An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
A MAKABARTA AKA HAIFE NI
Na Nabila Rabi'u Zango
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyarci shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Bismillahir Rahmanirrahim, inafarawa da sunan Allah megirma da daukaka. Yanda zanfara rubutun nan lafiya
Allah yabani ikon kammalashi lfy.
GARGADI..... Banyarda wani ko wata su juyamun littafi naba, ko kuma su canzamun labarina. Allah yabada ikon
kiyayewa.
GODIYA.....Ina mika godiya ta ga dukkanin masoyana wadanda nasani dama wadan da bansani ba, nagode da
irin kaunar da kuke mani, duk da bazan samu damar
binku inyi maku godiya ba, amma nayi amfani da
wannan dama ga duk wanda yakaranta yazama
amatsayin sakon gaisuwa zuwa gareshi. Allah yakara
dankon zumunci.
Season 1⚜5
Babban mutum ne, kuma kyakkyawan dattijo
wanda akalla baze wuce shekaru 50 aduniya ba, acikin
keken guragu aka turoshi wanda da alama yana fama da
mutuwar shanyewar barin jiki, daga dakin gashi aka fito dashi bayan angama gasa mashi jikinshi, wanda ake
masa duk bayan kwana 3.
Sarki Qaseem ne yashigo dakin wanda yakasance
kanine ga dattijon dayake bisa kujera. Sannu Yaya
yakarfin jikin? Kwalla ce tacika idonshi, wadda tariga da tazamar mashi sabo aduk lokacin dazeyi magana,
Babban bawan dayake kusa dashi wanda yazama shine
hadiminshi yasaka kyalle yayi saurin goge mashi idonshi.
Hannu Sarki Qaseem yadaga, nan take kowa yabar dakin.
Zama yayi kusa dashi yadafa kafarshi, fuskarshi cike da damuwa, yace Yaya dan Allah kayi hkr, yakamata ace
zuwa yanzu kayi hkr da abinda yafaru shekaru 18 dasuka
wuce. Akullum semunsa manyan malamai sunyi addu,a
akan damuwar datake cikin masarautar nan. Kuma
kasan ba,a fidda rai da rahamar Ubangiji. Murmushi yayi tare da girgiza kai, yana kallon kaninnashi, wanda yake so sosai, kasancewar shikadai gareshi kuma Uwa daya
Uba daya suke.
Sarki Qaseem shima murmushin yayi ganin Yayanshi
yanayi, yace tabbas Yaya yau naji dadin ganin murmushi
afuskarka, wanda rabon dakayi hakan tunkafin karasa
farincikinka. Segashi yau kayimun murmushi.
Dariya ce tafito daga cikin dakin, wanda wasu manyan
mata ne, zaune acikinshi. Daya daga ciki tace, ai wlh
Medaki kema kinsan bazan taba barin aci mana fuska
acikin gidan sarauta ba, kamar yanda kikazo kika sameni acikin gidan nan shekarata nawa kika sani muna tare da
Memartaba, kuma nayi hkrn zama dashi, harkikazo kika
sameni, kekanki dabakiyi biyayya ba, ai da tuni nayankar maki Ticket nabarin duniyar baki daya.
Dariya Medaki tayi tace haba Gimbiyar Babbar Gida, aini kinganni nan, tunda nataso haka Allah yayi ni, bandamu
dasena zama babba ba, inde zanzama 'yar kore kuma
inkarbu toni banida damuwa, zan iya yinkoma menene.
Dan haka kada kidamu, koda yanzu bamune matan sarki
Qaseem ba, aide kanin mijin mune. Kuma aide haryanzu
muna cikin masarautar.
Gimbiyar Babbar Gida tadauki apple tasa abakinta, ta
maida kallonta gurin Jakadiya, wadda take mata tausa
tace, Jakadiya bamu labarin cikin gida. Jakadiya ta gyara zama tace Allah yatemakeki Babbar Gimbiya, wadda
babu kamarta, ba,ayi ba, kuma baza,a tabayin kamarki
acikin gidan nan ba. Allah yakara tsawon kwana. Babu
wani labarin daze firgitaki acikin gida, kinriga dakinsan Gimbiya Shuwa haryanzu bata yarda dani ba. Narasa
dalilinta nayin haka, ace mace duk wani hali irin na
mijinta Sarki Qaseem tadaukeshi. Kodan ita tata sarautar gado ce, shiyasa bata yarda da kowa? Medaki tace haba
Jakadiya atunanina babu wani abu daze baki tsoro acikin masarautar nan, kinsan ketamu ce, muma haka. Dariya
tayi tace hakane, Gimbiya, karku damu asannu zakusha
labari.
Zaune take cikin wasu kodaddun kaya, acikin wata bukka
ta kara, wadda take daga gefen wata tsohuwar
MAKABARTA. Wani tsohon kwanone ahannunta,abinci
ne, aciki wanda gaba dayanshi bewuce rabin kwanonba.
Kyakkyawar matashiyace wadda bazata wuce shekaru 18
aduniya ba. Akusa da ita wata dattijuwa ce, wadda itama bazata wuce shekaru 38 aduniya ba, da kaganta zakasan
tana cikin yanayi na hauka, gaba daya kamanninta sun
bata. Jawota diyarta tayi tana mata magana irin ta
kurame, tana mata nuni da kwano alamun taci abinci.
Dariya Uwar tayi cikin halin hauka tace a,a Babyta yau bazanci abinci ba, kece zaki faraci, dariya yarinyar tayi mata, dan taji abinda tafada, sede kawai maidawa ne
bata iyayi (KOMEYE DALILI
O
🤔 OHO HO 路♀ MUJE ZUWA).
Matsawa Wadda naji ankira da Baby tayi kusa da
Mamanta tasa hannu tafara bata abincin, itama hannu
tasa tana bata abinci. Kwalla ne, suka zubo ma baby tayi saurin gogewa.
Wani Kyakkyawan Matashi ne, me kama da Larabawan
Shuwa, baze wuce shekaru 25 aduniya ba, da Sallama
yashiga dakin kyakkyawar matar, wacce take kishingide
abisa kafet din dakin. Murmushi tayi tace, Yarima Arif
sannu dazuwa. Kwanciya yayi kusa da ita yace yauwa
Momy na, sannu da hutawa. Kallon bayin cikin dakin
tayi, lokaci guda suka fita, Madarar shanu tamiko mashi, ya amsa yana murmushi, yace Momy naje gurin Abba
ance yana dakin ganawa da baki, kuma inason magana
dashi. Kanshi tashafa tace to ai sekayi hkr kajira yagama ko, wace irin magana kakeson yidashi? Momy dama
akan rashin lafiyar Baffa ne,tunda nadawo naga
yakamata ace anfitar dashi waje ko za,a dace. Murmushi
tayi tace Arif bakasan komai akan ciwon Yaya ba,
Abbanka yana kokari sosai amma koma menene idan
yafito zamu gana dashi. Kwallan idonta tagoge.
Kubiyoni domin jin labarin masarautar.
Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ...🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 5⚜10
Zaune suke adakin memartaba sarki Qaseem, Areef
yadora kanshi asaman kafar Abbanshi, Gimbiya Shuwa
Momyn Areef tana kusa da Sarki tana gyara mashi Inibi
tana mika mashi. Sarki yashafi kan Areef yace Yarima
inajinka wace magana kakeson kafadamun?
Tashi zaune Areef yayi yadauki inibi yasa abakinshi yace Abba dama akan maganar Baffa ne, naga yanda nabarshi
haka nadawo nasameshi, shine nace meze hana afitar
dashi waje koza,a dace. Murmushi Sarki yayi yace wlh
Yarima nafika son inga Yaya yawarke, kozamu samu
damar yin bincike akan babbar matsalar datayi
sanadiyar shigarshi wannan halin. To amma Abba baka
ganin fitar dashi ze iya temakawa gurin samuwar lfyrshi tunda acan sunfimu kayan aiki?
Hakane Yarima, amma babu yanda banyi da Yaya akan
yabari afitar dashi ba, yakiya gashi ba magana yakeyi ba, sede yana jin duk abinda muke fada, yana ganin kamar
gara abarshi yayi tazama haka, wanda kuma hakan
bashine mafita ba, dole se mutum yana da lfy yake iya
komai arayuwarshi, ni babban damuwata wadancan
munafukan matan nashi, danni wlh haryanzu banyarda
dasu ba. Gimbiya tace hakane Me martaba, sede kasan
bamuda wata hujjar dazata nuna mana sune sanadiyar
faruwar komai agidan nan, kamarde yanda kace acigaba
da addu,a hakan zamuyi, fatanmu de Allah yasa Fulani
da abinda ke cikinta koma menene, yasa suna raye,
kuma cikin koshin lafiya.
Sarki yace amin. Kallon Areef yayi yace Yarima yanzu
angama karatu gashi zaka fara aiki kaga dole ace kaima
kashigo sahun manya ko? Kwantar da kanshi yayi saman
cinyar Gimbiya ya lumshe idonshi, shiru yayi bece komai ba. Gimbiya tace Yarima yanaji kayi shiru kode boye
mana surikar tamu kakeyi? Murmushi yayi sosai wanda
har seda dimple dinshi ya lotsa duka 2, yace Momy
kubar maganar nan, niharyanzu banga macen danakeso
ba. Sarki yace aiko Yarima yakamata ace kafara
nemanta, dan kasan bazamu barka kazauna haka ba,
atsarin masarautar nan kasan baza,a barka kazauna haka
ba, damma de Yaya beda lafiya, ai da tunkafin kadawo
anduba maka acikin 'ya'yan sauran masarautun ansama
maka mata.
Dariya Areef yayi yace haba Abba niko aure zanyi ai
banason yar gidan sarauta, nafison insamu mace wadda
bata tashi acikin sarauta ba, kuma nibanason mace
wadda zatazo tarika rainamun iyaye, kawaide akaramun
lokaci ahankali zansamo wata wadda ra,ayina yayi dede
da ita.
Harararshi Gimbiya da Sarki sukayi atare, Sarki yace
uhm Yarima idanma mafarki kakeyi to kadena, acikin
masarautar nan babu yanda za,ayi kashigo mana da
bare, dole se yar sarauta, kana ganin yanda Momynka
dani kaina muka fito daga gidan sarauta, jininmu gaba
da baya cike yake da sarauta, kai kuma yanzu sekafara
zuwa mana da wani batu. Ka godema Allah Yaya beda lfy,
da kila seyafini daukar zafi akan wannan magana taka.
Duk da shima matar daya aura ta 2 data 3 basu fito daga cikin gidan sarauta ba, amma kowa yayi mashi uzuri,
matarshi ta 2, agidan nan kowa yasan yanda akayi ya
aureta, haka ma ta 3 dole ce tasashi ya aureta, sekuma
babban rabon daya shiga tsakaninsu, bayan wannan
babu abinda zesa Yaya ya auri wata mata wadda ba,a
gidan sarauta ta taso ba.
Gimbiya tace Allah yahuci ranka Me martaba, banason
ranka yana baci akan wannan maganar, abinda bamu
taba yima Yarima agidannan ba, Fada shine yau da
bakinka kake mashi, kaima kasan Yarima mebin duk
wani umarninmu ne, ai base anbata mashi rai ba,
sekasashi shiga damuwa, wanda kuma betaso acikinta
ba, karka manta mungina rayuwarmu abisa soyayya dan
Allah kada kabari zafin zuciya yacanza maka zuciyarka.
Sarki yakamo Areef wanda idonshi har yayi ja dan bacin
rai.
Kwantar dashi yayi saman kafarshi yana shafa kanshi
yace ba ina nufin bata maka rai bane, kaji, kawai ina
maka tuni da ra,ayin masarautarmu ne, banaso kasa
wannan aranka haryadameka. Hawayene suka zubo daga
idon Areef, cike da damuwa Gimbiya tamatso kusa dashi
tace kagani ko, kalli abinda kajawo mashi, yaushe rabon da Yarima yayi kuka agidan nan? Inajin tun yana yaro,
jawoshi tayi tamaidashi saman kafarta tace Ya isa haka
Yarima na, kasan Abbanka yana sonka baya son bacin
ranka yishiru hakanan.Sarki yace ya isa haka maganar
tawuce kaji, amma kaima kaje kayi tunani.
Lumshe ido Areef yayi, aranshi yana fadin akwai babban
aiki agabana, kuma gaskiya yanda ra,ayina yake bazan
taba canzashi ba, bana bukatar yar sarauta, duk da
haryanzu bansamu wadda nakeso ba, amma zantajira
seranan dana samu sannan, nasan suna sona, dole zasu
barni na auri ra,ayina. Amma dole nacirema su Momy
wannan ra,ayin nasu.
Anesa da masarautar Sarki Qaseem, wani dankaramin
gidane, me kyau, duk da karami ne, amma anyi mashi
gini mekyan fasali. wani tsoho ne, fari, yafito daga cikin gidan, daka ganshi zaka gane ba asalin bahaushe bane,
yafi kama da irin larabawan dasuka baro garinsu sukazo
nigeria har zama yakamasu anan, zama yayi bisa wata
kujera dake kofar gidanshi ya kunna redio yana kokarin
kamo tasha.
Tundaga nesa yahango fadawan sarki suna zuwa,
murmushi yayi, cikin hausarshi wadda bata gogeba, yace
aikin kenan, kullum azo adameni da kira, kuma haryanzu
ankasa samo mani Diyata, da abinda ke cikinta. Kwallar
data zubo mashi ce yasa hannu yagoge. Da sallama suka
karaso gurinshi, ahankali ya amsa masu. Daya daga cikin fadawan yace Barka da hutawa Baba, yace yauwa
sannunku, yauma wani kiran neko?
Murmushi Bafaden yayi yace a,a Baba, dama Sarki ne,
yace muzo mukawo maka kayan abinci. Murmushi yayi
yace to madalla, nagode, yajikin me martaba? Bafaden
yace to Baba dasauki zamuce, kasan sauki sede agurin
Allah, fatanmu de Allah yanuna mana inda Gimbiya take
ko zamu samu Hankalin kowa ya kwanta. Baba yace
addu,a kam kullum munayinta, sede haryanzu acikin
raina nakasa yarda cewa Rayhana itace tabar gidan Sarki da kanta, kuma nakasa yarda cewa bata raye, inaji
ajikina wata rana zamu gana da ita, fatana de Allah yasa kome tahaifa ace yana raye. Sukace amin Baba, bara
mushigar maka da abincin ciki, yace tonagode, dama
gashi bayin dasuke dafamun abincin sungama aikinsu
suntafi, kushigarmun dashi ciki.
Jakadiya ce take tafaman Sallama abangaren Gimbiyar
Babban Gida, daga ciki akace shigo mana Jakadiya, tace
Gafaranku de, ai nadauka ko bacci kikeyi, Allah
yatemakeki Babbar Gimbiyar Sarki, Allah yakaramaki
lafiya da tsawon kwana, Allah yabaki muma musamu
awajenki, ke kadaice Babbar mata agurin Sarki, duk
wanda yazo sede yabiyo bayanki. Daga gefe Gimbiya me
Daki tarika wurga mata harara jin irin kirarin datakeyi ma Kishiyarta.
Murmushi Gimbiyar Babban Gida tayi tamata nuni data
zauna, guri tasamu tazauna sannan takalli Gimbiya
medaki tace Ina gaisuwa ranki yadade. Murmushi tayi
tace sannu Jakadiya, daga ganin bakinki akwai magana,
meke tafe dake?
Babban labari ne yake tafe dani kuwa Gimbiya. Dazu
nazo wucewa tagefen Dakin memartaba Sarki Qaseem,
senaji yana magana kamar yana fada, dajin haka nayi
saurin daukar tsintsiya nayi kamar ina shara, sede na
boye fuskata, gudun kada aganni tunda ansan ba,a
bangarensu nake aiki ba, asalima nice mebada umarnin
ayi aikin........ nan takwashe duk abinda taji sunfada ta fada masu.
Tashi zaune Gimbiyar Babban Gida tayi, tace gaskiya naji dadin wannan labari naki Jakadiya, dan haka kina da
kyauta me tsoka. Washe baki Jakadiya tayi tace godiya nake Gimbiya, Allah yakara girma. Amma Me daki wace
irin shawara kike ganin yakamata mubi don mu samu
muyi amfani da wannan dama?.
Gyara zama tayi tace, inaganin tunda har Sarki ya furta Bayason Yarima ya kawo mashi bare, meze hana kisamo
daya daga cikin matan gidan sarautarku kimaidota gidan
nan. Murmushi Gimbiya tayi tace Medaki kenan, kina
tunanin Gimbiya Shuwa zata bari Yarima yaso wata data
fito daga bangare na? Kinfi kowa sanin bama ga maciji
da ita, dan haka wannan shawara taki bata karbu ba.
Jakadiya kawo mana mafita.
Kara hade rai Medaki tayi jin ba,a karbi shawararta ba, sede yata iya, tunda bata da karfi agidan, dole tabi
asannu kodan tasamu fada. Jakadiya tace Gimbiya
inaganin tabayan gida yakamata mubiyo masu, tunda
bazasu taba karbar abinda yafito daga gurinki ba,kamar
yanda mukayi da farko yanzuma hakan yakamata ayi.
Kayataccen murmushi Gimbiya tayi tace haka nake sonki
Jakadiya. Allah yakaimu.Yarima Areef ne kwance adakinshi, shida abokinshi Haisam, suna fira, Haisam yace Yarima yanaga kamar
wani abu yana damunka? Yamutsa fuska Areef yayi yace
kawai kabari Man, wlh jiya Abba da Momy suka kusa
samun hawan jini. Dariya Haisam yayi yace uhmm nasan
wasa kakeyi, yanda Abba Da Momy suke sonka, harzasu
iya bata maka rai, kaifa agurinsu haryanzu yaro ne, dan haryanzu baka girma da hawa cinya ba. Areef yace
banason sharri, idan wasu sukaji kace hawan cinya ai
sesu dauka rungumeni akeyi.
Dariya suka saka, Areef yace wlh Man ba maganar wasa
ba, aide kasan irin burina akan matar danakeso na aura
ko? Yace E, yauwa to jiya daga nafada masu kalar matar
danakeso shikenan, suka rufeni da fada, kasan ai ra,ayin momy da Abba duk daya ne, kuma nasan wannan
magana dasuka fada harcikin ransu. Haisam yace kada
kadamu, kaida ko matar ma baka samuba, meye naka na
damuwa?.
Areef yace kaide ai dole nadamu, kasan me kwarmin ido
dawuri yake fara kuka. Haisam yace abinda nakeso
dakai, addu,a zaka cigaba dayi domin itace mafita,
nikaina bana maka sha,awar auren macen gidan sarauta,
kasan mata da sarauta, basu iyata ba, nafison kaje waje ka auri wata daban, hakan zebaka kwanciyar hankali
sosai. Areef yace nima ai jinsu nakeyi, dan bansamu
wadda nakeso bane, shiyasa nayi shiru, amma duk
lokacin dana samu, agskiya sede kowa yayi hkr, dan
bazan iya biyayya anan gurinba. Haisam yace muje
mugaida Baban Umma fulani kwana 2 bamuje ba, tashi
Areef yayi yana fadin wlh nima yana raina, dan
bakaramin tausayi yake bani ba, ace mutum yazo gari da
iyalinshi amma yanzu beda kowa, matar ta mutu diyar
kuma babu wanda yasan halin datake. Muje mudawo,
dan dazu waziri yake fadamun gobe zamuje darazo wai Abba ze aikemu. Haisam yace kai gsky zanje, nima
inason zuwa Darazo, fita sukayi suna dariya.
Washe gari tunda safe suka dauki hanyar bauchi, daga
can suka wuce darazo, tare suke da Jakadiyar Gimbiya
Shuwa, dan itama garinsune shiyasa tabiyosu tanason
tayi kwana 2. gidan wani babban malami sukaje, kuma
dama shine malamin dayake masu addu,a akan batan
matar Sarki Fulani. Bayan sungama gaisawa, suka fadi
sakon Sarki, malam yace haryanzu muna nan muna
addu,a sede kuma babu abinda ya nuna mana bata raye,
akullum muna ganin tana raye, kuma akusa damu, danni
abinda nake gani tafi kusa dani akan inda kuke, to Allah shine masanin gaibu, shikadai yafimu sanin gsky. Zamu
cigaba da addu,a har Allah yasa mudace.
Ruwan addu,a yabada akaima Tsohon Sarki, godiya
sukayi mashi, Waziri yasa fadawa suka shigo da kayan
dasukazo dasu. Waziri yace to muzamu koma. Malam
yace tonagode, kallon Jakadiya yayi yace ammade
Jakadiya ke anan za,a barki kidan mana kwana 2 ko?
Tace E Malam, dama cewa nayi inzo inganku. Yace to ai
yayi dede kishiga daga ciki. Tashi tayi tace to Yarima
Allah ya kiyaye. Yace amin sekin dawo.
Bayan suntafi wani tsoho yazo yace yanason ganin
malam, malam yace ashigo dashi, bayan sungaisa Malam
yace Baba meke tafe da kai? Tsohon yace wlh wata
magana ce take tafe dani, nadade inaso inzo insameka
amatsayinka na babban malami agarin nan, duk da ba,a
cikin gari nake ba, amma inada labarinka, nine megadin
MAKABARTAR datake wajen gari. Akwai wani abun
mamaki dayake damuna, wanda yadade yana faruwa,
sama da shekara 18, akan wata mata da diyarta. Malam
yace Baba inajinka bani labarin abinda kasani.
Kubiyoni zakuji yanda komai yake. Nagode da
kaunarku.
Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 10⚜15
Malam yace inajinka Baba, dama Allah gafarta
malam, tsawon shekaru 18 dasuka wuce nakasance ina gadi a MAKABARTAR bayan, gari, akwai ranar danayi
rashin lafiya har kimanin tsawon sati guda banje gurin
gadi ba, arana ta 8 danaje, inadan zagaya
MAKABARATAR. Can daga nesa da ita naga wata rumfar
kara, wadda daga gani kasan bata dade dayi ba, kuma
gsky malam rumfar bawata rumfar arziki bace, dan
ansha yin ruwan sama tana yacewa, sede abun mamaki
da gari yawaye zan iske anmayar da ita.
Ganin wannan rumfa danayi bakaramin tsoro naji ba,
dan tunda nake gadi rumfata ce kadai agurin, matsawa
nayi abin mamaki malam senaji kukan jariri aciki. Bayan nayi addu,a sena karasa gurin. Inazuwa daga ciki
nahango wata babbar mata me alamun tabin hankali
tana rike da yarinya ahannunta.
Da sallama nashiga gurin, saurin dagowa matar tayi tana kallo na, guri nasamu nazauna, nace baiwar Allah
mekikeyi acikin MAKABARTA kuma hada yarinya
jaririya? Kawai senaga tanamun dariya, malam abinda
na lura wannan yarinyar diyarta ce, dan agabana naga
tafiddo nono tana bata.
Ganin wannan mata bazatayi mani magana ba, kawai
sena fita , cikin rumfata naje nadauko abincin danaje
dashi nakoma nakai mata. Inazuwa na iske yarinyar
hartayi bacci, matar namika ma abinci, segashi ta amsa
tana dariya, zama nayi harta gama namika mata ruwa
tasha, kallonta nayi nace baiwar Allah kozaki bini gidana inkaiki keda jaririyarki? Saurin kallona tayi tana girgiza kai, nace ba cutarki zanyi ba, amma akwai hadari
azamanki gurin nan.
Kuka naga tafara tana kara rike diyarta, haka nayita
lallashinta hartayi shiru, ganin idan nakara mata magana zatayi kuka yasa nafita nabarta. Ganin har magriba tayi duhu yakarayi se tausayinsu yakamani, komawa nayi
nasameta rike da diyarta, sun kwanta. Maganar dazu
nakara yimata. Amma abun mamaki seta samun kuka,
kamar daga sama naji wata murya tafara magana.
Yakai wannan bawan Allah me tausayi, kasani kamar
yanda kayi niyar temakon wannan mata da diyarta,
muma haka muke temakonta, kuma kaci sa,a dakazo da
niyar temako, dan munyi alkawarin duk wanda zezo da
niyar cutar dasu bazamu kyaleshi ba. Wannan mata haka
Allah ya kaddaro mata rayuwarta agurin nan, kuma
tunda ba,a sonta mu muna sonta, dan haka babu wanda
zamu bari yadauketa agurin nan. Kabarta, Allah yana
tare da ita, kuma muma muna tare da ita, amma tunda
kaima mazaunin gurin nan ne, zaka iya temaka mata.
Bakasan komai game da ita ba, mune muka sani, dan
haka munaso kabarta kamar yanda ka ganta, shiyasa
aduk lokacin daza,a kawo wata gawa babu wanda yake
cin sa,ar ganinta.
Malam tunda naji wannan magana na tabbatar ma kaina
lallai ba Bil,adama bane suke magana aljanune, hakan yasa na kyale matar nan, dan sunce basu san na matsa
mata da tambaya, haka muka cigaba dazama a
MAKABARTA tare dasu, yanda suka umarceni kada
infadama kowa, haka nayi shiru ko medakina ban
fadamawa ba, sede yan kayan diyana mata harma dana
medakina idan naga sun tsufa nakan dauka ince mata
wasu zan kaimawa.
Tun ina tsoron zama dasu har muka saba sosai, kuma
ina kokarin bata abinci, sede duk sanda naje inasamu
kamar taci abinci, dayake akwai rafi agaba damu, haka
nasamu bokiti ina kawo masu ruwa ina aje mata, dan
naga ita kezuwa tana dibar ruwan dakanta, kuma acikin
wata karamar robace. Haka rayuwarsu taci gaba da
tafiya, har wannan yarinya tayi wayo, da kaina naje nace tadena bata nono, nadauki yarinyar nafara bata abinci,
daga nan tafara cin abinci.
Aduk lokacin dana tafi daniyar fadama wani wlh malam
dana dawo zan iske bata gurin, setayi kwana 2 ko 3 bata dawo ba, haka suka kara jamun kunne akan inyi hankali,
tunda har aka haifi yarinyar nan agurin to nanne gurin
zamansu, duk ranar dana kara kokarin fadama wani duk
abinda yafaru dani ni najama kaina. Haka na hakura
mukaci gaba dazama, amma harcikin raina na kudurta
sena temaka masu, dan abinda suke masu ba temako
bane, duk da agurinsu suna ganin kamar temakonsu
sukeyi, amma abinda nagani taya za,ayi dan adam
yazauna a MAKABARTA kuma ace anan ze rayu.
Ganin idan nacigaba da matsa masu zan iya rasasu kuma
bansan inda zasu kaisu ba, yasa naja bakina nayi shiru, dannasan wata rana zantemakesu. Haka muka cigaba da
rayuwa, munyi sabo dau sosai, diyarta tayi girma sosai, ganin yarinyar tayi girman daza,ace tafara sanin addinita yasa nace bari infara koyamata daga cikin abinda nasani, duk da nima bawani ilimi mezurfi gareni ba, amma
Alhamdulillahi inada dede gwargwado. Dayake tunbayan
daya kamata ace yaro yafara magana yayi, amma shiru
ita yarinyar wadda Innarta tarada mata Baby, amma
nikuma ina kiranta da yar Baba sbd munshaku da ita
sosai, tun lokacin dana gane bata iya magana, sena lura da idan Innarta tayi mata magana tanaji, kuma nima
haka, tun alokacin nagane yarinyar tanada matsalar
rashin magana, wanda bansan dalilin hakan ba, dan duk
kurman dana sani inde ba harshenshi ne yadatse ba,
zaka sameshi bayaji, kuma baya magana, amma ita nata
seyazo dasabani.
Haka muka rika maganar kurame da ita amma idan itace
zatamun magana, amma idan nine zanyi mata lafiya lau
zanyi tunda tanaji. Dun daga wannan lokacin muka fara
karatu tundaha sarki harzuwa sallah da karatun da akeyi, sede nine kawai nake koya mata, idan bata gane ba,
tanamun alamu.
Mahaifiyarta wani lokaci se inga tazauna tana ta kuka wanda idan tafara batayin shiru seta dauki lokaci, konaje zan bata hkr yar Baba zatamun alamu da in kyaleta,
alokacin da girma yazo ma Yar Baba haka nazaunar da
ita nakoya mata yanda zata gyara jikinta, da abinda zata bari na ibada, da kuma yanda zata tsarkake jikinta idan lokaci yazo. Wlh malam hankalin yarinyar da natsuwarta
kadai ya isa yasa tashiga ranka.
Hatta da kitso wannan matar ita take yimata, sede ita
matar bata bari agyarata, shiyasa idan kaganta zakaga
gaba daya tafita hankalinta. Ko ciwo yasamesu nine nake samo masu magani, amma wadannan aljanu basu barin
ko matar tabar cikin MAKABARTAR, iyakarta bakin rafi,
shima tunda nake dauko masu ruwa tadena fita.
Akwanakin baya nayi rashin lafiya wadda ta tadamun
hankali, banyi tsammanin zan tashi ba, kullum tunanina
yazanyi da wadannan bayin Allah. Inacikin ciwon
nasamu na tafi MAKABARTA gurinsu, haka naje nasamu
Yar Baba duk tarame, kuka kawai takeyi, tana ganina ta
taso da gudu tazo tana murna, alokacin nagane dalilin
kukanta, harta da ita Matar marar hankali seda tayi ta
murna. To malam bayan nawarke kuma nafara tunanin
yanda zanyi, shine nasamu labarinka, nikuma nayi
alkawarin zanzo gurinka, duk da ayanzu bansan wane
mataki aljanun zasu dauka akaina ba, kuma zamuje
musamesu, ko kuwa sun daukesu. Wannan shine babbar
damuwar dana taho ina tunani.
Salati malam yafarayi, da tasbihi jin wannan al,amari.
Gyaran murya yayi yace tabbas Baba kazo da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 13