ace ana daura aure zaku tafi. Areef yace wlh Abba
koni dole ce zata sani yin nisa daku, kuma ina me
tabbatar maku shekara 3 zamuyi, niba burina beautytayi
zurfin karatu ba, kawai inaso tasamu karatu me kyau,
dan koda tayi karatun ni bazan barta taje wata University ba, kawai tasamu karatu kodan sbd rayuwarta data
yaranta.
Gimbiya tace gaskiya kayi magana me kyau, kuma nima
nagoy bayanka son dazamu nuna mata kenan mubarta tasamu ilimi me kyau, kuma tunda saudiya zakuje, nasan
zata samu ilimi me kyau, kaga daga kai har ita kunje kusa da gida, kafin kudawo zaku zagaya dangi.
Sarki yace shikenan, idan Yaya yadawo zamuyi maganar
dashi. Areef yarungume Abbanshi yayi yana dariya.
Gimbiya tace ammafa zaku rika zuwa bawai zama zakuyi
harseta gama ba. Sarki yace dama ai baza,ayi haka ba.
Haka suka cigaba da shirye shirye, Amare suna shan
gyara, dan masu gyara na musamman daga meduguri
aka dauko, Fulani daki guda aka ware mata ita da ne
gyaranta, tunda tashiga bata fito ba, akoda yaushe suna cikin gyara, sallah kadai da cin abinci suke tadasu.
Bakaramin kyau takarayi ba, tadawo tamakar wata
yarinya, komai nata yadawo kamar da. Beauty kuwa
masu gyaran har mamakin kyanta sukeyi, gashi dama
tunda aka fara gyaransu su Areef suka dena ganinsu, duk ya gama shuga damuwa.
Ayaune, masarautar BUBAYERO tacika da mutane, anata
gyara da shirin tarbar Sarki Hasheem. Kowa kagani cikin masarautar cikin farin ciki yake. Fulani tasha kwalliya kamar meshirin zuwa zaben sarauniyar kyau, tayi kyau
harta gaji, haka suka kaita dakinta dayasha gyara har yafi ranar da aka kaita kyau.
Motoci harma da mashina ne, suka je dauko Sarki. Ana
bude kofar jirgi mutane suka fara fitowa, sarki Qaseem
yazuba id kawai yaga ta yanda yayanshi zefito. Waziri
yafara hangowa, daga bayanshi ya hango Yayanshi cikin
shiga ta alfarma yayi matukar kyau, kamar bashi bane
yayi ciwo abaya ba.
Da kafafuwanshi 2 yarika saukowa daga jirgi, ai Sarki
Qaseem kasa hakura yayi ya karaso, cike da murna ya isa gurinshi uka rungume juna. Kowa na gurin seda suka
burgeshi. Haka suka nufi gida cike da farin ciki.
Suna zuwa Sarki Qasee yajashi zuwa part dinshi, yace
Yaya kashiga kashirya kada kafito seda dare, Fulani tana daki tana jiranka, nasan kagaji dayawa. Murmshi yayi
yace shikenan nagode, sena fito. Har falo yakaishi
sannan yafito fuskarshi dauke da annashuwa.
Tura kofar dakin Fulani yayi, lumshe ido yayi dan wani
da daddan kamshine ya bugar mashi hanci. Da sallama
yashiga, ai cak ya tsaya ganin Fulaninshi, da gudu tarugo ta rungumeshi, hannuwanshi 2 yasa ya rungumeta, wani
irin farin ciki sukeji dukansu.
Sun dade ahaka kafi tajashi zuwa cikin dakin, riketa yayi yana kallonta, yace anya ba masanye akamun da
Fulanita dana sani ba? Murmushi tayi tace kila, jawota
yayi, yace gaskiya nagodema Allah dayasa bantafi dake
ba, gashinan an maidomun da mata kamar yar shekara
18. Murmushi tayi tacire jikinta daga nashi tana fadin
sannu da hanya, muje kayi wanka kaci abinci.
Murmushi yayi yace nikam bazan iya cin abinci ba,
tunda naganki, dariya tayi tace a,a muje de. Haka tajashi zuwa bandaki. Bayan yafito ya shirya takawo mashi
abinci, da kanta tarika bashi yana jingine jikinta, kamar karamin yaro, yahanata sakat. Da haka tagama bashi
abinci, yaje yayi brush yadawo yana fadin taho kimun
tausa, bacci zanyi.
Murmushi tayi tanufo gurinshi, yace amma kicire
wannan kayan zasu damenim tace amma naga bacci
zakayi, ina ruwan kayana da kai, kanne mata ido yayi
yace e sonake musami AMINULLAH. Dariya tayi yajawota
shima yana dariya.
Koda Sarki Qaseem sukaje fada da dare, Sarki Hasheem
befito ba, ganin haka Waziri yace abari se gobe, azauna, akwai gajiya atare dashi, Sarki yace a,a amarci kawai
yakesha. Waziri yace kaima ai sekaje kasha naka.
Murmushi Sarki yayi yace kaima nan da wani lokaci kaza
fara shan naka. Dariya Waziri yayi yace seda safe, Sarki yace to Allah yakaimu.
Areef ze zaune afalon Jakadiya kamar zeyi kuka ya kalleta yace haba Aunty dan Allah sokukeyi inshiga wani hali,
kinfi kowa sanin damuwar danake ciki, shikenan ace
kullum so daya zanga beauty gaskiya bazan iya ba.
Ina gyaran nan danni akeyishi? To nide abarmun ita haka banaso. Dariya Jakadiya tayi tace yi hakuri bara inturo maka ita karkamun kuka, fita tayi sega beauty tafito.
Tsayawa yayi yana kallonta, tana zuwa tazauna kusa
dashi tana murmushi, yakamo hannunta yace haba
beauty nan shikenan sekirika guduna.
Kema bakison ganina ko? Girgiza mashi kai tayi, yace
yauwa kokefa beauty na, hannunta yasaki, yace jeki
dauko mani abinci yunwa nakeji, tashi tayi tadauko
mashi, akasa tadameshi, nan tazauna tazuba mashi.
Atare suka fara cin abinci, yana bata tana bashi, har suka gama sannan suka zauna yana mata fira.
Washe gari se bayan azahar sannan aka taru afada, atare Sarki Hasheem da Fulani suka fito, daka gansu kasan
suna cikin farin ciki. Bayan angama gaisawa, aka bude
taro da addu'a.
Sarki Qaseem yace Alhamdulillahi, munama Allah godiya
daya kawomu wannan rana Yaya yasamu lafiya, komai
na masarautar nan yazama dede, ina rokon Allah daya
kara tsaremu damu da yaranmu baki daya. Dan haka
inaganin zanmika ma Yaya kujerarshi, dama amatsayin
rikon kwarya na amsa.
Sarki Hasheem yayi murmushi yace, a,a ai kuma nida
mulki har abada, wanda nayi abaya ya isa, kaine zaka
cigaba da mulkarmu, kafin Yarima yakawo karfi se
abashi, amma wannan maganar ma kabarta.
Waziri yace wannan magana haka take, munriga da
munyanke zaka cigaba da zama Sarkin Gombe, har Allah
yakaimu lokacin dazaka sauka. Allah yatayaka riko.
Waziri yace magana ta 2 akan maganar bikinsu Yarima
ne, munsami labarin mahaifin Haisam zezo gobe da jama'arshi neman auren Ayman, dan haka nan da sati 2
za'ayi bikinsu in Allah yakaimu.
Kallon Baffan beauty yayi yace akwai wata magana da
Yarima yazo mana da ita, jiya Sarki Qaseem yake
fadamun. Anan yafada masu alfarmar da Yarima yake
nema. Shiru Baffan beauty yayi bece komai ba. Can
yadago kai yace ai hakanma yana da kyau, Se ayi magana
acan kasar asama mashi aikinyi kafin itama tagama
karatun nata. Allah yasa aje asa'a akuma samu abinda
akeso.
Sarki Qaseem yace kuma akwai dayar maganar, aure
danakeso inyi, dama akan Waziri ne da Jakadiya Safeeya, ina ganin insha Allah nan da sati 2 tare danasu Yarima
za,a daura. Dago kai Waziri yayi yasaki baki yana kallon Sarki Qaseem. Baffan beauty yayi murmushi yace lallai
kamar kashiga zuciyata.
Dan Allah Waziri kada kace komai, kawai kayi fatan
alkhairi, kasan baza zaba maka abinda zakayi dana sani
ba. Sunkuyar da kai Waziri yayi yana murmushi. Sarki
Qaseem yace ai ya amince, Allah yakaimu musha biki.
Shirye shirye ya kankama agidan su Yarima, iyayen
Haisam sunzo anyi magana, kuma har can misra an fada
masu, kuma sunce zasuzo. Baba Fulani ma yakira yan
uwanshi yafada masu, wasu daga cikinsu sunce zasuzo.
Duk wani shirin tafiyarsu Areef angamashi, anyi masu
visa, da takardar shedar zama akasar, kuma an sama ma
Areef aiki acan har gudan dazasu zauna ansamu. Dayake
abun namasu sarauta ne. Babu wani bidi'a dazasuyi
abikin, hakan yasa aka kira me wa'azi yazo yayi masu.
Ayau ne dubban jama,a suka halarci daurin auren
mutane, 3 nagidan sarautar BUBAYERO. Daurin aure ne
daya tara mutane dayawa, daga garuruwa daban daban,
harma daga kashashe. Bayan daurin aure akayi babbar
walima, anci ansha, kowa seda ya yaba da irin auren
wannan Masarauta. Gashide auren yaransu, abin sonsu
akeyi amma kuma babu wata bidi'a da akayi. Mutane
dayawa abin ya burgesu.
Adaren ne kafin azo daukar Ayman, Sarki yatarasu duka
domin ayi masu nasiha. Nasiha meratsa zuciya sarki yayi masu, bayan yagama Baffan beauty ma yayi masu. Yace
Amatullahi, kiyi hakuri kinga gobe da safe zaku tafi, babu ruwanki da kowa, bakisan kowa ba se mijinki.
Kada kiyarda wasu suzo maki dawani abu, yanda baki
magana, karkiyarda kibiyema kowa, kuma kimaida
hankali akan karatunki, inhar kinaso kidawo kusa damu,
amma idan bakiyi kokari ba, acan zakuyi tazama. Ko
kinaso kuzauna acan? Kai ta girgiza yace yauwa, Allah
yayi maku albarka. Kema Ayman, kindega abinda yafaru
azuwanki gidan nan, damma kinci sa,a gidanki daban ne,
amma duk da haka bana son kisaki jiki da mutane,
dangin mijinki kirikesu da hannu 2, kowa kizauna dashi
da zuciya daya, Allah zetemakeki akan makiyanki. Allah yabaku zaman lfy. Anan Waziri shima yayi masu tashi
nasihar, se yan uwan Ayman da dangin Fulani dasukazo,
kowa seda yayi masu nasiha.
Se kuka sukeyi, bayan angama masu Sarki Qaseem yace
kuje, yanzu za,azo adaukeki. Bayan suntafi, Sarki yace
Waziri kaima yanzu zamu kawo maka taka amaryar.
Dariya suka saka, gaba daya. Da misalin karfe 9 aka dauki Ayman, wanda Areef shima yadauki beautynshi amota
suka tafi rakasu.
Bayan kowa yatafi yarage daga amarya da ango se su
Areef. Haisam yace abokina yakamata muje inrakaku.
Duka Areef yakai mashi yace wlh kai dan iska ne, wlh se ince ba inda zani, Haisam yace da kyau, ai akwai wani
dakin, indarabon asamu dan gidanmu kuma shikenan.
Areef yace a,a ni baruwana kaine dan iska nikam nafison dan saudiya. Haisam ya kalleshi yace wlh abokina
banason tafiyar nan taku, shiyasama bazan je rakiya ba, amma zamu zo dan acan zamuyi honey moon dinmu,
Areef yace bakomai nasan sanda zamu tafi ma baku
tashi daga baccin gajiya ba.
Dariya Haisam yayi yace ammade ai munyi sallah ko,
Areef yace tobara mutafi nasan beauty na tagaji gara
muje ta huta, mike wa sukayi, Haisam ya rungume shi
idanunshi har yakawo ruwa. Shima Areef seda yazubar
da kwalla, sun dade ahaka, kafin suka saki juna.
Har bakin mota suka rakasu, Ayman da Beauty se kuka
sukeyi,da kyar Areef yacire beauty daga jikin Ayman.
Ayman tace Yaya yanzu shikenan gobe zaku tafi? Kallonta yayi zeyi magana kuka yataho mashi, kawai jan beauty
yayi suka shiga mota.
Amota yayi ta lallashin beauty, da kyar tayi shiru, haka suka nufi gida shima duk bayajin dadin rabuwarsu da
Haisam dan bakaramin sabo sukayi ba. Beda wani aboki
se shi, dashi kadai yasaba. Har dakinta na bangaren
Jakadiya Safeeya ya kaita sannan yatafi.
Kwallan data zubo mata ta goge, takalli Jakadiya Karima tace yanzu kalli yanda duniya tajuya mani baya, kamar
ni da mulki na da matsayina amma kalli yanda kowa
yamanta ni acikin gidan nan, biki akayi ayau amma
banida damar fita inje gurin. Jakadiya Karima tace,
Zakiyya kenan, idan zakiyi hakuri ki aje wata sarauta ki rungumi kaddara kiyi.
Har garama ke, zaki iya kirga kwanakin ki,nifa? Sede
afitar da gawata. Saboda haka kinganni nan namaida
gurin nan kamar gidana, idan harzaki rika yimani
maganar wata sarautarku, ina me tabbatar maki zanbar
maki dakin nan, kuma bazaki kara ganina ba, dan kinsan
babu wanda zezo yazauna tare dake. Shiru Zakiyya tayi
tana jinyanda Jakadiya take fada mata maganganu.
Murmushin takaici tayi tace duniya kenan.
Washe gari tunda safe aka fito rakiyarsu Areef, idanunshi
sunyi ja sosai, dan tunjiya yakema iyayenshi kuka, Abbanshi har cewa yayi kode afasa tafiyar ne, yace a,a
Abba, nasan damun tafi komai ze wuce.
Haka suka shiga mota aka nufi air pot dasu, ko acan da
kyar aka ciresu daga jikin iyayensu, suma seda sukayi
hawaye, suna kallo har jirginsu yadaga, sannan suka juya zuwa gida. Acikin jirgi kam lallashin beauty Areef yayi tayi, mutane se kallonsu sukeyi, dan sunga suna kama
sosai, gashi dama beauty da kyar tashiga jirgin, shiyasa tashige jikin Areef, ko ido takasa budewa. Shiyasa kukan nata yazama 2.
Suna sauka dama mota tana jiransu,daukarsu tayi suka
nufi gidansu, gida ne, mekyau, yaji komai, kayansu aka
shigo masu dasu. Wanka Areef yace suje suyi, rufe fuska beauty tayi tana murmushi. Cak yadauketa bema tsaya
jiran yardarta ba. Haka sukayi wanka suka fito, dakanshi yashiryata aka kawo masu abinci.
Da dare ma kawo masu abinci akayi, bayan sungama
yadauketa suka nufi toilet, wanka sukayi tare da alwala, sallah sukayi sannan yajawota suka nufi gado.
Washe gari da safe dakanshi yashiga kitchen yahada
masu break, bayan sungama yajata zuwa daki suka
koma bacci, seda azahar suka tashi, wanka sukayi sukaci abinci suka fito falo, takarda da biro yadauko yajawota suka zauna falo, yace beauty yau labari zamuyi fa.
Haka yayita rubuta mata yana bata tana rubuta mashi
abinda tasani, idan ta manta ya tuna mata.
Haka suka cigaba da rayuwarsu acikin gidan gwanin ban
sha,awa, akullum suna yin waya da yan gida, satinsu
guda sannan suka fara fita, aranar yakaita makaranta shi kuma yawuce gurin aiki, seda yayita lallashinta kafin ta hakura, yace dasun tashi zezo yadauketa.
Rayuwar Areef da Amatullah gwanin ban sha,awa, suna
matukar son junansu, akullum tare suke fita ya kaita
makaranta, shikuma ya wuce aiki, se da yamma suke
tashi, dayake makarantar hade take da islamiya, shiyasa sesun kai yamma, kuma Beauty tana gane karatun sosai,
babu ruwanta da kowa, karatunta tasa gaba.
Haka rayuwa tacigaba da tafiya, suna da wata 3 dayin
aure, ciki yafito ajikin beauty, bayan sunje asibiti akayi test aka gano ciki dan wata 2, bakaramin murna Areef
yayi ba, haka yakira gida ya fada masu, suma sunyi
murna sosai. Tunda suka koma gida yake riritata,
damma cikin beda laulayi,
Haka yakira Haisam yayi mashi albishir, shima alokacin
yake fada mashi Ayman ma tana dauke da ciki itama
wata 2, Areef yace amma naji dadi, zamu fara cika ma su Abba gida da jikoki. Haisam yace idan muna da rai
muma semu hada zumunci. Areef yace Allah ya kaimu.
Amma wai yaushe zaku zo, kasanfa muna son zuwa
ziyara gurin yan uwa, gurin dangin su beauty, danasu
Momy. Haisam insha Allah zamu shirya muzo. Yace to
Allah yakaimu
Baffan beauty ya kalli Fulani, datake kwance ajikinshi, dawowarsu daga asibiti kenan, fuskarshi dauke da
murmushi, yace babu abinda zance maki Fulanita, sede
godiya, tabbas ke haske ce acikin rayuwata.
Ashe inada rabon ganin yarana, aduniya. Ina rokon Allah ya saukeki lfy. Murmushi tayi tace amin. Yace ina ganin Gimbiya Suhailat zata rigaki haihuwa ko? Kai tadaga
mashi, tace wlh ni kunya nakeji, yace kunyar me kuma?.
Tace haba dan Allah, yanzu kana ganin Amatu ciki gareta, Ayman ma haka, ga Aunty, yanzu kuma ace nima haka,
kuma suk kusan tare zamu haihu. Dariya yayi yace kin
manta dayar ai, tace wa kuma? Yace matar Waziri mana.
Tashi tayi fuskarta dauke da mamaki, tace da gske Aunty Safeeya tana da ciki? Yace da gske mana, dazu yake
fadamun, nace kinga ikon Allah ko? Tace gaskiya kam,
wama yayi zaton Aunty zata haihu, yanda ta dade bata
taba haihuwa ba.
Yace aishi Allah babu ruwanshi, yana yin abunshi aduk
sanda yaso,babu ruwanshi da tsufanka ko yarintarka.
Fatanmu Allah yasa mugama da duniya lfy. Tace amin.
Amma de ba gida su Yarima zasu dawo ba idan zata
haihu ko? Dariya yayi yace wai naga duk kinbi kin damu, ina ruwanki dasu?.
Kinsande muna da inda zamu ajesu ko? Kuma zamu
sami masu kula dasu, dan haka ki kwantar da hankalinki.
Shiru tayi bata ce komai ba. Jawota yayi yace dazu
Yarima yake fadamun zasu je ziyarar yan uwa.
Murmushi tayi tace kagani ko,
Nibanje ba, ga jikarsu nan har zataje, yace karki damu
kema zakije, Allah yasaukeki lafiya. Tace Amin.
Zaman Haisam da Ayman, zama ne na so da kauna, yana
kula da ita sosai, itama haka, kuma tana daraja yan
uwanshi. Acikin satin ne, yagama shirya masu visa suka
daga zuwa saudiya domin zumunci.
Bakaramin dadi su Areef sukaji ba, da ziyarar dasuka
kaimasu, kuma agidansu suka sauka, ko abinci basa
tsaywa girkawa, sede sufita suci awaje, dagacan suwuce
gurin shakatawa. Dayake Beauty suna hutu.
Sun zagaya gurare dayawa, sannan suka shirya dukansu
suka nufi misra, yan uwansu bakaramin dadi sukaji ba.
Kwanansu 3 sannan suka wuce garinsu Fulani, suma sun
tarbesu sosai, sun sha gata, kwanan su 3 acan ma,
sannan suka dawo gida.
Kwana 2 su Haisam suka kara sukace zasu wuce, har
kuka sukayi dasuka rakasu, da kyar Areef yacire beauty
daga jikin Ayman, haka jirginsu yadaga suka dawo gida
yana lallashi.
Bayan wasu watanni Gimbiya Suhailat ta haifi diya mace, ansha hidima sosai, sede su Areef basu jeba, dan beauty tana Exams. Yarinya taci sunan mahaifiyarsu Sarki
Qaseem Fatima, ana kiranta da NOOR.
Bayan wata 2 da haihuwarta Fulani ma tahaihu yan biyu, mace da namiji,gaba daya gidan seda kowa yasan anyi
haihuwar yan 2, Sarki Qaseem bakaramin dadi yaji ba,
ganin Yayanshi yana samun haihuwa yanzu. Alokacin
beauty tagama Exams dinta, shima yadauki hutun
shekara.
Hakan yasa suka nufo gida, bakaramin farin ciki
mutanen gidan sukayi ba, apart dinsu da aka gina masu
anan suka sauka, wata dattijuwa aka kawo ma beauty
wadda zata rika temaka mata, ana cemata Ladingo.
Ranar suna akasama namijin sunan Mahaifinsu Sarki,
macen Kuma sunan Mahaifiyar Fulani. Ana kiransu da
AMEER DA AMEERA. Anyi shagali sosai, su beauty da
Ayman da Jakadiya Safeeya sunata fama da tsohon ciki.
Bayan suna da sati daya Ayman da Jakadiya Safeeya suka
haihu, Ayman ta haifi Namiji itama Jakadiya Namiji.
Beauty kuwa kuka tasaka dataji ance Ayman ta haihu.
Areef yatambayeta lafiya awayarta ta rubuta mashi ita fa tsoro takeji, dariya yayi uajawota yace ki kwantar da
hankalinki, babu wata wahala kinji ko? Kai tadaga mashi tana murmushi.
Adaren itama ta tashi da nakuda, dama beauty ga tsoro,
gaba daya taki sakin jikinta se kuka takeyi, tun Ladingo tana kokari harta gaji, Areef kuwa kamar shine yake
nakudar, kallonshi Ladingo tayi tace agaskiya Yarima ina ganin sede fa akaita asibiti, idan bahaka ba, za, iya rasa abinda ke cikinta.
Cikin rudewa yace to kihada kayan bara infada ma su
Momy. Cikin lokaci kankani aka nufi asibiti da ita,
hankalin kowa yatashi ganin yanda beauty tafita
hayyacinta. Suna zuwa aka nufi labour room da ita.
Kowa yakasa zama, Areef kuwa kuka yasaka, Haisam ne
yajashi suka fita waje yana lallashinshi.
Areef yace kasan Allah daga wannan haihuwar beauty
tagama haihuwa. Dariya maganar tabama Haisam sede
ya dake ganin halin da akeciki. Haisam yace addu,a zaka rika yimata, yace haba Haisam kalli fa yanda take shan
wahala, baiwar Allah wlh da ana karbar haihuwa dana
karbar mata. Amma anyi na farko anyi na karshe,
banason yaran dayan dazata haifa ya isa.
Haisam yace duk wannan ma bata taso ba, kaide muyi
Addu,a Allah yasauketa lfy. Areef yace amin. Amma.........
sunanshi yaji ankira cikin wata irin murya da Yaya Areef,, cak ya tsaya da magana dazeyi, yajuya yana kallon inda
yaji muryar tafito. Ai dasauri yanufi cikin asibitin Haisam yabi bayanshi.
Suna zuwa kusa da labour room din suka jiyo kukan
jariri, da gudu Areef yanufi dakin, cikin sauri Haisam ya rikeshi, yana fadin maza basu shiga, kajira afito da ita.
Areef yana hawaye yace kasakeni, wlh duk da bansan
muryar beauty ba amma nasan ita ce ta kirani, kasakeni
inje inga beauty na.
Da kyar su Waziri suka hanashi shiga, Momynshi ta matso tace haba Yarima kayi hakuri mana, kallifa yanda
ake kallonmu. Zonan kazauna kaji, yanzu za,a fito da ita.
Wani likita ne yafito fuskarshi dauke da murmushi
yanufo gurin. Sarki Qaseem ya tarbeshi yace yaya jikin
Amatullah?.
Likita yace Alhamdulillah tasauka lafiya, tasamu baby
girl, kuma duk suna cikin koshin lafiya. Sarki yace
Alhamdulillah. Likita yace yanzu za,a kaisu dakin hutu, idan kungama kusameni office, akwai wani albishir din.
Godiya sukayi mashi, yawuce. Areef yariga kowa shiga
dakin da suke, kotakan jaririyar be biba, gurin
beautynshi yanufa.
Hannunta yakama yarike sosai yana sannu beautu na,
nine ko? Murmushi tayi mashi, yace sannu bazan karaba
kinji? Kamar daga sama yaji tace Yayana ga babynmu.
Surin dago kai yayi yana kallonta. Itama shi take kallo, cikin farin ciki yanunta yama kasa magana, kai tadaga
mashi.
Ai yama manta da mutanen dakin kawai ya rungumeta
da karfi, harseda tayi dan kara. Momy tace lfiyarka
Yarima? Saurin sakinta yayi yajuyo yana sosa kai yace
wlh Momy beauty tayi magana.
Suma mamaki ne yakamsu, suka nufi gurinta. Murmushi
tayi tace Momy. Cike da farin ciki Momy ta matsa kusa
da ita tace da gaske ne, ashe? Ikon Allah, lallai Fulani zatayi farin ciki. Allah mungode maka. Sarki yace Sannu Amatullah, cike da kunya tace yauwa Abbah, yace bari
muje gurin likita mudawo.
Zaune suke a office din likita, bayan yagama rubutunshi yacire glass dinshi yace albishir din dana ce maku kilama idanunku sungane maku? Sarki yace tabbas yau munga
abin farin ciki, sede muyi ma Allah godiya. Likita yace haka ne, dama nafada maku, akowane lokaci maganarta
zata iya budewa, sbd akwai irinsu, kasan akwai wani
zakaga kurma ne, bayaji baya magana amma sakamakon
wani tashin hankali bakinsu yana budewa.
To itama Allah yasota gashi ta dalilin haihuwa bakinta
yabude. Kuma jikinta babu wata matsala, zuwa anjima
idan tahuta zaku iya tafiya, ga magungunan dazatayi
amfani dasu anan. Allah yabada lafiya. Godiya sukayi
mashi suka fita.
Segurin karfe 11 na dare suka koma gida, gaba daya
murna tacika gidan, Ayman jitake kamar itama tadawo
gida, dan Haisam yace tazauna tunda hidima tayi masu
yawa, agidan. Kowa cewa yake yarinyar tana kamada
Areef, shiko bakinshi yaki rufuwa, yamaki fita daga
dakin, seda Momy tayi mashi da gaske sannan yafita.
Haka akayita shirin suna, Momy tace ma, Haisam
yamaido Ayman gidan ayi suna gaba daya,daga baya
sesu koma. Aranar suna bakaramin taro akayi ba, diyar
Beauty aka samata Khairat, dan Areef da kanshi yace
babu sunan wanda zesa, shi khairat yajeso.
Yaron Ayman shima Haisam be tsaya saka sunan kowa
ba,yasa mashi Fahat. Waziri kuwa sunan Baffan beauty
yasaka ma yaronshi wato Hasheem, ana kiranshi da
Karami. Bakaramin dadi Baffan beauty yaji ba da irin
karar da waziri yamashi ba. Sarki Qaseem shine yasayi
komai na jariri harda ragunan suna.
Gaba daya masu laifin gidan aka fiddo haka aka raba
masu aiki, kowa danashi, Zakiyya abangaren masu abinci
aka kaita, tanayi tana kuka, ahaka suka gama, aka
sallamesu kowa aka bata nata.
Bayan kwana biyu mahaifiyar Zakiyyah ta kawo mata
ziyara, sunsha kuka sosai, ayanayin data ganta, kallonta tayi tace Zakiyyah kinga irin abinda nake fada maki ko?
Yanzu ina sarautarki da mulkinki gashi nan kinkare a
gidan kurkutu, acikin talakawa marasa galihu. Cikin kuka tace wlh Umma nayi dana sanin shiga wannan bakar
rayuwar dana shiga, kuma insha Allahu na dauki darasi.
Umman tace bakomai ai kin kusa fita kema kidawo gida.
Allah yayi maki sauyi da miji nagari. Ta dade kafin ta tafi, takawo mata abubuwa dayawa. Zakiyyah se kuka takeyi.
Seda suka sami wata 2 kafin sukayi shirin tafiya, visa
Sarki yasa akayima Ladingo yace sutafi da ita seta rika temaka mata. Haka beauty tacigaba dazuwa makaranta
tare suke tafiya da Ladingo, idan zasu shiga aji seta
barmata Khairat. Yanzu karatun yana mata sauki sosai,
dan har larabci tanaji tana maidawa.
After 2 years. Beauty ce tafito hannunta rike da takardu tana ta farin ciki tanufo gurin Areef da khairat dasuke tsaye jikin mota suna jiranta. Khairat tayi wayo sosai, sede haryanzu ba,ayi mata kanwa ko kani ba. Tana zuwa
tafada jikinshi tana murna. Kara rungumeta yayi yace
congratulation my beauty na. Allah yanufa yau kingama
karatunki.
Khairat tace Dady nima kadaukeni, dariya suka saka yace yi hakuri yau ranar Mimie ce, janta yayi suka shiga mota suka nufi gida. Party sosai suka shirya aranar, dan
beauty hada qur'ani tasauke, gashi aharkar boko yanzu
sede takoyama wani.
Bayan kwana 2 suka fara shirye shiryen komawa gida
dama tuni yagama hada komai na aje aikinshi. Bayan
suje sunyi tsaraba washe gari suka dira a nigeria. Kowa yayi farin ciki da dawowarsu. Haisam kamar ze zuba
ruwa akasa dan farin ciki. Beauty ta kalli Ayman wadda
cikinta har yafito kadan tana dariya tace Aunty yanaga
haka?
Hararta tayi tace kema zakiyi ne ai, haka suka nufi gida.
Babbar tarba, kowa yana cikin farin ciki.
Haka rayuwarsu tacigaba da tafiya acikin masarautar,
Areef yakoma aikinshi, suna zuwa cikin wanciyar hakali
shida Haisam.
Iyalen Baban darazo sunajin dadin zaman gidan
sarautar, babu abinda basa samu ta ko ina.
Ayanzu cikin masarautar karatu akeyi sosai, dan Malam
ya aiko da malaman dasuke koya masu karatu, gaba
daya bayin dasuke gidan, harma da masu laifi, ana fidda masu ranar karatu. Sosai suke jin dadin abinda ake
masu, gaba daya canji yasamu agarin Gombe, duk
wanda ya aikata wani laifi, ana yanke mashi hukunci
dede dashi.
Bayn shekara 2 beauty takara haihuwar da namiji, ana
kiranshi da Faisal, Ayman ma yaranta biyu, mace da
namiji, macen sunanta Labiba.
Ayau ne Zakiyya tafito daga kurkutu, rungume suke da
juna ita da Jakadiya Karima, kuka kawai sukeyi. Zakiyyah tace Allah yada fuskokinmu, da ace ba,a gidan nan kike
ba, dazanyi maki alkawarin kawo maki ziyara.
Amma yanda zanbar gidan nan bana fatan inkara
dawowa. Kiyafemun abinda namaki nima nayafe maki.
Jakadiya tace nayafe maki. Allah yabaki miji nagari kema kiyi aurenki. Da kyar suka rabu sunata kuka. Sallama
tayima sauran mutanen gurin tafito.
Mahaifyarta ce, tazo daukarta, haka suka nufi fada kallo daya zakama Zakiyya kasan tafita hayyacinta, gaba daya
tayi baki ta rame. Azaune suka iske iyalan masarautar,
kowa fuskarshi cike da annuri.
Kallonta sukeyi cike da tausayi. Zama tayi bayan
sungama gaisawa, ta kalli Baffan beauty, suna hada ido
ykara daure fuska ya dauke idonshi daga kanta. Wasu
hawayene suka zubo mata, ahankali tace
Nasan banida bakin dazan rokeka gafara, amma duk da
haka bazan yi kasa aguiwa ba, dan girman Allah kaya
femun abubuwan dana yimak. Hakika naga rayuwa,
kuma hakan kadan ya isheni darasi. Banaso in mutu da
hakkinka kayafemun.
Kuka ne yaci karfinta. Shiru yayi kamar bazeyi magana
ba, can yace bakomai nidama nadade da yafe maki.
Allah ya shiryeki. Matsawa tayi kusa da Fulani, takamo
hannunta, tana kuka tace Fulani dan .... saurin rufe mata baki tayi tana girgiza kai, hawaye suna fita daga idonta tace nayafe maki. Allah ya yafe mana baki daya.
Haka tayita rokon mutanen falon tana kuka, har seda
tasa wasu kuka. Tashi sukayi auka masu sallama, har
bakin mota aka rakasu, amma banda Sarki Qaseem,
Waziri da Baffan beauty. Seda suka tafi sannan suka
dawo.
Bayan kwana biyu da komawar Zakiyyah gida tadan
murmure, mahaifinta yakira Ummanta da ita suna zuwa,
ya kalleta yace, zakiyya ina tayaki murnar fitowa daga
gidan yari. Basena kara tunatar dake rayuwa ba. Nasan
azaman da kikayi kin kin koyi darussa da dama. To
Alhamdulillahi dama arayuwa ana son idan mutum yayi
kuskure yayi kokarin gyarawa.
Shiyasa Allah da kanshi ya saukar da hukuncin daza,ayi
ma masu laifi, domin yazama darasi agaresu. Mutane dayawa ta dalilin wannan hukuncin suke shiryuwa. Naji
dadi sosai danaga kin koyi darasi.
Abunda yasa nakiraki dama kinsan nace dakin fito zan
aurar dake,somin zamanki agidan nan babu abinda ze
amfana maki, se tarin bakin ciki. Dan haka nazaba maki
miji, amma idan beyi maki ba, kinada ikon canza wani
ba dole zanyi maki ba.
Goge hawayen idonta tayi tace, babu wani zabi
dazakamun inki binshi, nayarda da duk wanda
kazabamun. Murmushi yayi yace naji dadi, kuma
bakowa bane se Wazirina. Shikadai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 13