anan mutane suka haushi da duka har
gidanshi, seda sukayi mashi raga raga sannan abokanan
Cacarshi sukace sutashi subar gidan dasuke ciki zasu sayar sudau kudinsu.
Uwani da Nafeesa bakaramin shiga tashin hankali sukayi
ba, suna zaune suka farajin hargowar mutane, Mal. Audu
yana kwance ko tashi be iyayi yaji mutane sun shigo
sunfara yimasu wurgi da kaya, nan take zuciyarshi ta
buga ya mutu, koda mutanen suka zo gurinshi se suka
samu ya mutu, anan suka fadama Uwani sukayi
tafiyarsu, kuka suka saka Uwani tana fadin shikenan
katafi kabarmu da tashin hankali.
Da kyar suka samu wasu daga cikin abokananshi suka
yimashi wanka da sallah suka kaishi makabarta, duka
basufi mutum 10 ba wadanda suka kaishi. Bayan kwana
biyu da rasuwarshi Uwani tafara rashin lafiya, gashi
basuda abinci bare kudin magani, haka Nafeesa tayita
jinyarta, koda taje gurin saurayinta yabata kudi tasiyo mata magani korarta yayi dan alokacin ma tare da wata
tagansu, haka tadawo tana ta kuka. Lokacin da akayi 7 da mutuwar mal. Audu masu siyan gida sukazo, anan suka
koresu, duk inda sukaje neman temako babu me
temakonsu dan babu wanda besan halin Nafeesa da
uwani ba. Daga karshe suka baro garin har suka hadu da
Sarki.
××××××××××
Bayan kwana 7 da rasuwar Maman Nafeesa aka daura
aurenta da sarki, mutanen garin sunyi matukar
mamakin aurensu, sede wasu suna cewa auren tausayi
ne Sarki yayi. Duk wasu kayan aure Sarki ne yayi mata,
aka gyara mata bangarenta aka hadata da bayin dazasu
rika yimata hidima. Haka Sarki yasa Jakadiya takoya
mata duk wasu al'adu na masarautar.
Seda Nafeesa tayi wata 1 agidan sarki Jakadiya tana
gyarata sannan takaima Sarki ita, bakaramin kyau tayi
ba, dan gyara akayi mata bana wasa ba, fatar jikinta
kanta seda ta canza. Abubuwa da dama Jakadiya takoya
mata, wanda aciki harda biyayya ga gimbiya dan tafada
mata ko ita wacece kowa binta yakeyi. Haka kuma ta
bata Gimbiya Suhailat agurin Nafeesa.
Aranar da Sarki ya kwana da Gimbiya Nafeesa yasameta
bata da budurci ajikinta, yayi mamaki sosai, bayan sunyi sallar asuba yadawo yasameta tana kuka, zama yayi
yafara tambayarta lafiya, cike da kissa tace kayi hakuri rankai dade dama nasan tunda Mama tarasu bata ida
baka labarina ba, nasan dole zaka fahimci wani abu,
nasan kagane banzo da budurcina ba, hakan yasamo
asaline ta dalilin barayin dasuka shigo mana gida ana
gobe za'a koremu daga garinmu, sune suka yimani fyde
wanda shine dalilin ciwon Mamana dan Allah kayi
hakuri, naso ace tunkafin adaura auren mun samu dama
nayi maka bayani dako daya daga cikin bayinka kahadani
dashi.
Tausayinta yakara kama Sarki yace bakomai Nafeesa,
kada insake inji wannan maganar abakin kowa, kibarta tsakaninmu nayafe maki kinji, tace tonagode.
Haka zamansu yacigaba da tafiya, Sarki da kyar yasamu
yashawo kan Qaseem dan tunda yayi aure yake fushi
dashi. Gimbiya Shuwa da Gimbiyar Baban Gida da
Gimbiya medaki kwata kwata basa shiri, shiyasa babu
me shiga harkar wani, Su biyu sunware Gimbiya shuwa,
basa sata acikin harkarsu, sede itama Gimbiya madaki
wato Nafeesa awulakance take agurin Gimbiya babba, se
abinda tace takeyi, ita kuma tana kaskantar da kanta ne, kawai dan tasamu fada agurinta, dan Gimbiya Shuwa
bata kulata, sbd akidarta na tsanar wanda ba dan sarauta ba.
Sarkin Fada ne, da jakadiya zaune alambu. Sarkin Fada
yace waini Jakadiya haryanzu acikin matan Sarki babu
me ciki ne? Yamutsa Fuska tayi tace inaji fa Sarki beda rabon samun da aduniya, bare aje ga maganar magaji,
kaga ko mutuwa yayi ai sede abama Kaninshi. Sarkin
Fada yace kinko san banason Qaseem ya anshi mulki
kinsan yafi Sarki mugun hali, towai meze hana muyi
masu kullalla. Jakadiya tayi dariya tace lallai Sarkin fada baka da dama, aini nafison ace sunbata shida kaninshi,
shiyasa lokacin dayayi fushi dashi dan zeyi aure naji
dadi, sede dayake akwai kauna atsakaninsu kaga basu
wani dade ba, suka shirya.
Sarkin fada yace amma Jakadiya babu wata hanya
dazakibi kishiga jikin Gimbiya Shuwa? Zaro ido tayi tace ni? Rufamun asiri, kana ganin sbd tsabar jinkai irin nata haryanzu bata yarda da kowa ba, sede mijinta. kai de
kawai ayi sha'ani amma ina nan ina shirya masu gadar
zare kaide kawai ka tsaya kayi kallo. Matso kaji wata
magana. Ko kasan cewa nice nan na hana Gimbiya
Zakiyya haihuwa agidannan? Sarkin Fada yace lallai
Jakadiya nasara maki. Tace uhm kawai ka kalleni kabarni akwai sauran abubuwan bam mamaki atattare dani.
Kaide muje zuwa, da sannu sena tarwatsa farin cikin
masarautar nan, haka nake bani da kyau, banki kowa
yarasa ba, tunda har Allah yasa nazo a Jakadiya.
Muje zuwa danjin sauran labarin. Nagode da kulawarku.
Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
( Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 25⚜30
Masarautar BUBAYERO, babbar masarauta ce mecike da
tarihi, ashekaru 18 dasuka wuce Sarki HASHEEM shine
Sarki amasarautar, yana da Kani wanda suke Uwa daya
Uba daya, su 2 iyayensu suka haifa, kafin iyayensu
surasu mahaifinsu shine Sarkin agarin.
Sakamakon hatsarin jirgi dasukayi shida mahaifiyarsu
wadda ita kadai ce matarshi kuma uwar yaranshi, shine
yayi sanadiyar mutuwarsu. Bayan kwana biyu da
rasuwarsu .Waziri wanda shine mahaifin wazirin sarki
Qaseem, shine yatara jama,a domin anada sabon sarki,
ananne aka zabi Hasheem yayan Qaseem aka nadashi
Sarkin masarautar Bubayero. Kuma shima Waziri
yasauka daga mukaminshi yamika ma babban danshi
wato Wazirin Sarki Qaseem.
Alokacin Sarki Hasheem yanada Matarshi 1 mesuna
Zakiyyah, diyace ga Sarkin Yobe, kuma abokine ga
mahaifin su Qaseem, shiyasa suka hadasu auren
zumunci, duk da Sarki Hasheem baya sonta haka yayi
biyayya ya aureta. Mahaifiyar Zakiyya takasance su 3 ne agurin mijinsu Sarkin Yobe, amma dayake macece
wadda tasan kissa da iya tuggu hakan yasa tazamo yar
gaban goshi agurin mijinsu, baruwanta dabin boka ko
malam, tayarda da kanta.
Hakan yasa Zakiyyah tadauki duk wasu halaye nata.
Kuma da wannan halinne tajawo hankalin Sarki
Hasheem har yabata babban matsayi azuciyarshi.
Alokacin da aka nada mijinta Sarki bakaramin dadi taji
ba, sede babbar matsalar datake damunsu haryanzu
basu sami haihuwa ba, ko batan wata bata tabayiba.
Sede yanda takeyima Sarki yasa baya nuna damuwarshi
akan haka.
Jakadiya itace babbar baiwa datakema Sarki Hasheem
hidima tunkafin yazama sarki, ita kadai yabama amana
aduka bayin gidan, hakanne yasa lokacin dayahau
kujerar mulki yanadata Jakadiyarshi, ko Matarshi
batasan wasu sirrinkanshi ba kamar yanda Jakadiya
tasani, shiyasa kwata kwata basa shiri.
Bayan kaninshi yagama karatunshi akasar misrah
yadawo gida, alokacin Sarki yasa aka gyara mashi part
dinshi anan cikin gidan, kuma alokacin yazo mashi da
maganar matar dayakeso ya aura, Yayanshi bakaramin
dadi yaji ba, dan yana son kanin nashi kamar yanda
shima yakesonshi. Daya tambayeshi wacece yace mashi
diyar Sarkin Misra ce, atare sukayi karatu.
Babu bata lokaci yasa waziri yashirya masu tafi sukaje neman auranta, koda sukaje sunsami tarba me kyau,
kuma anan take aka bama Qaseem auran Gimbiya
Suhailat, Bayan sundawo aka fara shirin biki.
Sati 1 akasa yanazuwa akaje akadaura aurensu, suka
taho Gombe, sede Sarki Hasheem yace base anbasu bayi ba suna da isassun bayi, haka aka kawo amarya akasata
part dinta. Tunda suka hadu da Gimbiya Zakiyya taji ta
tsaneta, hakan yasa bata sakan mata fuska, kowa yanaji
da kanshi, ita Zakiyyah tana ganin ita diyar Sarki ce,
kuma matar Sarki, hakan yasa mulkin yayi mata yawa.
Ita kuma Suhailat tana ganin masarautarsu tafi tasu
Zakiyyah.
Bayan kwana 2 Sarki yasa Jakadiya tadebi bayi masu
yawa takaima Gimbiya Suhailat tazabi wanda takeso,
bayan tazaba Jakadiya tace tazabi amintattar baiwa
acikinsu, wani kallo tamata tace aini bana zabar
amintattiyar baiwa alokaci guda, dan haka ki kama
gabanki idan ina bukatar hakan basekin fadamun ba.
Jakadiya taji zafin maganar haka tajuya tawuce ranta
abace, sede dayake ta iya duniyanci bata nuna mata
afuska ba. Tsaki Gimbya taja, dan ita duk wanda befito
daga gidan sarauta ba gani take beda wani matsayi,
shiyasa ra'ayinsu da mijinta yazo daya, dan shima
sarauta tashiga jikinshi dayawa yana bata muhimmanci.
Sarki Hasheem yakasance mutum ne mesaukin kai
sosai, sede shima yana daraja sarautarsu sosai, kuma
baya son kai acikin masarautarshi, duk wanda ya aikata
laifi ana yanke mashi hukunci dede dashi.
Dalilin aurenshi da matarshi ta 2 kuwa yasamo asaline,
wata rana yafita rangadi shida Waziri da Kaninshi da
fadawa, sunzo wajen gari nesa da cikin gari, se suka
hadu dawasu bayin Allah agefen hanya uwa da diyarta,
yarinyar bazata wuce shekaru 17 ba, tana zaune kusa da
uwar tana ta kuka. Tsayawa sarki yasa akayi yasa aka
kirawosu, sede yarinyarce kawai tazo dan matar tana
cikin halin rashin lafiya bazata iya tashi ba. Tanazuwa tafadi kasa, Waziri yatambayeta meyasa suke zaune anan
haka?.
Tana kuka bata basu amsa ba, Qaseem ya daka mata
tsawa yace waike ba magana ake makiba kin tsaida
mutane, Kallonshi Sarki yayi dan yasan abinda
kaninnashi ya tsana kenan, murmushi yayi yamaida
kallonshi kan yarinyar. Ihun matar dasukajine yasa babu shiri Sarki da Waziri da sauran fadawa suka sauka daga
dokinsu suka nufi gurinta, yarinyar tarigasu zuwa
gurinta.
Jinine yake fita daga hancinta da bakinta, haka tarike hannun yarta hawaye suna fita daga idonta, akusa da ita Sarki ya tsugunna, fuskarshi cike da damuwa, yayi bakin cikin dabasu fito da mota ba, kallon Waziri yayi yace
yazamuyi da ita, yakamata akaita asibiti. Hannun matar
yaji takamo babbar rigarshi, dasauri fadawa suka matso
dansu cire, amma yadakatar dasu. Kara dukawa yayi
yace baiwar Allah kibari mukaiki asibiti kina zubar da
jini.
Kai tashiga girgizawa, ahankali tafara magana, babu
inda zanje dannasan rayuwata tazo karshe, sede ina neman wata alfarma agurinka. Sarki yace inajinki,
kadubi girman Allah, kamar yanda Allah yadauka kaka,
yafifitaka sama da sauran bayinshi badan yafisonka ba,
nasan matsayinka ya girmi alfarmar dazan fada maka,
sede inason kayi jahadi domin ka ceci marainiyar Allah
daga fadawa wata rayuwa.
Sarki yace inajinki, kifadi koma menene nikuma namaki
alkawarin zanzamo mecika makishi. Waziri, Qaseem
sukayi saurin kallon Sarki jin abinda yafada batare
dayasan me matar zata fada ba.
Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 35⚜40
Zaune suke a falon Malam Bello na Darazo, Sarki ne, se
Qaseem da Waziri. Malam Bello babban malami ne,
kuma attajiri, duk da yamanyanta amma sbd ilimin
dayake dashi idan kaganshi zaka dauka shekarunsa basu
kai nashi ba. Shine babban malamin garin Darazo
malamin sosai, yana temakon mutane dayawa agarinsu,
mutanen garin suna matukar sonshi da girmamashi.
Hakan yasa yagina katon gida me bangarori dayawa, ko
yaranshi maza 2 dasukayi aure acikin gidan suke zaune
da matansu, da yaransu, dama kuma beda yara dayawa
yaranshi 4, maza 3 mace 1, itama tayi aure acikin garin bauchi. Matarshi daya uwar yaranshi, se kanwarshi
kuma autar gidansu, tunda mijinta yarasu bata kara aure ba, dama kuma bata taba haihuwa ba, hakan yasa tace
bazata kara aure ba, itama ta manyanta akalla zatayi
shekara 35.
Mutane dayawa idan sukazo garin basuda masauki yana
basu guri acikin gidanshi, ko idan ya musuluntar da
wasu yana basu gurin zama, yana da dalibai dayawa
dayake karantarwa. Haka kuma baya aiki da aljanu, sede
yana fitar dasu kuma suma sunajin tsoronshi, kuma duk
wanda aka kawo marar lafiya yana temaka mashi, hakan
yasa mutanen garin dana wajen gari suke girmamashi.
Yadade yana yima masarautar Bubayero hidima tun
lokacin mahaifansu Qaseem, dan masarautar bata yarda
da malamin duba ko boka ba, hakan yasa koda iyayensu suka rasu basu yarda shiba, duk wani temako kowata
shawara sukan zogurinshi, kuma Sarki baya aiko kowa
gurinshi kode yazo tare dasu Qaseem da Waziri ko kuma
ya aikosu su 2, yauma sunzo domin neman wani
temako.
Bayan sungama gaisawa, Malam yasa ankawo masu
kayan motsa baki, dan sunyi waya da Qaseem tun jiya
yafada mashi suna hanya. Qaseem ne, yafara magana
cike da ladabi. Allah gafarta malam, kamar yanda muka
fara magana dakai jiya awaya. Dama bawani abu bane
akan matsalar rashin haihuwar Yaya, tun tuni naso muzo
shine yake hanawa, shine nace ai koma menene yanada
magani, shine mukazo muji daga gareka.
Gyara zama malam yayi yacire glass din dayake idonshi
yace, hakika nima nadade ina tausaya ma, memartaba,
kuma dama tun kwanakin baya damukayi magana dakai,
nafarayin istahara akan al'amarin. Kuma alhamdulillahi
dama kobakuzo ba nayi niyar kiranka, infada maka
abinda nagani.
Sede inaso kusani bakomai ne, ake fada ba dan kayi
istahara, amma tabbas akwai abinda nagani amma
nabarma kaina, kuma insha Allahu abinda ake so ahana
za,a sameshi, sede muyita rokon Allah, babu abinda
yagagareshi. Kamar kullum abinda nake fada maku kuyi
hankali da mutanen da kuke tare dasu bance kuyi
bincike ba, amma kada kayarda dakowa kuyarda da
kanku, shine zaku zauna lafiya.
Abinda nakeso kusani insha Allahu memartaba yanada
rabon samun haihuwa, sede abinda zan fada maku agsky
ayanzude rabon dana gani zesamu ba'a agurin matanshi
yake ba. Amma koma menene nasan zesamu haihuwa
insha Allahu, sede adage da addu'a inafatan kunfahimci
bayanina? Waziri yace munfahimceka malam, kuma
mungode Allah yasaka da alkhairi, muzamuzo mukoma.
Malam yace tonima inada wata alfarma danakeso kuyi
mani, Qaseem yace haba malam ai kawuce komai
agurinmu kafadi koma menene. To kamar yanda kuka
sani akwai kanwata kuma autarmu, kunsan mijinta
yadade da rasuwa kuma taki yarda tayi wani auren,
shine nakeso dan Allah kozaku tafi da ita can tarika
temaka ma matan sarki dawasu aiyuka inaganin yafi
zamandatakeyi anan tunda can akwai jama,a dayawa.
Sarki zeyi magana Qaseem yayi saurin fadin agaskya
malam naji dadin wannan magana taka, kuma inaso
abani ita inkaima Suhailat, dan mundade muna neman
wadda zata zama mekusanci agurinmu, kasan ni bakowa
nake yarda dashi ba, itama haka, amma tunda daga
gareka tafito, kuma jininkace nayarda da ita sosai. Kuma dama tana da tsohon ciki inata tunanin wadda zata
zauna mata. Mungode Allah yabamu zaman lafiya. Ya
sunanta? Malam yace sunanta Safeeya.
Murmushi Waziri yayi yace mungode malam Allah yasaka da alkhairi. Sarki yace mungode malam, kuma
insha Allahu zamu riketa amana. Malam yace nikeda
godiya, bari inje infada mata tashirya.
Daki yakira Safeeya, sundade suna tattaunawa banji
abinda suke fada ba, haka tafito tashirya tayima Matar
malam sallama da sauran matan gidan, hada kukansu,
haka suka shiga mota suka dauki hanya.
Gimbiya Suhailat taji dadin zuwan Safeeya, dan tanajin
labarin malam agurin Qaseem, shiyasa tajata ajikinta
sosai, dan har karatu take kara mata, hakan yasa suka
saba dawuri, duk wata shawara Gimbiya Suhailat tanayi
da Safeeya, haka kuma baruwanta dashiga part dinsu
Gimbiya Zakiyyah, asalima basu san dazuwanta ba,
kamar yanda babu wanda yasan tana da ciki harya tsufa,
shiyasa taji dadin zuwan Safeeya. Dan Waziri yahana
anuna Safeeya acikin gidan, har seda Sarki yace meyasa
Waziri yace yallabai dan Allah abarta, Qaseem yace
shikenan yanda kace Waziri.
Haka rayuwar gidan tacigaba da tafiya, Cikin Gimbiya
Suhailat harya shiga watan haihuwarshi, Qaseem da
Sarki suna farin ciki da cikin, dan kamar Sarki yafi
Qaseem farin ciki da Cikin, kuma betaba fadama
matanshi ba, dan gani yake kamar sun sani kuma beso
suga kamar shima yadamu darashin haihuwar.
Jakadiya dasu Gimbiya sun hada kansu, Gimbiya Zakiyya
babu abinda takeso kamar haihuwa, ayanzu bata da
abokiyar shawara se Jakadiya, duk wani sirrinta Jakadiya tasani, sede haryanzu bata karbi gurguwar shawarar
Jakadiya ba. Ita ko Gimbiya Nafeesa dama tasan bazata
kara haihuwa ba, dan tunzubar da cikin datayi har so 3, likita yace mahaifarta tasamu matsala. Shiyasa bata da
damuwa agidan, itade burinta kawai tasamu ta tara abin
duniyarta, shiyasa takebin Gimbiya Zakiyya soda kafa,
sede tabangare guda kuma sun hade kansu ita da
Jakadiyya.
Zaune Jakadiya take afalon Gimbiyar Babbar Gida,
kallonta tayi tace inajinki Jakadiya wace shawara kika
kawo? Gyara zamanta tayi takara rage murya tace
Gimbiya bawata shawara bace dama wata dabara
nakawo, nace meze hana kicema Memartaba kina da
ciki. Saurin tashi Gimbiya tayi tace bangane mekike nufi ba. Wace irin magana kikeyi haka, dama ana cikin karya
ne? Murmushi Jakadiya tayi tace Allah yahuci zuciyarki, bahaka nake nufiba. Kinga yanzu ku 2ne matan Sarki,
kuma kece Babba taya za,ayi muyarda wata tashigo daga
baya ace ta haihu ke baki samu naki ba.
Jiya mukayi magana da Sarkin Fada kinsan mutumina
ne, agurinshi nasamu labarin Sarki yace daya samu da
namiji tofa lallai shine zegajeshi, shine nace meze hana kawai kice mashi kinada ciki, idan yaso sekirika saka
tsummuna idan lokacin girman cikin yayi, kinga semuje
gidan marayu mudauko yaro namiji kinga kema kinyi na..... marin da aka dauketa dashine yasata tayi shiru.
Dasauri tamaida kallonta gurin Gimbiya datake ta huci
sbd tsananin bacin rai, cike da tsawa tace kitashi
kibacemun daga nan. Kuma ina me tabbatar maki da
duk ranar dana kara ganin kafarki acikin part dina wlh
sekinbar masarautar nan.
Cike da bacin rai Jakadiya tafito, hanyar lambu tanufa inda suka saba haduwa da Sarkin Fada, wata baiwace
tafito dagudu zata wuce, dasauri Jakadiya ta tareta dan tagane baiwar Gimbiya suhailat ce. Ke lafiya kike gudu
haka? Wlh dama sauri nakeyi inje inyima Sarki Albishir
Gimbiya tasauka lafiya tasamu da na miji. Kara goge
kunnanta Jakadiya tayi tace bangane mekike fada ba.
Dama Gimbiya ciki gareta? Kwarai ma kuwa, aiko Sarki
yasan tana dashi. Wani mugun murmushi Jakadiya tayi,
tace ki koma za'a isar mashi da sako.
Dasauri Jakadiya tanufi gurin Sarkin Fada, sundade suna magana daga baya tafito tana dariya tanufi bangaren
Sarki. Bakaramin dadin Sarki yaji ba, nan take yayima
Jakadiya kyauta metsoka, Qaseem ma seda yabata
kyauta, dan yana gurin aka fadi haihuwar.
Kafin wani lokaci gidan Sarki ya sheda haihuwar Gimbiya Suhailat, Qaseem boye farin cikinshi yarikayi, dan
bayason Yayanshi yashiga damuwa. Bakaramin tashin
hankali Gimbiya Zakiyya tashiga ba lokacin da labari yazo mata. Har kuka seda tayi, gashi takori Jakadiya, haka tasa aka kira Gimbiya Nafeesa ita tarika bata hkr, dan ita ko akanta.
Duk wata hidima Safeeya ce take mata, yaronta me kyau
sosai, tun yana jariri dayayi kuka se dimple dinshi ya fito.
Bayan kwana 7 akayi suna, Sarki da kanshi yasama yaron
suna, dan Qaseem yaso yasaka sunan Yayanshi amma
Sarki yace yabari zesa mashi suna, shikuwa yayi haka ne, dan yabama matar kaninshi hakkinta ko akwai sunan
datakeson tasama yaron. Lokacin dayasa Safeeya ta
tambayeta sunan datakeso asama yaron tace tanason
asamashi Areef, dan sunan kaninta ne, daya rasu. Sarki
yaji dadin tambayr dayasa akayi mata, koba komai yasan
ba,a shiga hakkinta ba.
Qaseem yayi mamakin sunan da Sarki yasama yaron,
koda yabincika yagane shine yasa atambayi matarshi,
bakaramin jin tausayin Yayanshi yayi ba, kuma yakara
jinjina adalci irin nashi.
Bakaramin taro akayi ba, hatta da yan uwanta seda
sukazo suna, su gimbiya Zakiyya sunga yanda ake mulki
da kuma dukiya, haka suka saki jiki kamar bakomai akayi suna lafiya, se alokacin suka san da zaman Safeeya, dan sunga komenene Gimbiya zata sa sede takirata, gashi
kuma ita batada uniform bare suce baiwace, alokacin
sunan ne Gimbiya Zakiyya tashirya da Jakadiya, dan
tasan koba komai tana mata amfani sosai.
Haka rayuwa tacigaba da tafiya, duk yanda suka so susamu wata hanya dazasu kunta tama Gimbiya suhailat
babu dama. Jakadiya da sarkin Fada kuwa kansu ahade
yake, dan sarkin fada seda yasan yanda yayi yarika shiga bangaren Qaseem, yanuna yana matukar son Areef
hakan yasa yashiga jikin Qaseem sosai, duk lokacin da
aka kawo Areef Fada, Sarkin Fada shine yake karbarshi
yayita renonshi harseyayi kuka sannan amaidashi.
Bayan shekara 1 Areef yakara wayau sosai, kullum afada
yake wuni tare dasu Sarki, kowa yasan irin son da Sarkin fada yakema Areef, hakan yasa itama Gimbiya suhailat
take mashi kyauta akai akai.
Lokacin da Areef ya cika shekara 1 da rabi aka yayeshi, dan baya zama agurin Gimbiya yafi zma afada shiyasa
kawai ta yayeshi. Duk wani makircin Jkadiya da Sarkin
Fada babu wanda yasani, wata rana suna cikin lambu
suna makircinsu, Sarkin fada Yace wlh Jakadiya idan har muka bari wannan yaron yagirma kashinmu yabushe,
Jakadiya tace meze hana mukawar dashi kowa yahuta.
Murmushi sarkin fada yayi yace shawararki tana kan
hanya. Shiru yayi jin motsi akusa dasu, saurin juyawa
yayi yanufi inda motsin yake, caraf yariko hannun wata
baiwa wadda tazo wucewa taji suna magana ta labe tana
jinsu.
Kuka tafarayi tana fadin wlh, banji komai ba, kuyi hkr, dankwalinta yacire yashaketa dashi harseda ta mutu
sannan, Jakadiya tace kaga shegiya, muzaki tonama asiri.
Yo da asirinmu yatonu ai gara kowa yamutu. Sarkin fada
yazamuyi da gawar, kasande idan aka duba ba,a ganta ba
dole ashiga nemanta. Murmushi yayi yace kada kidamu
mubarta anan ko anzo anganta babu wanda zece
kasheta akayi, daukarta yayi yajefata cikin swimming
pool din gurin suka tafi.
Da gudu Jakadiya tashiga bangaren sarki tana kuka,
Waziri yace lafiya ke kuma zakishigo mana haka? Tana
kuka tace wlh nazo wucewa naga kamar mutum acikin
ruwa shine nazo infada maku, ai dasauri suka mike suka
nufi gurin, fadawa waziri yasa suka cirota, koda suka
duba suka iske tamutu.
Sarki da Qaseem sun shiga damuwar abinda yafaru,
haka akayi mata wanka aka rufeta, koda akayi bincike
wata kawarta baiwa take fadin dama tana tsoron ruwa
lokacin da aka aiketa lambu daga lokacin bata kara
ganinta ba, sese akace ta mutu. Sarki yace kila zamewa
tayi tafada kuma babu wanda yaganta. Da haka akarufe
maganar, hankalinsu Jakadiya ya kwanta.
Wasu mutanene guda 2, tare da wani Dattijo daka ganshi
zakaga beyi kama da hausawa ba, yafi kama da larabawa,
gefenshi. Kuma wata kyakkyawar matace, fara tasss da
ita, itama babbar macece, gefenta wata santaleliyar
budurwace kyawunta yawuce afadeshi, daka gansu kaga
larabawan asali, yarinyar bazata wuce shekara 19 ba,
tare suke da kayansu suna tsaye ajikin wani dankaramin gida me kyau.
Mutane 2 dasuke tare dasu daya daga ciki yace to Baba
yakaga gidan yayi maka? Cikin hausarshi wadda bata
goge ba, yace e gida yayi tunda akwai dakuna 3 aciki
kuma kowane da bandaki nashi aciki ai yayi dede. Dayan
yace yauwa Baba kamar yanda muka fada maka zaka
rika bamu dubu 50 ashekara sune kudin hayar gidan.
Baban yace shikenan babu damuwa, amma akwai wutan
nefa ko? E Baba akwai komai har ruwa bamuda
matsalarshi.
Baban yace toyanzu kaine zakazo kadaukemu anjima
muje cikin kasuwa muyi siyayyar kayan amfani ko? E
Baba kome kakeso zanyi maka, kuma zan kaika inda zaka
samu kaya masu kyau. Yace toshikenan yaro nagode bari
mushiga daga ciki mu huta.
Wadan nan mutanen bawasu bane kamar yanda kukaji
ankira dattijon da Baba. Asalin sunanshi ABRAHAM ne,
kuma shi mutumin saudiya ne, yatabayin zaman Nigeria
har so 2, yayi aiki da hausawa agarin Bauchi, bayan
yakoma saudiya ne, ya yanke shawarar dauko iyalinshi
yadawo dasu Nigeria, kasancewar yaji dadin zamanshi
ABauchi gurin wani mutumin kirki, bayan yatafi seda
yayi wata 2 bedawo ba, se wannan dawowar dayayi tare
da iyalinshi, sede yayi rashin sa,a yana zuwa Bauchi
yasamu labarin rasuwar mutumin.
Yayi kuka sosai, dayake akwai Babban yaron Alhajin
atare sukayi aiki, kuma shi dan Gombe ne, hakan yasa
yanemi address dinshi yazo nan yasameshi, kuma shine
yayi mashi hanyar samun gidan dazasu zauna, dan yace
tund yariga da yabaro garinsu baze koma ba, shiyasa
yace zezauna agurinshi sucigaba da kasuwancin tare.
Matarshi daya da yarsu daya, mesuna Rayhana, suna
matukar sonta sosai, tana da ilimin boko dana addini,
gata da natsuwa baruwanta da hayaniya, tanason
iyayenta sosai. Bayan sun huta, dayamma akazo
akadaukesu suduka suka tafi kasuwa.
Jerin motocin Sarki ne suka shigo cikin gari suna jiniya sundawo daga Yobe, tacikin gari suka shigo dansu gaisa
da jama'a mutane se daga masu hannu sukeyi, dan
mutanan Gombe suna son Sarki Hasheem sbd yana
masu adalci.
Rayhana ce da Umminta suka fito daga wani store na
kayan kitchen, Mahifinta kuma yana daga dayan
bangaren tare da wanda sukazo suna siyan wasu kaya,
Rayhana takamo hannunn Umminta dansu tsallaka titi,
yaran dasuka dauko masu kayan suna binsu abaya.
Wata irin kara da Baba yaji ne, tasashi saurin juyowa
dashi da mutanen dake gurin. Innalillahi Wainna
ilaihirrajiun, shine abinda mutane suke fadi da gudu
Baba yarugo dan ganin abinda yake faruwa. Dasauri
sauran motocin suka samu guri sukayi parking suka fito
domin ganin abinda yake faruwa.
To jama'a muje zuwa anext page danmuji meyafaru.
Tnx alot for ur concern to me, my luvly friends.
Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 40⚜45
Rayhanace rike da Umminta akasa ta rungumeta tana
wani irin kuka yayinda jini duk yabata mata jiki. Babanta ne, yakaraso gurin ganin abinda yake faruwa shima
yaduka ya rungumo matarshi yana kuka, babu alamun
rai ajikinta, dan tunda motar tabigeta nan take tacika.
Driver daya kadeta ne, ya iso gurin, abayanshi kuma su
Sarki ne da tawagarshi suka nufo gurin dan yana daya
daga cikin motocin gidan sarki. Isowarsu tayi dede da
Rayhana tamike tana kuka tanufi drivern motar
tashakeshi tana kaimashi duka tana kuka. Dasauri Waziri dasu sarki suka karaso gurin, Waziri ne yayi kokarin
cireta daga jikinshi yana bata hakuri, komawa tayi gurin Umminta tazube tana kuka gwanin bantausai.
Qaseem da Wazirine suka isa gurin, shikuwa Sarki tunda
yadora idonshi akan Rayhana yaji wani abu ya soki
zuciyarshi, da kyar yasamu ya dedeta kanshi ya karasa
gurin, amma duk da haka yakasa dauke idonshi akanta.
Waziri yaduka kusa da Baba yakamoshi yana fadin kayi
hakuri Baba muje akaita asibiti. Dago kai Baba yayi yana kallonshi yace wane asibiti kuma, bayan tarasu. Cak
numfashi Rayhana ya tsaya jin abinda Babanta yafada,
nan take tasume. Mamaki ne, yakama mutanen gurin
lokacin dasuka ga Sarki yadauki Rayhana yayi hanyar
mota da ita, ganin haka Waziri yace ma Baba yatashi
sutafi asibitin, Waziri da kanshi yadauketa suka nufi
mota, Qaseem dayake bin Yayanshi da kallon mamaki
shima yanufi mota suka nufi asibiti.
Suna zuwa aka karbesu, dan danan aka fara bama
Rayhana temakon gaggawa, Umminta kuwa koda suka
aunata anan suka gano ta jima da rasuwa, anan sukayi
masu bayani, Seda Su Waziri suka rike Baba lokacin
dayaji bayanin likita, abisa kujera suka zaunar dashi,
anan Waziri da Qaseem suka shiga bashi hakuri. Baba
yace ashede kasarki anan take, jiya mukazo garin nan ashe bazaki rayu damuba. Haka yayita sambatu, suna
bashi hakuri.
Sarki kam hankalinshi yana kan Rayhana, yakasa tsaye ya kasa zaune, Qaseem ya maida kallonshi gurin Yayanshi,
tausayinshi ne, yakama shi, dan tunda yake betaba ganin Yayanshi cikin wannan yanayin ba, tashi yayi yanufi
gurinshi. Kafadarshi yadafa, juyowa yayi, yana kallonshi, hannunshi yakama suka nufi wata kujera suka zauna.
Qaseem yace Yaya kanutsu Fadawa da mutanen gari
suna kallonka, kuma kowa yasan bamuda alaka dasu
kada suyi tunanin wani abu. Sarki yace Matar tarasu ko?
Kai Qaseem yadaga mashi, Sarki yace Allah kaceci
baiwarka kada itama ta tafi. Qaseem yayita bashi baki.
Mintuna 30 Rayhana tadauka kafin tafarfado, alokcin har antafi da Umminta gidan Sarki, dan Sarki dayaji cewar
bakine agarin shine yaroki Baba akan suje masarautarsu
ashiryata ayi mata sallah acan se arufeta. Baba yaji dadin yanda yasamu mutanen kirkin dazasuyi jana'izar
matarshi. Suna zuwa gidan Qaseem yawuce part dinshi
yacema Safeeya tafito akaita asibiti zata zauna da wata kafin sudawo, haka yasa driver ya kaita yarakata har
dakinta shi kuma yakoma.
Koda Rayhana tafarka wata mata tagani akusa da ita,
cikin Hausarta marar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 13