yau, wato keda Sarkin
fada kundade kuna aikata alfasha, saboda kinga Sarki
beda lafiya, kai, wama yasan tun lokacin da kuke tare?
Hmmmm dama nafada, shiyasa duk abinda yafaru daku
wlh bazanji tausayinku ba, kema kijira sammaci anjima
ko gobe, dan tunda Waziri yakamaku da kanshi, kema
kinsan hukuncin kisane akanki.
Tir da ke, kina matar Sarki kinabin maza, mazan ma wai
Sarkin Fadan Mijinki. Kodayake ba laifinki bane, dama
shi talaka kome akayi dashi, seya baka kunya, yanzu
tayaya wanda yafito daga jinin sarauta ze aikata irin
abinda kikayi?
To wlh bari infada maku dake dasu gaba daya, daga yau
babu ni babu ku, kuma koda kunbude baki kunfadi
abinda nasa akayima Rayhana, babu wanda zeyarda
daku, dan bakuda sheda, kuma ni daga gidan sarauta
nake, zan iya amfani da karfin mulkina inkwaci kaina,
dan kunsan atsari na sarauta ba,a yanke hukunci dole
seda sheda bayyanan na, ku kam bakuda wata shedar
dazata nuna akwai sa hannuna aciki.
Kitashi kibani guri tunkafin azo aganki agurina. Cikin
kuka Medaki tace dan Allah kada kinmani haka, nabaki
duka yarda, banda kowa aduniyar nan kece silar jefani
cikin wannan harka dan Allah kada kice zaki juya mun
baya, kinsani duk wani abu da muka aikata shawararki
mukebi, saboda kece babba. Hannu tadaga mata tamike
tsaye tace nace kitashi kibani guri kada inkara ganin
kafarki agidana.
Ni nabi shawarar kiyi zina da kaskantaccen talaka kuma
yaron mijinki? Kafin asirinku yatonu kintaba fadamun
halin dakuke ciki? Dan haka wlh kinji narantse maki baruwana acikin harkarku, fita nace. Tashi Medaki tayi
tana kuka tafita waje. Wata irin dariya Gimbiya Zakiyya tasaka tace, uhmm dani kuke magana, anfada maku
sarauta haukace? Kaima sarkin fada nasan kana tunanin
katona asirina.
Ni kuma zan nuna maka bakada wayau,duk duniyar nan
babu wanda zeyarda da kai dan kafada masu munyi
harka tare, domin kuwa babu wanda yasan munyi daga
ni sekai, kuma agidan sarauta ba,a karbar shedar mutum
daya, kuma shedar ma tabaki. Dariya tasa tashige daki.
Saurin tashi Sarki Qaseem yayi yana kallon Gimbiya
Suhailat, bayan tagama bashi labarin abinda yafaru. Kai yafara girgizawa ta kalleshi tace dan Allah kayi hakuri, wlh banyi haka dan in cutar dashi ba, kuma ni bansan
Son dayake mata ya kai haka ba, kuma gani nayi nida kai munzaba mashi wadda ze aura shiyasa nayi haka.
Murmushi Sarki yayi yace kinzaba mashi de, kuma ita
Ayman din ai tasamu wanda take so, to koma bata samu
ba, yarinyar dayakeso ita zanbashi sede ita Ayman tazo
ta 2, domin kuwa kinso ki tabka babban kuskure, ko
rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba, yarinyar da kika gansu tare da Areef jinina ce, kuma shima jininshi ce, bari inje asibitin inga halin dasuke ciki.
Kuma kisani tunda har Ayman tasamu wanda takeso to
bazata auri Areef ba, da ace tana sonshi, to zanbashi
shawara ya aureta, amma tunda haka tafaru, kowa ze
auri zabinshi. Kuma kisamu kalaman dazaki bama Jadiya
Safeeya hakuri dasu, dan kinci mata mutunci, matar da
ta sadaukar da jin dadinta domin takaremu.
Matar da tabaro kowa nata, badan tana cikin talauci ba, a,a kawai dan tazauna damu da gaskiya. Juyawa yayi
yanufi kofa zefita, da gudu tarugo tarikeshi tabaya tana kuka tace, dan Allah hubby kayi hkr kada kamun irin
wannan horon, naji nayarda da duk abinda kace, kuma
nahakura Yarima ya auri koma wacece amma dan Allah
kafitar dani duhu, kuma kada kayi fushi dani kasan
bamu saba haka ba.
Murmushin jindadi yayi, sede bejuyo ba, yace ki kwantar da hankalinki, danki ze auri irin yarinyar da mukeso, yar gidan sarauta, albishir daya zan maki, wannan yarinyar
da kika gani ba kowa bace se diyar Yaya da Fulani. Kuma wani abun farin cikin yanzu haka Fulani tana cikin gidan nan, sauran bayani sena dawo zakiji, yana fadin haka
yayi waje. Wani irin yanayi tashiga, gaba daya tarasa
mezatayi, ga kunyar abinda tayi yadameta, musamman
idan ta tuno kalaman data fadama jakadiya, komawa
tayi daki tana tunani.
Cikin sa,a da kwarewa tare da temakon Allah beauty ta
farfado, numfashinta ya dedeta, sede haryanzu bata
bude ido ba, kuma bugun zuciyarta be dedeta ba. Likita
yace sukaita dakin hutu, nan da wani lokaci zata dawo
dede akwai abinda ya tsoratata shiyasa tashiga wannan yanayin.
Adede lokacin Sarki da Waziri suka iso asibitin,kai tsaye office din likita suka wuce, bayan sun gaisa yayi masu
bayanin halin da ake ciki. Sarki yace amma yaya jikin
yarinyar? Likita yace insha Allahu babu wata damuwa,
zata dawo dede. Amma Yarima jikinshi dasauki. Godiya
suka mashi yasa aka nuna masu dakin Areef da beauty.
Seda Sarki yafara shiga gurin beauty, kwance yasameta
kamar matatta, Jakadiya Safeeya tana gefenta se kuka
takeyi, sallamarsu ce tasa tayi saurin goge idonta, ta tashi tana mika gaisuwa, da kyar ya amsa, hankalinshi yana
kan beauty, sak kamarta da Fulani da Areef yake gani
afuskarta, wasu hawayen farin ciki ne, suka zubo mashi.
Kusa da ita ya matsa, fuskarta ya shafa ya kalli Waziri yace tabbas ita ce, ko ba,a fadamun ba nasan wannan
jinin Yaya ce, Allah sarki, Allah maji rokon bayinsa, insha Allahu ayau Yaya zesamu babban albishir, ayanzu base
gobe ba. Kallon Jakadiya yayi yace kifadamun Ina Fulani take, inje da kaina inkaima Yaya ita?.
Se alokacin Jakadiya ta tuna sunbarta agida, damma
tasan barci takeyi, sede tana duba agogo taga lokacin
tashinta yakusa, gashi basu kulle gidan ba, cike da tashin hankali ta kalli Sarki tace Rankai dade tana gida kuma
yanzu zuwa wani lokaci zata iya farkawa, gashi bankulle gidan ba, ina tsoron tafito, koza,a sa amaidani gida kada tafito?.
Waziri yace babu damuwa, muje muga jikin Areef
semuwuce tare. Sarki yace a,a tunda ance jikin nashi
dasauki kawai. Muwuce, Jakadiya tace to bari inma
Ayman magana seta dawo nan tazauna kada tafarka.
Waziri yace rankaidade muje gaba daya muga jikinshi
semu wuce.
Areef da Haisam suna cikin tsara yanda zasu hada plan,
Ayman tana gefe duk tashiga damuwa se kallon Haisam
takeyi tana tunanin idan aka rabasu bazata iya. Hakura
dashi ba. Turo kofar da akayi ne. Tasa su saurin kallon kofa, Areef suna hada ido da sarki yayi saurin komawa
ya kwanta tare da rufe ido.
Dariya yakusa bama Sarki, bayan sun shigo Sarki ya
matsa kusa dashi yace lallai yarona kai ragone tunda har zaka iya kwanciya asibiti saboda mace, to danazo ince
maka na amince da zabinka amma tunda naga baka
warke ba, nafasa, ai dasauri yamike yariko hannun Sarki yana fadin wlh nawarke koyanzu ma asallameni. Gaba
daya dakin seda suka sa dariya, hada Ayman me kuka.
Sarki yace ka kwantar da hankalinka babu wanda ze
hanaka auren zabinka, kuma jininka, bari muje gida
mudawo, kallon Haisam yayi yace ka kula dasu, ke kuma
me kukan soyayya sekiyi shiru tunda zaki samu abinda
kikeso, kitashi kije gurin Diyata kizauna zamu dawo
yanzun nan. Juyawa yayi yafita suma suka bisu abaya.
Cike da Mamaki Areef ya kalli Haisam yace Jinina, kuma diyar Abba? Tome yake nufi? Kafada Haisam yadaga
alamun shima besani ba, yace mujira sudawo maji daga
garesu.
Jakadiya Karima se kuka take tana fadin tsakanina da
Gimbiya Zakiyya Allah ya isa, muguwar mata tasamu
cikin bala,i kuma gashi yanzu mune akulle, bamuda wata
sheda dazata nunama mutane tanada hannnu acikin
abinda muka aikata. Kaicona ni Karima, ban rike amanar
da mutanan nan suka bani ba, naci amanarsu, nima
kuwa Allah baze barni ba. Yanzu shikenan haka za,a
yanke mana hukunci muna kallo abar Gimbiya?.
Wata irin dariya Sarkin fada yayi yace kidena bata
hawayenki abanza, waye yace maki itama zata kubuta?
Aini bana barin baya da kura, inde zanyi aiki to dole se nasamu madafa nake farashi, ko anfada maki nima irin
kwakwalwar jinin sarauta nakeda ita wadda bata da seti?
Kawai malama kizuba ido kisha kallo gobe.
Suna zuwa gidan afalo sukaci karo da ita tafito se raba idanu takeyi. Cak Sarki ya tsaya yazuba mata ido, tabbas ita ce, sede tarame, hannu yadaga sama yanama Allah
godiya, Waziri yace Jakadiya kamota muwuce. Hannunta
takama suka nufi waje.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 95⚜100
Da sallama suka shiga falon Sarki Hasheem, yana zaune
abisa kekenshi yana sana,ar tashi wato tunanin
Fulaninshi, matsawa kusa dashi Sarki Qaseem yayi.
Kafadarshi ya dafa ahankali yadago yana kallonshi, wasu siraran hawaye suka fito daga idanunsu su duka biyun,
alamu Sarki Hasheem yayi mashi da lafiya? Murmushi
yayi mashi yakama kekenshi yafara turawa.
Seda yakawoshi kusa da su Waziri sannan ya sake shi,
shide kallonsu kawai yakeyi, Jakadiya Safeeya takamo
hannun Fulani wadda take boye abayanta, tafito, adede
lokacin dasuka hada ido da Sarki Hasheem Fulani taji
kanta yayi wani irin sarawa.
Shi kam Sarki Hasheem besan lokacin daya mike tsaye
ba bakinshi yana motsi yana nuna Fulani da hannu ba, itakam nan take ta kwala wani irin ihu tafadi kasa, shima jikinshi ne, yafara rawa yazube kasa idanunshi suna fitar da kwallah.
Dasauri suka isa gurinshi, Jakadiya Safeeya kam gurin
Fulani ta nufa, sede tana tabata taji babu alamun
numfashi atare da ita, Waziri yakama Sarki Hasheem
yadora kan cinyarshi jikin sarki se rawa yakeyi yana kara nuna Fulani da yatsa, da karfi yace Fulani.
Jakadiya Safeeya takalli su Waziri tana kuka tace bata
numfashi fa. Sarki Qaseem wanda duk yagama rudewa,
yama rasa ina zeje, ya kalli Waziri yace yazamuyi ne?
Waziri yace kawai muwuce dasu duka asibiti ina ganin
zefi sauki.
Sarki Qaseem yace ma Jakadiya taje takira Suhailat tazo sutafi tare, anan Waziri yakira wasu fadawa suka kama
Sarki aka kaishi mota, Sarki Qaseem kuwa da kanshi
yadauki Fulani ya kaita mota. Waziri yatara manyan
fadawa kusan guda 20 yace nabaku umarnin bayan
fitarmu kada wani ko wata yakara fita koya shigo
masarautar nan, harse mundawo idan nabada umarni.
Jakadiya Safeeya kam tana zuwa part din Gimbiya
Suhailat, jikinta yafara rawa, dan batasan dawane ido
zata kalleta ba, ganin zata bata masu lokaci yasa kawai tashiga, alokacin Gimbiya tana zaune falo tabuga
tagumi. Saurin tashi tayi tana kallon Jakadiya cike da
fargaba tace.
Dan Allah kada kicemun narasa Yarima dan Allah,
sunkuyar da kai tayi tace baki rasa shiba, sede
memartaba ne yace infada maki kifito mutafi asibiti. Ai dasauri taje tadauko hijabinta tafito suka nufi mota, tana zuwa suka shiga wata mota ita da Jakadiya, su kuma suka shiga dayar Wazirri jasu zuwa asibiti.
Azaune, Areef yake bisa gadon beauty ya rike hannunta
idanunshi suna fitar da hawaye, kara kallonta yayi yace dan Allah beauty kitashi haka nan, wlh zan iya samun
matsala idan har baki farka ba. Haisam ne ya matso kusa dashi yadafa shi, yace kayi hakuri abokina zata samu
lafiya, bagashi kana kallo numfashinta yna tafiya dede
ba. Addu,a zaka yimata zata tashi.
Suna zuwa aka nufi emergency dasu, sede shi Sarki wani
daki aka kaishi tunda dama likitan yasan cesa dinshi,
akan Fulani likitoci suka taru suna bata temakon
gaggawa.
Gimbiya Suhailat da tambayoyi suka cika cikinta, gashi
tana son ta tambayi Jakadiya Safeeya amma kunya ta
hanata, ganin haka yasa Jakadiya tace Gimbiya muje kiga jikin Yariman mana, kamar jira takeyi ta tashi cike da
kunya tace muje de infara ganin jikin surikar tawa ko?.
Bakaramin dadi Jakadiya taji ba, dajin furucin Gimbiya, tace to muje, Gimbiya tace dan Allah kiyi hakuri da
abinda namaki, wlh idona ne yarufe, har na furta maki
wadan nan maganganun, amma kiyafe mun, kuma Hubby yayi mun bayanin komai nagane.
Tabbas soyayya baruwanta dawani mulki ko sarauta,
kudi ko talauci, wlh nayarda da zabin Yarima dari bisa
dari, ada kam nayi kuskuren cewa dole dan sarauta seya
auri jinin sarauta, segashi tun ba aje ko inaba Allah ya nunamun ishara, kuma nayarda da abinda nagani.
Murmushi Jakadiya tayi tace haba ai babu komai, nice
yakamata innemi yafiyarki, dan na rufe maki abubuwa
da yawa wanda ba laifina bane, amma muje kiga jikin
nasu, daga baya zakiji komai.
Hannun beauty dake cikin na Areef ne yafara motsi,
saurin kallonta yayi yana fadin Haisam wlh beauty motsi takeyi, kara matsawa kusa da ita sukayi, Ayman tace aiko Yaya ga idonta nan yana juyawa, Areef yace beauty bude
idonki nine akusa dake, babu wanda ze rabamu, dan
Allah kitashi Abba ma yana dubaki kuma shima ya
amince. Kallon Ayman yayi hawaye suna zuba a idonshi
yace dan Allah kuce ta tashi.
Adede lokacin da su Gimbiya suka turo dakin babu
wanda ya kula dasu dan hankalinsu yana gurin beauty,
tsaye Gimbiya tayi tana kallonsu, gaba daya tausayinsu
yakamata, gani takeyi duk itace tasasu awannan halin,
matsawa Jakadiya tayi kusa dasu.
Adede lokacin beauty tabude idonta, bata sauke su akan
kowa ba se akan Gimbiya Suhailat, ai kawai gani saukai ta tashi cikin tsorata ta kwala kara daga karshe tace
Mama............ gaba daya dakin seda suka firgita dajin abinda beauty tayi, saurin shigewa jikin Areef tayi jikinta yana rawa, kara rungumeta yayi yana shafa bayanta.
Se alokacin ya juya yaga Momynshi ce ashe beauty
tagani, saurin daure fuska yayi yace Momy dan Allah
kifita, kina ganin yanda beauty ta tsorata daga ganinki, tunda beauty take bata taba magana ba, amma ayau ta
dalilin tsoranki datakeyi gashi magana tafito abakinta.
Dan Allah kifita tunkafin takara ganinki tarasa ranta, wlh nima mutuwa zanyi. Cike da tashin hankali Gimbiya
tajuya tayi hanyar waje tana kuka, Jakadiya tayi saurin kamota tana fadin kada kifita kidawo zanyi mata
magana, kai kuma Yarima ka nutsu kasan dawa kake
magana.
Jawota tayi suka matso kusa da gadon beauty wadda
take kwance ajikin Areef, ahnkl Jakadiya ta dafa
kafadarta tace tashi kiji wani abu Yar Baba kinsan de
bazan cutar dake ba ko? To idan har kinyarda da hakan
inaso kitashi kuma kada kiji tsoron komai, Gimbiya tazo dan tadubaki kuma tafada maku tayarda zakuyi aure
keda Yarima.
Ai dajin haka beauty ta tashi sede bata rabu da jikin
Areef ba, shikam murmushi kawai yakeyi, yana kallon
Momynshi. Kusa da beauty Gimbiya ta matso takama
hannunta, tace diyata kiyi hakuri kinji wasa nakeyi maku,
babu wanda ze rabaku, nima inasonki, jawota tayi ai kamar jira takeyi tashige jikin Gimbiya, ai gabavdaya
dakin aka sa dariya.
Da wani irin ihu Fulani ta farka tana fadin wayyo nashiga 3 zasu kasheni, haka tayi ta ihu, ganin taki natsuwa
likitocin suka leka suka kirawo su waziri, addu,a Waziri yayi ta tofa mata shida Sarki Qaseem, cikin lokaci
kankani ta nutsu, sede gaba daya afirgice take.
Wani likita yace da alama tunaninta yadawo, sede
agskiya atsorace take, kila mutanen dasukayi mata
sanadiyar shigarta wannan halin sun tsoratata sosai, dan haka shawarar dazan baku idan har akwai malami, to ku
kaita yayi mata addu,a insha Allahu zata dawo dede.
Waziri yace mun gode sosai, amma kana ganin za,a iya
sallamarta ayau? Likita yace kwarai ma kuwa, ai babu
sauran wani abu dayake damunta, dan ta dade tana shan
magani, duk da ba mune muka bata ba, amma mungane
ana bata magunguna masu kyau. Sarki yace mungode
bari muduba jikin Yaya.
Shima Sarki Hasheem jikinshi yayi sauki, dan soyake
abarshi yaje yadubo Fulaninshi, amma likitan yahana,
turo kofar dakin sukayi tare da sallama, aibyana ganinsu Sarki yace ina Fulani ya jikinta? Gaba daya seda sukayi mamakin maganar data fito daga bakin Sarki, dan yau
shekaru 18 da watanni beyi magana ba. Da sauri Srki
Qaseem yaje gurinshi yana murmushi ya rungumeshi
yana fadin Yaya wlh itama ta warke ayau ma zamu koma
gida.
Cike da fara,a Sarki Hasheem yace da gaske? Waziri yace sosai ma, runtse ido yayi wasu hawaye suka zubo mashi
yace Allah nagode maka daka dawomun da Fulanita, ya
Allah katona asirin duk wanda yayi ma Fulani hakan ni
kuma nayi alkawarin wlh bazan barshi ba.
Likita yayi gayran murya yace Alhmdull, dama nace
maku yawancin irin wannan matsalar idan har mutum
yahadu da ita ta dalilin rasa wani abunda yakeso, to aduk lokacin daya ga wannan abun alokacin da beyi
tsammanin ganinshi ba, to inhar Allah yaso ze iya samun sauki.
To hakane yafaru da memartaba, jikinshi yasamu lfiya,
nan da wani lokaci zefara tafiya kamar kowa, amma
kada yayi garaje, gurin fara tafiya, yanzu haka zamu
bashi sanda wadda zata temaka mashi gurin tafiya.
Kuma zaku iya tafiya ayau, sede dole seyasha
magungunan dazamu bashi, suna zasu temaka mashi
jikinshi yayai kwari.
Sarki Qaseem yace yanzu kam tunda farin cikinshi
tadawo ai ba magani ba, komai zesha. Dariya suka sa
gaba daya, Sarki Hasheem yace yanzu de ku kaini inga
Matata ko kuma intafi da rarrafe, dariya sukayi likita
yace a,a ga kujera nan kuturashi yaga farin cikinshi.
Kwance take idanunta akulle, amma ba bacci takeyi ba,
tanaso tayi tunanin,sede data fara setaji kanta yana sarawa, da sallama suka shigo, lokaci guda ta bude
idonta, bata sauke su ako ina ba, se akan mijinta, jan jiki tayi ta tashi zaune, fuskarta dauke da murmushi, turashi sukayi har kusa da gadonta, sannan Waziri yakamo
hannun Sarki Qaseem sukayi waje.
Hannunshi yasa yakamo nata, fuskarshi dauke da
murmushi, saukowa tayi daga bisa gadon ta durkusa
kusa dashi ta shige jikinshi tana kuka, kara rungumeta
yayi yana shafa bayanta.
Dakin beauty suka nufa, azaune suka samesu se fira
sukeyi, suna dariya, beauty kuwa tana jiin Gimbiya, se
dariya takeyi, sede haryanzu tun maganar datayi tafarko bata kara cewa komai ba, Areef ma kasa matsawa yayi
yana manne da ita, wani irin farin cike ne yaratsa zuciyar Sarki Qaseem ganin yanda yasamesu.
Sarki yace waini ina Areef marar lafiya ne, munje
dakinshi mabu ganshi ba? Dariya suka saka, Areef yace
Abba ai nawarke, Gimbiya tace ba dole ya warke ba,
tunda yasamu abinda yakeso, dariya sukayi. Waziri yace
ai seku tashi mufara shirin tafiya gida tunda kun warke dare yayi sosai. Sarki yace gaskiya kam, yaude asibitin tazama ta masoya.
Haka likita yabasu sallama tare da magungunan Sarki
Hasheem dana Fulani, suka kama hanya zuwa gida, sede
haryanzu Sarki Hasheem bega beauty ba, dan seda suka
fara shiga mota sannan suma suka fito. Lokacin dasuka
isa gida kuma dare yayi sosai, hakan yasa Gimbiya taja
Ayman da beauty tace ma Jakadiya kema kitaho
mukwana anan kisan de Yaya baze baki Matarshi ku
kwana tare ba. Dariya tayi tace hakane, muje kawai.
Kallon su Areef tayi tace Haisam kaima kafada ma su
hajiya anan zaka kwana gurin budurwarka kada suji
shiru.
Rufe fuska yayi yana dariya yace ai nafada masu, tace
yauwa maganata tayi dede kenan? Adede lokacin da
motar su Waziri da su Sarki tashigo harabar gidan, suna haskawa jikin wata bishiya suka haske fuskar Medaki, ai dasauri takara labewa, domin ta dade agurin jiran dama
kawai takeyi tasamu tagudu, hannunta rike da dan
kullinta, sede babu wanda yaganta daga Sarki Qaseem ,
se Waziri wanda dama shine yake jan motar, Sarki da
Fulani suna baya, wani murmushi Waziri yayi , yawuce.
Bayan yayi parking motar yayi saurin fita yakirawo masu gadin gidan, ai Medaki tana ganin haka tayi surin
komawa part dinta, kara jaddadamasu yayi akan su kula
da tsaron gidan, kuma akulle kofa babu wanda ze kara
shigowa bare fita.
Haka suka raka Sarki da Fulani har falo, Fulani ta kalli Waziri tarike kanta kamar me tunanin Sarki yace lafiya
Fulani ko kanki yake ciwo? Kai ta girgiza, can kuma tayi saurin bude ido tace ina yarinyata? Sarki yace kina nufin
kin haifi cikin jikinki kuma yana raye? Kai ta girgiza tace dan Allah kubani diyata wlh nasan na haihu, kada
kucemun ta mutu.
Waziri yace ki kwantar da hankalinki, diyarki tana nan, araye asalima babu abinda yake rabaku, atare kuka
zauna, babu abinda yasameta, sede yanzu tana gurin
Gimbiya Suhailat, kuma nasan sun kwanta kinga dare
yayi kibari seda safe zaki ganta.
Murmushin jin dadi tayi ta daga mashi kai, sallama
sukayi masu suka fita. Sarki yace turani muje daki muyi wanka, murmushi tayi tafara turashi, atare sukayi wanka tana temaka mashi, bayan sunfito sukayi sallah sannan
suka kwanta suna me cike da farin cikin ganin junansu,
sun rungume juna kamar za,a rabasu.
Suna fita Waziri yakalli Sarki yace kaga abinda nagani
kuwa? Sarki yace nagani, kabari kawai Allah yakaimu
gobe nasan zamu gano sauran munafukan gidan nan.
Sallama yayi mashi kowa yanufi part shi.
Washe gari da misalin karfe 10 Malam na darazo ya iso,
aka saukeshi amasauki, bayan yagama cin abinci aka
kawoshi fada, alokacin su Sarki Hasheem da fulani sun
iso gurin tasha kyau sosai, tana zaune agefen Sarki,
bayan sungama gaisawa da Malam, ya tambayi jikinshi
yace Alhamdulillahi ai jiki yaya sauki, dama akwai dalilin dayasa kuma yanzu nasamu maganin akusa dani.
Dariya malam yayi yace to mungodema Allah, amma
abinda nakeso da akai, sekayi hakuri da duk abinda
zakaji ko zaka gani, ayanzu, nasan zaka shiga cikin
damuwa, amma munaso mukawo karshen muna fukan
gidan nan, kuma kaima nasan zaka so kasan wadan da
sukayi ma Fulani haka.
Sarki yace hakane, babu komai, Allah yasa inji alkhairi.
Malam yace amin, adede lokacin su Gimbiya Suhailat
dasu beauty, Ayman, Jakadiya , Areef da Haisam suka
shigo, ai beauty tana ganin Mamanta da gudu taruga
tafada kanta tana dariya.
Itma tana ganinta tayi saurin rungumeta tna fadin
yarinyata, Sarki da mamaki ya kamashi dasauri ya kalli
fulani yace wannan ce diyata? Kai tacdaga mashi, besan
lokacin da kwalla tacika mashi ido ba.
Waziri yabada umarnin afito dasu Jakadiya Karima,
sannan yasa Jakadiya Safeeya takirawo su Gimbiya
Zakiyyah da Medaki, wani bafade yasa yakirawo Baban
Fulani da Baban Darazo, kowa yasamu guri yazauna yana
kiran abinda za,ayi.
Nima nace bara in anje alkalamina injira shigowar su
Sarkin Fada.
Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 100⚜105Cikin isa da mulki Gimbiya Zakiyyah tashigo, ko sallama ma da kyar tayi, guri tasamu gefen Sarki tazauna, dan
batasan yasamu lfy ba. Kallonshi tayi fuskarta dauke da murmushi tace barka da asuba memartaba yajikinka?.
Sanin ko anyi mashi magana baya amsawa yasa tadauke
kanta bata kula da motsa bakin dayayi ba. Kallon malam
tayi tace malam barka da asuba, yace yauwa kintashi lfy.
Medaki ce tashigo jikinta duk yayi sanyi kamar
antsamota daga ruwan zafi.
Akusa da bakin kofa tazauna duk tagama rudewa, cikin
rashin jindadin abinda tayi Sarki Hasheem yace medaki
dawo nan mana. Ai Gimbiya Zakiyyah batasan lokacin
datace yaushe kafara magana memartaba?.
Murmushi yayi kawai yayi shiru, haryanzu babu wanda
ya kula dasu Fulani, bayan medaki tazauna kusa da
Gimbiya Zakiyyah, kallonta tayi tadan duko kusa da
kunnanta tana murmushin mugunta tace ina fatan kinyi
kwanciyar karshe agidan sarauta? Seki shirya karbar
hukunci.
Sallamar su Sarkin fada da Jakadiya ne tasa Medaki tayi saurin tashi tana hawaye. Wani murmushin jindadi Sarki
Hasheem yayi, ganin Jakadiyarshi, dama yana so ya
tambayeta domin ita yakeso yayima albishir na samun
diya da yayi, domin yasan tana daya daga cikin masu son yasamu karuwa.
Da fara,a yace Jakadiya matsonan infara baki albishir
medadi, ai jitayi kamar yan hanjin cikinta zasu fito,
kamar ance Fulani tadago kai, ai tana dagowa sukayi ido 4 da Sarkin fada. Wani irin ihu tasaka ta ture beauty,
tashi tayi kamar zata ruga tana fadin gashi nan yazo zasu kasheni.
Waziri da Sarki Qaseem bakaramin mamakin abinda
take fada sukayi ba, duk da dama suna zarginshi.
Jakadiya Safeeya da Gimbiya Suhailat ne suka rike Fulani, Sarki Hasheem kuwa jiyayi kamar yatashi, gaba daya
jikinshi rawa yakeyi, ganin haka Sarki Qaseem ya matsa
kusa dashi yadafashi yana bashi baki.
Gimbiya Zakiyyah kuwa batasan lokacin data mike tsaye
ba tana nuna Fulani, Medaki kuwa kukanta har yafito fili, duk da sanyi da falon yakedashi be hana zufa keto mata
ba. Gaba daya sauran mutanen Falon sun shiga rudani,
Areef kuwa matsawa yayi kusa da beautynshi yari keta
sosai, yadora kanta saman kafadarshi, dan yasan batason hayaniya, ita kam kuka tasaka tunda Fulani ta
tureta.
Malam da kanshi ya matsa kusa da Fulani datake kwance
akan cinyar Jakadiya tana ta kuka, addu,a yafara yimata yana tofa mata. Sarkin fada kuwa da Jakadiya zaman yan
bori sukayi suna rarraba idanu.
Sarki Qaseem ne yayi gyran murya sannan yace ya isa,
kowa yasamu nutsuwa kuma azauna domin muyi abinda
yakawomu. Malam yadade yanama Fulani addu,a kafin
tasamu tadawo cikin nutsuwarta. Sarki Hasheem kam
gaba daya kanshi yagama daurewa shiru kawai yayi yana
karanta addu'oi, hakan yasa yafara samun nutsuwa, sede
haryanzu idanunshi suna kan Jakadiyarshi data kasa
kallonshi.
Bayan kowa ya nutsu Waziri yatashi yace ma malam
yabude masu taro da addu,a. Bayan angama Waziri
yafara magana. Alhamdulillahi da farko zanfara dayima
Allah godiya daya kawomu wannan rana mecike da farin
ciki da kuma bakinciki.
Da farko zanfara gabatar da matar Sarki, kuma amarya
agurinshi wadda akafi sani da Fulani. Bayan shekaru 18
da wasu watanni bata gidan nan, inda aka samu wasu
marassa imani suka shigo har cikin dakinta suka
dauketa........ Sallamar Su Baban Fulani ce ta tsaida Waziri daga jawabin dayakeyi.
Fulani tana ganin Babanta ta tashi tanufi gurinshi, ai
shima yana ganinta yabude hannuwa tashige jikinshi
tana kuka. Shima kukan yakeyi seda suka bama kowa
tausayi. Bayan sun natsu suka zauna, Baban beauty kuwa
gaba daya mamaki yagama cikashi ganin abin al,ajabi.
Waziri yaci gaba da magana. Kamar yanda nace ba,asan
wadan da sukazo suka dauke Fulani ba, amma tunda
Allah yasa gata tadawo kuma tana cikin hankalinta.
Kuma zata iya nuna wadanda suka aikata haka akanta to
duk wanda yakasance cikin masu laifi, tabbas ze fuskanci hukunci me tsanani, kuma kowane irin matsayi gareshi a
masarautar nan.
Ai kamar daga sama sukaji Medaki ta tashi tana fadin
shikenan munshiga 3 wlh, ba laifina bane, duk kutsaya
wlh zanfadi iyakar gaskiyar dana sani. Gimbiya Zakiyyah tayi wani murmushi aranta tace lallai zaki sha
mamakina,ni nasan babu wanda zeyarda idan kikace
hadani.
Waziri yayi murmushi yace rankiyadade munajinki.
Tashi tayi tana kuka tafada masu duk abinda sukayi
itadasu Gimbiya Zakiyyah, akan batan Fulani, sede bata
fada masu abinda suke aikatawa da Sarkin fada ba.
Gaba daya falon aka dau salati, Sarki Hasheem kuwa
zama yayi kamar dutse, kallon Jakadiya Karima kawai
yake idanunshi na zubar da ruwa. Waziri yace da kyau,
tashi Gimbiya Zakiyyah tayi tafara magana cike da mulki.
Inada ja agame da maganar Medaki, wannan maganar datayi kawai tafa deta ne sbd wani dalilinata, amma
kowa yasan bana shiga harkar talakawa taya za,ayi
inhada baki dasu mu aikata irin wannan shirmen.
wanda kowa yasan duk wanda yafito daga gidan sarauta
bazeyi haka ba. Idan kuma har tace dani, ni nayarda
sukawo sheda, idan har aka sameni da hannu aciki
nayarda da duk wani hukunci daza,amun.
Waziri ya jinjina kai, alamar gamsuwa, ya kalli Medaki
yace kina da wata shedar dazata nuna mana tana da
hannu acikin abinda kika fada? Wata zufa ce takara keto mata, hawaye suna zuba a idonta tafara girgiza kai, tace a,a amma wlh dama
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 13