magana
me ban al,ajabi, kuma kaima kayi kokari sosai, wanda
bakowane ze iya abinda kayi ba, lallai duniya babu gsky, tsoron Allah yayi karanci aduniyarmu da zukatan
mutane, yanzu dan Allah ina wanda yakeda alhakin
haukatar da wannan mata zesa dumbin zunuban daya
dauka nata ita da yarta har na tsawon shekaru 18?.
Innalillahi Wainnailaihirraji'un. Yanzu Baba abinda
nakeso da kai, ka kwantar da hankalinka, insha Allahu
babu abinda ze sameka, kuma zamuje musamesu a inda
kabarsu, addu,a zata temakemu akan wadan nan aljanu,
kuma zanyi magana dasu, dan suma basuda niyar cutar
dasu, asalima suna temakonsu ne. Bara inkira sauran
dalibaina su shirya muje musamesu, amma ai bazamu
bar bayin Allah acikin daji ba, kuma a MAKABARTA.
Kodan lafiyar ita yarinyar.
Tashi yayi yakira yaranshi yafada masu su shirya zasuje wani guri, koda yadawo, yasamu Baba yana jiranshi,
haka suka dauki mota yasa aka kira Jakadiya da matarshi suka shiga, dan sutemaka masu gurin daukosu. Baba
addu,a kawai yakeyi Allah yasa su samesu, agurin.
Nima nace amin Baba.
Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 15⚜20
Hankali tashe Baba yafito daga motar yanufi inda
rumfarsu take, amma abun mamaki babu ita babu
dalilinta, idan ba wanda yasan da ita ba, babu wanda
zece mutane sun taba zama agurin. Wasu irin zafafan
hawayene suka fara zarya afuskarshi yan fadin Innalillahi wainna ilaihirraji,un. Zama yayi adede inda rumfar take yana kuka.
Malam ne, yakaraso gurin yadafashi yace Baba ba kuka
yakamata kayi ba. Insha Allahu nizan dawo dasu duk
inda sukaje, dama munsaba da aljanu, masu taurin
kaima ina gogawa dasu, har kafiran cikinsu muna fama
dasu, bare kuma wadannan da alama musulmai ne.
Baba yace wlh malam, da,a ace sun dauke su Yar Baba
bansan inda suke ba, gara ace banfada maka ba, muyita
zama dasu anan har mutuwa tazo tasamemu. Tsautsayi
ne, da kuma tausayi yasani karya dokar dasuka saka
mun.
Shiru malam yayi, can ya kalli daya daga cikin yaranshi yace daukomun shinfida acikin mota kataho mun da
gorar ruwa, bayan yakawo mashi ya amsa yafara alwala,
shikuma ya shinfida mashi abin sallah. Kallonshi yayi
yace kacemasu Jakadiya sukoma mota suzauna
harsenace sufito.
Sallah yafara yi, kowa yana kallonshi, seda yayi raka,a 4
sannan yazauna yafara karatu, da yayi seya tsaya yayi
adduo,i sannan yacigaba. Seda yadauki tsawon minti
talatin, sannan wata kura ta taso kafin wani lokaci sega rumfar su Yar Baba ta bayyana agurin datake. Hamdala
malam da Baba sukayi, dasauri Yar Baba ta iso kusa
dashi tana dariya. Daya daga cikin yaran malam, wani
yace Tsarki ya tabbata ga mahaliccin dayake tsara
halittun bayinshi. Anya wannan yarinya mutum ce? Aini
tunda nake bantaba ganin yarinya me kyanta ba, damma
wai tana cikin rashin galihu, wannan da,a birni take
gidan masu kudi ai se anrika boyeta.
Dariya nakusa dashi yayi yace kaima kenan dakake iya
magana. Baba se shafa kan Yar Baba yakeyi yana
murmushi, ita ko tashige jikinshi don da alama tsoron
mutanen gurin take, dan atsawon rayuwarta bata taba ganin kowa aduniya ba, daga Mamanta se Baba.
Mamanta kuwa kasa fitowa daga runfar tayi, se kuka
takeyi.
Malam yace Alhamdulillahi, Allah mungode maka, kallon
gefenshi yayi yace bayin Allah, meyasa bakuso atemaki
wadannan mutanen? Kowa yafara kallon inda malam
yake magana, sede babu alamun kowa agurin, maganar
mutum daya tafara tashi me cike da alamun ladabi.
Allah yagafarta malam, mundauki tsawon shekaru 18
muna tare da wadannan bayin Allah, mune muka temaki
wannan mata, alokacin da takusa halaka, wanda babu
wani dan adam daze iya temakonta, semu, kuma ga
dukkanin alamu munga kamar hadari ne, ya jefota gurin
datake, sede koda muka bincika bamuga alamun mota
tayi hadari ba, asalima mugunta akaso ayima wannan
mata. Shiyasa muka temaketa, sede haryanzu Allah
bebamu ikon gano dalilin daya kawota nan ba, kuma
babu wani asiri ajikinta, wannan lalurar datake tare da ita da alama kode ajikinta take, ko kuma buguwar datayi ne yakawo mata ita. Malam yace naji, amma me kuka
sani game da ita? Tsawon shekaru 18 dasuka wuce wata
rana da dare muna zaune afadarmu.
Se kawai mukaji fadowar wani abu akusa damu, sede abun mamaki, muna dubawa semukaga mace ce da
tsohon ciki, kuma cikin ikon Allah babu abinda yasamu
cikin, anan muka kara dubawa semukaga tabbas bil
adamace, anan nasa yarana dasu dubamun ko hadari ne
akayi, dayake akasan wani rami muke, hakan yasa nayi
zaton ko hadari ne, dan wani lokacin idan akayi hadari
mutane suna fadowa nan. Bayan yadawo yace mun
babu wata mota datayi hadari, kafin mu ankara
semukaji wannan mata tana nishi da karfi, nan take
nagane haihuwa zatayi, anan nasa akayima me dakina
magana.
Allah gafarta malam, ita dasauran wasu jinsinmu suka
temaka mata harta haihu, sede koda ta haihu bata cikin
hayyacinta, haka suka gyarata ita da diyarta, aka samo
kaya aka samata, anan nace su kwantar da ita kusa da
mahaifiyrta. Dayake safiya takusa, haka muka tashi
mukabarta agurin ita da yarinyarta, anufina idan gari
yakara haske kila wasu suganta sutemaketa.
Bayan dare yakarayi muka sake dawowa fadarmu,
abun mamaki kuma bamuga wannan mata ba, senayi
tunanin wasu sun daukesu, muna nan zaune sega daya
daga cikin yarana yazo yacemun ahanyarshi tazuwa nan
yaga anyi wata runfa agefen wata MAKABARTA sede yar
karama ce akayi, daya kara matsawa seyaga wata
jaririyace kwance acikin rumfar, saman hakukuwa
anshinfida mata zani tana bacci, daga waje kuma wata
mata ce kwance agaban rumfar, dan tayi masu kadan
bazasu iya shiga su 2 ba, asalima rumfar yara ce, abinda
yabashi tsoro yaga wata halitta daga cikin jinsinmu sede basa cikin zuri,armu wato musulmai, yaganta tana
kokarin daukar yarinyar.
Shine yaje gurin dasauri, to dayake sunsan kowaye kuma
suna tsorona, yana ganinshi yayi saurin bacewa. Shine
yazo yana fadimun, koda nasa adauko munsu senaga
wannan matar ce tajiya, nan take tausayinta yakamani,
anan nayi alkawarin kareta ita da yarta kuma babban
dalilin dayasa nabarsu aMAKABARTA, sbd bazeyiwu
nakaisu cikin jinsina ba, haka kuma nagane bil adama
basuda tausayi harsuka iya barin wannan mata ita da
yarta acikin daji babu metemakonsu, shiyasa nasa
yarana suka yimata rumfa babba wadda zata isheta ita
da yarta, kuma nasaka yarana suzama masu gadinsu.
Kasancewar bata da hankali yasa abubuwa da dama
mune muke temakonta dasu, tundaga abinci dakuma
ruwa, na hana yarana subarta tafita daga MAKABARATAR,
sbd ina gudun kaidin bil adama, ko gawa aka kawo babu
wanda yake iya ganinsu, nina zaba masu suyi rayuwarsu
ahaka. Aranar da megadi yazo lokacin yarana suna
sallah, basuyi tunanin wani zezo ba, hakan yasa shima
yayi sa,ar ganinsu.
Danaga shima yanada zuciyar imani hakan yasa na
kyaleshi yacigaba dazama dasu, sede banyarda
yafadama kowa ba, dan nasan zuciyar kowa daban take,
kuma yayimun alkawarin baze fada ba, mune muke
daukesu aduk lokacin dayayi niyar fadama wani.
Koyanzu yaci sa,a kaine yafada mawa, amma daba kai
bane, yanda muka daukesu nayi niyar bazan ajesu anan
kasar ba gaba daya, gara nakaisu wata kasa inda babu
wanda yasansu, nasan zasu temakesu. To malam
wannan addu,ar dakayi ita kadai tadawo damu. Kuma
nayima Baba hakuri tunda naga alkhairi yakeson su
dashi, yanzu Malam kome kayanke zamubi umarninka,
amma kasani duk inda zaka kaisu kada karabasu dan
yarinyar nan bazata iya zama awani guriba batare dasu
ba. Kaima Baba kasan yanda kuka shaku.
Malam yace naji dukkan bayaninka, kuma naji dadi sosai
daya kasance kaine katsinci wadannan bayin Allah, nasan irin halin temako dakake dashi bazaka taba barin wani
abun cutarwa yasamesu ba. Allah yabiyaka kaida
yaranka, hakika zakaran da Allah yanufa da cara, to ko
ana muzuru ana shaho seyayi. Tabbas wannan yarinya
Allah kadai yasan irin alkhairin data debo kuma shine
yaraya abunshi. Yanzu abinda nakeso infada maka,
gaskiya zaman yan adam agurin nan beyi ba, saboda
rayuwar gaba, kaga wannan yarinya tagirma, yakamata
ace tashiga cikin mutane, dan kada wata rana tafi haka
girma ace zata koma cikin mutane abun ya gagara, kalli
yanda take cike da firgici sbd ta ganmu wanda banga
laifinta ba, nasan bata taba ganin kowa ba, se mutum 2.
Dan haka nayi maka alkawarin zandaukesu zamuje mu
sama ma wannan mata magani, duk da kace ciwonta babu asiri ajiki, zamukaita asibiti aduba lafiyarta, kuma nizan rikesu tamkar jinina. Nagode sosai daka
fahimcemu. Godiya sosai Malam yayima wannan
shugaban aljanu sannan yabace.
Malam yace to Baba kajide yanda mukayi dashi, yanzu
yakake ganin za'ayi? Baba yace naji dadin abinda kayi,
kuma dama abinda nake fata kenan arayuwata inga
ranar dasu Yar Baba zasu bar gurin nan, shiru yayi yana goge kwallan idonshi. Malam yace yanzu kutashi muje
gida semusan abinyi. Jakadiya da matarshi yasa sukamo
maman Yar Baba, tana ganin zasu dauketa tafara kuka
sosai, da kyar suka kamata, shima seda Baba yaje
yakamota yarike hannunta dana Yar Baba sannan ta
bisu, gurin shiga mota kuka Yar Baba tasa masu, tsayawa tayi takishiga motar, duk tarike Baba, dakyar yasamu
tashiga, haka suka nufi cikin gari.
Zaune suke afadar Sarki Qaseem, Waziri yamika gaisuwa
tare dafadin Allah yatemakeka, munje kuma mun isar da
sakonka, malam yace afada maka sunanan suna addu,a
insha Allahu za,a dace, kuma yace afada maku Fulani
tana nan araye, sede haryanzu Allah be gwada mashi
inda take ba. Ga wannan ruwan addu,a ne yace akawo
na me martaba.
Areef ne ya amshi addu,ar ya ajeta agefen Sarki.
Gyaran murya Sarki yayi yace to Alhmdullh, inaganin
muma semucigaba da addu,a nasan wata rana Allah ze
bayyana mana Fulani da kuma abinda tahaifa, addu,ar
mu Allah yasa kome ta haifa ace shima yana raye. Waziri yace maganar gashin jikin memartaba, meze hana a
maidashi yazamana duk bayan kwana 2 sbd inaganin
hakan zefi temaka mashi. Sarki yace hakan ma yana da
kyau, muje abashi maganin. Areef yatashi yadauki
maganin suka nufi gurinshi.
Gimbiyar Babbar Gida suka samu agurinshi tana bashi
kayan marmari, sallama Waziri yayi, daya daga cikin
fadawan yaje ya sanar da ita zuwan me martaba.
Komawa yayi yamasu iso sannan suka shiga, bayan
sungaisa yatambayeta mejiki tace dasauki, tashi tayi
tafita, jakadiya ta mara mata baya.
Duka sauran bayin suka fita, se Babban Hadiminshi ne,
kuma wanda sarki ya aminta dashi ne kadai yarage,
karbar robar Sarki yayi yazauna kusa da Yayanshi, yace
sannu yaya, Malam yace yana gaisheka, kuma yace
abinciken dayayi yagano Fulani tana raye bata mutu ba,
insha Allahu zecigaba da addu,a za,a ganta. Kokarin dago kanshi yafarayi jin anyi maganar Fulaninshi, cike da farin ciki Sarki da Waziri suka temaka mashi yajingina, wani
murmushin farin ciki ne, ya bayyana afuskarshi. Shima
Sarki dasauran mutanen dakin kowa farin ciki ne, yacika fuskarshi.
Sarki yace hakane Yaya bata mutu ba, ga wannan
maganin yace abaka kasha, dan Allah kada kaki karba, kaga yau shekara nawa ana kawo magani baka sha, ayau
naga farin cikin dana dade bangani afuskarka ba, inaso
kasha maganin nan, kaga kaima zaka samu karfin yimata
addu,a.
Babu bata lokaci yabude baki, Sarki dakanshi yabude
robar yayi bismillah yafara bashi maganin, tas yashanye, aka dauko dayar robar Sarki yace wannan ajiki za,a shafa maka, kallon Waziri yayi, babu bata lokaci yakama keken yaturashi suka nufi daki. Cike da farin ciki Areef yafita yanufi bangaren Momynshi. Dede zewuce alambu
yahadu da sarkin Fada, kara hade fuska yayi, sarkin fada yamatso dasauri yana washe baki yace Allah yatemaki
mejiran gado. Hannu kawai Areef yadaga mashi yawuce,
da harara Sarkin Fada yabi bayanshi, kwafa yayi sannan
yayi gaba.
Bayan sunje gida dakyar Yar Baba tasaki Baba Jakadiya
takamata ita kuma Ladidi matar Malam takama Maman
yar Baba suka shiga ciki, haka yaran gidan suka rika sakin baki suna kallon Yar Baba, itam seboyewa take ajikin
Jakadiya. Daki takaita tazaunar da ita, haka suka kama
Mamanta suka nufi bandaki da ita, da kyar sukayi mata
wanka, sun sabata yafi so 5, haka suka fito da ita se kuka takeyi.
Dakin Ladidi suka kaita, sannan Jakadiya tariko Yar Baba takaita bandaki, kintsayawa tayi, dan bata taba ganin irin shiba, seda Jakadiya ta tsaya takoya mata yanda zata
wanke jikinta da soso haka tasata tayi wanka tawanke
mata kanta, sannan suka fito, kallo daya zakayima yar
Baba kagane tsanin kyan datake dashi, dan kamatake da
larabawa.
Bayan sungama shiryasu suka basu abinci anan maman
Yar Baba takwanta se bacci, yar Baba kuwa tanajikin
Jakadiya takwanta tayi shiru, ita kuma tana gyara mata
gashinta, wanda yaji mai se kyalli yakeyi, daga haka
itama tayi bacci. Malam ne yaleko yace idan sungama
sufito suji abinda ya yanke akan su Yar Baba.
Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 20⚜25
Malam yayi gyaran murya ya kalli Baba yace nataraku anan dan infada maku abinda nayi tunani akan
wadannan bayin Allah, da farko de dakai zanfara Baba,
kaga kamar yanda akayi mana bayanin akan 'Yar Baba,
bazata iya rabuwa da kai ba, shine nace meze hana idan
har kanajin zaka iya zama dasu, kayi hkr da waccan
sana'ar taka kadawo nan cikin gari kaida iyalanka
nikuma namaka alkawarin gurin zama harma da aikinyi
aduk inda kake so.
Amma Baba kaduba kagani mekace? Gyara zama yayi
yace agskiya Malam, nikaina banajin zan iya hkr da
rashin 'Yar Baba akusa dani, nayi sabo da ita sosai wanda basauki bane ace za'a rabamu, kuma kamar yanda nayi
alkawari zankula dasu nayarda zanbar aikina da
muhallina indawo nan mucigaba dazama.
Malam yace gaskiya naji dadi, kuma insha Allahu zaka
samu aiki me kyau, duk da acan ma aikin lada kakeyi nan ma wani aikin ladan ne, tunda temakon bayin Allah
zakayi. Zamucigaba dazama dasu anan kuma gobe
zamuje asibiti mukai ita wannan mata domin a aunata
asan wace irin kalar hauka gareta, idan maganin asibiti ne, se adorata akan magani, idan kuma na hausa ne,
semudawo acigaba dayi mata addu'a.
Jakadiya tace Yaya, dayake kanwarsu ce itace auta, tunda mijinta yamutu bata kara aure ba kuma bata taba
haihuwa ba, shine Malam yasama mata aiki agidan Sarki,
ta dalilinshi Gimbiya Shuwa tabata Jakadiya dan tace ta aminta da ita. Kallonta yayi yace inajinki meyafaru?
Saddar da kanta kasa tayi tacigaba da magana.
Dama wata alfarma ce nakeso zannema agurina kaida
Baba, amma dan Allah kada kucemun a'a. Wlh tun da
muka dauko bayin Allan nan naji 'Yar Baba tashiga raina, musamman dazu datake kwance akan cinyata senake
mata kallo kamar 'Ya ta dana haifa da cikina, duk da
Allah be bani haihuwa ba, amma ayau naji inada
sha'awar samun diya tabbas da za'a bani 'Yar Baba zanfi kowa farin ciki da hakan, kuma zantafi da ita can gidan Sarki mucigaba dazama da ita, amma Yaya mekace?.
Shiru yayi yana kallon kanwar tashi, yana ganin lokacin datake goge kwalla afakayce dan tasan yahanata kuka
akan rashin haihuwa. Tausayinta yakamashi, kallon Baba
yayi yace Baba mekace game da maganarta? Baba yace
ai Malam kai muke saurare duk abinda kayanke dede ne,
nide fatana kada akawo wani abun dazeyi sanadiyar
nisantani da kuma mahaifiyar wannan yarinya daga 'Yar
Baba. Allah yasani nidanake cikin hankalina zanshiga
damuwa sosai, bare kuma ita wadda ta haifeta.
Malam yace shikenan gobe idan mundawo daga asibiti
mukaji bayanin likita nikuma zan fada maku abinda
nayanke, amma Baba dan Allah kada kacemun a'a aduk
abinda zan zartar, kuma kaima insha Allahu babu abinda
ze rabaku da Yar ka, duk inda taje kaima zakaje. Bayan kowa yatashi Malam ya kwanta yana kara tuno yanda
wannan aljanin yafada mashi yanda suka tsinci wannan
mata, rufe idonshi yayi yakara tuno lokacin da Sarki yake fada mashi halinda Fulani take ciki alokacin dasuka
nemeta suka rasa. Ajiyar zuciya yayi yatashi cike da
tunani aranshi yana addu'ar Allah yasa tunaninshi
yazamo gaskiya, amma koma menene yace zeyi istahara
da dare.
Wai lafiya Yarima naganka cikin farin ciki haka?
Murmushi yayi yace wlh momy yau Baffa yayi
murmushi, kuma yasha maganin damuka karbo mashi
agurin Malam na Darazo, Tashi zaune tayi cike da
annashuwa tace lallai ga dukkan alamu kunzo mashi
dawani bayani me dadi ko? Nan yafada mata abinda
Malam yace, hamdala tayi tace ai insha Allahu Allah
zebayyana Fulani da ita da abinda akema bakin ciki
agidan nan, kasanni tausayin Baba nakeyi, shiyasa
banason haduwa dashi sede nayi mashi aike.
Yarima yace Momy niduk lokacin damuka hadu da
Sarkin Fada kawai se inji raina yana baci, kawai nide
mutumin be kwantamun arai ba, ganinshi nake da siffar
munafukai. Momy tace Allah sarki, kaine kake ganinshi
haka, amma aduk cikin fadar Sarki ai inaji babu wanda
yake maka son da sarkin Fada yake maka tun kana yaro,
kama cire wannan abun daga ranka kawai shedanne
yake maka wasiwasi azuciyarka. Shiru Areef yayi amma
sam zuciyarshi bata yarda da abinda tafada ba.
Bayan sungama shafa mashi maganin ajikinshi bacci
yadaukeshi, kamashi sukayi suka kwantar dashi bisa
gadonshi suka rufo mashi kofar, Sarki yace insha Allahu Allah yakusa kawo mana karshen wannan halin da muke
ciki. Waziri yace da alama wannan maganin zeyi aiki
ajikinshi dan tunda naga yasha naga wasu alamu. Sarki
yace Allah yasa, suna fita sukaci karo da Jakadiya, kara gaishesu tayi, Sarki ya kalleta yadauke kai, Waziri yace zaki iya tafiya dan me martaba baya bukatar wani abu,
kuma ma yasamu bacci, Jakadiya tace to ai shikenan
Allah yabashi lafiya, juyawa tayi ta tafi tana me hararar Waziri tagefe.
Da Sallama tashiga falon Gimbiya ita kadai tasamu se bayin dasuke mata hidima, zama tayi tana fadin Allah
yatemakeki, Allah yasa kifi haka, murmushi tayi tadaga
mata hannu, Jakadiya ta kalli sauran bayin dasuke falon, lokaci guda sukayi hanyar waje.
Gimbiya tace da alama akwai magana abakinki? Tace
kwarai ma kuwa Gimbiya, waigawa tayi tace amma
rankishidade banga Gimbiya karama ba, ko lafiya?
Yamutse fuska tayi tace oho kinsanta da nawa yanzu
haka tana can tana shiryawa kinsan yau ita zata karbeni.
Gyara zama Jakadiya tayi tace ai me martaba ma yasamu
bacci, kuma da alama ya karbi maganin dasuka bashi,
dasauri Gimbiya ta tashi zaune, tace haba Jakadiya wane irin labari ne marar dadinji kike fadamun haka?
Allah yahuci ranki Gimbiya 'Yar Babbar Gida, kaina bisa wuya, banga amfanina aduniya ba idan har nazamo daya
daga cikin masu bata maki rai, agafarceni Gimbiyar Sarki mace daya tamkar da dubu, kedayace me haske agurin
me martaba, duk sauran matanshi bayinki ne Gimbiya
me mulki gaba da baya. Wani kayataccen murmushi
Gimbiya tasaki, ahankali tace inajinki menene shawara?
Nagode Gimbiya, amma aganina meze hana mubi
shawarar dana fara kawowa daga farko inaganin ita
kadaice hanyar dazata bulle mana, dan mutanen nan
suntashi tsaye akan wannan al'amari inajin tsoron
abinda zedawo. Maganar Gimbiya medaki sukaji tana
fadin wannan shawara taki Jakadiya tayi dede, amma ina
ganin kamar haryanzu Yaya batayi na'am da ita ba.
Zama tayi tare da daukar apple tafaraci. Jakadiya tace
Allah yatemakeke Gimbiya, barka da fitowa, hannu
tadaga mata tamaida kallonta gurin Gimbiya tace Yaya
dan Allah wannan karin kada kice zaki ki karbar
shawararmu, wlh ayanzu kissa da tuggu basuci kawai
mubama Jakadiya dama kamar yanda tanema daga
farko.
Wani kallo Gimbiya tabita dashi, sannan tace wai meyasa kuka kasa fahimtata, koda yake ba laifinku bane daga ke har ita babu wanda yakeda jinin sarauta ajikinshi. Tashi tayi ranta abace tashige daki, da kallo Gimbiya medaki
tabita, Jakadiya ko cikin sauri tabi bayanta jiki na bari.
Karamin tsaki Gimbiya medaki taja ta tashi itama tabi
bayan Jakadiya tana Allah wadai da wannan kaskancin
datasa kanta ake mata.
Washe gari bayan sunje asibiti likitoci suka taru akanta, anyi mata gwaje gwaje kala kala, bayan sungama likitan
yakira malam office, seda yayi rubutunshi sannan yakalli malam yace, agsky munyi duk wani bincikenmu kuma
sakamako daya yake bamu, wannan mata lalurarta
acikin kanta take, kuma mtsalace mesauki, sede kafin
asamu abinda zedawo maka da hankalinka shine aiki,
abinciken damukayi mungano cewar buguwa tasamu
akanta, komade hadari ne, ko kuma akwai abinda
yabugar mata kai, wanda shiyayi sanadiyar
haukacewarta.
Amma abu mafi sauki shine duk ranar data kara samun
makamancin abinda yafaru da ita, kota bige ko kuma
ace arika nuna mata abubuwan datayi tarayya dasu kafin
tasamu matsalar to zata iya dawowa hankalinta. Dan
haka yanzu gida zaku koma da ita, akwai magungunan
dana rubuta sekuyi mata amfani dasu. Godiya malam
yayi mashi yakarbi takardar maganin yafita.
Koda sukaje gida ajikin Jakadiya Yar Baba takwanta
hartayi bacci, dan yanzu tafara sakin jikinta, sede daga Jakadiya bata yarda da kowa agidan se ita. Adaren ranar
bayan sallar isha'i malam yakara tarasu, hada Baba dan yaje yadauko iyalanshi yazo anan malam yabashi daya
daga cikin gidajenshi suka sauka aciki kuma yasa aka
zuba mashi kayan abinci dana amfani.
Malam yace to Baba kajide abinda likita yace agame da
ciwon wannan mata ko? Dan haka nayanke shawarar
za'a bama Jakadiya su ta tafi dasu can masarautar
datake, dan Sarki mutumina ne, dazu munyi waya da
waziri, kuma nafada mashi komai sede banfada mashi
tarihinsu ba, kuma Baba wannan tafiya hada kai za'ayita, acan zaka samu aikin dazakayi idan yaso daga baya idan
komai yadedeta zaka iya zuwa kadauki iyalinka.
Sede Baba banaso kafadama kowa labarinsu, kasan
mutane akwai son zuciya nafiso kabarshi atsakaninmu
wata rana zasuji labarinsu, kuma abangaren Jakadiya
Waziri yace zasu zauna, kasan kuwa bangarenta yana
daga bayan lambun gidan, bakowane yake zuwa ba, sede
kai tunda sunsan kowaye kai zaka iya zuwa aduk lokacin
dakakeso. Allah yabaka ikon rike sirrinku, sekayi ahankali da gidan sarauta, ba,a aboki agidan, kowa da halinshi
yake zaune, dan haka kazama cikin shiri gobe insha
Allahu zakutafi da safe. Allah yakareku daga dukkan
sharri.
Baba yace amin, kuma naji dadin abinda kamun, ga
iyalai na nan, nasan zaka kulamun dasu Allah yabaka
ikon zama dasu lafiya, amma taya zamurika magana da
kai? Murmushi malam yayi yace kada kasamu damuwa
akwai waya ahannun Jakadiya, kuma iyalanka zasu zauna
cikin kwanciyar hnkl, fatana Allah yabaku sa'a. Haka
kowa yatashi Jakadiya tanacike da murna, harta tashi
yace Jakadiya kisameni adaki, Bayan sun shiga naji
malam yafara magana, akwai abubuwa da dama da
zuciyata take sakamun akan wannan matar, shiyasa ma
nace zakutafi tare. Kara rage murya yayi yana mata
bayani,akan yanda yakeson abubuwan sutafi, sede duk
yanda naso inji abinda suke fada ya gagara, haka
nadawo inajiransu sufito, sundauki kusan awa daya suna
tattaunawa sannan tafito.
Washe gari dasafe Malam yabada mota akadaukesu suka
nufi babbar masarautar Gombe.
To jama,a bara muji menene asalin labarin wannan
masarauta.
Tuna baya,
Asalin Labarin.
MASARAUTAR BUBAYARO.
Muhadu a page nagaba.
Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 30⚜35
Qaseem yayi saurin fadin haba Yaya kasan mekake
fada kuwa? Sarki yace koma menene Qaseem nasan
baze wuce tace in....... kara kamo rigarshi datayi ne
yasashi yin shiru yamai da hankalinshi gareta. Bawan
Allah ga 'Yata nan, ita kadai Allah yabani, mahaifinta
yarasu nikadai narage mata, kuma nima gashi Allah
zerabata dani. Daga cikin wancan kauyen muka fito,
mutanen garin suka koromu sbd kawai wani yayi ma
mahaifinta kazafi, sakamakon hakan ciwon zuciya yayi
ajalinshi.
Mu kuma suka koromu komai basu bari mundauka ba.
Inarokonka kobayan babu raina kada kabari Nafeesa
takoma garinmu, kamar yanda kamun alkawari inason
rayuwar Nafeesa tayi albarka dan Allah kadaure ka auri
Nafeesa.
Qaseem cike da bacin rai yace dalla malama kifadi abu
meyuwuwa kinko san dawanda kike magana? Idan baki
sani ba, to........ tarin daya taso matane yasashi yinshiru suka maida hankalinsu kanta bakaramin shiga tashin
hankali Sarki yashiga ba, ganin tana wani irin aman jini, Nafeesa ko se kuka takeyi, Sarki yatashi yace ma Waziri adauketa ko akan doki ne, mutafi da ita asibitin cikin
gari.
Wani bafade Waziri yasa yadaukota, Haka Nafeesa ta
tashi tana kuka. Cak bafaden daya dauketa ya tsaya jin
jikinta yakara nauyi, Waziri yace muje mana katsaya
kana bata lokaci, Ranka yadade ade zo aduba wannan
baiwar Allah naji jikinta yasaki, dasauri Sarki yadawo
dabaya, suna zuwa Waziri yataba hannunta yaji yadawo,
yasa hannunshi gurin hancinta yaji ba numfashi, sam
yamanta da diyarta agurin yace Rankai dade inaji fa ta
mutu. Wani kara da Nafeesa tasaka nan take tafadi kasa
sumammiya. Sarki cike da damuwa yasa Fadawa suka
dauketa da mahaifiyarta aka dorasu akan doki aka nufi
gida dasu, Qaseem kanshi jikinshi yayi sanyi yatausaya
ma Nafeesa sosai.
Ko kafin sukai gida maman Nafeesa harta saki, dan akwai dan tafiya, suna zuwa sarki yasa aka kira Jakadiya nan
Waziri yayi mata bayanin komai aka shiga da gawar cikin gida. Ita kuma Nafeesa aka kira likitansu domin
yadubata.
Babu bata lokaci aka gama shiryata akayi mata sallah
tasamu jama'a sosai, haka aka kaita gidanta na gaskiya, jikin Sarki yayi sanyi sosai dan yasan yariga da yadauki alkawarin da dole yacikashi. Bayan sundawo yakira
Waziri dan suyi magana, bebi takan Qaseem ba, dan
yasan baze bada goyon baya ba.
Sosai Waziri yakara karfafa mashi guiwa kuma yakara
tunasar dashi muhimmanci alkawari, da kuma irin
jihadin dazeyi, Waziri yace kobaka aureta ba, kasama
mata miji acikin gidan nan ko awaje hankalinka baze
taba kwanciya ba sbd bakasan irin rikon dazeyi mata ba.
Sarki yace bakomai ai itama mutum ce, kamar kowa
kuma yin hakan dazanyi baze ragemun wani abuba, sede
Allah yasani atsarina banida ra'ayin auren macen da bata fito daga gidan sarauta ba, kuma wannan ra'ayi nane
shiyasa Qaseem yakeda irin ra'ayin, segashi nashi haryafi nawa. Nasan zeji haushi na, amma dole incika alkawarin
dana dauka dazaran Nafeesa tasamu sauki za adaura
auren banason tashiga cikin damuwa. Allah yabani ladar
abinda nayi.
Bakaramin tashin hankali Gimbiya Zakiyya tashiga ba da
Jakadiya takawo mata maganar auren Sarki ba, duk da
batason Jakadiya amma daga ranar tafara sakar mata
fuska dan tasan zatayi mata amfani. Koda tafada ma
mamanta shawara daya tabata, kada tasake tanuna
bacin ranta akan auren, kogurin Sarki banyarda ki nuna
bacin ranki ba. Da wannan shawarar Gimbiya tasamu
sauki aranta. Koda Jakadiya taga tafara samun sakin
fuska agurin Gimbiya seta kawo mata shawarar kozata
kaita gurin bokanta.
Dawani kallo Gimbiya tabita, cike da bacin rai tace waiku meyasa bakuda tunani idan zakuyi magana. Ko anfada
maki gidan sarauta gidan hauka ne? To kada kikara
zomun da wannan maganar banzar. Jakadiya cike da
ladabi tace Allah yahuci zuciyarki, kiyi hkr insha Allahu baza'a karaba, tace tashi kije idan kinsamo wata
shawarar wadda tayi dede da tsarina zaki iya dawowa.
Wacece NAFEESA?
Diyace ga malam Audu da Uwani sunkasance talakawa
ne, sosai mal. Audu beda wata sana'a data wuce Caca
haka Uwani muguwar masifaffiyar mata ce, dama cirani
yakawosu kauyensu alakocin Nafeesa tana da shekara
15, Uwani macece mesan kudi sosai hakan yasa take
dorama Nafeesa tallar gyada, duk sanda taje talla acikin tasha dakin wani saurayinta take zuwa yasiya duka
yabiya bukatarshi da ita. Seda tayi ciki har so 3 suna
zubarwa, kuma Uwani bata cemata komai, shikuwa mal.
Audu dama babu ruwanshi dasu.
Gaba daya sun dami yan garin, ana haka wata rana mal.
Audu yayi Caca aka cinyeshi beda abinda ze bada hakan
yasa yaje gidan wani mutum yasato rago, yana fitowa
aka kamashi,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 13