Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 11
shamsal yayi dariya sannan yace kwantar da hankalinka bazan bawa yarima rikon karagata ba saboda nasan shashashane ba abinda zai iya sai yiwa mata wayo da hikima wacce zai iya zartarwa,ka duba ka gani tun baifi shekara tara ba nake bashi horon yaki gashi ya gajeni a sadaukantaka. amma gashi akaron banza yaro dan shekara ashirin da daya kachal ya sare masa hannu sa'adda suka fafata Zainur bai dace da ya gajeni ba. duk da cewar ina matukar kaunarsa amatsayinsa na dana guda daya jal aduniya zan bar rukon karagata a hannun waziri, nayi imani cewa idan har kaine zakayi mini jagora acikin wannan tafiya da zamuyi to tabbas acikin kwanaki kadan zamu gano inda wadannan yara suke mu riskesu. sa'adda sarki shamsal yazo nan a zancensa sai boka daizun yayi ajiyar zuciya yace hanya dayace zamubi mu gano inda wadannan yara suke acikin kankanin lokaci. hanyar kuwa itace dolene mu nemo sarkin mafarauta a duk inda yake, idan muka hada karfi da karfe ni dakai zamu iya kamashi a hannunmu yayi mana jagora izuwa inda wadannan yara suke a cikin kwanaki kadan. to amma shima fa ya bace mana bat bamu san inda yakeba yanzu. bisa binciken da nayi yana nan a cikin daya daga cikin da zuzzukan dake wajen wannan birni namu ya buya kuma ya saddakar da cewa zai karasa sauran rayuwarsa tunda bashi da kowa aduniya sai tsafinsa da kuma dukiyar daya tara amma babu "da "bare jika kuma babu dangi. sa'adda boka daizun yazo nan azancensa sai sarki shamsal ya kamu da tsananin farinciki ya bushe da dariya . yayita kyakyatawa kamar bazai daina ba. daga chan kuma sai ya tsuke bakinsa ya turbune fuskarsa kamar an aiko masa da sakon mutuwa ya dubi boka daizun yace ai mai nema yana tare da samu, maza kaje ka kammala shirinka adaren yau zamu bar garin nan mu tafi farautar sarkin mafarauta a cikin dazuzzukan kasarnan. ba zamu daina farautarsa ba harsai mun ganshi mu idda nufinmu akansa. ba tare da wata gardama boka daizun ya rissina yace angama ya shugabana nantake boka daizun ya tafi izuwa gidanshi shikuwa sarki shansal sai ya tura aka kirawo yarima zainur tare da dukkan yan majalisarsa yasanar dasu hukuncin daya yanke na tafiya farautar sarkin mafarauta tare dasu hatyan. sannan kuma ya sanar dasu cewa yabar rikon karagarsa ahannun waziri. kodajin wannan batu sai hankalin yarima zainur ya dugunzuma ainun kuma yaji ransa ya baci bisa jin cewa bashi aka barwa rikon karagar mulikba. shin hakan yana nufin sarki bazai bashi gadon sarauta ba kenan? menene dalilin da zai sa ya hanashi alhalin shine kadai dansa aduniya ? wata zuciyar sai tace dashi ai saboda ka zama muskini ne mai hannu daya abin kunya ne ace magajin wanan karaga musaki ne aikuwa idan sarki yayi mini haka saina shuka masa bakin cikin dazai tafi dashi can kabarinsa. kamar yadda sarki shamsal ya shirya haka al'amarin da ya kasance. wato acikin wannan dare boka daizun ya kammala dukkan shirye shiryensa yazo gareshi ya tarar dashi ya gama dukkan shirinsa tuni har anbada rikon karagar mulkinsa. nantake sarki shamsal yaja matarsa gefe daya wato mahaifiyar yarima zainur inda babu wanda zayaji abinda zasu tattauna ya dubeta cikin nutsuwa yace yake matata kiyi sani cewa danki baiji dadin hukuncin dana yankeba na karanta hakan acikin idanunsa. to abinda nake so dake shine kiyi kokarin nusar dashi dalilin yi hakan agareshi kuma ki tausasa zuciyarsa don kada yayi yunkurin cin amanata ko yin wani abu na ba dai dai ba,kinfi kowa sanin halina. ni cinnaka ne bansan na gidaba idan har ya shiga gonata bazan daga masa kafaba duk da tsananin son da nake masa zan iya rasa dana na sami wani amma idan na rasa karagata ko mutuncina da darajata na rasasu kenan har abada. ni ba ragoba ne kuma ban gaji ragonta ba. kakana da ubana har suka bar duniya ba'a taba zubar da digon jininsu ba daga jikinsu ba afilin yaki haka nima don haka banga dalilin da zaisa na haifi ragon da zai kasa kare wannan martabarba. ko me zai sami yarima a rayuwa ragwancinsa ne ya janyo masa. da wannan furuci nake miki bankwana sai na dawo. koda gama fadin hakan sai sarki shamsal ya rungume matarsa suka kankame juna har zuwa tsawon yan dakiku daga can sa ya janye jikinsa daga jikin nata ya sumbaci goshinta. awannan lokaci yarima zainur yana tsaye yana kallonsu. maimakon sarki shamsal yaje inda yarima zainur yake ya runguneshi su yi bankwana dashi sai kawai ya daga masa hannu kuma ya juya masa baya ya tafi izuwa inda dokinsa yake ya kama ya hau. ba tare da wani bata lokaciba suka kama hanya shida boka daizun suka fice daga cikin gidan sarautar aka bisu da kallo kawai har suka bace da gani adaidai wannan lokacine hawaye ya subutowa yarima zainur ya tabbatar da cewa lallai son da sarki yake masa ya disashe. tun daga ranar da yarima zainur aka sare masa hannu sarki yaja da baya dashi yadaina so da kauna da kulawa kamar yadda ya saba nuna masa. sai da su sarki shamsal suka shiga cikin dazuzzuka guda dari da ashirin da daya suna neman inda sarkin mafarauta yake basu ganshiba. awannan lokacine sukaji sun sare suka fitar da rai ga samun ganinsa gaba daya. adaren kwana ashirin da dayan suka shigo dajin karshe wanda indai basu ganshi acikinsa ba to babu inda zasu ganshi sun san cewa ya fice daga cikin yankin kasar gaba daya. Awannan lokaci sun gaji likis kuma gashi dare ya soma rabawa don haka sai suka kafa tanti domin su yada zango. bayan sun gama kafa tantin sai suka fahimci cewa ruwan shansu ya kare don haka sai boka daizun ya dubi sarki shamsal yace ya shugabana ruwan shan mu ya kare don haka zan tafi nema ko zanga rafi akusa. dajin haka sai sarki shamsal yayi murmushi yace ai wannan ba laifi bane. nan take boka daizun ya dauki battocin ruwansu guda biyu ya nausa gabas boka daizun na cikin tafiya sai ya hango alamun wuta a nesa dashi.koda ganin haka sai boka daizun ya fara tafiyar sanda yana kuma karanta wadansu dalasiman tsafi acikin ransa. TARKON MUTUWA Abdul'aziz sani Madakin Gini Littafi na Uku Part B Nantake ya bace bat aka daina ganinsa kuma sai gashi yana tafiya a sama bisa iska maimakon a kasa bisa turba yadda za'a rinka jin takun sawayensa. Nanfa ya durfafi inda ya hangi hasken wuta sannu a hankali ya dinga kusantar wajen sai yaga ashe wata yar karamar bukkace awajen kuma agaban bukkar aka kunna wuta ana gasa wata barewa amma babu kowa awajen. Har boka daizun ya iso daf da barewar wacce ta gasu sosai har tana digar da mai baiga kowaba. nantake boka daizun ya hadiyi yawu bisa ganin wannan gasashshen nama domin tunda suka fito shida sarki shamsal a tsawon kwanaki ashirin da dayan ko sau daya basu ci nama ba. abincin guzurinsu kawai suke ci basuyi farauta ba ko sau daya ba. har boka daizur yakai hannunsa zai yanki wannan nama yaci sai kawai yaji an daka masa tsawa. a firgice ya waigo bayansa domin yaga wanda yayi masa wannan tsawa. take kuwa yayi arba dashi. bakowa bane ba face sarkin mafarauta. nantake aka fara kallon kallo.boka daizur yaji kamar ya bude bakinsa ya kwallawa sarki shansal kira amma sai yaki. tsawon 'yan dakiku suna yiwa juna kallon kar ta san kar sannan sarkin mafarauta ya bushe da dariya lrin ta mugunta yace sannunku da isowa dajin hajarul ausad yau kwanana bakwai acikinsa ina jiraku. anan ne za'a yita ta kare atsakanina daku. ko dai na hallakaku ko kuma ku hallakani. domin nasani cewa baku fito domin ku hallakaniba. sai domin ku kamani da hannunku ku tilasta mini nayi muku jagora izuwa inda su hatyan suke. kai yanzu a tunaninka hakan agareni abune mai sauki? nasani cewa idan kuka hada karfi da karfe kai da sarki zaku sami nasara akaina . amma taya kake zaton cewa zan baku wannan dama? ai tuni na dauki dukkan matakai na hana faruwar hakan. kafin sarkin mafarauta ya gama rufe bakinsa sai boka dazun ya shamma ceshi yayi nuni da hannunsa zuwa kansa. nantake wata irin gagarumar iska mai karfin gaske ta suri sarkin mafarauta tayi sama dashi ta rinka yin katantanwa dashi asararin samaniya. nan danan yaji yana neman fita daga hayyacinsa. ai kuwa shima sai yayi nuni da hannunsa izuwa kan boka daizun. take shima irin wannan iska ta sureshi tayi sama dashi ta dinga katantanwa dashi. sai gashi duk su biyun sun fita daga hayyacinsu. babu shiri kowanne ya janye hannayensa suka fado kasa tim a amtukar galabaice suna numfashi sama sama kamar ransu zai fita. maimakon su hakura sai sukaci gaba da yakar juna suka rinka watsawa kansu mugayen abubuwa kamar macizai,kunamai,da sauran kwari masu mugun dafi suka rinka cizonsu da harbinsu. nan da nan ko ina ajikinsu ya rinka kumbura suka dinga faduwa kasa suna ihu da birgima suna zubar da jini daga cikin bakinsu. duk wanda ya gansu cikinsu wannan hali dole ne ya ce duk mutuwa zasuyi. kawai kuma sai suka rinka tashi sama tamkar tsuntsaye masu fukafukai suka rinka yiwa junansu karo da ka afuska. sannan suka rinka naushin junansu .nan da nan suka sake galabaita ainun. jini ya dinga zuba daga sassan jikisu suna cikin wannan haline boka daizun ya kyallara ido yaga wata shudiyar laya mai dunkulallen dutse a wuyan sarkin mafarauta. shikuwa sai ya rike hannunsa da kyau sukaci gaba da dukan junansu ahaka. awannan lokaci suna shawagine asaman wani tsauni wanda kasansa ramine mai zurfin gaske kuma can karshen ramin ramin kogine wanda ruwansa ke gudu da karfin gaske . kwatsam ba zato ba tsammani sai sarkin mafarauta yaga sarki shamsal yayi tsalle ya taso sama izuwa kansa tamkar daga cikin baka aka cilloshi. kafin sarkin mafarauta yayi wani yunkuri tuni sarki shamsal ya gabza masa wani wawan naushi afuska damar da boka daizun ya samu kenan ya cizge wannan shudiyar layar daga wuyansa. nan take sarkin mafarauta ya sallamo kasa izuwa kasan wannan rami mai zurfi. saboda zurfin ramin su kansu su sarki sai da suka leko kasa amma basu iya ganin sarkin mafarauta ba. cikin tsananin farinciki boka daizun ya daga wannan sama ya kura mata idanu. nantake sai ga hoton su hatyan a cikin jirgin ruwa akan teku. koda ganin wannan hoto sai shima sarki shamsal ya kamu da tsananin farin ciki ya dubi boka daizur yace yanzu daga nan zuwa inda su hatyan suke tafiyar kwanan nawa ce? boka daizur yayi ajiyar zuciya yace idan akan doki zamu tafi tafiyar kwana goma sha tara ce. kuma kafin mu riskesu tuni jirgin ruwan ya isa birin istanbul. kaga kenan ba zamu riskesuba acikin tekun idan kuwa suka isa birnin istanbul acikin kwanaki uku kachal zasu fita daga wannan nahiya gaba daya idan kuwa suka fita shikenan dukkan shirin mu ya rushe. koda boka daizur yazo nan azanncensa sai sarkki shamsal ya firgice yace. yanzu mene abinyi yakai abin dogarona? boka daizur yayi shiru yana tunani har izuwa tsawon 'yan dakikku. daga can kuma sai yace zan iya kirkirar tsuntsun dazai daukemu yakai mu har bakin wannan teku a cikin kwana daya da yini daya. muna zuwa saimu dauki hayar karamin jirgi mai gudun gaske wanda zamu iya riskar jirginsu hatyan kafin su isa birnin iistanbul. kodajin wannan batu sai farinciki ya turnuke sarkmi shamsal yace maza kayi wannan tsuntsun tsafi mu tafi yanzu ba tare da bata wani lokaciba. kodajin haka sai boka daizun ya zauuna akan tsaunin dirshan ya debo wadansu 'ya'yan wuri guda hudu daga cikin aljihunsa yazube kasa gabansa. kawai sai ya zaro wuka acikin kubenta a kugunsa ya yanki tafin hannunsa. ya rinka diga jininsa akan 'yayan wurin yana karanta wadansu dalasimai na tsafi. cikin kankanin lokaci saiga wata irin gagarumar iska ta rinka kewaye 'ya'yan wurin wacce ta addabi sarki shamsal da boka daizur din da kansa tamkar zata suresu tayi sama dashu. jim kadan sai wadannan 'ya'yan wuri suka rikiide suka zama wani jibgegen tsuntsu wanda yafi girman jimina biyu. batare da bata wani lokaciba sai sarki shamsal da boka daizur sukayi sauri suka hau kan tsuntsun ya tashi dasu sama ya luluka sama acikin gajimare yana falfala azababben gudu Ashe alokacin da wannan ta taso sai wannan koriyar sarka ta sarkin mafarauta ta sulalo kasa daga aljihun boka daizul ta gangara kasan wannan tsauni ta fada cikin kogin ba tareda boka daizur ya ankaraba. sai da su boka daizur suka shafe tafiyar yini guda akan wannan tsuntsun suntafi sannan ya tuno da batun wannan sarka nantake ya fara laluben aljihunsa. koda ganin haka sai sarki shamsal ya dube shi cikin damuwa yace waishin mene kake nema? maimakon boka daizur ya bashi amsar wannan tambaya sai ya dauko madubin tsafinsa ya shafeshi da hannunsa na hagu. take duk abindaya faru ga sarkar ya bayyana akan madubin koda sukaga cewa sarkar ta fada kasan wannan tsauni sai suka takarkare suka rusa uban ihu atare cikin tsananin bakin ciki tamkar suyi kuka saboda sunsan cewa indai suna tare da wannan sarka to duk inda su hatyan suke sai sun samo su sarkar ce kadai zata iya bayyana wannan surrin yanzu dogaronsu daya ne. wato dolene suyi iya yinsu su riski su hatyan a cikin wannan teku. kamar yadda boka daizur ya fada haka al'amarin ya kasance wato acikin kwana daya da yini daya wannan tsuntsun tsafi ya sauko ya ajiye su abakin wannan teku inda tashar jirgin ruwa take . da zuwansu sai suka siyi wani karamin jirgin mai gudun tsiya suka shiga ciki su biyu kachal. boka daizur ne ya dinga sarrafa jirgin da sihirinsa ya rinka kara gudunsa suka dinga ratsa cikin teku tamkar sararin samaniya suke ratsawa tafiyar sa'a uku kachal sukayi suka hango jirgin su hatyan nantake farinciki ya baibayesu kawai sai sarki shamsal ya dauko takobinsa ya fara wasata saboda yasan cewa dolene tasha jinin babban makiyinsa nan da cikar dan lokaci. a chan cikin jirgin su hatyan lokacin da dakaru da ma'aikatan jirgin suka hango wani jirgin ya durfafesu yana wani mahaukacin gudu na ban al'ajabi wanda basu saba gani ba sai hankalinsu ya dugunzuma ainun sukayi zaton ko jirgin yan fashine don haka suka zare makamansu. suka zauna cikin shirin kota kwana. dudufniyar dakarun jirgin data ma'ikatance tasa suka farga suka san cewa lallai akwai wani bakon al'amari da yake shirin faruwa cikin hanzari hatyan ya fiddo wani dan karamin madubin tsafinsa da baifi girman tafin hannunsa ba ya shafeshi nan take yaga jirgin daya biyo nasun kuma yaga wadanda suke cikin jirgin wato su sarki shamsal da boka hatyan koda ganinsu sai hatyan ya mayar da madubinsa cikin aljihu sannan ya dubi sadirat yce duk abinda zai faru karki fito daga cikin wannan dakin harsai na umarceki yana gama fadin haka sai ya zare takobinsa kuma ya dauki garkuwarsa. koda ganin haka sai hankalin sadirat ya dugunzuma tace duk yadda akayi sarki shamsal ne ya riske mu har nan domin baka daukar garkuwa idan zakayi yaki da wadansu dakaru ko jaruman da basu amsa sunansuba dajin haka sai hatyan yace tabbas kin canka daidai amma abinda nakeso dake shine ki kwantar da hankalinki nayi miki alkawarin babu abinda zai sami daya daga cikin mu kawai ki bani rabin sa'a kachal zanje na hana su karasowa nan din ma ki sani cewa muna shiga birnin askandariya kuma da zarar mun shiga chan din shikenan mun tsallake duk wani taarkon sarki shamsal koda gama fadin hakan sai jarumi hatyan ya juya ya fice daga cikin dakin ya tafi izuwa saman jirgin rike da takobinsa tsirara adai dai wannan lokacine wata kurciya rike da wata takarda ajikin kafarta ta dira acikin jirgin dirarta keda wuya sa wani badakare yazo ya kama kurciyar ya cire mata takardar dake jikinta ya warware ya karantata afili kamar haka nine sarki shamsal tareda bokana daizur na tunkaroku sbd masu laifin da nake nema suna cikin wannan jirgi kada ku bari su fita gani nan isowa yanzun nan koda gama karanta wannan wasika sai barden ya juyo ya dubi hatyan wanda suffarsa ke Kama da ta bafatake dan shekara arb'in da wani abu ya kura masa idanu yace wanene kai? kodajin wannan tambaya sai hatyan yace wannan wacce irin tambayace ta rainin hankali? duk wanda ka gani acikin jirginnan ai bafatakene kuma birnin askandariya zasu don aiwatar da kasuwanci dajin wannan batu sai badakaren ya dakawa hatyan tsawa yace karya kakeyi tunda kuka shigo jirginnan kai da dan uwanka naji ban yarda dakuba don haka kune masu laifin dasarki shamsal yake nema. TARKON MUTUWA Abdul'aziz Sani Madakin Gini Typing: Prince Auwal Auzab Post: Sunusi SAS Littafi na uku 3 Part 3 C . To kasani cewa kun kawo kanku gurin da ake nemanku domin gaba dayan mutanen da suke cikin jirgir nan 'yan leken asirin sarki shamsal ne babu ta inda zaku iya guduwa gama fadin hakan keda wuya sai barden da ma'aikatan jirgin da dakarun suka bushe da dariya ba zato ba tsammani sai sukaga shima hatyan ya bushe da dariya awannan lokaci jirgin su sarki shamsal ya kusanto wannan jirgin da su hatyan suke dan tazarar dake tsakaninsu bata wuce kamu arba'in ba. koda ganin haka sai hatyan ya dubi matukin jirgin nasu suna hada idanu sai matukin jirgin ya dauke kan jirgin ya durfafi wani katon tsauni dake cikin tekun kodaganin haka sai hankalin kowa ya dugunzuma kafin dayansu yayi wani yunkuri tuni sunyi karo da tsaunin take jirgin ya tarwatse ya nutse akasan ruwan koda sarki shamsal da boka daizur sukaga abin daya faru ga jirgin su hatyan sai hankalinsu ya dugunzuma. daizur yace ya shegen yaron nan yayi tsiyar . amfani yayi da karfin sihirin tsafinsa ya haddasa wannan hadarin jirgin muyi sauri mu karasa muyi nutso izuwa kasan ruwan mu lalubo inda suke tun kafin su sami damar tserewa nan da nan kuwa jirgin su sarki shamsal ya iso bakin wannan tsauni da isowarsu sai sarki shamsal ya kwabe kayan jikinsa ya daka tsalle ya fada cikin tekun ya kama lalube acikin tekun ya kama dube dube akasan ruwan ba abinda ya gani face gawar tsirarun dakarun jirgin da ma'aikatansa suna ta ninkaya sunata kokarin ceton rayukansu da nufin su isa kan tsaunin amma sauran gaba dayan 'yan uwansu sun zama gawa kuma ba komai face sassan jikin jirgin da soke jikinsu alokacin dayayi wannan hadarin ya tarwatse. sarki shamsal yaci gaba da dube dube har cikin rugurgujajjen jirgin sai da ya duba ko'ina baiga hatyanba da 'yar uwarsa sadirat ba cikin kaduwa da mamaki sarki shamsal ya taso izuwa saman tekun ya nufi inda jirginsa yake kawai sai ya hango boka daizur kwance asaman jirgin kamar gawa ga jini na yoyo a hancinsa da bakinsa. cikin tsananin kaduwa da fushi sarki shamsal ya takarkare ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa kawai sai ya kwalawa hatyna kira yana cewa kai karamin alhaki matsoraci Ka fito fili idan ka isa na sani cewa kana nan kusa babu ta inda zaka iya gujemini tunda muna cikin tsakiyar teku wannan tsauni ne kai dai mafaka sai kuma jirgina guda daya gashi. kafin sarki shamsal ya gama rufe bakinsa sai ya hango jarumi hatyan tare da 'yar uwarsa sun mike tsaye akan tsaunin wanda yakasance dan karami atsakiyar tekun. awannan lokaci jarumi hatyan ya cire rigarsa. kirar jikinsa ta sadaukai duk ta bayyana kwanjinsa ya kumbura kuma duk jijiyoyin jikinsa sun tashi sunyi burdin burdin. fuskarsa sai gyatsine takeyi saboda fishi yana rike da takobinsa tsirara koda ganin haka sai sarki shamsal ya bushe da dariyar farinciki saboda yasan cewa komai yazo karshe . tuni ya cire rigarsa kawai sai shima ya daka tsalle daga cikin jirgin sa ya dira akan tsaunin ya zamana cewa tazarar da take tsakaninsa da hatyna bata wuce taku biyarba idan mutum yaga sarki shamsal da jarumi hatyan awannan lokaci yaga banbancin girman jikinsu da kirar jikinsu dolene ya tausayawa hatyan domin kamar a ajiye dan tsakone a gaban shirwa sarki shamsal ya ninka hatyan sau uku a komai. nanfa aka fara kallon kallo tsakanin sarki shamsal da jarumi hatyan alokacin dajikin sadirat ya fara karkarwa saboda tsananin tsoro kuma ta fashe da kuka . hatyan ya daka mata tsawa yace na gaya miki babu abinda zai samemu ki tuna cewa wannan azzalumin sarkin makiyinmu ne kuma azzalumi ne shi bai dubi zaluncin da dansa yayi mana ba na kashe iyayenmu sai don kawai na sarewa dansa hannu shine yakeson hallakamu. to ka sani ba yau zan mutuba saina rayu na girma na zama babban mutum asannan ne zan dawo birnin bindal na kasheka agaban danka yarima zainur domin daukar fansar ran iyayenmu wannan alkawarine na daukarwa kaina kuma saina cikashi. sa'adda jarumi hatyan yazo nan a zancensa sai sarki shamsal ya bushe da dariyar mugunta lokaci guda kuma ya murtuke fuskarsa yace banyi farautarka ba don abinda kayiwa dana sai domin na tsare mutuncina da karagata bokaye sun tabbatarmini da cewa idan har na bari kakai shekara talatin da biyar aduniya to tabbas zakazo har cikin gidana ka cini da yaki ko ayanzu bisa irin abubuwan da kayi na dabara,basira da hikima na gamsu cewa nan gaba zaka iya yimini juyin milki nayi mamakin yadda ka sammaci gaba dayan mutanen cikin jirginnan kasa jirgin yayi hatsari suka mutu dai dai kune suka rayu da kyar bayan sun galabaita nayi mamakin yadda akayi.ka shammaci boka daizur ka sumar dashi har naga jini yana zuba daga bakinsa da hancinsa waishin naushinsa kayi ko kuwa bayansa ka sudado ka buga masa makami? sa'adda jarumi hatyan yaji wadannan tambayoyi sai yayi murmushi yace ai duk wadannan abubuwan danayi suna daga cikin sirrin gumurzu da makiya bazan iya sanar dakai yadda nayi musu ba don kada kayi mini satar hikima. kada ka isheni da surutan banza muyi abinda zamuyi amma nayi maka alkawarin bazaka iya kasheniba anan kuma nima bazan iya kasheka ba sai wancan lokaci da nayi alkawari. gama fadin hakan keda wuya sai jarumi hatyan ya daka tsalle daga inda yake a tsaye tamkar an harboshi daga cikin kibiya ya kawowa sarki shamsal wawan sara a kafada da nufin ya cire masa hannu cikin baki zafin nama sarki shamsal ya sunkuya takobin ta sari iska kafin hatyan ya juyo da baya asaman tuni sarki shamsal ya damki makoshin hatyan ya shakeshi. sai gashi kafafun hatyan na wutsul wutsul asama. idanunsa kuwa suka juye bai san sa'adda ya saki takobinsaba ta fadi kasa. koda hatyan yaji ya fara jiyo kamshin mutuwa sai tattaro karfinsa gaba daya ya gabzawa sarki shamsal wawan naushi afuska take sarki shamsal ya saki wuyan hatyan ya fado Kasa amatukar galabaice yana tari gami da tofar da jinin wuya. shikuwa sarki shamsal saida ya yi baya taga taga saboda karfin naushin a lokacin da yaga wasu taurarun wuya akan idanunsa Asannan ne yaji danshi akan hancinsa koda sarki shamsal ya shafo hancinsa yaga jini saiya fusata ainun irin fusatar dabai taba yiba arayuwarsa ya kwarara uban ihu wanda ya firgita duk wata halittun dake kan wannan tsauni har da wadandama suke cikin wannan teku saboda wannan ne karon farko da wani jarumi ya samu nasarar fitar da jini daga jikinsa duk da cewar ya halacci yakoki da dama gami da gasar jarumtaka ba adadi ba tareda sarki shamsal a zare takobi ba saiya ruga izuwa kan hatyan ya sake damkar wuyansa ya shakeshi a tsaye ya rinka gabza masa naushi a fuska tun hatyan na kokarin kare kansa harya kasa nandanan fuskar hatyan ta kumbura tayi suntum, idanuwansa ma sukayi luhu luhu hakika duk wanda ya fika karfi sai dai kayi masa Allah ya isa duk da jarumtakar hatyan gami da juriyarsa sai gashi ya zama kamar tsumma ahannun sarki shamsal domin ko daga hannunsa baya iyawa koda sadirat taga halinda hatyan ya shiga saita sunkuci wani dutse ta rugo da gudu izuwa kan sarki shamsal ta maka masa dutsen akai take dutsen ya fashe ba tare da yayi masa ko kwarzane ba kawai saiya maketa ta zube kasa sumammiya sannan yaci gaba da gabzawa hatyan naushi afuskarsa har saida ya sumar dashi sannan ya jefar dashi akasa hatyan ya baje akasa tamkar gawa domin babu abinda yake motsi ajikinsa kamar gawa. asannan ne sarki shamsal ya zare takobinsa yazo ya durkusa agaban hatyan ya kamo hannunsa na dama ya daga shi sama sannan ya daga takobinsa da nufin ya sare hannunsa kamar yadda yayiwa dansa yarima zainur kwatsam ba zato ba tsammani sai sarki shamsal yaji an doki kirjinsa da mugun karfi saboda karfin dukan saida sarki shamsal ya wuntsula baya sau uku akan tsubirin kafin ya watstsake ya juyo yaga wanda ya doki kirjin nasa tuni an dauke hatyan da 'yar uwarsa sadirat an jefasu cikin wannan jirgi nasu sarki shamsal abinda idanun sarki shamsal suka iya nuna masa kawai shine an jefar da boka daizur gabansa alokacin aka tuka jirgin akayi gaba dashi da gudu nan take sarki shamsal yayi amfani da karfin tsafinsa don ya dawo da jirgin amma sai tsafin yaki tasiri kafin shudewar 'yan dakiku masu yawa tuni jirgin ya bace acikin tekun koda ganin haka sai sarki shamsal ya sake kurma uban ihu a karo na biyu ya kamu da tsananin bakin ciki harsai da kwalla ta cika masa idanu adaidai wannan lokacine boka daizur ya farfado daga dogon suman da yayi afirgice ya mike zaune ya dubi gabas da yamma ,kudu da arewa yaga babu jirginsu babu abokan gaba. ADAI DAI NAN NE LITTAFI NA UKU YA KARE Like and Comments is our encouragement, idan bakuyi sai muga kamar bakuso shiyasa idan mun fara muke dai nawa, pls like and comments. TARKON MUTUAL Littafi na hudu Part 4 A . . Gaba daya su jarumi hatyan,ai shida sarki shamsal kadai akan wannan tsuburi sai shima ya kwarara uban ihu ya durkushe kasa yana cizar yatsansa harsai da yayiwa kansa rauni bai saniba saida jirgin su hatyan ya shafe sa'a daya da rabi yana tafiya sannan ya iso tashar jigin ruwa ta birnin askandariya tun kafin sannan ne sadirat ta farfado daga dogon suman da tayi sakamakon mangarin da sarki shamsal yayi mata tana bude idanunta ta tsinci kanta acikin jirgin ruwa , acikin daki ga dan uwanta jarumi hatyan kwance yanata faman tari ,har a sannan baidaina aman jiniba saboda bugun dukan da yasha akirjinsa da fuskarsa agefe daya kuma sai sadirat taga wata tasa dauke da ruwan dumi da kuma tsumma alamar cewa an gasa masa jikinsa hakan nema yasa kumburin jikinsa ya dan ragu koda sadirat taga hatyan yana yunkurin mikewa zaune sai tayi sauri ta maida shi kwance tace kada ka mike yakai dan'uwana domin kasha bakar wahala dolene kayi jinyar 'yan kwanaki kafin ka sami kuzari ajikinka kuma dolene kasha magunguna da zasu sa jinin fuskarka ya warware daga kumburin da na kirjinka. kodajin wannan batu sai jikin hatyan yayi sanyi ya gamsu cewa bazai iya yin komai ba amma saiya bude baki yace waishin wanene ya cece mu daga hannun sarki shamsal harya shigo damu cikin wannan jirgin? saidrat tace nikaina bansaniba amma bari na fita naga ko waye ke tuka jirgin akwai alamun cewa matukin jirginne kadai atare damu nan take sadirat ta mike tsaye ta fita waje ta tunkari mai tuka jirgin. bayan ganin matukin jirgin sai zuciyarta ta buga da karfi saboda tsananin mamaki . macece ke tuka jirgin ma'abociyar dogon gashi mai tsananin sheki da wal'wali ya sauka har kasan duga duginta. koda ta jiyo sautin tafiya abayanta saita waigo sukayi arba da juna ba wata bace face sarauniya badi'atul nauwara fuskarta cike da annuri gami da murmushi ta dubi sadirat tace yaya jikin dan uwanki? kodajin wannan tambaya sai sadirat ta rugo izuwa ga badi'atul nauwara ta rungumeta cikin matukar farin ciki tana mai cewa 'godiya mara adadi a gareki ya abar kauna. hakika badon keba da tuni mun dade da zama matattu ni da dan uwana,wai shin ke kuwa yaya akayi har kika zo kan wannan tsauni kika ceci rayuwarmu? sa'adda sarauniya ta ji wannan tambaya sai tayi murmushi tace shin kin mantane nace zan ci gaba da baku kariya har ku isa birnin askandariya ? ai tun sa'adda kuka baro birnina nake biye daku da nawa jirgin baku saniba saboda akwai tazara mai yawa a tsakaninmu ina cikin tafiya ne a jirgin naga wani shirgegen tsuntsu dauke da mutane biyu ya wuce ta saman jirgina take jikina ya bani cewa su sarki shamsal ne yake ke biye daku kuma so suke

Chapter 4 of 11