ba. Kamar yanda nasamu farin
cikin raina banajin zan iya kara aure, shiyasa akace
auren soyayya yafi komai dadi.
Murmushi tayi ta kara shigewa jikinshi tace nikaina ina farin ciki da auren yaya, inajin Rayhana kamar kanwata, insha Allahu ajikinta zamu sami babban rabo.
Rungumeta yayi yace inafatan haka, inaso inga jinin Yaya agidan nan shine babban farin cikina. Fatana Allah
yadoramu akan duk wasu makiyanmu, dannasan
munadasu dayawa acikin gidannan, sede Allah ne kawai
yasansu. Gimbiya tace babu abinda zasuyi mana domin
munrigasu munce Allah. Jawota yayi yace yakamata fa
kiyima Areef kanwa dan kinsan ina son mace. Murmushi
tayi tace nima haka ina addu,ar Allah yabani mace, yace to tashi muje daki ai ba,a samun mace abaki. Dariya tayi yadagata suka nufi daki.
Afalon Medaki Jakadiya tasamu Sarkin Fada suna zaune
yanashan kayan marmari, medaki tana kusa dashi har
jikinsu yana gogar na juna, kofar da aka turoce tasasu
saurin matasawa, dan Medaki takori duk bayin.
Murmushin jin dadi jakadiya tayi ganinsu ahaka, aranta
tace kema kinshigo hannu.
Medaki duk kunya takamata, Jakadiya tace rankiyadade
ashe mutumin yana nan? Shiru tayi, Jakadiya tace uhm
kisaki jikinki kinganni nan nimafa haryanzu ina dan taba duniyancin nan ai mace fitila ce bata aiki dole seda batir.
Dariya Sarkin Fada yayi yace da gaskiyarki Jakadiya,
ainafada mata nidake da ita munzama aminan juna,
akwai amana atsakaninmu, dan haka bakinmu adinke
yake muci tare mu tashi tare babu wanda zeji kanmu.
Medaki tace amma gaskiya nagode, tunda nasan yanzu
munzama saniyar ware aidole musami abokin fira. Anan Jakadiya tafada masu rashin mutuncin da Gimbiya
Zakiyya tayi mata. Sarkin fada yace kirabu da ita, wlh
kotana so ko bata so seta aikata babban laifin daze
jamata kisa ko dauri acikin gidan nan, ita da anyi
magana seta nuna mana sarauta da mulki, zamu gwada
mata bakomai sarauta take bama mutum ba. Kibarta
mucigaba da binta wata rana zata dawo garemu, kuma
kada ki kara zuwa gurinta, da kanta zata nemeki. Ai ba ita takawoki gidanba, karewa ma kinfita matsayi agurin
Sarki, kawai agurin shinfida zata gwada maki. Dariya
suka sa gaba daya.
Haka rayuwa tacigaba da tafiya, babu ruwan wani da
wani, Jakadiya tadena zuwa gurin gimbiya Zakiyya, ko
aikenta sarki yayi dataje zata fadama Babbar Baiwarta
tajuyowarta. Sunhade kai da Medaki, Sarkin fada tuni
yasamu shiga agurinta, wata rana har kwana yakeyi
agurinta, kasancewarshi babban mutum me karfi hakan
yasa Medaki takejin dadin mu,amala dashi. Baruwanta
da daga hankalinta, sede idan ranar girkinta yayi taje tayi kwana 2 tadawo.
Sarki yana kokarin yin adalci atsakaninsu, sede Fulani
daban take agurinshi, duk ranar girkinta kowa seyasan
ita keda girki dan ko fada baya son zama sosai. Gimbiya Zakiyya kuwa kissar datake mashi ce take dan kara
sanyata aranshi. Medaki kuwa hakanan yake zama da ita
dan bewani gamsuwa da ita, shiyasa wani lokacin idan
kwananta ne ba kullum yake kusantar taba.
Bayan shekara daya, aka saka Areef makaranta dan
alokacin yana da shekara 3, har lokacin Fulani bata samu ciki ba, duk da Sarki yafara damuwa amma sbd son
dayake mata, ko maganar betaba yimata ba, akullum
yana addu,ar idan har haihuwa alkhairi ce agareshi to
Allah yabashi me amfani, idan kuma babu alkhairi Allah
yasa mashi dangana.
Jakadiya tazo shiga part din Gimbiya suhailata taji suna maganar cikinta har yakai wata 5. Bakaramin tashin
hankali tashiga ba, cikin sauri tajuya tanufi gurin Medaki da Sarkin fada. Suma hankalinsu yatashi dajin labarin,
anan Sarkin Fada yace yakike ganin za,ayi? Jakadiya tana huci, tace na rantse da Allah baza ahaifi cikin nan agidan nan ba, ai nafada babu wanda zekara haihuwa agidan
nan, dan haka gobe zanyi tafiya, kafin indawo ina me
tabbatar maku cikin zezube. Dariya sukayi Medaki tace
kinyi dede Jakadiya, Allah yabada sa,a. Bari indauko maki tawa gudunmuwar.
Safeeya ce tafito da gudu tana neman dauki, karo sukaci da Waziri zeje fada. Lafiya Safeeya naganki haka? Wlh
Gimbiyace bata lafiya se zubar da jini takeyi, naga
alamar ma kamar barine tayi, cikin sauri yadaga waya
yakira Qaseem, sannan ya aika wani bafade yakira
driver.
Likitane, yafito daga wani daki yace su sameshi office.
Bayan sunzauna yakalli Sarki da sauran mutanen, sannan
yace Rankaidade agaskiya sede kuyi hakuri domin
abinda ke cikinta yafita. Sede munyi bincike bamu gano
dalilin fitar saba, sede muce daga Allah ne. Qaseem yace likita yajikin nata? Yace dasauki babu wata damuwa
anjima kadan za,a sallameta. Sarki yace innalillahi wa
inna illaihirraji,un. Waziri yace se hakuri, Allah yamaida mafi alkhairi.
Bayan kwana 2 jikin Gimbiya yayi sauki sosai, sede
haryanzu tanajin zafin barin datayi, kallon Safeeya tayi tace wlh ina mamakin abinda nagani acikin baccina,
wanda shine yayi sanadiyar yin bari na. Kinsan jiya nace maki nagaji bacci kawai nakeji, harkikacemun inje inyi
alwala kafin inkwanta nace maki nide nagaji zanyi addu,a kawai, to wlh ina kwanciya bacci yadaukeni, banyi
addu,ar ba, kawai cikin bacci naga wasu irin mugayen
halittu marassa kyan gani masu ban tsoro sunbiyoni ina
gudu kawai nafadi, suka zagayeni, daya gada cikinsu
yataka cikina, shine kikaji wannan karar daniyi kawai
senatashi naga jini yana zuba.
Safeeya tace tabbas Gimbiya rashin addu,ar dabakiyi
bane yasa wannan al,amari yafaru dake, kinsan addu,a
tana da matukar mahimmanci arayuwa, kuma alwala
kafin mutum yakwanta bacci tana da matukar tasiri
ajikinshi. Kodazu munyi magana da waziri shima seda
yayi mamakin al,amarin. Kuma yafadama malam, yace
ajirashi nan da kwna 2. Gimbiya tace koma menene
Allah yamana tsari dashi.
Bayan kwana 2 Fulani da Sarki sukaje asibiti Waziri da
Qaseem ne suka rakashi, babu wnda yasan inda zasuje
sesu Gimbiya Suhailat. Bayan likita yasa anyi mata test aka kawo result, cike da farin ciki yasanar dasu abinda.
Yakejikin takardar. Kasa Sarki yasauka yayi sujada yana me godema Allah da kyautar da yayi mashi, kowa dakin
seda yaji tausayin sarki ganin kwalla tana fita daga
idonshi, duk sunyi farin ciki da wannan labari, itako
Fulani kasa dago kanta tayi.
Qaseem yace likita wata nawa ne? Wata 3 ne, Hamadala
Sarki yayi yakara yima Allah godiya. Waziri yace lallai likita anjima zakaga sakon tukuicin wannan albishir me
tsada. Sede munaso kada kabari kowa yaji wannan
maganar. Likita yace insha Allahu.
Suna fita Qaseem yakira malam yayi mashi albishir,
shima yayi farin ciki, kuma yace kada subari kowa yasan da cikin, dan abinda yagani akan barin da Gimbiya
Sauhailat tayi yabashi tsoro, dan haka akillaceta kada
tarika fita har wani yaga cikin, yace ze rika aiko da
rubutun dazata rika sha harta haihu insha Allahu, Allah zekare cikinta. Godiya sosai yayi mashi sukayi sallama.
Bayan sunkoma gida yafada masu abinda Malam yace,
Waziri yace wannan haka yake, nima nayi tunanin haka,
kunsan babu wanda yasan zuciyar mutane, abar maganar anan, kuma mucigaba da addu,a Allah
yasauketa lafiya.
Nikam nace amin Waziri.
Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 55⚜60
Haka Suka cigaba da renon cikin Fulani, babu wanda
yasan da cikin agidan, duk wata hidima Safeeya ce take
zuwa tana mata, Waziri da kanshi yahana kowace baiwa
shiga dakin Fulani, sede komenene akwai wani
amintaccen bawan da waziri ya yarda dashi, shi suke
bama sakon yashiga yafada mata, matakin tsaro sosai
Waziri da Qaseem suka dauka akan cikin Fulani, Sarki
har mamakin kulawar dasuke bama Fulani yakeyi, hakan
yasa yakara basu babban matsayi aranshi, yanajin Waziri tamkar yayansu.
Gimbiya Zakiyya abun duniya yafara isarta, gashi tayi
fada da Jakadiya, tanaso takirata amma girman kanta
yahanata. Ganin itace meso yasa ta aiki wata baiwarta
takira mata ita, alokacin suna part din Medaki ita da
Sarkin Fada. Dariya Jakadiya tayi tace ai nafada maku
wlh babu wanda zekara samun da acikin gidan nan,
kuma banida haufin Boka ya iya aiki. Sarkin Fada yace ai naga alama, tunda kikayi nasarar zubar da cikin Gimbiya, gsky na jinjina maki.
Karar buga kofa sukaji, dasauri Sarkin fada yamike
yashige daki, Jakadiyace ta tashi tabude, gaishe da ita baiwar tayi sannan tafada mata sakon Gimbiya Zakiyya.
Murmushi Jakadiya tayi tace kice inazuwa. Komawa tayi
tace seka fito matsoraci, dariya medaki tayi tace ai da gaskiyarshi, duk munfiki tsoro kekam kinci dubu, tace
wlh kuwa.
Abinda baiwar tafada mata take fada masu, dariya Sarkin fada yayi yace ai gara ki koma, Medaki tace nimade bana shiga gurinta sosai, amma tunda zaki koma nima zan
koma, Jakadiya tace bara naje inji dame tadawo.
Zaune take afalo bayan sungama gaisawa Gimbiya takara
kallon Jakadiya tana yamutsa fuska, tace wai naji ance
Gimbiya suhailat tayi bari? Murmushi Jakadiya tayi tace haka ne, ranki yadade. Gimbiya tace ammade nasan
akwai abinda yafaru ko? Dariya Jakadiya tayi batace
komai ba, dan bata manta da irin zagin data sha ba.
Gimbiya tace bani labari idan ko har naji dadinshi kinada babbar kyauta.
Jakadiya nan tasaki baki tabata labarin abinda yafaru,
tace wlh kuwa Gimbiya ai nafada maki tunda de baki
haihu agidan nan ba, amatsayinki na babba acikin gidan
nan ke kadai yakamata ki sama mana da agidan nan.
Wani murmushin jin dadi Gimbiya tayi tace gsky kin
bani labari medadi, hannu tasa tadauko kudi masu yawa
tabata amatsayin tukuici.
Godiya sosai Jakadiya tayi, Gimbiya tace kina de saka ido akan Rayhana ko? Tace e sosai ma, itama haryanzu babu
komai atare da ita, Gimbiya tace yayi kyau, aikinki yana kyau.
Har cikin Fulani yashiga wata 8 da sati 2 babu wanda
yasan da cikin, alokacin yafito sosai. Rungume take ajikin Sarki yana bata kankana abaki tana tayi mashi shagwaba, kallonta yayi yace Fulanita idan kika haifi mace wane
suna zamu samata?
Murmushi tayi tashafo fuskarshi tace idan namiji ne fa?
Hancinta yaja yace harga Allah inason diya mace shiyasa bantaba tunanin haihuwar namiji ba, nasan mutane
dayawa sunamun kallon wanda beda magaji, nikam
nikeda babban magaji, dan koda ace inada namiji ko
mutuwa tazo mani zan bada wasiyar abama Qaseem
sarautar.
Dan haka koda banida namiji bazan damu ba. Ko
kinason haihuwar namiji? Kai tagirgiza tace nima inason mace sosai, Allah yabani mace, yace amin. Kura mata
ido yayi, hura mashi iska tayi tace wannan kallon fa
namenene? Jawota yayi ya rungumeta sosai harseda tayi
kara ya sassauta mata, kallonshi tayi idonshi yayi ja
sosai, tashi tayi niyaryi yakara riketa, ahankali tace akwai abinda ke damunka ko?.
Kai ya girgiza yace kwana 2 ina wani mafarki wai muna
zaune kintashi kin ruga inata kiranki amma kinki kidawo, kuma har kika bace bankara ganinki ba. Jikinta taji yayi sanyi tace insha Allahu babu abinda zerabamu kai nawa
ne nima haka. Yace Allah yasa.
Karar buga kofa sukaji, Sarki yace shigo dan yasan inde aka buga kofa to wannan bawan ne,shine kuwa yashigo
yaduka kasa yace rankai dade Jakadiya ce, Sarki yace to kuma shine kabarta awaje, tashi yayi cikin sauri yafita.
Fulani tace bari inshiga ciki kafin ku gama, riketa yayi yace haba kiyi zamanki mana kinsan yanda nake da
Jakadayi ai, tace amma kasan malam yace..... bata karasa ba Jakadiya tayi sallama, cak ta tsaya ganin Fulani atsaye da katon ciki, Sarki wanda be kula da halin data shiga ba yace shigo mana Jakadiya.
Saurin seta kanta tayi ta shigo, tana zuwa tazube tana kwasar gaisuwa, zama Fulani tayi bayan sun gama
gaisawa, kwata kwata Jakadiya bata gwada taga cikin
jikinta ba, kallon Sarki tayi tace dama shigowa nayi inj ko akwai wani aiki da za ayi maka?.
Kai yagirgiza yace babu komai Jakadiya kije kawai, dariya tayi tace toshikenan afito lafiya, kallon Fulani tayi tace Gimbiya ahuta lafiya, fita tayi zufa tana fito mata. Sarki yace ai nasan Jakadiya bata iya daga kai ta kalleni, bare kuma ke, kinga batama kula da abinda ke jikinki ba,
nasan data gani zatafi kowa murna, dan tana daya daga
cikin wadan da suka shiga damuwa akan rashin
haihuwata. Shiyasa naso abari infada mata amma su
Qaseem da Waziri suka hana. Fulani tace idan na haihu
ai zataji, yace to Allah ya kaimu.
Hartuntube Jakadiya takeyi sbd sauri, jikinta har rawa
yakeyi sbd bacin rai. Ko sallama batayi ba tashiga falon Gimbiya Zakiyya, suna zaune ita da Medaki, Gimbiya tace lafiya Jakadiya zaki shigo mana guri babu sallama bare
neman izini? Zubewa kasa tayi tana haki tace Allah
yahuci zuciyarki, wlh wani bakin labari ne yake tafe dani, sede inajin fargabar fadin shi, amma idan kinmani izini zan iya fada. Gimbiya tace yi maganarki.
Abinda tahani ajikin Fulani tafada masu, cike da firgici Gimbiya Zakiyya ta mike, wata irin zufa tafara keto mata, Medaki tayi saurin tashi tariketa suka zauna. Gimbiya
tace wlh baze yuwuba, haba Jakadiya meyasa jakiyimun
haka? Amma mekika cemun kince babu komai ajikin
Rayhana? Jakadiya tace kigafarceni, wlh tun lokacin da
kika hanani zuwa gurinki alokacin naso infada maki bana ganin Gimbiya Fulani kona shiga gidan bata zama falo,
shiyasa bana sanin halin datake ciki.
Medaki tace toyanzu mekike ganin za,ayi kinsan de
baza'a barta ta haihu ba. Gimbiya Zakiyya tace idan har nabar Rayhana ta haihu agidan nan to wlh nikuma
aranar zanbar gidan nan, kai kuma ce niba 'yar halak
bace. Jakadiya meye shawara? Jakadiya tace Gimbiya
hanya daya ce, amma bazaki jita abakina ba, nasan
bakisonta, amma zanje insamu Sarkin Fada kinga shi
namiji ne, yafimu zurfin tunani, zanje inji yanda zamuyi.
Gimbiya Zakiyya tace banason kidau lokaci, kuma
kintabbatar Sarkin Fada ba munafuki bane, kina ganin
yanda yake shige ma Qaseem da matarshi, yaronsu ma
agurinshi yake zama. Jakadiya tace Sarkin fada
mutumina ne, banida wani abokin shawara aduk gidan
nan se shi, banida haufi akanshi, dan haka kibarni dashi anjima zakiji abinda muka yanke dashi. Amma bazamu
bari tahaihu agidan nan ba. Gimbiya Zakiyya cike da
bacin rai tace kaini harzamanta agidan nan banaso, sede kinsan banason maganar boka atsarina.
Sarkin fada kanshi seda yashiga tashin hankali dayaji
labarin cikin Fulani, mikewa tsaye yayi yace tashin
hankali, lokaci yayi dazamu fara aiwatar da aikinmu agidan nan, babu wani yaro daza,a kara haifa
amasarautar nan, dan haka kicema Gimbiya idan har ta
amince anjima da dare zanzo semu tattauna idan zata
amince da shawarata, kuma kifada mata babu wani
batun boka ko malam aciki. Jakadiya tayi ajiyar zuciya
tace yanzu naji natsuwa, bari inje insameta infada mata seka jini. Yace kigaishemun da Gimbiyata.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 60⚜65
Zaune suke afalon Gimbiyar Baban Gida, wani shu'umin
murmushi Gimbiya tayi, tashi zaune tayi daga
kishingiden datake, alokacin data gama jin bayanin da
Sarkin Fada yayi masu. Ahankali tace lallai dole nabaka kyauta me tsoka saboda wannan shawara daka
kawo,lallai kayi tunani mekyau.
Gaka de kafito daga cikin matsiyata talakawa, kuma kazo gidan nan amatsayin bawa, kafin daga baya kasamu
yanci, amma kana da tunani irin na yan sarauta.
Kodayake ance kunfi wasu mata zurfin tunani, naji dadin wannan shawarar taka kuma ita za'abi, dan haka kaje
kayi shiri kamar yanda kace zaka samu abokan aiki, bana son inkara jin labari mekama da Rayhana bare kuma
cikin jikinta.
Asalwantar da ita idan samune tabar duniyar gaba daya.
Badamuwata bace, inde nizan rayu to kowama yamutu
banida matsala, dama can bata fito daga jinin sarauta
ba, niko duk wanda baya daya daga cikin jininmu, wato
sarauta, dashi da kaskantattar dabba duk daya suke
agurina, koda kuwa na nuna mashi so, to bana gaskiya
bane, koyakikace Medaki?
Gaba daya falon yayi shiru jin irin kazaman kalaman da
Gimbiya Zakiyya take fadi akan talakawa, kallonsu tayi
taga gaba daya fuskarsu tacanza, se alokacin ta tuna
baram baramar datayi, cikin sauri tace shiyasa nake
godema Allah daya hadani da mutanen kirki irinku,
daban kuke agurina, kunfi kowa matsayi azuciyata acikin gidan nan.
Murmushin yake Jakadiya da Sarkin Fada sukayi, can Sarkin Fada yace bakomai Gimbiya muma muna tare
dake, kuma dasannu zamu nuna maki muma muna cikin
masoyanki, kinsan bawa akwaishi da amana. Murmushi
tayi tace yayi kyau.
Shima murmushin mugunta yayi ya kalli Jakadiya da
Medaki yakanne masu ido. Medaki tace yanzu yazakayi
kasanfa dole aikin yakasance ranar da Sarki baya
dakinta. Gimbiya tace kabari seyadawo gurina dan nasan
Medaki bawani sanin yanda zata dauke mashi hankali
tayi ba, kasan jinin sarauta ako ina daban yake, dan haka kabari nan da jibi. Yace angama ranki yadade.
Fita sukayi shida Jakadiya, acikin Lambun gidan suka
sami guri suka zauna, Jakadiya wadda acike take da
bacin rai ta kalli Sarkin Fada cike da bacin rai, tace yanzu haka zamu cigaba da zama tare da Wannan matar, diyar
cikinmu tana mana cin kashi akullum? Wlh dole
mugwada mata talaka ma, yanada yanci, kuma zata gane
bakomai bane jinin sarauta suka sani, mune acikin gidan nan, dan haka zamu gwada mata munfita sanin gidan
nan.
Dariya Sarkin fada yayi yace dadina dake saurin hawa,
kalli nan, aljihunshi yayi mata nuni dashi, sede banga
komenene aciki ba, lekawa tayi, tace meye amfanin
hakan? Dariya yayi yace kisa ido kawai malama, zakiga
yanda akeyin duniyanci, kinganni nan bana yarda da
jinin sarauta, duk yanda ka kai dayi masu hidima wata
rana dole sumaka butulci.
Shiyasa acikin aikina bana barin sahu, ko kuma baya da
kura, dan haka kizuba ido kigani wata rana dole Gimbiya tanemi juya mana baya, alokacin zan nuna mata asalin
kalata. Dariya Jakadiya tayi tace amma naji dadi, ai
nadauka duk zagin datayi mana zetashi abanza? Yace
tama isa, haba Sarkin Fada fa nake, kinsan yanda akayi
nasamu wannan matsayin kuwa, nikaina ina tsoron
kaina, bari infada maki abinda babu wanda yasani
agidan nan seni kadai, sekuma marigayi ya matata, itama dalilin sanin abinda na aikata yasa nakara mata iska,
wanda haryanzu babu wanda yasan da mutuwarta, kowa
yadauka yanda nace guduwa tayi sbd bata haihuwa
nikuma nace zanyi aure shine tagudu.
Har yanzu maganar ahaka take, alokacin Sarki dakanshi
yarika bani hakuri, Waziri da Qaseem kuwa cewa sukayi
kada insake inje bikonta, dama ba'a garin nan take ba,
nace masu ai tama tafi garinsu.
Murmushin jindadi Jakadiya tayi tace inajinka bani labari insha, kara gyara zama yayi yace alakocin da za'a nada
sarautar Sarkin Fada, mu 3 aka tsaida, sede yanda
mutane suka zabi sauran biyun suka barni hakan yayi
mani ciwo, shiyasa nashiga damuwa saboda nasa rai
akan sarautar, bayan an kara kuri'a aka tsaida mutum
daya acikin su biyun.
Hmmm kinsan menayi? Tace seka fada, cikin dare nashiga dakin Mati wanda shine za'a nada washe gari,
dama kuma tare suke kwana da abokin takararshi,
inazuwa na saka wuka nakashe Mati, Kallah yana
baccinshi besan abinda yake faruwa ba, haka na debi
jinin Mati duk nashafa ma Kallah ajiki harda fuska, kuma nadauki wukar nasaka mashi ahannu, haka najuya
nafita.
Inazuwa gida nayi saurin dibar ruwa domin nima jikina
duk yabaci da jini, hanyar bandaki na nufa kawai senaji maganar matata ta faramun salati, tana fadin inakaje da wannan daren, dama muna kwance naga sanda kadauki
wuka ka boye awondonka kafita, kuma gashi yanzu
kadawo jikinka duk jini. Anya megida ba wani abun kaje
ka aikataba?.
Aje bokitin nayi najata zuwa daki, anan itama na shaketa, nan take ta mutu, haka na hada duka kayanta na kullesu
adan kwali, naje cikin bayan lambun nan na haka rami
sannan naje nadaukota ita da kayanta narufesu aciki,
namaida kasa sosai, yanda babu wanda zesan anrufe
wani abu nazuba, dama kuma gurin ba'a shigarshi sosai
ai kingani.
Washe gari da safe naji ana kururuwa, ina fita naga
mutane sunzagaye Kallah yanata kuka jikinshi duk jini ga wuka ahannunshi, yana fadin wallahi banine na kashe
shiba. Haka aka jashi zuwa fada, bayan anyi bincike aka gane sahun hannunshi ajikin wukar, nan take shima aka
yanke mashi hukuncin kisa. Sede babban abin ban
haushi wannan shegen Wazirin wanda yakeda dogon
hangen nesa, da zurfin tunani, shine yaja Sarki daki,
bansan mesuka ceba, Sarki yazo yace hukuncin kisan
daurin rai da rai agidan yari za,ayi mashi, bahaka naso ba, amma sanin kowa yaji hukuncin nasan baze taba fita
ba hakan yasa hankalina ya kwanta.
Bayan kwana 2 kawai naji ance niza,a bama sarautar.
Dadi sosai naji, sede ban gwada afuskata ba, Sarki yake cemun meyake damuna haka, anan nafada masu karyar
kwanana 4 banga medakina ba, dama mundade muna
rigima, shine kawai natashi naga takwashe kayanta
tacemun garinsu zata tafi. Nace masu nayi neman
harnagaji banganta ba. Anan kowa yatausayamun
sukayita lallashina, dahaka washe gari akamun sarauta.
Kuma daga ranar babu wanda yakara tamabayar
medakina, asalima Waziri cewa yayi kawai inkara aure,
nikuma nace tunda bana haihuwa bazanyi aure ba,
shiyasa suka kyaleni.
Tokinji babban sirrina, kuma nafada makine, saboda
nasan bazakici amanata ba. Wani irin murmushi
Jakadiya tayi nikaina bangane kona menene ba, tace
haba aini taka ce, cikinmu daya. Sarkin Fada yace
kisamomin maganin saka mutum bacci, amma na
fesawa, tace angama.
Fulani ce zaune afalo ita da Babanta sunata fira, tundazu yazo sundade suna fira, yakasa tashi yatafi, itama bataso yatafi, kallonta yayi yace Rayhana inaso bayan kin haihu idan abinda kika samu yayi kwari, zamuje gida domin
mugansu, kuma suga abinda kika haifa, kinga zasuji dadi.
Tace nima Baba inason zuwa gida, insha Allahu dana
haihu kamar da wata 7 semutafi ko? Yace hakan yayi,
amma kibari sekin haihu sekima mijin naki maganar.
Hannu yasa a ajjihunshi yaciro wani zobe mekyau,
yamika mata, sakashi tayi ahannunta, ta kalli Babanta
tace wannan fa? Kwallan idonshi yagoge sannan yace
zoben mariganyi yane, nima jiya ina duba kayanta,
kinsan tunda tarasu bandaga kayanta ba, to acikin wata
jakarta naganshi shine nace bari inkawo maki kisaka
ahannunki. Itama kwallan ta goge tace nagode Baba,
yace bakomai bari intafi yamma tayi, tace Baba kabari se anjima mana, yace a,a ai na dade, gara intafi sena kara dawowa. Har bakin kofa tarakashi idanunta sunkasa
dena zubar hawaye, shikanshi kwallace tacika mashi ido.
Sun jima abakin kofa yana lallashinta kafin yatafi.
Gimbiya Suhailat ce da Safeeya sukazo duba Fulani
takawo mata farfesun yan ciki, zaune suke tanaci sunata fira, Gimbiya tace kinde kusa haihuwa kihuta, nasan
insha Allah nan da kwana 7 zaki cika wata 9 dede, nasan kozaki kara kwanaki bazaki kara dayawa ba. Fulani tace
nima nagaji nakosa in haihu, sede bansan abinda yasa
ba, yan kwanakin nan se intaji yawan faduwar gaba.
Safeeya tace kada kidamu kirika fadin Innalillahi
Wainnailai Hirraji'un, insha Allah zaki samu sauki, kuma koma wani abune zesameki zezo maki dasauki. Tace
shikenan nagode, Gimbiya suhailat tace bari mutafi
nasan yanzu Yaya zeshigo, Fulani tace ai banan yakeba. E
duk dahaka aidole yazo yaganki kafin ya kwanta. Fulani
tace Allah banaso kutafi, to kibar Aunty Safeeya ta kwana anan tunda nikadai zan kwana. Dariya Gimbiya tayi tace
a,a kibari kawai mutafi.
Kamar zatayi kuka tace dan Allah Aunty. Safeeya tace to bari inje idan yatafi seki kirani sena taho, murmushi tayi tace yauwa nagode, haka suka yimata sallama suka tafi.
Suna fita tashiga daki ta kwanta, ba dadewa Sarki yashigo dakin, kusa da ita yaje yakwanta ta bayanta
yarungumota yana me tusa kanshi cikin wuyanta,
murmushi tayi tace sannu da shigowa, yace yauwa,
inacen sunrikeni afada, nikuma duk nakosa inzo kada
kiyi bacci bamuyi sallama ba, tace kaima kasan bazan iya bacci bankarbi sakon seda safe daga gareka ba.
Kara rungumeta yayi, yace aide jibi kamar yanzu muna
tare, tace sosai ma, kallonta yayi yace kinyi kyau sosai Ummin AMATULLAH. Dariya tayi takara shigewa jikinshi
tace wato harma kasan mace zan haifa, kuma kasa mata
suna? Yace sosai ma, tace ai nadauka sunan Ummanku
zakasa? Yace naso insaka sunanta, sede yanda na dade
ban haihu ba, kuma Allah yabani yanzu shiyasa naga yadace insaka wannan sunan kinsan idan akace
Amatullah ana nufin amintattar Allah, idan kuma namiji
ne, tozansa AMINULLAH. Shima fassarar duk daya ce.
Murmushi tayi tace kayi gaskiya, idan Allah yakara bamu wasu se asaka, yace hakane, zatayi magana yahade
bakinsu guri guda, sundauki lokaci me tsawo ahaka,
ganin yafara fita hayyacinshi yasata saurin sakinshi ta matsa. Runtse ido yayi yana maida numfashi.
Ahankali cikin mutuwar jiki tace nasan Gimbiya Yaya
tana jiranka adakinka, yakamata katafi, bude idonshi
yayi sede idon yayi ja sosai, maidawa yayi yarufe, sega kwalla sirara suna saukowa, dasuri tamatsa kusa dashi
tace meyafaru? Saurin rungumeta yayi yana fadin dan
Allah kada kibarni kinji, wlh kece farin cikina, duk ranar da babuke akusa dani rayuwata bata da amfani.
Saurin rufe mashi baki tayi tana fadain wai meyafaru
kake wannan maganar? Murmushi yayi yace bakomai,
kawaide ina fada maki ne, tun safe yau nakejin faduwar
gaba, addu,ar danakeyi ce tasa nakejin sauki.
Tace babu abinda zefaru se alkairi, katashi katafi kada tayi fushi, yace wlh da ace Medaki ce, nasan zata iya
saidamun kwananta, amma Zakiyya ko duniya zan bata
bazata yarda ba. Tace a,a nima banaso nafison kwanana
yazo da kanshi.
Murmushi yayi yace bazaki gane yanda nakeji bane
shiyasa, tashi yayi yace muje kirakani to, tace to kuma idan katafi waze sani bacci? Yace kai namanta, jawota
yayi yakwantar da ita akusa dashi, tausa yafara yimata
ahankali yanayi yana mata fira medadi, tun tana bashi
amsa haryaji shiru.
Zama yayi yana kallonta yadauki kusan minti 30 yana
kallonta, daga karshe ya sumbaci goshinta, wuyanta da
bakinta sannan yatashi yafita jikinshi asanyaye.
Washe gari tunda asuba, Sarki yatashi dawani irin firgici, sakamakon mafarkin dayayi, Gimbiya Zakiyya tace lafiya
naga kana zufa? Tashi yayi bece mata komai ba,yanufi
part din Fulani. Turus ya tsaya ganin bata cikin dakin, kuma dakin duk ahargitse, karar ruwan dayaji ne,
abandaki yasa yaji hankalinshi yadan kwanta, juyawa
yayi yaje yayi wanka ya nufi masallaci.
Tare dasu Qaseem da waziri suka taho, Waziri yace lafiya rankaidade naga tundazu kamar kana da damuwa?
Kallonshi yayi, yace wlh wani mummunan mafarki nayi
kuma da Fulani nayi mafarkin, shine nashiga dakinta da
asuba sede naga dakin ahargitse, kuma Fulani bata yima
daki haka, sede karar ruwan danaji abandaki yasa
hankalina ya kwanta, amma kuma haryanzu gabana
yana faduwa.
Waziri yace to kayi mata magana abandakin kaji ta
amsa? Yace a,a Qaseem yace Yaya mudeje ka kara
dubawa ko? Waziri yace haka yakamata.
Part din suka wuce, sede afalo suka tsaya shi kuma yawuce dakin. Karar dasukaji ce tasasu saurin shiga
dakin, Sarki suka gani kwance kasa da alama faduwa
yayi, hawaye suna zuba a idonshi, dasauri Qaseem
yamatsa kusa dashi yana fadin yaya lafiya?
Da hannunshi yayi masu nuni dawani guri, jini suka gani agurin, ga kofar bandaki abude ruwa na zuba a famfo,
babu alamun mutum aciki. Da kyar Sarki yake fadin
babu ita wlh bata nan, Waziri yafita waje dasauri, haka yarika bin masu gadin gidan sede babu wanda yace yaga
wani abu yafaru cikin dare, abu kamar wasa har rana
tafito babu Fulani.
Gaba daya gidan antaru ankira hukuma ansanar da ita
sede haryanzu babu wanda yakira yace ansamu wani
labari akanta. Sarki
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 13