dadi wadda suka koya agurin
Babanta danshi zaman dayayi anan yasa ya iya hausa,
kallonta tayi tace Ina Ummi na? Matsawa Safeeya tayi
takamota tace kiyi hakuri tana daki, kai Rayhana tashiga girgizawa tana fadin ance ta mutu ai. Kuka tasaka marar sauti, sede daka jishi zakasan yana ci mata zuciya. Ahaka aka turo kofar dakin, tana daga kanta taga Babanta ne da wasu mutane, shima idonshi yayi ja sosai. Dasauri
yakaraso gurinta ya rungumeta shima yasa kuka, tsaya
su Sarki sukayi suna kallonsu cike da tausayi.
Ganin tasamu sauki likita yasallamesu. Bayan sunfito
Rayhana tana jikin Babanta hawayene kawai suke fita
daga idonta, Baba yakalli Sarki yace Yallabai inaganin
Zamu koma garinmu gobe, banga amfanin zamana anan
ba, dama nazo daniyar zama anan, amma tunda narasa
matata gara mukoma nida yarinyata. Mungode Allah
yasaka da alkhairi, kuma munyafe ma wanda ya banketa,
sede yaje yayi azuminshi.
Shiru Sarki yayi yanajin wani zafi aranshi, kasa magana ma yayi ya tsaya yana kallon Rayhana. Qaseem ne yayi
saurin fadin a,a Baba yanzu kaga dare yafarayi, muje
gida koma menene semu tattauna.
Part din Gimbiya Suhailat Qaseem yace Safeeya tawuce
da Rayhana, shikuma Baba suka nufi bangaren Waziri
dashi, Part din Sarki Qaseem yawuce dan tunda suka
shigo yawuce part dinshi. Kwance yasameshi abisa
gadonshi yana kallon sama. ( Niko nace Kadde ace su
Sarki anshiga layi ne ).
😉).
Zama Qaseem yayi yadafashi cikin sanyi murya yace Yaya tundazu naga kashiga cikin damuwa, wanda kuma
bahaka muka taho da kai ba, damuka dawo Yobe,
kafadamun damuwarka, idan baka fadamun ba, wazaka
fada mawa? Tashi Sarki yayi yakalli Qaseem yace
shikenan yanzu Qaseem tafiya zasuyi? Ai yakamata ace
tunda harsunzo daniyar zama garinmu kuma sukayi
rashi tadalilinmu yakamata ace mubasu muhalli akusa
damu suzauna, wlh Qaseem haka nan araina naji banaso
sutafi. Murmushi Qaseem yayi yace kada kadamu Yaya
munyi magana da Waziri bazamu bari sutafi ba. Sarki
besan lokacin da wani Murmushi ya kwace mashi ba.
Tashi Qaseem yayi shima yana murmushi yace Yaya bari
inwuce seda safe. Harya kai bakin kofa yajuyo yace Yaya Allah tabbatar da alkhairi. Dasauri yafita yana dariya.
Murmushi Sarki yayi ya girgiza kai yanajin wani sanyi
yana ratsashi.
Rayhana kuwa tana falon Gimbiya Suhailat sunata
lallashinta. Cike da tausayi Gimbiya tace kiyi hakuri kinji, daga yau munzama yan uwanki, bazakiyi maraicin Uwa
ba, kinga nima ba'a nan kasar nake ba. Daga yau kinga
nasamu yar uwa, haka sukayita lallashinta hartasamu
taci abinci tayi wanka suka nufi dakin Safeeya suka
kwanta.
Washe gari Baba yasa aka kira mashi Rayhana tana zuwa
suka fara kuka, Waziri yace suje fada Sarki yanason
ganinsu. Bayan Sungama gaisawa Sarki yakara yimasu
ta'aziya. Anan waziri yafada ma Sarki sunyi magana da
Baba yace ya hkra zasu zauna, sede yafiso yakoma gidan
daya kama yazauna aciki.
Qaseem yace Baba dan Allah kayi hkr kazauna tare damu
kaga Rayhana zatafi jin dadin zama anan saboda akwai
mutane, amma acan daga kai se ita, kuma daka fita zata
zauna ita kadai, kaga kadaici zeyi mata yawa. Baba yace shikenan naji zanbarta anan amma nikam nafiso
nazauna acan. Waziri yace shikenan Baba munyarda,
amma zakayi hkr kadawo kusa damu, kaga can yayi nisa
kuma zakayi nisa da 'yarka, akwai wani gida nesa kadan
da masarautar nan za'a gyara makashi se asaka maka
wadan da zasu rika yimaka hidima seka zauna, kaga koba
komai kana kusa damu. Baba yace to nagode sosai, Allah
yakara budi.
Kallon Rayhana yayi wadda tayi lamo ajikinshi, cikin
larabci yayi mata bayanin komai, shiru tayi tana kuka,
kai tashiga girgizawa tace ita bata yarda ba, da kyar
yasamu yashawo kanta. Haka yayi masu bayani ta
amince, bakaramin dadi Sarki yaji ba, tagefen ido
Qaseem yakalleshi shima yayi murmushi ganin farin ciki
kwance afuskar Yayanshi.
Haka aka gyarama Baba gidan aka zuba komai, yakoma
ciki, Qaseem da kanshi yazabi bayi maza da mata dazasu
rika yimashi aiki. Rayhana kuwa ankawo mata kayanta,
kuma Gimbiya Suhailat da Qaseem sunce agurinsu zata zauna.
Gimbiya Zakiyya da Gimbiya me daki bakaramun jin
haushin abinda akayi sukai ba, baram ma Gimbiyar
Babbar Gida, gani take kamar anmaidata saniyar
ware,Jakadiya wadda itace take kawo masu duk wani
labari daga fada. Kallon Jakadiya Gimbiya tayi tace
agskiya jikina bebani zaman wannan balarabiyar agidan
nan akwai alkhairi ba. Kawai ni tunkafin inganta wlh naji na tsaneta, tsana ma ta sosai, dan haka dole musan wane irin kulli zamuyi mata tabar gidan nan.
Jakadiya tace Gimbiya da ace Gimbiya suhailat tana
daukar zuga kuma tana bani fuskar shiga gurinta danaje
mata dawani kaidi wanda na tabbata setayi sanadiyar
fitar wannan yarinyar agidan dan sena nuna mata
mijinta akwai dalilin dayasa yakawota gidanshi tazauna.
Gimbiya medaki tace kai amma Jakadiya kinkawo
shawara me kyau, kuma dole sekin san yanda zakiyi
kisamu kishiga jikinta. Gimbiya Zakiyya tace ni nasan me za'ayi, ina Sarkin Fada, ai mutuminta ne, dan haka
tagurinshi zamu samu damar aikata abinda mukeso.
Jakadiya tace angama ranki yadade. Murmushin farin
ciki tayi takoma ta kwanta tana fadin seyanzu nafara
jindadin aiki dake, dan kinfara kawo shawara irin tamasu tunani, wato yan gidan sarauta. Kallon Gimbiya medaki
Jakadiya tayi, suka hada ido, su duka sunji zafin maganar data fada masu, amma haka nan suka hadiye bacin
ransu.
Kwance Gimbiya Suhailat take ajikin Qaseem yana wasa
da gashinta, Gimbiya tace Hubbi kasan mene? Yace sekin
fada, wlh naji dadin zuwan Rayhana gidan nan, naji dadi sosai daka kawomun ita part dina, inajinta ajikina sosai.
Qaseem yace nasan zakisota, shiyasa nakawo maki ita,
kinsan nasan duk wani abu daya dace dake. Kinma san
menene? Tace a,a inaso kikara kula da ita sosai, dan inaji ajikina Yaya kikema kiwo. Dariya suka saka tace kai
Hubbi da gske? Yace sosai ma, kodazu munyi maganar
da waziri, shima ashe yagane abinda Yaya yake ciki. Kai amma naji dadi, aikuwa zankoya ma Rayhana yanda zata
kwace Yaya daga gurin wadan can matan nashi.
Jinjina ta musamman gareku masoyana. Nagode sosai,
sekunjini a next page😘
.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 45 ⚜50
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 45 ⚜50
Sarkin Fada ne zaune afalon Gimbiya Suhailat, Areef
yana bisa cinyarshi yanata wasa yanacin biscuit,
Murmushi Gimbiya tayi tace Sarkin Fada kaida mutumin
naka ne? Washe baki yayi yace barka da fitowa ranki
yadade uwargidan Yallabai.
Zama tayi, bayan sungaisa Areef ya mika hannu alamun
tadaukeshi, murmushi tayi tace a,a nibazan dauke ka ba, ai nadauka kamanta dani, kara wangale baki yayi kamar
yaji abinda tafada. Hannu tamika mashi segashi yataho.
Lafiya de Sarkin fada naganka awannan lokacin? Kanshi
yadan sosa ahankali yace lafiya lau, dama wani dan
labarine naji awaje shine nace bari inzo inji daga uwar dakina ko haka zancen yake, dan abun yashafeki, nikuma
aduniya babu abinda zanji dangane dake ace nabarshi.
Inajinka, E to, to dama de akan wannan bakuwar
balarabiyar ne datake zaune agurinki, shine naji mutane suna cewa wai yallabai Qaseem ne yakawota, koshima
zebi sahun Memartaba ne yabi Sunnah. Kuma da alama
itace ze aura ko? Wani murmushi Gimbiya tayi takara
kallon Sarkin Fada, gaba daya babu natsuwa atare dashi, kozama yakasayi.
Kara murmushi tayi tace tonagode, amma nibani da
labari, sede kazauna inaji yakusa shigowa semuji daga
gareshi, zaro ido yayi yace haba Gimbiya rufamun asiri, ina ni ina zama inyi irin maganar nan da Yallabai, nifa dama ban tabbatar ba, kawai kinsan bazanso arika
maganarki ina guri ba, shiyasa nace gara inzo inji da
kunnena. Murmushi tayi tace gaskiya kam ka kyauta, to
bahaka maganar take ba. To harnaji dadi, aini bazanso
ayima uwar dakina abokiyar zama ba. Tonizan koma,
ahuta lafiya. Mikama Areef hannu yayi nan yataho suka
fita.
Murmushi tayi ta girgiza kai, kallon wata baiwa tayi tace takira mata Safeeya. Bayan tazauna ta fada mata abinda
Sarkin Fada yace mata. Shiru Safeeya tayi nadan lokaci, sannan tace nifa Gimbiya dama nafada maki banyarda
dashi ba, ina yawan ganinsu tare da Jakadiya, amma
kikace kinyarda dashi. Gimbiya tace bakomai Safeeya ki
kyaleshi ni haryanzu ina mashi kallon mutumin kirki, kila da gaske yaji maganar, kinsan gidan nan akwaisu da
gulma, bare sunga ankawo yarinya mekyau dole surika
tsegumi. Safeeya tace amma duk da haka kirika kula
sosai Gimbiya, ba'a saurin yarda da mutum, nasan kuma
wannan halin kine, amma naga kinyarda dashi. Tace shikenan Allah yashige mana gaba, tace amin.
Haka suka cigaba da rayuwa, su Gimbiya Zakiyya duk
yanda sukaso su hada tuggu akori Rayhana sunkasa.
Sarki kuwa Son Rayhana yayi girma azuciyarshi, gashi
baya ganinta dan bata fitowa sede idan zataje gaida
Babanta ita da Safeeya, ganin abun zedameshi ya yanke
shawarar fadamasu Qaseem.
Waziri ne da Qaseem Zaune afalon Sarki, su dukansu
cike suke da murnar abinda Sarki yafada masu, dama
kuma abinda suke jira suji yafada kenan, dan Waziri
yace ma Qaseem yabari shida kanshi yayi masu
maganar.
Waziri cike da murna yace agskiya naji dadin wannan
labari, nima tunda naga yarinyar kawai naji ta kwanta
mun arai, duk da bata fito daga gidan sarauta ba, amma
inaganin aurenku akwai alkhairi aciki. Amma mekace
Qaseem? Murmushi yayi yace aini nakasa magana sbd
farin ciki.
Duk da inada ra'ayin kin auren wadda bata fito daga
gidan sarauta ba, amma nikam nayima Yaya sha'awar
auren Rayhana, sbd mune muke tare da ita nasan halinta
mekyau gashi babu ruwanta, tana da addini, Allah ya
tabbatar da alkhairi.
Sosai Sarki yaji dadin maganarsu, kallon Waziri yayi
seyayi shiru. Waziri yace to ai ba tsayawa zamuyi ba,
zanyi magana da Malam domin yayi mana addu'a akan
al'amarin, kome yafada semuyi magana da Baba.
Qaseem yace wannan yayi dede, Allah yate maka. Waziri
yace amma inaso abar maganar anan, harse komai ya
tabbata, kasan halin mutane. Sarki yace wannan yayi
dede.
Bayan kwana 2, malam yakira Waziri suka yi magana
akan istaharan dayayi. Waziri yaji dadin abinda malam
yace, sundade suna kara tattaunawa akan masarautar,
sannan sukayi sallama. Qaseem yakira yafada mashi
komai, sannan suka fadama Sarki. Sosai yaji dadi, waziri yace zasuje suga Baba.
Gimbiya Suhailat da Safeeya sunji dadin maganar, sede
Rayhana batasan abinda akeyi ba. Da dare Gimbiya
Suhailat takirata, bayan tazo Gimbiya ta sheda mata
dalilin kiranta. Sunkuyar da kai tayi tana murmushi bata ce komai ba, Safeeya tace Rayhana kiyi magana mana
kin amince? Da gudu ta tashi tana dariya tashige daki.
Dariya Gimbiya tayi tace Allah mungode maka, gaskiya
naji dadi sosai. Allah yashige mana gaba. Safeeya tace
amin, amma ina tausaya mata gata karama babu
ruwanta zata shiga cikin matan Sarki.
Gimbiya tace kinsan yanda Yaya yake sonta kuwa?
Betaba auren Soyayya ba seyanzu zeyi, kinsan baze bari
wani ya wulakanta taba, kuma akusa dashi za'a ajeta,
bakiga ana kara gyara part dinshi ba? Nasan de kawai su
Gimbiya Zakiyya zasu sha kayan haushi sede suyi hakuri.
Nikam yanzu zan kara koyama Rayhana zama dasu,
kuma dole ayi mata gyara na musamman, nasan dawuri
za'ayi bikinta amma duk da haka daga gobe zata fara
amsar gyara.
Bayan su Waziri sunje gurin Baba sukayi mashi bayanin
daya kawosu, sosai Baba yaji dadin maganar, nan take ya amince, masu suka bada kudin neman aure dubu dari
biyar. Anan aka yanke rana sati 2. Godiya sukayi mashi
kuma suka fada mashi basu bukatar komai.
Zaune Jakadiya take afalon Sarki, Bayan sungama
gaisawa yakalleta cike da girmamawa, danshi yana
matukar girmamata, dan sunyi sabo sosai, komatanshi
bayajinsu kamar yanda yake jinta, sun share shekaru
tare tun farkon zuwanta gidan, take mashi hidima,
shiyasa yabata amana sosai. Kallonta yayi yace dama
nakiraki ne dan inbaki sako kifada ma su Gimbiya
Zakiyya da Nafeesa maganar aurena nan da sati 2.
Akwai Yarinyar da take zaune gurin Suhailat wadda
mukazo da mahaifiyarta nan akayi mata sutura wadda
driver na ya kade harta rasu. To itace nakeso na aura.
Washe baki tayi tace amma naji dadi sosai, kallonshi tayi tace Rankai dade da alama naga kana son Rayhana sosai,
bantaba ganinka cikin wannan farin cikin ba alokacin da zakayi aure ba, se wannan karon. Ko aurenka na farko
banga wannan farin cikin atare da kaiba. Murmushi yayi
ya sosa kai, dan yanajin Jakadiya kamar mahaifiyarshi
dan tagirmeshi, yace wlh Jakadiya ina mata son daban
taba yima wata mace ba. Dariya tayi tace Allah ya shige mana gaba, kuma anan danaga ana gyara za'a ajeta ko?
Yace haka ne.
Murmushi tayi tace gskiya nafi kowa farin ciki da
wannan al'amari, sbd yanzu Uban gidana zesamu abinda
ranshi yakeso. Dan haka zan daukota domin akoya mata
zama agidan sarauta. Kallonta yayi yace ai inaganin
kamar Suhailat tana koya mata, babu damuwa nasan
zata kula da ita sosai. Jakadiya tayi murmushin yake tace toshikenan bari inje infada masu Gimbiyar. Check
yadauko guda 2 yace takaimasu kowa dai dai. Wasu kudi
yadauko yamika mata yace ga wannan kema kirike
ahannunki. Godiya tayi mashi tafita.
Gurin Sarkin fada tawuce, abinda yafaru tafada mashi,
sosai suka shiga tashin hankali. Sarkin Fada yace kina
ganin Sarki baze iya samun haihuwa da wannan yarinyar
ba kuwa? Kinsan fa ance larabawa albarka garesu.
Jakadiya tace kada kadamu nasan abinda zanyi, damma
Sarki yace ba,a gurina zata zauna ba da tunkafin tashiga gidanshi zanyi kokarin hanata haihuwa, amma kasan ni
amintattar Sarkice dan haka kome nakai zesata taci, dan haka kada kadamu inde ina raye bazan bar Sarki yaga
kwanshi aduniya ba. Shekarata nawa ina mashi hidima
amma haryanzu nakasa zama wata acikin gidan nan,
haka zankare a Jakadiya?.
Sede inzama fitila ina haska wasu ni ina kona kaina, ai rashin gata ba hauka bane, dan haka gara kowa yayita
zama ahaka, shima wannan yaron dande ka hanani
dayanzu na aiwatar mashi. Sarkin fada yace kiyi hakuri
wannan yaron yashiga rai na, Allah yasani badan so
nafara daukarshi ba, amma daga baya yashiga raina
sosai, dan haka kibarshi, ninasan ko Sarki yamutu sede
Qaseem yahau kujerarshi bade Areef ba, dan haka
mutsaya akan sarki da matanshi. Yanzu kije ki kaima
Gimbyar Baban Gida mugun labari, dannasan ita kadai
zata shiga damuwa, banda Medaki, itakam ai tamu ce.
Dariya Jakadiya tayi tace wlh bakada dama. Yace Allah
kuwa kinsan daza,a bani Gimbiya medaki ai dana more,
tun lokacin datazo gidan nan miyau na yabiya kawai
senaji wai Sarki ze aureta. Jakadiya tace ai naga alamar itama yar hannu ce, amma matso kaji. Wata dariya suka
kwashe da ita Sarkin fada yace kina ganin haka za,ayi?
Tace sosai ma, amma bayanzu ba senan gaba idan komai
ya zama dede.
Wani uban gumi ne yake fitowa daga jikin Gimbiya
Zakiyya, kara kallon Jakadiya tayi tace yanzu jakadiya har saurin zuwa ki kawomun wannan bakin labarin kikeyi?
Jakadiya tayi kasa da kai tace Allah yahuci zuciyarki,
shima Sarki ba sonta yake ba, kawai tallarta Babanta yayi mashi, kuma kinsan Sarki dasaukin kai shiyasa ya amsa,
amma dakanshi yafadamun ke kadaice macen dayakeso
aranshi, duka sauran ya auresu ne abisa lalura. Dan haka ki kwantar da hankalinki.
Komawa tayi tazauna, saurin zuba mata ruwa jakadiya
tayi tamika mata. Bayan tasha tace yanzu ya za'ayi
kenan? Jakadiya tace Ranki yadade kamar yanda kika
saba, hakan zakiyi, kinsan Sarki yana yabonki akan
halayyarki tarashin tada hankali aduk lokacin dazeyi
aure. Yace shiyasa yake kara sonki. Murmushi Gimbiya
tayi tace shikenan, amma wannan karon bazan kyale
wannan yarinyar ba. Jakadiya tace ai bazamu barita
dadeba.
Ita kuwa Gimbiya medaki duk da taji haushi kadan
amma ana bata magudan kudi tamanta da fushin.
Jakadiya tace dama nasan bazaki damu ba, se waccan
sarkin kishin, ita tana ganin kamar ita kadai sarki yakeso dan tafito daga gidan sarauta. Medaki tace aisetayi tayi nikam inde da kudi ya auri 10 ina ruwa na, nasan kawai
zanrasa kulawar danake samu duk bayan kwana 2 ,
nasan hakanne kawai zedameni dan Sarki akwai iya shiga
rai. Dariya Jakadiya tayi tace ai Gimbiya nasan
matsalarki, kuma wannan badamuwa bace kede kawai
kirikeni zaki samu yanda kikeso. Sarkin fada ma yanzu
yaganni zanshigo nan yace ingaisheki, kinsan ke kadai
yake gaidawa aduk matan gidan nan gaskiya yanaji dake.
Medaki tayi dariya tace ai yana da kirki damma kada ace
wani abu ai daya rika rakoki munashan labarai.
Murmushi Jakadiya tayi tace ah, tunda kinaso ai angama.
Sati 2 Gimbiya Suhailat tadauka tana gyara Rayhana,
takara kyau, sosai kyanta haryaso yayi yawa, tasha gyara sosai. Duk wata kissa Gimbiya ta koya mata, dayanda
zata zauna da matanshi, babu abinda bata koya mata ba.
Duk wanda yakwana yatashi agarin Gombe babu wanda
besan Sarki zeyi aure ba, gaggarumin biki aka shirya
gidan kanshi yasha gyara, hankalin Gimbiya Zakiyya
bakaramin tashi yayi ba, dan tagano irin son da Sarki
yakema Rayhana, tun daga dukiyar dayake kashewa da
kuma irin hidimar da taga Qaseem yanayi, wanda tasan
shikanshi yana murna da bikin.
Taso ta tadama Sarki hankali akan auren, amma
mamanta tanaji tahanata, tace bakida hankali Zakiyya?
Kina ganin akan abinda yakeso baze iya wulakantaki ba?
Tunwuri idanma wasu ne suke zugaki togara kidawo
hanya, kina ganin nice karama acikin matan Abbanki
amma yanzu nice nazama babba, dan haka banyarda
kikara tada hankalinki akan auren nan ba. Kuma banyafe
maki ba, idan har kika yarda wata tajaki kukaje gurin
wani malami ko boka. Hakuri Gimbiya Zakiyya tayi ta
bata kuma tayi mata alkawarin bazata je gurin kowa ba,
kuma bazata kara tada hankalinta akan auren ba. Da
haka ta kwantar da hankalinta, sede tayi alkawarin idan har tuggu da kissa suna sa mutum yaci riba zatayi
amfani dasu takori Rayhana daga gidan Sarki.
Ayau ne miliyoyin jama'a daga jahohi daban daban da
manyan sarakuna na garu ruwa suka halarci bikin Sarki
Hasheem da Rayhana, wanda aka daura akan sadaki
million 1, kowa yasheda wannan auren Soyayya ne Sarki
yayi, ankashe dukiya sosai, anci ansha maroka da
mawaka sun sami kyauta sosai. Adaren ranar Sarki da
sauran Sarakuna da manyan masu kudi sukayi kayatattar
walima ababban dakin taron masarautar Bubayero.
Bayan sungama kowa yanufi masaukinshi, kuma ranar
aka kai amarya Rayhana dakinta dayasha dukiya kamar
ba,a nigeria ba. Yayin da wasu suka cika da farin ciki
alokacin Gimbiya Zakiyya tarasa inda zata sa kanta sbd
tsabar bakin ciki. Jakadiya kuwa jan Sarkin Fada tayi suka nufi part din Medaki acan suka zauna suna bikinsu.
Nima nace yakamata abar amarya da Ango su sha
amarcinsu.
Nagode sekunji ni a next page
.
.😘.
Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 50⚜55
Washe gari. Basu suka tashi ba, se 8:00, dasauri Sarki
yatashi ganin ko sallah basuyi ba, gaba daya kunyar fita yakeyi dan yasan kowa nagidan yasan baya fashin sallah
amasallaci, babban abin kunya ma abokananshi sunce
zasu biyo sugaisa da Amarya kafin su wuce, gashi nan
yamakara.
Kallon Rayhana yayi wadda take kwance fuskarta tayi
haske ga sahun kwallan datayi jiya nan kwance
afuskarta. Murmushi yayi yashafi gashinta wanda ya
hargitse, ahankali yace kece farin cikina GIMBIYA
FULANI. Kiss yayi ma goshinta yatashi yaje yayi wanka
yana fitowa yatada sallah, bayan yagama ya dauko Waya
yakira Qaseem, yana dauka yace ai Yaya dayanzu
zankiraka ince bakifa suna Falo harsun kusa gama
karyawa. Sosa kanshi yayi yakara kallon Fulani yayi
murmushi yace Uhm ka aika Safeeya taje takiramun
Jakadiya tazo gurin Fulani nizan fita gurin baki.
Shiru yayi sannan yace amma Yaya meze hana
kamaidata dakinta se inturo Safeeya tazo ta kula da ita, kasan bazata yarda Jakadiya ta kula da ita ba, tunda basu saba ba. Murmushi Sarki yayi yace shikenan to bari in
maidata dama dan naga Jakadiya ita kadai keshiga
dakina shiyasa nace haka amma yanzu zan maidata
dakinta. Kashe wayar yayi kunya duk takamashi yanzu
yazecema mutane.
Bayan yamaida Fulani dakinta wanda kofa ce kawai
tarabasu da falon Sarki, duk abinda yakeyi tana jinshi
kunya ce tahanata bude ido. Zama yayi yana kallonta,
can kuma yatashi yafita yanufi gurin baki, akofa yahadu da Safeeya, cike da girmamawa ta durkusa tagaisheshi,
amsawa yayi yana me mata fara'a. Yace yauwa Safeeya
idan tashirya kaya suna nan su zata saka zasu gaisa da
baki. Da to ta amsa mashi yayi waje, yana fita fadawa
suka mara mashi baya suna kwasar gaisuwa.
Duk wanda yaganshi aranar yasan yana cikin farin ciki,
dan duk yanda yaso yaboye fara'arshi kasawa yayi. Yana
shiga falon baki suka fara yimashi tsiya, sosai yake dariya dayake yashigo cikin abokanshi. Wani Sarki yace gskya
Hasheem bantaba ganin wannan farin cikin atare da kai
ba, kada muna skul baka wannan fara'ar. Lallai baseka
fada ba, kowa yasan yanzu ne kayi auren soyayya. Wani
yace aidole yayi farin ciki wlh auren so daban yake,
shiyasa banyi aure ba seda nasamu wadda nakeso. Haka
sukayita barkwanci suna dariya, wani yace kaga kada
muyi rana gara afiddo mana Amaryar data hanaka sallah amasallaci muganta muga wane irin zabe ne kayi haka.
Dariya yayi yace a gaskiya sede muje Falona babu wanda
ze fitomun da mata tana amarcinta tafito waje. Dariya
suka saka yafita.
Abakin kofarshi yahadu da Jakadiya, saurin dukawa tayi
tana mashi kirari, murmushi yayi yace Jakadiya kina
lafiya? Tace lfy lau Rankai dade, dama tundazu naso inzo induba yakuka kwana sekuma naji ance badakai akayi
sallah ba, shine nace to kobaku tashi dawuri ba?.
Murmushi yayi yace hakane, ai har Safeeya tazo tana
gurin Fulani. Fulani? Jakadiya takara maimaita sunan
aranta. Murmushi tayi tace to ai shikenan, bara inje
ingyara dakin yace to. Dakin Fulani yawuce, tunkafin ya isa wani da daddai kamshi ya dakar mashi hanci wanda
yayi sanadiyar saukar kasala ajikinshi. Lumshe ido yayi aranshi yanakara jin son Fulani.
Kwankwasa kofar yayi, da sauri Safeeya taje tabude.
Dukawa tayi tana fadin ai har angama, murmushi yayi
yace nagode, Jakadiya zata kawo maki tukuicinki. Godiya takara yimashi tafita. Yana shiga yayi mutuwar tsaye,
ganin irin kyan da fulani tayi kamar ba mutum ba.
Tasbihi yafarayi aranshi yana kara yabon irin kyan
Fulani.
Zaune take tunda taji shigowarshi ta dukar da kanta,
hannunshi taji ya zagaye mata kafadu dasu, saurin rufe
ido tayi, mikar da ita yayi suna fuskantar juna,
murmushi yayi ya matso da fuskarshi dede ta ta
harsunajin numfashin juna, ahankali yace Fulanita babu
gaisuwa? Saurin kwantar da kanta tayi bisa kirjinshi tana murmushi, kara rungumeta yayi sosai kamar ze maidata
ciki, kamshin turaren da Gimbiya Suhailat tabama
Safeeya tasa mata duk yafara rikitashi.
Sassanyar muryarta ta doki kunnanshi dafadin Ina
kwana. Seda ya hadiyi miyau sannan ya amsa tare da
lalubo lips dinta yahade danashi. Sun dade ahaka har
yana neman wuce gona da iri yaji karar kofa. Dagata yayi yace kinga kinmantar dani mutane suna jiranmu,
gaskiya senayi da gaske kada kirika sani jin kunya afada.
Kamata yayi suka fito.
Akofar falon ya tsaya yakara gyara mata mayafinta, yace gskiya dande kada suce namasu rowa dabazaki fita kowa
yakallemun ke ba. Ahaka suka shiga falon tana jikinshi, kallo ne yadawo kansu, kowa seda ya yaba da zaben
Sarki, anan suka rika yimashi tsiya, itade sede murmushi, ko fuskarta kasa dagawa tayi, ahaka suka gama gaisawa,
kyaututtuka da dama suka bata, daga masu kudi se zinari wasu hada kyautar mota. Tasamu zinarai dayawa da
kudi, wasu kayan ma an nadesu bansan ko menene ba.
Sallama sukayi mata, Sarki yace bari inmaidata daki kada tayi tuntube. Gabada sukasa dariya.
Qaseem da Waziri tare da Sarki dasauran fadawa suka
taka masu hargurin motocinsu, kowa yaji dadin haduwar dasukayi haka suka tafi suna cike da farin ciki, dan sundade basuyi irin wannan haduwar ba. Bayan
sungaisa dasu Waziri yawuce part dinshi dominsu karya.
Da Jakadiya yahadu tagama gyara mashi daki ankawo
abinci tashirya masu, yace sannu da kokari Jakadiya,
tace sannu da dawowa, Yace yauwa kije falon baki akwai
kayayyakin Fulani kyautace da abokanai na sukayi mata,
akwasosu ki kawomun su dakina, hannu yasa a aljihu
yaciro kudi masu yawa zasu kai 100k, yabata yace yauwa
gashi kibama Safeeya tukuicinta ne ayi mani godiya da
irin gyaran datayi ma Fulani dazu. Amsawa tayi ta tashi tawuce.
Wani irin kululun bakin ciki ne, yarufe Jakadiya, ganin irin kudin da Sarki yabama Safeeya, aranta tace wato
mutanan nan so sukeyi sucireni daga jikin Sarki,
ayanzunne yakamata insamu dukiya daga gareshi ta
dalilin Amaryarshi nasan akanta ze iya yima mutum
kyautar mamaki, amma dan bukulu suka turo wata tazo
tayi aikin da nice nakeyinshi aduk sanda Sarki yayi aure.
Tabbas sena tashi tsaye akan Safeeya naga alama nan
gaba Sarki ita zemaida yar gaban goshi.
Ninasan mezanyi, anfada maki sona da yakeyi haka
nabarshi. Tsaki tayi tawuce falon domin kwaso kayan,
mamaki da tsoro ne, suka cikata lokacin datayi arba da
irin kayan da tagani afalo. Gaba daya tarikice ganin irin wannan dukiya. Aranta tace badan Sarki yaga kayan nan
ba, wlh dasenayi nawa. Wata babbar jaka tajawo tasaka
kayan duka aciki tadauka tanufi dakin sarki dasu. Bata
samesu afalo ba, da alama abincin ma adakinta suke ci.
Tsaki taja tace shikenan kuma za,a maida mana Sarki
bita zai zai, yo aduk matanshi akwai wadda yataba shiga dakinta ma? Lallai Gimbiya zankai maki labarin daze
tarwatsa zuciyarki, wanda zesa ki karya akidarki ta rashin zuwa gurin boka, ai wlh tunda nabace dole insamu
abokan tafiya. Murmushi tayi lokacin data tuna yanda
Sarkin fada yafara samun shiga gurin Medaki. Kwafa tayi tajuya tafita.
Wasu zafafan kwalla ne, suke fitowa daga idon Gimbiya
Zakiyya, duk irin jiji da kanta, yau gashi agaban Jakadiya tana kuka, damma Jakadiya takori sauran Bayin.
Lallashinta Jakadiya tacigaba dayi tana kara kwantar
mata da hankali.
Gimbiya hakuri zakiyi, amma dole sekintashi tsaye, wlh
bakiga irin makudan kudin da aka bama Fulani ba, dan
sunan danaji Sarki yakirata dashi kenan. Babbar
damuwata yanda taki barinshi yafito fada, abinci ma
adakinta sukaci. Infada maki...... Marin da taji ya sauka akuncinta ne, yasata saurin hadiye sauran gulmar data
kwaso. Cike da tsoro takara dukar da kai tana neman
gafara.
Ke wace irin dabba ce? Wlh bansan ke dakikiya bace se
yau, anfada maki gidan sarauta gidan bayine? Inbanda rashin sanin darajar sarauta taya zakizo kina fadamun
irin wadan nan sakarkarun maganganun irin na jahilai
irinku. Ina cikin damuwa zakizo kina fadamun abinda
bantambayeki ba. Bance kifadamun abinda sukayi ba,
kawai na tambayeki ina Me martaba shine zaki wage
sakaran bakinki wanda yasaba dashan bakar kuka da
daddawa kizo kina fadamun maganarsu.
Daga yau kika kuskura kika kara fadamun abinda banice
na tambayeki ba, wlh, kinji narantse maki sekinbar
masarautar nan. Kara dukawa Jakadiya tayi, tana bata
hakuri, tashi tayi ta tureta tashige daki, tana fadin karna kara ganin kafarki anan sena nemeki. Wasu hawayene
suka zuboma Jakadiya, diyar cikinta saboda kudi da
mulki yau itace take zaginta da cin mutunci har haka.
Tashi tayi tana fadin yo idan har nabarki kikaci ribar
zaman gidan sarauta ai ba macece ta haifeni ba.
Qaseem ya kalli Gimbiya Suhailat yace ni kaina yau ina
cikin farin ciki bansan abinda yasa ba, Yayana yana cikin farin ciki dole in kasance acikin farin ciki, inama ace Rayhana itace matar Yaya ta farko, nasan har abada baze kara marmarin kara aure
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 13