Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
motar hawa bai da ita kuma malamin makaranta na kasa albashin nasa nawa ne da zai iya rike yar gidansu da ta saba da jin dadi ko ta wane fanni? Ko ma me ye dai ummi tayi na'am da tahir sai dai ko yaushe tana jan kunnen rabi tana nuna mata cewa kada ta sashi sosai a ranta abin da zai yiwu shi ake yi, abba ba zai amince da wanan yaron ba. Rabi ta ce ummi dan Allah ki daina karyar min da zuciyata a kan tahir, gwargwadon wayewa ta addini da ilimin addin yana da shi, haka ilimin zamanin ma arzikin na Allah ne ai. Ummi ta ce ba ni za ki gayawa haka ba bani ce mai faìmtar haka ba abbaku ya dace ki gayawa dan ni tun kan a haife ki na dade da fahimtar haka. Ina so ne ki ko yi yadda za ki hakura da Tahir tun kan Abbanku ya dawo yadda in ya dawo din ya rabaku ba za ki sha wahala da zuciyarki ba za ki saba. Wannan ita ce gaskiyar magana. Ta ce ummi ban san yadda zan iya sabawa da hakan ba, kamar yadda ban san sanda na fara son tahir ba.Shi kansa tahir din mamakin yadda ya samu karbuwa a gidansu Rabi'a yake, shi yana dari dari ganin matsayinsa bai kai ba Rabi ta nuna ya isa, tana bashi matsayin da yake ba shi mamaki, har fushi take in taga ya ki sakin jikinsa, wannan ya faranta mai rai yana ganin ya tsinci dami a kala bai san rigimar da take kwance a gidan su rabi ba. Ana ya gobe abbansu zai dawo daga chaina gida ya kacame da shirye shirye taryarsu anyi girke girke kala kala, ana sa ran da magariba zasu sauka a nan kano. Rabi da asiya anci ado za a taryar abba, asiya ta ce amma dai yau tahir ba zai zo ba ko? Kin ba shi dama kullum yana zuwa gidan nan kun yi mugun sabo da da juna ga lokacin rabuwa ya zo. Rabi ta ce tabbdijan ke kina tsamanin akwai wanda zai iya rabani da tahir? Asiya ta ce ofcourse ko yaya nura ba zai barki da tahir ba ballantana abbanmu. Ta jinjina kai ta ce da ace tahir ya ce zaizo yau ba zan hanashi zuwa ba shin nima ina bukatar ganin kaya na. Dan ko bai zo yau ba goben nan in Allah ya kaimu zan gabatar da shi ga abban duk abin da zai ce ya fada matukar aure zanyi tahir zan aura. Ni ba auran kudi zan yi ba zanyi auran soyaýa ne, tahir kuwa yana sona ne saboda Allah kullum fatanshi Allah ya nuna mai randa zan zamo matarsa. Asiya ta ce babu abin da ya fi adu'a muhimmanci, idan Allah ya kaddara taìr mijinki ne isar Abba ba za ta yi tasiri a kan ku ba. Ana idar da sallar isha'i jirgin da ya dauko su abba daga lagos ya sauka a kano, su asiya da Rabi da fati da idris da direbansu suna jiransu, kowa a gunsa yake kallo saboda masifar kyansu akwai daukar hankali, Abba ya dinga rungumar ya yansa daya bayan daya suka taho gida. Tun a hanya Abba ya jawo Rabi'a jikinsa ya ce nafisa ba ta zo ba ko? Ta ce ta yi waya dazun ta ce in Allah ya kaimu gobe tana hanya. Ya ce Rabi ke da Asiya kunyi babban kamu. Rabi ta firgita tace kamar yaya fa. Abba ya dauko wayarsa ta ha6u ya hasko hoton wani dan ubansun matasì dan gayu kamar bature ya ce wannan shi ne sultan dan waziri sarkin Alkahira ne, mahaifinshi mutumina ne sosai satin da ya wuce sun zo china sì sultan da mahaifinsa ya ga hotunanku a jakata ya nuna ki ya ce yana so, na ce na bashi. Yaro ne matashi dan gata shi kadai ne namiji a gun iyayansa babu duniyar da ba su mallaka ba, shi kuma abokinsa da suke tare mai suna nazir ya ce yana son asiya mahaifin nazir shi ne ministan tsaro na dukka kasar tasu. Gaba daya kan rabi ya yi dum zuciyarta ta yi bakikkirin da kyar ta amshi wayar da Abba yake nuna mata hoton sultan da nazir ta zubawa sultan ido, karyar mutum ya ce zai kushe sultan kyau dai na da namiji bata ga abin da ya ragu ga sultan ba sai dai tuni zuciyarta ta tsumu da tausayin tahir da kaunasa yadda yake nuna mata bai da wani gata sai na Allah da manzonsa, matsayinsa na maraya, bai dogara ga kowa ba sai Allah sai ita da zuciyarsa ke so fiye da kowace irin mace a duniya. Lokacin da suka iso gidansu ta mikawa asiya waya duk walwalwalarta ta koma ciki gaba daya jikinta ya yi sanyi. Ana zaune a falo suna cin abinci kowa na raha ban da ita, Abba ya gaji ya ce Rabi yaya na ga duk jikinki yayi sanyi? Ko ba ki son sultan ne? Ummi ta ce Ai abba bayan tafiyarku china ta samu wanda take so. Tun kafin maganar ta yi nisa ya fi kyau ka baiwa sultan fatima.Abba ya ajiye cokali ya bata rai ya ce A ina ta samu wanda ta ke so din? Kafin mu rabu da su sultan a china sai da muka gama magana fa yanzu haka wani satin in Allah ya kaimu za su zo nan kano su gana da su wani satin a daura aure a yi biki su tafi london inda sultan da nazir ke aiki, su kuma zasu ci gaba da karatu. Ummi ta ce to ai dama kama ta ya yi kafin ku sanya magana ka dawo gida ka tuntubi su rabin in suna so sun amince. Ya katseta cikin hushi ya ce saboda su ne suka haifan bani na haifesu ba, kenan bani da ikon in zartar da hukunci a kansu sai na yi shawara da su ko? To bari ku ji wadannan matasa 2 sultan da nazir banga wani abu na jin dadi duniya wanda ba su mallaka ba ba zan yarda in yi asararsu a gidana ba alhali su suka ce suna so ba tallarku na yi musu ba. Sun yi daidai da ra'ayina ba ruwana da kuna so da baku so zan aurar da ku garesu dan ni banga makusa a tare da su ba. Ke asiya kin ga nazir a waya kin amince da shi ko kema kina da wanda kika zabawa kanki? Kanta na kasa kamar tayi kuka ta tsani dabi'ar mahaifinta na kallafa rai kan abin duniya, duk da ace ma zai ba da su haka nan ne ba tare da ya nuna kwadayinsa ga abin duniya ba a zo ana wulakantasu a kan kudi da sauki bayan kudin nan kana da su ba rasasu ka yi ba. Sai da ya maimaita tambayar ta cikin nauyin baki ita ce na amince Abba ina son ku tayani addu'ar Allah ya sa son gaskiya yake mini ba son sha'awa ba, nima Allah ya sa in soshi so na tsakani ga Allah ba son abin duniya ba. Yaya nura ya fiddo ido ya ce ke wa kike gayawa haka? Ta ce ka yi hakuri yaya gaskiya daci gareta. Abba ya ce Asiya, nasir yana sonki da gaske karki damu. Ba ta kuma cewa komi ba ya waiwaiya ga Rabi ya ce to ke kuma fa, shin kin amince da zabin nawa ko zabinki zaki aura? Cikin makyarkyatar murya ta ce Abba dan Allah ka yi hakuri ka yafe min da a ce ban sawa zuciyata son wani ba zan amince da zabinka dan in samu albarkarka ina son tahir ka taimakeni ka barni in aure shi. Abba ya ce uhum Rabi'a da a ce babu fatima a gidan nan sai in dage sai kin auri sultan, dan ba zan iya amincewa in rasashi ba, wata garabasa ce ta zo mini, sai dai duk da haka ki sani zan amince ki auri zabinki ne idan ya cika sharadina idan zan bada diyata aure. Kun daf da sanin sharadin in Allah ya kaimu gobe ki kawo mini shi in ganshi in ya isa ya zamo surukina sai in baiwa sultan fatima ta kammala secondary din a london. In kuwa bai isa ya zamo surukina ba to kuwa ba makawa sultan ne mijinki. A dakinsu Rabi'a kuka take tana karawa, Asiya tace dama kin hakura da tahir, abba ba zai baki shi ba kar ma ki sha wahalar kawoshi ya wulakantashi a banza. Fatima ta ce Allah anti ni ban taba ganin kyawawan maza irin sultan din nan da nazir ba, a waya fa muka gansu ba a fili ba, ke kuwa me zaisa ki batawa kanki lokaci kan wani tahir? Rb ta ce abin da nake so ku gane shi ne so daban kyan halitta daban, ni son tahir nake kawai a karan kansa ba launinsa nake kallo ba. Syy ta sha bambam da abubuwan da mu tane suke kallo su so mutum. Ina matukar tausayi Tahir sboda ya kallafa rai akaina, ina son na aure shi sboda ya fi mini wadannan matasan da kuke gani kyale kyale ne kawai. Nafi hangowa kaina zaman lafiya da kwanciyan hkl a auran thr fiye da auran sultan. Ftm ta mike zaune ta ce Dan Allah anti Rb me ya sa baki sö sakin jiki ki mori yaruwa ne? Idan mutum bai mori lokacinsa na rayuwa ba sai yaushe? Asiya ta ce ina ma ba haka tsarin bab yake ba da shi ne zamu more, yanzu ina zancan wani morewa a tare da mu anan sai da mu dan a samu kudi? Rabi ta ce ni dai kam gobe zan kai tahir gaban abba.Asiya ta ce to kuwa ki kwana kina adu'ar ko abba bai amshi tahir ba kar ya wulakantashi ta ce Adu'ar ma za tayi tasiri ya amshe shi insha Allah. Sassafe rabi'a ta kira tahir a waya, ya daga aguje ya ce Ranki ya dade kin tashi lfya. Ta yi yar siririyar dariyar da yake mugun so ta ce lfy kalau tahir Abba na ne ya dawo daga chana jiya yana son ganinka dan na gabatar mai da maganarka a matsayin wanda nake son aura. Numfashinsa yayi kamar zai dauke dan firin cikin ganin Abbanki saboda wani salo ne na motsa soyayyar mu ta samu ci gaba. Abinda ya razanani shine da kika ce kin amince da ni a matsayin wanda za ki aura, wlh Rabi'a idan na kalleki na dubi yanayina sai inji na firgice hankalina ya tashi, sanin cewa ko ta ina aka biyo kin mini nisa da yawa, in banda Allah shi ne mai yadda ya so ta ina da matsayi irin naki zaki kamata ki ce kin amince za ki aura? Bayan kina sane da cewa ni ba kowa bane ba dan kowa ba ban ajiye ba ban ba wani ajiya ba. Ta ce ya isa haka At-tahir ka gama magana da kace Allah ne mai yadda ya so. Bayan azzahar ka zo kawai. Bayan sun aje wayar tahir rasa inda zaisa kansa yayi dan farin ciki wai shi ne zai mallaki kyakkyawar yarinya irin wanan. Ya shiga gida ya shaidawa hajiya yaya ya hasko mata hoton rabi a waya ita kanta....... Zaharaddeen Shomar Whatsapp number : 08168575100 Launin Fata 1-04 Posted by ANaM Dorayi on 09:22 AM, 06-Oct-15 Under: Launin Fata Tare da Alkalamin Rabi'at Abubakar Nasidi Ita kanta firgita ta yi ta ce kai tahir ina kai ina wannan balarabiyar 'yar? Wlh ka rufawa kan ka asiri kada ka dauko abinda yafi karfinka, ina ka ga kudin da zaka auri wannan yar, ina kaga inda zaka ajiye ta? Ya ce yaya wannan yarinyar tana sona za ta iya zama duk inda na ajiye ta. Bata da girman kai da son duniya zata baki mamaki in kinganta. Ta ce ni dai kam da zaka bi shawarata da ka hakura da yarinyar nan ka nemi daidai da kai ka aura. Ya ce yaya kiyi mini addu'a kawai ba zan iya rabuwa da yarinyar nan ba ko zan aure ta ta dinga tattakani ne. Yaya ta bishi da kallo yana jinjina kai. Karfe 2 daidai suna kofar gidansu Rabi'a shi da abokinsa Ibrahim. Gwargwadon halin da suke da shi da wayewarsu sunyi ado sun yi kyau suna ta kamshin turare. Ibrahim ya dubi gidansu Rabi'a ya ce anya tahir yarinyar nan da gaske tana sonka? Me kagani Ibrahm? Dubi fa gidansu kana da abinda zaka nemi aure a wannan gidan? Tahir ya yi dariyar nishadi ya ce Ibrahim lallai bani da kudin da zan kawo wannan gidan dan suna da komi. Allah da yake da kowa da komi shi ya sanya soyayya ta a zuciyar Rabi ba tare da na isa ta so ni ba. Ya ciro waya ya kirata ya ce gasu sun zo nan da nan ta fito ta ci uwar kwalliya da atamfa english ban iya bayyana kyan da tayi. Dole ne Rabi ta firgita duk wanda ya hada ido da ita tayi kyau matuka duk da cewa ta lullube jikinta da babban mayafi ta dauki rayuwa da sauki da yawa. Ta shigar da su ta falon baki na abbansu ta sanya musu abinci suka kwashi girki suna hira kana ta shiga cikin gida ta ce da abban ga tahir ya zo.Ya ce je ki shigo da shi nan. Abba na kishingide a kasaitaccen falonsa na cikin gida wanda ya fi kowanne falo a gidan. Tahir gani yake babu a kure a falon ummi da suke zama su yi hira ba da wancan falon na baki, yau da ya shigo wannan falon na Abba ai kauyanci suka nuna sosai shi da Ibrahim saki baki suka yi galala suna kallo duniya, tun daga nan Abba ya fara jan tsaki ya murtuke fuska. Jikin Rabi ya kara yin sanyi ta zauna daf da kafar Abba yayin da su tahir suka zube kasa suka gaidashi ya amsa a lalace ya mike zaune sosai ya ce ke wai ina taìr dinne kin zaunar dani kina bata min lokaci. Cikin in ina ta nuna tahir da yatsa ta ce ga shi nan. Cikin tsawa ya ce wa? Ya nuna shi da yatsa. Ta ce Eh shi ne Abba. Ya ce amma lallai sai yau na san baki da hankali da tunani. Ya maido idonsa ga Tahir ya ce kai yaro sunanka Tahir ko? Ya ce Eh abba suna na kenan. Ya ce waye mahaifinka a garin nan. Tahir ya dauko tariin gidansu tiryan tiryan ya fadawa abba. Abba ya ce idan ita Rabi mace ce tana da karancin tunani a matsayinta na mace mai raunin shekaru kai ya dace a ce tunaninka ya dara nata. Yanzu saboda Allah ka dubi kamar wannan da zankadediyar yarinya kamar wannan kana matsayi irin naka bakin mutum bakin ma kuma talaka ka ce kana so a baka ka aura? Na farko baka da gidan zama kace a gidan iyayanka na gado za a sammaka dakin zama, baka da ko motar hawa sai machine' kana koyarwa kana daukan albashi a wata a haka kake ganin zaka iya rike min wannan yariyar wadda abincin da zataci na kwana bakwai zai iya kashe albashinka na wata 3, ba wai dan yawan abincin ba sai dan tsadarsa,(Babdijan Abba kadau duniya dazafi, cewar ANaM) Kuma suturar da take sawa albashinka na wata shida ne zai iya sayan kala daya kana nan cikin ya san 2. Ballantana a gangaro motar da take hawa in zata fita wadda har ka mutu albashinka in zaka daina ci ka daina sha kana tarawa ba zaka iya saya mata motar da take hawa a gidan nan ba. Haka kayan kwalliyar da take amfani da su ba zaka iya saya mata ba. Ballantana a zo ga batun lafiyarta in bata da lafiya ina fita da ita ne kasar waje a dubata, babu asibitin da ya yi mini a nan kai kuwa ko a nan dinma asibitocin da ba zaka iya biya ba sun fi yawa. To ina ga in anzo raguwar bukatu na rayuwa. Ni kuma kaga ba zan yarda in saida akuya ta dawo tana ci mini danga ba. Yayana tun suna kanana nake kashe musu kudi in wadata su da abinci mai kyau, abin sha mai kyau, sutura mai kyau, makaranta mai kyau, asibiti mai kyau, makaranta mai kyau, asibiti mai kyau, mahalli mai kyau in shekara goma sha takwas ko ashirin ina wannan rana tsaka in dau yata in ba namiji da ba zai iya dorawa inda na tsaya ba? Sai dai ta koma ta ci baya a gidansa ko kuwa ni inci gaba da bata abin da ta saba rayuwa da shi a gidana? Ya girgiza kai impossible, kai kanka ka san ina da gaskiya saboda haka da Allah daga yau ki yiyaye Rabi'a ba sa'ar auranka ba ce ko ta ina. Na yi ma wannan bayani ne dan ita ta kawoka gabana a wautarta zanbi abinda take so. In da a kofar gida na ganka kamar kai bakin mutum talaka ka ce ka zo gidana neman aure da yau a kulle zaka kwana. Saboda kazo mini da rainin wayo. Tashi maza ka kama gabanka. Tunda tahir ya sunkuyar da kai yana sauraron Abba bai dago ba ko motsi bai yi ba sai da ya gama haka shima ibrahim tare suka mike suka ce mun gode Abba mun barka lfy. Ya bisu da kallo yana murmushi ya ce Allah sarki matashin kwai mai wautar karo da dutseRabi na zaune kan kujera ta kifa kanta a cinya tana jin cin fuskar da abba ya karewa masoyinta, tsananin kunya ya hanata dago kai tana ji su tahir suka fice daga falon, bata san me zata ce da su ba, kila tahir yace ta kawo su ne dan a wulakantasu dama dai ta san hakan ce zata faru. Abba ya sa hannu ya dago kanta ya ce Rabi ni kam kin bani mamaki dan Allah ina ke ina wannan bakin mutumin? Shin kina duban kanki sosai kuwa? Ki dubi baiwar kyakkyawar haliuar da Allah ya yi miki amma ki lalace gun wannan yaron? Da bakinsa fa ya ce mini bai da gidan kansa in na bashi ke a gidan iyayansa zai zauna bai da motar da zai dinga kaiki in da zaki in bukatar fita ta taso. Haba Rabi'atu duk abinda kike so zai iya yi miki ki lalace gun wannan? Ta fashe da kuka ta ce Abba wai shin wake ba da arziki ne in ba Allah ba? Akwai wanda aka haifa da arziki? Ko kuwa akwai wanda zai tafi lahira da kudi? Kowa a nan duniya ya samu kuma nan zai barsu. Rabon bawa da arziki mutuwa, babu mai fidda rai da rahamar Allah, Allah shi ne mai bayarwa Abba. Abba ya ce uhum wannan wa'azin da kike mini na nufinin ke dai kina nan kan bakanki kina son tahir ko? Ta ce dan Allah ni dai ka yi hakuri ka taimakeni ka bani shi ina sonshi. Ya tsuke fuska ya ce Rabi'a in har kina son zaman lafiya ki daina batun wannan yaron. In har kinga kin aureshi sai dai bayan raina ko kuma kin gujeni saboda shi kin bar gidan nan amma ba da yawuna ba. A kofar gidan su Rabi ya tsaya ya rike kai da hannu idanunsa sun yi jazir ya ce ibrahim ya ya zanyi da son da nake wa yarinyar nan ne? Ibrahim ya ce yaya za kayi kuwa ban da ka hakura? Ka taba ganin an yi hakuri da soyaya Ibrahim? Tahir ya yi tambayar cikin yanayi na tanyin kai da karaya. Ibrahim ya gyada kai ya ce eh kwarai kuwa soyayya kuwa ita ce a kai hakuri da ita dan kuwa ba ta da magani sai hakuri. Hausawa ma kance. In so cuta ne hakuri magani ne.Bai da ce ka bari maganar nan ta dame ka ba. Ni da kai mun san haka na iya faruwa idan ka kalli Rabi da gidansu da yanayin rayuwar da suke ciki zaka tabatar gaskiya mahaifinta ya gaya ma? Cikin abinda ya lissafa wanne ba haka ba? Saboda haka ina baka shawarar ka hakura da Rabi'a ko misali ya baka da wahala albashinka ya rike ta. Maganganun ibrahim na kara dagawa tahir hankali ya ce mu tafi kar zuciyata ta buga. Dakin ummi ta shiga ta isketa ta idar da salla ta zube a gabanta tana kuka ta gaya mata wulakancin da abba ya ma tahir. Ummi ta aje carbi ta ce wannan kenan da kike bata hawayenki kike a banza kan abinda kinfi kowa sanin faruwarsa. Ta ce ummi ni yaya zan yi ne? Ummi ta ce hakuri mana? Sanin kanki ne fitina ce babba in har kika ce zaki yiwa abba gaddama. Ta mike ta shige dakinsu Abba kuma ya shigo da bambami ya ce maryam kece kika baiwa Rabi damar tayi soyayya da irin mutanan da kun san bani ra'ayin su ko? Ta ce duk sun zuciyar mutum ya san wani bai da ikon cusa son wani a zubiyar wani sai yadda Allah ya nufa bai ki ba ka iya bada shawarar a hada wane da wance aure, Allah ya sa soyaya a tsakaninsu duk da haka in sun so juna baka isa ka ce kai ne ka sa musu son junansu ba kowa ya san hukuncin Allah ne. Abba ya ce to naji ba kece kika sa sonta a zuciyarta ba amma dai kece ganin bana nan kika bata damar sauraronsa har ta shaku da shi take ganin ya dace ta aureshi alhali kun san ko na sha giyar wake ba zan yarda in ba shi ita ba. Ta ce Alhaji auran fari shari'a ta yarda iyaye su zabawa yayansu mijin aure. Amma shari'ar ba ta haramtawa yar ta kawo wanda take so ba matukar an yarda da sana'arsa da addininsa saboda gaskiyar magana ni bani tare da kai kan wannan bahagon ra'ayin naka' tana son shi, shi ma yana sonta yaro ne mai mutunci mai kamun kai, ya mallaki abinda masu kudin ba su mallaka ba. Ya ce ke da Allah rufe mini baki kin yi aikin banza ke da ita, ko da aka kula soyaya bana nan ai yanzu na dawo kuma an nemeni idan an isa a kaita gidansa ba da sa hannuna ba mana kara kawo mini zancan wannan yaron daga yau na soke shi a gidan nan in ba haka ba za ku fuskanci bacin raina. Na bawa sultan Rabi dole shi zata aura baku isa ku bata mini tsari ba. Tsakiyar dare Rabi ta kira tahir a waya yana jin muryarta ya yi wata boyayyar ajiyar zuciya mai dauke da damuwa ya ce Rabi me ya hanaki bacci har yanzu? Abin da abba na ya yi maka banji dadi lamarin ba. . . Ya katse ta daina bani hakuri dan kuwa ba laifi yayi mini ba gaskiya ya gaya mini, ya tunasar da ni abin da tunvni na san da shi makuwar soyayya ce ta sa ta kasa yin tasiri a zuciyata in ankarar da kaina hakan. Rabi'atu hakika bani da kalmar da zan iya yi miki godiya da ita saboda kin bani matsayin da ban kai shi ba a zuciyarki. Wanan kadai ya isa yasa in ci gaba da ganin girman mahaifinki ba zan kullaceshi a zuciyata ba, saboda ya haifo ya mai mutunci mai daraja wadda tasan abin da take. Rabi'a a rayuwa irin tamu da yadda zamani ke tafiya da mu samun mace kamarki wadda ta kai matsayi irin naki ta saurari namiji mai matsayi irin nawa zai yi wahala. Duk abubuwan da abba ya lissafa ba zan iya rike ki da su ba haka yake' babu uban da zai so yarsa tana cikin jin dadi ya kaita ga wahala. Idan jin dadin bai dara na gidansu ba to bai dace ya yi kasa da na gidansu ba, ke wadanda ma basu da halin wadata yayansu da abubuwan jin dadin rayuwar fatansu su kai yayansu in da zasu huta. A duniya babu wanda bai son ya ji dadi sai dai in bai samu ba. Rabi'a ta ce tahir bana son wadannan maganganun naka, kara bata min rai suke zamu auri juna tunda muna son juna insha Allahu a duniya babu namijin da nake son aura sai kai, kuma kai din zan aura,dame zan auri ya irinki? Ke daga baya fa nima naga wautata, ko ba a gwadaba linzami ai yafi karfin bakin kaza. Ta ce tahir idan ka fasa aurena ne ka gaya mini? Duk maganganun dai a kaina ake kuma na ce naji na gani ka daina damun kanka. Ya ce Rabi'a ki dubi yanayin rayuwarki tana da nisan gaske da tawa. Ta ce da can baka san da hakan ba kace kana sona kana son mu yi aure ka cusa soyayyarka a zuciyata a lokacin da ban taba soyayya ba ban taba san wani namiji ba. Ka amince da abinda na gaya ma kawai (ta kashe wayarta). Shi da ita babu wanda ya yi barci a ranar kowa tunaninsa daban ne da safe ta shiga dakin ummi suka gaisa ta ce ummi ina son ki taimakeni daga auran miji irin na yaya nafisa, zuwa auran mijin da zai dace da rayuwata. Ummi ta ce Rabi'a bani da karfin da zan yi haka ko da kuwa ba irin wannan ra'ayin ne da babanku ba ina son ki kyautatawa sultan zato ba duka aka taru aka zama daya ba, masu dukiya da yawa mutanan arziki sun wa addini hidima sosai a zamanin manzon Allah (S A W) sayyadina Abubakar saddik (R A) Mai dukiya ne shi ne wanda aka ce da za a tara imanin duk mutanan duniya ba zai kai rabin imaninsa ba haka Abdulrahman bin Auf (R.A) mai dukiya ne shi ne sahabin farko na sababbai goma da aka yiwa albishir da alanna tun suna duniya. Kasancewar sultan mai dukiya ba shi ke nuna bai da kirki ba, akwai talakan da ga talauci ga shi bai da hali na gari ga girman kai bai ba komai fa sai munin hali. Dan kabir mijin nafisa ya zamo haka bai yiwuwa a ce sultan haka yake. Abin da yasa kika ga nima ina kalubalantar lamarin halayyar da Abban naku ke nuna wa ce bana so. Komi girman ka a idon mutum matukar ka nuna ka damu da abin hannunsa ba zai ci gaba da kallonka da daraja ba. Ance idan kana son Allah ya soka to ka guji duniya. Idan kana son mutane su soka to ka guji abin hannunsu. Wannan ita ce gaskiyar magana mama dai wane taimako kike so in yi miki. Rabi ta gyara zama ta ce yawwa ummi so nake ki taimakeki ki sayawa tahir gida ki bashi mota kudin da yake dan tarawa zai sayi nasa gidan sai ya yi hidimar neman aure na da su, nima zan sai da duk golds dina in ba shi kudin ya ba Abba tunda dai Abba kudi ne kawai a gabansa ba mutunci ba. Ummi ta yi shiru kanta na kasa zuwa can ta ce Rabi'a

Chapter 3 of 12