Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kuwa tun faduwar dayayi haryanzu akwance yake tun maganar dayayi da farko bekara cewa komai ba. Gimbiya Suhailat da Safeeya se kuka sukeyi, Baban Rayhana kuwa zaune kawai yake, idonshi harsun kumbura sbd kuka, yakasa cewa komai. Abu kamar wasa har dare yayi babu Fulani, yan sanda harsungaji da nema, hankalin kowa atashe yake, banda munafukai, sede Jakadaiya tana zaune kusa da Sarki, idonta itama ya kumbura dan kuka, mutane se hakuri suke bata. Waziri yakira malam yayi mashi bayanin halin da,akeciki, shima ya jajanta masu. Yace sujirashi zuwa washe gari. Washe gari tunda asuba. Malam yakira waziri yace mashi agaskiya Fulani tana cikin mawuyacin hali, sede besan inda take ba, amma kuma tana raye, za,a cigaba da addu,a. Anan yafada mashi halin da Sarki yake ciki, anan malam yace bakomai nan da kwana 2 zezo se asan abinda za,ayi. Jikin sarki babu sauki, ko abinci bayaci se dakyar suke matsa mashi yaci kadan, Ranar da Malam yazo ne, suka shiga suka tattauna da mayan fada, kuma suka yanke hukuncin nada Qaseem amatsayin Sarkin masarautar Bubayero. Lokacin da Qaseem yaji kin amincewa yayi. Da kyar suka shawo kanshi, washe gari aka nadashi Sarki. Bakaramin tashin hankali Gimbiya Zakiyya tashiga ba, se fada take tana fadin wannan ai shine kai kai koma kan mashekiya, wato munyi abu kuma yadawo kaina, kai bazeyuwu ba yanzu shikenan natashi daga matar Sarki? Wlh dasake. Jakadiya tace haba Gimbiya najifa ance rikon kwarya ne aka bashi, da sarki yasamu lfy zemaida mashi mulkinshi. Haka sukayita bata baki, da kyar ta hakura, abu daya ne yasata kara yarda mulki zedawo hannunsu dataji ance Qaseem yace baze dawo gidan Sarki ba. Bayan anyi nadi malam yakoma Darazo, haka akacigaba da nema ma Sarki magani da adduo'i, ankaishi asibitoci dayawa amma jikinshi babu sauki, matsalar shanyewar barin jiki ne tasameshi, hakan yasa aka fara yimashi gashin kashi, sede babu yanda basuyi ba akan afitar dashi waje, amma sarki yaki yarda koda suka fadama malam, seyace su kyaleshi, babban abinda zesa yadawo dede to ganin Fulani ne, hakan yasa suka kyaleshi aka cigaba da yimashi maganin gida. Medaki kuwa cin duniyarsu sukeyi da tsinke, ita da Sarkin fada. Duk wani munafunci yadawo daga Jakadiya se Sarkin Fada. Gimbiya suhailat da Safeeya haryanzu sunajin kadaicin rashin Fulani, Babanta kuwa tundaga ranar yadena zuwa ko ina kullum yana kofar gida, sede masu aiki suzo suyi mashi aiki sutafi. Wannan shine asalin labarin Masarautar Bubayero. Zamucigaba da cigaban labarin anext page. Nagode Ur's NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤 AMAKABARTA AKA HAIFENI 🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤 (The story of hard kingdom) Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 65 ⚜70 Tafiya sukeyi amota, Jakadiya Safeeya, kallon Wannan mahaukaciyar kawai takeyi, tana kara tuno maganganun da malam yafada mata ana gobe zasu taho, waigawa tayi takara kallon Yar Baba wadda tayi lamo ajikin Baba tana ta bacci. Aranta tace tabbas suna kama sosai ma, sede kawai wahalar duniya zatasa baza,a iya gane kamar suba. Dole nayi yanda malam yace idan har muna son musami abinda muke so. Tunawa tayi da abinda malam yafada mata akan Waziri, aranta tace tabbas da ace kowane Sarki zesamu mutum me amana kamar Waziri dayaji dadi, addu,a tayi akan Allah yate makesu akan mutanen masarautarsu. Alokacin dasuka isa Masarautar Bubayero Jakadiya Safeeya tayima Waziri waya akan sun iso, alokacin gurin karfe 12 , Waziri yace togani nan zuwa. Yana zuwa yabada umarnin abude masu gate, direct gurin part din Sarki Qaseem suka nufa, dayake ranar asabara ce, kuma azahar batayi ba, babu kowa awaje se bayin dasuke kai da kawowa. Suna fitowa Jakadiya Safeeya takama matar, shi kuma Baba yakama Yar Baba Waziri yayi masu jagora zuwa bangaren Jakadiya Safeeya, dayake, dakuna ne, guda 2 se falo da kitchen, kuma kowane daki akwai bandaki aciki, idan kaga yanda Gimbiya Suhailat tasa aka gyara ma Jakadiya Safeeya part dinta zaka dauka nawata mekudice, babu abinda ba,a zuba ba na kyale kyale afalon, dakunan ma haka, gidan yayi kyau sosai. Duk da abangaren Gimbiya takecin abinci amma a kitchen dinta ma akwai kayan girki da kayan abinci. Bayan sun shiga Waziri yakalli Baba yace sannunku da hanya, Baba yace yauwa munsameku lafiya? Yace lafiya lau, Waziri yace Alhamdulillahi Baba gashi kazo masarautar mu, kuma insha Allahu zakaji dadin zama damu, sede akwai abubuwan danakeso ka kiyaye kuma ka kula dasu, na farko de nasan malam yafada maka yanayin yanda gidan sarauta yake, dan haka abu daya zan fada maka shine akwai Wani mutum Sarkin Fada, inaso duk yanda zeso yashiga jikinka kada kabari wata magana wadda tashafeka tahadaku, zan kaika gurin Sarki amatsayin wanda malam yaturo domin kazauna tare damu, ka kula dashi sosai dasauran mutane, idan muka fita zan kaika gurin Baban Gimbiya Fulani, mutum ne, nagari kuma shima dattijo ne, nasan zakaji dadin zama dashi, koba komai daka zauna kana fira da mutanen gidan nan gara karika zuwa gurinshi kuna fira. Baba yace nagode sosai, kuma insha Allah zaka sameni merike alkawari, fatanmu de Allah yabama wannan baiwa tashi lafiya, suka ce amin. Waziri yace muje ingwada maka masaukinka kafin Sarki yafito, kallon Jakadiya Safeeya yayi yace nasan akwai abubuwa da dama dasuke bukata, anjima kamar da yamma zankawo maki kudi, sekije kasuwa kisiyo masu kayan amfani, game da sutura ma, duk kisiyo masu, idan yaso seki hado da dogayen riguna surika sawa kafin tela ya gama dinkawa. Kallon Yar Baba yayi yace daga cikin gidan nan kada kifita ko ina kinji? Ta daga mashi kai, yace yauwa, dakin fita akwai mutanen dazasu kamaki, saurin boyewa tayi bayan Jakadiya safeeya jin abinda Waziri yafada. Murmushi yayi yace tsoro kamar farar kura. Tashi sukayi shida Baba, yace Sena dawo anjiman, tace to mungode, nima abinci zan dafa masu kafin inshiga gurin Gimbiya. Yar Baba tashi tayi ta matsa kusa da mamanta wadda take zaune akasa tayi shiru tana ta wasa da kafet din falon, kwanciya tayi bisa cinyarta, tana mata murmushi, dankwalin kanta mamar tacire, tafara yimata wasa da gashin kanta, ita kuma se lumshe ido takeyi. Jakadiya Safeeya tana kallonsu tace ikon Allah, Uwa da Diya se Allah, gaba daya sungama burgeta, murmushi tayi tace Allah yasaka maki, akan duk wanda yayi maki wannan abun. Tashi tayi tanufi kitchen. Waziri ne, zaune afadar Sarki, bayan sungama gaisawa yafada mashi Jakadiya Safeeya ta dawo, tare da wani tsoho, malam yace sutaho tare, yazauna anan, amma nabashi masauki abangarena, shine nace bari infada maka. Murmushi Sarki Qaseem yayi yace, Waziri ai duk abinda kayi dede ne, babu laifi, kazaba mashi duk aikin daze iya mesauki kasan abinda zaka rika biyanshi ai? Yace hakane, godiya muke. Sarki Qaseem yace Waziri akwai maganar danakeso muyi akan Yarima, kasan yagama karatunshi kuma yacemun shi aikin gwamnati yakeson yayi, to munyi magana da abokina harma an daukeshi , ranar litinin zefara zuwa, anan gidan gamnati, sun bashi assistant director. Kuma nasan saboda abokinshi ne yanace yanason yayi aiki acan, dan shima acan yake aiki. Kasan wani magana dayazo mani da ita? Munyi mashi maganar aure, Momynshi tanaso tayi mashi maganar diyar yayarta datake can kasarsu, amma seta fara tambayarshi koyana da wadda yakeso, budar bakinshi se cewa yayi yafison yasamu wadda bata fito daga gidan sarauta ba. Haba Waziri yama zece haka, ko Yaya daya auri mata 2 ba yan sarauta ba, ai matarshi tafarko daga gidan sarauta tafito, shine mukace bamu yarda ba, amma zaka iya kiranshi ka karaji daga bakinshi, kasan banason bacin ranshi, inaso kanuna mashi nayarda yafara auren yar sarauta daga baya se ya auri zabinshi. Waziri yace wannan ba wata matsala bace daza'a bata rai, kabarni dashi zanji tabakinshi tunda beriga yasamu wadda yakeso ba, ai dasauki, kuma zanga abokinshi Haisam nasan shima zeyimashi magana. Murmushin jin dadi Sarki Qaseem yayi yace. Hakan yayi kyau, muje muga jikin Yaya. Jakadiya Safeeya ce zaune afalon Gimbiya Suhailat, Gimbiya tace bakiji yanda naji ba, yan kwanakin nan dabaki nan, idan Sarki yafita sede inta zama nikadai, dariya Jakadiya Safeeya tayi tace nima duk banji dadi ba, ya Sarki da jikin? Gimbiya tace jiki kam dasauki, da ranar dasu Waziri suka kawo mashi magani, dakuma maganar da malam yayi akan Fulani ranar har murmushi seda yayi, kuma nantake yashanye maganin, inasha Allahu zesamu lafiya. Jakadiya tace Allah yabashi lafiya, ina dana Yarima?. Hmmm Yarima rigima, kinsan abinda yazo mana dashi kuwa? Tace a,a. Nan tafada mata yanda sukayi dashi, tace kuma nibazan amince mashi ya auri kowa ba, se jinin sarauta, Jakadiya tace kiyi hakuri, ita harka ta aure ba,aso ana tsanantawa acikinta, addu,a yakamata kiyi mashi amatsayinki na mahaifiyarshi se Allah yayi mashi zabi nagari. Gimbiya tace hakane, amma nafison yabi zabin dana yimashi, diyar yayata nakeso ya aura,duk da ban fada masuba, banaso infada masu Yarinyar tasa abun aranta, nasan bayanzu zatayi aure ba,shiyasa nayi shiru harseya amince, sannan nayi masu magana. Jakadiya tace bakomai Allah yashige mana gaba, nima zanyi mashi magana tunda de besamu wadda yakeso seya auri zabinku, idan yaso daga baya seya auri zabinshi. Gimbiya tayi murmushi jin dadi tace shiyasa nake sonki. Allah yayi mana zabi nagari. Da yamma kamar yanda Waziri yace, haka yasa driver yadauki Jakadiya Safeeya yanufi kasuwa da ita, acan tasiya masu kayan amfani dayawa, sede yawan siyayyar duk ta Yar Baba tafi yawa, kananan kaya ma duk nata sunfi yawa, dasauran kayan amfani na yan mata. Data gama suka wuce gurin tela, anan tayi mashi bayanin yanayinsu tabiya kudin dinki yabata ranar karba. Jakadiya Karima ce zaune afalon Gimbiyar Babbar Gida tare da Medaki, Gimbiya tace waini Jakadiya kina kula da Suhailat kuwa? Kada fa ta shammacemu kamar yanda Rayhana tayi mana. Jakadiya tace haba Ranki yadade ai ita da haihuwa sede alahira, kada kidamu bazan baki kunya ba. Murmushi tayi tace, haka nakesonji. Medaki tace bari intashi inje nasan yanzu angama shirya Sarki inje induba jikinshi, yamutsa fuska Gimbiya tayi ta kauda kai, Jakadiya tace afito lafiya Gimbiya. Tana fita Gimbiya taja tsaki tace aikin banza kamar wata tsiya zata iya yimashi, ni wannan mata tsau tsayi ne kawai yasa Sarki ya aureta, shide talaka duk yanda akayi dashi baya iya sakewa. Shiru de Jakadiya tayi bata ce komai ba, tashi tayi tace bari inje gurin Sarkin Fada. Koda Jakadiya Safeeya takoma part dinta har lokacin maman Yar Baba bata tashi daga baccin datakeyi ba, saboda acikin maganin da likita yabata akwai mesa bacci, dan yace idan tana yawan bacci kwakwalwarta zatafi samun hutu, YarBaba kuwa tana zaune tana kallo. Jakadiya tace Yar baba zokiga wani abu, tashi tayi tamatsa kusa da ita tazauna tare da jingina da jikinta, jakadiya Tayi murmushi tace, hmmm ke kam mage ma nan taganki tabarki inde gurin sonjiki ne. Dariya Yar Baba tayi takara kwantawa jikinta. Kayan tafiddo tafara nuna mata, hada inner wears duk tarika gwada mata yanda ake saka su, se murna Yar Baba takeyi, Jakadiya tace zankoya maki yanda ake amfani dasu duka, kuma kinsande nafada maki banason kazanta ko? Kai ta daga mata, tace yauwa, yanzu tashi muje ciki kiyi wanka semu fara. Ranar litinin Areef yafara zuwa office, aranar duk macen data ganshi se miyanta ya tsinke, sbd kyawun da yayi, tare suke da Haisam, Areef yace nifa nafara tsarguwa, naga se kallona akeyi. Dariya Haisam yayi yace kada kadamu sunga dan saurayi me kyau ne. Duka ya kaimashi yana fadin kai dan iska ne, yace emana kasani ko anan kasamu zabinka tunda babu yar gidan sarauta acikinsu. Areef yace Allah ya kyauta, anfada maka ni matata zatayi aiki ne, lallai ma, kai bakasan irin macen danake so na aura ba. Kawaide katayani da addu,a. Haisam yace ato idan kuma nizan rigaka aishikenan,Areef yace nima zanfi son haka, da haka suka isa Office dinsu. Jikin Sarki Hasheem yafara sauki sosai sbd yanzu yanashan magani tunda yaji maganar da Malam yayi, kuma yana cin abinci sosai, hakan yasa Sarki Qaseem yace afara fita dashi fada hakan zerika rage mashi zaman kadaicin dayakeyi. Haka suka cigaba da rayuwa agidan Sarki, babu wanda yasan dazamansu, aduk lokacin da Baba yaso ganin Yar Baba yakanje yaganta susha fira, har mamakin ganin yanda tacanza cikin lokaci kadan yakeyi, gashi tsafta agurinta kamar da ita aka halicceta, akullum setayi wanka so 3 kuma ko sallah tayi setayi kwalliya, Jakadiya safeeya kam har mamakin saurin fahimtar datake da ita take, kome takoya mata ba wuya tadaukeshi. Akullum da dare kafin su kwanta se sunyi karatun littattafai, dan zaman datayi takara sanin abubuwa dayawa agurin Jakadiya safeeya, harta da girki tafara koya mata, sbd tace idan bata nan setarika dafa masu. Duk da ankawo dinkunansu amma bata son saka atamfa ko less, tafison tasa kananan kaya, Mamanta kuwa tunda takeshan magani, yanzu haukanta da sauki, batayin komai, sede tazauna tayi shiru idan kuma kaga tana dariya to ita da yarta ce, duk da baccinta yafi yawa akan idonta biyu. Zaune Areef da Haisam suke acikin lambu suna hutawa, babu kowa agurin, danshi Areef becika son fadawa suna binshi ba, yafison daga shi se Abokinshi Haisam wadda yakasance da ga dupty gvernor na gombe, kuma tare sukayi karatu dashi. Yar Baba tana gama kwalliya tafito dasauri dan ta nuna ma Jakadiya dan tasan bata fita ba, tana zuwa falo taga bata nan, kitchen tashiga nan ma bata ganta ba, turo baki tayi dantagane tafita, hanyar dataga tana bi tashigo ko tafita tabi, tana zuwa ta tura kofar cikin sa,a tajita abude, murmushi tayi tafita. Cike da tsoro tafara takawa tana bin cikin lambun, swimming pool tagani kallonshi tayi. Taci gaba da tafiyarta, can taji dawisu yafara kuka, ai batasan lokacin data juya dagudu zata koma inda tafito ba, cikin rashin sa,a tayi tuntube da dutse kawai tafada cikin ruwan. Su Areef dasuke zaune nesa da ruwan sukaji karar wani abu acikin ruwa, koda Areef yakai kallonshi ga ruwan kawai yaga mutum yana ta daga hannu da kafa acikin ruwa. Cikin sauri yatabo Haisam yana nuna mashi, duk da basu san kowaye ba, Dasauri suka nufi bakin ruwan. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady ) 08028525263 [23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤 AMAKABARTA AKA HAIFENI 🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤 (The story of hard kingdom) Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 70 ⚜75 Babu bata lokaci Yarima Areef ya fada cikin ruwan, yana zuwa kusa da ita yadaukota, alokacin tasha ruwa harta suma, fitowa yayi daga ruwan tana rungume ajikinshi, abisa kafet din dasuke zaune yakwantar da ita yadora kanta saman cinyarshi, Haisam yana biye dashi duk sun rude. Kallon tsoro, mamaki suka farayi mata, addu.a duk wadda tazo bakin Areef yinta yakeyi danshi gani yake kamar ba mutum bace. Haisam yace Areef bakada hankali kana ganin kamar ba mutum ba amma zaka dorata akan cinyarka? Tunda de kacirota tashi mutafi, fara jan hannun Areef yayi. Areef da jikinshi yagama mutuwa sbd tsabar firgici bema san yanayi ba. Da karfi yajashi sannan yadawo hankalinshi, katashi mubar gurin nan, nidama can nafara zargin gurin, gashi yanzu munfara gani. Areef yafara girgiza kai, yamaida kallonshi kan kyakkyawar fuskarta, sannan yace ba aljana bace, duk da bantaba ganinta amasarautar nan ba, amma kalli kafarta babu alamun tako ajiki. Haisam yace anfada maka aljanu basa fitowa asiffar mutane? Hmmm kaga malam wannan yarinya kyanta yayi yawa, wlh zantafi inkira mutane ko katashi mutafi. Idanun Areef suka cika da kwalla yakalli Haisam yace dan Allah, katsaya ni nayarda mute maketa ta farfado, kaga zamu fidda kanmu daga zargin da muke mata. Haisam yace naji, idan ma Mutum ce daga ina tafito? Areef be tsaya bashi amsa ba, kawai yaduka tare da saka bakinshi cikin nata yafara hura mata iska, shiru yaji, yamike yana kara kallonta. Kamshin jikinta duk yagama cika mashi hanci, Haisam yace kadanna cikinta, hannu yasa, jikinshi se rawa yakeyi yafara danna cikinta, can sega ruwa yafara fitowa ta bakinta, haka yayi tayi, harseda tagama fitar da ruwan datasha. Tari tafarayi hakan ya tabbatar masu data farfado, cike da firgici ta tashi ta shige jikin Areef, duk ta kanan nadeshi, tafara kuka. Areef kasa magana yayi, dan duk tasakan mashi kasala ajiki, dukawa Haisam yayi yace ya isa haka, tashi muji daga ina kike. Kintashi tayi, sede tadena kukan datakeyi , tayi lamo ajikin Areef kamar wata yar baby, Areef kuwa kallonta kawai yakeyi, bemasan abinda Haisam yake fada ba, ganin haka yasa Haisam ya bugi kafadar shi, dasauri yamaida kallonshi gurinshi, gira yadaga mashi yana fadin kallon fa nameye?. Kabari mutambayi yarinya daga ina tashigo amma kawani rungumeta kamar kana shirin bata mama. Murmushi Areef yayi yana sosa kai. Dagota yayi, ahankali ta tashi tana kallonshi, sede taki barin jikinshi, se rawar sanyi takeyi. Areef yace daga ina kike, meyakawoki nan har kika fada ruwa? Hannu ta daga tana mashi nuni da hanyar part din Jakadiya Safeeya. Haisam yace baki iya magana ne, kinaji ana maki magana zaki tsaya kina mana maganar kurame, kuma gashi alamu yanuna kinji me yace. Komawa tayi jikin Areef zata kwanta, dan gaba daya wani zazzabi takeji, sanyi sekara shigarta yakeyi. Dasauri Haisam yajawota yana fadin yau ko sunanki mage senaga karshen son jiki. Areef yace haba bros kabita ahankali mana, kama hannun Areef tayi tarike sosai tafara kuka. Tsaki Haisam yaja yace toni zantafi. Areef kamar zeyi kuka yace plsss kabari muji daga bakinta. Kallonta yayi, yace Beauty tashi kifadamun daga ina kike kinji, kinga kada yatafi yabarni kuma nasan mutane zekira kuma kamaki zasuyi, ai dasauri ta tashi tarike hannunshi, shima tashi yayi yana murmushi. Haisam yace daganinta batada gaskiya gashi daga yin maganar kamawa tamike. Hannu tasa tana kara nuna mashi hanyar data fito, Areef yace baki iya magana ne? Kai tadaga mashi, tare da fara janshi zuwa hanyar. Atunaninshi ko sanyi ne yahanata magana, hakan yasa yafara binta. Da har Haisam ya kyaleshi se kuma yayi tunanin kada ta cutar dashi seyabisu. Sunkusa zuwa gurin sukaci karo da Jakadiya tafito daga cikin gida hankalinta atashe. Cak ta tsaya tana masu kallon mamaki, kara kallon Yar Baba tayi, nan hankalinta yafara tashi ganin kayanta ajike, sede ganin wanda suke tare, yasa taboye tashin hankalinta. Da gudu taruga ta rungume Jakadiya Safeeya, janta tayi zuwa cikin gida, suma suka bi bayansu. Seda tashiga da ita daki tasata tacire kayan tace tasaka wasu kafin tafito, juyawa tayi takoma falo. Bayan sungama gaisawa, Areef yace Aunty ashe beauty agidanki take? Kawai muna zaune nida Haisam agurin lambu semukaji karar wani abu acikin ruwa, muna dubawa ashe ita ce tafada, koda nacirota, ta suma, da kyar ta farfado. Shine tabamu tsoro, dan bamutaba ganinta agidan nan ba, gashi kuma kyanta ya kai akirata da aljana. Koda muka fara tambayarta bata bamu amsa ba, sede kuma tanajin abinda muke fada, shine daga karshe tajawo ni muka taho nan. Ajiyar zuciya Jakadiya tayi jin bayanin da Areef yayi mata. Murmushi tayi tace Allah sarki sannunku nagode sosai, inbadanku ba kila data halaka, mantawa nayi ban kulle kofar ba, kuma nasan nitafito nema dan banyi mata sallama ba dazantafi. Shirun dakaji tayi ai bata iya magana, tunda aka haifeta ahaka take, sede tanajin duk abinda aka fada. Tausayinta ne yakamasu, jikinsu duk yayi sanyi bakamar Haisam. Areef yadaga baki zeyi magana kenan tafito, baki yasaki yana kallonta, gani yake kamar ba ita bace, tasaka riga doguwa me siririn hannu tayi mata kyau sosai, kalarta Ja ce, gashi bata daura dankwali ba, fuskarta tasha kwalliya kamar meshirin zuwa gasar kyau, hannunta rike da comb, tana zuwa tafada jikin jakadiya ta mika mata comb din. Murmushi tayi tace Uhm Yar Baba sarkin kwalliya yanzu seda kika kara wata kwalliyar? Kwantawa tayi jikinta takamo hannunta tadorashi akan wuyanta, jakadiya tace kai naji jikinki dazafi, ko ruwan dakika shiga ne, ze sakar maki Zazzabi?. Kai tadaga mata, tana lumshe ido, Haisam yace Aunty ai dama yakamata abata magani tasha, kada yarufeta. Jawo hannunta takarayi tana mata nuni data sharce mata gashinta, fara Sharce mata tayi tana fadin kuma gashi babu magani agidan nan, sede inje gurin Gimbiya kozan samu. Haisam yace a,a bari kawai idan muka fita semu siyo mata, kallon Areef yayi yace kai kuma mr. Watching seka tashi mutafi musiyo magani, shiru yayi mashi yana kallon yanda tarufe ido tana bacci, ga gashinta daya gama tafiya dashi. Dan bakinta yasha red janbaki, tayi mashi kyau sosai. Dukan dayaji akafadarshi ne yamaido dashi tunanin dayakeyi. Hararar Haisam yayi, gwalo yayi mashi yana murmushi. Areef yace Aunty amma bansanki da diya ba ina kika samota? Tace tare muka dawo da ita daga Darazo, acan gidan Malam take, diyar Dan uwanmu ce. Zekara magana Haisam yace katashi muje musamo mata magani bata lafiya, idan mundawo seka idasa tambayar taka. Tashi yayi yana sosa kai yana murmushi yace Aunty semun dawo. Kallonshi tayi tace dan Allah banason inji wannan maganar agurin kowa, koda kuwa Gimbiya ce, ko Sarki, kuje kudawo zakuji dalilina nafadar haka. Suka ce to, fita sukayi Areef yanayi yana waige, bugewar dayayi da kofa ce tasashi saurin dafe goshin shi. Dariya Haisam yasa hada rike ciki, suna fita Areef yakai mashi duka yana kara dafe goshin shi. Haisam ya tsagaita dariyarshi yana fadin sannu abokina ai bansan kaji zafi ba. Areef yace kacigaba lokacinka ne dariya ma yanzu kafara yimani inde akan beauty ne. Haisam yazaro ido yace akwai wata a kasa kenan? Areef yayi murmushi yace a,a sede asama dan iska. Dariya suka saka kafin suka nufi hanyar parking space. Cak sarkin fada yatsaya ganin abinda beyi tsammani ba, adede lokacin dayake fitowa daga part din Medaki, daka ganshi kasan baya cikin nutsuwarshi. Wani irin kallo Waziri yake binshi dashi, cikin tsarguwa Sarkin fada ya matso yana washe baki yace rankaidade barka da fitowa, nima yanzu nafito zani fada shine Jakadiya Karima take shedamun Gimbiya Medaki tana nemana. Toyanzu nashiga ko minti 3 ma banyi ba, tambayta tayi shine kaga nafito. Muje fadar ai can kayi ko? . Da ido Waziri ya kafeshi, bece mashi komai ba, kifce kifce yafarayi yana fadin ai semu wuce ko? Murmushi Waziri yayi ya girgiza kai yace muje, haka suka nufi fada cikin Sarkin fada duk ya duru ruwa, se addu,a yake Allah yasa Waziri be harbo jirginshi ba. Baban Fulani ne zaune akofar gidanshi tare da Baba suna ta fira, dan zaman dayayi bakaramin sabo sukayi ba, Baba yace gaskiya ina tausaya maka halin daka shiga, tabbas ka hadu da jarabawa, sede kuma hakurin dakayi gashi nan Allah yabarka da lafiyarka, kuma dama anason me hkr aduk lokacin da wata jarabawa tasameshi. Baban Fulani yace hakane, nima ada nayi niyar komawa kasata, sede ganin irin karamcin da mutanen nan sukayi mani da kuma rashin sanin Rayhana tana raye ko mace, wannan dalilin shine babban abinda yahanani tafiya, amma insha Allahu nasan za,a ganta tunda de anfada mana tana raye. Baba yace ai Allah baya bacci, koma a ina take wata rana zata dawo. Koda su Areef suka koma jikin Yar Baba yarikice, Zazzabi ya saukar mata sosai, dan bata tabayin zazzabi mezafinshi ba, se kuka takeyi dama kuma gata raguwa, kwance take ajikin Jakadiya Safeeya suka shigo bakinsu dauke da sallama, dasauri Areef yazauna kusa da Jakadiya yana fadin Aunty bade jikin bane?. Tace wlh kuwa, tunda kuka fita ta kwanta shikenan zazzabi yarufeta, Haisam yace Aunty kawai kutashi mutafi asibiti, zaro ido tayi tace A,a kawai ku kawo maganin inbata nasan zata samu sauki, kaga abincinma taki ci. Zata kara magana kenan taji motsi adakin Maman Yar Baba, saurin tashi tayi ta kwantar da ita bisa kujera tace inazuwa bari inshiga bandaki, Yarima kabata abinci kila taci seku bata maganin nasan zata samu bacci, bari infito. Abakin kofa tasameta, dama tasan lokacin cin abincinta yayi jira take Yar Baba ta kyaleta taje ta tadata tabata abinci tasha maganinta, saurin kama hannunta tayi tasama kofar key suka koma ciki, bandaki tajata seda ta wanke mata baki tayi fitsari, sannan suka dawo tazauna dan tabata abinci. Abincin yadauka ya matsa kusa da ita, hannu yasa yadagota, tana tashi ta lafe ajikinshi, zama yayi akan kujerar, hakan yasa takara shigewa jikinshi. Dariya Haisam yayi yazauna yana fadin wlh Beautyn Areef keda mage bansan wanda yafi wani son jiki ba, Areef yace kaga malam kabarta taci abinci tunda ba,a jikinka ta kwanta ba. Haisam yace ato adebi ahankali dan wlh kosannu bazan cemaka ba idan kacemun,,,,,,, gira yadaga mashi yana murmushi yace ai kagane?. Areef yace kaide kasani dan iska kawai, kamata yayi ya rungumeta ahankali yace kinajina ko beauty? Kai tadaga mashi tana turo baki, murmushi yayi yace yauwa idan bakiso inkira mutane sukamaki to kici abinci inbaki magani zaki warke, ai dajin haka tabude baki. Dariya Haisam yayi yace anya beauty bata tsoron mutane kuwa? Wannan shine karo na biyu danaga tana tsoro idan ance mutane. Areef yace haka ne, nima nalura da haka, kuma inaso Aunty tafito tadan bani labarinta, dan ban gamsu da bayaninta nadazu ba, yarinyar nan tafi kama da diyan larabawa. Haisam yace shiyasa naga kuna dan kama , harararshi yayi yace ta ina? Haisam yace wlh ba batun wasa ba, dazu data kulle idonta na kalleta naga kundanyi kama, musamman tagurin idanunku da bakinku. Areef yace kaji dashi, nibanga wata kama ba, kyaleshi yayi yadauki cokali yafara bata abinci. Hankalinshi gaba daya yana gurin kallon yanda take cin abincinta, shikanshi abun burgewa ne, tana jikinshi ahaka tagama cin abincin, shiko Haisam kallonsu kawai yakeyi, yafiddo waya yana daukarsu vedio, sun bala,in burgeshi, gani yake kamar atare aka halicce su. Magani ya ballo sede da kyar tasha, shima seda yayi mata wayo, tana gamasha ta koma jikinshi ta kwanta, kallonta yayi yace bacci zakiyi? Kai tadaga mashi, tare da lumshe ido, ko minti 5 ba,ayi ba. Bacci yadauketa. Areef yace beauty bakida matsala, yarinya cekace jaririya acikin minti 5 harkinyi bacci. Bayan tagama bata abinci tabata magungunanta, sannan tajata zuwa bandaki, wanka tayi mata, bayan sunfito tagoge mata jiki, ta dauko wata doguwar riga tasa mata, kwantar da ita tayi bisa gado. Idanu ta kura mata ganin yanda dan kwanakin dasukayi tasake sosai, kara kallonta tayi, gabanta taji yana bugawa dasauri, matsawa tayi kusa da ita dan takara tabbatar da abinda tagani. Tabbas wannan matar zargin malam yazama gaskiya, wasu hawayen farin ciki ne, suka rika fito mata, zama tayi takama hannunta tana fadin ita ce, wlh itace, dama nasan malam baze taba fadin abu yazama ba haka ba, aiko ayau Sarki zeji labari medadi. Waya tadauko takira Malam, bayan sungaisa, yace Safeeya yanajiki cikin farin ciki haka? Wlh malam tunaninka yazama gsky, dama kace kana tunanin wannan matar kamar Gimbiya Fulani, wlh, itace, nadade dafara tunanin haka tun akan diyarta, kamarsu da ita nake gani afuskarta, sede bakowane ze gane hakan ba, amma nide wlh yanda nasan Fulani kamarta bazata iya bacemun ba. Hamdala Malam yayi yace nadade da tunnin haka, sede kinsan irin wannan al,amarin ba,a saurin yanke mashi hukunci, dole muyi ma Allah godiya, kuma zansa ayi sadaka, sede akwai abu daya danakeso daga gareki, wannan

Chapter 6 of 13