Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 11
rayuka tayaya zan iya fuskantar wannan mahaukaciyar macijiya? . ANAN muka kawo karshen littafin tarkon mutuwa na bakwai 7 , Zaku jini a littafi na takwas 8 nan bada dadewa ba. TARKON MUTUWA BOOK 8 PART A Lokacin da nasmal yaji tambayar da hatyan yayi masa ta cewa ta yaya shikadai zai iya kare miluyoyin rayuka kuma ta yaya zai iya fuskantar wannan mahaukaciyar macijiya saiya kyalkyale da dariya lokaci guda kuma ya turbune fuskarsa y dubeshi yace yakai abokina inaso ka sani cewa bawai don kafi kowa karfi da iya yaki ba ne akace kai zakayi wannan aikiba sai saboda kaine yanzu kake kan kadaminka ma'ana duk wani jarumi mai sa'a yanzu abayamka yake kuma duk wanda yaja dakai saiyaci kasa taurari sun nuna hakan kuma masana tarihi da masu binkice sun tabbatar da cewa kaine jarumi na farko wanda yaja da sarki shamsal a nahiyar ku yakai labari her gaba da gaba kunyi dashi amma bai sami nasara akan ka ba shin kana da wata tambayar ne wacce kake son jin amsarta yanzu? lokacinda jarumi hatyan yaji wannan tambaya sai yayi shiru yana dan tunani ya kasa cewa komai daga can kuma saiya dago kansa ya dubi nasmal yace wacce irin jarrabawa zakuyi mini acan birnin wacce indai na tsallaketa zan iya kareku daga sharrin wannan macijiya? idan her zan haye jarrabawar nan na kareku mai yasa bazanyi kokarin kare sauran kasashen duniyaba wadanda zasu fuskanci wannan matsala? dajin wannan batu sai nasmal yayi murmushi sannan yace komai mukaddarine babu wani shiri ko sihirin da zai iya sauya kaddara hatyan ya gyada kai yace mai yasa kana matsayin dan sarki guda amma ka taho daji farauta akasa haka batareda ka hau dokiba alhalin tafiyace ta tsawon kwanaki uku? nasmal yace mu agarin mu duk wanda yakeyin doguwar tafiya akan doki ragone amfanin doki kawai shine ayi ado da biki dashi yanzu sai muci gaba da tafiya domin mu isa can gida akan lokaci saboda nasan jama'armu zasu kosa da isowarmu koda gama fadin hakan sai yarima nasmal ya juya ya nufi hanyar da zata kaishi her birnin nasu da ganin haka sai sadirat ta rugo wajen hatyan tace waishin maganganun me kuke tayi ne? ko kallon ta hatyan baiyiba ya juya ya nufi nasmal yana mai cewa zakiji komai idan muka isa can birnin su cikin hanzari itama tabi su hatyan sunata yin sauri domin su riski yarima nasmal Acan birnin sarauniya badi'atul nauwara kuwa lokacin da ta kadaita acikin turakarta tareda tsohuwa ummulkhairi afarkon dare saita mike tsaye ta tube kayanta dake jikinta ta dubeta tace saiki fara aikinki dajin haka sai tsohuwa ummulkhairi tayi murmushi tace haba ranki ya dade shin kin mantane cewa nan acikin turakarki ta barci muke ai saidai mu karasa cikin kewaye ki shiga cikin bahon wanka tunda wanke jikinki za'ayi gaba daya badi'atul nauwara tayi murmushi ba tareda tace komaiba saita shige izuwa cikin kewaye ummulkhairi na biyeda ita abaya nantake badi'atul nauwara ta shige cikin bahon wanka ta zauna itakuma ummulkhairi saita bude jakarta ta debo wani garin magani ta zuba acikin ruwan bahon ta kama cuccuda jikin badi'atul nauwara aikuwa sai bakin shunin ya dinga ya ribga fita tamkar ana wanke kura da ruwa nanda nan fatar jikin badi'atul nauwara tayi kyau kamar yadda take da sannan taje ta caba ado na fada sannan sukaje gaban madubi suka tsaya ummulkhairi na gyara mata adon koda badi'atul nauwara ta karewa kanta kallo taga tsananin kyawunta da allah ya bata kuma ta tuno da cewa wanda takeso yana can cikin hatsari sai nantake idanunta suka ciko da kwalla har hawaye ya zubo mata bata an karaba koda ta fahimci cewar ummulkhairi taga zubar hawayenta sai kunya ta kamata don haka saita yunkura cikin sauri domin ta goge hawayent sai ummulkhairi tayi farat tace kada ki tsayarda wannan hawayen naki ya shugabata domin zubarsace kadai zai rage radadin dake cikin zuciyar ki ki sani cewa uwar gidana ma mai girma anisa kullum sai ta zubar da irin wannan hawayen naki kuma akan irin dalilinki ma'ana matsalarku dayace koda jin wannan batu sai badi'atul nauwara ta juyo da sauri ta kama kafadun ummulkhairi ta ruke da karfi tace waishin me kike nufi da wannan batu naki? ummulkhairi tayi ajiyar zuciya sannan tace keda kawarki anisa kunason saurayi daya kuma dukkanku baku taba son waniba faceshi kowacce acikin ku zata iya sadaukar da soyayyar ta ga 'yar uwarta saboda aminci da kauna duk ku biyun kun boye sonda kukeyiwa hatyan zangaya miki wani sirri guda daya bisa gaskiya sirrin kuwa shine anisa ce ta fara son hatyan tun kafin ki sanshi amma tunda suka rabu basu sake haduwaba sai awannan karon da ya baro kasarsu shikansa har gobe yana da burin sake haduwa da ita domin baiga fuskartaba awancan lokaci dolene kusan hanyar da zakubi ku warware wannan matsalar taku acikin sauki yadda dayarku ba zata rasa rayuwarta ba kokuma taci amanar 'yar uwarta lokacin da ummulkhairi tazo nan azancenta sai hankankalin badi'atul nauwara ya dugunzuma ainun ta rasa abinda ke mata dadi aduniya kuma saita kamu da tsananin mamaki ta dubi uummulkhairi tace yanzu keda duk kinsan wadannan abubuwa amma baki sanar daniba donme zakiyi mini haka? ummulkhairi ta numfasa tace idan her na sanar dake wannan al'amari tamkar naci amanar uwar gijiyata ce tunda itama ban sanar da ita abinda na saniba nice na matsa akan saina biyoki zuwa nan sannan zan wanke miki wannan shuni domin mu tattauna akan wannan matsala ki sani cewa uwargidana anisa tana tsafi kuma tsafi yana tasiri akanta ke kuwa bakya tsafi kuma tsafi baya tasiri ajikinki ninan da kike ganina na kasance gawurtacciayr matsafiya don haka nasan abubuwa da yawa ayanzu haka babban makiyin masoyinku wato sarki shamsal yana turawa su hatyan mugayen masifun da zasu hallakar dasu da farko ya tura musu sihirtattun zakuna da kadoji sun tsallake sharrinsu yanzu kuma zai tura musu da dabbar da tafi dukkanin dabbobin duniya bala'i da hadari wacce ake kira da uwar macizai kodajin wannan batu sai idanun badi'atul nauwara suka zazzaro kuma hankalinta ya dugunzuma ainun fiye da koyaushe ta dubi uummulkhairi tace tabbas na sami labarin uwar macizai awajen mahifina ya gaya mini cewa babu wani matsafi da zai iya taso uwar macizai daga barcin da takeyi face wani boka guda daya kuma bokan yafi shekara dari da hamsin da mutuwa tayaya yanzu zakice sarki shamsal zai taso ta? ummulkhairi tayi ajiyar zuciya tace ba sarki shamsal bane zai taso taba bokansa ne daizur kuma yakasance jika ga wancan bokan daya mutu na tamanin da takwas kuma ya gaji duk wani sihirin tsafi daya bari tunda mahaifinki ya baki labarin uwar macizai kinsan duk irin bala'in da zata haifar aduniya idan ta bayyana manyan bokayen duniya sun gano cewa mutum dayane zai iya kashe wannan macijiya bokayen dake nahiyar bakaken fata sunyi imani cewa jarumi hatyan ne zai iya kashe wannan macijiya amma mu anamu binkicen na nahiyar fararen fata munyi imani babu wanda zai iya kashe wannan macijiya face jarumin da baya tsafi kuma tsafi baya tasiri jikinsa sannan kuma dolene ya kasance ma'abocin wani sabon addini wanda ake kira musulunci kaf nahiyar bakaken fata babu wani jarumi da baya tsafi kuma tsafi baya tasiri ijikinsa awannan nahiya tamu kuma kece kadai jarumar da take da wannan baiwa amma kuma baki kasance ma'abociyar wannan sabon addini ba shin kinsan wannan addini wanda ake kira musulunci? kodajin wannan tambaya sai sarauniya badi'atul nauwara tayi shiru tana tunani izuwa wasu 'yan dakiku sannan tayi farat tace mahaifina ya bani labarin wannan addini kuma ya bar mini wani littafi wanda yake dauke da cikakken bayani akan wannan addini da yadda ake shigarsa kodajin wannan batu sai farinciki ya turnuke ummulkhairi tace ya zama wajibi ki shigeshi idan har kinason ki ceto rayuwar masoyinki kuma ki ceto dubunnan ruyukan dake wannan nahiyar tamu da kuma nahiyar bakaken fata da zarar kin gama karanta wannan littafi gamida shiga cikinsa saikiyi shiri kibisu jarumi hatyan izuwa wannan birni da suka nufa na bakaken fatav domin acan ne macijiyar zata fito ta cikin teku idan ta gama dasu jarumi hatyan da wannan birni zata dawo ta rushe duk kasashen dake wannan nahiya hatta birnin sarki shamsal kuwa domin shikansa boka daizur bai isa ya iya sarrafa macijiyarba ya shugabata idan baki hanzarta yin abindana umarceki ba kawarki anisa da masoyinki hatyan zasu rasa rayuwar su kafin ummulkhairi ta ta gama rufe bakinta tuni sarauniya badi'atul nauwara ta falfala da gudu izuwa cikin daki sai takama bude buden akwatunan da aka tara aciki wadanda sunfi guda dubu ta rinka binkice su daya bayan daya A can birnin sarauniya anisa kuwa lokacin da.... TARKON MUTUWA BOOK 8 PART B A can birnin sarauniya anisa kuwa lokacinda sarki shamsal ya baiwa boka daizur umarnin taso uwar macizai da gaggawa sai boka daizur ya fiddo madubin tsafinsa ya ajiyeshi agabansa ya fara karanta wadansu dalasiman tsafi sudai wadannan kalmomicguda dari ba uku ne kuma boka daizur na gama karanta sune uwar macizai zata farka daga barcin da take koda boka daizur yazo kan kalma ta casa'in da biyar sai kawai sukaga an banko kofar dakin da suke ciki afusace cikin tsananin fushi sarki shamsal ya mike tsaye yana mai zare takobinsa kawai saiyaga sarauniya anisa ta shigo tareda dakarunta na yaki kimanin su dari uku kowannensu ya dana kibiya akan baka sun saita sarki shamsal da boka daizur afusace anisa ta dubi sarki shamsal cikin daga murya tace saboda kawai ka hallaka mutum biyu kacal zaka fito da abin da zai iya hallaka duniyar gaba daya wannan wanne irin rashin imani ne hade da son zuciya to kasani cewa idan kuka ci gaba da kokarin aiwatar da wannan nufi naku kaida bokan nan naka kibiyoyi dari ukune zasu nutse ajikinku yanzu alhakin kasheku ba ahannuna yakeba kuma ka sani cewa ba wai tsoronka nakejiba tundaga farkon zuwanka amma ka sani cewa kazo gabar da dole sai nayi kokarin dakatar dakai sa'adda sarauniya anisa tazo nan azancenta sai sarki shamsal ya turbune fuskarsa yace yake wannan karamar karuwa vkiyi sani cewa ni murucin kan dutse ne ban fitoba saidana shirya tayaya kike tunanin cewa zaki iya hanamu aiwatar da wannan babban aiki to ga fili ga mai doki sai mu zuba mu gani maza bisa kanki maza kisa dakarunki su harbemu idan her kibiyoyin naki zasu iya cutar damu kafin sarki shamsal ya gama rufe bakinsa tuni anisa ta baiwa dakarun nata umarnin suyi harbi koda kibiyoyin suka fito daga cikin baka sai suka kame asama suka kama da wuta gaba dayansu suka kone kurmus suka zube kasa amatsayin toka faruwar haka keda wuya sai sarki shamsal ya mike tsaye yana mai kyalkyalewa da mahaukaciyar dariya sannan yace Yanzu kuma me zaki iyayi? shin zakiyi amfani da karfin sihirinkine wanda yafi namu? kai boka daizur maza ka karasa wannan aiki nikuma ka barni da wannan sarauniya naga iya gudun ruwanta nasan kin gama da hadimaina da suke waje amma ki sani inzaki hada gaba daya dakarunki su zo su hadu anan basu isa su tsayarda muba her boka daizur ya budi baki zaici gaba da karanto wadannan dalasiman tsafi sai sarauniya anisa ta daka masa tsawa ya tsuke bakinsa sannan ta dubi sarki shamsal afusace tace tun daga kuruciyata zuwa girmana nake tanadi akanka domin tun zamanin iyaye da kakanni masarautarku suke kuntatawa masarautun da suke wannan nahiya tamu ka sani cewa dan hakkin daka raina shike tsone maka ido tabbas ka fini shekaru kafini karfin damtse amma baka fini iya yaki da tsafiba kawai na boye tawa baiwarne amma yanzu zan nunata idan ka kasheni sai kuci gaba da aiwatar da nufinku idan kuma nice na kasheka shikenan na kawo karshen mulkin zaluncinku awannan nahiya anisa na gama fadin haka saita cire rigar da take jikinta mai kama da alkyabba tayi wurgi da ita saigata cikin shigar yaki wadansu tufafine ajikinta na bakar fata kuma matsatstsu takalmin kafarta ma na bakar fatane dogo iya kauri mai madauri wata zabgegiyar takobice agadon bayanta nantake sarauniya anisa ta dubi dakarunta tayi musu wata inkiya nantake suka fice daga dakin suka turo kofa suka rufe ta waje harda sa makulli anisa ta dubi sarki shamsal cikin alamun tsananin kiyayya tace na sallama rayuwata don ceton masoyina hatyan da 'yar uwarsa sadirat da kuma miliyoyin rayukan da kakeson salwantarwa ka sani cewa nida sarauniya badi'atul nauwara ne muka taimakawa hatyan ya tsira daka dukkanin harinka acan teku inda kuka rutsashi kana shirin sare masa hannu badi'atul nauwara ce tazo ta naushi bayanka kafin ka juya ta daukeshi daga wajen anan garin kuma nice na batarda duk wata shaida alhalin yana cikin wannan gidan sarautar aboye abinda yasa kuka kasa gano hakan da karfin sihirinku shine sarauniya badi'atul nauwara tama cikin garin nan kuma kasan cewa tsafi baya tasiri indai tana wuri koda gama fadin haka sai anisa ta gyara tsayuwarta ta zare takobinta sannan ta gyara rukon garkuwarta awannan lokaci fuskar sarki shamsal ta fara gyatsine saboda tsananin fusata don haka sai shima ya zare tasa takobin cikin kakkausar murya yace na rantae da girman kabarin ubana sainayi miki kisan wulakanci tunda dasa hannunki acikin zagon kasan da akayimini kuma koda annobar uwar macizai bata hallaka kawarkiba sai na bita har birninta nayi mata irin kisan da zanyi miki kodajin wannan batu sai anisa ta bushe da. dariya tace yanzu nan kai aganinka zaka tsira da rayuwarka ne her ka cika wannan buri da kake furucinsa? idan baka saniba ka sani domin na fuskanci kana da jahilci akan sanin tarihin duniya her kullum kuma har abada mulki da zalunci baya dorewa kafin kai anyi manyan sarakuna da suka fika karfin damtse dana sihiri da karfin mulki da zalunci amma akaron banza suka dinga gushewa kafin anisa ta gama rufe bakinta tuni sarki shamsal ya dako tsalle daga inda yake tsaye tamkar daga kan sifirin yake ya kawowa sarauniya anisa mugun sara akafadarta da nufin ta tsargeshi gida biyu ba zato ba tsammani sai yaga ta kare saran ba tareda karfin saran yasa ta fadi kasaba kafin ya kawo mata wani harin tuni ta doki kirjinsa da gwuiwar kafarta ta hagu, saboda karfin dukan saida yayi baya taga taga amma ya tsaya cak ya sake taso mata suka sake kacamewa da azababben yaki mai matukar ban tsoro da ban al'ajabi shidai sarki shamsal yana yakin ne da dukkan karfinsa cikin kunar rai domin zuciyarsa tafarfasa take kamar zata kone yana mai yiwa kansa tambaya cikin zuciyarasa yana mai cewa yanzu dama akwai macen da zata iya tarata da yaki awannan nahiya amma ban saniba? tayaya wannan yarinya t iya yaki haka kuma ta kasance mai bakin zafin nama irin wannan gamida tsagwaron karfin damtse? shikuwa daizur jikinsa ne ya kama kyarma saboda tsananin tsoro domin baiyi zaton anisa ta kai wannan matsayiba kuma duk abinkicensa na tsafi bai taba ganin sirrintaba saida sarki shamsal da anisa suka shafe sa'a guda suna wannan gumurzu acikin wannan daki ya zamana cewa sun lallata duk wasu kujeru da kayan alatu da suke cikin dakin amma dayansu bai sami nasarar koda lakutar jikin dayaba shikuwa boka daizur dayaga masifar tayi yawa saiya rikide ya zama dan mitsitsi tamkar kuda ya makale acan saman rufin dakin yaci gaba da kallon wannan gumurzu LIKE AND COMMENT IS OUR ENCOURAGEMENT TARKON MUTUWA PART 8 C lokacin da sarki shamsal yaga sun shafe tsawon sa'a guda suna kaiwa juna sara da. suka cikin tsananin zafin nama juriya da bajinta amma babu wata nasara kuma anisa bata gaji ba saiya ja da baya ya gyara tsayuwarsa yana tunanin salon fada da zai sake dashi da Ita awannan lokaci duk hannayensu radadi suke saboda gajiyar ruke kotar takobi kuma duk takubban nasu sun daauki zafi sosai kamar acikin wuta aka gasa su koda anisa taga sarki shamsal ya danja da baya sai tayi masa dan murmushi na yarda da kanta tace nasan kayi mamaki yadda nake da kwarewa da juriya irin taka ba komai ya jawo hakanba face nayi binkice akanka sosai kuma na samu duk irin horon daka samu sarki shamsal ya maidawa anisa martanin murmushi yace ai abu daya zakiyi ki burgeni me zai hana mu zubar da makaman mu mu gwada 'yar kashi? koda jin wannan batu sai anisa ta sake bushewa da dariya tace ashe bani d hankali kenan idan her baka manta ba ai tunda farko na gaya maka ccewa kafini karfin damtse to sabodame zanyi gangancin jarraba nawa akan naka? ka sani cewa indai akwai takobi ahannuna karfin damtsenka ba zaiyi ta siri akaina ba amma idan kana shakkar hakan to ka sauya salon yakin naka k gani zaka sha mamaki yau sai na rushe dukkan burinka na duniya kuma cikin biyu dolene daya ya faru ko ni na kasheka ko kuma kai ka kashe ni ko kuma muyi ragas sa'adda sarauniya anisa tazo nan azancenta sai sarki shamsal ya bushe da dariya sannan yace ke karamar karuwa ki sani cewa duk wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi, ke sa'ar dana ce don haka na fiki wayo kuma nafiki sanin tuggun yaki na fiki shan gwagwarmayar duniya kuma na fiki sa'a yau shekara ta arba'in da bakwai kenan ina kan sharafina duk abinda nasa agaba na sainaga bayansa don haka ke baki isa ki rushe mini burinaba caraf saii anisa ta tari numfashinsa tace wannan shine babban kuskurenka arayuwa domin kana mantawa cewa dolene mai laya ya kiyayi mai zamani, ka sani cewa sarki goma zamani goma mu 'ya'yan yanzu kwakwalwarmu tafi taku. TARKON MUTUWA PART 8 D mu 'ya'yan yanzu kwakwalwarmu tafi taku dogon nazari gamida hangen nasa da kuma basirar binciko abubuwan cigaba wannan dogon surutun da mukeyi bashida amfanin komai face bata mana lokaci kawai mu gani akasa ni burina ka sauya salon yakin naga yadda ta kaya kafin sarki shamsal ya bude baki yace wani abu tuni anisa ta dako tsalle daga inda take ta kawo masa sara ,naushi, da bugu da hannayenta da kafafunta duk alokaci guda cikin bakin zafin nama sarki shamsal yayi kokarin kare duk hare harenta amma duk da haka saida ta sami nasarar yankansa akan kwanjinsa na hannun dama kuma ta doki kirjinsa yaje ya manne ajikin garu kawai sai gani tayi kamar an cilloshi daga cikin baka kafin tayi wani yunkuri shima y rama abinda tayi masa ya yanketa akan cinyar hannunta na dama kuma ya daki kirjinta ta fadi kasa wanwar saboda karfin dukan nasa ya ninka nata harsaida ta furzar da jini daga bakinta tana kwance akasa sai sarki shamsal ya dako tsalle ya kawo mata suka aciki da takobinsa anisa ta mirgina can gefe guda ta kaucewa sukar takobin ta doki kasa ta lume kafinya zaro takobin ta mike tsaye zumbur sun sake kacamewa da azababben yaki saida suka sake shafe wata sa'a gudar suna wannan dauki ba dadin ya zamana cewa kowannensu ya sake samun nasarar yankar abokin gwaminsa sau biyu wato dai kowannensu anyi masa rauni uku amma saboda azabar naci da juriya basu fasa ci gaba da artabun ba koda sarki shamsal ya fahimci cewar bashi da tabbacin samun nasara akan sarauniya anisa saiya daga kansa sama ya dubi boka daizur wanda ya zama dan mitsitsi ya daka masa tsawa yace wai shin me kake jirane ai tunda na tare maka wannan hatsabibiyar maza ka karasa aikinka koda jin haka sai boka daizur yai wuf ya fiddo madubin tsafinsa yaci gaba da karanta wadannan dalasiman tsafi daga inda ya tsaya al'amarin daya dugunzuma hankankalin sarauniya anisa kenan ta kara zage damtse wajen kokarin kaiwa boka daizur hari domin ta hallaka shi amma sai sarki shamsal ya tareta suka cigaba da bakin artabu mai matukar ban tsoro wanda komai zai iya faruwa kafin cikar rabin sa'a boka daizur ya gama karance wadannan dalasiman tsafi faruwar hakan keda wuya sai uwar macizai wacce ke kwance akan karkashin teku tana barci na tsawon shekaru dari da arba'in ta yunkura ta taso izuwa saman tekun, yunkurin da tayine yasa tekun tayi girgiza ta kama ambaliya ashe wannan tekun mahadace ta dukkan tekunan duniya hakan ne ya haifar da girgizar kasa ako'ina acikin duniya ya zamana cewa tekun ta kama ambaliya ruwa na shiga gari yana cinye mutane da gidaje babu inda ba'aga wannan tashin hankalinba don haka anan birnin sarauniya anisa tana cikin yin wannan yakida sarki sshamsal ne tekun ta balle ta fado cikin gari gaba daya gidan sarautar saidaya ruguje kuma ya nutse acikin ruwa, mutane da yawa suka hallaka wasu suka jirkita sarki shamsal da boka daizur kuwa akan wani akan wani katako suka dafe ruwa ya tafi dasu bisa taimakon karfin sihirin tsafinsu suka tsira itama sarauniya anisa tsafi tayi t kira wani sihirtaccen tsuntsunta ta dira akansa ta kama shawagi asararin samaniya tana ganin irin mummunar barnar da ruwa yayi mata wanda ya haddasa asarar dubunnan ruyuka da dukiya mai yawan gaske saboda bakin ciki da takaici nantake sarauniya anisa ta fara zubar da hawaye ,bisa dole ta sauko kasa izuwa cikin ruwa ta fara kokarin ceton rayukansu Al'amarin su jarumi hatyan kuwa ya rage saura baifi sa'a daya da rabi su isa birnin su yarima nasmal ba kawai sai suka jiyo rurin uwar macizai adaidai lokacin da ta yunkura ta taso sama daga cikin tekun nantake kasa ta kama girgiza babu shiri su hatyan suka ruke hannayensu don kada su fadi kafin su nemi matsera kasa ta fara tsatstsagewa daga bayansu tana ruftawa kasa tana kusantata babu shiri duk su ukun suka falfala da azababben gudu har hatyan yayi dan nisa saiya tuna cewa ai 'yar uwarsa sadirat bata da karfin gudu irin nasa don haka saiya waigo da baya a firgice yana mai tsayawa hatyan ya kurma uban ihu sakamakon hango abindake shirin faruwa kasa ce ta zabtare adaidai inda sadirat take ta tafi izuwa kasa zata nutse ba zato ba tsammani sai yaga yarima nasmal ya dako tsalle izuwa gareta ya cafo hannunta kuma nantake ya rikide ya zama katon tsuntsu yayi sama da ita ya juya da baya ya tunkaro hatyan dukda tsananin gudu irin na hatyan sai gashi zaizayar kasa na neman cimmasa domin tazarar dake tsakaninsu bata wuce taku biyuba saura taku daya kacal kasar ta cimmasa ne tsuntsu nasmal ya sureshi yayi sama dashi sai gashi su biyu shida 'yar uwarsa suna reto ajikin kafafun tsuntsun adaidai wannan lokacine suka iso birninsu yarima nasmal tun daga sama sukaga irin mummunar barnar da girgizar kasa ta haifar musu sai hankalinsu ya dugunzuma saboda fiye da rabin gidajen birnin sun lume acikin ruwa ga gawarwaki nan na mutane da dabbobi suna yawo akan ruwa har asannan kuma kasa bata daina girgizaba lokaci guda kuma sai komai ya tsaya cak! aka daina girgizar kasar ashe ba komai ya janyo hakanba face uwar macizai ce ta tsaya cak! abakin gabar teku baya ta gama fitowa da dukkannin jikinta gaba daya kawai saita daga kanta sama ne ta dubi gabas da yamma kudu da arewa tana shakar numfashi da kamshi sirrin yin haka kuwa shine tanaso ta jiyo inda kamshin hatyan da 'yar uwarsa sadirat yake ta kai farmaki wajen ashe abinda ya hana ta jiyo kamshin nasu shine girman fuka fukan tsuntsun tsuntsun yaci gaba da tafiya dasu acikin sama harsaida suka iso tsakiyar gidan sarautar birnin wanda kadan daga cikinsa ne ya ruguje kuma tuni a lokacin ma'aikata nata kokarin gyara gamida kwashe. ruwan dayayi ambaliya acikinsa sarki da mukarrabansa na kai kawo acikin gidan sarautar suna kallon masifar da ta faru kawai sai sukaji wata iska mai karfi acan sama koda suka daga kawunansu sama sukaga katon tsuntsu dauke da mutane biyu suna saukowa kasa sai suka kamu da tsananin farinciki nantake garin ya kaure da kade kade gamida bushe bushe da kuma wake wake wani gagarumin buki ake kamar ma an manta da wannan masifa data faru tsuntsun na sauke su hatyan da sadirat sai shima ya rikide ya zama nasmal ya rungume shi yana mai cewa lale marhaban da dana babban gwarzo tabbas saura kiris mu fita daga muguwar fargabar da muke ciki tundaga gashi ka kawo mana wanda muke sa ran zai kare mu daga wannan masifa koda gama fadin hakan sai sarkin ya janye jikinsa daga cikin na nasmal yaje ga hatyan ya rike masa hannu suka gaisa yace marhaban da jarumi hatyan daga makeri satyan kuma almajirin sarkin mafarauta na birnin bindal dukda cewa hatyan ya san al'amarin tsafi sai da yayi mamakin yadda wannan sarki yasan komai haka dangane dashi 〇 sarki ya cire hannunsa daga cikin na hatyan ya mikawa sadirat itama suka gaisa ya dubeta cikin murmushi yace sannu da gwagwarmaya 'yata hakika kin fuskanci tsananin fargaba acikin wannan tafiya amma kiyi hakuri komai ya kusan zuwa karshe da izinin abin bautarmu da yake sadirat bataji yarensa ba bata san me yafadaba saitayi kasake tana kallonsa, al'amarin daya sa dariya ta kwacewa hatyan kenan ya dubeta yace barka da zuwa yayi miki gamida jajen wahalar da mukasha kodajin haka saita rissina ga sarki tana mai nuna alamar godiya awannan lokaci ne mahaifiyar nasmal ta ratso ta tsakiyar taron ta rugo gareshi suka rungume juna tana mai murnar dawowarsa mahaifiyar tasa ta juyo ta kurawa sadirat hannu sannan ta dubi nasmal tayi masa murmushi gamida inkiya wacce tasa sarki da dukkan jama'ar dake wajen banda hatyan da sadirat suka bushe da dariya nantake sadirat taji ajikinta cewa lallai akwai wani abu akasa wanda ya shafi dan sarki kuma ya shafeta tunda saida aka kalleta kuma akayi inkiyar sannan akayi wannan dariya adaidai wannan lokaci ne babban boka na birnin ya ratso cikin taron yaransa biyu na biye dashi bokan ya kasance dogon mutum mai kirar samudawa kuma mai suffar jarumai indai a fagen jarumtakane birnin kaf yarima nasmal ne tsaransa basu taba jarraba jarumtakar junaba amma kowa na shakkar kowa ana kiran wannan boka da suna aimar aimar ya gaji bokancin birnin ne awajen ubansa kuma fiyeda shekaru dari biyu baya zuriyarsuce ke ruke da wannan mukamin aimar ya kasance matashi kamar yarima nasmal kuma mutum ne mai tsananin kishin kasarsa da jama'arsa wani abun mamaki shine da yarima nasmal da boka aiman basa ga maciji amma kuma basu taba zage zage ba ko fada saidai kace na ce kuma duk masifar da zata sami daya dayan bazai taimaka masaba atakaice dai akwai tsama q tsakaninsu wannan tsama ta samo asaline tuun suna yara 'yan kimanin shekaru tara tara abindaya faru shine wata rana sa'adda suka shiga daji farauta sai suka hango wata barewa acan nesa dasu kadan nantake sukayi gasar cewa babu wanda zai harbi barewar da kibiya saidai suyi gasar gudu wanda duk y kurewa barewar gudu ya kamata ta zama tasa agaban sarki da mahaifin aimar aka kulla wannan gasa nantake kuwa aimar da yarima nasmal suka bi barewar da gudun tsiya izuwa cikin jeji tun su sarki na hangosu harsai da suka bace musu da gani shidai karfin gudu baiwane kawai ba tsafi bane ko tsagwaron kwarewa yarima nasmal yafi aimar karfin gudu da juriyar daukarr lokaci amma shi aimar din maguji ne na gaske don haka da farko sa'adda suka fara tseren gudun sai da suka shafe rabin sa'a suna gudun kafada da kafada aka rasa wanda zai tserewa wani idan nasmal yaga aimar ya dan bashi tazara sai shima ya dage ya riskeshi duk wannan abindake faruwa tazarar su da barewar batafi kamu goma ba koda suka sake shafe rabin sa'ar sai aimar ya fara sarewa saboda gajiya aikuwa sai nasmal ya bashi tazarar tsawon taku biyar kawai sai gani yayi baifi saura taku biyuba tsakanin nasmal da wannan barewar aikuwa sai aimar yasa kafa ya tade nasmal ya fadi kasa yanaji yana gani wannan barewar ta tsere cikin tsananin fushi nasmal ya mike tsaye ya zare takobinsa yayi kan aimar kawai sai aimar ya tsaya cak yana kallonsa yana murmushin mugunta koda nasmal yazo dafda aimar ya daga takobin sa sama sai ya kasa sara masa aimar ya tuntsure da dariya yace maza ka kashe magajin dirkan wannan birnin ai kasan hukuncin kisane koda jin wannan batu sai jikin nasmal yayi TARKON MUTUWA PART 8 2D n ai kasan hukuncin kisane koda jin wannan batu sai jikin nasmal yayi sanyi ya sauke hannunsa kasa kuma ya maida takobinsa ya dubeshi afusace yace daga yau nida kai babu abota babu taimako kuma babu yarda her abada Lokacinda boka aimar ya iso gaban ssarki shima da yaransa guda biyu sai suka rissina suka gaida sarki sannan aimar ya durkusa yace ya shugabana munyi babban sa'a da nasmal ya rikide ya koma tsuntsu alokacin daya daukosu hatyan da 'yar uwarsa domin girman fuka fuknsane ya hana uwar macizai jin kamshin su hatyan har suka iso nan gidan sarautar amma da zarar daya daga cikinsu ya fita daga nan zataji kamshin sa ta taso idan kuwa ta taso komai da kowa saiya hallaka yanzu muna da damar da zamu gabatar da wannan gasa domin mu gani ko jarumi hatyan ne bakon jarumin da zai iya kashe wannan uwar macizan koda boka aimar yazo nan azancensa sai kan hatyan ya daure yace a ransa au har a yanzunma babu tabbacin cewa nine zan iya kashe wannan macijiya harsai an gudanar da wata gasa aikuwa indai hakanne to tsafi ya zama shirmen banza tunda baya iya tabbatar da abu guda daya lokacin da sarki shamsal yaji batun boka aimar sai yayi murmushi yace wannan yayi kyau yanzu tunda day uwar ba zata motsa ba face daya daga cikin wadannan baki ya fita daga cikin nan muna da dan kwanciyar hankali saboda haka sai bakin namu suje suci abinci su huta inyaso saida yamma mu gabatar da wannan gasa gama fadin haka keda wuya sai yarima nasmal ya kama hannun hatyan ya jasu domin su tafi makwancinsu amma sai aimar yayi wuf ya sha gaban sadirat ya dubeta cikin murmushi kuma ya bude baki cikin yarenta yace lale marhaban da zinariya abar kyalkyali wacce na dade ina jiran ganin haskenta ya sadirat 'yaga makeri satyan Cikin tsananin mamaki sadirat ta bude baki da nufin ta tambayi aimar yadda akayi ya santa kuma ya iya yarenta ,amma sai nasmal ya shiga tsakaninsu ya dubeshi yace baka da ikon yin magana da wadannan baki nawa face da izini na Wannan yasa nima na tsaya anan. wannan ci gaban 8 D ne shiyasa nasa 2D. Part E Loading..... TARKON MUTUWA PART 8 E Gama fadin hakan keda wuya sai nasmal ya kama hannun hatyan dana sadirat ya jasu da sauri suka nufi wani bangaren

Chapter 9 of 11