Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels LAUNIN FATA Littafi na daya 1 Rabi'atu Abubakar Nasidi Ebook creator:- Shuraih Usman @http://fb.com/hausaebooks Showing posts filed under Launin Fata Launin Fata 1-01 Posted by ANaM Dorayi on 10:04 AM, 03-Oct-15 Tare da Alkalim Rabi'at Abubakar Nasidi Fatan zaku karance da Dan Uwaku ANaM Dorayi Falon ya yi tsit gaba daya iyalan gidan na ciki kowanne kansa a kasa suna sauraron abinda zai ci gaba da biyo bayan bambamin da dattijo sir Abdulkareem baba ke zazzagawa diyarsa Rabi'atul Badawiyya wadda ke durkushe a gabansa rungume da yarinyar goye da bata wuce watanni goma ba a duniya. Ya ci gaba da fadin na taraku ne a nan don ku zama shaida kamar yadda na taraku a baya kuka zama shaida a kan abinda na gayawa Rabi ko ba ayi haka ba? Sai da ya maimaita tambayar babban cikinsu Rufa'i ya ce an yi haka Abba, duk da haka muna baka hakuri..... Ya daka mai tsawa tunda ka tabbatar mini an yi haka bani bukatar a bani wani hakuri dole a yi abinda na ce. Kar bi wannan bakar 'yar da ta zo mana da ita ta rakaka har inda ta yi auran ta mayar musu da 'yarsu. In ba haka ba wannan bata zama min gida. Ya juya har ya kai bakin kofa ya dawo ya ce kar in dawo in samu yar nan a gidan nan ran kowa zai iya baci idan ba a yi abin da na ce ba a kiyaye. Yana fita Rabi ta dora hannu aka ta fashe da kuka ta ce ni na shiga uku, yaushe zanji dadi ne a duniya. Yarinya yar watanni goma za a kai gidan daba a kaunata ni kaina ake ba? Gidan da wahalarsa ta sa na fito ba dan bana son mijina ba. Wacce irin rayuwa za ta yi a gidan wannan yar. Ko shakka babu ba zan bada yata ba a kai ta gara in hakura da zaman gidan nan. Mahaifiyarta ta taso cikin tausayawa ta ce Rabi rayuwa fa Allah ce duk wanda Allah ya nufa zai rayu babu wanda ya isa ya hanashi rayuwa. Ke ko duk duniyar nan zata hadu a kan bata son rayuwar wani idan Allah ya nufa rayayye ne zai rayu. Ci gaba da kafiya ga mahaifinki abu ne da zai ci gaba da kawo illa ga rayuwarki ba zai bari ki samu nutsuwa da walwala ba. Idan kika yi hakuri Allah ya ji kanta ya kaita hannu na gari ki tuna rayuwarki ba itace rayuwar wannan yarinya ba, idan kin dage sai kin rayu da ita sai Allah ya karbi rayuwar taki ta kuma ta na raye tunda rayuwar ta Allah ce rai da yake jikin mutum kayan aro ne, duk wanda wa'adi ya cika mai shi zai karbi abinsa ne kiyi yaya.Rabi ta kalli diyar ta nono na bakinta, baiwar Allah bata san abin da ake yi ba tana barci ta dagata ta rungume kam kam tana kukan da ya baiwa kowa tausayi ta ce nabila zan bada ke ba dan raina ya so ba sai dan babu yanda zanyi ina fatan Allah ya kaiki hannu nagari wanda zai tausaya miki dangin babanki basa kaunata na san kema ba zasu kaunaceki ba amma na san rayuwa ta Allah ce.wannan jarrabawa ce wata rana lbr zata zama, domin babu wani abu da ya taba dawwama dadi ko wahala. A hankali ta maida ita cikin zanin goyonta ta mikawa yayanta Rufa'i ya karba ya rungumeta a jikinsa a sanyaye. Ya ce ki yi hakuri Rabi dole ne komai girman da uwa bata son rabuwa ballantana yarjaririya kamar wannan. Allah yana sane da halin da kike ciki shi ne mai magani zai miki magani kin sani babu yadda za mu yi da maganar Abba in banda haka ba mai rabaki da yarki a yanzu. Ta zaro yan kayan nabila daga cikin nata ta kulle a leda ta dauko wata yar sarka ta azurfa siririya ta rataya mata a wuya ta mike ta shigo daki ta kwanta. A wannan lokaci fatanta mutuwa kawai ta zo, nono na zuba hawaye na zuba dan tsanani sai ta kama karanta adu'ar. Allahumma la sahla illa ma ja'altahu salha wa'anta taj alul hazna iza shi'ata sahla. A hankali sai barci ya dauketa zuciyarta dauke da tunanin baya ASALIN ALHAJI ABDULKAREEN BABA LABARAN Dan kasar yamen ne, ya zo Nigeria dalilin kasuwanci, tun yana zuwa ya koma har ya dawo da iyalansa gaba daya ya gina gidan shi a kano suke zaune a wanan lokaci yayansu uku. Hajiya maryam itace matar tasa muhammad Rufa'i shine na farko sai nafisa sai muhammad narardin, wadanda ta hafa a can na nan wadda ta fara haifa itace Asiya sai muhammad Bashir sai Rabi sannan fatima zahra sai idris dan auta da suke cewa khalifa. Duk inda mace mai saukin kai da hakuri ta kai hajiya maryam ta kai, ko kusa bata dauki duniya da zafi ba, tana tafiyar da rayuwarta cikin sauki, yayin da mijinta Alhaji Abdulkareem yake mafadacin gaske, babu hakuri a harkarsa, duk wanda yake tare da shi ya san wannan. Tun daga kan makota da abokan huldarsa a kasuwa ballantana iyalinsa. Ya shigo Nigeria da kafar dama bai jima ba ya shiga sahun masu kudin da ake fadarsu a duk fadin jihar kano. Alhaji abdul mutum, ko abokan harkarsa a kasu sai larabawa yan uwansa. Saboda yadda ya tsani bakar fata ko mi son da yake wa abu in har a gun bakin mutum zai saya to ya hakura. Zirga zirgarsa tsakanin Ngr da kashashen lrbw irin su Sudan, saudi arabiya, egypt da malaysia da can kasarsa yemen da sauransu. Duk karshen sati ya kan tara iyalinsa kaf a gana hirar tuna baya a yi raha ayi addu'o'i ga wadanda suka mutu a ci a sha, kafin a tashi gargadin da yake musu shi ne baya son hulda da talaka. Baya son hulda da bakin mutun idan sun kaucewa wanan za su zauna lafiya da shi. Idan ba haka ba zasu gamu da hushinsa wanan huduba bata yiwa hajiya maryam dadi tana ganin kuskure ne babba yake dorasu a kai. Talaka da bakin mutum duk Allah ne ya halicce su bata isa tayi mai musu ba saboda masifarsa gaban yayanta sai ya iya rufe ido ya ci mata mutunci ba damuwarsa bane. Dan haka duk lokacin da ya gama nashi hudubar ya tashi in gari ya waye zata tarasu in bai nan ta ce da su Yanda nake matsayin mahaifiyarku a gunku nake da hakki kuyi mun biyaya akan duk wata hanya da nake son kubi matukar ba ta kaucewa hanyar Allah ba haka mahaifinku yana da hakkin kuyi mai biyayya. Sai dai bana jin dadin muguwar da bi'ar da yake doraku a kai. Ko wannenku a anan yasan Allah ne ya halacci mai kudi ya halacci farin mutum ya halacci baki, duk mai hankali da tunani ba zaiki wani dan bai da dukiya ba, ba zaiki wani don bai da farar fata ba. Watarana rufa'i ya kada baki ya ce da ita ummi idan bamu bishi ba yaya zamuyi? Sanin kankine gaba dayan mu karkashin sa muke da zarar mun kaucewa abinda yake so sai ya wulakantamu ya kore mu. Itama Rabi ta sami bakin magana ta ce ummi wlh nima raina ba karamin baci yake yi ba in naji abba yana fadar haka sai in dinga ganin kamar ba magana bace irin ta dattijo mai ilimi wanda yasan abun da yake yi ba. Nafisa ta ce to wai me akeyi da talauci, annabawa ma da sukafi kowa daraja agun Allah naiman tsari sukeyi da shi balantana mu? Ni banga laifin baba ba dan ya ce mugujewa talaka. Ai nufinsa mu diyansa ne mata kada mu dauko mai talaka. Haka ku maza kada ku dauko mai aure gidan talakawa, yanda yake mai kudi yafison harka da daidai shi, kwarya tabi kwarya. Idris ya tabe baki yace nima haka dai naganiNura ya ce to ma in banda abinsu gida kamar namu yadda abbanmu ke kashe mana kudi gun cin abinci mai kyau mu sha mai kyau suturu da kayan ado masu kyau, amma sai mu lalace a auren talaka? Haba in anyi haka ai anci baya, ina amfanin shuka idan ba a yi girba ba? Abba ya sha gaya mana cewa yana kashe kudinsa a kanmu ne dan mu zame masa riba, idan mun tashi aure mu na da tagomashin da zamuyi tsadar da zamu auro mata masu tsada a gida mai tsada. Ku kuma mata duk wanda zai zo auranku ko kallon fatarku yayi ya san an kashe muku kudi dole sai yana da kudin da zai iya daukarku idan wanan bai samu ba ina amfanin kudin da yake narkarwa a kan mu? Rabi a ta ce kai ni a ganina wannan ba tunani ne mai kyau ba yaya nura, ni dai a guna talaka da mai kudi duk daya ne, don a Alkur'ani mai girma Allah ya ce babu wanda yafi wani a cikinku a gun Allah sai wanda ya fi tsoron Allah. Duba da wanan ayar za ku ga cewa fifiko gun Allah shi ne abin nema a rayuwar mutum ba zai samu wannan fifikon ba kuwa sai ya kasance mai tsoron Allah. Fifikon jinsi ko yare ko dukiya ba sa amfanarwa mutum komai a ranar lahira matukar bai bi Allah ba. Nafisa ta zabga mata harara ta ce to sarkin wa'azi sai ki dauko duro ki hau ki yi ta yi. Muhamma Bashir ya ce kyaleta ta fadi ra'ayinta kowa ba ra'ayinsa yake fada ba. Fatima ta ce ni dai ba ruwana duk wanda Allah ya bani ina so in mai kudin in talakan mi dai nafi son in yi auran soyayya ba auran kudi ba. Babu wani kudi da zai tsolewa gidan nan ido mu da abbanmu ke buf mana dakin kudi mu debi yadda muke so mu yi abin da muke so. To wane kudi zamu je kwa dayi a gidan wasu? Rufa'i ya ce daga randa abba ya ji kina cewa in mai kudi in talaka kin daina cin kudinsa dan ba a banza yake buf muku dakin kudinsa ba yana son ya fanshe ne a gaba. Ummi duk ta gama sauraransu ta gyara zama tayi murmushi ta ce a takaice dai nafisa da nura da Rufa'i ra'ayinku daya in har zan gaya muku kuji ku sauka daga ra'ayin mahaifinku dan ku zauna lafiya. Gidan kyawawa ake kiran gidan tun daga titi ka tambaya inkiyarsu kenan, kowanne na takama da kyau na a gayawa duniyar farare ne kai kai kamar a taba jikinsu jini ya fito, duk wanda ka gani sai ka zata yafi duk yan gidan kyau sai kaga wani sai kaga yafi shi kyau. Babu abin da ya damu umminsu da cin buri a kansu, rigimar tana gun abbansu wanda ya dau burin duniya ya dora musu kamar shi ne ya fara haihuwar yaya masu kyau. Mutanan unguwarsu kaf sun san dabi'arsa ta girman kai da daukan dan adam ba a bakin komai ba shi yasa basa ma shiga harkarsa gaisuwa ma sai sama sama. Duk abinda aka gaya mai ba zasu je baba zai bar matarsa ta je ba haka diyansa . Hajiya maryam na son hulda da mutaner yaki yarda duk randa yaga wani bakuwar fuska a gidannsa sai ya kare mata cin fuska tas a gaban bakon dole ta hakura c mai shiga gidanta ita c ta zuwa gidan kowa a matkotan sai gidajan abokanan sa masu kudi dai dai da su. Abin yana mata ciwo sai dai da yake babu yadda ta iya, fadan da yafi karfinka sai ka mai da shi wasa dan ka zauna lafiya. Rufa'i na da sassaucin ra'ayi akan ra'ayin mahaifinsa a boye yana hulda da ckaken talakawa a makaranta har yanata bakake yana yi saboda ra'ayinsa na kashin kansa yafi sha'awar mace chaculate colour ba fara kal ba. Nura shi ne mai ra'ayin rikau irin na mahaifinsu shi yasa suka fi daidaitawa yafi sakar masa kudi nura dan duniya ne dan fafa na gani kasheni a dinka sutura a hau mota ana zaga gari idonsa ya bude sosai da bariki duk wannan bai damu mahaifinsu ba tunda dai bai jajibo mai talaka da bakin fata ba an gama haka nafisa yar lelen abbansu ce tafi kowa iya jin kai da yanga a gidan dukansu suna da kyaun ta ya hadu da gayu idan ta dau ado ta shiga mota tana tukawa kai kace tauraruwa zahra cikin taurari haka take zama cikin sauran mata karya ne nafisa ta wuce guri ba ta ja hankalin mutane an maida hankali ga kallonta ba. Fatima ke take mata baya a nan inda halinsu ya bambanta shi ne fatima bata tsani talaka da bakar fata ba jin kansu dayanga ne iri daya.Masu halayyar mahaifiyarsu a gidan Rabi da Asiya suna adawa karara da Nafisa Bashir da irdis ra'ayin ba ruwanmu ne .. .. Rufaida da nura sun gama karatun su ne a malaisia sna aiki a nan kano duk karkashin kamfanin abbansu a baya musu rowar kudi duk abinda iyalan sa ke so an gama, matsalarsa daya fada shima sai ka saba masa. Kai tsaye a iya cewa basu da matsala a rayuwa ta fannin kudi dai kam. Sai a wannaan shekarar akayi auran Rufa'i da irin diyar da abba yake so, diyar kakadan a karasu ta yemen a nan Nigeria, gata farar fata ga uwa uba dukiya. Sunanta zainab suna mugun sö juna ita da rufa'i haka iyayansu na son hajiya maryam ce kadai yarinyar bata kwanta mata a rai sosai ba. Saboda lokacin da aka fara maganar auran sai rufa'i ya dauko ya kawota dan ta gaida iyayensa. Hajiya maryam na zaune a kan kujera a falonta suka shigo suna manne da hannun juna shi da ita har shi rufa'in na dan jajjanyewa saboda kunyar umminsa ita kuwa zainab ko a jikinta sai dada mannewa take a jikinsa tana shagwaba. Rufa'i ya zauna kan kujerar zaman mutum 2 sai ta zauna a jikinsa ta lankwashe a kafadarsa a haka ta gaida ummi. Haushi ya kama ummi ta mike ta bar musu falon, har zainab ta nunawa Rufa'i rashin jin dadinta da haka ya ce kar ta damu kunya ce da umminsa saboda shi dan fari ne. Suka bar maganar a haka bayan ya kai zainab gida ya dawo ummi ta dube shi ta ce wannan yarinyar itace irin yayan da abcnku ko yaushe yake burin ku auro saboda farar fata ce kyakyawa, kana iyayanta na da kudi kuma sanannu mutane ne bai damu da cewa tana da tarbiyya ko babu ba. Yaya tarbiyar gidansu da iyayanta suke? Shi fari da dukiya kadai ya dame shi wannan kuskure ne da ba za ka fahimce shi ba sai nan gaba. Rufa'i bai faìmci abinda ummi take son ya fahimta ba saboda son da yakewa zainab, dan haka ya share batun ummi ya ci gaba da harkokin gabansa.Lokacin da aka yi daurin aure da biki abbansu ya gina mai gida na kece raini a tsadadiyar unguwar nan Nasarawa GRA da sai masu kudin gaske ke iya zama a cikinta. Ya ce kuma kada a kawo zainab da ko allura sun gama shirya gidansu. Amma ina sai mahaifin zainb ya ce tuni ya gama shiryawa yarsa gida da komai ango ne zai biyota gidanta dake sultan road duk a kano. Su yi hakuri haka tsarinsu yake gida ne na bada labarin kyansa da tsaruwarsa ba zai taba yiwuwa ba an kashe kudi iyaka. Duk saboda buri da son duniya wannan bai damu Abba da rufa'i ba suka bi a haka, ga gidansu ga komi ya bi zainab gidanta bayan an gama biki an kaita. Wannan ma ya bata ran ummi amma ba ta ce komai ba ta sa musu ido. Matsalar zainab ta farko da rufa'i ya fara fuskanta bata iya komi ba sai soyayya. Yar gata ce yar shagwaba da ma tun ran da za a kawota har gida ubanta ya kirashi ya ce to fa shi yarsa ba ta saba da wahala ba, kuma tattalin farinciki ta ake a gidansu dole ya dora a inda suka tsaya. Ita kadai ce diyarsu mace suna sonta fiye da zatonsu. Sun bashi i ta ne don ta nuna shi take so fiye da kowane namiji su kuma ra'ayinta shi suke bi. Basu son diyarsu ta shiga wata matsala dole ne ya kiyaye da wannan tun daga wannan lokaci jikin rufa'i yayi sanyi ya jiyo kamshin gaskiya a maganganun mahaifiyarsa da tace aure a gidan tarbiyya ya fi aure a gidan dukiya tarbiyya ita ce zata dore dukiya fararriya ce kararriya. Bai gaya mata yadda suka yi da iyayen zainb sai abbansu ya gaya mawa, shi abban ya rufe shi da fada ya ce ni bani son irin wannan korafin menene a ciki don sun ce yarsu yar gata ce? Shin ba yar gatan bace? Idan c yar gatan ce ba ma ba zata dace da kai ba. Rufa'i ya tafi a kan haka bai fara gane kuranshi ba sai da zainb ta yi sati 2 a gidansa kullum umminsa ke aiko direba da abinci safe da rana da daddare, zainab bata san komi ba sai dai ta ci ta kwanta hatta pant dinta shi ke wanke mata tun randa ya zo ya iske mai wanki na shanyar pant da bra dinta a harabar gidan ran sa ya baci sosai ya ga ina mai wanki ina ganin sirrin matarsa?Da ya yi mata magana sai cewa tayi bata iya wanki ba ko a gidan su wanke mata ake yi, ala dole ya shiga wanke mata da kansa duk sanda ta yi wanka nan zata bar mai a toilet ya wanke ko da kuwa da jinin haila a jiki. Wannan lamari ya dagawa Rufa'i hankali ya HUrasa wanda zai gayawa lokacin da zainb ta yi sati 2 a gidansa umi ta kirashi ta ce to kai abinci ya kare matarsa ta gama hutawa in zata dinga dafawa to in kuma siya zai dinga yi to. A ranar ya shaidawa zainb ya da ce ta fara girki ta galla mai harara ta ce kaga na yi ma kama da mai shiga kicin? Ni ko ruwan tea ban taba dafawa ba ban san yadda ake dafawa ba ma ga masu aiki nan? Ya ce girkin masu aiki zan ci? Ta ce idan ba za ka ci girkin masu aiki ba ga restaurant nan kala kala ka iya dinaga sayowa. Haushi ya turnuke shi ya ce ban saba ganin ana sayen abinci ba a gidanmu ni ma ba zan iya ba da mutuncina da komai ba zai yiwu in dinga yawan siyan abinci ba.... Zaharaddeen shomar Whatspp num; 08168575100 Launin Fata 1-02 Posted by ANaM Dorayi on 09:03 AM, 04-Oct-15 Under: Launin Fata Kuma ni ban saon cin abincin yan aiki ba har yau ummana bata daina shiga kicin ba duk kuwa da cewa muna da yan aiki. Ta ja tsaki ta tabe baki ta ce wannan matsalar ka ce babu abin da ya daman. A ranar dan takaici rufa'i bai yi barci ba bai kwana kuma a dakin zainb ba, wani abin haushin gari na wayewa ta yi tafiyarta gidansu ta shaidawa iyayanta wulakancin da Rufa'i ya yi mata a jiya. Yana gida yana mamakin halin zainb yana tambayar kansa haka ake zaman auran dama. Sai ga mahaifinta ya zo har gidan ya same shi da fada inda yake shiga ba nan yake fita ba. Ya ce kai ni fa ban baka diya ta dan ta zamo baiwa ta rinka maka bauta ba. Shi yasa na aje mata yan aiki su yi mata duk abin da take so, bance ka biya ba ni zan biyasu ina dalilin matsa mata kace sai tayi wani girki? Wadannan 'yan aikin da na ajiye mata babu wani kalar abinci da ba za su iya dafawa ba. Fadan da ya fi karfin mutum dole ya mai da shi wasa haka rufa'i ya bada hakuri aka ce kuma dole shi zai je ya dauko zainb.Da yaje haka mamanta itama ta dora kan fadan baban zainb, zainb din ta bishi ita kuma da yanga da shagwaba haka ya bisu yadda suke so dan babanshi ya ce ita ce matar da ta dace da shi. Ba a duban tarbiyya da shari'a sai dukiya da launin fata kawai da yare. Duk abinda zai dace da rayuwa, addini da shari'ar mu ta musulunci sun zo mana da shi. Daga lokacin da mutum ya kauce ya bi rudin duniya da soye soyen zuciyarsa sai yaga bacin rai a lokacin da mutum zaiyi aure abin duba shine abinda zai dace da rayuwa kan tsarin shari'ar musulunci da addini. Ba abin da zuciya take so take farautar nema ba, rufa'i dai ya san ya yi auran soyayya, soyayya akwaita zainb ta iya soyayya tana sonshi a shimfida gwanace tana gamsar da shi. Sauran ma'amalolin rayuwa kuwa kullum aya take gasa masa a hannu, bai isa tayi ba daidai ba ya yi magana, ta kan rufeshi da fada ta gaya ma iyayanta su kare mai tas bai da bakin magana. Da ya gaji da tsiyarsu haka ya sa mata ido take cin karanta ba babbaka bai da bakin kai kararta gun umminsa dariya zata yi mai, mahaifinsa da zai gayawa fada zai kara mai yace ya fiye korafi zaman aure dan hakuri ne ya ce dubi dukiyar da mahaifinta yake jibge muku duk wata ga kudi a kai akai, koda daina aiki kayi dukiyar mahaifin zainb zata rike ku. Lamarin Abba ya dinga ba Rufa'i mamaki, abban baida wata magana sai kudi, kudi dai. Gidan rufa'i kenan. Nafisa kuwa lokacin da ta kammala karatunta a jami'ar ahamadu bello ta zaria ta dawo tare da wani hamshakin dan kasuwa dake zaune a kaduna amma fa kamar shanshani yake kan yawo bai iya zaman sati biyu a Nigeria yana yawon kasashen duniya sunansa kabir, matashi ne mai tashen naira shekarunsa kusan arba'in bai taba sha'awar aure ba sai da ya dora idonsa kan nafisa lokacin da tazo bikin yaye su nafisan bisa gayyatar da wani abokinsa yayi masa. Ya ruf sosai a kan nafisa tayi daidai da duk wani ra'ayi nasa da bukatarsa a kan diya mace. Kabir gogaggen matashi ne dan duniya na gaske, yadda kasan sauyi riga ka cire kasa wata haka ya mai da diya mace, kasuwancinsa ya kawo mai kudi sosai, yana shigo da motoci ne da tayoyi da duk wani abinda mota ke bukata daga kashashen duniya kana yana kwangilar kayan gine gine na zamani daga Al-kaira. Bai dauki kudi abikin komai ba, yanzun nan sai ya yi wa mutum kyautar da zata firgitashi. Bai san ajiye kudi ba in ya samu kudi ya kashe yayi bushasha kawai ya sani. Motocin da yake hawa yan ubansu ne na yayi, wani lokacin mota sabuwar yayi a gunsa ake fara ganinta. Abokansa sun dauka itama nafisan holewar za a yi da ita ya ce wannan matar Aure ce in ta amince, ya sha yanga kafin ta amince din kuwa ya hanata sakat sai da ta kawo shi ga babansu. Bai samu fara'a sosai ba saboda na farko dai bakin fata ne sannan ba dan boko ba ne. Jikin kabir yayi sanyi ya tafi ba kwarin gwiwa abban ya ce nafisa ina ke ina son bakar fata? Ta marairaice ta ce Abba babanshi ne baki mahaifiyarsa shuwa ce kuma yana da kudi. Ba a son ran Abba sosai ba ya amince da auran, kabir ya fahimci mahaifin nafisa na da shegen son kudi shi dama kudi ba matsalarsa ba ne dan haka ya saki jiki ya dinga jibge musu dukiya ya shirya mata gida kamar Aljannar duniya a malali low cost a nan cikin garin kaduna. Lefen da yayi mata akwati set ashirin kaya masu tsadar tsiya, ga motoci guda 2 na kece raini, duk wata karya an kare ta a neman auren nafisa, tana son kabir saboda dan gayu ne dan fafa dan karya, ga iya magana, idan yana tsara mace sai ya kashe mata baki ta kasa magana shi kuma yana son ta saboda kyan ta da gayunta da iya yanga. Cikinsu babu wanda ya yi tunanin tarbiyya ko bincike kan wani abu da shari'a ta gindaya a yi yayin neman aure. Rayuwa kawai aka sa gaba ummi bata ce ko mai ba sanin ba yanda za a yi da maganar

Chapter 1 of 12