suke samu.
Tarasa cikakken Ilimin addini dana Boko, batasan kowa
acikin yan uwanta ba, batasan yaya mutane suke ba, har
seda Allah yakawota cikin gidan nan. Kalli Umminta,
tasamu kanta acikin hauka harna tsawon shekaru 18.
Agaskiya mutane basa kyautawa.
Nayi alkawarin zan jiyama beauty rayuwa medadi,
wadda batayi irinta abaya ba. Zan sama mata makaranta
me kyau wadda zata samu cikakken ilimin addini dana
boko. Fatana Allah yabani tsawon rai in cika wannan
burin dana dauka. Kamar yanda Sarkin fada yake ikirarin yasa anciremun son sarauta azuciyata, to be cuceni ba.
Kanshi ya cuta, kuma naji dadin hakan, zanyi amfani da
damar dana samu dan insamu lokacin beauty na, nasan
inda inason sarauta bazan iya samun lokacinta ba, bare
incika mata burin dana dauka, dan haka zan rokisu Abba ayi bikinmu akusa dan bana tunanin zama da beauty
akasar nan.
Zantafi da ita wata kasa harseta samu ilimi me kyau
sannan mudawo. Haisam yace gaskiya ka kyauta, sede
kasan da kyar idan su Abba zasu yarda, yanda beauty
bata taso agidan nan ba zasu so ace sun sami lokacin
zama da ita. Areef yace katayani addu,a insamu shawo
kansu.
Washe gari da misalin karfe 10 na safe tawagar Sarkin
Yobe wato mahaifin Zakiyyah da mahaifiyarta suka iso
masarautar BUBAYERO. Dan tun ajiya Sarki Hasheem
yasa Sarki Qaseem yafada masu halin da ake ciki. Ba
karamin tashin hankali suka shiga dajin wannan labari,
ba kamar mahaifiyarta datasan ta dalilin haka zata zama abin tsangwama acikin kishiyoyinta.
Zaune suke afalo, sede Familyn gidan ne, kawai aciki,
tare dasu Mahaifan Zakiyyah, se kuma Waziri, malam da
Jakadiya Safeeya. Agefe guda kuma Zakiyyah ce zaune
atakure guri guda se kuka takeyi.
Mahaifinta ne yayi gyaran murya yafara magana. Hakika
Zakiyyah kinbani mamaki da irin abinda kikayi, saboda
kawai kishi irin naku na mata, yanzu inda Allah yabaku
sa,a kunsamu damar kashe Fulani da shikenan kema
kinza me kisan kai ko?.
Ko agidanku dakika taso acikin kishiyoyi kika samu
mahaifiyarki, kintaba ganin ance ta harari wani acikinsu?
Duk da takasance karama acikinsu amma hakan besa ta
rainasu ba. Agaskiya banji dadin abinda kikayima
kishiyarki ba.
Kuma naji dadin hukuncin da aka yanke maki, wannan
shine dede ga duk mutumin da yace Son zuciya zerika bi
arayuwarshi, koyanzu da kikaga munzo bawai munzo
bane dan ke, munzo ne, kawai dan inbada hakuri agurin
mutanen da kika zalunta, babu ruwana da hukuncin da
aka maki, haka zaki zauna tare da sauran masu laifi har shekaru 5, idan Allah yasa har lokacin ina raye nibazan hanaki zama gida na ba, amma kisani kina dawowa zan
aurar dake ga duk wanda naga dama.
Dayake Sarki Hasheem yace kada wanda yafada masu
abinda suka aikata da Sarkin Fada hakan yasa basusan
maganar ba. Dan Sarki yace yanajin kunyar mahaifinta
shiyasa yahana afada masu abinda tayi, duk da ba
laifinta bane.
Kuka sosai Zakiyyah takeyi ta matso kusa da Babanta
takama. Kafarshi tace dan girman Allah Baba kayafemun,
wlh nikaina nayi nadamar abinda na aikata, babu irin
shawarar da Umma bata bani ba, amma nabiyema
hudubar shedan na aikata abinda yazubar da kimar
masarautarmu, dan Allah kuyafe mani koda mutuwa
zata riskeni acikin kurkutu.
Seda kwalla tacikama mahaifinta ido, damma bakin glass
ne a idonshi, juyawa tayi kusa da Ummanta takifa kanta bisa cinyarta tasaka kuka, tarasa bakin magana, itama
Ummar kuka takeyi sosai, seda suka bama mutanen
falon tausayi.
Mahaifin Zakiyyah ya kalli Sarki Hasheem da Fulani, yace iname neman gafara agurinku, tabbas Zakiyya ta aikata
kuskure dan Allah kuyi hakuri, muzamu koma seku
aiwatar da duk hukuncin da kuka yanke ma kowa, kada
tausayi ko wani kusanci ya hanaku cika umarnin Allah da Manzonsa.
Tashi yayi yana goge kwallar data zubo mashi, yanufi
kofa yana fadin Zakiyyah nayafe maki duniya da lahira,
Allah yasa wannan abu daya faru yazama kaffara agareki, idan munkara haduwa zanyi farin ciki da haka idan
kuma ta Allah takasance se ince Allah yasadamu da
alkhairi, haryanzu kinada lokacin tuba, kada kiga
anyanke maki hukunci ki kasa cigaba da neman gafara
agurin Allah.
Yana kai nan kuka yaci karfinshi yayi waje, fadawanshi
dake bakin kofa suka mara mashi baya. Tashi Umman
Zakiyyah tayi itama zata tafi, Zakiyyah tariketa tana kuka, tace Umma bakice komai ba, dan Allah kimun magana
kada in mutu da fushinki. Jawota tayi ta rungumeta tace.
Nayafe maki Zakiyyah Allah ya yafe maki, insha Allah
zanrika kawo maki ziyara harkifito, idan kuma na mutu,
addu,ar ki nake nema, idan kinrigani mutuwa, addu,a ta
zata sameki har kabarinki. Sakinta tayi tanufi waje
dasauri tana kuka.
Da gudu Zakiyyah tabita, sede kafin ta isa harsun tada
mota sun nufi gate, haka taruga da gudu, tana binsu,
suna fita aka kulle kofar, anan tazube tana kuka, duk
mutanen gidan suna kallonta.
Acikin mota kuwa Umman Zakiyyah se kuka takeyi, haka
Sarki yajawota yana lallashinta. Tace shikenan yanzu
kowa seyasan abinda Zakiyya tayi, shikenan yanzu
banida sauran kima agurin mutane. Sarki yace namaki
alkawarin babu wanda zesan abinda Zakiyyah tayi, sede
idan tadawo gida, zamusan abinda zamu fada. Kwanciya
tayi tana fadin nagode.
Tunda suka fita Sarki Hasheem yake kuka, yakasa
denawa,gaba daya tausayin Zakiyyah da iyayenta
yakamashi, kuka yakeyi kamar karamin yaro, gaba daya
jijiyoyin kanshi sunfito, ganin haka Waziri yayima
Likitansu waya, yazo.
Bayan yagama dubashi yayi mashi wasu allurai kuma aka
bashi magani, ko minti 5 bekara ba yayi bacci. Likita
yace jininshi ya hau sosai, kuma zuciyarshi tana bugawa dasauri, saboda tashin hankalin daya shiga, zeyi bacci na tsawon awa 8 kafin ya farka, idan yatashi ayi kokarin
mantar dashi duk wata damuwa dazata kara dawo
mashi. Sallama yayi masu yafita. Anan suka kulle mashi
dakin suka fita.
Sarki Qaseem yace Malam muje agama abinda za,ayi kozamu dena kallon fuskokin wadancan munafukan.
Waziri ya kalli Areef yace kaja beautyn taka kubar gurin nan banaso taga komai, idan zaka dawo kayi kallo to ita de kabarota acan.
Haisam ya kalli Ayman yace kema wuce mutafi banason
kirika mun kuka, murmushi tayi tace aini babbace kuma
nafi Beauty sanin matsalolin rayuwa. Dan haka kabarni
in kalla, hakan ze karamun imani dajin tsoron aikata
kowane irin zunubi. Murmushi yayi dan yaji dadin
kalamanta.
Gaba daya mutanen masarautar harma da mutanen
waje seda suka cika babban filin da ake wasan dokuna
na Masarautar BUBAYERO, dan kowa yanason yaga
yanda za,a aiwatar da wannan hukunci.
Hada manyan malaman masarautar suma sun halacci
gurin, haka aka fito da masu laifi kowa yasaka kayan yari ajikinshi, gaba daya kunyar mutanen gurin sukeji, gani
sukeyi kamar duka mutanen duniya ne, aka tara agurin
ganin irin yawan da mutanen suke dashi.
Kowa neman boyewa yakeyi bayan dan uwanshi,
Zakiyyah duk tafi kowa jin kunyar jama'an gurin, jitake kamar kasa ta tsage tashige. Duk abinda takeyi Malam
yana kallonta, besan lokacin da kwalla tazubo mashi ba.
Bawai tausayinta yasa shi kuka ba, kawai daya kalli yanda take boyewa dan kawai taga yan tsirarrun mutane,
wadan da ko rabin garin Gombe basu kai ba, amma
shine take jima kunya. To inda ranar lahira ce Allah ya tadata agaban biliyoyin mutane yazataji? Wannan
tunanin shine abinda yasaka Malam kuka.
Bayan sun tsaya agurin da aka tanadar masu, kowa
yasamu nutsuwa, sannan Malam yahau kan wani guri
medan tudu shida Sarki Qaseem da limamin masallacin
masarautar, tayanda kowa ze iya ganinsu.
Seda Malam yasa liman yabude masu taron da addu'a
sannan yafara magana. Har yanzu hawaye basu dena
fitowa daga idonshi ba, musamman daya hau sama yaga
mutane sun nutsu gefe guda kuma ga masu laifi suma
sun tsaya suna kuka.
Kyalle yasa ya goge idonshi sannan yafara magana.
Alhamdulillahi, kamar yanda kowa yasan dalilin taruwar
mu agurin nan, kuma naji dadi matuka da Allah yasa
naga Mata da Maza, Yara da Tsofaffi, sun halacci gurin
nan.
Saboda kowa ze kalli yanda kowa ze amshi hukuncinsa.
Nasan yawancin mutanen gurin nan masu hankali,
wannan taron kadai ya isa ya tunatar da kowa tashin
kiyama, da kuma tsayuwar hisabi.
Da farko inaso indanyi amfani da wannan dama inyima
jama'a tunatarwa akan rayuwar duniya data lahira,
hakika wannan abu da mutanen gidan nan suka aikata
yasa mutane dayawa zasu koyi darasi.
Zanyi magana akan abu 2.
AMANA, da ZINA.
Wa iyazubillah. Hakika mutane dayawa sun shagala
azamanin nan gurin Cin AMANA. Basajin kunyar ha'intar
makusantansu. Dama Manzon Allah (s.a.w), yace idan
karshen duniya yazo amana zatayi karanci, bawa ze iya
cin amanar Uban gidanshi, kamar yanda Da ze iya cin
amanar mahaifanshi.
Ayanzu halin damuke ciki kenan mutane basu dauki cin
amana abakin komai ba.
(1) Kamar yanda yazo acikin hadisin Manzon Allah tsira
da amincin Allah su tabbata agareshi. Inda Abdullahi bn Abbas (RA) yace. Lallai kyawawan aiyuka suna sanya
mutum hasken fuska da na zuciya da yalwar arziki da
karfin jiki da soyayya daga bayin Allah.
Kamar yanda sabon Allah yake sa fuska da zuciya duhu
da raunin jiki da tawayan arziki da kiyayya daga mutane.
Rawahul Muslim.
(2). Allah ta'ala yana cewa. Kuma wadanda sukayi kokari ga nemar yardarmu. Lallai muna shiryar dasu ga
hanyoyinmu, kuma lallai tabbas Allah yana tare da masu
kyautatawa.
(Suratul Ankabut, Aya ta 69).
(3) Allah ta'ala yana cewa. Babu wata musiba dazata
sameku, face sai sakamakon abinda hannuwanku suka
aikata.
(Suratul Al shuura Aya ta 30).
Sadakallahul Azim.
Kai jama,a, ina zamu kai wannan girman zunubi damuke
daukar ma kanmu? Hakika Allah baya yafe laifin wani
akan wani. Baka tunanin idan kaci amanar wani Allah
yadauki ranshi ko ranka batare daka nemi yafiyarshi ba?
Jama'a yakamata mutuba zuwa ga Allah, wlh duniyar
nan tafiya takeyi.
Kada muyarda wasu subamu amana mu ci masu, ayanzu
wanda ka yarda dashi shine wanda yake cutarka. Allah
yasa mufi karfin zuciyarmu. Kowa da anyi magana seya
ce Shedan. Kada kumanta shifa Shedan seyasamu kofar
shiga jikin dan Adam yake iya shiga har yasamu damar
yimasa mummunar huduba.
Idan har mukayi riko da gaskiya da Amana, muka koma
ga Allah, tabbas ze cecemu daga sharrin shaidan. Idan
baku manta ba, duk yanda shedan yakai ga hallakar da
bayin Allah baze taba samun nasara agurin wadan da
Allah ya tsare ba. Ba kuma tsayawa zakayi harse kasamu
tabbacin lallai Allah ya tsareka sannan zaka rika addu,a ba.
Manzon Allah dakanshi yana neman tsari daga sharrin
shaidan, wanda kowa yasani yafi karfin shedan, Allah
yariga da ya haramta ma shedan kusantar manzonsa.
Amma duk da haka Annabi be kwanta ba yace Allah
yatsa reshi baze nemi wani tsari daga gareshi ba.
To kai waye dabazaka nemi tsari daga sharrin shaidan ba? Yakamata kowa yadage da yaki da zuciyarshi, ita
kadaice hanyar dazata tseratar damu. Allah yasa
mudace.
Magana ta biyu akan ZINA. Innalillahi Wa inna
ilaihirraji'un. Wannan abu itace abinda yake damun
mutane dayawa, babu yara, ba manya, marasa aure, har
masu aure. ZINA wata musiba ce acikin al'umma.
Allah ya haramta zina, shiyasa ma yace kada ku
kusanceta. ZINA tana tarwatsa duk wani mutunci na dan
Adama, tana sa talauci. Shiyasa Allah yakawo hukuncin
ZINA acikin alkur'ani me girma.
Dan haka ayau kowa zega irin hukuncin daya kamata
ayima duk wanda ya aikata ZINA. Allah yashiryar damu
da iyalanmu, baki daya. Kafin afara akwai jawabin da
Sarki zeyi maku.
Komawa baya Malam yayi yana share kwallan idonshi,
Jama,a da dama agurin seda suka zubar da hawaye akan
jawabin da Malam yayi. Sarki Qaseem yafara magana,
shima daka kalli idonshi zaka gane kuka yayi.
Alhamdulillahi, kamar yanda Malam yayi mana jawabi,
nasan mutane dayawa sun kara sanin me ake ciki
arayuwa. Kamar yanda zamu fara aiwatar da wannan
hukunci, ina me fada da babbar murya, daga yau, duk
wanda aka kara kamawa acikin kasata, dumu dumu da
laifin aikata ZINA , kowani laifi, tabbas se hukunci yahau kanshi.
Ko wanene, kuma ko wacece, kowane irin matsayi
mutum yake dashi, zamu buga tambari wannan doka
zata fara ayau. Kuma naji dadi sosai da dokar zata fara daga cikin Masarautar mu, acikinta ma hada masu
sarauta aciki. Karewa ma, hada matan Sarki Hasheem
guda 2. Tunda har muka iya aiwatar da hukunci akansu.
Babu wanda za,a kara daga ma kafa idan ya aikata zina,
watakila hakan yakawo mana sauki acikin kasarmu. Daga
karshe ina yima Allah godiya daya nuna mana wannan
rana. Sauka yayi idanunshi suna fitar da kwalla.
Anan Waziri yasa aka cire Zakiyya da Jakadiya Karima,
dasu Mati da Lado gefe guda, kuma aka fadama mutane
irin hukuncin da aka yanke masu. Medaki se Kuka takeyi.
Tanufo gurin su Gimbiya Suhailat da Fulani, wadanda
suma kukan sukeyi.
Har kasa ta duka sede takasa yin magana saboda kukan
datakeyi, hannuwanta biyu kawai tahada alamun neman
yafiya tacigaba da kuka. Kamota sukayi suka rungumeta
suna kuka.
Seda suka saka kowa kuka agurin, wasu mata sukazo
suka kamata, seda tayi addu,a sannan aka sata cikin
ramin aka rufe jikinta akabar fuskarta. Tunda su Fulani sukaga haka suka bar gurin suna kuka, mata dayawa
seda suka bar gurin, hatta da Sarki Qaseem fada yakoma
yana kuka, kasa tsayawa yayi agurin.
Bayan anyi mata addu,a akasa yara suka fara jifarta, ahaka harseda ta mut
.
u😭. Wa iyazubillah. Allah ka tsaremu Wa iyazubillah. Allah ka tsaremu daga aikata ZINA. Amin.
Zakiyyah agurin tazube asume saboda tsabar kaduwa,
Jakadiya kam kuka kawai takeyi. Haka wasu suka dauketa
aka shiga da ita ciki.
Boka da Sarkin Fada aka kira. Idanun Sarkin Fada sunyi
jajur saboda kuka, haka shima yaje gurin Waziri, da
Sauran mutane, yana kuka yana neman yafiyarsu. Bayan
anyi masu addu'a aka dorasu saman wani table, aka
samasu bakar hula afuskarsu sannan aka ture su daga
kan table din. Haka sukayita lilo har suka mut
.
u😭. Wa iyazubillah. Allah ka tsaremu Sannan
aka tasa keyar sauran masu laifi zuwa kurkutu, alokacin Zakiyyah ta farfado itama aka hada da ita.
Gaba daya mutanen dake gurin babu wanda bezubar da
hawaye ba, jikin kowa yayi sanyi, tsoro yashiga
zukatansu. Haka aka taru akayi masu sallah aka wuce
dasu makabarta.
INNALILLAHI WA INNAILAIHIRRAJI'UN😭. Wa iyazubillah. Allah ka tsaremu
. A
😭. Wa iyazubillah. Allah ka tsaremu
llah kasa mufi
karfin zuciyarmu. Bazan iya cigaba. Da typing ba se zuwa gobe idan Allah ya kaimu. Abinda nafada da kuskure
Allah yayafe mani.
Nagode da kulawarku, sekunjini anext page insha
Allah.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 115⚜120
LAST PAGE
Washe gari Sarki Hasheem yasamu karfin jikinshi, da misalin karfe 10, gaba dayansu suka taru a babban falo, bayan anbude taro da addu,a anan aka fada ma Sarki
Hasheem duk abinda yafaru jiya, sosai ya tausaya ma
Medaki.
Malam yace to Alhamdulillahi, muna godiya ga Allah
daya nuna mana wannan rana, inafatan wannan abu da
yafaru agidan nan ze zame ma kowa darasi, abinda
yarage mana shine mucigaba da neman tsari daga
sharrin masu sharri, kuma kowa yadage da addu,a, kada
kuyi la'akari dacewar wani yana maku addu'a.
Idan har zaka iya saka wani yamaka addu'a to kai meyasa bazaka iya rage wani abu daga cikin darenka
katashi karoki mahaliccinka ba? Allah da kanshi yake
fada akwai wani lokaci acikin dare wanda yake sakkowa
daga sama yazo ya karbi addu'ar bayin da sukayi
awannan lokacin. Da aka tambayi manzon Allah wane
lokacine wannan? Yace daga karfe hudu zuwa asuba.
Duk wanda yatashi awannan lokacin yayi sallah tabbas
Allah ze karbi addua'arsa. Ina me maku nasiha da ku
daure kurage jindadin duniya kusami lokacin ganawa da
ubangijinku acikin dare, ibadar rana kadai bazata isheka ba, saboda duk yanda kaso kebewa da rana kace zakayi
ibada ta tsawon minti 30 kadai, dole se wani abu yashigo maka katashi.
Amma idan akace maka da dare ne, kana da lokaci me
yawa. Kuduba manzon Allah, shifa yariga dayasan anyi
mashi albishir da aljanna, amma duk da haka yakan
tashi cikin dare yayi ta ibada. To kai waye dabazakayi
koyi dashi ba? Wanda aduk cikinmu babu wanda yakeda
tabbacin shiga aljanna. Dan manzon Allah yace akwai
wadan da zasu dade suna aikata aikin alkhairi, amma
karshen wuta ce makomarsu. Kamar yanda wasu zasu
dade suna aikata zunubi amma aljannace mako marsu.
Dan haka aduk lokacin da kukaga wasu suna aikata
alfasha, kada kabata lokacinka gurin aibantasu, kai zaka cinye ladar daka tarama kanka, amai makon haka kayi
masu wa'azi idan har kaga zasu dauka, idan kuma abin
yafi karfinka to kabisu da addu'a.
Manzon Allah yace aduk lokacin da wani bawa ze
rokama wani dan uwanshi abu agurin Allah, batare da
sanin wancan ba. Mala'iku zasuyi rika yimashi addu'ar
duk abinda yarokama wancan shima.
Daga karshe, ina kara maku nasiha dakuji tsoron Allah,
kuma kucire son zuciya a zukatanku, Allah ze temakeku
aduk inda kuke, kuma kuzauna da kowa da zuciya daya,
idan shi bahaka yake zaune daku ba, wata rana Allah
zetonashi kowa yaganshi, kamar yanda yayi ma wadan
da suka wuce. Ina fatan kowa zerike duk abinda nafada
maku.
Gyaran murya Sarki Qaseem yayi yace, hakika munji
dadin irin fadakarwar da malam kayi mana, akwai
abubuwa da dama daka tunatar damu, wadanda
munshagala dasu abaya, hakika mutum yatashi yaroki
Allah da kanshi shine abinda yafi, domin idan kadogara
da wani, wata rana Allah yana uya daukeshi, shiyasa
akace daka bama mutum kudi yasayi abinci. Gara ka
bashi gona yayi noma, haka kuma daka bashi kudi gara
ka sakashi makaranta.
Wata rana seya temaki kanshi da al'umma. Mungode
kwarai da kulawarka agaremu, Allah yabar zumunci,
kuma insha Allahu zamu kawo gyara sosai amasarautar
nan, ta yanda zamu temaki sauran bayin dasuke cikin
masarautar nan, suma susami ilimin addini kada rayuwarsu takare abauta.
Malam yace idan kukayi haka tabbas zaku kawo cigaba a
masarautarku, kuma yin hakan zesa wannan masarauta
ta daukaka, harma wasu masarautun suyi koyi daku. Ni
kuma nayi alkawarin turo manyan yarana suzo suma
subada tasu gudunmuwar, kaga ahakane, suma bayi
zasu gane cewa suma mutanene, kamar kowa. Ina rokon
Allah ya amshi wannan niya taku, kuma yasama abun
albarka. Ina ganin ayau zanzo in koma.
Waziri yace mungode sosai Malam, Allah yasaka da
alkahairi, kuma ina ganin kafin kawuce, zamu zabeka
amatsayin wanda ze daura mana sabon Sarkin Fada.
Malam yayi murmushi yace, to inaganin yakamata
abama wanda yakamata abama sarautar tun farko, kafin
aci amanarshi. Koba komai, zeji dadin hakan, kuma
sauran mutane zasu kara yarda dacewa duk zakaran da
Allah yanufa da cara, to ko ana muzuru ana shaho
seyayi, yasha wahala ta dalilin sarauta, ya kwashe
shekaru dayawa acikin kurkutu. Tabbas babu wanda ya
dace da wannan sarauta se shi.
Kallon Sarki Hasheem yayi yace, inaso inji wane suna
kasama diyar tawa, kafin inkoma? Murmushi yayi yakara
kallon Fulani sannan yace agaskiya tunkafin a haifeta
dama nazaba mata suna, badan komai nazaba mata
sunan ba, sedan inyi godiya ga Allah abisa kyautar da
yayi mani nasamun karuwa.
AMATULLAHI, shine sunan dana zaba mata. Lumshe ido
Areef yayi jin yanda sunan ya burgeshi. Malam yace
Alhamdulillahi wannan suna yayi dadi, AMINTATTAR
ALLAH kenan, to Allah yasa albarka acikin sunanki da
rayuwarki gaba daya. Kowa yace amin.
Waziri yace Malam inaganin zaka kara dawowa nan kusa
domin kadaura mana aure amasarautar nan, Murmushi
yayi yace lallai kam nima naga alama, dan tunkafin inzo nasan da wannan labari, zuwana kuma yakara tabbatar
mani da hakan, dan Yarima yafi kowa kaffa kaffa da
diyar tawa, yanda kasan ance za'a kwace mashi ita.
Dariya suka saka gaba daya. Anan Baban Fulani shima
yayima Malam godiya sannan yakara yima Baba na
Darazo godiya.
Sarki Qaseem yace ai basu kadai ba, gawasu masoyan
nan agefe, dan haka tare za,a yi muhuta gaba daya. Kowa dariya yayi. Malam yace to Allah ya nuna mana, amma
banaso asaka danisa, gara tazauna da mijinta, hakan ze
sa tasamu kwanciyar hankali. Anan aka rufe taro da
addu'a.
Kwana 3 aka dauka a masarauatar ana zaman jimami,
jikin Sarki Hasheem yayi sauki, sede haryanzu yana cikin damuwa, kuma befara takawa da kanshi ba, dole seda
sanda, hakan yasa Sarki Qaseem da Waziri suka nemi
shawarar likita, shine yace idan ze yarda afitar dashi
waje.
Zasuyi mashi wani gashi, insha Allah ze dawo dede.
Bayan sun sameshi da maganar babu musu ya amince,
hakan yasa Waziri yace dashi za,a tafi. Sarki Hasheem
yace amma da Fulani zamu tafi ko? Murmushi sukayi
sukace ai badamuwa.
Lokacin da Sarki Qaseem yasamu Gimbiya Suhailat da
maganar cewa tayi suyi hakuri abarta akwai abinda
zatayi mata kafin sudawo angma. Yace a,a kinsan Yaya
baze yarda ba, kawai kibashi matar shi. Da to kawai ta
amsa mashi.
Amma azuciyarta tayi alkawarin bazata bari sutafi tare
ba, dan Fulani tana bukatar gyara sosai, shekaru 18
acikin hauka, kuma har haihuwa tayi. Dole ma tayi duk
yanda zatayi tahana atafi da ita.
Zaune suke afalo ana tashirin tafiyarsu, dan anjima
kadan zasu tafi,Fulani datake zaune agefen Sarki, tayi
saurin rike cikinta. Dasauri Gimbiya Suhailat tace lafiya de Fulani?
Nana hankalin kowa yadawo kanta, Sarki Hasheem yace
adauketa muje asibiti mana. Gimbiya tace a,a inajin
baciwon asibiti bane,birin ciwonmu ne, na mata bari
muje cikin gida. Sarki Hasheem yace ina ganin za,a daga tafiyar nan kafin tasamu lafiya.
Waziri yace a'a Memartaba, kada wannan yadameka,
tafiyarmu bazata wuce kwana 10 ba, inaganin kayi
hakuri tunda har angama komai kuma agobe za,a fara
gashin nan, kaga likitan yace akwai inda zeje, saboda
kaine yadaga tafiyar.
Kayi hakuri muje domin neman lafiyarka, nasan ayanzu
kanajin babu dadi kowa yana hidimarshi amma kana
zaune, guri guda, idan zajayi tafi seda sanda. Sarki
Qaseem ya matso kusa dashi yace dan Allah Yaya kada
kaki yarda ayi tafiyar nan, wlh Allah kadai yasan halin damuke ciki akan rashin lafiyarka. Shiru yayi, hawaye
suna zuba daga idonshi.
Hannunshi Sarki Hasheem yakama shima idanunshi
sunyi ja, yace karka damu dan uwa na, acigaba da
shiri,Allah yasa ayi asa'a. Murmushin jindadi yayi
yarungume Yayanshi yace nagode Yaya. Sarki Hasheem
yakalli Beauty yace zo Amatullah mu gaisa mana.
Murmushi tayi ta tashi tanufi gurinshi tana zuwa tazauna kusa dashi ta dora kanta saman kafarshi. Hannu yasa
yashafi fuskarta tace yauwa Amatullahi, Allah yabaki
lafiya kema kirika magana kamar kowa. Areef yace
Amma Baffa tayi magana so daya a asibiti.
Waziri yace insha Allahu wata rana zata yi magana, dan
likita yace matsalarta ne sauki ce, kuma base an kaita
asibiti ba, zata iya yin magana akowane,lokaci, yace idan har taga wani abu daya tsora tata bakinta ze iya budewa.
Sarki Hasheem yace insha Allahu zata samu lafiya. Kuma
da mun dawo za,ayi maganar bikunku, Yarima seka
fadama abokinka dan ahada tare, ko Ayman? Murmushi tayi ta tashi tafita.
Lokaci yana cika suka fito domin tafiya, seda aka kai
Sarki Hasheem gurin Fulani sukayi Sallama, sannan suka
nufi air pot. Suna zuwa aka fara kiran sunaye, haka suka rungume juna shida Kaninshi, har kua seda sukayi. Yana
kallonsu har jirginsu yadaga sannan suka dawo.
Dariya Gimbiya Suhailat da jakadiya Safeeya sukayi,
Gimbiya tace ai nadauka Fulani bazakiyi yanda nace
maki, ba, dan kina tausayin mijinki. Fulani tayi
murmushi tace, duk yanda nake tausayinshi ai gara
inzauna indawo da martabata ni kaina wani lokacin kyan
kyamin kaina nakeji, kiduba fa kigani duk wata kazanta
damuke fitarwa haka zanyita ingama babu wani wanka.
Kai gaskiya mutanen nan sun cutar dani.
Jakadiya Safeeya tace wai ahaka ma kinsamu bakar da
ba, kuma kinga acikin kwana goma zaki samu gyara
sosai, wanda Sarki zeyi farin ciki da haka. Gimbiya tace ai wannan gyaran na musamman zakisha, suma Yarana
nasu nadabanne.
Kallon Jakadiya Safeeya tayi tace akwai wani abu danake so inhada, amma anjima idan hubby yadawo zamuyi
maganar, kema yakamata, ai ko? Jakadiya tace bangane
ba? Murmushi Gimbiya tayi tace a'a bakomai dama gani
nayi Waziri tunda matarshi ta mutu be kara aure ba,
kuma dama diyarshi daya sunyi mata aure. Shine naga
kema mijinki yarasu ai.
Dariya Fulani tayi tace kai amma wlh Aunty kin iya
hangen nesa. Tashi Jakadiya tayi tana murmushi,
Gimbiya tace, ina kuma zakije? Fita tayi bata cemata
komai ba. Gimbiya tace Allah da gaske nakeyi, kuma
insha Allahu wannan abu seya tabbata, zansa Hubby
yafadama Malam, kinga se ayi tare dana su Amatu.
Fulani tace Allah yasa.
Zaune suke acikin lambu, beauty Amatullah tana zaune
agefen Areef yana koyamata karatu, su Haisam suma
suna gefe guda suna firarsu. Areef ya kalli Haisam yace wai abokina ya kukayi da Dady akan maganar Ayman?.
Murmushi yayi yace yafi kowa mafarin ciki shida Momy
dasukaji maganar, yace idan Baffa yadawo zasuzo. Areef
yace ai gara azo a aurar damu kowama yahuta ko Beauty
na? Kai tadaga mashi tana murmshi. Haisam yace Beauty
bahaka zakice ba, a,a zakice.
Hararshi Areef yayi yace todan bukulu ai seka hanata,
kuma wlh wannan sunan yafita abakinka, tunda de
ansamata suna kawai ka kirata da Amatullahin ta.
Haisam yace bazan kiraba, ni nariga dana saba.
Murmushi Areef yayi yace shikenan, nina zanrika kuran
Ayman da Angel. Apple din dayake kusa da Haisam
yadauka ya jefeshi dashi, dasauri ya cabeshi yana dariya, Haisam yace wlh baka isa ba. Areef yace tokaima kadena
fada mata beauty. Haisam yace nayarda, dannaga alama
nizakafi kwara.
Dariya suka saka Areef yace dade yafi maka, amma ni
inkirata. Beauty kaima haka, ai bazeyuba. Haisam yace
towai kai yamaganar fitarku waje bayan aure? Areef yace wlh har yanzu banyi maganar dasu Abba ba, amma yau
zanje insamesu. Idan har sukaki zan hadasu da Malam.
Haisam yace insha Allah ma zasu amince, duk da nima
bazanso kamun nisa ba, amma saboda cigaban Amatu
kawai zan hakura, nima inaso inga tadawo kamar kowa.
Gimbiya Suhailat tana kwance ajikin Sarki Qaseem suna
fira, tace Hubby, dama wata shawara ce, nace bara
infada maka kafinsu Yaya su dawo se afada masu aji
mezasu ce. Kara yawota yayi yace fada inajinki. Anan
tafada mashi abinda takeso.
Murmushi yayi yace wlh kamar kinshiga zuciyata, na
dade ina wannan tunanin, kawai ciwon Yaya ne,
yahanani fada amma tabbas idan suka dawo zansamu
Waziri da Yaya da maganar. Wannan abu ne me kyau.
Kema Allah yabiyaki da kika kawo wannan shawarar.
Sallamar Areef ce ta katsesu, abakin kofa ya tsaya, dan dama al'adarshi ce duk inda yaje baya shiga se anbashi
izini kida gidansu ne. Murmushi Sarki yayi yace Allah yayi maka albarka Yarima, hakika ina farin ciki da irin
halayenka da kuma tarbiyarka, ace mutum yaje kasar
waje yayi karatu amma duk da haka tarbiyarshi bata
lalace ba, asalima karuwa tayi. Babu abinda zanma Alkah se godiya, domin nasani shine ya tsare bawansa.
Bayan sun gyara zamansu ya amsa Sallamar yace shigo
Yarima, shigowa yayi yazauna kusa da Abbanshi tare da
dora kanshi saman kafarshi yace sannunku da hutawa
Abba. Shafa kanshi Gimbiya tayi tace yauwa sannu
Yarima. Sarki yace zanga ranar dazaka girma Areef, ace
haryanzu kana hawa cinya.
Dariya yayi yace ai babu rana Abba, yace akwai mana,
nan da wata daya kam ai zaka zama megida. Kafin kaima
kasamu naka dan, kaga saka barmashi ko. Gimbiya tace
ai anan zasu zauna ko? Abba yace emana, ai bama son
muyi nisa da juna, zamansu cikin masarautar nan zefi.
Tashi Areef yayi yana sosa kai yace Abba dama wata
alfarma nazo nema, yace fadi duk wata alfarmarka, ni
kuma zanyi maka. Anan yafada masu abinda yakeso.
Shiru sukayi, yace dan Allah Abba.
Sarki yace bawai naki bane, ina duba yanda Yaya zeji,
kasan yanada bukatar ganin Amatu akusa dashi, amma
se
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 13