Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
11 / 11
jarumi hatyan da 'yar uwarsa sadirat suna cikin kewar mahaifansu kuma suna son su ziyarci kabarin iyayensu sannan sunason su sake ganawa da sarkin mafarauta koda sarki yazo nan azancensa sai farinciki ya lullube badi'atul nauwara tace yakai wannan sarki mai daraja kayi sani cewa nayi alkawarin zanyi duk wannan abu da ka umarceni dayi kuma kaima ina mai godiya agareka ubangiji ya saka maka da alheri nantake sarki dasu nasmal dasu hatyan suka dunguma gaba daya suka koma cikin gidan sarautar jama'ar gari kuwa sai suka rude da shewa gamida farinciki garin ta dauka gaba daya anata kade kade da wake wake na murnar zuwan sabon addini dakuma samun kwanciyar hankali na kashe uwar macizai duk inda mutum ya zaga agarin babu abinda zaiji mutane na tattaunawa face batun jarumtakar badi'atul nauwara da kuma sabon addinin musulunci amasauki na musamman aka sauki badi'atul nauwara kuma jarumi hatyan da sadirat ne debe mata kewa suka ci abincin dare tare suna cikin cin abincin ne hira ta barke a tsakanin su badi'atul ta dubi sadirat cikin murmushi tace yake kawata an bani labarin gasar da akayi yau tsakanin yarima nasmal gashi babu wanda ya sami nasara to yanzu a tsakanin yarima nasmal da boka aimar wa zaki zaba amatsayin mijinki? kodajin wannan tambayar sai kunya ta kama sadirat tace to ai irin wannan matsalar ce akan dan uwana hatyan shikansa ya kasa gane macen daya dace ya zaba amatsayin matar aure atsakanin gimbiyoyi guda biyu idan har zai iya fitarda zabinsa yanzu anan gabanmu nima zan iya fitarda nawa zabin.... SAI JAHANGO, TO ALLAH YARU'EN. TARKON MUTUWA LITTAFI NA TARA Part 9 C . Kodajin wannan tambaya sai kunya ta kama sadirat to irin matsalar ce akan dan uwana hatyan shi kansa ya kasa gane macen daya dace ya zama amatsayin matar aure tsakanin gimbiyoyin nasa guda biyu idan har zai iya fitar da zabinsa yanzu anan gaban mu kodajin wannan batu sai badi'atul nauwara ta murtuke fuskarta ta sauya maganar da cewa yanzu yaushe ya kamata muyi shiri mubar garin nan don komawa tamu nahiyar ? kodajin wannan batu sai hatyan yayi murmushi yace ai yanzu tunda mun zama ma'a bota addinin musulunci bamuda wani shiri saina ubangijin musulunci saboda haka zaifi kyau mu tsaya mu dan sami ilimi na addinin daga cikin littattafan tarihin da suke cikin birnin nan don mu koyi yadda ake ibada zamufi jin dadin fara wannan babban aiki dake gabanmu mu jaddada addinin anahiyarmu kafin sannan ma kan uwar mazizai ya bushe zamu daukeshi babu nauyin komai muji dadin tafiya tare dashi kodajin wannan shawara sai murna ta kama sadirat da badi'atul nauwara saboda sanin cewa yazo da shawara mafi kyau da alheri wɑɳɳɑɳ รɦiɳɛ ɑɓiɳ ɗɑyɑ Բɑʀu ɑɓiʀɳiɳ รu yɑʀiɱɑ ɳɑรɱɑʆ ɓɑyɑɳ รɑʀɑuɳiyɑ ɓɑɗi'ɑtuʆ ɳɑuwɑʀɑ t ɓɑyyɑɳɑ tรuʆuɱ tɑ kɑรɦɛ uwɑʀ ɱɑcizɑi Acan birnin sarauniya anisa kuwa bayan ta sauko case daga kan tsuntsun tsafi ta taimakawa jama'ar ta dayawa wajen ceton rayuwarsu daga annobar ambaliyar ruwa da rugujewar gidaje saidata tara gaba dayan yan majalisarta d bokayenta afadarta alokacin da komai ya lafa ta dubesu tace yaku jama'ata dukkaninku kunga masifar data samemu kuma ba komai ne ya haddasa hakan ba face bayyanar uwar macizai kuma ba kowane ya tasheta ba face sarki shamsal saboda kawai ya kashe mutum biyu rak acikin wannan duniya bisa binciken da nayi yanzu na gano cewa sama da mutum miliyan dubu uku ne suka rasa rayuwakansu a sassan duniya, dukiya kuwa bata da adadi wacce ta salwanta atarihin duniya ba'a taba samun mugun tarkon mutuwa irin wannan, lallai sarki shamsal ya cika mara imani da tausayi kuma babu mai son zuciya kamarsu to yanzu dai gashi komai ya lafa alokaci guda shin uwar macizai ta kashe mutane biyun da akeso ta kashe ne ko kuwa itace ta mutu? amsar dana kasa samu kenan domin nayi iya bincike na naga hakan amma madubin tsafin yaki nuna mini komai al'amarin daya firgita ni ainun domin ban taba haduwa da matsalar dana kasa gano mafitarta ba amadubin tsafina ba sai wannan karon bisa wannan daliline na taraku anan inason gaba daya bokayenmu ababan dogaron birnin mu kuma dirkokin wannan birnin su hada karfi da karfi yanzu su binciko mana abindake faruwa domin musan matakin da zamu dauka babban dalilina akan hakan shine yanzu fa sarki shamsal ya tsaga jini abinda nake nufi shine tunda her ya sami nasarar kashe hatyan da 'yar uwarsa da uwar macizai tofa nan gaba zai iya tunanin amfani da uwar macizai wajen murkushe dukkanin manyan sarakunan duniya domin ya kasance shine yake mulkin duniya duka yanzu na umarceku yaku manyan bokayenmu daku hanzarta yin wannan aiki domin na zartar da hukunci koda sarauniya anisa tazo nan azancenta say gaba dayan bokayen da fadawanta sukayi tsuru tsuru suka kama kallon junansu kawai aka race wanda zaice kala al'amarin daya fusata sarauniya anisa kenan bata san sa'adda ta daka musu tsawa ba tace shin kurame ne ku bakuji abinda na fadaba ne kokuwa kunason kuci amanar kasarku ne? dajin wannan batu sai babban boka na birnin wanda ake kira da suna muzaid bin amfasi yayi gyaran murya ya bude baki cikin rawar murya tamkar wanda aka cika bakinsa da laka yace ya shugabata al'amarin nan babbane ,idan aka tono cikinsa zamu iya rasa addininmu d muka gada tun iyaye da kakanmi zaifi kyau mu bar wannan magana kawai muci gaba da zuba idanu muga abin da kaddara zata kawo kodajin wannan batu sai anisa ta zabura cikin tsananin fushi ta zare takobinta lokacin da jikinta ya kama kyarma ta dakawa boka muzaid tsawa ya firgita ainun her hantar cikinsa ta kada sannan ta dubeshi tace kai muzaid na rantse da darajar iyaye na akan kishin kasata da addinin da muka gada ina yi make kashedi na karshe kafin takibina tasha jinin jikinku gaba dayanku nan ka hanzarta sanar sani abinda ke faruwa kodajin wannan batu sai gaba daya bokayen da 'yan majalisarta suka furgice dama dukkaninsu sun tsufa babu dan kasa da shekaru saba'in kuma sun san cewa bazasu iya sarrafa sarauniya anisa ba da karfin damtse kona sihiri can sai wani tsoho mafi tsoro acikinsu wanda baya son mutuw yayi caraf yace ya shugabata kiyi mana rai ni zan gaya miki gaskiya al'amarin daya faru tun dazu muka zauna muka gama binkice muka gano cewa an kashe uwar macizai kuma ba wanine ya kasheta ba face kawarki sarauniya badi'atul nauwara itama ba karfinta bane sa'ace da karfin......... ...... caraf sai boka muzaid ya shammaci mai maganar ya gabza masa naushi awuya take mai maganar ya zube kasa sumamme boka muzaid ya dubi sarauniya anisa afusace yace ba zamu gaya miki wannan sirriba saboda bamaso ki rushe mana addininmu don haka mun zabi mu bayar da jininmu don kare addininmu maza ki hanzarta kashemu ke muke jira .kodajin wannan batu sai sarauniya anisa ta kyalkyale da dariya lokaci guda kuma ta murtuke fuskarta tace ai kuma yanzu na gane abinda ya faru sarauniya badi'atul nauwara ta sami nasarar kashe uwar macizai ne da karfin ubangijin musulunci saboda me kuna ganin gaskiya karara amma zaku taketa ? kodajin wannan batu sai gabe dayan bokayen da fadawanta suka sakeyin tsuru tsuru alamomin rashin gaskiya suka bayyana karara akan fuskokinsu koda ganin haka sai sarauniya anisa tayi murmushi tace kuyi sani cewa tun ina yarinya karama 'yar shekara tara naga wani littafi acikin gidan tarihin kasarnan wanda aka boye shi a inda babu wanda zai iya daukoshi amma saboda hatsabibanci na sai dana daukoshi na karance shi tsaf asirrance na mayar dashi ba tareda wani ya gani ba babu komai acikin wannan littafi face tarihin ma'abota addinin musulunci da kuma ma'abotansa kalmomin da akayi amfani dasu acikin wannan addini kunne bai tabajin kamarsu ba kuma mutum ko aljan bashida basira ko hikimar da zai iya shirya wannan zance zance ne irin wanda da zarar kunne yajisu sai dukkanin tsigar jiki ta tashi take zuciya take karbarsa ya mamaye tsoka, kashi da jini saboda zance ne na gaskiya wanda babu karya acikinsa tun asannan ne jikina ya baini cewa lallai wannan addini shine addinin gaskiya sauran addinai kuwa mutane ne suka kirkireshi saboda son zuciya da son duniya kuyi sani cewa zabi biyu gareku kacal kodai ku karbi wannan addini ku tsira da rayuwarku data 'ya'yanku kuma ku tsira da kasarku ko kuma ku rasa komai da kowa domin idan rana ta fito hannu baya kareta lokacin da bayyanar hasken gaskiya yazo dolene duhun karya ya yaye shawara ta rage ga mai shiga rijiya ni yanzu zan tafi neman kawata sarauniya badi'atul nauwara aduk inda take domin na karbi wannan addini na gaskiya ahannunta kodai ku karbi addinin ko kuma na dawo na share ku na kafa addinin gaskiya abayan babu ku kafin daya daga cikin bokayen yace wani abu tuni sarauniya anisa tayi girgiza ta bace bat daga cikin dakin taron tamkar bata taba wanzuwa ba al'amarin daya firgita bokayen da fadawan kenan suka shiga duba madubin tsafi domin suga inda take amma sai abu ya gagara al'amarin daya kara firgitasu kenan hankalinsu ya dugunzuma ainun suka rasa abindake musu dadi aduniya al'amarin sarki shamsal kuwa lokacin nan da kasa ta kama girgiza dashi sa'adda ya dafe akan wannan babbar gada da take birnjnsa koda gadar ta karye ta rikito dashi kasa izuwa cikin ramin dake karkashinta mai mugun zurfi sai ya kurma uban ihu ya dimauce yamanta da batun ya ceci kansa ta hanyar amfani da karfin sihirin tsafi bisa rashin sa'a kuwa saiya fado akan wani karfen gadar namtake karfen ya gutsire masa kafarsa guda ta hagu ya baje awajen sumamme scan cikin birnin bindal kuwa bayan komai ya lafa anyi asarar dukiya mai yawan gaske sai yarima zainur yayi shiri tareda dukkan dakarunsa suka fito izuwa wajen garin don ganin barnar da annobar ta haddasa musu saboda sunji karar karyewar wannan babbar gadar koda suka iso wajen sukaga yadda gadar ta rabe gida biyu sai suka cika da tsananin mamaki suka rugo izuwa bakin ramin suna lekowa sai suka hango sarki shamsal akwance akasan gadar asume ga kafarsa guda ayanke tana zubar da jini mai yawan gaske koda ganinsa acikin wannan hali sai yarima zainur ya tarkare ya bushe da mahaukaciyar dariya al'amarin daya matukar baiwa dakarunsa mamaki kenan amma da yake sunsan cewa bashida imani kamar uban masa sai suka basar zainur ya dubi mutum hide daga cikin dakarunsa yana mai daka musu tsawa ya basu umarnin suyi sauri su sauka kasan ramin su dauko sarki shamsal nantake kuwa aka zarga igiyoyi suka sauka can kasan ramin suka dauko sarki shamsal assume aka koma cikin birnin bindal har aka ajiye sarki shamsal akan gado bai farfadoba daga dogon suman da yayi sai bayan sa'o'i uku sun shude koda sarki shamsal ya bude idanunsa ya tsinci kansa akan gadonsa kuma acikin turakarsa saiya kamu da tsananin mamaki kawai saiya yunkura da nufin ya mike tsaye amma sai yaji ya kasa sakamakon bashi da kafa guda nantake zufa ta karyo masa jikinsa ya kama karkarwa cikin tsananin tsoro ya kama mayafin da aka lullube jikinsa dashi ya janye shi kawai saiyaga bashi da kafa ya tabbata ya zama musaki koda tabbatar da hakan saiya takarkare yakwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa tamkar zaki uban dawa yayi ruri faruwar hakan keda wuya saiga yarima zainur ya shigo cikin turakar shi kadai fuskarsa cike da annuri yana yiwa sarki shamsal murmushin mugunta koda zainur yazo daf da sarki shamsal yadda tazararsu bata wuce taku ukuba sannan ya tsaya suka dubi juna kawai sai zainur ya bushe da dariyar mugunta lokaci guda kuma ya turbune fuskarsa yace duniya rawar 'yan mata na gaba ya koma baya yakai abbanaka tuna cewa lokacin da hatyan ya sare mini hannu guda na zama musaki saika tsaneni kuma ka kyamaceni yau gashi kaima ka zama musaki ka rasa kafarka guda kaga kenan bani da wani laifi idan na tsaneka agaban idanunka yanzu zanci karena babu babbaka zanyi duk abinda na so baka da ikon hanani kamar yadda kake yimini abaya cikin tsananin fushi sarki shamsal ya dakawa yarima zainur tsawa yace idan har kaga ka cigaba da mulkin nan to bana numfashi aduniya zainur ya sake bushewa da dariya akaro na biyu sannan yace to ai yanzu gaka kana numfashi saika hanani na gani motsa mana kai ba sadauki bane? kodajin haka sai sarki shamsal ya yunkura domin ya duro kasa daga kan gadon saiyaga ashe an daure dukkanin hannayensa biyu da wata irin murtukekiyar sarka ta bakin karfe itama daya kafar tasa lafiyayyar an daureta ajikin manyan dirkokin dakin aka daura sarkokin koda ganin haka sai sarki shamsal ya fusata ainun ya takarkare ya hada karfinsa waje daya ya fara janyo sarkokin yana ruri da kururuwa wohoho! mai karfi sai allah ya isa nanfa yarima zainur ya fara ganin abin al'ajabi tamkar sihiri domin nantake sarki shamsal ya fara jijjigo dirkokin ginin suka fara karyewa ginin dakin ya fara karyewa ginin dakin ya fara rushewa adimauce yarima zainur ya ruga waje da gudu yana mai kwalawa dakarunsa kira yana fitowa wajen dakin yaga wata masifar wacce tafi wacce ya baro kuma ba komai yarima zainur ya ganiba face barkewar yaki acikin gidan sarautar da farko ruwan kibiyoyi ya gani suna zubar da dakarunsa sannan ya jiyo sautin haduwar takubba acan kofar fada kuma yaga wasu dakarun afirgice suna debo makaman yaki suna rugawa wajen fadar cikin tsananin dimauta ya tambayi daya daga cikin dakarunsa abinda ke faruwa afirgice badakaren yace dashi ai jarumi hatyan ne ya shigo birnin tareda wasu dakarun bakaken fata suna daf da isowa nan gidan sarautar kodajin wannan batu sai yarima zainur ya fusata ainun ta zare takubba guda biyu ajikinsa ya nufi kofar fadar aikuwa tun daga nesa ya hango hatyan, nasmal, badi'atul nauwara da boka aimar sunayin mummunan barna domin duk inda suka da gaba saidai kaga maza na zubewa kasa kamar ana sassabe agona zainur ya dubi gabas da yamma kudu da arewa yaga ko'ina gawarawakin dakarunsa ne kwance dukkanin dakarunsa wadanda yake takama dasu sun zama gawa nantake hankalinsa ya dugunzuma ya firgita kawai saiya juya da sauri da nufin ya ruga inda bargar dakawai take kawai sai jarumi hatyan ya dako tsalle daga inda yake tamkar daga cikin baka aka harbashi ya dira agaban zainur ya ritsashi da takobinsa wacce ta rine da jini ya dubeshi yace ''yakai abokin gaba yau babu damar gudu domin yau ranace ta daukar fansa kwatsam sai suka hango sarki shamsal ya durfafosu yana dingisa kafarsa guda daya janye da dirkokin gini guda uku ruke da sarkoki kowa awajen saudi yayi mamakin irin wannan tsananin karfin damtse irin na sarki shamsal domin awajen kaf babu sadaukin da zai iya janyo wadannan dirkokin masu mugun nauyi haka kuma gashi bashida kafa guda koda ganinsa sai jarumi hatyan ya dubeshi cikin murmushi yace yau ga da ga kuma uba sannan ga makiyansu lokacin daukar fansa yayi kamar yadda nayi alkawari na na daukar fansa ran iyayena agaban idanunka yanzu zan kashe mahaifinka agaban idanunka caraf sai sarki shamsal ya busheda mahaukaciyar dariya sannan ya hade fuskarsa ya dubi hatyan yace yakai wannan yaro aiko giwa ta fadi kasa tafi karfin a dasa mata wawa idan gaba dayan dakarun dake nan wajen zaku taru akaina ni kadai bazakubiya kasheni ba da karfin damtsenku kona iya yakinku lallai saina hallaka ku gaba dayanku duk da cewa na rasa kafata guda daya sannan na juyo izuwa kan dana da makarrabansa wadanda sukaci amanata nayi musu hukunci daidai da laifinsu kafin wani awajen yace wani abu sai sarki shamsal ya tsinki sarkokin dake hannunsa daga jikin dirkokin da karfin tsiya sannan ya suri takubba guda akasa ya dako tsalle a sama ya kawowa hatyan mugayen sara guda biyu cikin bakin zafin nama hhatyan ya kare saran da takobinsa da garkuwarsa amma saboda karfin saran saida ya fadi kasa aikuwa yana kasan y dinga kawo masa munanan sara da suka ya kuntatashi yana neman hallakshi k0da ganin abindaya faru sai badi'atul nauwara, nasmal da aimar suka rugo da gudu suka kawo masa dauki sauran dakarun su hatyan kuwa da 'yan tsirarun dakarun zainur saisuka zuba ido suka zama 'yan kallo shima yarima zainur din saiya ruga izuwa bayan wani ya labe yana kallon abindake faruwa nantake aka ruguntsume da azababben yaki tsakanin sarki shamsal da da jarumai hudu amma sai gashi shikadai ya zame musu alakakai sun rasa yadda zasuyi dashi dukda cewa kafa daya ce dashi amma yana iya juyawa ko'ina ya tare sara da suka sama da kasa gefe da gefe kuma ta maida martani kuma ya rinka hadaw da naushi da bugu saigashi kafin dakika ashirin dakkanin jaruman hudu ya hada musu jini da majina kawai sai yayi wata katantanwa atsakiyarsu ya tarwatsasu kuma ya sami nasarar yankar kowannensu suka fadi can gefe daya suna masu dafe raunikan da yayi musu alokacin da jini ke zuba wohoho dole ne ace da mijin iya baba duk wanda yaga irin wannan gagarumar jarumtaka da sarki shamsal ya yayi awannan lokacin dolene yayi masa jinjina cikin hanzari duksu hudun suka mike tsaye zumbur suka yunkura zasu sake afkawa sarki sshamsal sai jarumi hatyan ya dakatar dasu ya dubesu yace wannan fadan ba naku bane ku barni dashi da izinin ubangiji sai na sami nasara akansa kodajin wannan batu sai jikinsu badi'atul nauwara yayi sanyi suka ja da baya shikuwa hatyan sai ya fuskanci sarki shamsal acikin zuciyarsa yana mai cewa ya ubangijin musulunci idan harka yarda da imanin da nayi dakai to ka bani sa'a da nasara akan wannan tsohon azzalumi kamar sarki shamsal ya san abin dake cikin zuciyar hatyan saiya dubeshi ya bushe da dariyar mugunta yace ka daina kamun kafa da wani sabon addini naka kayi zaton cewa zaka iya samun nasara akaina zaifi kyau ka farka daga wannan mataccen mafarki ni zaki ne uban dawa kuma ni dodon jarumaine da sadaukai sallamata ma mutuwa ce hatyan yayi murmushi yace daga yau gudu ya kare nayi gudu kamar raina zaifita saboda tsoronka amma yau ubangijina ya cireni mini tsoronka kuma zakaga karfinsa kafin shamsal ya kara cewa komai hatyan ya ruga izuwa kansa yana mai kwalla kabbara aikuwa shima saiya tareshi suka ruguntsume da azababben yaki awannan rana su badi'atul nauwara sunga jarumtaka irin wacce basu taba ganiba kuma sunga gumurzu wanda ya firgita su ya dugunzuma hankalin kowa da komai dake birnin bindal adalilin masifar yakin mutum saida fiye da rabin gidan sarautar ya ruguje gobara ta tashi awurare da dama saida hatyan da sarki shamsal suka shafe sa'a biyar suna bakin gumurzun yaki hatyan ya cigaba da ambaton ubangiji acikin zuciyarsa hakanne yasa ya sami gagarumin karfi da kuzarin da yaki gajiya kowa awajen saida yayi matukar mamaki dakyar da sidin goshi hatyan ya shammaci sarki shamsal ya gabza masa wawan naushi akunnensa n hagu take shamsal ya dimauce ya fita hayyacinsa damar da hatyan ya samu kenan ya soka masa takobi amakoshinsa ta faso ta wuyansa ya fadi case matacce koda yarima zainur ya ga an kashe mahaifinsa sai ya yunkura ya ruga izuwa wajen gidan sarautar amma sai aimar da nasmal suka sha gabansa suka tareshi nantake aka zuba masa sarka aka tafi dashi gidan maza bisa cewar sai kotu ta zauna za'a yanke masa hukunci nantake badi'atul nauwara ta sa aka bude wata katuwar akwatu tasa aka fiddo kan Uwar macizai koda jama'ar birnin bindal suka yi arba da kan uwar macizai sai suka rude suka kama sambatu badi'atul nauwara ta dubesu ta daka musu tsawa tace nice na kashe uwar macizai da karfin ubangijin musulunci kuma gashi yanzu agaban idanunku hatyan ya kashe sarkinku da karfin ubangijin addinin musulunci alhalin a nahiyar gaba daya babu mai karfin damtsensa shin zaku karbi addinin gaskiya ko kun zabi mutuwa? kodajin wannan tambaya sai gaba daya jama'ar birnin mazansu da matansu yara da manya suka yi mubaya'a suka hada baki sukace munyi imani da ubangijin musulunci nantake farinciki ya lullube su badi'atul nauwara suka kama yiwa allah godiya bayan komai ya lafa sai jarumi hatyan yace to yanzu sai ki kaimu inda sarkin mafarauta yake amma kafin nan menene matsayina awajenki? dajin wannan tambaya sai badi'atul nauwara tayi murmushi ta kwalawa sarauniya anisa kira ba zato ba tsammani sai akaga anisa ta fito daga cikin wani rusashshen gini ta nufo inda suke fuskarta cike da murmushi da isowarta sai badi'atul nauwara tace a addinin musulunci namiji yana da ikon auren mata hudu shin yanzu kin amince ni dake mu zamo matan jarumi hatyan? cikin tsananin farinciki da murmushi anisa tace na amince dari bisa dari nantake jama'a suka kaure da kabbara shikuwa aimar saiya daga hannu akayi tsit sannan ya dubi sadirat yace to ke kumafa? addinin musulunci bai yadda mace ta auri maza biyu ba to tsakanin ni da nasmal wa zaki aura? sa'adda sadirat taji wannan tambaya sai tayi murmushi tace yadda za'ayi ku koma birninku asake yin wannnan gasar wanda duk yakai dabba kurzal kasa to shi zan aura Alhamdullillah anan mukazo karshen wannan labari na tarkon mutuwa ina godiya gareku sakamakon kasancewa tareda ni ayayin rubuta wannan labari tun daga na daya zuwa na tara da kuma baku hakuri akan rashin posting da wuri da wadanda suka kasance dani HABIBULLAH KBR. SAI KUMA NI SUNUSU SAS NAKE CE MUKU SAI MUN HADU A WANI LITTAFIN MAI SUNA hikayoyin sadaukai. WhatsApp 07067470752 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 11 of 11