Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na fito dashi... Batool, neelam da kamal suka hada baki, kee!! Suna nuna jumy da hannu su.. Jumy tayi murmushi, ta kada musu kai, sannan ta mike, tace kuyi decorating dakin, ku shirya masa duk abunda kuke so, zan kawo muku ya ashraf yanzun nan inshaAllah.... Sannan ta fito daga dakin, ta jingine a jikin bango, ta dafa kirjin ta... "Madha afeal alan?"(what do I do now) fuskar ta kamar mai shirin yin kuka... "Hadha alshshakhs almuteajrif lys faqat tafi maei"(dat arrogant person will not jst come with me)..ta daga hannun ta sama, ya rabb ka taimaka min, wannan bawan naka ya yarda ya fito tare dani.... Ta damtse hannun ta, take taji karfi yazo mata, ta fice cikin sauri zuwa dakin nasa..... Sorry I disappointed u yan'uwa, YASH NE TA GANIπŸ˜‚ ~*AFRAH*~ [10/22, 2:35 PM] +234 814 393 3159: πŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”Ž ____________________________ *JUMAYMA* γ€Š ~yar bincike~》 *Jasus* *Spy* Episode~59-60 "Tana kaiwa bakin kofar dakin nasa, taja burki, gaban ta nadan faduwa, ta runtse idon ta, tace,"lets do this jumayma"ta daga hannunta takai kan kofar, tayi knocking. . "Knock...knock. ..knock, shiru ba'ayi magana ba balle ace ta shigo, tadan kai kanta wurin kofar ta kasa kunne ta dan taji ko motsin sa daka ciki, amma inaa shiru ba wani motsi ko kadan. "Ta turo dan bakin ta, arrogant like always, mtsww .. Breath in.. and out.. tayi, sannan ta sadakar, ta murda handle din kofar... Luckily, kofar a bude take..ta kusta kan ta a cikin dakin, tsit ba motsin kowa a ciki, ga wutar dakin a kashe, ko'ina yayi duhu... Jumy ta dinga ware waren idanuwan ta, tana kokarin karasawa ciki.. Sai ganin haske tayi ya mamaye dakin,an kunna wutar, aka ce da husky voice " *mai ya shigo dake nan*?!!!!!!! Gaba daya jumy rikicewa tayi, ta rasa ina zata saka kanta, gaba daya batayi tsammanin yana cikin dakin ba,ta juyo a rikice zatayi magana, sai suuuu...towel din da ke kasan dakin ya kwashe ta.. Gwajab...ta fadi a tsakiyar dakin... Ashraf dake tsaye sanye cikin jallabiyya baka, fuskar sa a daure take tsam, amma ganin yadda jumy ta kwashi kasa... " bai ma san lokacin da Ya kwashe da dariya...hahahhhhh, jumy ta dawo da rau'nannun idanun ta da suka fara ajiye kwalla.. ta kalli ashraf...tunda take dashi yau ne first da ta taba ganin sa yana dariya haka .. (maganar batool ta dawo mata a brain" *kullum rana irin ta yau zaki ganshi cikin bacin rai*") Duk azabar da take ji, a take taji zafin ya wuce..., sai kallon fuskar ashraf takeyi yana kyalkyata dariya harda neman zama kan sofa din dake kusa dashi.... Ta cije light pale pink lips dinta, tayi dan murmushin wahala, tana kokarin mikewa... Ya ashraf! Mai abun dariya anan? Ta fada a shagwabe... Ashraf a take ya daure fuskar shi, ya mike, what? What r u doing here, mai ya shigo dake dakina? Ko batan hanyan kika kara yi?πŸ’πŸΌ Jumy na shirin amsa masa tambayar sa, tayi one step kenan, towel din nan ya sake kwashe ta da kasa suuu...sai gwajab ta sake faduwa dirshen... Bata san lokacin data fasa ihu ba, ooooouchh...ya illahi.. Ashraf ya sake kwashewa da dariya.... Jumy ta dago cikin fushi tace, mugu kawai(bata san ma maganar ta fito ba)...ashraf ya juyo ya kalle ta, yana kokarin tsaida dariyar da yake mata.... Yaganta rashe rashe...yanayin fuskar ta kawai ya tabbatar masa cewa she's really hurt. ... Ya karaso wurin ta, ya mika mata hannu, ta amsa da sauri... Ashraf ya fisgo ta..yayi da mugunta ne , amma saboda he's weak, ranar sau daya kawai yaci abinci... Aikuwa sukayi karo da jumy...sai gwajab suka fada kan bed din dake bayan su... Jumy data runtse idonta, jin sun fadi kan bed kuma itace a saman ashraf, yasa ta bude idonta, ta kalli fuskar ashraf da sauri, ya cije leben sa yana buga hannayen sa a bed din da gani yadan bugu... Jumy ta mike, ta kalle sa, yayi wani shane'shane a bed yana cije cijen lebe.. Ta kwashe da dariya itama..hhhhhh..ashraf ya kallo ta a dan fusace, amma yana kallo kyakkyawar fuskar ta,yadda take dariya, sai ma burge sa tayi, ya sauke ajiyar zuciya...come on, kin kusa kashe ni kuma kina min dariya? Jumy ta daga hannayen ta sama, yi hakuri, ashraf ya mike yana dafe da cikin sa.. Man am darm hungry, cikinsa ya wani yi kara kululu....yana kiran ma'azuu Jumy ta juyar da idon ta, yes! Bari nayi amfani da wannan damar.. Ta dan matso kusa dashi..tace ya ashraf, kana jin yunwa ne? Yadan tabe bakin sa not really. .. Jumy ta rike dariyar dake cinta, uhm da kana jin yunwa ne, dana ce akwai sauran pepperoni pizza din dasu batool suka rage... Ashraf yadan kallo ta da gefen ido, cikin sa ya kara kukan yunwa.. Jumy ta mike, tana shirin ficewa toh ni bara na tafi.., amma addu'ar ta daya ya kirata kafin ta ficen... Kamar daga sama...taji yace, ammm kinaji? Jumy ta juyo da sauri..na'am.. Ashraf yace jeki kawo min pizza din..amma bawai ina jin wani yunwa bane.. Jumy saura kadan dariya ta kufce mata, mutum na dafe da ciki amma yafi admitting yana jin yunwa... Jumy tadan juyar da idonta, bazan kai inda suka ajiye ba, sai dai muje ka dauko da kanka... Ashraf yadan yi shiru nadan wani lokaci...kafin ya mike okay fine muje... Jumy tace yesss!!!! Finally, a zuciyarta... "Tana gaba yana biye da ita, suka zo wuce dakin su tasleem, tasleem na amsa waya ta hango su, ta ja dugun tsaki, village crock... "Dakin batool ta shiga, ashraf ma ya shiga... Dakin yayi dubu, an kashe wutar.. Ashraf na shirin magana, yaga an kunnar wutar dakin... Yeeeeeh...happy birthday ya ashraf..... Batool, neelam, da kamal suka fada a tare.... sai jalal dake tsaye shima yana danna waya... Ashraf yayi tsaye baki a bude...ya kalli jalal ! Man what is all this? ??? Jalal na mutmushi ya daga hannayen sa sama, ask them dem man ya nuna su kamal. . Batool da neelam suka zo suka rungume shi...sai murna sukeyi... "Kamal yayi wa jumy jinjinaπŸ‘πŸΌπŸ‘ŒπŸΌ, tayi murmushi, kafin nan tazo zata fice daga dakin... Jalal ya cafko hannunta, ya girgiza mata kai... Ta juyo a hankali, ta hango batool da neelam sun tasa ashraf a gaba, suna feeding dinshi, snacks. ... "Ranar sunsha party, tasleem ta leko itama, haka ma hanan, data shigo sai ta shiga manne wa ashraf din.. Jumy dake zaune gefe ita da jalal suna magana, tadan kallo su, gaban ta ne yadan fadi, tayi saurin dauke idonta, gaba daya dakin da partyn suka gundure ta..ta mike ta kwace plate ta fice daga dakin, dan tama lura da yadda tasleem ke wurga mata harara.... "Jumy na fita ashraf yabi bayan ta da kallo, hakanan shima yaji hayaniyar ta ishe sa... "Tana zuwa kitchen taji wayan na vibrating, ta kalli kofa taga ba kowa a wajen, sannan ta dauko wayar daga cikin wandon ta. A tunanin ta team leader ne, sai taga ummy dinta ce, ta aiko mata da wani video, cikin zakuwa ta kunna video din... "Wata kyakkyawar balarabiya ce a zaune, sai wani magidanci mai kyawun gaske, yana yanayi da yan nigeria, sai wani saurayi kuma a bayan su" Jumy kwalla ya taro mata a ido, Ummy, Abbu wa akhy yusuf, ta daura leben ta kan screen din wayar tayi pecking, a tare family din suka furta mata *(eyd mawlid saeid habibty)Happy birthday dear*!!!!!...sai video din ya kare.. "Sakin baki tayi, like seriously? Ta manta da yau ne birthday dinta?, ta dafe goshin ta, am also + one today, ta maida wayarta cikin wandon ta da sauri... Tayi sad face, I really miss my family, da ina tare dasu bazan taba manta "yau ne ranar zagayowar haihuwata ba"... Kacab a kunnen ashraf, da karasowar shi kenan bakin kofar kitchen din... "Today is also ha birthday! !! Can't believe, ya saki wani sanyan'yan murmushi...sannan ya daga kansa sama, she helped me yau, na kara experiencing farin ciki a ranar birthday dina, dole ne nima na taimaka mata, na sata farin ciki a yau.... Karasawa yayi cikin kitchen din, jumy najin shigowar shi, ta dawo daga duniyar tunanin ta.. Ashraf ya wani daure, jeki dauko mayafi, akwai aikin da zaki min...bai jira mai zata fada ba ya fice... Jumy ta tabe baki, sannan ta koma dakin su, ta iske ba kowa a ciki, sai hayaniyar su data ji a side din su mami... "Tafiya sukeyi, dare har ya fara yi duhu ya bayyana... Shiru dai ba wanda ke magana, har suka kai wani babban shopping mall, ashraf yayi parking ya fito.. Jumy ta tsaya tana tunanin mai kuma suka zo yi anan? ko shopping zai yi na birthday dinsa, dan taga kashe kudi a wurin kamar shan ruwan pure water ne... Ashraf ya kwankwasa window dinta, oya fito mana, ni bana da time din wasting abeg... Jumy tadan fakaici idonsa, ta murguda masa baki... "Sun shiga shopping mall din, ya mugun haduwa, domin taga sun nufa male section, sai taga ya nufa female. ..tadan tabe bakin ta, sarkin yan'mata... Tsaye jumy tayi kawai, ashraf dake tsaye shima ya juyo ya kalle ta, mai kike jira? Jumy ta kalle sa da mamaki, ban gane ba? Ashraf ya karaso wurin ta, yadan yi mata rankwashi akai, ban sani ba, ya jawo wani dan kujeran zama ya zauna, sannan ya nuna kayan dake wajen, ki dauki komai kike so... Jumy ta ware ido tana kallon shi, yaja tsaki yaci gaba da danna wayar sa.. sai da sukayi 15mins amma jumy ko tsinke bata dauka ba, ashraf ya mike a kule, yayi gaba... Jumy na biye dashi, wurin jewelleries, ya tsaya yace ki dauki abunda kike so, jumy tadan kalli abubuwan dake wajan, duka designers ne, tace ni baana son komai..."jst want to be with you" tayi saurin kauda tunanin nan daga zuciyarta, oh ya rabb I can't fall for him. .. Jawo hannun ta da ashraf yayi yasa tayi saurin dawo wa daga dream world din da ta tafi.... "Jawo hannun ta yayi, ya dauko wani diamond bracelet, mai kyaun gaske... Jumy ta ware idonta, ya akayi yasan tana son bracelets kuma especially diamonds. ...(hhh poor jumy stop dreaming, ya gani ranar mana da kukaje shopping din tafiyar sa Egypt) Zura mata bracelet din yayi a soft hannun ta, ya dago dauke da murmushin da ko shi kansa bai san ya iya saba, ya daga mata gira, yayi? Itama bata san lokacin data mayar masa da martani ba.. Pls idan kunga mistake kuyi ignoring ban samu editing bane ~*AFRAH*~ [10/22, 2:37 PM] +234 814 393 3159: πŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”Ž ____________________________ *JUMAYMA* γ€Š ~yar bincike~》 *Jasus* *Spy* Episode~61-62 "Ka'da masa kai kawai jumy tayi, ashraf yadan ja baya kadan, ya sake dauko wani diamond ring, mai shegen kyau, ya zura mata a finger dinta "hulu jiddan"(so sweet),jumy ta fada a zuciyarta . ashraf na shirin yi mata magana, message yayi popping a wayar dake aljihunsa, ya saki hannun jumy a hankali.... Sannan ya ciro wayar daga cikin aljihun sa ya bude message din.. *Message indox* *from MaMieπŸ“±- _ashraf where do u go dis late?, u should come back home quickly, n pack , kasan gobe morning flight zamu bi_. Maida wayar yayi a aljihunsa, ya dago da hazy eyes din sa, sai kacab cikin chocolate eyes din jumy, data kurawa fuskar sa ido tana kallo, ganin ya kallo ta, yasa tayi saurin dauke idonta, tace uhm muje gida koh? dare yayi... Ashraf ya tabe baki, ya daga kafada, yace muje, yayi gaba, jumy tabi bayansa, tana kara kallon hannunta, tana murmushi... "Sun biya kudin abunda suka siya, daga nan suka wuce mota... " a cikin motar, ashraf nata speeding, a tunanin jumy gida zasuje, but a mamakin ta, sai dai ta gansu a wani exclusive Chinese restaurant. .. Parking motar yayi ya fito, jumy ta saki baki tana kallon wajen, "and how did he know ina son Chinese foods? Woow today is really getting fun... Fitowa tayi cikin natsuwa, tabi bayan ashraf. Table aka nuna musu suka karasa suka zauna, sannan aka kawo musu list din dishes su zaba, ashraf yayi musu ordering simple Chinese glass noodles with black bean soup, sai lemon n orange juice.. Jumy ta shiga kallon yadda aka tsara restaurants din, duk abubuwan da suka yi decorating din wurin, Chinese cultured ne, d place is really amazing, jumy ta fada cike da farin ciki.. Ashraf dake ta faman kallon ta yana murmushi, ya girgiza kansa, juyowar da jumy tayi, ta kalle sa ,yasa yayi saurin dauke kwayar idonsa daga kallon ta. "Waitress din wurin, yar Chinese, ce ta ajiye musu bowls din abunda sukayi ordering, kamshi ya cika wurin, jumy ta bude hanci taja kamshin sosai,"yummy"... "Daukar Chinese sticks tayi (abunda suke amfani wirin cin abinci) harta rike yadda akeyi, sai kuma ta canza da sauri ta daburce... Ashraf da har yayi spoon biyu, ya dago ya kalle ta, sai faman yaki takeyi da sticks din.. Yadan murmusa, sannan ya dauki fork din dake kusa dashi, ya mika mata, iyayi kawai, use wanda zaki iya mana, ta amsa tadan fakaici idonsa, ta murguda masa baki, sannan ta fara cin abincin ta.. "Basu dade sosai ba, jumy ta dago kanta dan yiwa ashraf magana, amma mai... Hango shigowar, wadan nan gangs din tayi, wadan da tayi fada dasu dazu a warehouse..those scary thugs, suna kokarin shigowa restaurant din.. Da sauri jumy ta mike, ta kalli ashraf, muje gida dare yayi fah sosai.. Ashraf ya wurga mata harara, na sani ai, mtsww, ya dauki juice din shi hankalin sa kwance, yana sipping, a zuciyarsa yace,"what is dis lady thinking, zan cinye tane cikin daren nan or what"ya sake jan tsaki.... Jumy da duk hankalin ta a tashe yake, ta daga murya cikin tsawa tace.. ASHRAF KA TASHI MU TAFI!!!!!! Gang leader ya juyo da sauri, sai hango jumy yayi tana kokarin jan hannun ashraf su fice... Ya kalli sauran kattin dake bayansa, su biyu, yace ita ce wancan koh? Suka kada masa kai, yayi nuni da hannunsa, muje...fuskar nan tasa a daure gam, ba alamar imani... "Jumy na kamo maxi hand din ashraf, cikin fusata ashraf ya mike, wai ke miye haka, nace..... Bai gama karasa abunda zai ce ba.. Kattin nan suka karaso cikin hanzari, fisgo jumy sukayi suka rirrike ta...sai fisge fisge take tayi.... Ashraf ya juyo cikin bacin rai, ya kalli wadan nan gangsters din, what d hell do you think you are doing? !!!!!. Ogan yace da husky voice dinshi, STEP ASIDE DUDE! ! Ashraf ya juyo cikin fusata, zai maida wa ogan magana...sai jin saukar wani katako ne hannu ne, shidai bazai iya ma fassara shi ba,yaji kansa, ya amsa, zafi ,radadi, duk suka mamaye masa brain, idon sa ya fara ganin bibbiyu, a take ya sulale kasa a sume...... "Jumy tayi kukan kura...ashraf!!!!!!!..take fuskan nan ta koma ta zakanya... Tasa kafarta ta dake musu kafafu, a take suka sake ta, jumy ta gyara zaman gyelen kan ta, sannan tahau suburbudar wadan nan kattin, ganin she's unbelievable, and also good in martial arts, suka ware cikin sauri... "Da sauri jumy ta karaso wurin ashraf,tana kiran sunan sa cikin rudewa, takai hannunta kan wuyan sa, ta sauke lumfashi mai nauyi, ta sake kai hannu kan kofofin hancinsa, yana lumfashi, ta runtse idon ta ta bude, am a bad person, hawaye suka sulalu mata, I jst put an innocent person in trouble.. "Masu aikin wajen suka taimaka mata, aka saka ashraf a mota.. Jumy ta zagaya wurin zaman driver, ta shiga cikin sauri, ta tada motar suka bar wajen... "Tana driving tana kallon side din da ashraf yake, Allah yaso ta, motar nada computer, zaka iya searching location a nan... Sai da suka kusa isa gida, sannan ta samu gefen hanya tayi parking, lokacin taga ashraf na motsin... "Indo indo!!!! Abunda ya fara furtawa kenan, jumy ta fito daga motar, ta zagaya wurin sa, ta bude kofar side dinsa, ta dago da kansa, tace ya ashraf, gani nan, ba abunda ke damun ka koh? Ashraf na ganin fuskar jumy, ya rungume ta cikin sauri, hope basuyi miki komai ba, hope dey didn't hurt u? Jumy kwalla suka fito daga idonta,"I hate my self for making worried akan abunda baka san ma anyi ba"...ta runtse idonta, yau ne ranar farko data taba, jin quiltiness akan yana yin aikin ta, she's fooling them all, duk ranar da suka taba gane ita spy ce a gidan su....gaban ta ya fadi...ta kalli fuskar ashraf,"I L... Dago da kan da ashraf yayi ne, ya tsaida ita daga tunanin da take... Ya kalle ta, idon sa yadan yi jaa, ya kalli inda suke, da mamaki yace, ya akayi muka zo nan? Dammm, gaban jumy ya fadi, tace uhm uhm, wani wani ne daga restaurant din ya taimake mu, bai ma dade da tafiya ba, ta nuna wani balarabe daya juya baya yana tafiya, ga gashi can ma baiyi nisa ba... "Ashraf ya lumshe ido ya bude, kafin da kyal ya fita, ya koma mazaunin driver yaja su zuwa gida.... ****** Washe gari da asuba, jumy ta fito, cikin sando taje kicin ta bude wa Yash kofa... Ya shigo, suka gaisa a takaice, kafin nan sukayi dakin sufyan safana... _dan plan din da sukayi ranar shine, ashe bayan meeting din da sufyan yayi da jamal casino, daga nan kasar England ya wuce, so da asuba, yash zai zo suje ya bude wa jumy save din_. Suna isa dakin, wurin save din suka nufa, suna yi suna duba bayansu, yash na zuwa, ya gwada password yakai uku,amma all are wrong, can ya jawo ya kalli jumy, agent, what is d name of sufyan's first daughter? Jumy tace hanan, yash yakai hannunsa zai danna hanan, kuma try din sune na karshe... Jumy tace noo yash, wait, not hanan I remember, its tasleem.. Yash ya dannah tasleem, sai '''din...'', save din ya bude.. Yash ya kalli jumy, itama ta kalle sa, sukayi murmushin jin dadi, yash ya dauko files din, ya mikawa jumy, ta amsa cikin sauri, yash ya mike, ya sara wa jumy, is now up to u agent! !! Sukayi dariya, jumy tadan saka hannu a aljihun ta, ta dauko wani business card, take dis yash... Yash ya amsa yace, for.. Jumy tace, u have to leave dis country, go to Egypt my father is a AMBASSADOR there, JUNAID KHATOON... U are not save here, sufyan zai zarge ka.. Yash ya kada kai, bravo agent, thanks alot, jumy tace no need u also helped me.. Sauri sukayi suka fita daga dakin, yash ya fice, jumy ta koma daki, ta iske batool nata kwasar baccin ta, ta karasa wurin kwanciyarta, ta kunna Skype dinta, team leader, am done! !!! Ta fada cike da murna, yayi murna shima sosai, ta nuna masa files din, yace but jumaymah, u cant leave the mansion so early, wait for 2weeks before leaving, jumy ta sara masa cike da farin cikin kammala BINCIKEN[truncated by WhatsApp] [10/22, 2:40 PM] +234 814 393 3159: πŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”Ž ____________________________ *JUMAYMA* γ€Š ~yar bincike~》 *Jasus* *Spy* Episode~63-64 *NIGERIA- abuja******* "Sai da yamma likis, suka sauka, kowannen su na cikin gajiya, dan haka direct daki kawai suka shige. Jumy dakin ta, ta shiga, ta ajiye jakarta dake hannunta, sannan ta tube kayan jikinta, ta fada toilet. Wanka tayi kawai ta fito, ta tsaya a gaban mirror, hannun ta takai kan goshin ta, dan goge ruwan dake wajen, a ta madubin ta hango bracelet da ring din take hannun nata, naga ta saki wani irin murmushi... Tadan lumshe idon ta, ta bude, ta sauke ajiyar zuciya, takai leben ta kan ring din, ta sumbace shi... Zaman dirshan tayi kan gadon ta, tayi mika tana hamma.."ana muttaeab"(am tired)... Ta jawo jakarta, ta dauko wata yar top red, ta saka, ta daura towel din a kugun ta, sannan naga kamar an tsika reta, ta mike tana murna sosai, I can't believe it!!! I just completed my MISSION!!!!.ta nuna kanta, my second mission ....ta daka tsallen murna, ta shiga rawa tana baza gashin kanta tana tsalle tsalle kamar wata karamar yarinya, data samu ice cream a hannu, kunsan dai yara dason kayan zaki.. "Yeeeeh"yeeeh"ana saeid jiddan (am so happy)...ta sauke lumfashi, ta dire a gadon ta "ya rabbih ashkur lak"(ya rabbih I thank you)...sannan ta kwanta, barci barawo yayi awon gaba da ita *GIDAN SUFYAN SAFANA WASHE GARI***** I can't believe this nafeesah...sufyan na gani a tsaye, duk ya rikice, gaba daya ya fita daga hayyacin shi... Mum ta mike tana karairaya, tazo ta jawo hannun shi, come on, sit dear, sufyan ya fisge hannunsa, ya zo ya zauna a bed side, ya goge zufar dake kansa, nafeesa bazaki gane bane, dat Is d only way da nake samun extra cash, and now, ya girgiza kai cikin fushi... Mum ta kalle shi, da dan mamaki dauke a fuskar ta, amma ya akayi files din sukayi disappearing daga save din, bacin tunda mukaje dubai, no one have ever enter your side... Sufyan ya dafe kansa, I know, nasan ba wanda zaiyi karfin shiga, kuma ba wanda yasan ma da save a cikin dakin, but bayan naje England jiyan, sai business partners dina suka bukaci wani item, na kira yash dan ya hau available flight, yazo England da item din, amma sai number dinshi baya shiga... Nabar komai da nake, na biyo evening flight, na dira a dubai daddare, lokacin duk harkun isa nigeria ma, na shiga dakina, naje na bude save din, but nothing is left, duka files din sunyi disappearing. .....muryar shi ta shake, wani kwalla mai zafi ya digo daga idonsa... Mum tace one thing is clear here u knw, *yash* ne ya kwashe files dinnan... Sufyan yayi saurin kallon mum, amma nafeesa what can a illiterate orphan do with those files? Come on it will jst b useless to him. Mum taja tsaki, all those middle class people, they never wish good thing for other people, shegen kishin su, da mugunta, you never know, mum ta yarfar da hannunta a iska. .. Sufyan yaja tsaki, give so,I will surely finished dat bit**ch..wallahi sai yayi regretting din abunda ya aikata.. Mum tadan matso kadan kusa dashi, ta dafa kafadar sa, yanzu dai kasan your business has been stopped, saboda indai ba files din nan u cnt do any business, kuma bazaka iya investigating case din nan ba, dan police sukaji wani abu fishy, asirin mu tonuwa zai yi, why not ka yarda da shawarar dana taba baka,10yrs agoo...ta fada tana kallon fuskar sufyan. Sufyan ya kalle ta, u mean maganar hada jalal da tasleem aure...? Mum ta kada kai, dole ne mu samu wani babban share a cikin dukiyar safwan, kuma aurar da tasleem a family din shine kawai mafita a yanzu... Sufyan yayi ajiyar zuciya, bana jin yaya, mother nake ji, mum tadan ja tsoki, ka cika tsoron tsohuwar nan wlh...kawai kaje wurin yayan direct, kace kana so ayi bikin jalal da tasleem cikin sati daya ko sati biyu hakannan, saboda kaje check up a England, dr yace you hav little time, for living, kasan yadda yayanka ke sonka, he will agree to that, tunda yasan dama kana da heart problem.. Sufyan yayi murmushi, nice idea my wife, ya jawo ta ya rungume ta suna dariya a tare.... "Yaya kaji dai abunda doctor ya fadamin, _sufyan ke fadin haka, a halin yanzu zaune suke da safwan safana a garden din gidan sa,_. Safwan ya dafa sufyan, brother kabar sa damuwa a ranka, akan ciwon nan, damuwar da kake ne yake sa ciwon naka yana tsanani, Allah kadai yasan lokacin mutuwar bawan sa, doctors are jst guessing. Sufyan ya saddar da kai kasa, yaya akwai abunda ya kawo ni, nake so na roke ka? Safwan ya ajiye cup din hannunsa, what do want? I will surely give u idan har ina da hali.. Sufyan yace, dama zumunci ne nake so mu hada, ina son ganin farin cikin yarana kafin nabar duniyar nan, safwan yace kabar maganar nan sufyan, sufyan ya dago kansa, yace yaya inaso ne mu hada jalal da tasleem mu aurar dasu.. Safwan yadan kalli sufyan da sauri, zamu aurar dasu sufyan, amma ai sai shi jalal din ya samu mata , hakama sai tasleem ta fito da miji koh.. Sufyan yace ba haka nake nufi ba, ina nufin mu hada su aure, kaga zumunci ya kara kulluwa kenan.. Safwan ya murmusa, ba damuwa, jalal mai biyayya ne, kada ka damu, sufyan yayi mirmushi, amma yaya bikin ina so ayi shi nan da sati biyu... Safwan ya girgiza kai, sufyan ka cika sama ranka damuwa I jst finished telling you fa, Allah kadai ne yasan lokacin da bawa zai ja lumfashin sa na karshe, anyway toh shikenan Allah ya kaimu.. **** Abunda yasa na kira ku nan, shine, mun gama yanke shawara ni da uncle dinku, zamu hada ku aure... _jalal, tasleem, mamie da grany ne zaune a babban falon safwan_. Da sauri jalal ya dago kansa, ya kalli daddy dinsu cikin mamaki , aure daddy? Daddy yace eh aure our lawyer, nasan duk cikin ya'ya na kafi daraja ni , nasan kai mai biyayya ne, Allah yayi maka albarka.. Mami tace amin, grany tace zumunci nada kyau , naji dadi kwarai da kuka yi tunanin yin hakan, Allah ya raya min ku, ya kuma kare mun ku daga sharrin mahassada... Daddy yace amin, kuma mun yanke shawarar, nan da sati biyu za'a daura auren.. Mami tace da sauri haka? Grany tace sati biyu kamar muna korin su.. Daddy yace muna da reason din saka shi kusa, tasleem data duke kai, sai mirmushin murna take, Allah kawai take gode ma, ya bata rabin ranta.. Shi kuwa jalal, maganar daddy ba karamin tada masa hankali tayi ba, mikewa kawai yayi yabar falon ransa a dakule. ~*AFRAH*~ [10/22, 2:42 PM] +234 814 393 3159: πŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”Ž ____________________________ *JUMAYMA* γ€Š ~yar bincike~》 *Jasus* *Spy* Episode~65-67 "Yana fitowa daga main house din, ya hango neelam da jumy a garden, suna zaune, sai dariya suke kyalkyatawa, ya kurawa jumy ido yana kallon yadda take darawa, tana yiwa neelam gwalo, yaja lumfashi mai zafi, yaji wani abu ya tsaya masa a wuya, a fusace ya fice zuwa dakin sa. "Neelam,ta kalli jumy, kinsan ko, akwai wani American movie da muka kallah last month , its a SPY film, gaban jumy ya fadi.., neelam tace its very interesting fah, but..gaskiya aikin is dangerous, kuma mutum zai ringa zaman rashin gaskiya da mutane... Jumy gaba daya taji, zufa ta keto mata, batool ce ta karaso wurin su rike da waya a hannun ta _sanye take cikin skirt din atamfa sai top_, ta samu wuri ta zauna, neelam tace yauwa ya batool kin tuna wannan spy film din nan da muka kalla da grany ranan... "Batool tadan yi tsaki ta juyar da idonta, spying is not good at all..., kamar fa leken asirin wani ne, kuma kinsan bad side din shi, neelam tace noop, batool tace, suna boye identity dinsu ne... Neelam ta dan tabe bakin ta, tace, harfa komawa sukeyi house helpers kawai dan kawai suyi spying mutane...har indo kana iya jin wai itama spy dince, neelam ta kashewa batool ido...koh indo?..neelam ta rike dariya dake cin ta.. Jumy ta dago da sauri ta kalli neelam, a'a wallahi ni ban ma san miye supai ko suusupay kuke cewa.. Neelam ta kwashe da dariya, cool down indo, nasan ke bazaki taba zama spy ba, spys are very unique... Jumy bata ma san lokacin data mike ba, gaba daya yanayin ta ya canza, sai zufa dake keto mata, fuskar ta tayi pale.. Neelam tace, ha'an indo muna labarin mu zaki wani tafi? Batool tayi crossing legs dinta, haba neelam kinsan fa halin su ya kamal da tsiwa...jumy tace uhm uhm lokacin aikin na ne ma yayi ne, ta fara tafiya cikin sauri dan bata ma so neelam ta tsaida ita... "Tana jin lokacin da neelam tace, ai spys dinan ki barsu, ji fa a film din, d spy fooled a family, by using d identity of a sweet sixteen.

Chapter 8 of 12