Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 11
koken kartin da hatyan ya karya . adai dai wannan lokacine wannan matar mai gidan abincin ta taho da sauri wajen hatyan tace ina kuma zaku tafi baku biyani kudin babbar barnar da kukayi min ba? kodajinhaka sai hatyan yayi murmushi yace nawa zamu biyaki? matar tayi masa wani murmushi irin na karuwanci tace tunda dai kaine ka biya dinare hamsin charaf sai sadirat tace haba yan wadannan tsofaffin kujerun da teburan da aka karya sune dinare hamsin sai matar ta rufe sadirat da fada tace shin bakya ganine anfasa min tambula da kofuna guda dari ko kece mannadinin hari sai an biyani dinare hamsin ko kuwa rijiya ta bayar guga ya hana dajin haka sai hatyan ya tari numfashinta yace kadaki danu ga dinare dari ma nan take ya debo dinare dari ya bata . ai kuwa sai matar ta daka tsalle ta sumbaci hatyan agoshi sannan tace idan kuna neman gurin kwana a unguwar daisul nake gida mai lamba goma kofata abude take agareka basai ka biya ba shidai hatyan baice da ita kalaba kawai sai ya dafa kafadar sadirat yace zo mu tafi nan take takobin dake hannunsa ta rikide ta koma sanda sadirat ta kama sandar suka nufi hanyar fita daga gidan abinci amma sai wannan boka da dakarun birni kimanin su saba'in suka sha gabansu Bokan ya dubi hatyan fuskarsa a murtuke yace kana zaton zaka iya yaudarar kowane da dan guntun sihirinka na tsafi? to nagane ku ko ku su waye kaine hatyan wannan yarinyar kuwa yar uwarka ce sadirat kune wadanda aka baza hotunanku ako ina cikin garinnan kuma sarki shamsal ne yake nemanku ruwa a jallo kuna zaton zan iya bari ladan dinare dubu dari ya wuceni?........ TARKON MUTUWA Abdulaziz Sani madakin Gini Typing:- prince auwal auzab Post:- AA Misau Littafi na biyu 2 Part 2C . Koda bokan yazo nan azancensa sai wannan mace mai gidan abinci ta zazzaro idanu cikin tsananin mamaki jikinta na kyarma ta kurawa hatyan idanu hatyan ya dubi bokan cikin murmushi na yarda ka gane ko mu su waye amma ina mai shawartarka daka cire hannunka daga cikin wannan lamari idan kuwa kaki to zakayi biyu babu ma'ana ka rasa ladanka sannan kuma ka rasa lafiyarka idan ka matsama ranka ma zaka rasa haba day~ kodajin wannan batu sai wannan bokan ya bushe da dariyar mugunta yace ai inda ba kasa nan ake gardamar kokawa fa ga fili ga mai doki sai akasa tseren muga abinda zai faru da jin haka sai hatyan ya tura sadirat ta koma bayansa sannan ya daga sandarsa sama take ta sake zama takobi ai kuwa shima bokan sai ya zare takobinsa ya dubi dakarun sarkin yace ku ku koma gefe daya ni zan kamasu a hannu mu tafi dashi gidan sarki ba tare da gardama ba dakarun suka koma gefe daya dasu da sadirat da mai gidan abincin suka zama yan kallo nan take su hatyan suka ruguntsume da azababben yaki mai tsananin ban tsoro da ban al'ajabi. sai da suka shafe kusan dakika tamanin suna kaiwa junansu sara da suka cikin zafin nama da juriya da bajinta ba tare da dayansu ya sami nasara akan dayaba koda hatyan yaga zai bata masa lokaci sai yaja da baya ya dubeshi cikin murmushi yace yakai wannan boka hakika na yarda ka iya yaki amma bari na gwada karfin damtse mu gani kafin bokan yace wani abu tuni hatyan yadako tsalle ya gabza masa wawan naushi a fuska saboda karfin naushin saida ya kife da ribda ciki alokacin dahar hakoransa guda sukayi fitar burgu daga bakinsa ya baje kasa sumamme koda ganin abin da faru ga bokan sai dakarun suka firgita suka ja da baya suka baiwa su hatyan hanya suka wuce ita kuwa wannan mata mai gidan abinci sai ta biyo hatyan da gudu ta sha gabansa tace amma fa ka cika gwarzon jarumi mai tarwatsa maza don Allah ka dawo izuwa aininhin siffarka mana naga kyakkyawar suffarka dajin haka sai hatyan yayi murmushi agareta yace kada kidamu zamu sake haduwa kawai sai ya juya ya dubi wandannan dakarun na garin idan kuka sanar da sarkinku kun gammu sai na kasheku dayanku bazai tsiraba ku fadawa bokan nan wannan sakon idan ya farfado daga suman da yayi yana gama fadin haka ya kama hannun sadirat yajata suka fice daga gidan abincin suka sake nausawa cikin gari suna tafiyar sauri sauri gudu gudu acan gidan abinci kuwa wannan boka bai farfadoba daga dogon suman da yayiba sai bayan rabin sa'a afirgice ya mike zaune ya kama kalle kalle kawai sai yaga an gyara wajen fes kamar ba'ayi yakiba agun. duk karyayyun kujerun da teburan an kwashesu an zuba wadansu sababbi ga kostomomi azaune suna cin abinci kowa na harkar gabansa dakarun da sarki ya hadashi dasu kuwa don aiwatar da wannan aiki babu ko mutum daya daga cikinsu koda ganin haka sai ya mike tsaye zumbur ya fara neman wannan mata mai gidan abinci kawai sai yaji an taba kafadarsa ta baya afirgice ya waiga sai yaga ashe wadda yake nemace cikin alamun tsananin damuwa da zumudi ya dubeta yace yake sardila ina wadannan yaran sukayi? sardila tayi dariya sannan tace ai kayi babban kuskure da bakayi amfani da karfin sihirinka ba tun farko boka azwan ya numfasa yace ai wannan yaron ba karamin takadiri bane nasan tsafinsa babbane. abin danake so dake shine zan zuba ido akan gidanki domin zai iya kawo miki ziyara tunda dai kin bashi adreshinki yanzu zan koma gidan sarauta na sanar da sarauniya halin da ake ciki domin ta karo mini yawan dakaru ai komai hatsabibancinsa sarkin yawa yafi sarkin karfi kada ki kuskura ki barshi ya sake guduwa idan har yasake dawowa koda gama fadin haka sai boka azman ya ruga waje ya kama dokinsa ya kwance ya haye kuma ya zubureshi da gudu izuwa gidan sarki , shidai wannan babban birni ana kiransa da suna madinatul sarkuf kuma yana karkashin mulkin wata sarauniya mai suna badi'atul nauwara badi'atul nauwara ta kasance kyakkyawar budurwa ta gaban kwatace kuma shekarunta ashirin da daya cif cif wato ita da jarumi hatyan sa'annin juna ne badi'atul nauwara shahararriyar mayakiyace kuma basadaukiya wadda tasha jarumantaka ne anono domin uwarta ce shugabar sadaukai ~ na kasar gaba daya mahaifinta kuwa wanda tagaji sarautar a hannunsa shine sarkin yakin birnin kafin ya zama sarki amma shi ma yau shekararsa shida da rasuwa. mahaifiyarta ta rasu sakamakon ciwon hanta da yaci karfinta badi'atul nauwara bata tsafi kuma baya tasiri akanta saboda tsananin jarumtakarta da iya yakinta da sanin tuggun yaki wanda mahaifinta ya koyar da ita shi yasa duk sarakunan dake kusa da ita suke shakkarta. jama'ar gari kuwa suna matukar kaunarta saboda yawan adalcinta aduniya babu abinda badi'atul nawwara ta tsana kamar zalunci taga adalci a tsakanin talakawa da masu mulki da attajirai ta kanyi amfani da kudin baitil mali ta siye kayan abinci a hannun manoman garin ta rage farashinsa ta siyarwa da talakawa don magance yunwa da talauci akasar wannan halayya ta sarauniya badi'atul nauwara tasa yan majalisarta da manyan attajiran kasar suka tsaneta kuma sun sha shirya hanyar da zasubi su kawar da ita daga kan mulkinta amma sun kasa bisa dole suka hakura suka barta akan karagarta lokacin da sakon sarki shamsal ya riski sarauniya badi'atul nauwara taga hoton jarumi hatyan dana yar uwarsa wadanda shekarunsu basu kai talatin ba sai bata dauki abinda wani mahimmanci ba saboda taji ajikinta cewar duk yadda akayi ba wai laifi sukayiba zaluncin sarki shamsal ne kawai ya fado kansu Abinda tayi kawai shine ta kirawo azman ta hadashi da dakaru ashirin kacall tace ta dora alhakin kamo hatyan a hannunsa. tayi hakan ne don kada ace batayi komai ba amma tasan cewa boka azman da wadannan dakaru basu isa su kamo wadannan masu laifiba tunda harma suka iya guduwa daga birnin shamsal. 'ya'yan sarakai dana attajirai da dama na wannan birini sun nemi auren sarauniya badi'atul nawwara amma sai taki yarda da dukkaninsu lokacin da fadawanta suka matsa mata akan ya kamata tayi aure domin ta kare martabarta da ta masarautarta sai ta dubesu tace duk wadanda suke sona da aure ba don Allah suke sona ba sai domin dukiya,mulkina,da kyawuna. da yawansu suna son su aureni ne saboda su sa; lusuranci da wannan gidan sarautar domin wata rana mulkin ya koma gidansu. bazan taba yin aureba koda zan tsufa na mutu akan karagata ba face na.sami masoyi wanda zai soni soyayyar gaskiya ba tareda da yasan koni wace ba kuma.saina.tabbatar da cewa.badon kyawuna.yake sona ba sannan kuma dolene yafini karfin damtse da jarumtaka ta hakane kadai nasan cewa zai iya kare.hakkina da mutuncina. sarauniya badi'atul nauwara na zaune acikin fadarta. fadawa da manyan mutanen gari ana.zaune ana yin fadanci saiga boka azman ya shigo cikin fadar aguje kuma adimauce da zuwansa gaban karagar sai ya zube akasa yana rawar murya da jiki yace . ya shugabata yau naga wadannan masu laifi wadanda sarki shamsal yake nema ruwa ajallo. kodajin wannan batu sai fadar ta rude da mamaki gami da kace na ce harsaida sarauniya badi'atul nauwara ta daga hannu sannan akayi tsit tamkar mutuwa tagifta badi.iatul nauwara ta ce a ina kagansu kuma yaya akayi baka kamosu ba? nantake boka azman ya kwashe labarin abinda ya faru agidan abincin sardila ya zaiyane kodajin wannan labari sai jama'a suka sake cika da mamaki akaci gaba da hayaniya . ita kuwa saruniya saitayi shiru tana tunani har tsawon .yan dakiku dagachan sai ta dago da kai ta dubi boka azman tace tabbas wannan mai laifi ba karamin jarumi bane zanso nayi arba dashi naga irin jarumtakar tasa a zahiri abinda nakeso dakai shine zan kara baka dakaru guda arba'in ku sake nemansu. tunda dai duk irin kamannin da mai laifi zai juye sai ka ganeshi zaku iya kamoshi. boka azman ya dubi sarauniya cikin alamun tsananin damuwa kamar zaiyi kuka yace ya shugabata dakaru sittin fa kenan kacal kika bani ai kamata yayi ki bani dakaru dubu dari domin hatsabibancin wannan mai laifin ya wuce yadda kike zato kodajin haka sai sarauniya tayi murmushi tace kai dai kawai kace ka tsorata dashi amma yaushe ace akan mutum daya jal zan baka dakaru dubu dari. kaje kayi aikinka kawai idan ka kasa ni zan yi da kaina. tana gama fadin hakan sai ta mike tsaye ta kirawo shugaban dakaru tace maza aje a bawa boka azman karin dakaru arba'in kuma a bashi kudin abincinsu dana wahalhalinsu. kaji aikin mai adalci wacce bata danne hakkin kowa shugaban dakarun ya russuna yace an gama ya shubata nantake shida boka azman suka fice daga fadar ita kuma sarauniya badi'atul nauwara ta shige izuwa cikin gidan sarautar nantake fadawanta ma suka watse . kowa ya kama gabansa. lokacin da sarauniya badi'atul nauwara ta shige can cikin kuryar turakarta ta sanya kayan barci sai ta zauna akan gefen gadonta alokacin da wata kuyangar ta kawo mata ruwan inibi a kofi ta karba ta dan kurba kadan sannan ta jiye kofin.akan tebur har ta yunkura zataje ta kwanta sai maganganun boka azman suka fado mata arai . nan take ta mike tsaye ta dauko taswirar fuskar jarumi hatyan da yar uwarsa sadirat ta kura musu idanu har izuwa tsawon dakiku take ta gane cewa ai wadannan matasa yan uwan junane dolene su kasance uwa daya uba daya sabodame sarki sarki shamsal yake neman wadannan yan uwan biyu a raye ko a mace ko a raye har ma ya sanya lada mai tsoka.haka ga duk wandaya kawosu? tabbas ina bukatar naji cikakken labarin wadannan yan uwa domin nasan hanyar da zanbi na taimakesu tunda dai suna cikin kasata a halin yanzu. idan har inason jin labarinsu kuwa dolene sai dai nayi bad da kama na tafi nemansu da kaina gama fadin hakan keda wuya sai sarauniya badi'atul nauwara ta baje akan gadonta domin tayi barci inyaso idan dare ya soma yi sai tayi bad kama ta shige cikin garin. al'amarin su jarumi hatyan kuwa lokacin dasuka sake karadawa cikin gari sai ya dafa sadirat akafada nantake suka sake rikidewa suka koma 'yan mata guda biyu kuma bakaken fata don kada wani wanda ya gansu a gidan abinci ya sake ganinsu a siffar almajirai da dan jagora ya shaidasu . nan dai suka ci gaba da tafiya ko waige basayi harsaida suka je karshen kasuwar sannan suka zauna sukayi kamar ciniki sukayi don bagarar da masu farautarsu . lokacin da sadirat taga sun shafe lokaci maitsawo zaune awajen saita dubi hatyancikin.alamun damuwa tace waishin zaman me muke tayine a nan wurin? baka tsoron a sake shaidamu azo da dakaru masu yawan gaske ayi mana shigar rago? kodajin wannaan tambaya sai hatyab yayi murmushi yace waishin sau nawa ina fada miki cewa indai kina tareda ni ki daina tsoron kowa? akwai dabarar da nake shiryawa wacce ita kadai zamubi mu tsira da rayuwarmu mu kwana hankali kwance inyaso da asubah .kafin gari yayi haske sai mu kara gaba........ AA Misau TARKON MUTUWA Abdul'aziz Sani Madakin Gini Part 2 C Haka dai hatyan yayita jan sadirat da hira har magaruba tayi adai dai wannnan lokacin ne sardila mai gidan abinci ta taso daga sana'arta ta gaban su hatyan ta wuce amma ko kallon su hatyan batayiba. sai da ta danyi nisa da tafiya sannan hatyan ya kama hannun sadirat suka mike tsaye suka kwashe kayansu da sauri suka bi bayanta cikin sanda da buya ba tareda tasan suna binta ba. sai da suka yi nisa da barin harabar kasuwa sannan aka iso wani wuri mai kama da daji sannan hatyan ya baiyana tsulum agaban sardila acikin ainihin siffarsa. tana ganinsa ta firgita ainun ta wangamebaki zata rusa ihu amma sai yayi wuf ya toshe mata baki da tafin hannunsa ya dora mata wuka akan.wuyanta yace idan kika yi mini ihu saina yanka ki. kiyi duk abindana umarceki idan kina son ki tsira da rayuwarki. gama fadin hakan keda wuya sai ya janye hannunsa daga kan bakinta alokacin ne tayi doguwar ajiyar zuciya ta dubeshi cikin alamun tsoro tace me kake so nayi ma? awannan lokacin ne sadirat ma ta fito daga cikin duhuwar da take boye ta tsaya abayan hatyan. hatyan ya dubi sardila yace so nake ki kaimu gidanki mu kwana amma ba wancan gidan da kika saba kwana ba . ki fadi ko nawa kike so mu biyaki. kodajin wannan batu sai hankalin sardila ya kwanta tayi murmushi tace shin zaku iya biyana dinare dubu daya. dajin haka sai sadirat tayi farat tace haba kwana dayan da zamuyi jal shine saimun biya dinare dubu to nawa ne kudin gidan gaba dayansa sardila tace karfa kimanta cewa masu laifine zan boye na basu mafaka. me kike zaton zai faru idan asirina ya tonu? duk abindana mallaka agarin nan sai sarauniya ta kwace kuma karshe aturani kurkuku duk da cewa kuwa sarauniyar mu mai adalci ce gama fadin hakan keda wuya kawai suka hango boka azwam tare da dakaru da gudu sun fito daga cikin kasuwar cikin hanzari duk su ukun suka fada cikin kodajn wannan batu sai hatyan ya kyalkyale da dariya yace kome kike takama dashi ni daidai da kene. ina shawartarki daki gagauta ficewa domin muma tafiya zamuyi mu bar muku birninku tunda kun matsa mana sarauniya ta sake bushewa da dariya a akaro na biyu tace ai bakin alkalami ya riga ya bushe . babu ta inda zaku iya fita daga garin nan batare da an kamakuba. nan da cikar rabin sa'a dakarun sarauniya kimanin dubu dari uku zasu zo suyiwa unguwar nan kawanya kunsan kuwa sarkin yawa yafi sarkin karfi kuma kasani cewa ko tsafi kuke takama dashi tofa baya tasiri acikin garin nan. saboda sarauniyar mu bata tsafi kuma baya tasiri akanta. tana gama fadin haka sai ta zare takobinta tana mai gyara tsayuwarta ta dubi hatyan tace . ka mika wuya ko na yi maka raunin da zaka mutu da tabonsa. koda sarauniya tazo nan ajawabinta sai shima hatyan ya zare takobinsa kuma ya gyara tsayuwarsa kamar yadda tayi yace "na rantse da kabarin iyayena idan ban sami nasara akanki ba kema baki isa ki sami nasara akaina ba " gama fadin hakan keda wuya sai duk su biyun suka ruga da gudu izuwa kan juna suka ruguntsume da azababben yaki mai matukar ban tsoro da ban al'ajabi wanda ya firgita sadirat ainun ta ruga izuwa karkashin wani katon tebur na karfe dake tsakar gidan ta dunkule jikinta tamkar bushiya amma saboda shegen naci nason ganin jarumtakar mutum biyun sai ta ci gaba da kallon gumurzun nasu sai da suka shafe kusan rabin sa,a suna kaiwa juna sara da suka cikin bakin zafin nama da bajinta ba tare da dayansu ya sami nasara ba, koda ganin haka sai suka sauya salon fadan suka hada da tsalle gami da kwance kwance da kuma kai naushi da bugu. da zarar hatyan ya sami nasarar naushin sarauniya a fuska ko a kirji kafin ya kaimata wani naushin sai kaga ta rama kamar yadda yayi mata nanfa suka hadawa junansu jini da majina tun suna yin fadan da karfin jikinsu da kuzarinsu sai daya zamana cewa dakyar suke iya daga hannayensu kai da gani kasan cewa karfinsune yazo daya suna cikin wannan haline sukaji ana kwankwasa kofar gidan da karfi dajin hakan sai sarauniya ta ja da baya ta daina fadan sannan ta daga muryarta da karfi tace ku dakata anan waje kada wanda ya shigo take su hatyan suka gane dakarun sarauniya ne sukazo kuma ga yadda suka jiyo dudufniyar su da alama suna da yawan gaske kawai sai sarauniya ta mike tsaye ta fuskanci jarumi hatyan ta cire mayafin data rufe fuskarta dashi koda su hatyan sukaga kyakkyawar fuskarta da jikinta sai suka rude sarauniya badi'atul nauwara tasa hannunta ta goge jinin dake jikin lebenta sannan ta dubi hatyan cikin murmushi tace nice sarauniya badi'atul nauwara mai mulkin wannan birni mai suna madinatul salkuf. yanzu haka dakaruna sun iso wannan unguwar sun zagayeta babu ta inda zakubi ku iya guduwa ku tsira amma zan kubutar daku saboda dalili daya. dalilin kuwa shine naji kayi rantsuwa da kabarin iyayenka hakan ya nuna mini cewa ku marayune kamar ni wato baku da iyaye . duk da cewa banji tarihin rayuwarkuba kuma bansan laifin da kukayi wa sarki shamsal ba. amma jikina ya bani cewa kuna da gaskiya zaluntarku kawai zai yi . zan baku dama ku gudu amma yakai wannan gwarzon jarumi kayi sani cewa ina binka bashin wannan fada. lallai sai mun sake haduwa domin mu fitar da raini na dade ina neman jarumin dayake da karfin damtse da iya yaki irin... auwzab... nawa ban samuba sai kai a yanzu dolene mu karasa yakinmu .domin mu banbance tsakanin aya da tsakuwa anan gaba idan muka sake haduwa anan gaba . ku zauna acikin gidannan ku kwana.kada ku fito sai asubah tayi. asubah nayi ku nufi yammacin garinnan.kuyi ta tafiya zaku iski tashar jirgin ruwa . ku hau jirgi ya ketare daku iyakar wannan kasa tawa zaku riski wani gari agaba. zan baku gudun mawoyin da zasu ceceku. koda ta gama fadin hakan sai ta juya ta fice daga cikin gidan. tana fita sai ta janyo kofar gidan ta rufe inda tayi arba da dakarunta tare da boka azwan yana jagorantar su. sun ruko saldirat a hannu sunyi cirko cirko. kawai sai sarauniya badi'atil nauwar ta dubi boka azwan tace ku saki saldira bata da hannu akan boye wadannan masu laifi domin basa cikin wannan gida . maza ku ruga gaba dayanku izuwa gabashin birnin nan. can sukayi da gudu bisa dawakai kada ku barsu su ketare iyakarmu. kodajin wannan batu sai boka azwan da gaba dayan dakarun suka ruga izuwa inda dawakansu suke suka hayesu suka zaburesu da gudu suna masu tunkarar gabashin birnin . tafiyar su keda wuya sai sarauniya ta dubi sardila tace shiga ki baiwa su hatyan kulawa mai kyau . asuba nayi ki tashesu daga barci subar garinnan. tana gama fadin haka sai ta juya tayi tafiyarta ta kutsa kai cikin unguwar tana mai rufe fuskarta tamkar bata kasance sarauniyaba. sardila ta fada cikin gidan da sauri ta rufo kofa. kamar yadda sarauniya ta tsara haka al'amarin ya kasance . asubah nayi sai sardila ta tashesu daga barci suka kimtsa sannan sukayi bankwana. nantake hatyan ya bude jakar guzurinsa. ya debo dinare dubu da biyu ya mikawa sardila yace. ga kudin hayar gidanki dana abincinki. dajin haka sai sardilat ta kasa karbar kudin kuma nantake idanunta suka ciko da kwallah har hawaye ya zubo mata tace yaya ina matsayin marainiya zan kasa taimakon marayu yan uwana? maraicine yasa na taso acikin irin wannan rayuwa da kuka ganni aciki tun ina yarinya shekara takwas aduniya na iya aikin wahala domin na tserar da mutuncina karuwanci sata da caca duk nayi agarin nan amma ban taba taimakon wani da darhami dayaba arayuwata. ahalin yanzu na mallaki gidaje da gonaki,shanu da tumaki barkatai, idan an lissafin masu arzikin garinnan dolene asani acikin su. duk abinda nayi muku na bar muku domin nabar tarishi arayuwata cewar nataba taimakon yan uwana marayu da wannan haramtacciyar dukiyar dana tara ku sani idan natuna wannan dukiya sai naji na tsani kaina kuma naji mutuwa kawai nake sonyi domin bata da amfani rayuwata. dan babu da uwa ko masouyin kwarai. koda sardilat tazo nan azancenta sai ta fashe da kuka al'amarin daya kara karyar da zuciyar hatyan da sadirat kenan suma sukaji suna matukar tausayinta don haka ba susan sa'adda suka rungumeta ba duk su biyun suka fashe da kuka aka rasa wanda zai rarrashi wani atsakaninsu saboda suma nasu maraicin suka tuno. sai da suka dan jima kankame da juna sannan suka janye jikinsu daga cikin nata nandai suka kwashe kayansu tayi musu rakiya har izuwa bayan gari inda suka hau dawakansu suka sukwanesu suka durfafi hanyar da sarauniya ta umarcesu subi. tun kafin su isa inda tashar jirgin ruwan take hatyan yayi tsafi suka sake rikidewa izuwa siffar fatake kuma mazaje yan kimanin shekaru arba'in da daya. da isarsu bakin gabar jirgin ruwan sai suka iske wani babban jirgi ya gama lodi wanda jama'ar dake cikinsa akalla sunkai dari shida da arba.in. shidai wannan jirgi hawa biyune ma'ana akwai dakaru akasansa da samansa. sai kuma can karshen saman inda mutum ke ganin ruwan tekun afili. mafi yawan jama'ar dake cikin wannan jirgi fatakene wadanda suka nufi birnin askandariya domin can ne inda jirgin ya nufa. indai mutum ya isa birnin askandariya tofa yana daf da fita daga nahiyar gaba daya. saida su hatyan suka ninka kudin shiga jirgi sannan suka sami damar shiga jirgin sannan suka sami damar shigar da dawakansu. aka kai dawakan inda aka tanada don dawakai nanma suka biya kudin shigar dasu. daga nan aka tafi dasu izuwa dakinsu suka shiga suka baje akan shimfida cikin farin ciki bisa ganin cewa suna daf da tsira da rayuwarsu daga sharrin sarki shamsal Anan muka kawo karshen littafi na biyu. 07067470752 TARKON MUTUWA Abdul'aziz Sani Madakin Gini TYPING: PRINCE AUWAL AUZAB POSTED: SUNUSI SAS FACEBOOK: www.Facebook.com/Sunusi.ahmadstk littafi na uku 3 PART A Kawai sai sadirat ta rungume hatyan cikin farinciki mara misaltuwa tace shikenan mun tsira daga sharrin abokan gabarmu yakai dan uwana yanzufa saura kiris mufice daga wannan nahiya gaba daya. kodajin wannan batu sai hatyan yayi doguwar ajiyar zuciya cikin alamun karayar zuciya yace akwai matsala yake yar uwata. kiyi sani cewa har acikin wannan jirgi da muke akwai yan leken asirin sarki shamsal da yawa. tun afarkon shigowarmu cikin jirgin nan na fahimci hakan. inba don mun chanja kamannin muba da farat daya zasu gane mu. duk da hakan sai munyi mugun taka tsantsan,gaskiya sarauniya badi'atul nauwra tabamu babbar gudun mawa wacce ba zamu taba mancewa da ita ba. inbadon ita ba da yanzu bamu iso nan ba. sardila ma ta taimakemu sosai ni ina mamakin irin wannan sa'a tamu ma har da muke haduwa da masoyan da suke taimakon mu alhalin basu sanmu ba muma bamu sansu ba ki sani cewa ko isasshen barci bamu isa mu dinga yi ba acikin wannan jirgi domin makiya zasu iya amfani da damar hakan su gane ko mu su waye su cutar damu. kada ki manta cewa a mace ko araye sarki shamsal yake son ganinmu. kodajin wannan batu sai hankalin sadirat ya dugunzuma tace to yanzu yadda bamuyi wani barcin kirkiba jiya da daddare yaya zamuyi yanzu? nifa kaina har ciwo yakeyi saboda jin barci. hatyan yace yanzu ke ki kwanta kiyi barci ni kuma zanyi gadinki idankika tashi daga barcin dan kanki sai nima na kwanta kiyi gadina ammafa da zarar kinji wani motsi komai kankantarsa ki tasheni daga barci saboda komai zai iya faruwa ako yaushe kuma kadaki yarda da kowa acikin jirgin nan koda kuwa ma'aikatan jirgin ne. dajin haka sai murna ta kama sadirat ta kwanta ta kama barci abinta tamkar ba'a cikin tashin hankali takeba. shikuwa jarumi hatayn sai ya dubi hoton zanen wani gunki dake jikin bangon dakin na wata sarauniya . nantake sai ya tuno da sarauniya badi'atul nauwar nanfa ya tuno da lokacin da suka fafata kazamin yaki da ita kawo izuwa lokacin data kwaye fuskarta suka yi arba da juna.sannan ya tuno da irin maganganun da ta yi masa da yarda akarshe ta taimakesu suka fice daga cikin birninta har suka iso wannan waje . koda jarumi hatyan yazo nan atunaninsa sai yaji akaron farko yaji son ya sake ganin wani mutum wanda suka taba haduwa kuma suka rabu. ma'ana babu abinda yakeso a.rayuwarsa sama da sake saduwa da sarauniya badi'atul nauwara. to wai shin menene dalilin da yasa naji ina son na sake ganinta? amsar da hatyan ya kasa baiwa kansa kenan. ashe ita ma sarauniya badi'atul nauwara ta tsinci kanta itama cikin irin wannan hali wanda hatayn ya tsinci kansa acikinsa wannan dare lokacin data koma gidan sarautarta ta shiga cikin turakarta ta kwanta akan gado bayan ta sanya rigar barcin ya gagareta domin nantake ta shiga tuna duk abubuwan da suka faru tsakaninta da jarumi hatyan. abin daya fara burgeta a tare dashi shine tsananin jarumtakarsa da juriyarsa ta yaki gumurzu wacce ta zamo iri daya da tasa abu na biyu shine da yakara burgeta shine alokacin data bayyana fuskarta da jikinta a gareshi bataga yayi irin dimaucewar da maza suke yi ba idan suka ganta. kuma bataga yayimata kallo ba wanda yake nuna yana sonta ba. kawai dai yayi mata kallon mamaki bisa ganin kyawun da Allah ya bata. anya kuwa hatyan bashi bane irin namijin da na dade ina nemaba . wanda nake ganin cewa shine yafi dacewa da ya zama abokin rayuwata. to ai kuma hatyan ba sa'a na bane akalla na girmeshi da tazarar shekaru takwas zuwa tara. koda yake ai babu ruwan so da girma,kudi ko matsayi idan har hatyan shine irin masoyin da nake nema to tabbas zanyi masa ragowar jarrabobin da zan tabbatar da hakan da zarar mun sake saduwa. haka dai sarauniya badi'atul nauwara taci gaba da yin wannan tunani har barci ya saceta bata sani ba. Acan birnin bindal kuwa lokacin da sarki shamsal yaga gaba daya dakarun guda dubu dari hudu wadanda aka tura farautar su jarumi hatyan izuwa kowanne bangare na kasar sun dawo babu wata nasara sai ransa ya baci kuma hankalinsa ya dugumzuma ainun yarasa abinda ke masa dadi aduniya . nantake sarki shamsal ya tura aka kirawo masa boka daizur ya dubeshi yace yakai abin dogaron bindal kayi sani cewa abari ya huce shi yake kawo rabon wani. duk da cewa mun baza dakarun mu da yan leken asirin mu izuwa dukkan kasashen dake wannan nahiya kuma mun baza hotunan wadannan yara ako'ina. zuciyata na yawan bugawa da karfi akan wannan al'amari inaji a jikina cewar wannan yaro zai iya tsallake dukkan tarkokin mu. bazan iya ci gaba da zaman ranar da za' akawo min labarin cewa an kamasuba a wata kasa . kasani cewa idan har ya sami nasarar fita daga wannan nahiya tamu abune mawuyaci mu iya kamashi kuma komai daren dadewa sai ya dawo kasar nan cikin gagarumin shiri domin daukar fansa gami da karbar karagata. abinda nake so dakai shine kaje kayi shiri kazo mu tafi farautar wannan yaro a yau dinan ba zamu dawo gidaba face mun riskeshi mun tsinke masa kai. asannan ne zan sami nutsuwa da kawanciyar hankali lokacin da sarki shamsal yazo nan a zancensa sai hankalin boka daizur ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe ya sunkuyar da kansa kas yayi shiru yana tunani har zuwa tsawon yan dakiku daga chan. saiya dago da kansa ya dubi sarki shamsal cikin alamun damuwa yace ya shugabana tashin hankalina dai guda dayane. yanzu idan zaka tafi wa zaka barwa jiran karagarka? kodajin wannan tambaya sai sarki

Chapter 3 of 11