Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 11
su ritsaku acikin tekun nan su hallakaku . kuyi hakuri da ban iso akan lokaciba har sarki shamsal yaci karfinku ya kusa hallakaku adai dai wannan lokacine jirgin ya iso bakin wannan gaba koda ma'aikatan sukayi arba da sarauniya badi'atul nauwara sai suka zube kasa suka kwashi gaisuwa nantake sarauniya badi'atul nauwara taja shugaban ma'aikatan gefe daya suka tattauna ba tare da bata wani lokaci ba aka shiga cikin jirginnan aka dauki jarumi hatyan aka shigar dashi cikin wani keken dokin suka zauna akaja aka tafi dasu izuwa cikin gari. tafiyar su keda wuya sai ma'aikatan tashar jirgin suka janyo wannan jirgin wanda su hatyan sukazo a cikinsa izuwa gefe daya suka cinna masa wuta harsaida ya kone kurmush tokarma sai aka kwasheta duka aka watsa ta acikin tekun yadda babu wata shaida da zata nuna alamar cewa akwai alamar jirgin da yazo wajen. al'amarin su sarauniya badi'atul nauwara kuwa lokacin da suka baro bakin tashar jikin ruwan sai suka ci gaba da tafiya ba sassauci harsuka iso birnin askandariya wani abu daya daurewa hatyan kai shine duk da cewar ko ina ga hotunansu nan amanne acikin birnin,jikin katangun,bishiyoyi ,da gidaje kuma basa yin tafiyar data wuce rabin sa'a ba tare da sun iso inda dakarun birnin keyin bincike ba amma duk inda sukazo da zarar anga wannan keken doki da suke ciki sai abasu hanya su wuce ba tare da an bincikesu ba ko cikin keken dokin ba ba'a lekawa bisa wannan daliline sadirat ta kasa hakuri ta dubi sarauniya tace ya shugabata ni fa wani abu ya shige mini duhu, me yasa tun a bakin tashar jirgin ruwan nan banga an tuhumemuba alhalin gashi ko'ina an baza hotunan mu nida dan'uwana ,ana nemanmu ruwa ajallo? yanzu ma da muka shigo cikin garin nan naga an zuba tsaro ko'ina wasuma daga cikin dakarun idan suka leko waje daga cikin keken dokin ina hada idanu dasu amma sainaga sunkawar da fuskarsu sunci gaba da harkokinsu. koda sadirat tazo nan azancenta sai sarauniya badi'atul nauwara ta kyakyace da dariya sannan tace ai mulkin babban birni mai tarin al'umma da karfin arziki anahiyar nankaf banda birnin bindal babu birnin dayafi nawa daukaka shikansa wannan birnin na askandariya yana kasan nawa kuma sarauniyarsu kawata ce aminiyata tun kuruciya akwai zumunci mai karfi atsakaninmu tun iyaye da kakanni. tunu na tattauna da ita akan matsalarku kuma mun gano cewa zaluntarku sarki shamsal yayi hatta kashe iyayenku da dansa yayi da kuma yunkurin yi miki fyade duk munje munbi diddigin komai bisa wannan daliline muka dauki alkawarin taimakon ku har izuwa lokacinda zaku sami damar ficewa daga wannan kasa Dukda cewa jarumi hatyan na cikin mawuyacin hali na rashin lfy,ko kyakkyawan motsi baya iyawa amma tunda ya farajin muryar sarauniya badi'atul nauwara sai farin ciki ya turnukeshi ,yayi ta satar kallonta ,da zarar yaga ta juyo zasu hada idanu sai yayi saurin kautar da idonsa haka dai sarauniya badi'atilnauwara da sadirat sukaci gaba da hira har suka iso gidan sarautar birnin askandariya gidan sarautar yakawatu ainun kamar yadda aka kawata gidan sarautar sarauniya badi'atul nauwara da isowarsu tsakiyar harabar gidan sarautar dai suka iske sarauniya anisa a tsaye tare da hadimanta da kuyanginta suna jiran isowarsu, nan take aka fiddo jarumi hatyan daga cikin keken dokin aka dorashi akan wani gado mai kama da makara aka shige dashi izuwa gidan sarautar koda akazo giftawa dashi ta gaban sarauniya anisa sai tayi masa kwakkwaran kallo guda daya ta yi murmushi. sannan ta kautar dakai ta nufi inda sarauniya badi'atul nauwara take ta rungumeta cikin farin ciki tana mai cewa lale marhaban da babbar kawata kuma babbar aminiyata awannan lokaci, tuni sadirat tabi hadiman da suka dauki hatyan da sauri abaya. sarauniya anisa ta kama hannun sarauniya badi'atul nauwara tajata suka nufi turakarta suna tafe suna hira cikin nishadi da farinciki tamakar 'yan uwan da suka jima basuga junaba. da isowarsu cikin turakar sai aka kawowa badi'atul nauwara abinci da abinsha sama da kala goma sha tara aka zube agabanta bisa wani babban teburi take sarauniya anisa tayi mata tayi har badi'atul nuwara ta yagi cinyar kaza takai bakinta da nufinta ci,saita fasa ta ajiye al'amari da yayi matukar baiwa sarauniya anisa mamaki kenan ta dubeta tace me yasa kika ki cin abincin? badi'atul nauwara tace tayaya zan iya cin abinci ba tareda abokan tafiyarmuba maza kisa akaini inda aka kaisu domin naga halin da suke ciki, ina fatan dai tuni kin baiwa likitocin umarnin suje su duba lafiyar jikinsu? kodajin wannan batu sai sarauniya anisa ta kyalkyale da dariya tace kawata kenan lallai idan kaga kare yana lasar takalmi to dauka zaiyi damuwarki akan hatyan ta fara yin yawa ,anya kuwa baki kamu da sonsa ba? kodajin wannan tambaya sai badi'atul nauwara tayi murmushi sannan tace da ganin sarkin fawa sai miya tayi zaki? tsananin tausayinsu ne yasa nake damuwa da al'amarinsu kin sani cewa na tsani zalunci mun dade ni dake muna tunanin hanyarda zamu bi mu kawar da zalunci awannan nahiyar amma mun kasa saboda al'amarin yafi karfinmu. masana da masu bincike sun gano cewa wannan yaro hatyan shine zai kawo sauyin komai awannan nahiya bisa wannan daliline na siyar da rayuwata kuma nayi karambanin wasa da karagata domin ceto rayuwarsa kinsani cewa idan sarki shamsal ya gano cewa ina da hannu akan taimakon su hatyan saiya yakeni ya rushe mulkina ya dawo da birnina karkashin nasa yanzu ke atunaninki duk nayi wadannan abubuwa ne saboda soyayya? sarauniya anisa tayi dariya akaro na biyu tace babu abinda mutum bazai iya yiba akana soyayya....wlh kuwa ko nima ina yin fin hakan indai akan so ne ni auwzab badaga nan ba . amma babu komai ai sannu bata hana zuwa saidai adade ba'aje ba shi so baya buya komai daren dadewa sai ya fito fili. abu na biyu da nakeso na sani shine yanzu ba ke kadai bace acikin tarkon sarkin shamsal ba. nima ina ciki tunda na baiwa su hatyan masauki nasa akula da lafiyarsa,kuma na boye shi atakaice dai ni dake yanzu duk masu laifine duk hukuncin da za'a yanke miki nima shi za'a yanke mini. koda gama fadin haka sai sarauniya anisa ta mike tsaye ta kama hannayen sarauniya badi'atul nauwara ta rukesu tace kwantar da hankalinki yake kawata kiyi sani cewa har abada asirinmu bazai tonuba awajen sarki shamsal. da farko kije ki ziyarchi kabarin iyayenki ki yi musu addu'a saboda babban kokarin da sukayi miki ya zamana cewa bakyayin tsafi kuma baya tasiri ajikinki. wannan daliline yasa sarki shamsal bazai taba gano cewa kece kika ceci su hatyanba. sannan duk wata shaida da zata nuna akwai hannunki ataimakon hatyan na gogeta,baza'a taba ganintaba. hatta jirginki wanda su sarki shamshal suka gifta da shi asama lokacin da suke kan jibgegen tsuntsun tsafi . idan sukazo garinnan sai sunyi bincike akansa. nasani cewa kinbar jirgin ya nutse a karkashin ruwa. don haka tuni na tura an dauke jirgin daga karkashin ruwa an batar dashi sannan kuma nasa an kera irinsa sak. an kawoshi bakin tashar jirgin ruwan garinnan yadda idan su sarki shamsal sunzo zasu riske shi kuma nashirya komai zasu tarar da cewa jirgin na fatakene. duk irin binciken da sarki shamsal zaiyi bazai iya gano komaiba. a yanzu haka suna tafe izuwa birnin nan. shi da kansa, boka daizur amma babu abinda zai faru. harsu gama bincikensu su kara gaba. ni kawai tashin hankalina daya ne sarki shansal bazai daina bin su jarumi hatyanba. kuma bazai daina farautarsuba.tabbas akan hamyoyinsu ma na gaba sai ya dana tarkunan mutuwa na farautarsu wadanda sai da tsananin rabo ne zaisa su tsira da rayukansu. lokacin da sarauniya anisa tazo nan azancenta sai badi'atul nauwara ta kawo gwauron numfashi ta ajiye sannan tace hakika duk abinda kika fada gaskiyane to amma muddin ni dake zamuci gaba da basu kariya aduk inda suke babu abinda zai samesu. kisani cewa tsiransu shine tsiranmu domin duk ranar da suka fada hannun azzalumi sarki shmsal muma asirinmu ya tonu domin zai sami damar ganin duk irin taimakon da muka basu. koda jin wannan batu sai hankalin sarauniya anisa ya dugunzuma ainun tayi shiru tana nazarin al'amarin acikin zuciyarta. abinda nakeso dake shine ki yi mana tunani akan hanyar da zamubi muci gaba da bawa su hatyan kariya har zuwa lokacin da hatyan zai koma birnin bindal ya dauki fansar abinda akayi masa. nima zanje nayi nawa tunanin daga yau zuwa kwanaki uku in yaso sai kowannan mu yazo da tunaninsa muga yadda zamu hada karfi da karfe don cikar burin mu. yanzu zanje na kwanta na huta don kawarda gajiyar tafiyar dake tare dani. koda gama fadin haka sai sarauniya badi'atul nauwara ta juya ta fice daga cikin turakar sarauniya anisa ta nufi inda masaukinta yake wanda ya kasance wani kasaitaccen gida acikin gidan sarautar inda aka saba bata aduk sa'adda ta kawo ziyara wannan gida akwai kuyangi, barori da kuyangi da hadimai da sauransu PLS LIKE AND COMMENTS TARKON MUTUWA Littafi na hudu Part 4 B . . Tawuce tashiga masaukinta ta kwanta amma sai takasa bacci saboda tinanin su jarumi hatyan sai tai karo da shugaban dakarun da yake gadin gidan yace ina zataje haka?? Kodajin wannan tambaya sai sarauniya badiatul nauwar tayi murmushi tace ba wata matsala, kawai dai nakasa barcine shine na yanke shawarar na fito na kaiwa abokan tafiyata ziyara domin naga halin da suke ciki musamman ma maralafitar kodajin wannan batu sai shugaban dakarun yayi dan guntun murmushi yace ai suma yanzu barcin sukeyi da dai zaki hakura saida safe zaifi miki kyau badi'atul nauwara ta gyada kai tace a'a na damu kwarai ko kallo daya nayi musu zai wadatar basai na tashesuba, na rokeka dakayi mini jagora izuwa masaukin nasu domin ni ban saniba ba tareda wata gardama ba shugaban dakarun ya juya ya nufi wani bangare na daban na gidan sarautar,, badi'atul nauwara na biye dashi abaya, koda suka iso inda masaukin su hatyan yake sai badi'atul nauwara taji zuciyarta ta buga da karfin gaske kuma nan take hankalinta ya duguzuma ainun fiye da koyaushe , ba komai ne ya janyo hakaba face tsananin kishi gamida tsananin mamaki, abindaya fara fado mata arai shine yanzu dama akwai wannan kasaitaccen guri acikin gidan sarautar nan, amma anisa bata taba saukata acikinsa ba duk da irin amanar dake tskanin mu? gama yiwa kanta wannan tambaya keda wuya sai taga ashe sabon gini ne abindaya kara firgita ta kenan tace aranta tabbas anisa tana son hatyan to amma yaushe ta fara sonsa alhalin ma bata taba ganinsa ba sai yau din nan? hakadai badi'atul nauwara tacigaba da wannan zargi acikin zuciyarta har suka iso masaukin kai tsaye shugaban dakarun ya nuna mata kofar shiga turakar dasu hatyan ke kwance ya juya ya barta awajen cikin sanyin jiki ta nufi kofar ta murda mabudin kofar ahankali ta dan jawo kofar kadn koda ta leka ta hango hatyan tare da yar'uwarsa sadirat kwance akan gado suna ta faman sharar barci sai zuciyarta tayi sanyi nan take taji wani irin farinciki ya lullube zuciyarta saida sarauniya badi'atul nauwara ta shafe kusan sa'a guda tana mai kurawa hatyan idanu tana murmushi batareda tasan cewa ta dade awajenba gyaran muryar shugaban dakarun ce yasa ta firgita kamar wacce ta farka daga barci ta waigo ta dubeshi afirgice shugaban dakarun ya rissina kansa na kallon kasa yace ranki ya dade kin dade anan a tsaye gashi har alfijir yakusan ketowa. daji haka sai badi'atul nauwara taji kunya ta kama hamma da yake tasan cewa baisan abinda take kalloba sai tayi murmushi tace hakane ai hakanne kadai zai deben kewar rashin barcin yau tana gama fadin hakan saita juya ta koma masaukinta ta kwanta wani ikon Allah kuwa kwanciyarta keda wuya ta kama gyangyadi. kafin cikar wasu yan dakiku barci mai nauyi ya saceta inda ace wani ya shigo cikin dakin awannan lokaci da ba karamar kunya zatajiba, domin ambaton sunan jarumi hatyan takeyi acikin mafarki. barcin sa'a daya da rabi kacal badi'atul nauwara tayi kawai sai taji ana tashinta afusace ta bude idanunta da nufin taga wanda ya tasheta da fada cikin mamaki sai taga ashe sarauniya anisa ce da kanta take tashinta, cikin hanzari gami da mamaki badi'atul nauwara ta mike zaune ta dubi anisa tace lafiya kuwa na ganki a daki da sassafe haka? anisa tayi dan guntun murmushi cikin alamun yarda da kai tace sarki shamsal tareda dakarun sa da bokansa sun iso nan da kankanin lokaci zasu iso fadata kodajin wannan batu sai badi'atul nauwara ta firgita domin bata taba jin zuciyarta ta buga da karfiba irin yanzu tamkar bata kasance jaruma ba koda anisa ta fahimci hakan saita kyalkyale da dariya sannan ta dubeta tace haba kawata yanzu saboda kawai na ambaci sunan sarki shamsal saiki firgita haka,, shin kin mantane cewa ke jarumace ta gaske mai tsananin sa'a da rabo bisa duk inda kikasa agabanki? shinkin mantane. cewa tsafi baya tasiri ajikìnki? banga dalilin da zaisa ki daga hankalinkiba tunda baki da tsautsayi kodajin wannan batu sai badi'atul nauwara ta gyada kai tace ni bana shakkar duk abinda zai sameni tunda duk tsuntsun daýaja ruwa shi ruwa ke duka tsorona shine abinda zai sami hatyan da yar'uwarsa sadirat zaifi kyau na rasa rayuwata amaimakon rayuwarsa ta salwanta. sa'adda sarauniya anisa taji wannan batu sai tadanyi dan murmushi mai kama da yake sannan ta dafa kafadarta tace ki kwantar da hankalinki yake 'yar uwata kiyi sani cewa babu abinda zai sameki ko hatyan da'yar uwarsa sadirat muddin ina kina tare damu ayanzu shine abu na narko da zai fara rufa mana asiri tunda tsafin su sarki shamsal bazaiyi tasiri ba. ahalin yanzu tuni na boyesu jarumi hatyan da'yaruwarsa sadirat acikin wannan gidan sarautar a inda babu mai iya ganinsu komai irin tsananin binciken da zasuyi don haka kema zam boyeki a irin wannan wuri tashi muje na kaiki. cikin sauri badi'atul nauwara ta bi sarauniya anisa a baya alokacinda ita anisa ta surfafi bangon kudu na cikin dakin da isarsu sai anisa ta shafi wani zane na tsuntsun dawisu take bangon dakin ya rabe gida biyu sai ga wata hanya zururu izuwa cikin wani gidan kasa, maidauke da matattakalar bene kawai sai anisa ta dubi badi'atul nauwara ta ce nagina wannan wurine saboda irin wannan rana ta yau kishiga ciki zaki sami komai dakike bukata koda zaki zauna acikinsa babu abinda zaki rasa saidai kawai kadaici dazai sameki, cikin tsananin alamun damuwa badi'atul nauwara ta dubi anisa tace meyasa bazaki kaini can inda kika boye su hatyan ba na kasance tareda su. wai shin me yasa kika ba su masaukin da yafi nawa daraja? anisa ta sake duban badi'atul nauwara cikin murmushi a karo na biyu tace kiyi hakuri kawata ayanzu bani da lokacin dazan iya yi miki cikakken bayani amma da zarar sarki shamsal da bokansa sun gama binciken su sun tafi zamu zauna kiji bayanin komai, kin san koni wacece kuma kin yarda dani dari bisa dari har abada bazan taba cutar dakeba, kamar yadda kema bazaki cutar daniba, don haka kawai kiyi duk abinda na umarceki dayi. kodajin haka sai badi'atul nauwara ta juya tabi cikin wannan bango daya bude ta taka matattakalar bene izuwa gidan kasa ita kuwa sarauniya anisa sai ta sake shafar saman wannan zanen tsuntsun dawisu nan take bangon daya rabe biyu ya koma ya hade tamkar bai taba rabuwa ba faruwar hakan keda wuya sai sarauniya anisa ta juya da sauri ta fice daga cikin wannan turaka tana fita ta iske dakarunta masu take mata baya da kuma manyan hadiman ta suna jiranta nantak suka rufa mata baya izuwa fadarta tuni a wannan lokaci sarki shamsal da boka daizur sun iso cikin gidan sarautar sarkin fada yayi musu jagora izuwa cikin fadar sarauniya anisa tana zaune bisa karagar mulki ga fadawanta da sauran jama'arta sun kewayeta ana tafiyar da harkokin mulki saiga boka daizur da sarki shamsal sun shigo cikin fadar sarkin fada nayi musu jagora tun daga nesa da sarauniya anisa ta hango su ta mike tsaye daga kan karagar mulkinta fuskarta cike da annuri da gami da murmushi tatari su sarki shamsal tana mai nuna tsananin farincikinta da ganinsa koda ta iso daf dashi saita kama hannun sarki shamsal na dama ta sumbaci saman hannun cikin girmamawa tace lale marhaban da sarkin sarakuna kuma jarumin jarumai na wannan nahiya gaba daya, ya shugabana banyi mamaki da wannan ziyara takaba ta bazato tunda kana farautar makiyanka guda biyu kodajin wannan batu sai sarki shamsal da boka daizur sukayi shiru sannan sarki shamsal ya dubi anisa yace hakika kinyi gaskiya yake wannan sarauniya anisa tace tun dazu da na ji labarin shigowarka birnina nasa aka gyara maka masauki kuma akayi maka masauki tanadin abincin da kafiso gami da ababen sha akwai tsala tsalan yan mata wadanda suka kware wajen debe kewa kuma akwai abinci da abinsha irin wanda kafi so arayuwarka. kodajin wannan batu sai sarki shamsal ya tirbune fuskarsa kamar an aiko masa da sakon mutuwa al'amarin dayai matukar razana sarauniya anisa kenan taji hantar cikinta ta kada kuma taji kamar ta saki fitsari awando amma sai ta dake don kada sarki ya fahimci rashin gaskiyarta ta dan russina tana mai sunkwuyar dakai kasa tace ka gafarceni yakai wannan sarki idan wannan batu nawa ya bata maka rai kodajin haka sai sarki shamsal ya takarkare ya bushe da dariyar muganta tamkar baya da wata damuwa,, lokaci guda kuma sai ya hade fuskarsa ya dubeta yace yake wannan sarauniya kiyi sani cewa a duk lokacin da muke kan farautar abokan gaba bama ci kuma bama sha kuma bamayin nishadi tamkar zakin dayake fama da matsananciyar yunwa kuma yagama karade daji yana neman abinci bai samuba ina mai tabbatarmiki da cewa ni yanzu babu wani mahaluki wanda na yarda dashi awannan nahiya tamu. a takaice dai ban yarda da kowaba don haka kowa zai iya cutar dani ya boye abokan gaba ta danazo nema dakaina cikin wannan birni naki don na bincika ko ina da ina, tun kafin na fara binciken ina mai shawartarki da idan kinsan inda wadannan makiya nawa suke toki hanzarta fito dasu ki damka minsu ahannuna idankuwa kikaki kuma na samesu acikin birninki na rantse da gemun mahaifina saina baje wannan birni naki gaba daya nayiwa kasa ado da jinin jama'arki duka ko kazarku guda daya bazata tsira da rayuwrtaba, sa'adda sarauniya anisa taji wannan batu saita danyi guntun murmushi mai nuna yarda dakai ba tareda alama ta fargaba ba tabbas kowa agidansa sarkine cikin jin izzar mulki sarauniya anisa ta gyara zamanta akan karagarta ta mulki tana mai dora kafarta daya bisa dayar sannan tace yakai wannan sarki mai daraja kayi sani cewa kofofin ko ina da ina acikin wannan birni abude suke agareka domin kayi bincike idan her ka kamani da wani laifin boye makiyanka nayi maka alkawarin zan kashe kaina agaban idanunka. kodajin wannan batu sai mamaki ya kama kowa da yake wajen nantake jikin sarki shamsal yayi sanyi amma sai sarki shamsal ya sake duban ta cikin alamun rashin yarda kuma ya maida mata da martanin murmushi na mugunta yace nayi farinciki da wannan mataki da kika dauka ina mai sanar dake akwaì hadimaina wadanda suka kware ainun wajen iya bincike suna nan tafe izuwa wannan birni naki nan da gobe da yammaci tare dasu zanyi wannan aiki inaso ki bani izini na shiga koina acikin gidajen birnin. TARKON MUTUWA Littafi na hudu Part 4 C . . Dajin wannan batu sai sarki shamsal ya yi kwafa cikin kunar rai yace aikuwa indai muka kama su jarumi hatyan acikin wannan birni sai na wulakanta wannan sarauniyar ainun wulakancin da bata taba ganiba arayuwarta nan take shamsal ya juya ya dubi anisa cikin murmushin yake ya ce shikenan na amince da wannan sharadi naki amma ki sani cewa zan iya fara bincikena ako yaushe daga yanzu kuma ko cikin turakrki ne zan iya shiga babu hijabi dajin haka sai sarauniya anisa tayi murmushi ayau dinnan babu wata kofar dakin da za'a rufe awannan gidan sarautar hatta kofar dakin barcina kuwa inayi maka lale ako yaushe. anisa na gama fadin hakan saita mike tsaye daga kan karagar mulkinta ta dubi sarkin gida tace akai sarki da bokansa masaukinsu,, kuma duk sa'adda yake son fara bincike kayi masa jagora ka nuna nasa ko'ina acikin gidan sarautarnan sarkin gida ya rissina yace angama ya shugabata nan take sarauniya anisa ta juya ta nufi kofar fita daga awannan lokaci sarauniya anisa tana sanye da wata doguwar riga irin tasu ta mulki wacce ta kasance matsatsiya kuma launinta shudine anyi mata adon furanni da zaren zinare gaba daya surorin jikinta sun fito karara acikin wannan riga don haka sarki shamsal baisan sa'adda ya rudeba,, kuma ya kidime duk da cewa shi arayuwarsa mace bata dameshi ba nan take sarki shamsal ya ayyana aransa cewa baitaba ganin mace mai kyauwun surar jikin anisa ba arayuwarsa anisa ta kasance kyakkyawar budurwa kamar sarauniya badi'atul nauwara amma ta fita tsawo da kadan kuma ta fita cikar zati da cikar sura tanada yalwar gashin kai na musamman domin kalarsa ba baki bane shudine kuma haka aka haifeta dashi, ruwan kwayar idanuntama shudine wadanda suke matukar kara mata kyau bisa wannan daliline ko yaushe anisa takeyin ado da shudin sutura kowa yana al'ajabi da wannan baiwa tata ta shudin idanu da shudin gashi babu wani da namiji dazai yi arba da sarauniya anisa baiji kyanta da surar jikinta sun bashi sha'awa ba face ya kasance mara lafiya ita kanta tana alfahari da wannan baiwar da Allah ya bata hatta yan uwanta mata sunayin sumbatu akan hakan, akwai lokacin da sarauniya badi'atul nauwara ta dubeta tace yake kawata kiyi sani cewa inda ni namijice to da saidai na mutu a kokarin samun soyayyarki, idan kuwa na rasaki saidai na mutu gwauro domin babu irinki aduniya ban taba jiba ko labari, kodajin wannan batu sai sarauniya anisa ta kyalkyale da dariya sannan ta hade fuska tace ai kuwa duk wanda zai mallaki zuciya ta ina tausaya masa cikin mamaki badi'atul nauwara ta dubeta tace bangane kina tausaya masa ba kamar yaya kenan? anisa tayi murmushi tace kafin na aminta dashi na bashi soyayyata saina bashi wahala tamkar ransa zai fita saboda wadansu mugayen jarrabobi zanyi masa badi'atul nauwara tace kekuwa wadanne irin jarrabobi zakiyi masa? anisa tace wadannan kuma sirrine na barsu acikin zuciyata bazan iya fadawa kowaba sai mai tsantsanin lura da kaifin tunanine zai iya ganosu,, ko ya gansu da idanunsa ayayin da abin yake faruwa idan muna tare. ficewar anisa keda wuya daga cikin fadar sai sarkin gida ya wuce gaba,, sarki shamsal da boka daisur suka bishi abaya har suka isa masaukinsu gidane guda acikin masarautar wanda akayi na musamman don saukar sarakuna irinsu sarki shamsal komai na kawa dana jin dadin rayuwa an tanadeshi acikinsa, hadimai kuwa gasunan birjik, kai kace suke yiwa sarauniya anisa hidima bayan sarki shamsal sun zauna acikin wani babban falo sai aka kawo musu abinci dana sha kalakala masu daraja,, nantake kamshin ya cika falon gaba daya, boka daisur baisan sa'adda ya wangame hancinsaba ya faralumshe idanu koda kuyanginda suka kawo abincin suka juya suka fice daga cikin falon sai boka daizur yayi wuf yakai hannun sa izuwa kan wata katuwar kaza ya yago cinyarta zai kai bakinsa,, sai sarki shamsal ya daka masa tsawa ba shiri ya jefar da cinyar kazar sarki shamsal ya dubeshi a fusace yace baka da hankali ne daga kawo abinci zaka kamaci? kodajin haka sai boka daisur ya bude idanunsa ya fara karanto wadansu dalasiman tsafi kawai sai ya bude idanunsa ya dubi sarki shamsal yace babu wata guba acikin wannan abinci,. ba tareda fargabar komaiba suka kama cin abincin harsaida suka gama kimtsa cikinsu dayansu baice kalaba asannan ne sarki shamsal ya mike ya juyawa boka daisur baya yace maza ka sakeyin bincike ka gani ko anan cikin gidan sarautar aka boye su hatyan da'yaruwarsa sadirat kai kodama binciken naka ya nuna basa nan to bazamu fasa namu bincikenba na zahiri, ni yanzu zanje na kwanta domin na rama bashin barcin da mukayi amma dare na rabawa zan tashi mu fara aiki sarki shamsal na gama fadin hakan sai ya nufi cikin dakin barcin yaje ya kwanta akan wani luntsumemen gado yayi rub da ciki nan take kuwa barci ya saceshi harda minshari, al'amarin boka daizur kuwa saida kuyanginda suka kawo musu abinci suka dawo suka kwashe kwanukan abincin suka fice sannan yatashi ya rufo kofar falon da tagogi sannan yazo ya zauna ya fiddo madubin tsafinsa ya ajiyeshi akan wani tebur dake gabansa ya shafeshi da hannunsa na hagu domin yaga duk abinda ke faruwa acikin gidan sarautar ako wanne lungu da sako kwatsam ba zato ba tsammani sai yaga madubin tsafin yayi bakikkirin babu alamar haske al'amarin dayai matukar firgitashi kenan yayi wuf ya dauke madubin tsafinsa ya zurashi a aljihun rigarsa ya mike tsaye cikin razani, gami da tashin hankali. tabbasyanzu ya tabbatar da cewa tsafinsa bashi da wanì amfani awannan birni nan take mamaki ya baibayeshi ya kama tunani da mamaki inda ya tambayi kansa acikin zuciyarsa yace mene dalìlin dayasa tsafi yaki aiki agarinnan alhalin ma yayi aiki agarin sarauniya badi'atul nauwara, kuma yayi tasiri duk da cewa ance ita bata tsafi kuma baya tasiri ajikìnta koda daizur yazonan azancen zucinsa,, sai zuciyarsa ta buga da karfi yace anya kuwa sarauniya badi'atul nauwara na nan acikin birninta? ai indai tana birninta babu yadda za'ai tsafina yayi tasiri. to amma kuma lokacin da mukayi bincike munganta afadarta amma sau daya kuma kafin mu fara bincikenmu ne anya kuwa bayaudarar mu tayiba ta rigamu zuwa garinnan, idan kuwa hakane to tabbas da hannunta aboye su jarumi hatyan kai ammafa abinda kamar wuya saboda batayin tsafi kuma babu wani abin hawa dazai kawota kafin mu iso tunda dai mu akan tsuntsun tsafi mukazo yanzu idan na gayawa sarki cewa tsafina yaki tasiri agarinnan to zai fusata ainun yace na raina masa hankali tunda nace dashi yayi aiki abirnin sarauniya badi'atul nauwara banida abinyi yanzu face nasa ido sosai akan binciken da zamuyi yanzu,, tunda dai ina zargin cewa badi'atul nauwara tana cikin garinnan idan kuma tana nandin to itama sarauniya anisa tana da hannu gabaki dayansu tunda dama kawartace tun kuruciyarsu koda boka daizur yazo nan a tunaninsa saiya baje akan doguwar kujera,, amma sai daya dade yana tunanin zuci gami da zulumi sannan barci ya daukeshi, TO ANAN AKAZO KARSHEN LITTAFIN TARKON MUTUWA NA HUDU SAI MUN HADU A LITTAFI NA BIYAR 5 TARKON MUTUWA TARKON MUTUWA LITTAFI NA BIYAR PART A & B Kash ! rashin sani yafi dare duhu hakika masu iya magana sunyi gaskiya da sukace ga magani a gonar yaro amma bai saniba Ashe mabudin dakin kasa inda aka boye su hatyan da yaruwarsa abakin kofar shigowa falon take,sai andaga daddumar da ma ake takawa sannan a zare wani tubalin zinare da aka shimfida akasa akayi ado dashi,kuma na farko Sannan zata bude a taka matattalalar benen izuwa kasan da daddumar sai da boka daizur ya dafa ya tattaba tubalin zinaren duka, gamma tunaninsa da basirarsa batakai kan ya care tubalinba . bayan sun gaji da bincike basuga komai ba sai sarki shamsal ya dubi sarauniya anisa yace ki gafarcemu yake wannan Sarauniya kiyi sani cewa aiki ne yajanyo muka saki wanna wahala ayanzu dai bamuga Komai ba amma hakan ba yana nufin mun cire zargi daga ranmu baneba kamar yadda nake fada miki abaya zamu fara yin bincike na biyu yayin da hadimaina kwararrun iya bincike suka iso ayau dinnan yanzu nida bokana Zamu koma masaukinmu mu kwanta domin Rama barcin da muka rasa a yanzu ba zamuci gaba da bincikeba sai da farkon yammaci gama fadin Hagan keda wuya sai Sarki shamsal da boka daizur sika juya suka fice daga cikin turakar suka isa masaukinsu, suka koma suka fara sabon barci ba tareda sunyi kalaciba, wanna shine abin da yafaru abirnin askandariya a Daren dasu Sarki scandal suka hallara zuwa kashe gari acan birnin bindal kuwa tin lokacin da Sarki scandal yabar gari domin tafiya farautar babban abokin gabarsa wato hartayn sai aka shiga wata babbar masifa wacce ta dugunzuma hankalin gaba daya masu mulki da manyan Gari baki daya ba komai bace wanna masifa ba face mulkin yarima zainur ya shirya rundina a cikin Daren kawai sai wayar gari akayi akaga an kama gaba daya manyan garin wadanda suka kasance amintattun sarki shamsal wadanda zasu iya sadaukar da rayuwar su dominsa an kashesu sauran yan majalisar kuwa da manyan gari sai gasu sun taru afada gaban yarima don yin mubaya a yana zaune akan karagar mulki wani bakon boka ma abocin kwarjii yana tsaye abayansa Yarima yanata kyakyata dariyar mugunta yagaji a wannan lokaci fadar tayi tsit babu abinda akeji kai bawai acikin fadarba har acikin gari ma duk inda ka gifta sai dai kaji tsit saboda tsananin firgitar da jama’a sukayi saboda sun sami labrin cewa yarima zainur ya yi juyin mulki nan take yan mata da zawarawa suka farayin hijirar sirri don kada zaluncin sabon sarki ya fada kansu bayan yarima zainur yayi dariyar farinciki ya gaji saiya dubi gaba daya yan majalisar dake cikin fadar da dukkan fadawa da dakaru wadanda har izuwa wannan lokaci a firgice suke kamar kace kyat su saki fitsari awando yarima zainur yayi ajiyar numfashi cikin murmushi yace yaku jama’ata kuyi sani cewa komai nisan jifa kasa zai fado ina mai tabbatar muku da cewa lokacin zaman mahaifina akan wannan kujerar mulkin ya kare har abada bazai sake zama akan wannan kujeraba.don haka yanzu sabon sarki sabon birni sabuwar rayuwa kamar yadda nayi muku alkawari tun adaren jiya kowannenku zan linka.masa albashinsa kuma zan rinka kyautata muku sabanin mahaifina da wani hakkin nakuma cin yewa yake abinda nake bukata daku kawai shine kada dayanku yasa mini ido akan harkokina ko yace zai ja dani indai kukayi hakan zaku sami arziki mai yawa daga gareni wanda baku taba samuba nasani cewa hankalinku a tashe yake akan tunanin cewa idan sarki ya dawo bazai kyalekuba kasheku zaiyi to ku kwantar da hankalinku ku sani cewa babu abinda sarki zai samo awannan tafiya face ajalinsa tabbacin haka shine gaba daya bokayen dake wannan nahiyar tamu sunyi bincike sun tabbatar da hakan wannan boka da kuke gani kusa dani shine boka arzus bin sharkub shima ya tabbatar da hakan bisa wannan dalili nema yazo ya zauna tare dani. domin biyan wata bukatarsa wacce ta kawoshi wannan nahiya tamu tsawon shekara talatin baya bai sami damar cikata ba koda yarima zainur yazo nan azancensa sai gaba daya mutanen da suke cikin fadar suka kamu da tsananin mamaki kuma dukkaninsu suka kurawa boka

Chapter 5 of 11