Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 11
har kusan rabin sa'a dayansu bai sami nasaraba tmakar karfi yazo daya. al'amarin daya fusata jarumi hatyan kenan. kawai sai ya sauya salon yaki ya hada da tsalle da kwance kwance gami da kai naushi da bugu hannu da kafa . ai kuwa nantake labari yasha banban sabida cikin kankanin lokaci ya fara kuntata zainur sqboda bai iya irin wannan salon yakin ba sosai kuma gashi zafin naman hatyan ya ninka nasa sau goma. tun yarima zainur ma iya maida martanin sara da suka har sai daya kasa yazamana cewa da kyarma yake iya kare kansa. ana cikin hakne hatyan ya shammaci zainur ya gabza masa wawan naushi afuska da kafa. daboda karfin naushin saida yarima yayi katantanwa sau hudu atsaye kafin ya dawo haiyacinsa tuni hatyan yasa takobinsa ya sare masa hannunsa na dama. take ya tsinke ya fadi kasa yarima zainur ya kwallara uban ihu sakamakon tsananin zafi da zugin da yaji ya durkushe kasa bisa gwuiwarsa guda yayinda jini ke tq bulbula daga dungulmin hannunsa nasa kawai sai hatyan ya tsaya akansa ya tofa masa yawu a fuska agaban talakawan gari yace yau ina karfin naka kuma ina sarautar taka. ina hannun da kake yiwa yan mata fyade dashi? dajin wadannan tambayoyi sai hawayen takaici ya zubowa yarima zainur ya dubi hatyan yace naramtse da girman abin bauta sai mahaifina ya dau fansa akanka. idan yakamaka ba zai kasheka ba sai ya yanke maka dukkan hannayenka da kafafunka tukunna. kodajin haka sai hatyan yasake tofawa zainur yawu yace inba don nadau alkawarin sai nakashe mahaifinka agaban idanunka da yanzu zan kasheka amma bakomai nasan cewa daga yau baka da hannun yiwa yan mata fyade na taimaki talakawan garinnan. idan ka koma gida kagayawa mahaifinka cewa nin3 jarumin da bokaye suka gaya masa cewa zan karbi karagar mulkinsa don haka.ya zauna ya jira ranar dawowa ta. tabbas yanzu yafi karfina bazan iya dashiba. amma zanje nayi shiri na dawo gareshi alokacin daya dace . koda gama fadin hakansai hatyan ya ruga izuwa inda sadirat take zaune tana kuka ya kama.hannunta ya tasheta tsaye yace yake yar uwata zamanmu a garinnan ya kare .dolene mu tafi izuwa inda zan tserar da rayuwarki iyayen mu sun mutu bamu da hujja ta sake zama anan . wanda ya rage mana kawai shine sarkin mafarauta. idan muka zauna agarinnan zamu janyo masa kisa. gama fadin hakan keda wuya sai hawaye ya zubowa hatyan yaja sadirat izuwa inda dokinsa yake ya dorata akai. shima ya hau kan dokin yayiwa sarkin mafarauta kallon karshe duk su biyun suna zubar da hawaye . ko tsinke su hatyan basu dauka ba amatsayin guzuri kawai sai suka zaburi doki suka nausa cikin daji nan danan suka bace bat tamkar basu taba wanzuwaba. awannan lokacine zainur ya mike tsaye da kyar yana tangadi kamar wanda yasha giya ya bugu ya cire rawanin wani badakare ya nannade dungulmin hannun nasa dakyar amma sai ya kasa zama akan dokin ya kwanta cikin matukar karfin hali ya kamo linzamin dokin ya dan ja. dokin ya kama tafiya a hankali ya nufi hanyar da zata mayar dashi gidan sarauta. maimakon yarima zqinur ya isa gidan sarautar acikin sa'a daya saidaya shafe sa'a biyu saboda ya kasa sarrafa dokin yadda zaiyi sauri dokin na isa kofar gidan sarautar sai yarima ya fado daga kansa ya baje kasa sumamme . a guje dakaru sukazo suka daukeshi suka tafi dashi izuwa ga sarki. koda akazo da yarima gaban sarki ya takarkare ya kwarara uban ihu sannan ya kwallawa likitansa kira. nan da nan kuwa saiga likitan yazo. nanfa ya kama aiki akan yarima amma yarima bai farfadoba sai bayna sa'a guda. yana bude idonsa sai sarki ya dubeshi fuskarsa nayin gyatsine yace wanene yayi maka wannan danyen aiki? yarima zainu ya budi baki yace hatyan ne dan gidan makeri satyan.amma na kashe satyan. kodajin haka sai sarki shamsan ya dafe kansa da hannayensa biyu kuma ya durkusa kasa cikin tsananin takaici ya dakawa yarima tsawa yace . cikin tsanani takaici ya dakawa yarima tsawa yace me yasa kaje gidan satyan bana hanaka zuwa ba? duk yadda akayi satyan nada ya mace kuma kayi yunkurin yi mata fyade koma kayi mata hakane? yarima ya budi baki yace hakane dama satyan nada da babban jarumi haka wanda har ya iya sare ma hannu? yarma yace kwarai kuwa ni arayuwata ma in banda kai ban taba ganin wani jarumi mai irin jarumtakarsa da zafin namansa ba.: kuma yace na gaya maka cewa shine jarumin da zai karbi karagar mulkinka a hannunka tabbas yasan yanzu kafi karfinsa amma ka saurari dawowarsa cikin gagarumin shirin yaki. koda jin haka sai sarki yahamsalya sake kwarara uban ihu a karo na biyu wanda ya firgita duk wata halitta dake gidan sarautar kawai saiya mike tsaye zumbur ya shige cikin dakinsa yayi gagarumin shirin yaki sannan ya tura aka kirawo sarkin yaki ya bashi umarnin a shirya dakaru kamar guda dubu hudu su rabu izuwa gabas da yamma kudu da arewacin birnin, su bazama neman hatyan dan makeri satyan, nantake sarkin yaki yaje ya cika umarni shikuwa sarki shamsal sai ya hau dokinsa tare da tsirarun dakaru suka tafi izuwa gidan makeri satyan kafin su sarki su iso gidan makeri satyan tuni gaba daya mutanen dake unguwar sunyi hijira sun gudu izuwa wadansu unguwoyin sabo da sun san halin sarkinsu na rashin imani dolene hatyan ya shafa musu kashin kaji shi kuwa sarkin mafarauta tuni ya dauke gawar satyan data matarsa ya tafi dasu chan wani jeji ya bunne su yana kuka da bakin ciki sannan shima ya sake nausawa cikin daji rataye da jakarsa ta guzuri da nufin ya tafi kenan har abada bazai sake dawowa birnin bindal ba tunda dama bashi da kowa face wannan abokin nasa guda daya wato satyan gashi an kasheshi. lokacin da sarki shamshal da tsirarun dakarunsa suka iso kofar gidanmakeri satyan sai suka iske unguwar tayi tsit tamkar makabarta nantake sarki shamsal yasa dakaru suka shiga cikin gidan satyan suka duba ko ina amma basu ga kowaba. suka shig gida gida nan ma basu ga kowa ba. al'amarin daya fusata sarki kenan yace 。: akona gaba daya gidajen dake ungwar kuma aje ayi bincike agano mazauna unguwar akamosu akawo su fada. nantake dakaru suka cinnawa gidajen unguwar wuta gaba dayansu suka kone kurmus. mazauna unguwar kuwa daya bayan daya aka dinga kamosu ana gana musu azaba suna bada bayanin abin daya faru amma duk da haka ba'a kyalesuba domin akarshe kurkuku aka akaisu aka kulle bayan sunsha muguwar wahala sannan ne sarki ya sami labarin cewa hatyan ya dauke 'yar uwarsa sadirat akan doki sun gudu. abinda yasa dakarun da aka tura farautarsa basu ganshiba shine yafi sa'a uku da tafiya don haka yayi musu nisa sosai . dama kwanaki bakwai sarki shamsal ya baiwa wadannan dakaru guda dubu dari hudu akan suje suzo da jarumi hatyan da 'yar uwarsa sadirat . kowacce runduna tadakaru dubu dari saida ta dangane da karshen iyakar birni bindal aranar da kwanaki bakwai suka cika koda sarki shamsal yaji cewa ba'a gansu ba sai ya kamu da tsananin mamaki gami da tsananin fushi kuma hankalinsa ya dugunzuma ainun. ya zamana cewa ko barcin kirki bayayi saboda kullum sai yayi mafarki mai ban tsoro . acikin mafarkin sai ake nuna masa cewa ga jarumi hatyan ya dawo birnin bindal tare da miliyoyin dakarun yaki an kachame da azababben yaki an kone gidan sarautar . bisa wannan daliline sarki shamsal ya tura aka kirawo masa bokansa abin dogaronsa boka daizun ya sanar dashi halin da yake ciki kuma ya bukaci ya samo masa mafita . nan take kuwa boka daizun ya zuba alkalumansa na tsafi ya shiga aiki. bayan yayi dan dogon bincike saiya dago kai ya dubi sarki shamsal lokacin da ya jike sharkaf da gumi kuma idanunsa suka kada sukayi jawur kamar garwashin wuta babu kyan gani sannan yace ya shugabana hakika al;amarin wannan yaro akwai rikitarwa. domin akwai sa'a da nasara acikin harkokinsa tabbasa idan har ba'a gano inda yakeba an kasheshi ba to sai wannan mafarki naka ya tabbata abinda na iya gani kawai shine wannan yaro tuni ya fita daga kasarka tare da yar uwarsa domin tafiya ya rinka yi ba dare ba rana. kai lokacin da dokinsa ma ya sare goya yar uwarsa yayi abaya yayita gudu da ita har tsawon kwananki ashirin ba tare daya tsayaba. ko sau daya bai tsaya ba don ya huta saidai kawai yasha ruwa ya mikawa yar uwarsa abinci da ruwa taci ta sha yana kan gudun saboda yasan cewa an biyo bayansa yanzu haka yashiga wata kasa amma na kasa gano bangaren da take. duk yadda akayi wannan yaro yana da sirrin batar da sawun hanya . anya kuwa ba shida watal halaka da mafarauta ba ? kodajin wannan tambaya sai sarki shamsal yayi shiru yana tunani har zuwa tsawon lokaci sannan ya dago kai ya dubi boka daizur yace mahaifinsa aminin sarkin mafarautane . kodajin haka sai boka daizur haba shiyasa na kasa ganin komai akan wannan yaro kayi sani cewa duk garinnan babu wanda yakeda karfin sihirin tsafin sarkin mafarauta . ni kaina awajensa nayi kartun tsafi amma har na kammala bansan rabin nasa ilimin ba. daga bayane nashiga duniya nasamo wadansu sirrikan amma duk da hakan ina shakkar sarkin mafarauta . Toh mun kawo karshen littafi na daya , in sha Allah gobe zamu fara littafi na biyu, Al Amin Misau ke magana TARKON MUTUWA Abdul'aziz Sani Madakin Gini 07067470752 Typing. Prince Auwal Auzab Post. Sunusi SAS Littafi na biyu 2 Part 2A . Duk inda sarkin mafarauta yake ka tura aje azo maka dashi amma bari na bincika naga inda yakedin. koda gama fadin haka sai boka daizun ya zura hannun cikin aljihu ya fiddo madubinsa na tsafi ya ajiye a gaban sarki sannan ya shafi madubin da hannunsa na hagu maimakon madubin yayi haske ya nuna abinda ake so a gani sai yayi duhu dudum ba a ganin komai ko da ganinin haka sai boka daizun yayi ajiyar zuciya yace hakika ai sarkin mafarauta yaudararka yayi kuma yaci amanarka tabbas da taimakonsa wannan yaro hatyan da 'yaruwarsa suka sami nasarar guduwa kodajinhaka sai bakin ciki ya turnuke sarki shamsal yasake kurma uban ihu akaro na biyu kamar zai fashe da kuka sai daya shafe kusan dakika dari da ashirin yana huci da numfarfashi tamkar wani kumurcin maciji sannan yace yakai abin dogarona kayi sani cewa zama bai kamaniba dakaina zan tafi farautar wanna yaro domin na kasheshi tungabanin lokacin da zai dawo ya riskeni harcikin masarautata ya cini da yaki taimakon da nake nema awajenka guda dayane. inason ka banj hadimanka na aljanu kamar guda dari biyar wadanda zasu dauki manzannina sukaisu izuwa ga dukkan kasashen dake wannan nahiya tamu . zasu kai wasiku ne gami da hotuna masu dauke da taswirar hatyan da yar uwarsa acikin kowacce wasika zan gaya kowanne sarki dayasa abaza hotunan hatyan abirni da kauye duk inda aka gansu akamasu a tsare su akurkuku. sannan kuma zansan ya lada mai tsoka na dubban darhami ga duk wanda ya sami nasarar chafkesu. inason cikin kwananki uku kachal agama rarraba wadannan wasiku da hotuna kodajin wannan batu sai boka daizun ya kyalkyale da dariyar mugunta yace ya shugabana hakika kazo da shawara mai kyau domin itace hanyar da zakabi ka hana hatyan da yaruwarsa samun damar fita daga wannan nahiya kuma acikin kankanin lokaci zasu dawo hannuka tabbas kwakwalwarka tana aiki sosai gami da hangen nesa kodajin wannan zuga sai sarki shamsal ya bushe da dariyar farinciki yashiga yiwa kansa kirari batare da bata lokaciba sarki shamsal ya tura akazo da wani makocin satyan sannan aka kirawo masanin zane take makocin ya baiyyana kamannin fuskar hatyan da fuskar yar uwarsa sadirat cikin kankanin lokaci mai zanen yafitar da taswirar tamkar sune awajen ba zanasu akayiba shikuwa boka daizun sai yayi tsafi takardar zanen ta tsaga kanta har guda dubu dari . daga nan kuma sai aka tara manzanni aka rarraba musu wasiku da hotunan hatyn. dayawa aka kirawo aljanu suka tafi dasu izuwa dukkan kasashen dake nahiyar ++ AUWZAB al'amarin yarima zainur kuwa sai daya kwana ashirin da daya akwance yana jinyar dungulmin hannunsa sannan ya warke ya sami karfin jikinsa . duk lokacin daya kalli dungulmin hannunsa kuma ya tuno da cewar bai sami nasarar yiwa sadirat fyadeba . saiya fashe da kukan bakinciki daga wannan lokaci yammatan birnin bindal suka sami nutsuwa da kwanciyar hankali domin yarima zainur bai sake yiwa wata fyadeba. kawai ma sai yazamana cewa ya daina neman mata koda karuwai kuwa kuma bashi da wani buri wanda yafi yaji cewa an kamo hatyan da yaruwarsa sadirat idan har sukazo hannu to yaci alwashin saiya cika burinsa akan sadirat agaban hatyan kuma yayi amfani da lafiyayyen hannunsa ya sare hannun daman hatyan kullum yarima zainur cikin sambatu yake na fadin wannan buri nasa kamar wanda ya zautu . WANNAN SHINE ABINDAYA FARU ABIRNIN BINDAL BAYAN KASHE IYAYEN JARUMI HATYAN SUKUMA SUNYI GUDUN HIJIRA TARE DA YAR'UWARSA SADIRAT SUN NAUSA DAJI BA TARE DA SUNSAN INDA SUKA DOSA BA. al'amarin su jarumi hatyan kuwa lokacin daya zaburi dokinsa da gudu izuwa cikin daji sadirat na goye abayansa saisuka ci gaba da tsala gudu akan doki baji ba gani kamar ba zasu taba tsayuwaba. saida suka shafe sa'a uku suna yin gudu sannan dokin ya fara gazawa ya zamana cewa ya rage karfin gudunsa kai sai da takai cewa ma dokin ya galabaita ya fara sassarfa kamar zai durkushe kasa koda ganin haka sai jarumi hatyan ya ja linzamin dokinsa ya sauka . saukarsu keda wuya sai hatyan ya saki dokin ya kadashi ya ruga izuwa wani bangaren dajin cikin kaduwa sadirat ta dubi jarumi hatyan tace ya zaka sallami dokin alhalin bamu san iyakar inda tafiyarmu zata yankeba.? kodajin wannan tambaya sai jarumi hatyan yayi doguwar ajiyar zuciya yace ai wannan doki amfaminsa ya kare awajenmu tunda ya taimkemu wajen bawa makiya tazara mai yawan gaske amma idan mukaci gaba da fiya dashi sawayen kofatonsa ne zasu tona mana asiri. yake yar uwata ki kwantar da hankalinki kiyi sani cewa indai kina tare dani babu abinda zai sameki. sadirat tace ni kaina ina jin hakan ajikina amma abinda nake jiye mana shine yankewar guzuri ni kam Hankalina atashe yake saboda naga abincin daya rage acikin jakarka kadai. kodajin wannan batu sai hatyan yai murmushi yace ai indai muna cikin jeji ji nake kamar muna gidane agaban umma.da.abba kodajin haka sai idanun sadirat suka ciko da kwalla, hawaye ya subuto mata ta rungume hatyan kuma ta fashe da kuka tana mai cewa yanzu shikenan mun rasa abba da umma har abada. kuma ko kabarinsu bazamu sake ganiba? wata.kilama a.filin Allah akabar.gawarwak insu anan zasu bushe harsu dai daice sa'adda jarumi hatyan yaji wannan batun na yar uwarsa sadirat sai shima zuciyarsa ta karaya har hawaye ya.subuto masa ya dubeta yace gawar iyayenmu bazata tabeba domin na tabbatar da cewa sarkin mafarauta zai kwashesu yayi musu kabari kada ki manta cewar komai daren dadewa sai munkoma birnib bindal na dauki fansar ran iyayenmu lallai saina.kashe sarki shamsan agaban idanun yarima zainur kuma na haye kan karagar mulkinsa domin kawo karshen zaluncinsa. yanzu dai bari mu nemi inda zamu dan yada zango muci abinci mudan huta sannan muci gaba da tafiya. kodajin haka sai mamaki da tsoro ya kama.sadirat tace yanzu kana nufin kace adaren nan zamuci gaba da tafiy maimakon mu sami inda.zamu fake mu kwana? hatyan yace ai tsayuwar mu adaren nan har takai ta sa'a guda hatsarine agaremu saboda na tabbatar da cewa sarki ya turo dakarunsa subiyo bayanmu kokarina shine mufuta daga kasarnan gaba daya mu shiga wata kasar . daga chan ma ci gaba da tafiya harsai mun fice daga nahiyar nan gaba daya sannan zamu sami kwanciyar hankali .gama fadin haka keda wuya sai hatyan ya kama hannun sadrat ya jata suka kara gaba amma saitaga ya kan sunkuya kasa ya debi kasa ya shinshina kuma taga ya sauya hanya . al'amarinda yayi matukar bata mamaki kenan ta dubeshi tace waishin mene.ma'anar wannan abu da kakeyi? hatyan yace inayin haka ne domin na gano zamu samu rafi a kusa domin musa kuma muyi guzurinsa da yawa kiyi sani cewa ruwa yafi abinci mahimmanci arayuwar dan adam domin zamu iya kwananki bakwai babu abinci amma ba zamu iya jure kishirwa ta yini ukuba aikuwa kamar tsafi sai sadirat taga sun iso kusa dawata korama mai dauke da ruwa garaigarai . ruwan tafiya yake da gudu yana kwaranya kasan wani dutse . cikin farinciki suka ruga izuwa bakin koramar suka sa hannayensu suka kwarfo ruwan suka sha. daga nan sai htyan ya bude jakar guzurinsa yadauko abinci wanda bai wuce loma gomabaa suka ci tare suka sake kora ruwa gama hakan keda wuya saiya cika battocin su da ruwa ya mika mata ta rike yace yanzu zan goya ki abayana zanyi gudu dake na tsawon kwanaki ashirin. duk sa'adda kikaji kishurwa ko yunwa ki dauki abincin da yake cikin battarki kici kuma kisha ruwan battarki ki sani cewa a tsawon kwana ashirin ba zamu tsaya ba domin ki huta koda kuwa kin gaji da zama abayana lokacinda hatyan yazonan azancensa sai sadirat tayi mai kallon mahaukaci tace ni bantaba jin inda bil'adama ya yita jure guduba harna tsawon kwanaki ashirin ba baci basha ko kuwa kana nufin wani aljanin zamu hau? wai shin idan ma wata lalura ta kamanifa tafitsari ko kashi? kodajin wadannan tambayoyi guda biyu sai jarumi hatyan ya bushe da dariya yace aikuwa zan baki mamaki saboda ni tun ina da shekara goma aduniya duk sa'adda na shiga daji farauta sainayi kwana ashirin ina gudu baci sai shan ruwa. kuma wannan gudu da nakeyi tsere nake da wata sihirtacciyar bauna harsai na kure mata gudu na risketa mun fafata kazamin yaki akarshe saidai wuya tasa ta juya da gudu ta barni gudun kwana ashirin da nakeyi dadai yake da tafiyar kwana saba'in da tara akan doki wannan gudu nawa baiwa ce zallah ina nufin da ita aka haifeni kodajin wannan batu sai mamaki ya turnuke sadirat.kuma hankalinta ya sake kwanciya taji ta sake samun nutsuwa ta cewar wannan kani nata.zai iya kareta daga sharrin sarki shamsal batare da bata lokaciba kuwa sai hatyan ya rankwafa sadirat ta hau bayansa ya goyata sannan ya daureta tamau ajikinsa battar ruwansa kuwa na ruke ahannunsa na dama takobinsa kuwa na.sakale a cinyar sa tadamansa kawai sai ya falfala da azababben gudu izuwa cikin daji nanfa sadirat ta dinga ganin abu kamar wasa. domin saboda karfin gudun hatyan har tashi sama yake yana tsallake gajerun bishiyoyi da yan duwatsu da kwazazzabai . wani lokacin kuma sai taga kamar akan iskar cikin sararin samaniya suke tafiya saboda karfin gudun sau tari bata sanin sa'adda barci yke dauketa kuma.duk sa'adda da ta farka da taji kishirwa sai ta bude battarta ta kwankwada.ta koma barcinta . abu dai kamar wasa sai suka shafe kwana ashirin suna.tafiya. tuntana kirga kwanakin har lissafin ya kwace mata ta manta abinda yafi daure mata kai shine tunda aka fara wannan tafiya bata gajiba kuma bataji kashi ba ko fitsariba.tamkar bataci ta sha ba abinda kawai takeji shine yunwa da kishirwa kuma.da.zarar taji su din sai ta dauko abincinta da battar ruwanta wadanda suke jikinta kawai taci kuma tasha........ TARKON MUTUWA Abdul'aziz Sani Madakin Gini 2 B A ranar kwana na ashirin dinne suka hango kofar wani babban gari daga nesa awannan lokaci safiyace cikin farinciki hatyan ya tsaya da gudu ya kira sunan sadirat amma sai yaji shiru bata amsaba koda yadan waigo sai yaga ashe barci takeyi nan take ya kwanceta daga bayansa sannan ya shimfideta akasa. asannane yaji wata irin muguwar gajiyar gudun dayasha ta zo masa gamida matsananciyar yunwa don haka baisan sa'adda ya sulale kasa ba karar faduwar tasace tasa sadirat ta farka daga barcin da takeyi . tana bude ido taga hatyan akwance akasa jikinsa na kakkarwa tamkar mai cutar farfadiya cikin rudewa ta kamoshi ta dora kansa akan cinyarta ta yayyafa masa ruwa nantake yayi dogon ajiyar numfashi ya budi baki dakyar yace da ita ta bashi abinci cikin rawar jiki ta bude jakar guzurinsa ta fiddo abinci wanda bai wuce loma biyarba tarinka bashi abaki da hannunta abincin na karewa ta kora masa da ruwa asannanne hatyan ya dan dawo cikin hayyacinsa ya dubeta yace nagode da kika ceceni daga yunwar kwana saba'in da tara cikin tsananin mamaki ta dubeshi tace bangane yunwar kwana saba'in da tara baca, nake cewa kayi gudun kwana ashirin zamuyi? hatyan yace ai guduna na kwana ashirun daidai yake da tafiyar kwana saba'in da tara akan doki kinga kenan tafiyar da mukayi yanzu ta kusan wata ukuce wannan ne dalilin da yasa komai saurin dakarun da sarki shamsan zai turo su kamamu bazasu iya riskarmu ba yanzu dai ga wani babban gari nan agaban mu kuma dolene mu gaggauta shiga cikinsa domin haryanzu jikina rawa yakeyi saboda yunwa inason na sami abinci isashshe naci na koshi ammafa bazamu iya shiga cikin garinba kai tsaye dolene muyi yar dabara saboda tsaro gama fadin hakan keda wuya sai ya dafa kafadarta ya karanta wadansu dalasimai na tsafi faruwar hakan keda wuya sai nan take shi ya rikide ya zama tsoho rike da sanda ahannunsa ita kuma saita zama yarinya karama yar kimanin shekara goma kawai sai ya dubeta yace sunanki sahalu maza yimin jagora mushiga cikin garin nan muna bara batare da wata gardama ba kuwa sadirat ta kama sandar dake rike ahannunsa tajashi suka nufi kofar babban birnin kai tsaye bada wata fargaba ba da isowarsu bakin kofar birnin suka kamu da tsanani mamaki kuma tsoro ya shigesu amma sai suka basar suka ci gaba da bara don kar mutane su ganesu bakomai ne ya basu tsoro da mamaki ba face ganin taswirar fuskokinsu bisa takardu an lika ako ina a jikin bango baja baja kuma ajikin taswirar an rubuta cewa wadan nan manyan masu laifine na sarki shamsan don haka ana nemansu ruwa ajallo duk wanda yakamasu ko yafadi inda suke za'a bashi ladan dinare dubu dari ....gaskiya ni auwzab nasan inda suke zanfada abani rabona..... hatyan da sadirat na cikin karanta wannan bayani abakin kofar birinin sai shugaban dakarun dake tsaye awajen wani narkeken katone sai ya dubesu yace kai wannan almajiri su waye ku kuma taya akai kuka iso nan alhalin kai makahone shikuma dan jagoranka yaro ne dan karami? kodajin wannan tambaya sai hatyan ya rikirkice irin yadda tsofaffi keyi yace yaro harkasa hantar cikina ta kada saboda wannan tsawa taka mu bakine daga kasar misra kuma tare muke da wani ayari na fatake acikin jirgin ruwa jirgin namune yayi hadari a kusa da gabar wannan birni naku ya nutse akarkashin ruwa kadanne daga cikinmu suka ragu shine muka rarrabu acikin daji saboda firgita. dakyar muka gane hanya muka iso nan kodajin wannan batu sai wani can daga cikin dakarun yace hakika wannan makaho yayi gaskiya domin tun shekaran jiya ire iren wadannan fatake suka shigo garin nan suka bada labari irin wanda wannan ya bayar kodajin haka sai shugaban dakarun yasa aka budewa su hatyan kofa suka kunna kai ciki suka durfafi cikin gari kai tsaye ba tare da fargabar komaiba nan dai suka tambayi hanyar kasuwa aka nuna musu . kawai sai hatyan yace da sadirat ki nemi babban wuri inda ake sayarda abinci mai rai da lafiya ki kaimu Kodajin haka sai mamaki ya kamata tace yaya mu da bamu da kudi zakace muje wajen abinci mai tsada ? kodajin haka sai hatyan yayi murmushi yace waya gaya miki bamu da kudi? to ki sani cewa duk kudaden da sarkin mafarauta ya tara mini suna hannuna. ba wai abinci mai tsada ba hatta gidan kwana mai tsada zamu kama haya amma ba zamu wuce kwana ukuba agarinnan zamu kara gaba don kada asirin mu ya tonu ..ni auwzab zantonama kuwa ehe... kuma kinsan cewa so mukeyi mubar nahiyar gaba daya ba tare da sadirat tayi wata gardama ba. sai taci gaba da jan hatyan sukaci gaba da tafiya acikin kasuwar har suka iso wani babban gidan abinci kai tsaye suka kunna kai ciki suna shiga suka iske jama'a azazzaune sunacin abinci ai kuwa sai jama'a suka zuba musu idanu gaba daya. abu na farko dai kowa yana mamakin abinda ya kawo almajiri irin wannan gidan abinci mai tsada haka idan har yana da kudin siyan abincin da manyan mutane suke siya to lallai yana da makudan kudade ajikinsa hatyan ya yiwa gaba daya mutanen dake dakin siyan abincin kallo daya amatsayin shi makahone sai yaga cewa daka dakarun birnin acikin batar da kama sai wadansu jarumai masu kirar karfi kuma mafi yawansu suna rike da takardun taswirarsa data sadirat. acan gefe daya kuma sai yaga wani boka azaune akan tebur shi kadai tunda suka shigo gidan bokan ya kurawa hatyan idanu ko kiftawa bayayi nantake hatyan yasa jinin jikinsa yasan cewa wannan boka ya gane koshi waye kawai sai hatyan yayiwa sadirat rada akunne yace muje kan wancan teburin da babu kowa mu zauna kuma duk bala'in da zai faru anan karki kuskura ki tashi daga inda kike kodajin wannan batu sai hankalin saidirat ya tashi don tasan cewa dolene ayi fitina acikin wanan dakin abinci. nan sadirat ta ja hatyan takaishi izuwa teburin da babu kowa akai suka zauna har a sannan kallonsu akeyi da mamaki zamansu keda wuya sai wata ma'aikaciyar gidan abincin doguwar mace mai dan kyau wacce shekarunta bazasu haura talatinba tazo garesu tadubi sadirat tace dan samari me za'a kawo muku? farat daya sai hatyan ya tari nunfashin sadirat yace ni katuwar kaza zaki kawo mini gami da shin kafa da ruwan inibi kodajin haka sai matar ta bushe da dariya tace haba shiyasa jikinka yake da kyau baba fatar jikinkama bata da alamar tsufa dolene ka zamo lafiyayyayen namiji mai kwari zan iya aurenka inda kana sona kodajin haka sai sadirat ta murtuke fuskata dubi matar tace nidai ki kyalemin babana kije ki kawo mana abinci kawai kuma nima irin nasa zaki kawo min matar tai murmushi tace babu laifi idan da yayi halin ubansa ai barewa batayi guduba danta yayi rarrafe koda gama fadin hakan sai matar taje ta kawo musu abinci a farantai biyu ta ajiye agabansu nanfa suka kama cin abincin hannu baka hannu kwarya saboda rabonsu da cin abinci mai dadin haka tunkafin su baro birnin bindal. koda jama'a suka ga yanayin cin abincin su hatyan sai suk bushe da dariya saboda azatonsu kauyawane don basu saba cin abinci maidadin haka ba. wannan boka fuskarsa amurtuke bai yin dariya kuma bai dauke kansa daga kansu hatyan ba har suka kammala cin abincin. bayan sun kammala cin abincin har sun wanke hannunsu sun karasa shan ruwan inibin sai hatyan ya sanya hannunsa acikin jakar guzurinsa ya dauko zinare sannan ya ware iya kudin abincinsu ya bayar ashe daga cikin jaruman da suke zaune agefe daya kimanin su ashirin barayine kuma suna lura da jakar guzurin da ke hannunsu hatyan kawai sai daya daga cikinsu yazo wajen su hatyan ya zare wuka ya dora awuyan hatyan ya daka masa tsawa yace kai tsohon banza maza ka bani jakar guzurinka ko kuma yanzunnan na shaftarema makogwaro tuni awannan lokaci jikin sadirat yafara karkarwa saboda tsoro shikuma hatyan yayi kamar yatsoratan ya yunkura kamar zaisa hannunsa ya cire jakar amma sai yayi wuf ya kwaci hannun barawon ai kuwa sai barawon ya kwalla uban ihu ya saki wukar dake hannunsa ta fadi kasa saboda ji yayi kamar hannunsa zai karye kawai riko yaji irinna sadaukai koda ganin haka sai yan uwan barawon suka mike zumbir suka zare makamansu suka afkawa hatyan. kafin su riskeshi tuni sandar hanunsa ta rikida ta zama takobi nanfa suka rugumtsume da azababben yaki aka fara kakkarya teburan abinci jama'a suka far kama gudu da ihu kafin kace wani abu saura wannan boka da dakarun birnin kawai atsaye gefe daya suna kallon gumurzun da akeyi sai kuma wannan mace wacce ta kawowa su hatyan abinci atsaye gefe daya tana ihu da fada wai an lalata mata dukiya ashe gidanabincin nata ne cikin abinda bai wuce dakika dari da shirinba hatyan ya kakkarya wadannan barayi kimani su ashirin ya zubar dasu kasa sunata koke koke takobinsa kawai kare hare harensu ya keyi da ita amma bata sha jikin ko dayabada tsagwaron karfin damtse ya gama dasu shikansa wanna boka da dakarun birini da mai gidan abincin sunyu matukar mamakin karfin hatyan itakuwa sadirat tunda aka fara fadan saita dunkule akan kujerar da take zaune ta hade kanta da cinyoyinta.bata dagoba saida taji gidan yayi tsit batajin komai sai koke

Chapter 2 of 11