Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
10 / 11
daban na gidan sarautar alokacin da sadirat ta ringa waigen aimar shikuma ya bita da kallo dauke da wani tattausan murmushi mai nuna cewa ya dade yana kaunarta da begenta tuni kishi ya turnuke yarima nasmal bisa ganin yadda sadirat ke waigen aimar domin azatonsa ta kamu da sonsa ne hatyan da sadirat sunyi sha'awa mutuka bisa ganin yadda tsarin ginin gidan sarautar yake da kuma irin kayan kawar da aka zuba masa kasancewar yasha banban da irin nasu cikin wani katon gida aka shiga dasu mai dauke da babban falo aka barsu kan kujeru na alfarma aka zaunar dasu kuyangi bayi da hafiman dake cikin gidan sun haura guda dari nan da nan aka kawowa hatyan da sadirat abinci mai daraja iri iri har kimanin kala goma nandai suka zauna tareda yarima nasmal sukaci suka sha bayan sun sami nutsuwa ne nasmal ya rinka yiwa hatyan bayanin yadda al'adunsu suke da kuma harkar masarautarsu da addininsu wanda yakasance suna bautar wadansu aljanune duk abinda nasmal ya fada sai hatyan ya fassarawa sadirat izuwa yarensu wadansu abubuwan idan sukaji saisu bushe da dariya domin sai suga su agarinsu wannan abin ma kauyanci ne hakadai idan suka yita hira har dare ya raba duk tsawon wannan lokaci sadirat ta lura cewa nasmal satar kallonta kawai yakeyi amma da zarar yaga zasu hada idanu sai yayi sauri ya kauda kai hakanne yasa ta gane lallai ya kamu da tsananin santa nantake ta tuno da irin kallon da boka aimar ya dinga yi mata da kalaman da yayi mata wanda ya tabbatar da soyayyarsa agareta koda sadirat tazo nan atunaninta saitaji zuciyarta ta buga da karfi kawai saita tambayi kanta tace to waishin nida bantaba yin soyayyaba ban ma san yadda akeyiba taya zanyi soyayya da wadannan samari biyu wanda dukkannin su suna nuna mini so? tabbas kowannensu yana da siffar kamala gamida kyawun daya kamata asoshi shikenan kaddara zata fitar da wanda yafi dacewa wɑɳɳɑɳ รɦiɳɛ ɑɓiɳɗɑyɑ Բɑʀu gɑรu ʝɑʀuɱi ɦɑtyɑɳ ɓɑyɑɳ รuɳ iรɑ ɓiʀɳiɳ Բɑʀkѳ ɳɑ ɳɑɦiyɑʀ ɓɑkɑkɛɳ Բɑtɑ ɑʆѳkɑciɳɗɑ ɗɑɓɓɑ tɑ ɓɑyyɑɳɑ wɑtѳ uwɑʀ ɱɑcizɑi a can birnin sarauniya badi'atul nauwara abinda ya kamata tayi batayi kasa aguiwa ba saita kama binkice acikin gidan sarautar tana neman littafi mai dauke da tarihin addinin musulunci da kuma shikansa addinin da yarda ake shigarsa saida suka shafe kusan rabin sa'a tanata dube dube sannan ta ganshi acan kasan wata doguwar durowa dake manne ajikin bango cikin farinciki ta zauna ta bude littafin ta fara karatunsa tundaga farko har karshe afarkon yammaci ne ya fara karatun littafin wanda ya dauke hankalinta gaba daya yasata manta da batun yunwa ,kishirwa, gajiya da barci domin arayuwarta bata jin managanu masu ratsa jikiba kamar na cikin littafin bata tabajin kalmomin hikimaba d basira irinsu nantake jikinta gabe daya yayi sanyi kuma zuciyarta tayi imani da duk abinda take karantawa taji ta gamsu dari bisa dari cewar wannan littafi akwai ayoyin alkurani mai tsarki aciki tareda hadisan manzon allah s.a.w aciki koda sarauniya badi'atul nauwara tazo inda aka rubuta kalmar shahada saita karantata afili bata saniba aikuwa sai nantake taji tsigar jikinta duk sun karbi kalmar kuma sunyi imani da ita awannan lokaci tsohuwa ummulkhairi na zaune acan gefe daya tana kallon badi'atul nauwara kuma tana sauraronta koda sarauniya badi'atul ta biya kalmar shahada afili sai bokanya ummulkhairi ta firgita ainun taji kamar an watso mata wuta bata san sa'adda ta kurma uban ihuba ta fadi can gefe daya tana haki kamar wacce tasha faman gudu hakanne yasa badi'atul nauwara ta kara imani domin ta tabbatar da cewa tsafi da sauran addinai karyane addinin musulunci shine gabansa kuma shine addinin gaskiya cikin murna da hanzari badi'atul nauwara ta mike tsaye zumbur da nufin taje tayi shirin tafiya izuwa nahiyar bakaken fata don tunkarar uwar macizai sai kawai sukaji birnin gaba daya ya kama girgiza kasa na neman darewa al'amarin daya razana bokanya ummulkhairi khairi kenan domin ta gane cewa uwar macizai ce ta taso daga karkashin teku saboda tsananin razana bokanya ma nantake jikin ummulkhairi ya fara karkarwa, idanuwanta suka zazzaro tamkar tasha yaji kai atakaice dai batama san sa'adda bawali ya kwace mataba daboda tsananin razana itakuwa sarauniya badi'atul nauwara lokacin da taga wannan masifa ta taso dakinda suke ciki yana neman rushewa saikawai ta bude wannan littafi dake hannun ta ta fara karanta wani wuri da aka jero inda sunayen allah kyawawa suke ta aiyana aranta cewa tana neman taimakonsa Allah mai girma, fara karanto sunayen allah tsarkaka keda wuya a cikin bakin badi'atul nauwara sai aka daina girgizar kasar, komai ya dawo daidai tamkar wani baitaba faruwa ba a birnin al'amarin daya matukar daurewa ummulkhairi kai kenan ta tamu da tsananin mamaki lokacin sarauniya badi'atul nauwara da bokanya ummulkhairi suka fito daga cikin wannan daki suka iso fada sai suka cika da tsananin mamaki bisa abinda suka yi arba dashi da kuma abinda sukaji bakomai suka gani ba face 'yan gudun hijira sama da mutane dubu dari daga sauran makotan birane sun cika fadar suna koke koke wasu sun jikkita sun sami raunika da yawa ajikinsu, suna fadin cewa birninsu ya rushe gaba daya kuma ruwa yaci garin nan dai badi'atul nauwara ta suka akayi bincike sai aka gano cewa birninta ne kadai ba'a sami wannan masifa ba amma ko ina anyi asarar dubunnan ruyuka koda jin wannan batu sai bokanya ummulkhairi taja dogon numfashi tace tabbas addinin musulunci shine addinin gaskiya ya shugabata kiyi sani cewa darajar sunayen ubangijin musulunci da kikayi ta karanrowa dazu shine ya kare birninki daga wannan masifa ta bayyanar uwar macizai lallai yanzu na gamsu cewa addinin musulunci shine addinin gaskiya kece kadai zaki iya kashe wannan mmacijiya don hhaka dolene ki gaggauta yin wannan tafiya inba hakaba kuwa masoyinki dakuma kawarki suna daf da mutuwa dakuma rayukan miliyoyin mutane sannan zaki iyayin hakan idan imaninki g ubangijin musulunci yana nan acikin zuciyarki bai gusheba kodajin haka itama badi'atul nauwara ta maidawa ummulkhairi murmushi cikin kankanin lokaci aka shiryawa sarauniya badi'atul nauwara guzuri akan wani ingarman doki kafin ta tafi saida ta tara gaba daya jama'ar birninta ta basu labarin gaba daya abinda ya faru tundaga lokacin da taje birnin kawarta sarauniya anisa kawo izuwa yanzu koda jin wannan labarin sai gaba dayan jama'ar birninta suka durkushe kasa bisa guiwoyinsu suna masu cewa mun bayarda gaskiya da ubangijin musulunci kodajin haka sai farinciki ya lullube badi'atul nauwara nantake ya dubi ummulkhairi tace kekuma fa menene matsayinki yanzu? ummulkhairi tayi murmushi tace nima nayi imani da ubangijin musulunci nantake badi'atul nauwara ta mikawa ummulkhairi wannan littafi tace inason gaba daya jama'ata ki shigar dasu cikin wannan addini mai girma kuma ki koyar dasu komai na cikinsa nantake badi'atul nauwara tayiwa jama'ar ta sallama sannan ta kama d0kinta ta hau harta yunkura zata tafi sai ummulkhairi ta yi sauri t ruko dokin ta dubeta tace ya shugabata ki zamo mai juriya da hakuri aduk halin da kika tsinci kanki aciki ki sani cewa ubangijin da kikayi imani dashi ayanzu zai jarraba ki da tsananin wuya domin yaga iya karfin imaninki lallai masu hakuri suna tareda nasara koda jin wannan batu sai badi'atul tayi murmushi tace ku tayani addu'ar samun nasara domin kashe wwannan muguwar macijiya ne kadai zaisa gaba daya jama'ar dake nahiyar mu da sauran nahiyoyi suyi imani da wannan addini na gaskiya tana gama fadin haka saita kada linzamin dokinta ta juya da baya tana mai zaburarsa. da gudu ta fice daga cikin birnin gaba daya alokacin da ummulkhairi da sauran jama'ar garin suka bita da kallo tun suna hangota harsaida ta kure musu da gani suka daina hangota yazamana cewa sai kurar dokinta lokacin da sarki shamsal tareda boka daizur suka sami nasarar tsira da rayuwarsu daga cikin tekun da kyar da sidin goshi akan wannan katako saida katakon yayi tafiyar sa'a uku da rabi dasu sannan ya kawo su bakin gabar teku dukkannin su sun galabaita ainun sakamakon tsananin galabaitar da sukayine tasa barci ya sace su basu sani ba ruwa na watsosu bakin gabar tekun sai sarki shamsal ya fara farfadowa daga barcin koda ya bude idanunsa yaga boka daizur nata shara barci bai farkaba ssai nantake dabara ta fado masa yace yauwa yanzu tunda boka daizur bai farkaba zanyi amfani da wannan damar na dauko madubin tsafinsa na duba domin naga halin da kasata take ciki shin wazirina ya ruke mini amanata da nabar masa kuma awane hali dana yarima zainur yake gama aiyana hakan keda wuya sai sarki shamsal ya zura hannunsa acikin aljihun boka daizur ya dauko madubin tsafinsa ya shafeshi da hannunsa na hagu nantake madubin ya nuna masa duk aabinda ya faru tundaga ranar da suka baro kasar da yadda yarima zainur ya shirya juyin mulki ya kashe gaba daya makusantar sarki shamsal ya hada kai da sauran 'yan majalisar yaci gaba da tafiyar da harkokin mulkin son zuciya fiye da wanda yakeyi sannan kuma yazamana cewa sama da mutum dubu hamsin ne suka hallaka sannan kuma rabin gidan sarautar ya ruguje amma yarima zainur da mukarrabansa babu mutumin daya hallaka daga cikinsu koda gama ganin wannan al'amarin sai zuciyar sarki shamsal ya fara tafarfasa kamar zata kone donhaka baisan sa'adda ta kurma uban ihuba karfin ihun nasane ya tashi boka daizu gada barcin da yakeyi boka daizur ya farka afirgice alokacin daya ji kamar kunnensa zai dode ya mike zumbur kafin yayi wani yunkuri sai sarki shamsal yayi wuf ta zare takobinsa ta dora kaifinta akan makoshinsa ya dubeshi jiki na tsuma yace saboda me ka yaudareni kaki gaya mini gaskiyar abinda yake faruwa abirnina? ashe dana yarima zainur yayi juyin mulki ya kashe duk makusantana masu biyayya agareni ba tareda fargabar komaiba boka daizur ya sa hannunsa ya ture takobin sarki shamsal daga wuyansa ya dubeshi afusace yace wanene ya gaya maka cewa ana hada gudu da susa duka alokaci daya ai sai ayi biyu babu masifar dake gabanka ta wannan yaro tafi ta barnar da danka....... TARKON MUTUWA PART 8 F yace saboda me ka yaudareni kaki gaya mini gaskiyar abinda yake faruwa abirnina? ashe dana yarima zainur yayi juyin mulki ya kashe duk makusantana masu biyayya agareni ba tareda fargabar komaiba boka daizur ya sa hannunsa ya ture takobin sarki shamsal daga wuyansa ya dubeshi afusace yace wanene ya gaya maka cewa ana hada gudu da susa duka alokaci daya ai sai ayi biyu babu masifar dake gabanka ta wannan yaro tafi ta barnar da danka yayi maka tunda aduk sa'adda ka koma gida zaka iya gyara duk barnar da yayi maka ka dawo da komai daidai kamar yadda ka tafi ka barshi amma idan kayi sakaci wannan yaro hatyan ya tsira da rayuwarsa to kanaji kana gani zaizo har masarautarka yacika da yaki kuma yayi maka kisan gilla koda jin wannan batu sai gardama ta karke atsakanin sarki shamsal da boka daizur sukayita gardama da cacar baki har ran sarki shamsal ya baci baisan sa'adda ya fusata ba ainun ya shammaci boka daizur ya gabza masa naushi a wuya saboda karfin naushin saida boka daizur ya kife kasa sumamme ko motsin kirki baiyiba sai kawai sarki shamsal ya juya ya nufi hanyar da zata kaishi birnin sa yabar boka daizur akwance agabar teku tamkar gawa sarki shamsal baisan sa'adda ya rinka falfala guduba acikin daji yana sauri burinsa kawai shine yaga ya isa birnin sa domin ya kawar da bakin ccikin zuciyar sa abinka da wanda ya saba shafe kawanaki yana gudu saigashi tafiyar tasa tanayin sauri burinsa kawai shine yaga ya iso birninsa saiya gaji ainun sannan yake tsayawa ya huta ko ya yada zango hakadai yaci gaba da wannan gudu ba sassauci har tsawon kwanaki sannan ya fara hango birninsa daga can nesa al'amarin daya sa ya kara aimi kenan domin ta iso ashirinsa kai tsaye kawai kai tsaye zai wuce izuwa fadarsa kuma yana isa zai hau dakarunsa da sara da suka daduk wanda ya baiwa yarima zainur goyon baya yayi juyin mulki sannan ya kamo yarima zainur din yayi masa kisan gilla agaban kowa domin sauran 'yan majalisar tasama susan cewa ba sassauci ga duk wanda ya bada hadin kai awannan juyin mulki da akayi alokacin da baya nan koda sarki shamsal ya iso kan wata gada wacce akayita asaman wani rami mai zurfi wanda dagashi sai kofar shiga birninsa ya ci gaba da gudu akan gasar tamkar zai tashi sama yana isowa tsakiyar gadar ne yaji birnin gaba daya ya kama girgiza aikuwa sai gadarma ta fara tangal tangal zai fado kasan ramin saiyai wuf ya cafo gadar ya fara reto akan gadar alokacin da akaci gaba da yin girgizar kasar itama gadar ta kama rawa tana reto tana neman fadowa kasa cikin ramin al'amarin daya dugunzuma hankankalin sarki shamsal kenan domin ya fahimci cewar duk ma abinda ke faruwa uwar macizai ce ta sake motsawa idan kuwa taci gaba da motsi to yanaji yana gani zai mutu akasan wannan rami ba tareda yaje tayi abinda yazo yiba koda ayyana hakan sai takaici da nadama suka kamashi yace aransa yanzu dai gashi nida kaina na taso abinda zai zama ajalina gamida rushewar duniya gaba daya kawai saboda son zuciyata da son rayuwar duniya tabbas zanyi biyu babu inda na dauki shawarar boka daizur ban taho nan ba da yanzu san iya saka shi ya tsayar da uwar macizai koda sarki shamsal yazonan atunaninsa sai hankankalinsa ya sake dugunzuma saboda asannan ne ya tuna cewa ai bayan ya gama duba madubin tsafin na boka daizur cikin ruwa ya cillashi koda boka daizur ya farfado daga suman da yayi sakamakon naushin da yayi masa bazai iya tsayarda uwar macizai ba wɑɳɳɑɳ รɦiɳɛ ɑɓiɳɗɑ yɑ Բɑʀu gɑ รɑʀki รɦɑɱรɑʆ ɓɑyɑɳ yɑyi kuรkuʀɛɳ รɑɓɑwɑ uɱɑʀɳiɳ ɓѳkɑɳรɑ LIKE AND COMMENT IS OUR ENCOURAGEMENT . Anan muka kawo karshen littafi na takwas 8 In Allah ya kaImu gobe zamu dora da na tara 9. TARKON MUTUWA BOOK 9 A Acan birnin su yarima nasmal kuwa bayan su hatyan sunci sun sha saiduk su biyun barci ya sacesu saboda gajiyar tafiya yammaci nayi sai suka ji an kwankwasa musu kofar dakin da suke ciki karar kwankwasa kofar ce ta tashesu suka farka hatyan ya mike daga kwance yana hamma mai nuna alamar cewa barcin bai ishshi ba yaje ya bude kofar yarima nasmal ne atsaye akofar fuskarsa cike da murmushi ya dubi hatyan yace kai kadai ake jira afara wannan gasa don haka sai kayi hanzari ka fito mu tafi kodajin wannan batu sai hatyan ya juyo da sauri ta dubi sadirat yace tashi ki kimtsa, lokacin zuwa filin gasa yayi kafin sadirat ta mike daga kan gadon da take kwance tuni hatyan ya fada cikin kewaye domin yayi wanka awannan lokaci sadirat na cikin mayafi alullube kawai sai taga yarima nasmal ya shigo cikin falon tana ganinsa saita murtuke fuska tace bai kamata ka shigo mana dakiba ayanzu, shin zaka iya fita daga waje kodajin haka sai nasmal ya juya mata baya yace ki gafarceni kanwata dama nazone domin cika umarnin sarki amma burina shine kema ki shirya kiyi sauri domin mu tafi izuwa filin gasar da wuri tareda ku nasmal na gama fadin haka saiya juya ya fice daga cikin falon Fitarsa keda wuya sai itama sadirat ta mike da sauri takama shiri cikin kankanin lokaci suka gama kimtsawa hatyan da sadirat suka fito daga cikin masaukinsu suka jera tareda yarima nasmal suka fice daga cikin gidan sarautar gaba daya suka nufi inda filin gasar yake tun daga nesa suka dinga jiyo hayaniyar dumbin jama'a acan filin gasar alamar cewa filin gasar ya cika dam da jama'a filine makeke mai matukar tsawo da fadin gaske wanda ya kewaye birnin gaba daya, tsaitsaye afilin gasar kuwa jaruman gasar mutum shida kacal wadanda suka kasance zabga zabga samari matsafa kuma majiya karfi boka aimar na tsaye atsakiyarsu kuma shi ne mafi tsawo da kwarjini acikinsu agefe daya bisa wasu kujeru na alfarma sarki ne da fadawansa akewe da filin gasar kuwa sarki ne da sauran jama'ar garin mazansu da matansu anata kace nace kowa ba fadin albarkacin bakinsa akusa da jaruman gasar kuwa wata katon keji ne wanda ke dauke da wata katuwar dabba ce wacce ba'a iya ganinta saboda gaba daya kejin arufe yake amma ana iyajin gurnaninta mai matukar ban tsoro ko yaya dabbar ta motsa acikin kejin sai aji kamar kasa na motsi saboda nauyin takun sawayenta koda jama'a suka hango jarumi hatyan sun durfafo filin gasar sai suka rude da shewa gami da tafi shi kuwa boka aimar yana ganin yarima nasmal dafda sadirat sun jero tareda hatyan na hagunsu sai ransa ya baci yaji kamar yaje ya janye sadirat daga kusa dashi harsai da suhatyan suka iso tsakiyar filin gasar suka tsaya cannon jama'a sukayi tsit aka daina yi musu ihu da jinjina hatyan da nasmal suka rissina ga sarki da 'yan majalisar sa suka kwashi gaisuwa sarki ya karbi gaisuwar tasu itakuwa sadirat tuni awannan lokaci sarki yasa ankaita gareshi ta zauna bisa karadarsa daf dashi bayan sarki ya karbi gaisuwar su hatyan saiya mike tsaye daga kan karagar tasa ya fara bayani alokacin da filin gasar yayi tsit kamar mutuwa ta gifta sarki yace yaku jama'ata kun sani cewa tsawon shekaru muna jiran zuwan wannan rana domin munsan da tasowar annobar uwar macizai bisa binkicen da matsafan mu sukayi wanda zai iya karemu daga sharrin wannan masifar ta uwar macizai bakone bai kasance daga cikin muba WANNAN WAJEN AN SAMI TSALLAKE DAGA NA'URAR BUGA LABARIN bugu da kari shi wannan maciji namu bincike ya nuna cewa yafi dabba kurzal karfin gudu da karfin damtse kowa ya sani cewa awannan nahiya tamu gaba daya ba'a taba samun jarumin da yafi dabba kurzal karfin gudu da karfin damtse ba amma wadannan jarumai guda takwas dake cikin filin wannan gasar ba'a taba jarraba karfin gudunsu ba dana damtsensu ba akan wannan dabba kurzal ba kuma dukda cewa an tabbatar da cewa sun cika jarumai ababan kwatance bisa wannan daliline muka shirya wannan gasa domin mu ga iyakar kwazonsu kuma mu gane ko wannan bakon jarumin zai iya lashe gasar to shine zamu dada tabbatar da cewa zai iya karemu daga sharrin uwar macizai yanayin wannan gasa shine za'a bude wannan dabba kurzal ta fita da gudu jaruman gasar zasu kasa tsere da ita acikin wannan katon fili duk wanda ya risketa kafin ta isa kusurwa harya iya ruketa ya kamata da kokawa ya kaita kas shine ya lashe wannan gasa tsakanin da yarima nasmal da kuma babban bokanmu mai daraja aimar duk wanda ya sami nasara zan bashi damar ya zabi duk macen da yakeso awannan fili a aura masa ita koda jin wannan batu sai gaba daya jama'a suka hau shewa itakuwa sadirat sai hankalinta ya tashi sakamakon jin wannan jawabi bisa cewa aimar d nasmal zasu iya zabarta idan har suka lashe wannan gasar shin hakan yana nufin kenan za'ayi mata auren dole kenan ko ba zabinta bane? tana cikin yin wannan tunanine kawai saita jiyo karar bude kejin dabba kurzal aikuwa kurzal na dira da kafafunta sai gaba daya birnin yayi girgiza saboda nauyin sawayenta kurzal nayin arba da ruwan jini acan kusurwar karshe saita falafala da azababben gudu izuwa wajen ba shiri suma jaruman gasar suka bita aguje domin su risketa nanfa aka kasa mugun tsere atsakanin dabba kurzal da jaruman gasar amma sai ga shi dabba kurzal ta basu tazara mai yawa an rasa wanda zai cimmata jarumi hatyan ne akan gaba sai boka aaimar da yarima nasmal wadanda ke biye dashi kuma ajere suke ma'ana sunyi kunnen doki akarfin gudun nasu koda sukaga hatyan yadan basu tazara mai yawa ta kimanin taku goma sai hankankalinsu ya tashi suka kara zage damtse wajen gudunsu domin su cimmasa amma sai abu ya gagara aikuwa ragowar jaruman gasar mutum biyar tuni ma sun sare har wasuma sun fara faduwa koda aka shafe 'yan dakiku ana gudun sai yazamana cewa tsakanin hatyan da dabba kurzal bai wuce taku ukuba sai filin gasar ya rude da shewa gami da tafi sadirat kuwa batama san sa'adda ta mike tsaye ba tana daka tsalle sama don murna da farinciki bisa ganin yadda dan uwanta keneman lashe gasar aikuwa sai gani akayi hatyan ya dako tsalle asama ya dira akan wuyan dabba kurzal ya kama kahonninta biyu ya ruke ya fara kokarin tsayarda ita aikuwa sai ya kasa tsayarda ita dukda cewa kafafunsa sun taba kasa suna turjiya acikin kasa suns tayar da kura adaidai wannan lokacine nasmal da aimar suka zuba idanu domin saga yadda zata wakana tsakanin hatyan da dabbar suma su sarki da sauran jama'ar suka kame kamar gumaka suka zuba idanu suna kallon ikon allah nanfa hatyan da kurzal sukaci gaba da kokawa yana kokarin ya kayar da ita ita kuma tana kokarin turmusheshi kota sokeshi da kahonninta amma ta kasa saida suka shafe kusan rabin sa'a suna wannan artabun anrasa wanda zai sami nasara akan wani awannan lokaci ne dabba kurzal ta shammaci hatyan ta zura kanta akarkashin kafafunsa aikuwa saita dagashi sama tayi wurgi dashi acan gefe daya yafada kan karfen da yake kewaye da filin gasar bayansa ya bugu sosai ya baje kasa ya kasa mikewa koda ganin haka sai sadirat ta firgita ta mike tsaye zumbur ta kurma uban ihu kuma ta falfala da azababben gudu izuwa cikin filin gasar ta isa kan hatyan ya fara dudduba shi cikin rudewa boka aimar da yarima nasmal kuwa sai suka afkawa dabba kurzal suka fara kokarin turmusheta da dukkan karfinsu amma sai abu y gagara sai gashi tana makesu suna faduwa kasa Ita kuma tana kokarin hallaka su al'amarin daya firgita kowa kenan afilin har sarki ya bayarda umarnin dakaru su hallaka dabba kurzal sai kawai akaji birnin gaba daya ya fara girgiza kafin a ankara gidaje sun fara rushewa kasa kuma ta fara tsagewa mutane da komai na ruftawa cikin ta nanfa mutane suka dimauce filin gasar ya hargitse mutane suka kama guje guje da iface iface kwatsam sai akaga kan uwar macizai ta leko tsakiyar filin gasar tamkar daga can kololuwar samaniya aka zuroshi al'amarin daya matukar firgita kowa kenan nantake uwar macizai ta fara shakar numfashi tana neman inda hatyan da sadirat suke koda ta hangosu acan tsakiyar filin gasar sai ta saki wuyanta ya tafi izuwa garesu sululu……… tamkar an harbo kibiya koda kan nata yazo dafda su sai ta wangame katon bakinta wanda fadinsa yakai kamu dari shida zurfinsa yakai rijiya gaba dubu da nufin ta hadiyesu koda hatyan da sadirat sukaga abinda ke shirin faruwa sai suka rusa ihu cikin tsananin razana domin sungama saddakar da cewa sun mutu Kwatsam ba zato ba tsammani sai suka ga badi'atul nauwara ta dako tsalle sama tamkar acikin baka aka harbata sai gani akayi kawai ta gabzawa uwar macizai wawan naushi akan tsakiyar kanta tana mai kwalla kabbar kuma ta dira akan wuyan ta saboda karfin naushin saida hannun badi'atul nauwara ya lume acikin kan badi'atul nauwara ta zaro hannunta daga cikin kan uwar macizai saiga jini yana tsiri a sama tamkar idanuwar ruwa ta balle kawai sai gani sukayi jikin uwar macizai ya lagube kasa ya fadi a lokaci guda tamkar giwaye dubu ne suka bude ne suka fadi alokaci guda hakanne yasa wasu gidajen birnin suka sake rugujewa suka bace koda ganin abinda ya faru sai sarki da dukkanin sauran jama'ar garin sukazo gaban sarauniya badi'atul nauwara sukayi mata sujjada saboda su azatonsu wata ubangijiyace ta sauko domin ta kawo musu agaji hatyan da sadirat kuwa koda sukaga ashe sarauniya badi'atul nauwara ce ta kawo musu wannan dauki sai suka rugo izuwa gareta cikin tsananin mamaki da farinciki suka rungumeta suna masu yi mata godiya har izuwa wannan lokaci gaba daya mutanen birnin basudago da kawunansu ba daga sujjadar da sukayiwa badi'atul nauwara ba badi'atul nauwara tayi gyaran murya sannan tace niba ubangiji bace bakasance mutum kamar ku sunana sarauniya badi'atul nauwara kuyi sani cewa nasami nasarar kashe wannan macijiyar ne d taimakon ubangijin musulunci wanda shine ya halicci mutum da aljan shine yayi sammai da kassai da duk abinda yake tsakaninsu komai da kowa yana karkashin mulkinsa tun farkon haduwata da jarumi hatyan da 'yar uwarsa na tausaya musu bisa masifar da suka shiga nandai sarauniya badi'atul ta kwashe labarin duk abinda ya faru abaya ta zaiyanewa mutane tun daga lokacin data fara zuwa birnin bindal sa'adda tayi bad da dakama kuma ta rufe fuskarta amatsayin... TARKON MUTUWA BOOK 9 B badi'atul nauwara tayi gyaran murya sannan tace niba ubangiji bace bakasance mutum kamar ku sunana sarauniya badi'atul nauwara kuyi sani cewa nasami nasarar kashe wannan macijiyar ne d taimakon ubangijin musulunci wanda shine ya halicci mutum da aljan shine yayi sammai da kassai da duk abinda yake tsakaninsu komai da kowa yana karkashin mulkinsa tun farkon haduwata da jarumi hatyan da 'yar uwarsa na tausaya musu bisa masifar da suka shiga nandai sarauniya badi'atul ta kwashe labarin duk abinda ya faru abaya ta zaiyanewa mutane tun daga lokacin data fara zuwa birnin bindal sa'adda tayi bad da dakama kuma ta rufe fuskarsta amatsayin bafatakiya ta sauka agidan makeri satyan koda jin wannan labari sai jarumi hatyan ya kamu da tsananin mamaki cikin matukar sanyin jiki hatyan ya tako d kafafunsa ya taso daga inda yake ya zo har inda badi'atul nauwara ke tsaye yazo daf da ita ya kura mata idanu yana mai nunata da dan yatsa guda yana murmushi amma kuma ya kasa cewa komai koda ganin haka sai badi'atul nauwara tayi murmushi tace shin bakaine kace duk inda ka sake ganina ba sai ka shaida ni ba? kafin ni na shaidaka kai meyasa yanzu ka kasa shaida ni? kodajin wannan tambaya sai dariya ta kwacewa hatyan yace tabbas kin shammaceni amma ki sani cewa abaya duk sa'adda na hada idanu dake sai zuciya ta ta buga kamar zata tsage nakanji ajikina kamar kece wadda begenta da tunaninta suke ta faman ruri acikin zuciyata tabbas so guda daya ne kuma kece abar sona yau na bayyana miki sirrin zuciya ta shin kema kinajin irin wannan acikin zuciyar ki kamar yadda nakeji araina? sa'adda sarauniya badi'atul nauwara taji wannan ttambaya sai tayi dan guntun murmushi tace yanzu ba lokacin soyayyabane domin akwai gagarumin aiki agaban mu ka sani cewa kashe wannan macijiya baya nufin duniya zata zauna lafiya domin abune mai matukar wuya ga sarakunan duniya su karbi wannan sabon addini da nazo dashi acikin ruwan sanyi bani da sauran kwanciyar hankali face naga wannan addini na musulunci ya sami karbuwa ako'ina acikin manyan biranen duniya yanzu zan tuntubi sarkin wadannan mutane domin naji ra'ayinsu bisa bayanin da nayi musu lokacinda badi'atul nauwara tazo nan aazancent sai mamaki ya kama hatyan yace wai shin yaya akayine kika iya yarensu yarima nasmal haka ? kodajin wannan batu sai badi'atul nauwara tayi murmushi tace koya nayi kamar yadda kaima ka koya awajen sarkin mafarauta na garinku kodajin haka sai mamaki ya turnuke hatyan yyac yanzu dama sarkin mafarauta yana raye kuma kinsan labarin sa? badi'atul nauwara tace ba wai labarin kadai na sani ba kuma inayi maka albishir da cewa sarkin mafarauta yana nan araye bai mutuba lallai ya tsira da rayuwarsa alokacin da sarki shamsal ya jefoshi daga rami mai zurfi na sadu dashi harya kaini inda kabarin iyayenka suke na ziyarcesu koda jin wannan batu sai hatyan ya sake kamuwa da tsananin farinciki itakuwa sadirat batasan abinda hatyan da badi'atul nauwara suke tattaunawa ba saboda acikin yaren su yarima nasmal suke tattaunawa hatyan ya dubi badi'atul nauwara cikin kaguwa yace yanzu ina zamuje naga sarkin mafarauta? badi'atul nauwara ta numfasa tace ya boye kansa a inda babu wani mahaluki da zai iya ganinsa kuma nayi masa alkawarin bazan kai kowa wajenba sai bayan komai ya lafa ma'ana ka dauki fansa akan sarkinm shamsal da dansa yarima zainur ka kawar da zalunci abirninku ka shimfida zaman lafiya yanzu dai mu karasa wajen wannan sarkin muji ra'ayinsa shin yayi amanna da wannan addini da nazo musu dashi yanzu kodajin wannan batu sai sarki ya yafuto nasmal da hannu yazo gareshi sannan ya kwashi gaisuwa sannan nasmal ya dubi sarki cikin nutsuwa yace yakai abbana da idonka kaga abin al'ajabin daya faru wanda tun kuna kanana kukejin labarinta masana da masu binkice sun tabbatar d cewar babu wata dabba maigirmanta da karfinta kuma acikin sa'o'i kadan ita kadai zata iya hallaka duniya baki daya amma gashi acikin dakiku kadan sarauniya badi'atul nauwara ta hallakata bisa taimakon ubangijin musulunci lallai kuwa ashe ubangijin da ya iya hallaka wannan macijiya shine ya halicceta wanda kuma shine ya halicci komai da kowa shin yanzu kaima kayi imani dashi? kodajin wannan tambayar sai sarki ya numfasa yana mai gyada kai sannan yace nayi imani da ubangijin musulunci dari bisa dari kawai sai ya dubi jama'arsa gaba daya nantake dukkan jama'ar birnin suka budi baki sukace muma munyi imani da ubangijin musulunci nantake farinciki ya lullube badi'atul nauwara hatyan, da sadirat da boka aimar da yarima nasmal ma sukazo sukayi mubaya'a sarki ya mike tsaye ya tako da kafafunsa yazo har gaban sarauniya badi'atul nauwara ya dubeta yace yake wannan wannan sarauniya mai daraja dolene ayi miki jinjina domin kinyi jarumtakar da har duniya ta kare baza'a mance dakeba amma ki sani cewa kashe wannan macijiya ba shine karshen zalunci ba a duniya akwai manya manyan sarakuna masu girman kai da tsatstsauran ra'ayi wadanda suka tsani musulunci da ma'abotansa fiye da yadda suka tsanin mutuwarsu ki sani cewa fiye da shekaru arba'in baya muna da tarihin wannan addini ayanzu haka akwai littattafai na ilimin addinin ajiye kuma aboye acikin gidan tarihin kasarnan amma saboda kakannin mu basuyi imani dashi ba shiyasa bama kulawa dasu ayanzu da mukaga zahiri da idanunmu kuma mukayi imani dashi dolene mu zakulosu muyi aiki dasu don mu bautawa ubangijin musulunci ni. yanzu shawarar da zan baki itace kisa ayanko kan uwar macizai a fede shi ya bushe ki tafi dashi izuwa nahiyarku duk kasar da kikaje dolene sarkinsu da bokayensu suyi imani da wannan addini na gaskiya duk wadanda kuwa suka bijire miki ki yakesu domin kafa mulkin adalci babbar gudunmawata agareki itace zan debo zakwakuran mayakana guda dubu arba'in na baki ki tafi dasu izuwa birnin sarki shamsal saboda nasan

Chapter 10 of 11