Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 11
arzus bin sharkuf idanu cikin firgici shekarar da boka arzus ya sauka anahiyar yayi abubuwan al’ajabi da yawa wadanda suka daurewa mutane kai yazamana cewa ana girmamashi kamar za’a bauta masa komai tsananiin cuta indai bata ajali bace,to indai boka arzus yazo ya tsaya akan mutum to sai ya warke ya mike sumul tammkar bai taba cutaba komai talauci idan mutun mulki yake nema sai ya samu ba neman suna ko daukaka, bisa wannan daliline sarakan nahiyar sukayi ca akan boka arzun kowannensu na zuwa da bukatarsa yana biya masa amma sarkin birnin bindal wato mahaifin sarki shamsal ne bai taba zuwa gareshiba saboda shi yana ganin shi bashida wani abu da zai nema awajensa saboda Allah ya horemasa lafiya daukaka gami da arzikin da babu me kamarsa awannan nahiyar, bisa wannan daliline yazamana cewa ansami rashin jituwa tsakanin koka arzur da sarki watarana boka arzur na tare da manyan sarakuna guda uku na nahiyar a gidansa dake can tsakiyar wani daji wanda ake kira jahal sai kawai aka hango wani abu a can sama tamkar tauraruwa ya taho yana feshin wuta kuma ya nufo inda boka arzur ke zaune. Nan take wadannan sarakuna uku tare da gaba dayan hadiman boka arzur suka firgice suka ruga da gudu suka kama buya a cikin gidan,ya zamana cewa boka arzur kadai aka bari a zaune,ko alamar tsoro babu a tare da shi,saboda ya yarda da kansa ma sai ya dora kafarsa daya bisa dayar ya kurawa wannan tauraruwa idanu yana jiran isowarta. sai da ya rage saura baifi taku biyarba tsakaninsu sai tauraruwar ta fado kusa da shi agabansa ta rikide ta zama sarkin bindal a cikin gagarumar shigar yaki. nan fa wayanda suka boye,suka fara firfitowa suna kallon ikon Allah,kawai sai akayi kallon yan dakiku sannan boka arzur yayi murmushi ya mike tsaye daga kan kujerar da yake zaune ya dube shi yace”lale marhaban da kai,”wanan Sarki mai daraja tabbas nayi farinciki da wannan ziyarar taka wacce ban taba zatoba don haka nayi maka alkawarin zanbiya maka duk irin bukatar dakazo mini da ita kodajin haka sai sarkin bindal ya turbune fuska yace banzo gareka don neman wata bukataba saboda baka da abinda bani dashi na zone na baka umarni katashi daga cikin yankin kasata inason ka hada naka da anaka ka bar mana nahiyarmu acikin kwanaki uku kacal inba hakaba kuwa zaka rasa rayuwarka nine kadai sarkin da kowa yake shakka a wannan nahiya anayi mini ladabi kamar abin bauta amma yanzu komai na neman dawowa gareka to ka sani ba’ayin sarki biyu agari daya na fuskanci cewa idan na kyaleka kaci gaba da harkokinka da sannu zaka raba mu da mulkinmu koda sarki yazonan azancensa sai boka arzur ya takarkare ya bushe da dariya lokaci guda kuma ya turbune fuskarsa yace yakai wannan sarki ka sani cewa tinda nazo wannan nahiya da niyyar na mulketa, da acikin daredaya zan gama da ita .to amma nazone sabo wani buri guda daya wanda ya rage mini arayuwata Koda kuwa ban cika wannan burin a zamaninku ba sai na cikashi ana yayanku ko jikokinku,burin kuwa shine ina so na hattama wani sihirin tsafi wanda na farashi tun ina da shekaru tara aduniya wannan tsafi bazai kammalu ba har sai sarakai dari da daya sun durkusa a gabana bisa gwiwoyinsu na dafa kawunansu yayin da sukazo neman bukata ,wato nasa musu albarka ahalin yanzu sarakuna arba’in da dayane jal suka durkusa agareni ina neman hamsin da takwas kuma dole sai awannan nahiya takune zan sami wadannan sarakunan da nake nema saboda haka babu wanda ya isa yasa nabar wannan nahiya face ba na num fashi adoron kasa ko mujima ko mu dade kai ma sai kazo ka durkusa agabana idan baka durkusa mini ba sai danka ko jikanka yazo ya durkusa mini gama fadin hakan keda wuya sai boka arzur ya bushe da dariyar mugunta yayita kyakyatawa kamar ba zai dai naba al’amarin daya matukar fusata sarkin bindal ke nan kawai sai ya zare takobinsa ya dako tsalle daga inda yake tsaye tamkar an harboshi daga cikin baka cikin bakin zafin nama boka arzur ya kaucewa mummunan saran da sarki ya kawo masa wanda saura kiris ya sare masa kai kawai sai akaga shima boka arzur ya daga hannunsa sama takobinsa ta baiyana yatari sarki suka ruguntsume da azababben yaki ya zamana cewa suna kaiwa junansu sara da suka cikin zafin nama juriya da bajinta ta ban al’ajabi sai da suka shafe sa’a guda suna bakin artabu da kyar kowanensu ya sami nasarar yankar abokin gwaminsa shi dai sarkin bindal agefen hannun hagu ya yanki boka arzur shikuma boka arzur akan cinyar dama ya yanki sarkin bindal raunin baiyi wani zurfi sosaiba koda sukaga cewa jarumtakarsu tazo daya sai suka koma yakar juna da karfin sihirin tsafi wohoho masifa ba’asamata rana wadannan sarakuna uku dake wannan wurin tareda hadiman boka arzur sunga turnuku irin wanda basu taba ganiba kuma sunga tashin hankali wanda ya firgitasu sukaji kamar su haka rami su shige ciki hatta bishiyoyi da duwatsu dake cikin dajin sai da suka rinka farfashewa suna karyewa .saboda bala’in da jaruman biyu suke haddasawa wani lokacin sai su rikide su zama manyan dabbobin daji suyita gumurzu shikansa dajin girgiza yakeyi kamar kasa zata rufta duk abinda yake cikinta ya rufta ciki ahaka sai da suka shafe sa’a uku suna masifaffen yaki har sai da kusan ko ina ya kama da wuta adajin asannan ne boka arzur da sarkin bindal suka jugata ainun suka zube kasa sunata faman yin haki da numfashi kamar ransu zai fita. sai da suka dan jima kwance akasa suna hararar juna sannan sarki bindal ya mike tsaye ya dubi boka arzur cikin tsananin fushi da kiyayya yace narantse da girman iyayena daga yau babu wani sarki dazai kara zuwa gareka ya durkusa agabanka muddin ina numfashi adoron kasa kodajin wannan batu sai boka arzur ya mike tsaye zumbir yace nima na rantse . da gemun ubana har abada zuriyarka bazasu zauna lafiya ba har tsakanin iyaye da ‘ya’ya sai an sami sabani kuma sai wannan masarautar tabar hannunku ta koma hannun wayanda ma basu gadaba dajin wannan batu sai sarkin bindal yayi girgiza ya zama tururuwa ya cilla izuwa cikin kololuwar sama ya bace acikin gajimare tamkar bai taba wanzuwaba WANNAN SHINE ASALIN TARIHIN DANGANTAKAR BOKA ARZUR DA GIDAN SARAUTAR BIRNIN BINDAL TARKON MUTUWA 5 B boka arzur makiyin ubankane babu hujjar da zatasa ya soka kawai zaiyi amfani dakaine don biyan bukatarsa dazarar anci moriyar ganga za’a yar da koranta ne zaka yi nadamar wannan butulci dakyiwa mahaifinka kuma saika zubarda hawaye da idanunka kafin ta gama rufe bakinta tuni yarima yadaka mata tsawa yana mai cewa don me bazanci amanar mahaifina ba alhalin ya juya mini baya tun daga ranar da hatyan ya sare mini hannu daga wannan ranar ya tsaneni,yadaina nuna min so da kauna jama,a sun fuskanci cewar bazai taba bani karagar ba, saboda na zāmana sarki yanzu tafi duk inda kikeso kije domin tafiyar taki zata fiye mana alheri gaba daya, dajin haka sai mahaifiyar yarima ta juya ta fuce da sauri afusace tafice daga cikin fadar tana zubar da kwalla saboda bakin ciki da takaici ma ko waigowa bata sakeyi ba shikuwa yarima koda yaga mahaifiyar tasa ta tafi saiya bushe da dariyar farinciki sannan ya dubi sarkin dogarai yace inaso yau da yamma ku zagaya gida gida ku kamo min gaba daya ‘yan matan garin nan da zawarawa matasa banda tsofaffi kuzo min dasu nan kodajin wannan batu sai boka arzur ya yi wuf ya dakatarda sarkin dogarai ya kama hannun yarima yajashi izuwa gefe daya inda babu wamda zaiji abinda zasu tattauna ya dubeshi yace idan kaci gaba da wannan huldar ta mata duk abinda mukasa agaban mu rushewa zaiyi kodajin wannan batu sai hankalin yarima ya dugunzuma takaici ya turnukeshi ya rasa abinda ke masa dadi aduniya saboda a iya rayuwarsa babu abinda ransa yakeso sama da yiwa mata fyade cikin alamun tsananin damuwa yarima ya dubi boka arzur ya ce shin zan iya tura dakaru zuwa wasu kauyuka adebo min wadan nan mata? boka arzur ya kada kai yace ya shugabana dolene fa ka kawar da wannan halayya taka idan har kanaso kayi nisan kwana akan karagar mulki,, domin zina gami da zubar da jini suna lalata sihirin tsafin danakeyi yanzu kodajin haka saiya juya da sauri ya fice daga cikin fadar cikin matsanancin fushi ya nufi bangaren da turakar sarki take da shigarsa cikin babban falo na sarki shamsal sai yayi arba da wani babban hoto na sarki shamsal wanda wani kwararren mai zane ya zana an sakale wannan taswira acan saman bango koda yarima ya kalli wannan hoto sai yaji ya tsani mahaifin nasa fiyeda ko yaushe don haka sai ya zare takobinsa ya daka tsalle sama ya datsa hoton gida biyu ya fado kasa karar sare hoton ne yasa hadimai suka rugo da gudu izuwa cikin falon, sai sukaga hoton sarki shamsal agabansa kuma arabe gida biyu sai gaba dayansu suka sunkuyar da kansu kasa kawai sai yarima ya daka musu tsawa yace su fice daga cikin fadar gaba daya kafin kace me? sun fice gaba dayansu babu ko mutum daya nan take yarima yaje inda aka ajiye tambulan kayan shaye shaye kawai saiya suri tambulan din giya guda daya ya kafa abakinsa yakama kwankwada harsaida giyar ta kare kaf ko digo daya babu saura sannan yai jifa da tambulan din kasa ya fashe yana tangadi ya nufi cikin turakar barci,, har wadansu kuyangi guda hudu sun biyoshi abaya saiya daka musu harara suka koma da sauri kawai saiya banko kofar dakìn ya fada kan gado ya baje nantake kuwa ya kama barci harda munshari acikin garin bindal kuwa tuni labari ya riski jama’a cewa boka arzur ya hana wannan sabon azzalumin sarki yin mugayen halayensa bisa hakane yan mata da zawarawa suka kamu da farinciki hakama iyayensu nanfa iyaye da sauran mutanen gari suka ci gaba da tsegumi iri iri wasu suce ai har mulkin zaluncin da sarki shamsal yakeyi ada yanzu zai ragu tunda an sami sauyin sarki wasu kuma suka dinga cewa ai babu tabbacin hakan sai dai abinda aka gani tunda boka arzur ne ke mulkin birnin afakaice tunda sai abin daya fada akeyi wannan shine abinda yafaru abirnin bindal bayan tafiyar sarki shamsal Acan birnin askandariya kuwa jarumi hatyan da ‘yar uwarsa sadirat tunda suka bingire akan gado suka kama barci tamkar gawa dayansu bai farkaba har sai da dare ya raba tsakiya dai dai wannan lokaci ne jarumi hatyan ya farka yana mai bude idanunsa a hankali.ba tare da jin wata gajiya ko tsamin jiki ba sai ya mike zaune ya dubi yar uwarsa sadirat yaga ko motsin kirki batayi sai yayi murmushi sannan ya mike tsaye ya kama kai kawo acikin turakar yana mai mamakin yadda akayi yaji kwarin jikinsa tamkar wani abu bai taba lafiyarsaba nantake tunani iri iri ya fara fado masa arai,da farko yace yanzu idan sarki shamsal ya iso garinnan ya riskemu nida yar uwata ai mun jefa anisa da badi’atul nauwara acikin masifa lallai yana da kyau agoben nan mu bar garinnan mu kara gaba wai shin da gaskene anisa tana sona kamar yadda naga alamun cewa badi’atul nauwara tun haduwarmu ta farko? tayaya zan hada soyayyar aminai guda biyu kuma gashi kowacce acikinsu tayi mini halaccin da bai kamata na juya mata baya ba koda gama fadin hakan sai hatyan ya lura ai wannan daki da suke ciki bashine dakin da aka saukesuba da farko to yaushe aka dawo dasu nan basu saniba amsar da hatyan ya kasa baiwa kansa kenan alokcin da hankalinsa ya dugunzuma sakamakon rashin ganin kofar fita daga wannan daki da suke ciki cikin kaduwa da mamaki hatyan ya shafa dukkanin bangwayen dakin amma yaji shiru kamar maye yaci shirwa hakadai yaci gaba da dube dube da tabe tabe gami da leke leke har karkashin gado amma duk baiga wani wuri mai alamar kofar fita ba domin ko ina a shafe yake adaidai wannan lokacine sadirat ta farka daga barcin koda taga hatyan yanata lalube kuma ta lura cewa an sauya musu daki sai itama hankalnta ya tashi,ta tashi tsaye da sauri tasha gabansa tana mai cewa wai me ke faruwa naga an chanja mana masaukin mu? kodajin wannan tambaya sai hatyan ya dawo cikin hayyacinsa yayi ajiyar numfashi sannan yace ina ganin dai saboda tsarone yasa aka kawomu nan babu mamaki su sarki shamsal sun iso sun fara bincike kodajin wanna batu sai saidira taji zuciyarta ta buga da karfin gaske fiye da ko yaushe nan take jikinta ya kama kyarma koda ganinhaka sai hatyan yayi murmushi ya dafa kafadarta yace ki kwantar da hankalinki yake yar uwata kiyi sani .cewa babu abinda zai samemu kuma ina tabbatar miki da cewa idan har sarki shamsal na nan to yau zai mutu kodajin wanan batu sai sadirat ta sake firgita ta dubi hatyan cikin firgici tace yakai dan uwana kada ka kuskusra kace zakayi wani abu domin baka da nasara akan sarki shamsal yanzu sai dai nan da wadansu shekaru kamar yadda bokaye suka fada hatyan yace nidai banyi imani da duk maganganun bokayeba abinda na yarda dashi kawai shine sa’a da rabo kin sani cewa ke baki isa ki hanani aiwatar da duk abindana so yiba don haka kawai ki zuba ido koda gama fadin hakan sai hatyan yaci gaba da neman kofar fita daga cikin dakin ita kuwa sadirat sai hankalinta ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe kwatsam sai su kaga wata kofa akasa ta bude da kanta saiga matattakalar bene wacce tayi sama TARKON MUTUWA 5 C Al’amarin da ya daure musu kai kenan suka fahimci cewar inda suke dakin kasa ne, har hatyan ya yunkura zai hau kan matattakalar benen ya fice sai ga sarauniya anisa ta shigo ta cikin matattakalar benen tare da wasu hadimanta guda uku anisa tayiwa hatyan wani irin kallo na zargi gamida dan guntun murmurshi tace kadaina tunanin zaka kaiwa sarki shamsal harin bazato don kawar dashi domin bazaka taba samun nasara ba kamar yadda yar uwarka ta fada maka haka al’amarin yake, karonka da sarki shamsal na farko kayi matukar sa’a da kawata badi’atul nauwara ta kawo maka dauki idan ka kuskura ka sake tarar sarki shamsal a karo na biyu mutuwa zakayi indai ni ko ita bamu kawo maka daukiba koda sarauniya anisa tazo nan azancenta sai mamaki ya turnuke hatyan nan take ya gane cewa tabbas itama sarauniya anisa tana da abinda take takama dashi walau tsafi ko jarumtaka tunda tana fadin cewa zata iya bashi kariya yana cikin wannan tunanin anisa ta katseshi tace yanzu gari ya waye kuma tun adaren jiya sarki shamsal da bokansa suka bincike ko ina acikin wannan gidan sarautar nawa suna nemanka basu gankaba a yanzu haka suna chan akwance suna barci nan da cikar kamar sa’o’i uku wasu kwararrun hadimansa masana iya bincike zasu iso garinnan idan suka iso kuwa sai sun gano inda kuke saboda haka dolene sai kun fice daga garinnan yanzu a sirrance ku sani cewa tafiyar sa’a biyu da rabi kacal zakuyi abangaren kudu ku fice daga cikin wannan nahiya gaba wadannan hadiman nawa suna tare dani zamuyi muku rakiya izuwa iyakar kasata da nahiyar dake gaba kuma zamu kawar da duk wata shaida da zata nuna sawunku ko wata alama ta cewar an fita daga garinnan yanzu sai kuyi sauri ku dauki kayanku mu tafi domin bamuda isasshen lokaci koda sarauniya anisa tazo nan azancenta sai jarumi hatyan yaji wani irin bakin ciki ya turnukeshi badon komaiba sai saboda ya ayyana aransa cewa takowanne hali sai ya kaiwa sarki shamsal harin bazato har masaukinsa ba tareda wata gardamaba sai hatyan da sadirat suka dauko jakunkunansu anisa da hadimanta guda uku suka yi musu jagora suka fice daga cikin gidan sarautar ta wata barauniyar hanya wacce komai kwakkwafin mutum bai isa ya iya gano akwaitaba can bayan gidan sarautar bangaren kudu suka fito ta karkashin kasa kuma ta cikin wani rairayi wandaya lullube wata kofar katako dafitowarsu sai suka mayarda kofar suka rufe rairayi ya lullube tamkar bata taba wanzuwaba agurin tuni sun iske wadansu kosassun dawakai guda shida daure awajen suna harbin iska akan dawakai biyu akwai guzuri na matafiya kawai sai sarauniya anisa ta dubi hatyan tace ku kama wadancan dawakan biyu masu dauke da guzuri ku hau sune naku kafin dayansu yayi wani yunkuri tuni anisa ta kama daya daga cikin ragowar dawakan ta hau koda hatyan yaga irin hawan dokin da tayi sai ya kamu da mamaki domin da gani kasan cewa ta kware kuma sai manyan jarumaine suke yin irin wannan hawan alokacin da tayi tsallene rigar jikinta ta bayyana tana sanye da matsatstsun tufafi na fatar damisa wadanda suka bayyana gaba dayan siffofinta kuma a sannan ne gashin kanta dake daure ya zubo kasa harkan duga duganta koda jarumi hatyan yayi arba da wannan kyakkyawar sura tata saiya dimauce domin a sannan ne ya gane cewa tafi sarauniya badi’atul nauwara komai na kyan sura, kyan fatar jiki da kuma kyawun fuska batare da bata lokaci ba suka sukwani dawakan su da gudu izuwa cikin daji sarauniya anisa ce akan gaba ai kuwa nan da nan ta baiwa su hatyan tazara mai yawa sadirat ce acan karshen baya sannan hadimanta guda uku, tsakanin dokinta dana hatyan akwai tazarar kimanin taku ashirin koda ganin haka sai shima ya karawa nasa dokin kaimi ya zabureshi da gudun gaske koda anisa ta fiskanci cewa hatyan ya karawa dokinsa kaimi don ya kamota sai itama ta karawa nata dokin kaimi nan danan tazarar dake tsakaninsu ta sake ninkawa takai kusan taku arba’in koda sadirat da sauran hadiman sukaga an musu nisa sai suka kara zage dantse lokacinda hatyan yayi iya yinsa yaga ya kasa kamo sarauniya anisa saiya fusata ya daka tsalle sama daga kan dokinsa ya dirgo kasa yaci gaba da falfalawa da gudu da kafafunsa shi kuwa shikuwa dokin nasa saiya bishi a baya wohoho! wanda Allah ya baiwa kyautar baiwa babu yadda za’ayi dashi sai kallo kafin cikar dakiku arb’in tuni hatyan yazò ya gifta sarauniya anisa akan dokinta harya bata tazarar data bashi yana riskarta yayi mata murmushin sai kinzo hatyan yaci gaba da gudu har izuwa wasu dakiku masu yawa kwatsam ba zato ba tsammani saiyaji taku bayansa al’amarin dayai matukar bashi mamaki kenan domin shi azatonsa babu wani doki ko bil’adama da zai iya cimmasa agudu face sarki shamsal nan take yaji zuciyarsa tadan buga da karfi kawai saiya tsaya ya juya domin yaga kowanene ke shirin cimmasa ba zato ba tsammani sai yaga ashe anisace itama ta duro daga kan dokinta itama taci gaba da gudu cikin matùkar mamaki yayi sauri yaci gaba da gudun don karta wuce she nan dai suka jera sai gashi ya kasa tsere mata al’amarin dayai matukar bashi mamaki kenan waishin dama akwai wanda yake da. irin baiwar da muke da ita nida sarki shamsal? saida suka shafe kusan rabin sa’a suna gudu sannan ne sarauniya anisa ta fara rage karfin gudunta koda ganin haka sai hatyan yayi murmushi yasan cewa adade anayi sai gaskiya kuma sai miya ta kare sannan ake sanin maci tuwo ko tafiyar dakika goma basù karasaba sai kawai yaga anisa ta zube kasa sharaf tana haki sai hatyan a kyalkyale da dariya yace iyakar juriyar taki kenan a gudu kodajin haka sai anisa ta maida masa da martanin dariya ta dubeshi alokacin daya zauna dishan daf da ita yana haki tace ai nan ne daf da iyakar nahiyarmu da nahiyar dake gabanmu daganan tafiyar sa’a shida kachal zakayi ka shiga nahiyar kasashen bakaken fata kodajin wannan batu sai hatyan ya jiwata irin matsanaciyar damuwa tazo masa tamkar yace ya fasa ci gaba da tafiyar waishin rabuwa. da anisa ce bayaso kokuwa ya gaji da wannan gudun ceton ran da sukeyine? amsar daya kasa baiwa kansa kenan duk su biyun sai sukayi shiru har izuwa tsawon yan dakiku adaidai wannan lokacine suka fara hango hadiman anisa da sadirat bisa dawakai daga chan nesa da kuma nasu dawakan guda biyu hatyan yayi ajiyar numfashi yana mai dan sunkwui dakai kasa yace yake wannan sarauniya yanzu gashi zamu rabu kuma banida tabbacin zamu sake saduwa a wannan rayuwa keda kawarki badi’atul nauwara kunyi mana taimakon da bamu da abinda zamu saka muku dashi nida yar uwata kodajin wannan batu sai tayi murmushi tace ai rabuwarmu anan ba itace rabuwarmuba duk inda kuke muna tare daku kada ka damu abu daya nake so dakai ka zamo mai halacci kuma kayi hukunci bisa adalci ga duk mutuminda mu’amala ta hadaka dashi kaso mutum gwargwadon yadda yasoka abu na karshe ka kula da kanka karka bayarda zuciyarka ga kowa sai wanda ka tabbatar da cewar shine yafi dacewa dakai sa’adda anisa tazonan azancenta sai jarumi hatyan ya dubeta cikin matukar mamaki gami da rashin fahimta yace ya shugabata gaskiya kin batar dani ko ince wadannan maganganun naki sunfi karfin fahimtata shin zaki fahimtar dani? dajin haka sai anisa tayi murmushi tace kada ka damu da sannu zaka fahimci komai anan gaba abu na karshe dazan sanar dakai shine idan ka isa gari na gaba kada ka yarda da kowa face wanda ka karanci halayyarsa,, ka fahimceshi amatsayinka na bako duk inda ka shiga ka boye baiwarka kuma ka kankantar da kanka ga jama’ar gari ta hakane kadai zaka san sirrin gari da jama’ar sa ka jajurce wajen neman halak babu ruwanka da haram ko zalunci kayi taimako ga mai bukatarsa ka zamo mai tausayi da jin kai hakan zaisa kasake nasara bisa duk abinda kasa agabanka daga yau ka jajurce wajen bawa kanka horon yaki da fada idan har kanason kadauki fansar ran iyayenka akan sarki shamsal domin karo dashi sai an shirya koda kuwa shekarunka sunkai lokacinda da bokaye ke fadi da wannan furuci nake yi maka bankwana sai mun sake saduwa nan da wani lokaci kadan domin lokacin komawata birnina yayi domin hadiman sarki shamsl masana bincike sun kusa karasowa gama fadin hakan keda wuya sai gasu sadirat sun iso nantake hadiman nan uku suka fara goge sawayen dawakan nasu ita kuwa anisa saita rungume sadirat tana mai yi mata ban kwana taja dokinta ta kama ta hau ta zabureshi da gudu alokacin da hatyan ya bita da kallo zuciyarsa cike da wasu tambayoyi gamida rashin fahimta su kuwa hadiman nan uku sai suka ci gaba da aikinsu na share sawayen dawakan kuma kowannensu na ruke da dokinsa ar sukayi nisa da ganin haka sai hatyan da sadirat suka kada dawakansu suka tsallaka nahiyar suka nausa cikin daji KU SHA RUWA mukoma bakin fahama zamushiga LITTAFI NA 6 TARKON MUTUWA Littafi na Shida 6 Part 6 A . . Sarauniya badi'atul nauwara nata faman sharar barci akan gado sai kawai taji hasken ranaya dallare mata idanu tana bude idanun ta kuwa sai tayi arba da kawarta sarauniya anisa zaune akan kujera daf da gadon da take kwance ta kura mata idanu tana yi mata murmurshi badi'atul nauwara ta mike zaune zumbur ta dubi anisa cikin kaduwa da firgici tace me ake ciki? ina su hatyan? ina fatan dai asirin mu bai tonu ba kodajin haka sai anisa ta kyalkyale da dariya Sannan tace ai tuni su hatyan sun shiga wata nahiyar babu yadda za'ayi sarki shamsal ya sake ganin su sai dai kawai zasu iya haduwa da mugayen tarkunansa akan hanyarsu yanzu kece kadai matsalata cikin firgici badi'atul nauwara ta sake duban anisa tace tayaya akayi na zama matsala agareki? anisa tace nan da cikar sa'a daya jal kwararrun hadiman sarki shamsal zasu iso masa bincike tabbas zasu iya gano wannan daki da kike ciki yanzu kinga kuwa idan suka ganki zargi ya tabbata akan mu hanya dayace zamu bi mu kawar da wannan matsala cikin zakuwa badi'atul nauwara ta ce wacce hanya ce kenan? anisa tace dolene mu batar da kamanninki yadda babu mai shaidaki hakan bazai taba yiwuwa ba face mun shafe gaba dayan jikinki da bakin lalle wanda sai an kwana bakwai ana wanke shi sannan zai fita tabbas idan aka shafe ki dashi zata za'ayi ke bakar fatace kuma komai kwakkwafin mutum bai isa ya iya shaidaki ba sai bayan sarki shamsal ya bar garinnan sannan za'a wanke miki wannan lalle kodajin wannan batu sai hankalin badi'atul nauwara ya dugunzuma ainun saboda ko kadan batason abinda zai taba lafiyar jikinta kai gani takema kamar idan aka shafe ta da wannan lalle shikenan har abada haka zata kasance amatsayin bakar fata yayin da anisa ta lura da wannan damuwa tata saita dubeta cikin murmushi tace indai kin yarda dani amatsayin aminiyarki to ki cire duk wata damuwa dake ranki ko kuwa kina tunanin cewa zan iya cutar dake ne? kodajin wannan tambaya sai anisa tayi murmushi cikin yake tace haba yake kawata ai amana guda daya ce nayarda a shafeni da wannan lalle amma ina neman alfarma guda daya ki sani cewa inbanda mahaifiyata duk fadin duniyar nan babu wanda ya taba ganin tsiraicina don haka wanda duk zaiyi wannan aiki inason ya kasance macece kuma mai shekaru irin na mahaifiyata...hmmmmm amma banda matan yanzu duk samari sungama...... kodajin wannan batu sai sarauniya anisa tayi murmushi tace aikuwa kamar kin sani mai wannan aiki wata kwararriyar macece wadda ahalin yanzu shekarunta sunkai arba'in da shida duk duniya babu wanda yakaita kwarewa a iya kunshi kuma itace ta kirkiri wannan lalle da kanta yanzun nan zata zo tayi miki wannan aiki ba tareda bata lokaciba gama fadin hakan keda wuya say sarauniya anisa ta kama hannun sarauniya badi'atul nauwara suka mike tsaye tare sannan ta jata suka fice daga cikin dakin suka nufi wani bangare daban na gidan sarautar yar gajeriyar tafiya sukayi suka iso kofar wani karamin daki da zuwansu sai suka tsaya chak anisa ta dubi badi'atul nauwara ta tura kofar ta shiga tana shiga sai zuciyarta ta buga da karfin gaske sakamakon yin arba da ummul khairi bakomaine ya haddasa hakanba face kasa gano inda tasan wannan mata tabbas ta taba ganinta a wadansu shekaru da suka shude kuma tafi tunanin cewa tana yarinya ne karama nandai badi'atul nauwara ta turo kofar dakin tasanya sakata da hannunta alokacin da ummul khairi ta dago kai ta kura mata idanu tanayi mata murmushi amma idanunta cike suke da kwallah al'amarin dayai matukar kada sarauniya badi'atul nauwara kenan kuma ya bata mamaki don haka batasan sa'adda ta durkusa kasa agabantaba ta dubeta cikin girmamawa tace yake wannan ma'abociyar kunci ina dalilin zuwan kwallah a idanunki sakamakon ganina? sa'adda ummulkhairi taji wannan tambaya sai hawayenta ya zubo tace yake 'yata yanzu ashe dama 'ya zata iya mantawa da uwarta? rabona dake tun sa'adda da mahaifiyarki ta kawo ziyarar karshe nan garin nice wacce tayiwa mahaifiyarki kunshi da kitso harya zamana cewa munshaku ainun dake agidana kike kwana dare da rana bama rabuwa idan ban mantaba idan an bude gashinki akwai wani tabon ciwon kuna da kika yi adakina da wutar jin dumi alokacin da ake wani hunturun sanyi koda gama fadin hakan sai ummulkhairi ta yiwa badi'atul nauwara nuni da wani katon madubi dake manne ajikin bango tacè jeki gaban wancan madubin ki kwaye keyarki mu gani batareda wata gardamaba sai badi'atul nauwara taje gaban madubin ta juya masa baya ta kwaye gashinta daya zubo kasan keyarta ai kuwa saiga wannan tabon wutar nantake ta tuno da inda abin ya faru alokacin batafi shekara bakwai ba aduniya gama tunanin keda wuya sai badi'atul nauwara ta ruga izuwa ga ummul khairi ta rungumeta tana mai zubar da hawaye tace tabbas ke uwace agareni domin tun ina karama kin wanke dukkan jikina bainda wata fargaba atare da ke tana gama fadin hakan ta kama cire tufafin jikinta da kanta har sai da tayi zigidir agaban tsohuwa ummulkhairi ita kuwa ummulkhairi saita dauko wani akushi cike da wani bakin lalle mai kyalli da maiko na musamman ta kama shafeshi adukkan jikin sarauniya badi'atul nauwara da zarar ta shafa lallen sai badi'atul nauwara taga nan take lallen ya bushe ajikinta kuma ya saje da fatarta tamkar dama can bakar fatace ba faraba al'amarin dayai dugunzuma hankalinta kenan jikinta ya fara kyarma amma sai ummulkhairi ta dafa kafadarta tace kwantar da hankalinki yake 'yata kiyi sani cewa ina wanke wannan lalle kamar yadda ruwa yake wankè datti ajikin tufafi dajin haka sai hankalin badi'atul nauwara ya kwanta ta saki jikinta akaci gaba da shafeta kafin rana ta fadi tuni hadiman sarki shamsal kwararrun iya bincike sun hallara abirnin askandariya sudai wadannan hadimai su dari da ashirin da dayane kuma an zabosune daga kasashe daban daban acikinsu mutum dayane jal aka dauko daga birnin bindal gaba dayansu tsofaffin dakarun yakine wadanda suka kware wajen iya leken asiri kuma kallo daya zakayi musu kasan cewa yan duniya ne wadanda sukaga jiya sukaga yau kuma sukasan dukkan kissa da tuggun rayuwa da isowar wadannan hadimai sai aka yi musu iso har cikin fadar sarauniya anisa inda ta taresu hannu biyu ta shaida musu cewa ubangidansu sarki shamsl yanzu haka yana chan ma $aukinsa yana barci sakamakon ya kwana yana bincike da kansa abirnin kodajin wannan batu sai shugaban hadiman wani dattijo dan shekara saba'in wanda duk gashin jikinsa farine fat babu baki sai yayi ajiyar zuciya cikin takaici saboda yasan cewa sarkì shamsal ya tafka kuskure na farko nandai saraunya anisa ta dubi shugaban hadiman tace yanzu za'akaiku masauki domin ku je ku kwanta ku huta kuma a kawo muku abinci dajin haka sai shugaban hadiman yace a'a ranki y dade ai dokar wannan aiki namu bamacin abincin kowa sai wanda mukazo dashi ............... ..anan zantsaya kada nacikaku da surutu dan haka kowa yan sirara yasaki ransa yahuta kafin muci gaba da sankamowa. TARKON MUTUWA Littafi na Shida 6 Part 6 B . . Muna fatan zaki bamu hadin kai bisa duk abin da muka bukata domin idan kika ki za'a iya samun sabani tsakanin ki da mai girma sarki shamsal lokacin da shugaban hadiman yazo nan azancensa sai zuciyar anisa ta buga da karfi domin ta fahimci cewar ta hadu da tsohon dan duniya wanda zai iya tono asirinta amma sai ta dake bata nuna alamar karayar taba ta dubi Tsohon da kwarin guiwarta tace zan baku cikakken hadin kai amma bisa irin sharadin da ke tsakanina da sarki shamsal sharadin kuwa shine ban yarda

Chapter 6 of 11