sai ta kiyaye dan gaba. Abba ya ce kai bana son rashin kunya ka bawa yata takarda ko mu hadu a kotu. Kb ya mike ya shige daki ya fito da wata yar akwati cike da kudi sabbi kai yan naira 1000, bandir bandir ya ajiye a gaban Abba ya ce ba ni da niyyar sakin matata ba zan hanata zama a gidansu ba, duk sanda ta gaji da zaman ta iya dawowa ga kudi nan ka kai mata tunda ita kudi ne a gabanta ni kudi ba matsala ta bane. Ya koma daki ya danno kofa ya bar abba zaune turus daga bisani ya dauko akwatin kudi ya dawo kano ya ba nafisa da ummi lbr yadda suka yi da kb. Ya ce Nafisa hakuri za ki yi ki koma gidan kb tun da dai muna samun kudi a jikinsa ki ci gaba da hakuri da halayansa. Ummi ta ce tabdijan yanzu duk wannan wulakancin da ya yi maka bai sa kun dauke hankalin ku daga kan abin duniya ba, shin meye baka da shi ne Abba da kake kwadayin abin wani?Abba ya buga mata tsawa ya ce ke baki da wayo ne? An gaya miki dukiya tana wa mutum yawa ne? Yanzu ne lokacin da mutum zai yi tattalin rayuwarsa saboda gaba kafin lokacin ya kure maka. Nan gaba ka yi kwanciyarka a gida ka ci duniyarka da tsinke. Ummi ta girgiza kai ta ce Allah ya kyauta. Tun nafisa na jin zafin KB har hubdubobin mahaifinta suka shigi zuciyarta da karfi ta manta son abin duniya ya rufe mata ido, ta kira kb a waya da kanta ta ce ya zo ya dauke ta zata dawo, ya ce da shi ya kaita, in zata dawo ta dawo in ba zata dawo ba tayi ta zama shi dai ba zai fasa dana matar duk da yaga tayi masa ba. Bakin ciki kamar ya kashe nafisa haka ta koma bisa hudubobin mahaifinta. Dama aure ne aka yi shi bisa sha'awar suffofin jiki lokacin da kowa ya gane waye dan uwansa salo ya sauya. In kida ya sauya rawa ma sauyawa take. Gidan nafisa kenan. Yayin da nura da ya kasance ba zancen aure a ranshi sai tsabar duniyanci da son jin dadi, babu takurawa a tsarin mahaifinsu kowanen da yana tafiya ne kan abin da yaga dama, ko Abba zai takurawa kowa a kan batun aure ba zai takurawa nura ba saboda yafi amfani da ra'ayinsa da abinda yake so. Asiya da Rabi halayyarsu daya basa tare da Abbansu ko kadan ra'ayinsa bai musu ba sunfi shiri da umminsu tafi jansu a jiki tare suke duk wata shawara da za su yi, tare suka yi candy lokacin bashir yana jami'ar malasia yana karatu asiya na son tafiya jamiar bayero ta nan kano yayin da Rabi tafi son shiga legal ta karanta fannin shiyar usulunci. Wata rana da yamma sun fito zasu kasuwa ita da asiya,da fatima Asiya ta lullube jikinta da farar lafeaya fatima ta yafa mayafi ita kam Rabi hijabi ta sa har iya kwaurinta ta dau nikab ta kara saboda bata son kallo a kofar gida suka gamu da Abbansu ya ce ina zaku haka ke kika rufe fuskarki kamar wata dodo? Cire shi da Allah sokuwa wadda har yanzu bata gano inda duniya ta sa gaba ba, ke dai ga alamu bazan ci ribar kudin da na ke kashewa a kanki ba. A sanyaye Rabi ta fidda nikab ranta a bace ya ce bani shi nan, dube ki kamar wadda aka haifa a daji.Suka shiga mota tana mamakin halin mahaifinsu ba abinda ya yi mai zafi da tsarin kan shi dan kuwai ya sami kudi ya maida yayansa kamar wasu hannun jarin da zai dinga samun kudin shiga da su. Ya aurar da nafisa ga mai kudi maganar haihuwa bai damu ba ya ba Rufa'i diyar masu kudi itama iyayanta sun ce haihuwa ba yanzu ba duk bai damu ba. A kofar shiga sahad store na zoo Road wani matashi baki sidik ya kafawa Rabi ido har ta rasa meye abin kallo ne a jikinta, ita ba wata shiga tayi ta fitina ko jan hankali ba tayi tsaki ta wuce gaba ta tsani a dinga kallonta haka. Har suka gama siyan abin da zasu siya suka fito wannan matashin yana tsaye inda yake wannan karon ma ita yake ta aiki kallo. Daf da shi direbansu yayi parking za su shiga mota ya karaso kusa da rabi yayi musu sallama. Fatima ta galla mai harara ta ce malam lafiya? Asiya ta ce haba fati me ye haka mutum yayi mana sallama ba ki amsa ba ki haushi da fada? Ta ce walaikumussalam. Yayi murmushi ya ce barkanku da yamma. Ta amsa Alhamdulillahi kana lafiya. Ya ce lafiya kalau dan Allah waccan yar uwar taki neke son magana da ita in ba zata damu ba. Asiya ta ce gaskiza yanzu muna sauri ne sai dai ka iya gaya mata abinda kake son gaya mata a cikin minti 2. Ya ce hakan ma na gode. Ya dubi rabi ya ce baiwar Allah dan Allah gidanku nake son in sani. Ta dago kyawawan idanuwanta ta dube shi, ta ce ko zan san dalilin da yasa kake son sanin gidanmu? Ya ce eh, bahaushe kance in kaga kare na shinshinar talalmi dauka zai yi, niyyar Alheri ce ta shiga zuciya ta ayanzu yanzu a kanki shi ne nake son gabatar da kaina in na san gidan ku kumma in an bani izinin in zo saboda nan ba gurin magana bane. Rabi'atu ta dube shi ta yi jim bakin mutum ya je gidansu. Ai sai Abba ya kusan dukanta ita kuma ba ta iya wulakanci ba kawai sai ta yi kundunbala ta gaya mai kwatancan gidansu ta bashi izinin yazo har ta gaya mai sunanta.Godiya mai yawa ya mata tashiga mota suka tafi, duk da sassaucin ra'ayin Asiya sai da ta ce mata kin yi wauta Rabi, maganin kar ayi kada a fara, kema kin san in Abba ya ganki da wannan mutumin kin banu. Ta ce to ya zanyi? Bana son wulakanta mutane, kai tsaye kaga mutum a hanya ka wulakantashi akwai matsala saboda baka san wane irin mutum ne ba. Fatima ta ce ke dai anti Rabi da kin sani hakuri kika bashi da wukancin da Abba zai mashi gara ki bashi hakurin ki sani ko kun rage saura ku biyu kacal ke da shi a duniya Abba ba zai baki shi ba. Ta ce a a dama nima kun ji na ce ina sonsa ne? Nufina idan ya zo in bashi hakuri cikin ruwan sanyi a rabu lafiya. Asiya ta ce to Allah ya sa a rabu lafiyan lamarin Abban ne akwai wahala **** A ranar Abba bai dawo gida da wuri ba sai kusan goman dare yayin da tun bayan sallar isha'i aka aiko ana sallama da Rabi'atu. Ummi ta rike baki ta ce Oh yau na ji abinda ban taba ji c waye ya samu nasara a kanki Rabi'a. Fatima ta ce wlh ummi wani bakin mutum ne ya ganmu dazun a sahad store ya ce yana sonta ta yi mai kwatancan gidan nan dan kawai ta sa Abba ya zo yana fada, da ganinshi kuma kinga talaka... Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Launin Fata 1-03 Posted by ANaM Dorayi on 01:09 PM, 04-Oct-15 Under: Launin Fata Ummi ta zabga mata harara ta ce to sai me dan talaka ne kuma baki? Na sha nuna muku cewa akidar da mahaifinku yake kai ba akida ce ta gaskiya ba. Tashi kije ku gaisa Rabi. Rabi ta mike sanye da hijabin da ta yi sallar isha'i ta fito kofar gidansu inda ta iske shi yaune akan farin mashin din (vespa) ta dan rusuna ta gaidashi ya amsa cikin fara'a ya ce ba ki tambayan suna na ba Rabi'atu. Tayi murmushi ta ce na san zaka gaya min ba sai na tambaye ka ba. Ya ce haka ne to sunana Tahir sunan mahaifina Al-amin, mahaifiyata kuwa sunanku daya Rabi'atu shi yasa kika kara shiga raina. Sai dai Allah ya yi mata rasuwa tun ina da shekara 5 a duniya na girma ne a hannun kakata wadda ta haifi mahaifina. Shama shekararsa daya kenan da rasuwa sai kannansa da yayyansa da muke tare da su gida daya kowanen da iyalansa, kasancewar gidanmu babban gida ne sosai. Ta ce Allah sarki Allah ya jikansu. Yace Amin na gode Rabi. Ta ce ina jin tausayin maraya rashin iyaye yana da ciwo sosai ko don ni ina da kwalafuci da son iyaye ne? Ya girgiza kai ya ce E haka ne Rabi'atu iyaye suna da shiga rai kinga ni ban san mahaifiyata ba, lokacin da Allah ya karbi rayuwarta ban yi wayon da zan tantance da ita in shaku da ita ba amma duk da haka zuciyata tana matukar sonta, idan naga mai sunan ta sai inji ina kaunarta ina bata girma na musamman. Lokacin da idanuwana suka yi arba da ke dazun na yaba sosai da yadda na ganki cikin sutura ta mutunnci har na dinga tunanin ko ke matar aure ce ke, direbanku na tambaya cikin hikima ba tare da ya gano manufa ta ba ya shaida mini cewa ke ba matar aure ba ce jikina a sanyaye na nufo ku na yi muku magana duba da yanayinku kufini karfi talaka kamata ya doshe ku da batun soyayya to amma abin mamaki sai zuciyata ta kasa juriyar kyale ku ku tafi na tabbatar in har kuka tafi ban yi muku magana ba na yi wa kaina ganganci. Duk da cewa bani da tabbacin zaku saurare ni, bahaushe kance da rashin kira karan bebe ya bata haka na daure na karfafi zuciyata da add'ar neman nasara ban taba zaton zaku saurareni ba sai gashi kun saurare nin, har sai da na dinga tunanin ko dai mafarki nake yi ne? Kalaman tahir suka dinga ratsa gabban jikin Rabi tana tsoron dawowar babanta bakinta ya mata nauyi ta kasa yi mai bayanin da ta fito da shi a bakinta, lokaci guda tausayi da kauna suka yi tasiri a zuciyarta suka dan jima suna hira bai tambaye ta matsayinsa a zuciyarta ba saboda fargabar amsar da zata ba shi. Ya yi mata sallama ta koma cikin gida tana murna Abban bai dawo ya iskesu ba. A falon ummi ta iske Asiya da ummin suna hira ta zare hijabinta ta zauna, Asiya ta ce in ce ko kin mai bayanin ba zai samu aure a irin gidan nan ba?Rabi'a ta waiwayo suka hada ido ta ce tahir ya bani tausayi sosai ban mai wannan bayanin ba. Asiya ta ce kada ki bari ba zuciyarki ki wahala a banza Abba ko ya sha giyar wake ba zai yarda ki auri bakin mutum ba ko da yana da kudi kuwa. Ki dubi mijin anti nafisa fari ne kal kai kamar a taba jikinsa jini ya fito, babanshi ne kawai baki amma da kyar abba ya yarda da auransu kuma dan yaga irin wanda yake so ne, bai san ciwon kudi ba in banda haka da bai bashi ita ba. Ummi ta ce watan wata rana fa dole abba ya ga sauyin da baya son gani a gidan nan. Rabi ta mike ta shige daki. Tahir ya kamu da son rabi soyayya mai tsananin gaske ta yadda har yake jin kamar in babu ita ba zai iya ci gaba da rayuwa ba son da ya shige shi mai karfin gaske ne, cikin kwanaki 2 rayuwarsa ta sauya zuwa tunanin mai wahalar da zuciya. Yanayin Rabin da yake so yanayi ne na mata masu tsadar gaske yanayin gidansu tun daga get zaka fahimci ba gida ne na zuwan talaka baYa yi mamakin yadda ta karbe shi kamar ya isa ya zo neman auran nata bayan shi kansa ya san bai isa komai ba. Tahir ya tashi a cikin maraicin uwa bai samu kulawa sosai ba kasancewar yana da mahassada da yawa ta bangaran matan babansa kafin rasuwar baban nasa a dalilini suna ganin baban nashi na sonsa fiye da dukkan yayansu shi kuma maraicin tahir din yake dubawa da nutsuwarsa, tun tahir na dan karami yake fuskantar hassada daga matan ubansa da yan gidansu, haka dai ya rayu yau wuya gobe dadi, yayi diploma dinsa a fannin education a jami'ar bayero yanzu haka yana koyarwa a nan kano. Shekarunsa na haihuwa ashirin da bakwai, rayuwarsa na cike da nutsuwa da sanin abin da yake bashi da hayaniya da neman rigima, dai dai gwargwado yana taimakon kakarsa da ta rike shi da yan uwansa gun uwa. Tun da ya hadu da Rabi ya dauke ta ya manna a ransa yake jin jikinsa ba dadi yau da yake ba aiki da ya shiga dakin kakarsa hajiya yaya tana zaune kan sallaya tana lazimi ta idar da sallar walaha.Ya zauna kan wata tsohuwar kujera katako ya zabga tagumi sai da ta gama ta jawo wani dogon kofi da koko a ciki ta tura mai ta ce ban karbar maka kosai ba dan kar ya huce bari in amso maka gun tabawa yanzu. Ya dubeta a wahalce ya ce bar kosan nan yaya kokon ya isheni. Tayi mai wani irin kallo ta ce ban gane maka ba. Cikin yan kwanakin nan duk ka sauya ko ba ka jin dadi ne? Ya ce lafiyata lau yaya wata yarinya na gani ina so sai dai tafi karfina. Ta koma ta zauna tana kallonsa ta ce lokaci da dama na sha tuna maka cewa kai maraya ne, dan abin da kake samu na alcshinka zai isheka rayuwa idan har ka dauko dai dai da kai. Ya yi ajiyar zuciya ya ce yaya so ba haka yake ba? Babu ruwan so da mai kudi ko talaka ba ruwansa da mai iyaye ko maraya zai shiga zuciya ne an sanya ko ba sanya ba. Ta ce to shikenan yanzu ka san abin yi tunda kai da kanka kasan tafi karfinka, amma kake dada sonta, idan so cuta ne hakuri magani ne? Ya ce yaya hakuri ba ya yin tasiri ga zuciyar da tayi nisan shakuwa da soyaýar gaggawa irin wa6an. Ta ce idan hakuri bai yi tasiri ba wahala ta yi tasiri ko? Ta fice ta bar shi nan zaune bai san abin yi ba. Da yamma ya yi kundunbala ya kara nufar gidansu Rabi, yayi sa'a ya hadu da su ita da Asiya da Fatima a hanya sun dawo daga islamiya da fara'a sosai suka amshieshi, Asiya da Fatima suka yi gaba suka bar su tsaye a gun. Tahir ya ce Rabi'a soyayyarki ta rabani da duk wani zaman lafiya da nake da shi a rayuwata gashi kuma ga dukkan alamu ke ba ki san ina yi ba. Ta ce Ah haba yaya zaka ce haka? Ya ce dole in fada mana tun da baki amsa tayin soyayya, ita ba a binta a hankali idan kace zaka yi a bari ya huce sai ta zamo rabon wani ba naka ba. Tayi murmushi to ka dai yi hakuri da sannu zaka ji komai. Ya ce to hakuri ya zama dole tunda haka kike so a yi, Allah ya sa in ji Alheri.Suka jima suna ìra tana cike da fargabar kar babanta ko yaya Nura su zo su sameta ta yi sa'a har suka yi sallama ya tafi ba wanda ya zo. Tun shigowa gida ummi ta ce da ita Rabi ki sallami yaron nan kada wata ran Abbanku ya zo ya yi mai wulakanci. Asiya ta ce mini dan mutunci ne da ganinsa salihin mai kamun kai, bai dace Abba ya mai wulakanci ba gara ku rabu lafiya. A sanyaye ta ce ummi ni fa ina sönsa dan ni dan mutunci kawai nake so ba mai dukiya ba dukiyar da kake da ita ta isheni rayuwa har in taimaki wani ma, babu dalilin da zai kai ni kwadayin abin duniya guna wanda zan aura. Ummi ta yi murmushi ta ce inama abbanku zai barki ki tafi kan ra'ayinki da kin samu rayuwa mai kyau da kwanciyar hankali gidan mijinki. Yanzu ina amfanin rayuwar takaicin nafisa ke yi? Ko da yaushe ina jin tana bugowa Abba waya tana gaya mai matsalolin mijinta. Ba abinda ya ajiye sai shan giya da neman mata idan tayi magana ya lakada mata duka, abin da ya dame shi in ubanta yaje ya danne mai baki da kudi ya dawo? Kuma yayi kicin kicin cewa ba zata haihu ba bai son haihuwa, dan mutunci mai tarbiya zai yi haka? Duk wanda ya biyewa kyale kyalen duniya a aure sai yayi nadama wlh. Idan aka yi soyayya da aure a tsarin da shari'a ta zo da shi da aeini aka so juna saboda Allah aka auri juna saboda Allah, aka zauna dan Allah da manzönsa wlh ko babu da ko kwandala rayuwarku za ta yi albarka za ku samu zaman lafiya da kwanciyar hankali, babu wani abu da zai zamo barazana ga rayuwarku wanda zai hanaku kwanciyar hankali. Ba wani abu ne ke bani takaici ba ga auran nafisa neman matan da mijinta yake abin tsoron shine kada ya kwaso cuta tana zamanta ya zuba mata sun riga sun nuna mai kwadayinsu ita da abbanku har bai shayin ya takata dan ya san zai biya kudin takawar da ya yi mata. Haka yayanku Rufa'i shima bai da kwanciyar hankali a gidansa bai isa ya gayawa matarsa ta yi ba sai dai ita ta gaya mai ita da iyayanta, yana namiji tana mace ta ce lokacin haihuwa bai yi ba ya yarda a haka saboda duk wata duk wani abin bukatar rayuwa ana jifansa da wasu makudan kudade.An dora rayuwa kan tafarkin son duniya da kwadayi dadin da ake son a ji ya ki samuwa. Ina amfaninsa? Rabi'a ta yi tagumi ta ce ummi ba wani taimakoko da zaki iya yi mini Abba ya fahimci ra'ayina da nasu ya sha bambam? Ta ce uhum Rabi'a kin san halin sa da zarar na yi magana raina sai ya fi baci fiye da kowa sai dai addu'a. Bayan kwana 2 da yin wannan abba da Rufa'i da nura suka tafi kasar chaina shigo da wasu kaya kamfaninsu, za su yi watanni 3 a can, hakan ya baiwa Rabi damar cwa tahir damar zuwa gidansu duk lokacin da ya ga dama. Har falon ummi take shigo da shi a shirya mai abinci, su sha hirarsu sosai ta soyaya. Lokaci guda ta nuna mai tana sonshi zata aure shi, haka itama ummi ta yi na'am da shi Asiya ma tana kaunarsa a gun fatima da idris ne bai samun fuska a ganinsu ko ba ra'ayin rikau na abbansu tahir bai da matsayin da zai zo gidansu neman aure. Mutumin da ko

Chapter 2 of 12