Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
saman cinyarta tana murmushi. Haisam yace tashi muje masallaci kada Abba yace beganmu ba, Jakadiya tafita tace sekun dawo, akwai abinci akitchen idan kundawo, suka ce to. Areef yaduka kusa da beauty yace wato yau kinga yar uwa shine ko ki kalleni ko? Kai tagirgiza ta tashi ta kalleshi. Dariya Haisam yayi yace beauty bakida matsala, kome akace kiyi sekiyi, gaskiya nan gaba zankoya maki bakomai zaki rika yiba. Duka Areef yakaimashi yana fadin todan bukulu, ai seka hanata, Allah yakashe yabani idan munyi aure base narika magiya ba shine zakace wani tadena. Haisam yace sosai ma, har wannan son jikin duk sena hanata. Dariya Areef yayi yanufi hanayar fita yace tunda kaine mijin ai se ingani, aini naji dadin wannan abu, sonjiki. Ai shine abinso, fita sukayi suna dariya. Ayman tace sister da kikayi wanka kinyi alwala ko? Kai tadaga mata, tace yauwa tashi muje kiyi sallah nima inyi alwala inyi, hannunta takama suka nufin daki. Sarkin fada ne tsaye abakin kofar Gimbiya Zakiyyah se waige waige yakeyi kamar marar gaskiya, wani abu yadauko aleda yasa a idonshi, kafin yashiga gidan, alokacin tagama sallah tafito falo, da sallama yashiga, cike da mamaki tace kai? Waya baka ikon shigowa part dina? Ko kuma wani yace maka ina nemanka? Kai yadago suka hada ido, wani irin abu taji ya tsikareta, saurin rufe ido tayi, ganin halin data shiga yasa yayi murmushi aranshi yace anzo gurin. Kallonta yayi yace nadauka ai kinason ganina shiyasa nazo amma bari inkoma. Saurin bude ido tayi tasaki murmushi tace ni na isa nace ka koma? Shigo sannu da zuwa, zama yayi abisa kujera, tace a,a muje daga ciki kada wasu suganka. Murmushi yayi yatashi yana lashe baki aranshi yana fadin wayyo ni. Daki suka shiga tace meza,a kawo maka? Murmushi yayi yace bakomai zoki zauna kawai fira nazo muyi, wani irin yanayi taji tashiga, tahowa tayi kusa dashi tana wani girgiza, kusa dashi tazauna tace togani, kallonta yayi yakamo hannunta yace babu wanda zeshigo ko? Lumshe idanu tayi alokacin taji wani bakon yanayi yashigeta, tace ina zuwa bari inbada sako akulle mun gidan kuma kada abar kowa yashigo, yace akulle gida nida ba nan zan kwana ba, wani irin kallo tayi mashi tace, kama isa, ai tunda kashigo sede da asuba kafita. Dariya yayi yace duk abinda kika fada dede ne rankiyadade, murmushi tayi tafita. Wani irin tsalle yayi na farin ciki, hannunshi yasa a aljihu yaciro wani abu aranshi yana fadin saboda tsaro. Bayan sundawo daga sallah part din Jakadiya Safeeya suka wuce, anan suka samesu afalo beauty tana kwance kan cinyar Ayman ita kuma tana ta wasa da gashinta tana bata labari, da sallama suka shiga, Haisam yace to wlh baze yuwu ba, wannan matar taka zata sama Angel dina taurin cinya, Areef yace wlh kai dan iska ne, agaban beauty kake wannan maganar sokake ka kangararmun da ita, bacin kasan yarinya ce. Ai dasauri beauty ta tashi jin abinda Areef yafada, kafafuwa tafara durzawa akasa tana turo baki tana kunkunai. Dariya Ayman da Haisam sukayi, Ayman tajawota tace yi hakuri, shine yace maki yarinya ko? Kai tadaga tana kara turo baki, kamar zatayi kuka, ai ganin haka yasa Areef ya matso yaduka kasa kusa da ita yana fadin yihakuri beauty na wasa nakeyi kinji? Kai ta daga tana murmushi, Areef yace yauwa beauty na, tashi muci abinci in baki tsara barki. Tashi tayi tanufi kitchen. Haisam yace gsky kaci sa,ar mata wannan saurin sauka haka, to wlh kaji tsoron Allah, Areef yace da tsoronka nakeji? Sarkin sa ido kawai, kuma badakai zanci abinci ba, nida beauty zanci. Haisam yace Allah nagode maka nima daka hadani da abin sona ayau, nadana shiga 3 agurinka, Angel muma tare zamuci ko? Kai tadaga tana murmushi, lokacin da beauty tafito tasan alokacin ake bama mamanta abinci, harta nufi dakinta se kuma ta tuna da maganar Jakadiya Safeeya,,,,,,,, kada kisake kishiga dakin can idan akwai mutane agidan nan, idan ba haka ba, kamata zasuyi bazaki kara ganinta ba. Maganar Areef ce tadawo da ita, beauty mezakiyi awannan dakin kuma? Juyowa tayi tana murmushi ta girgiza kai, tanufo gurinsu, ansar abincin yayi ta koma tadauko sauran, atare yazuba masu yamika ma Haisam yace ganaku nan, dariya yayi yajawo yazuba masu, Areef yace taho beauty na muci, zama tayi kusa dashi, sede bega ta jingina dashi ba, murmushi yayi aranshi yace su beauty anfara girma kenan, abaki yafara bata tanaci, shima yace nima bani zakiyi ko? Kai tadaga tana murmushi, haka sukarika cin abincinsu sun manta dawasu Su Haisam. Dariya Jakadiya Safeeya tayi jin abinda Gimbiya Suhailat tafada, tace ai sundawo tundazu suna gidana, acan nabarsu suna cin abinci ma. Wani murmushin jin dadi Gimbiya tayi tace ai nasan Yarima zeso Ayman, gashi lokaci guda har sun saba, wato kunyata sukeji shiyasa suka tafi can. Jakadiya tace emana agida na za,ayi firar ai, kinsan Yarima. Naguri nane, ai, gimbiya tace aise suyita ta tafiya nima haka nakeso, Allah yabama Yaya lafiya musha biki. Kallon agogo Jakadiya tayi tace bari inje gida seda safe Gimbiya. Kallonta tayi tace haba de tunyanzu sallar isha,i ma yanzu za,ayi, wai meyasa yanzu bakison zama anan sosai, musammamma da dare? Gaban Jakadiya yafadi, aranta tace nasan Fulani tana can takusa tashi ai dole inkoma kada su Yarima suganota. Dasauri tayi murmushi tace ai dole intafi inje inji inda aka tsaya amaganarsu, murmushin jindadi Gimbiya tayi tace hakane fa, Jakadiya tace nikam yanzu ai nasamu yan fira tunda de kunya tahanasu zama anan, dan yarima ma cewa yayi bayaso kusani harse Sarki yasamu lafiya yasan dayayi maku magana za,a sa rana. Gimbiya tayi dariyar jin dadi tace kibarni dasu, zamu gwada masu bamusan komai ba dakanshi zezo mana da maganar, bari hubby yadawo infada mashi, sosai Jakadiya taji dadin maganar Gimbiya, sallama tayi mata tafita. Koda taje kowa yana zaune tare da masoyiyarshi, Areef yanata koyama beauty rubutu da karatu, kitchen ta wuce ta dauko abinci tace sannuku da aiki, Yarima yace Aunty har kindawo? Tace bari inshiga ciki inci abinci inyi wanka sukace to afito lafiya. Haka rayuwarsu tacigaba da tafiya babu wanda yasan abinda yake tafiya atsakanin masoyan. Abangarensu kuwa soyayya me karfi tashiga tsakaninsu, akoda yaushe suna part din Jakadiya Safeeya, Areef yadage sosai yana koyama beauty karatu da rubutu, suna dawowa office beda gurin zama se gurinta, dayake itama tanada basira beda gurin zama se gurinta, dayake itama tanada basira kome yakoyamata take daukeshi, ayanzu har rubutu ta iya, dan tana hada kalmomi. Ganin haka yasa hankalin Jakadiya yafara tashi, samunta tayi tafada mata kome Yarima ya tambayeta kada tabashi amsa, idan ba haka ba, duk ranar da yasan labarinta bazata kara ganinshi ba kuma zesa akoresu, kada kisake kice mashi A MAKABARTA AKA HAIFEKI, kawai kifada mashi abinda nafada mai, kinji ko? Ta daga kai, da wannan hankalin Jakadiya Safeeya yadan kwanta, kuma akaci sa,a shima be cika yimata tambayoyi ba. Abangaren Gimbiya Zakiyya kuwa ta kwace ma Medaki Sarkin fada, dan duk dare agurinta yake kwana, wani irin sonshi takeyi, har bataso yayi nisa, sosai Medaki tashiga damuwa sede tunda Jakadiya Karima tayi mata bayanin komai, shima Sarkin Fada yace mata yayi hakane dan kawai yarama irin cin mutuncin datayi masu ne, kuma kudinta yakeci sosai, kuma yana kawoma su Medaki, hakan yasa hankalinta ya kwanta idan yasamu lokaci kuma yana zuwa gurinta. Haka rayuwar gidan tacigaba da tafiya Waziri akullum yana kara sakama Sarkin fada ido, dan sunyi waya da malam yace mashi yayi kokari yagama hada duk wata sheda daza,a fara tuhumar Sarkin fada yana nan zuwa tunda jikin Sarki yafara sauki, yanaso akawo karshen matsalar gidan. Gimbiya Suhailat ce tafito tana neman Ayman, ganin bata ganta ba, wata baiwa tace sunfita bagaren Jakadiya Safeeya. Murmushi tayi tace yaude bari inje da kaina inga wata wainar ake toyawa, kuma in nuna masu nasan abinda suke boyemun, ai gara azo ayi bikin nan kowama yahuta. Allah nagode maka da zaka cikamana burinmu, bari indawo in bama Yaya albishir medadi, itama nasan zataji dadi ace Ayman dinta zatayi aure. Fita tayi wasu bayi suna take mata baya, suka nufi bangaren Jakadiya Safeeya. Zaune suke afalo, Areef da beauty suna zaune bisa doguwar kujera, sungama karatu, yana bata biscuit abaki, suna ta firar su gwanin ban sha,awa, Haisam da Ayman suma suna zaune kasa yana bata ice cream tana ta zuba mashi shagwaba. Jakadiya kam tana dakin Fulani tagama yimata wanka tana sa mata kaya, tayi kyau sosai, hutun datake samu kyanta yafito har kiba tayi. Jakadiya tace insha Allhu komai zezo karshe da malam yazo kema kije gurin mijinki koze samu sauki. Wazirine da Sarki Qaseem suka fito zasuje bangaren sarki Hasheem, dede gurin part din. gimbiya Zakiyya zasu wuce, sega Jakadiya da Sarkin Fada sunfito daga gidan, Sarkin Fada se gyara wando yakeyi, suna fitowa suka kwashe da dariya, hannu yamika mata suka kashe, yace kai wlh yau nasha roman Gimbiya, sosai, kinsan tundazu naso infito ta hanani, ashede haka Sarki yakejin dadinshi. Jakadiya tace ba dole sunemeka ba, tunda kana dauke masu nauyin abinda musakin mijinsu yakasa ba, ai wlh.......... Maganar ce ta makale sakamakon idanu data hada dasu Waziri. Hannu tasa ta tabo sarkin fada dayake shirin yin magana. Wata irin zabura yayi alokacin da idanunshi sukaga abinda take nuna mashi, wani irin kallo Sarki da Waziri suke binsu dashi,,,, kuttt suka hadiyi wani miyau me daci, ga wata irin zufa datake fito masu. Shinko su waziri sunji firarsu? Kubiyoni anext page danjin abinda yafaru. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤 AMAKABARTA AKA HAIFENI 🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤 (The story of hard kingdom) Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 85 ⚜90 Idan ran Sarki Qaseem yayi dubu to yabaci dajin irin kalaman Sarkin fada da Jakadiya Karima, Waziri ne, yajuya ya kalli Sarki Qaseem, shi kanshi ya tsorata da ganin yanayinshi. Cikin sauri yataboshi, yana kallonshi yayi mashi alamu da ido. Juyawa yayi murmushi dauke afuskarshi yakalli su Sarkin fada yace dama gurin memartaba zamuje kuma segashi munhadu, ko kuma daga can kuke? Dasauri Sarkin fada yace wlh kuwa shinema mukashiga gurin Gimbiya muyi mata albishir naganin halin da Sarki yake ciki. Gaskiya munji dadi sosai, jikinshi yayi kyau, yanzun nan nashiga ko kinti 2 banyi ba, shine ma muka fito da Jakadiya. Amma ai kuma yanzu kukazo nan, ko kun dade tsaye anan? Waziri yayi murmushi yace ai ko second 2 bamuyi anan ba, kuka ganmu, bari mukarasa. Wata irin ajiyar zuciya suka saki, har suna hada baki gurin fadin to adubashi, Jakadiya Karima tajuya tanama Sarki Qaseem kirari, hannu yadaga mata tare da kakalo murmushi sannan suka wuce. Sarkin Fada yace wai! Allah yasomu damun kama kanmu ashema basujimu ba, Jakadiya tace kaide bari, nidama nasan dakyar idan sunjimu, dan Sarki Qaseem mutum ne wanda beson jin abinda bedameshi ba. Sarkin Fada yace haka ne, shima ai Wazirin na Allah ne, babu ruwanshi dajin gulma, akwai addini, muje gurin Medaki itama inkwashi rabona. Jakadiya tace to amma gaskiya yau nima inaso muje dakina. Wani kallo yayi mata, sannan yace haba Jakadiya da girmanki kike fadin haka, ai kibarma Gimbiyoyin Sarki, ke kam yanzu ai kinwuce wannan matsayin. Hade rai tayi tace amma ai duk tsufa na ban kaika ba ko? Dariya yayi yace haka ne, amma kinmanta namiji baya tsufa? Kawai kibar wannan maganar muje inyi abinda zefishsheni. Wani guri kafin akai part din Sarki Hasheem suka samu suka zauna, idanuwan Sarki Qaseem har rufewa sukeyi sbd bacin rai, da kyar ya iya daga baki yace, dan Allah Waziri kace abinda naji ba gsky bane, nabama mutanen gidan nan amana musamman wadannan 2, acikinsu Yaya yafison Jakadiya Karima, nima haka, dan Allah Waziri. Wani irin tausayinsu ne yakama Waziri, ganin idanun Sarki Qaseem sunyi ja yasashi matsawa kusa dashi tare da dafashi yace. Memartaba wane irin matsayi kabani azuciyar ka? Kallonshi Sarki yayi yace aduk gidan nan kaine mutumi nafarko damuka fara aminta da kai, kawuce kowane irin matasayi agurinmu har ka kai matsayin dan uwa agurinmu. Bari kaji aduk fadin duniyar nan kai kadai muke iya fadama sirrinmu, shiyasa bama jayayya da duk wata shawara dazaka kawo mana. Kawai kafadi abinda ke ranka namaka alkawarin komenene zankarbe shi, nasan bazaka taba fada mana abinda ze cutar damu ba. Gyaran murya Waziri yayi, fuskarshi cike da annurin kalaman dayaji daga bakin Sarki Qaseem, ahankali yafara fada mashi duk irin abubuwan daya fara gani agurin Sarkin fada, har firar dasukayi seda yafada mashi, daga karshe yace zakayi mamakin idan nafada maka Gimbiya Fulani tana cikin gidan nan tsawon watanni 3?. Seda Sarki yakusa kwarewa saboda firgita, kai waziri yadaga alamun da gaske yake, sannan yacigaba, akwai abubuwa da yawa wanda bakusansu ba, daga ni se Malam, se Jakadiya Safeeya kadai muka sansu, amma inaso abari se gobe idan Malam yazo zeyi maku bayanin komai, sede abinda nakeso kasani bawai munboye Fulani da wata manufa tamu bane, a,a wannan umarnin Malam ne. Kuma alokacin da muka kawota gidan nan, babu wanda yasan itace, dan tun lokacin data bace tsawon shekaru 18, har zuwa yanzu tana cikin yanayi na hauka, kuma wahala data sha ne yasa muka kasa ganeta, acikin yan kwana kin nan dayake tana samun kulawa agurin Jakadiya Safeeya, dan agurinta take zaune, tofa alokacin ne, tafara dawowa kamanninta, sbd tana samun tsafta, shine Jakadiya ta ganeta. Bayan tafada ma Malam, yace kada tafada ma kowa, kuma yakirani yafada mun, nima yace kada infada ma kowa, dan wadan da suka aikata mata wannan laifin suna cikin masarautar mu, dole semunbi asannu zamu iya ganosu. Ajiya mukayi waya dashi yace mun zezo gobe domin yanaso yakawo karshen halin da masarautar mu take ciki. Babban abin farin ciki tahaifi cikin dake jikinta, Allah ya azurta ta dasamun diya mace, aranar data bar gidan nan kamar yanda su Malam suka sami labari daga gurin wadan da suka tsinceta, to aranar ta haihu, kaga yanzu Yarinyar tana da shekara 18 da watanni. Babban abinda yasa nataboka alokacin damu kaji abinda su Sarkin fada suke fada shine, kasan idan baka iya kama barawo ba, to shine zekama ka. Nadade dasanin halin da Sarkin fada yake ciki shida matar Sarki Medaki, suna aikata kazamar harka, kusan kullum agurinta yake kwana, nasamu wannan bayanin ne daga gurin daya daga cikin bayin dana sa ya kular mun da duk wani motsi na waziri. Dan haka ayanzu base gobe ba, inaso kabani dama nasa akama Sarkin Fada da Jakadiya akullesu har zuwa gobe, idan Malam yazo se afito dasu, nasan idan aka maimaita masu laifin dasukayi, zasu tona duk abinda sukayi. Hawayen dake idanun Sarki Qaseem yagoge, saboda bakaramin kaduwa yayi dajin labarin Waziri ba. Da ace beji abinda suka fada dazu ba, kuma ace ba waziri bane yafada mashi dabaze taba yarda da abinda aka fada ba, kallon Waziri yayi yace ayanzu bani da sauran bakin magana, da kai da Malam nabaku damar ku aiwatar da duk wani abu da yayi dede da hukuncin masarautar nan, sede abu daya nakeso, inaso akawo ma Yaya Fulaninshi yagani, kila ta silar haka yasamu sauki, banaso afadi wani abu harse yasamu sauki, dan yaji duk irin abinda mahintan makusantanmu suka aikata. Waziri yace godiya nake, bara inje insa akama su, kafin wani tunanin yashige su sugudu. Sarki Qaseem yace shikenan bara inshiga gurin Yaya kada yaji shiru. Da sallama su Gimbiya Suhailat suka shiga falon Jakadiya Safeeya, adede lokacin da Beauty tana karbar biscuit ahannun Areef shi kuma yana ta mata wasa da hankali, se dariya sukeyi, hannu tasa zata karba, cikin rashi sa,a tafada jikinshi. Kwanciya tayi saman cinyarshi tana ta dariya shima haka. Cak Gimbiya ta tsaya da sauran Sallamar data fara, tsayawa tayi tana kallonsu cike da mamaki, da takaici, sam bata kula dasu Ayman ba, sede kawai taji dariya agefenta, saurin kallon gurin tayi, ai jitayi kamar tazube dan takaici, Haisam ne, yake kokarin saka ma, Ayman sweet abaki, sunata dariya abinsu. Kamar daga sama sukaji wata irin tsawa, wadda tasa beauty saurin kankame Areef, tayi,wani Uban ashar Gimbiya tasaki, wanda ita kanta batasan ta iyashi ba. Gaba dayansu hankalinsu atashe suka juyo suna kallonta, cike da kaduwa Haisam da Ayman suka sauko kasa, shikam Areef sam abun be daga mashi hankali ba, kara rungume Beauty yayi saboda kukan datasa mashi, sam bata taba jin wata aba wai ita tsawa ba, tunda take, hakan yasa tayi mugun tsorata. Gimbiya cike da bacin rai tace kai dan Ubanka bazaka saketa ba, kabani hankalinka? Jakadiya ce tayi saurin fitowa daga dakin fulani, dan dama tayi bacci ta tsaya gyara mata dakinne kafin tafita, tana cikin gyara taji wannan hayaniya. Alokacin data fito saura kadan tazube saboda kaduwa, cak ta tsaya bakin kofa tana zaro ido tare da kallon Gimbiya. Areef yakama beauty suka sauka kasa, dan shima alokacin da Gimbiya tamashi wannan zagin bakaramin kaduwa yayi ba, dan tunda yake betaba jin irin zagin abakin momynshi ba, ko fada bata taba yimashi ba. Wani irin murmushin takaici Gimbiya tayi, ta kalli Jakadiya, rai abace tace sannu munafukar Allah, mayaudariya, maha inciya, ashe dama abinda kike kullawa kenan? Kinaso ki batama yarona tarbiyya tunda ke baki dashi? Wato duk ginin da nakeyi kece kike rushe shi? Kinje kinsamo wata matalauciyar yarinya kin hadata da Yarima, ita kuma diyata kin hadata da abokinshi. Ashe dama duk zaman damukeyi zaman munafurci ne ? Wai meyasa duk wanda be fito daga gidan sarauta ba, zaka sameshi maci amana ne? Lallai zamanki yazo karshe agidan nan, bazan kara amincewa da banzan halinki ba. Kai kuma Haisam kake kowa? Inaso kasani Ayman Yarima zata aura, garama ka tattara soyayyarka kayi waje da ita, ko kuma kaima kaje kasamu diyar dan siyasa ka aura, danmu bama auratayya da yan siyasa, domin Sarauta gado ce, kuma ajininmu take, kufa?. Mulki ne, da lokacinku yacika ko kunaso ko bakwa so, dole kusauka kubama wanda yaci, dan haka kada inkara ganinka agidan nan, bare kuma tare da Yarima ko Ayman. Ke kuma kisaurari hukuncinki, matsawa tayi ta ture beauty wadda tundazu take kuka. Hannu Areef yasa yariketa sosai shima hawayene suke zuba a idonshi, da kyar yace Momy dan Allah kiyi hakuri wlh beauty itace rayuwata, idan kika rabani da ita mutuwa zanyi, ture ta tayi takama hannunshi dana Ayman wadda itama kukan takeyi, Haisam ne kawai medauriya acikinsu, amma har jakadiya kuka takeyi. Jansu tarikayi kamar yara har suka fita daga falon, dasauri Jakadiya ta matsa takamo beauty ta dagata zasu shiga daki, kuka kawai, takeyi harda sheshsheka, tana tashi takoma tazube kasa sumemmiya. Abakin kofar falon Areef ya toge, duk yanda Gimbiya taso tajashi kasawa tayi, hannunshi ya fisge alokacin dayaji Jakadiya tasa wani irin kuka tana fadin munshiga 3 Yar Baba dan Allah kitashi, dasauri yakoma falon, Gimbiya tabishi tana fadin kadawo nace maka ko. Yana zuwa yaga beautynshi kwance akasa babu alamun rai atare da ita, wata irin kara shima yasaki tare da dafe kanshi yazube kasa asume. Urs. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤 AMAKABARTA AKA HAIFENI 🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤 (The story of hard kingdom) Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 90⚜95 Da gudu Gimbiya da Haisam sukayi kansu, tana zuwa takama Areef hankali tashe tafara jijjigashi tana kuka, Jakadiya Safeeya ma beauty tarika jijjigawa tana kuka. Haisam ne yayi kokarin fita waje yakira wasu bayi maza, suka dawo tare. Su suka dauki Areef shi kuma yadauki beauty suka fita, Jakadiya, Gimbiya da Ayman suna binsu abaya, cikin mota yasakasu, Jakadiya tashiga tare da Ayman ya kulle kofar ko kallon Gimbiya beyi ba yaja motar suka barta nan tsaye dan babu halin tabisu, tunda Sarki Qaseem besani ba. Komawa tayi part dinta tana kuka, kara tunano kalaman Areef tayi,,,, Momy wlh kika rabani da beauty nima mutuwa zanyi. Hannutasa tarufe duka kunnuwanta tana fadin bazaka mutu ba Yarima, kaine farin cikina, dan Allah kar kamun haka. Saman kujera tafada tana kuka bayinta se hakuri suke bata. Waziri ne, tare da wasu manyan bayi maza suna binshi abaya, hanyar lambu suka nufa dan yafi zaton suna can, koda sukaje basu same su ba, tunawa yayi da Medaki, hakan yasa suka nufi can. Alokacin Sarkin Fada da Medaki suna cikin daki, ita ko Jakadiya Karima tana zaune falo tana kallo ta tasa farfesun kaji tanaci. Wata baiwa ce tashigo falon, ai dasauri Jakadiya tace Uban wa yabaki izinin shigowa? Bana hanaku idan muna gidan nan kushigo ba?. Dukawa tayi tace Allah yabaki hakuri, dama Waziri ne, ya tambayeni ko keda Sarkin fada kuna ciki, shine nace masa kuna nan, shine yace amaku magana. Cikin Jakadiya ne yayi wani kara, nan take zufa tafara keto mata, batasan lokacin data saki cinyar kazar datake hannunta ba. Cike da tashin hankali tace ubanwa yace kifada masa muna ciki? Innalillahi wainnailaihirraji,un. Munshiga 3 kada de ace asirinmu ne yake shirin tonuwa? Tashi kiba mutane guri munafuka. Hanyar dakin Medaki tanufa, har tuntube takeyi, tana zuwa tafara bubbuga masu,alokacin sunyi nisa cikin harka, dade sukaji bugun yayi yawa, shine Sarkin Fada yayi saurin zira babbar rigarshi, ko wando besa ba, haka yaje yabude. Ai yana fitowa Jakadiya tajawoshi tana fadin munshi 3 gasu Waziri can abakin kofa suna jiranmu. Zaro ido yayi yana fadin waya fada masu muna nan? Tace kaide kawuce muje, bawannan bane agabanmu, yanda zamu kare kanmu bakamar ma kai, danni wlh tawa mesauki ce, tunda ni macece kuma kowa yasan inada hakkin shiga duk inda nakeso amasarautar nan. Sarkin fada yace kiwa Allah kije kice ke kadai ce, bakisan inda nayi ba, nasan zasu kyaleki. Zaro ido tayi tare da dafe kirji tana fadin Jar Uban nan, ai wlh baka isa ba, ai gara ma kai, kome akayi maka kasha dadi, nifa? Menasha, kun hadani da naman kaza da kallo kunshige daki, ai wlh inde nafita kaima seka fita. Bugun kofar falo ne, ya sasu saurin kallon gurin alokacin Medaki tayi saurin fitowa da daurin gaba ajikinta, kanta ko dan kwali babu, tana fadin wai meke faruwa haka? Shigowar Waziri ce tasata yinshiru, idanu 2 suka hada dashi, hakan yasa yayi saurin kauda kanshi, ai dasauri takoma daki, kallon Sarkin Fada yayi wanda ko rawani babu akanshi, dagashi se babbar riga,, jikinshi kam ko wando babu. Hannu Sarkin Fada yadora akanshi yana fadin shikenan yau kuma ahaka tazo mani. Waziri cike da bacin rai yasa fadawa sukamashi, Jakadiya Karima tace ai dama kullum ina fada maku kune bakwaji, yau ga irin ta nan, nikam baruwana, Allah yakara, hanyar waje tanufa tana shirin fita. Wani kallo da Waziri yayi mata yasa dole taja burki tana raba idanu. Wazirin yace ku kamosu dukan su akaisu kurkutu zuwa gobe, kuma inaso kusaka kwakkwaran tsaro agidan nan, yanzu zan fadama sauran masu tsaro, kada abari kowa yafita daga gidan nan koda kuwa matar Sarki ce, koma waye dole akirani kafin yashigo ko yafita. Haka aka tasa keyarsu zuwa kurkutu. Medaki kuwa tana daki tarasa inda zata sa ranta. Suna zuwa asibiti aka karbesu akayi emergency dasu, kowa aka fara bashi temakon gaggawa, cikin lokaci kankani Areef ya farfado, sede beauty ko alamun motsi batayi, hakan yasa likita yace akai Yarima dakin hutu, nan suka cigaba da duba Beauty. Tunda Areef ya farfado yafara kiran beauty, kuka yasakama Haisam da Jakadiya Safeeya, se lallashin shi sukeyi, Areef yace wlh idan wani abu yasami beauty na, nima Momy zata rasani. Haisam yace kadena fadin haka Areef insha Allahu zata warke. Karar wayar Haisam ce ta katsesu, Areef yace idan Momy ce kace mata ban farfado ba dan Allah. Yana dagawa tace Haisam yaya jikin Yariman? Wani irin haushi yaji, wato ita ta danta ma kawai takeyi. Ahankali yace Momy Areef yana cikin wani yanayi, addu,a kawai zakitayashi. Cike da tashin hankali tace ina likitan banishi, yace suna can akanshi suna bashi temako. Dan Allah Haisam kace ma likita yayi duk yanda zeyi kada dana yarasa ranshi, ko wani abun yasameshi dan Allah. To kawai yace mata, yakashe wayar. Runtse ido Haisam yayi yana karajin haushin kalaman Momy, Areef yace hankalinta yatashi ko?. Kai kawai yadaga mashi, yace ina ganin matsalar mu zatazo cikin sauki, sbd Momy tana sonka sosai, dan haka dole muhada mata plan. Murmushi Areef yayi yace haka ne, abokina nagode, yanzu muje inga jikin beauty na. Jakadiya Safeeya tace a,a Yarima ka kwanta jikinka babu kwari, likitoci suna kanta suna nema mata sauki. Komawa yayi yakwanta zuciyarshi tana zafi. Sarki Qaseem ne, afalonshi hankalinshi tashe da abinda Waziri yafada mashi sungani apart din Medaki, haka yazauna yadafe kanshi da hannu 2, jin haryanzu shiru bega Gimbiya Suhailat tafito ba, yasa yatashi yanufi dakinta, kwance yasameta tana ta kuka, cikin sauri yakarasa gurinta tare da kamota ya rungume. Kara rungumeshi tayi tasaki wani sabon kuka, shafa bayanta yafarayi yana fadin meyafaru kike kuka haka? Kanta tadago, tana share hawaye tace shikenan munshiga 3 Hubby, zamu rasa danmu guda 1 da Allah yabamu. Cike da tashin hankali Sarki yace bangane mikike nufi ba, meyasamu Areef din ? Ko hadari yayi? Kai tashiga girgiza mashi, tace yana can asibiti likitoci ma sunkasa samo kanshi. Sarki yace dan Allah kitashi kifadamun abinda yafaru, wlh zuciyata gab take da bugawa, bakisan irin tashin hankalin daya sameni ba, kifadamun abinda yafaru tunkafin nima kirasani. Ai dasauri Gimbiya ta tashi tana kallonshi, se alokacin ta kula da yanayinshi, idanunshi sunyi ja sosai,cike da kaduwa tace hubby dan Allah meyafaru, kallonta yayi dan yafara kulewa da ita, tureta yayi cike da bacin rai, yace ya ina tambayarki kina tambayata dan kin rai nani, kawai kifadamun abinda yafaru idan bahaka zanbar maki gidan. Matsowa tayi ta rungumeshi tana kuka, dan tunda suke betaba yimata irin wannan ba, asalima bata taba ganinshi cikin irin wannan yanayin ba. Dagowa tayi tajawoshi suka zauna bisa gado, kanshi tajawo tadora saman cinyarta tana ta shafa kanshi, lumshe ido yayi, yana sauke ajiyar zuciya. shiru sukayi nawani lokaci, jinyayi shiru yasa tadagshi ta tashi takawo mashi ruwa mesanyi, dakanta tabashi, kofi guda ya shanye, sannan takara jawoshi yakwanta akan cinyarta. Ahankali tana shafa kanshi tace hubby karika fadin Innalillahi Wainnailaihirraji,un, kayi haka harso 5, sannan infada maka abinda yafaru, amma ina fatan bazakamun fada ba idan kaji abinda nayi? Cike da fargaba Medaki tashiga falon Gimbiya Zakiyyah, alokacin tana zaune tana hutawa, kallonta tayi tace kekuma lafiyarki zaki shigo mani gida ahaka, ko Sarki ne ya mutu? Medaki tazauna tace ai da mutuwa yayi zefi sauki da halin dazamu shiga nida ke, da su Jakadiya, cinkin lokaci kadan. Tashi tayi daga kishingiden datake tana yamutsa fuska tace bangane abinda kike nufi ba? Anan tafada mata duk abinda yafaru, har halin datake ciki ita da Sarkin Fada seda tafada mata, dan ita tariga da tagama yarda da ita, tunda taga halinsu daya ne. Wani irin miskilin murmushi Gimbiya Zakiyyah tayi, tayi mata wani irin kallo, tace. Lallai bansan ke Jahila bace se

Chapter 8 of 13