Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
hawayen dake shirin fito musu a idanuwan su.. "Da yamma jumy ta isa mansion dinsu, abbu da yusuf ne a falo, cikin farin ciki suka tarbe ta, ummy ma ta fito cike da fara'a ta rungume diyarta, jumy hakanan taji kuka yazo mata ta kara shigewa jikin ummy tana rusa kuka, abbu da ummy suka shiga lallashinta, yusuf na zolayarta. ******* "Bayan sati daya da tafiyar su jumy, abun duniya yayi wa ashraf yawa, dama Allah yaso shi, week din contract dinsu da collage din ya kare, london ya koma ya amsa hutu na wata daya, dan duk ya rame kullum yana cikin tunani, morning flight yabi zuwa gida Nigeria. ******** "Da yamma ya iso Nigeria, kamal ne da neelam suka zo daukar shi daga airport, sai jan sa sukeyi wai ya wani kara kyau da haske, ashraf dai fake smile kawai yake binsu dashi. "Suna isa mansion din SAFWAN SAFANA, direct main house suka nufa, mami da grany tare da daddy suka iske a falon, ashraf ya bisu cikin girmama wa ya gaidar dasu, grany tace, da alama dai sabuwar surukar tamu ba karamin aiki tasha ba wurin saita mana ashraf, mami, daddy, kamal da neelam suka kwashe da dariya, banda ashraf da yayi shiru kawai yana binsu da kallo. ******* "Bayan sati biyu da dawowarsa, jalal da tasleem suka shigo naija suma, _bayan wulakancin da jalal yasha yiwa tasleem, kusan watanni biyu, abun duniya yayi wa tasleem yawa, wata friend dinta da suke neighbours a dubai din, ta bata shawara data canza halayenta, ta ringa yi masa duk abunda tasan yana so, tasleem zuwa tayi wurin jalal da cup of coffee, ta tsugunna ta basa hakuri cikin nuna dana sani, sannan bata boye masa komai ba, ta sanar dashi itace ta zuga ashraf yayi wa jumy fyade, ba karamin mamaki jalal yaji ba, ya kuma yi mamakin yadda tasleem take mugun sonsa haka har ta iya plotting irin shu'umancin nan, hakuri ya bata shima, sannan sannu a hankali suka fahimci junan su_ ******* "Ranar da suka dawo, a daki jalal da tasleem suka iske ashraf, a kwance,ya fada duniyar tunani sosai, jalal ya dafa shi, ya girgiza masa kai, thinking is not good for your health man, ashraf ya dago da sauri, yana kallon jalal, ya sauke idanunsa kasa, yace am sorry bro, jalal ya dago da kansa, its not your fault ashraf, tasleem ta karasa wurin su, ta duka ta bawa ashraf hakuri tace tayi dana sani sosai, pls ya yafe mata, ashraf yayi murmushi, ya kalli jalal da tasleem, am so sorry bro but I full all of you, banyi raping din jumayma ba! Suka kalle shi da confused face, wacce jumayma?, ashraf ya saki lumfashi, sannan ya sanar musu komai akan jumayma kuma fake indo... "Batool da hanan da saukar su kenan suma, sun dawo semester break, neelam da kamal dake bakin kofa suka karaso ciki suma, suna mamakin duk abunda ashraf ya gama fada yanzu, hanan tace, tana kallon ashraf,may be she refused because of me, tayi sad face, tasleem tace no saboda ni dai, I really show hatred to the poor gal, kamal yace, ya isa haka,now miye abunyi?, dolene mu dawo da STAR din ya ashraf nan gidan, and all apologise to her... Jalal yace why not muje Egypt din?, ashraf ya bude baki zaiyi magana wayarsa tayi ringing, ya dauka yace hello? "Daga dayan side din yusuf ne _da saukar su kenan a Nigeria, shi da uncle, ummy da jumayma, sunzo ganin yan'uwan abbu dake gombe_ Dariya yusuf yayi, yace we are in Nigeria right now dude, ware idonsa ashraf yayi sosai, nigeria!!!? Ya fada. Ciki da mamaki. Yusuf yace yes of course, _dan ya gama sanin duk damuwar da jumy keyi tun dawowarta saboda ashraf ne, dan tun lokacin da ashraf ya dame sa akan yana son sanin aikin da jumy keyi, ya fahimci akwai wani dake tafiya tsakanin su_ Ashraf ya shiga murna sosai kamar karamin yazo, yace man am so happy, suka dai yi yar fira kafin ashraf ya kashe wayar, Ya kalli yan'uwan sa yace jumayma and her family are in Nigeria right now... Gaba daya suka hau ihun murna, jalal yace we have to meet with them as soon as possible, yes sukace gabadayan su, ashraf yace no need, zasu zo har nan gidan, gaba daya suka kallo shi, yace wait for some hours, ya saki wani irin murmushi, u all will see my sparkling Star. ... **** "Uncle please can we visit a friend of mine, before we head off to gombe? Abbu ya dafa yusuf, but we won't stay long there, yusuf yayi murmushi okay thanks uncle. .. Taxi suka shiga, dama ya turo masa address, ya nunawa mai taxi din, shaf shaf suka shigo area din.. Jumy ta ware ido, ina akhie zai kaisu, abbu ma dai kallon yusuf yayi, yace your friend stay here, yusuf ya kada kai, ummy dai na zaune shiru abunta, tana rike da hannun jumy. A babban gate din mansion din Safwan safana mai taxi ya tsaya, hanjin cikin jumy suka motsa, fitowa sukayi gaba daya, yusuf ya karasa wurin gate din yayi knocking. Ba'a dade ba aka bude musu suka shig , dan ashraf ya riga ya sanar wa security da zuwan su, jumy sai baza idanu takeyi gabanta na faduwa, abbu ya juyo ya kalli yusuf sure ia here? Yusuf yace yes sir.. "Main house suka nufa, yusuf yayi knocking, bude kofar aka yi hankali, abbu ne a gaba sai yusuf a gefen shi, sai jumy da ummy a bayansu. Ashraf, jalal, tasleem, hanan, kamal, batool da neelam ne suka bayyana a bakin kofar, gaba daya suka baki wurin cewa UNCLE JUNAID!!!!! Suna kallon abbu,Fuskokin su dauke da mamaki tsantsa.... "Zaune suke gaba dayaa falo, kowa yayi shiru, abun aljabi ne ya faru, jumy sai wani rufe fuska takeyi tana shigewa jikin ummy, ashraf kuwa mamaki, confusion duk sun hade masa a kai. Daddy yayi gyaran muryan, ya kalli abbu, wato junaid Allah da iko yake, yanzu dama diyarka itace spy din data taimake mu? Mami tayi murmushi, ni kaina ban lura da yanayin ku sai yanzu. Grany tace, ai matsalar kenan, zamanin yanzu kwata kwata ba zumunci, yanzu ace junaidu cousin da Aysha (mamie) ne amma ace ko diyarsa bamu sani, kullum ya tashi zuwa sai dai yazo mana shi daya, ko baarabiyar matarsa sai yau muke ganin ta... Jumy wani banbara kwai taji, abbu dinta cousin din mamie dinsu ashraf ne? Abbu ya sauke ajiyar zuciya, ni kaina nayi mamaki da yusuf ya kawo mu nan gidan, dan ban taba tsanmanin cewa yasan su ashraf ba. Jalal yayi dariya, mu nan har munyi shirin zuwa Egypt. . Mami tace kuyi mai acan? Neelam tace ai sweet inlaw din tamu, ya jumyama ce, tana maganar tana kallon ashraf, dake zaune yana kallon jumy kasa kasa.. Daddy da abbu suka kwashe da dariya, grany tace kai haba dai, toh Allah ya kara dankon zumunci. Ummy dai da kallo take binsu, kamal ne yazo wurin ta ya zauna, yace kuna ta fira kunbar auntie a duhu, batool tace eh wallahi, hanan tace inlaw ki fassara mata, tayi maganar tana kallon jumy,jumy tayi dan murmushi, sannan ta kalli gefen ashraf, ya kashe mata ido daya, jalal yace tasleem ta shiga da jumy dakin su. *****bayan kwanaki biyu, yan'uwa kuwa ya nemi gafarar kowa, jumy da tasleem yanzu sun zama new friends, su hanan da batool da neelam suna girmama su, kamal da ashraf tare da jalal sun matsawa daddy yayi wa abbu maganar auren ashraf da jumy, dan haka ya samu abbu aka nemi shawarar ummy da mami da grany, kowa ya amince, aka saka biki nan da wata daya, dan abbu zai koma bakin aikin sa. ****bayan wata daya. An DAURA AUREN JUMAYMA KHATOON DA ASHRAF SAFWAN SAFANA. Gaba daya gidan a cike yake, sai shagayi akeyi, kowa ka gani cikin farin ciki yake, su batool and rest ansha gayu., sai parati akeyi a cikin mansion. Amarya jumayma na daki tare da tasleem da wasu yan uwan abbu, kamal ya shigo dauke da I paid din ashraf a hannunsa, ya mikawa jumy, here ,ya ashraf yace some people wants to talk to you, jumy ta amsa, tana kallon kamal da alamar tambaya, ya daga kafada irin dnt knw too, yana cewa idan kin gama ki bawa neelam ko hanan su kawo masa a side dinmu. "Tana kallo screen din taga, yash, sheerya, marwa, team leader, gaba dayan su suka hada baki wurin cewa, *Happy marriage life agent jumayma khatoon* !!! Wani irin mamaki da farin ciki jumy taji, tasa hannunta da yaji henna design mai kyaun gaske, ta dafe bakin ta, suka kwashe da dariya, MRS ASHRAF congratulations!!!! Tayi dariya tana cewa thanks thanks very much guys , tayi peck a tafin hannun ta ta hura musu... "Sai data dade tana ta fira dasu, tasleem na gefe na mata dariya, da gani tayi missing dinsu, da kuma aikin ta.... Tana gama magana dasu, taji massage ya shigo a wayarta, ta duba taga ashraf ne, _ki same ni a garden kawai_ ya turo a takaice, tayi murmushi tana shafa screen din wayar, sannan ta mike ta sulale daga dakin. "A zaune ta iske shi yana shan juice, ta karasa wurin sa cikin sanyin ta, yana jin ta tsaya a gaban sa, ya dago da cute eyes dinsa, ya fara kallonta tundaga kasa zuwa kyakkyawar fuskarta, data sha makeup, mikewa yayi, ya dauko wata red rose flower daga aljihunsa, mikawa jumy, yace, *I LOVE YOU MY STAR*, jumy ta sakar masa wani irin murmushi, tasa hannun ta dayaji henna ta amsa rose din, sannan ta kalli cikin idonsa tace I LOVE TOO HAYYATY, yasa hannu cikin zafin nama ya jawo ta jikinsa, ya matse ta a kirjin shi, sai sauke lumfashi sukeyi a tare, ashraf yadan dago da fuskar jumy, ya rike da duka tafin hannunsa, my star my love, my wife. ....sai kallon cikin idon juna sukeyi, cike da so da kauna, jumy ta saki murmushi, tace my love my heart my husband, ashraf ya runtse idon sa yana jan lumfashi, jumy tadan kalli fuskarshi, cike da so da shauki, ta dago daga kafarta kadan, ta hada lips dinta da nashi, ashraf ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi, yasa hannu daya ya riko kugunta, daya kuma ya dafe kanta hade da gashin kanta, ya shiga kissing dinta, cike da kauna... Washe gari Duka family suna falo,ana ta fira cikin barkwanci, jalal duk ya ishi jumy da zolaya, tasleem na taya sa, batool ta mike tana cewa, what about we take a happy family selfie..? Hanan ta mike itama yeah pls pls, kamal zaiyi magana sukaji sallamar mum.. *Mum!!!!!!* tasleem da hanan suka hada baki, mum ta karasa ciki sumi'sumi, tazo gaban daddy da mamie ta durkusa, tace su yafe ta, _dan bayan kama sufyan da akayi, kudi sosai mum ta kwasa ta ware, tabar yaranta_. Daddy da mamie sukace sun yafe mata,abbu da ummy da yusuf suna ta magana kasa kasa da arabic, mum tazo wurin tasleem da hanan tadan durkusa, suka juya mata baya da sauri, jumy ta mike ta karasa wurin su, tace please forgive your mum, tayi nadamar abunda tayi, kuma Allah ya riga ya kadddara hakan zai kasance, jumy tayi ta lallashin su hade da musu wa'azi. Hanan ta mike taje ta rungume mum tana hwaye, hakama tasleem, mum ta jawo jumy dake kusa dasu, ta hada su , su uku ta rungume tana kuka tana neman yafiyar jumy, dan yadda tayi ta treating dinta... Batool tace hooh hooh, let's stop the crying scene and take the family selfie...., kamal yadan buge mata kafa, anty parrot, tadan harare shi tana turo baki, neelam dake kusa da grany tace, damun cire grany a pic kada ta bata mana, jalal yadan dungure mata kai, shut up joor, mami, daddy, ummy, abbu sukayi dariya, grany kuwa hankalinta nakan screen din wayar ashraf, dake kallon video din daya dauki jumy a india, grany ta tabe baki, yaran zamani da soyayya, ga mutum nan amma hoton shi ake kallo ohhh🤔, hanan da batool suka mike suka jawo su jumy da ashraf suka hade wuri daya... "Sannan duka family ma suka hade suma.., kowa fuskarshi dauke da farin ciki, jalal ya daga selfie stick din ya dauke su...., family selfie, kowannen su nayin posing dinshi... Nima AFRAH na kara yar Samsung dina, na jawo, ZUBY CHIROMA, AFRAH WAZIRI, MY AYEESH, ZARAH IDRISS,AMINA.M.ALI , HALAMCY NAH, SUMAYYA IBRAHIM, FATIMA SADA (cousin),nace come on girls mudau selfie,😂 sai da duk suka mouth pointing suna jiran flash shot, wayata tayi short down lols..😜.... *END* *GODIYA* dukkan godiya da yabo sun tabbata ga ubangiji ALLAH, sarkin dayai wuta da aljanna, yayi sammai da kassai, yayi duniya da lahira baki daya." *TO THE FANS OF JUMAYMA* nagode kwarai da gaske da soyayyar da kuka nunawa jumayma, naji dadin yadda kuke bani karfin gwaiwa, ina godiya sosai, ina kuma fatan Allah daya barmu tare cikin so da kaunar juna. "Kuskuren da aka samu a wannan littafi duk ina neman afuwa please, masu min gyara ina godiya kwarai da gaske, ALLAH YABAR ZUMUNCI. *GODIYA GAREKU*.. Ummy aisha👌🏼 Munay unnie Rash kardam Nafee anka Harpsart rano Jamila muhammad ali Ummu adnan Anee lurv S.a azeez Khady chafe Miss umar Nana fa'ad Ummy hambali Chuchu💞 Queen meemi Safah And All the members of *EXCELLENT WRITERS* ALHAMDULILLAH Agent Jumaima Khatoon Complet Ebook creator by Shuraih 99% . Shuraih Usman This Ebook is available at http://shuraih.waphall.com And free its not for sale its for readers who like hausa novels . An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 12 of 12