Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mai santsi, da taushi, dan ba karamin kashe wa kansa kudi yake yi ba_. Ya sosa kan nasa, yana sauke ajiyar zuciya, can kuma ya mike, ya nufi karamin fridge din dake dakin, ya bude, ya dauko whisky dinshi, ya dawo ya zauna kan bed din. Mtswww she's a ordinary house help, ya dan mari kumatunsa, come on ashraf, mai kake shirin jawo wa kanka, da girman ka, da irin level dinka, mata na rushing dinka, _zuciyarsa tace masa"amma kake kishin yar aikin ku"?_ da sauri ya girgiza kai, bana kishin ta, ba zan taba kishin taba, ya daga kwalbar wisky dinshi, ya shiga kwan'kwada, yana yamutse fuska, dan yadda giyar ke sauka a makoshin sa, yana zafi. Koma wa nayi wurin tasleem, tana kwance a dakinta, tana chatting tana shan fruit hankalin ta a kwance. Jumy tayi sallama ta shiga, tasleem ta juyo ta kalle ta, ta yamutsa fuska, har kin gama aikin dana baki ne? Jumy ta kada kai, ya tafi, tasleem ta kada kai, ta koma ta kwanta, jumy tace ga kayan, tasleem ta watsa mata harara, kije dasu kawai.jumy ta dan murmusa, nagode, sannan ta fice, tasleem tabi bayan ta da harara. A kicin naga jumy na wanke vegetables, _bayan ta canza kayan ta, ta koma ta kwashi pappers dinnan, sannan ta koma kan aikin nata_ Jalal ne ya shigo kicin din, jumy ta juyo ta kalle sa. Yana daga bakin kofa, yace yau kiyi min rice pudding. Ya juya zai fice, jumy tayi saurin tsaidashi, ya jalal kuyi hakuri... Jalal ya tsaya amma bai juyo ya kalle taba, ta kara da cewa, nasan banyi dai dai ba, bai kamata na bar aaikina ba, naje wurin wani ba. Jalal ya juyo dauke da murmushi, ya girgiza mata kai, nasan ba laifin ki bane, so, kada ki damu, huh ya fada cikin raha. Jumy tayi masa murmushi itama tace toh. Yana fita, taji wayar kicin din na ringing, taje ta dauka, tace yes? Muryar ashraf taji cikin maye sosai, you cant never ever have a place in my heart, understand! ? Ya fada cikin tsawa.. Jumy hankalinta yadan tashi, ta ajiye wayar da sauri ta fito daga kicin din, ta nufi dakin nasa. ********** A kwance shabe'shabe ta iske shi, a kasan gadon, yana ta wurna kwalbar giyar sa...duk dakin ya hargitse... Jumy ta karaso wurin sa, kana lafiya kuwa? Ashraf ya dago idanunsa da sukayi jaa, kamar wasu chilly pepper. Yana ganin ta, ya kwashe da dariya, ya dago hannunsa, ya kai kan kumatun ta, jumy najin soft hands dinsa a jikin ta, tayi saurin kauda fuskarta... Ta mike, ta mika masa hannu dan ya tashi, ya riko hannunta, amma domin ita ta dago shi, sai shine ya fisgo ta...ta fado a kansa... Da sauri ta dago manya'manyan idanunta, ta kalli fuskar ashraf din, ya lumshe idonsa ya bude, ya kurawa kwayar idonta kallo,sai da yayi seconds bai kyafta idon ba. Jumy tayi kokarin mikewa, amma ashraf ya rike ta gam a jikin sa... Ya fara magana cike da maye, u can't win my heart, ya nuna zuciyarsa, ur not my type at all, yasa yatsan sa yadan daki goshin ta, u r jst a no body, but a village house help, sai kuma yasa hannunsa ya rufe bakin sa, oops sorry ya kwashe da dariya. .. Jumy ta girgiza kai, cike da takaici, tazo gidan nan ne dan tayi BINCIKE, but look, ta juyo ta kallo ni AFRAH, *LOOK AFRAH, am here nursing a drunkard*, ta kalli ashraf daya yi passed out, kansa kan bed dinsa yana sharar barcin sa... Am so so so much tired of being here, ta fada a fili, its sucks! Ta mike jikin hanzari.. Da kyal ta iya, kinkimar ashraf ta maida shi kan bed, ta rufa masa bargo, sannan ta gyara masa dakin ta fice. Da sauri ta kammal aikin ta, ta koma dakin ta, tayi wanka, ta dauko pappers dinnan taci gaba da manne su wuri daya.... Har kusan karfe 11 tana aikin hada pappers dinnan.. kanta duk ya dau zafi. Ring ring, wayarta ta hau kuka, tasa hannu cikin kasala ta dauki wayar... Ummy daga dayan side din, tace, my daughter, wani irin sanyi ne ya ziyarci zuciyar jumayma, my ummy, ummy tace, hayyaty, hope your fine? Da muryar damuwa tayi maganar. Jumy ta sauke ajiyar heart, ummy am fine alhamdulillahi, n you wa' abbu? Ummy tayi mirmushi tace we r all fine, amma muryanki sounds some how, tell my child mai ke damun ki? Jumy ta sauke lumfashi, ummy help me with Du'as. Ummy tace, my child, u should always, make time n talk wit ur creator, Allah mai taimakon bayin sane, duk lokacin da muka bar kusantar ubangijin mu, bazamu taba samun kwanciyar hankali ba, and ur work needs all dat my child. . Jumy taji wani kwanciyar hankali ya sauko mata, tasan kam yanzu bata wani yin ibadah yadda ya kamata, gashi dama gidan da tazo, basu damu da bauta wa ubangiji yadda ya kamata ba, ita mutum daya taga yana zuwa masallaci a gidan (jalal), tayiwa ummy godiya kafin sukayi sallama. A daren sai da jumy tayi sallar nafila, kuma alhmdllh, taji zuciyarta tayi sanyi. Washe gari kuwa, wani karfi taji kamar an kara mata, ta daga hannu tayiwa Allah godiya, "I will always be grateful to u ya rabbih" A hankali ya fara bude idanun sa, idonsa yayi masa wani irin nauyi, da kyal ya iya dan bude su, biji, biji ya fara gani, kafin ya wartsake... Ya mike, dafe da kansa, da yayi masa nauyi... What really happened? Yake tambayar kansa, cos duk ya manta abunda ya faru jiya... Ya dan runtsee ido yana kokarin tuna abunda ya faru, amma memory deleted, sai ma ciwo daya ji kansa na niyyar farawa... Ya mike da kasala a jikinsa sosai, ya shiga toilet ya watsa ruwa... Ya gama saka kaya kenan, akayi knocking kofar dakin nasa.... " *include me in ur du'as*" *love you all honies* ~*AFRAH*~ [10/22, 1:37 PM] +234 814 393 3159: πŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”Ž ____________________________ *JUMAYMA* γ€Š ~yar bincike~》 *Jasus* *Spy* *By* *AFRAH* episode 45-46 *Salamu'alaikum readers, thanks so much for reading dis story of mine, jazakhallahu'khairan* *Jiya am so sorry nayi mistake wurin numbering din,42-43 ne* ******** Washe garin ranar, duka family din safwan safana d millionaire, suka nufi airport, a luxurious motocin su. Bayan duk an shiga jirgin, jumy ta karaso wurin da batool ta nuna mata, a matsayin wurin zaman ta. Ashraf ta gani a wurin shima a zaune, ya lumshe idanunsa, ya saka air piece a kunnensa. Jumy ta tsallaka, dama side dinta ne wurin window din, ta zauna tana sauke lumfashi. Ashraf najin zaman mutum kusa dashi, yayi saurin bude idonsa, yana juyowa gefen sa, hazy eyes dinsa suka sauka cikin chocolate eyes din jumaymah.. Kallon ta yayi, na wani dan lokaci, kafin ya dauke kansa. Aka fara yiwa passenger's, magana, ana basu instructions, na yadda zasu saka seat belt cos jirgin na niyyar tashi. Jumy harta fara niyyar sakawa, sai kuma ta tuna, da sauri ta fara kiciniyar, yadda zata saka seat belt dinta. Ashraf yadan kallo ta da gefen idonsa. Yaga sai battle takeyi da seat belt din, yadan yi tsoki, mtsw, sannan ya kar'karto ta, ya mikar da hannun sa, yasa yatsun sa ya dago nata hannun ya ajiye akan cinyarta. Ya saka mata seat belt din.. Jirgi ya fara motsawa, nan ma jumy ta runtse idonta gam, ta runtse hannayen ta, ita a dole tsoron tashin jirgi takeyi.. Ashraf na ganin ta, yayi dariya a zuciyarsa, poor thing, her first time I knw. Jumy najin yadda jirgin ke motsi, *but seriously afrah, normally ina jin tsoron tashin jirgi ba tun yau ba* _jumy ta fada min ni afrah_ Bata yi wata'wata ba ta karkata, wurin ashraf, ta kamo, gefen hannun sa, ta rike shi gam idanunta aa runtse gam.. Ashraf ya juyo da sauri da niyyar yi mata fada.. But sai ya shagala da kallon kyakkyawan fuskarta mai kayar caramel , _she's really cute ya fada yana kura mata ido, with those long dark lashes, with cute nose dat fit ha face, her dusty pink lips, yana kokarin shafa fuskar nata, ta yunkura, ta gyara zaman ta, ta juyo ta kalle shi, kayi hakuri...ya juyar da kansa kawai. Ya jalal, hope zamuje yawo sosai a dubai, idan mun isa,koh? _tasleem ke tambayar jalal dake gefen ta yana duba wani book a hannunsa_ of course kawai ya iya ce mata. Yadan tabe baki, tasleem s ta juyo suka hada ido da mum, mum tayi mata nuni da ta ci gaba da masa firan. ************* *DUBAI* Da yamman dare suka iso dubai, motoci ne manya manya, suka zo daukar su. _dan safwan da sufyan safana suna dubai din ma su jun jiya, _dan jumy taji jalal yana waya da daddy dinsu, lokacin da taje kai masa usual dinsa"coffee"_ Wani babban gidane, naga an shiga dasu, woooooow na furta dan ba karamin kyau gidan nan gare shi ba....na saki baki na shagala da kallon wannan gida... Jumy dake kokarin fitowa daga mota, ta karaso wurin na, ta saka hannu ta rufen bakin. _control afrah, kin manta ne, family din millionaire safwan safana ne fa...oops I see_. Sun shiga cikin katafaren gidan, mai dauke da golden brown tiles a kasa, da manya manyan riyal chairs, yabulen golden n purple ga flowers ko ina fresh fragrance ya cika ko'ina... _*kuyi imagine any most beautiful gida da kuka bata gani*_. Mami ta kalli tasleem, remember, dakunan ku a second floor by right, sannan ta juyo ta kalli jalal, ku kuma naku a third floor, nafeesa muje dakin mu koh, mum tace gaskiya kam dan na gaji dayawa, sukayi hanyar dakin nasu a kasa. Grany ta kalli jumy dake tsaye, tace ita indo sai ta zauna a gidan batool ko tunda neelam da hanan zasuyi sharing nasu... Batool tace ta zauna dani no pee pee, tasleem ta tabe baki ta haura sama, mami na tafiya tace okay kowa yace ya kwanta its late. Jumy ta shigo purple room din batool, ba karamin kyau dakin gare shi ba. Batool dake zaune a bed side tana kokarin saka night wears dinta. Indo zo ki amsa, I totally forgot ne ma..tace wa jumy dake tsaye. Ta jawo bag din dake kusa da gadon, grany tace na baki wannan.. Jumy ta karasa ta amsa, ta zauna a kasan carpet, ta bude bag din. Gowns ne masu kyau, just irin wadan da grany din ke yawan saka wa ne, sai set din kayan barci. Jumy ta washe baki, kai gaskiya nagode sosai, Allah ya kaimu gobe lafiya, nayi mata godiya.. Batool tayi murmushi, tana kokarin ciro wayarta daga jaka, dake ringing. .. Jumy ta mike ta canza kayan ta zuwa na barcin, riga da wando masu santsi, sannan ta shiga ta dauro alwala. Batool ta ajiye wayar hannun ta, sai kuma ga call ya sake shigowa, tayi dan tsaki, hanan din nan ko she's a total a parrot. Tana dauka taga, number din jalal ne,ta saita kanta kadan, tace hello bro, okay yanzu kuwa, ta ajiye wayar. Indo! Ta kira jumy dake gyara zaman kayan su a dakin, ta saka hijabi da gani space din sallah take nema. Na'am ta fada tana juyowa, batool na gyara kwanciyarta, tace ya jalal yace ki kai masa coffee, jumy tace toh amma ina ne kicin din? Batool tace uhmπŸ€” floor din kasa ne, kije ta wurin dinning akwai kofa a wurin nan ne, jumy ta kada kai ta fita, bayan ta sa hannu ta gyara zaman hijabin ta. Ta sauko kasa cikin sauri, amma kasan yayi duhu sosai, sai lalube lalube takeyi,inda zata ga switch din wuta ta kunna. Ganin ba'ta wa kanta lokaci takeyi, yasa ta lallaba, har ta kai wurin kojerun falon, bayan ta wuce kujera daya... bata san akwai wata kujerar ba ta wurin, ta taho cikin karfin ta, sai.....gwajab, ta fadawa kujerar.... "oooooouuuchhhhhhhhhh taji muryar da batayi tsanmani ba...... *Allah ya baki lafiya my unnie munay, includes ha in ur du'as pls* ~*AFRAH*~ [10/22, 2:11 PM] +234 814 393 3159: πŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”Ž ____________________________ *JUMAYMA* γ€Š ~yar bincike~》 *Jasus* *Spy* *By* *AFRAH* Episodes 47-48 "Bayan kowa ya haura sama, dan yin barci, ashraf ya haura shima zuwa dakinsa. " ba karamin haduwa dakin yayi ba, shi kadai ke da balcony a cikin duka na third floor din. "yayi wanka, ya fito ya sanya jallabiyar sa brown,sannan yayi sallah(oh oh jumy ina kike,) "Yana kammalawa, ya zauna kan bed dinsa, yaji gaba daya bayajin barci, wayar sa ya dauka dake kan bed din,ya fito zuwa falon kasa. " ya kwanta a kujera yana chatting da friends din chilling dinsa, a haka har barci ya fara daukar sa.. Cikin barcin nasa, yaji wani abun mai taushi, hade da nauyi ya fado masa a jiki, "ooooouccchhhh !!!ya furta yana cije leben sa, wayar sa ya jawo data fadi ta gefen sa,... Back*** "Wayarsa ya jawo cikin sauri, ya haske fuskar jumy, sai kyafce'kyafce takeyi da ido, dan hasken ya kashe mata ido sosai, kuma bata ganin fuskar wanda ke hasko tan. Yunkurawa yayi, daga kwancen da yake, jumy ta mulmulo kasa ta fadi, hasken wayar ya haske su, ashraf ya girgiza kai yana zuyar da idonsa. Mai kike yi anan? Jumy ta mike tana rike da kugun ta, kitchen nake nema. Mtsww ya mike ya kunna mata wutan wurin, sannan ya koma ya zauna abunsa. Tana ganin kofar da batool ta fada mata, ta bude ta shiga. Bata sha wahala wurin neman abubuwan hada coffee dinba. Tana cikin daura cup din a kan tray, taga hasken motoci, daga window din kitchen din suna karasowa wurin.... Ta kalli gabas da yamman ta, sannan ta matso kusa da window din, ta bude kadan ta leka.. Motocine guda biyu, sukayi parking ta wurin window din kicin din, ta bayan gidan kenan. Wasu mutane ne, arabs, sanye cikin bakaken jallabiya, jumy ta ajiye cup din hannunta , ta bude kofar kicin din a hankali tana kallo bayan ta, dan kada ashraf yaji motsin ta. Tana fitowa ta shiga bin wadan nan mutane, wani wuri taga sun shiga kamar dai garden amma akwai building, ciki suka shige, ta lallabo cikin sauri, ta karasa, ta window din ta leka su, *sufyan safana* ta hango cikin manyan kaya, zaune shi da wani guy a kusa dashi.. Business sukeyi da wadan nan arabs din.. Jumy ta dan lashi leben ta, ta daga hijabin ta, cikin wandon barcin ta, akwai wani wandon karami mai aljihu, ta saka hannu a ciki, wayarta ta dauko, dan kullum da wayarta take yawo.. Ta kunna ta saita ta wurin window din tana daukar su video, a cikin jakar taga sun fito da wasu ledoji, da farar hoda a jiki, jumy ta ware idonta, sai jin daya daga cikin arabs din tayi, yana cewa, its really great doing business with you *SAFWAN SAFANA* ta kara matsowa cikin hanzari, sai taga Sufyan ya murmusa, ya mikawa arab dinnan hannu, my pleasure. .. Jumy taja baya kadan, MADHA! Wat? Is dis, uncle sufyan, safwan kuma, tana cikin tunanin nan, taji suna niyyar bude kofa su fito... Da sauri ta gudu bayan wurin, tana leken su, taga arabs din sun wuce, sufyan ma yabi wata rare door dake bayan gidan, cikin wasu flowers, wannan saurayin a bayansa dauke da bags din, suka fice. ... What is she still doing?, har yanzu bata gama bane?. _ashraf ya fada haka yana hamma, ya zauna harta fito, dan yaga bata san gidan sosai ba, kada ta kara bace wa aciki, amma shiru shiru har yanzu_ mtsww why am i even bothered about her? ya mike ya nufi kitchen din cikin kasala... Lokacin jumy ta fito daga boyon da takeyi, tayi saurin karasawa kitchen din, tana rufe kofar,"mai kikeyi har yanzu!" Muryar ashraf taji a bayanta.. Ba karamin tsorata tayi ba, ta juyo da sauri ta jingine da kofar tana sauke lumfashi, wayarta dake hannunta, tayi saurin cu'sa ta cikin wandon ta... Ashraf yaja tsaki kadan, kizo ki tafi! Munafuka, ta juyo tace tooh gabanta na faduwa, ta dauki cup din coffee dinta ta fito.. Suna haurawa sama, yana gaba tana biye dashi, suna kaiwa second floor, ya juyo ya kalle ta, ya nuna cup din hannun ta, for ya jalal, ya tambaya? Ta kada masa kai, ehh, ya miko hannun sa, kawo na kai masa, its late nw kije ki kwanta kema... Tana mika masa, hannun su ya hado dana juna, ta dago idanunta, mai kalar barci, ta kalli ashraf din... Shima ita yake kallo, a take sukaji wani sanyi ya ratsa su , at once kuma sanyin ya fice, ta lumshe ido ta janye hannayen ta, ashraf ya amsa ya juya shima, gaban sa na bugawa bum! Bum! Bum!.. Tana komawa daki taga batool harta kai Germany, ta girgiza kai,Allah yasa ma tayi sallah. Sallaya ta dauko cikin kayanta, ta shinfida tayi sallah, sannan ta dauko wani babban bargo, da ta gani a cikin wardrobe, ta shinfide shi a kasa, ta kwanta.. "Lumshe idonta tayi, sufyan safana, safwan safana, who among them am I supposed to investigate? Ta bude idonta, ta jawo jakarta, wasu papers ta dauko, its clear anan, safyan safana has invested in *JAMAL casino*, and jamal casino, suna cikin black list na harkoki da kayan maye,419 n rest. Ta dauko wayarta, and here, Sufyan safana in other hand, dealing with drugs, ohhhh rabb, ta saka hannayenta cikin gashin kanta, am freaking out! Ta shiga rubutawa team leader dinsu, reports, bai jima ba ya turo mata reply. " *investigate SUFYAN SAFANA* ta runtse idonta, oohs this is just complicated. Washe gari da safe, mami da mum suka hau hidima, ordering din abinci sukayi daga wani 5 ster hotel, kusa dasu. hanan , batool, neelam, tasleem sun fita jogging da ya kamal.. Jumy kuwa na third floor tana gyarawa j.k.a, dakunan su. Ta gama na kamal , sannan ta shiga na jalal, ta iske shi yana karanta wani book, sunsha fira kafin ta fita, ta shiga dakin ashraf.. Yana zaune yana sarrafa computer, ta zo ta fara linke kayan dake saman kujerar dakin.. Important work yakeyi da computer, amma zuciyar sa sai ingiza shi takeyi, ya juyar da idonsa, sashen da jumy take, aikin ta takeyi, ya kura mata ido yana kallo.... "Wait have you complete fall for ha?" Zuciyarsa ke tambayarsa wannan question din. "No! Allah ya sawake she's a house help fah" "Den y are u looking at her wit so much emotions"haha daz love " Ya girgiza kan sa, ya mike kamar wanda aka tsikara, ya bude kofa ya fice, abunsa. Jumy tabi bayan sa da kallo,"ooh ya rabb not him please"ta fada a zuciyarta,"ana ghyr qadir ealaa al' hubh hdha alsh shakhs" bazan iya son wancan mutumin ba, ta yamutsa fuska, nt my style at all... ~*AFRAH*~ [10/22, 2:18 PM] +234 814 393 3159: πŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”Ž ____________________________ *JUMAYMA* γ€Š ~yar bincike~》 *Jasus* *Spy* *By* *AFRAH* episode~49-50 " *After the sallah, chop the meat, d meat d meat" LOLS HAPPY SALLAH to all of you, my SWEET HEARTS muah, hope kowa ta ajiye min naman sallah nah*?πŸ€” "Tana kammala gyara masa dakin, ta sauko kasa dauke da towel din datake goge goge a hannun ta na hagu. Grany, mami, mum suna zaune a manyan kujerun dake falon. Sai ashraf dake kwance a kujera shima yana kallon tv, pretty little liars. "Indo break dinki yana kitchen _mami ta fadawa jumy dake shirin shigewa kitchen din_ Toh mami, ta fada a sanyaye, mum dake latsa waya ta watsa mata harara. Tana gama cin abincinta, ta fito daga kitchen din, tazo wurin grany ta zauna daga kasa, tayi mata godiyar kayan data bata, grany ta shafa kanta, tace ba komai indo, tashi kije ki huta kema, nasan yau kinsha aiki. Jumy tayi murmushi, sannan ta mike tana shirin daga kafar ta.... Su hanan,batool, neelam, kamal, da tasleem suka shigo gidan a gajiye, _ko waccen su na sanye cikin, wando blue da riga dark pink, ba dankwali, sai de sukayi parking gashin su_. Hanan data fada kujerar da ashraf yake a kwance, kan jikinsa ma ta fadan, ta sauke ajiyar zuciya. Swt bro morning, ta fada a gajiye, ashraf ya mike yana kokarin zama, hanan ta jayo hannunsa ta rike gam a cikin nata.... Kamal ya zauna kusa da grany shi da tasleem, sai batool dake zaune a one seater sofa, neelam na tsakiyar su mum da mami... "Mami yaushe su daddy da uncle sufyan zasu iso ne? _kamal ne ke tambayar mami, yana latsa wayarsa_ Mum tace, by 2 to 2:30, suna hanya ma, kamal yace, sharjah is far from abu dhabi kenan? Mum tace no flight zasu hau, dan akwai meeting din da zasuyi a nan. Mami ta mike tana cewa,ina jalal yazo na aike sa, tayi hanyar haurawa sama.. Grany dake zaune kusa da kamal, ta yamutsa fuskarta, kamal ya juyo ya kalle ta, ke kuma fah, grany ta toshe hancin ta, dan Allah kuje ku watsa ruwa, haba daga shigowar ku sai gidan ya dau warin zufa," Gaba dayan su suka kallo grany, tasleem ta mike ta kalli jumy dake son haurawa sama.... _tana niyyar tafiya su kamal suka shigo, taga hanan ta fadawa ashraf a jiki, hakanan taji zuciyarta bataji dadi ba, balle da hannan din ta rikewa ashraf hannu, "ohh ya rabb what am I doing "? Ta hade miyau kut, sannan ta nufi haurawa sama_. Indo!!! Tasleem ta kira ta, jumy ta tsaya ta juyo, tasleem tace, kije ki kawo mana juice, jumy tace toh ta nufi kitchen din, a sanyaye, dan taso taje ta rubuta report akan sufyan safana, what !mutumin data gani jiya, yanzu taji ance zai dawo tare da safwan daga sharjah such a 2face liar! Orange juice mai sanyi, ta zuba a cups ta daura a tray, sannan ta fito falon. Kowa tabi ta kaiwa, saura hanan, hakanan taji bata son kallon inda suke ma.. Hanan tace, you please hurry, jumy kafafun ta na rawa, ta damtse hannunta, dan ta samu karfin karasawa. Idonta na kallon carpet din kasa, ta taho cikin sanyin ta, bata lura da takalmin hanan dake ajiye wurin ba.... Sai dai taji tayi tuntube, ta tafi suu.... Saii gwajab saman ashraf tayi masauki, juice din hannun ta, ya zube masa a white shirt din dake jikinsa.. Gaba daya kallo ya dawo wurin su.. A tsorace jumy ta mike, hanan ma ta mike a fusace, ta daga hannu ta wanka wa jumy mari... Tasleem dake zaune tana sipping juice dinta, tayi crossing legs, ta kalli mum sukayi murmushi a tare. What! Bakya ganine or what? Hanan ta fada, tana zarewa jumy ido. Ashraf ya mike shima, fuskar sa a daure ya wuce fuu... Hanan ta harari jumy sama da kasa, sannan tabi bayan sa. Mum tace, kee sai ki wuce ki bawa mutane wuri koh?stupid kawai. Grany ta girgiza kai, ta matso kusa da kamal,tace, indo bata da laifi ko? Kamal ya kada kai, tsautsayi ne ya juyar da bakinsa gefen su mum, suka kalli juna da grany, sannan suka mike suka bar falon. "Jumy daki ta koma ta zauna a kasan gadon, ta daura kanta saman cinyarta, wani hawaye taji yazo mata, she hav never been humiliated like dis, for crying out loud, just look at d kid, ta runtse idonta hawayen dake ciki suka sulalu.... Batool ce ta shigo dakin,ta karaso wurin ta, ta dafa kafadar ta, tace, a sanyaye, "sorry indo", jumy ta dago ta kalle ta, ta sakar mata murmushi. "Swt bro, sorry, dont mind the bitch. _hanan ta fada tana karasawa cikin dakin ashraf_. Ashraf dake cire rigar jikinsa, ya juyo idonsa yayi jaa, ya kalli hanan a fusace, why do you slap ha!!!? Did I asked you too? Or is it ur body? Hanan ta saki baki tana kallon shi.. Common swt....zatayi magana ya katse ta, leave please! Am not in d mood now.. Hanan zatayi one step ta karasa wurin sa, yace a fusace "leave"! Ta daga hannayen ta sama, ta juya a kole ta fita.., ta sauke ajiyar zuciya, I must surely teach that bitch a lesson! !!!. Su daddy sun dawo, duka family na babban falo, suna fira da dariya, ana ta ciye ciye, jalal ya mike, dauke da plate din samosas, ya sulale ya fice, tasleem kawai ce ta lura da fitan nasa, sai ashraf... A dakin batool ya samu jumy, ta gama sallame sallah kenan, ya zauna kan bed din ya jira ta shafa addu'arta. Mi'ka mata plate din hannunsa yayi, jumy ta amsa tana murmushi. "So ya yau din, boring I know koh? Jumy ta gyara zaman ta, yeah ta fada tana niyyar saka hannu ta dauki samosas, _yanzu jalal yana mata turanci wai dan ta kara kwarewa_. Yayi murmushi, na sani ai, by looking at ur pale face. Jumy ta juyar da idonta, jalal ya mike yana cewa, zanje amso sakon mami, we will talk later, jumy ta sakar masa murmushi tana tauna samosas din dake bakin ta... Bayan ta gama cin samosas dinta, ta fito dauke da plate din a hannun ta, wata hanya ta gani tayi gabas straight, dama tunda suka zo take ganin wurin a rufe, bt now a bude ta ganshi... Ta juya ta kalli bayan ta, ba kowa a wurin tsit, sannan ta bi wannan hanyar nan, ta daura plate din hannunta saman AC din dake wurin.... Wani kofa ta gani, a jiki ansa sufyan master bedroom, ta juyar da idonta gefen ta, ba kowa ta wurin ma, sannan ta bude a hankali ta shiga... Dakin is undescribable, babban gaske ne, yaji kayan more rayuwa sosai... Batayi wata wata ba, ta shiga BINCIKEN duk lakoki da files din da ke dakin... Ta saukar da ajiyar zuciya, ganin duk files din dakin shirme ne, ta tsaya a tsakiyar dakin, ta rike kugun ta, idonta ya hango mata wani" save" babban gaske, ta karasa wurin shi, ta shiga gwada password amma inaaa duka is incorrect. .. Motsin bude kofa taji daga bayan ta... Hancin cikin ta suka motsa, ta mike da sauri daga wurin "save" din ta zo wurin wani labule babba, ta daga da sauri ta shige bayan sa.... Ana bude kofar......... Bata ankara ba, taji wani soft hand ya cafko hannunta....ya fisgo ta zuwa baya.....sai ganin ta tayi a wani balcony, tana shirin juyowa. ... Aka sake fisgo ta, aka jingine bayan kofar da wajen, ita da wanda ya fisgo tan suka matse a bayan kofar.... Ta dago manyan, chocolate eye balls dinta, ta kallo wanda ya janyo ta.... Dai dai lokacin ashraf ya juyo da fuskar sa gare ta.... Ta sake ware idonta, cikin hazy eyes dinsa....kafafunta na rawa, kamar bazasu iya daukar ta ba. Sai da sukayi seconds a haka, eye balls dinsu na bin na juna, kafin karfi yadan zo wa jumy.., ta bude bakinta, da yayi mata nauyi, zatayi masa magana... Sukaji kamar an bude labulen wajen balcony din... Ashraf yayi saurin sa tafin hannunsa ya rufe mata bakin ta.....sannan ya kara matso ta sosai, har lumfashin sa na bugon fuskarta, their nose are touching each other. ..... Happy sallahπŸ—πŸ– ~*AFRAH*~ [10/22, 2:22 PM] +234 814 393 3159: πŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”ŽπŸ”Ž _____________________________ *JUMAYMA* γ€Š ~yar bincike~》 *Jasus* *Spy* Episode~51-52 " _lokacin da jalal ya dauki samosas ya fita, ashraf ya dauki chocolate guda uku ya tashi shima, hanan ta shagwabe fuska ta kalle shi, swtbro ina zakaje? Ashraf yadan tsugunno kusa da fuskarta, yayi magana a hankali" ina ruwanki da inda zani je uhm? Ya daga mata girar sa daya, yana mata murmushin mugunta_". _direct dakin batool ya nufa, hango jalal yayi ya fito daga ciki yana murmushi, hakanan yaji wani abu ya tsaya masa wuya"what is between the two?"mtsw y am I even giving ha dis, ya kalli chocolates din hannunsa,"zuciyarsa tace, because u like ha"ya girgiza kai da sauri, yah !! am ashraf safwan safana,hw cn I love a common house helper? No it can be man, yaja wani tsaki ya sauko

Chapter 6 of 12