Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 11
kuci zarafin kowaba acikin wannan birni nawa koda kuwa bawane mara 'yancin kansa ku sani sarki shamsal ya amince da wannan sharadin don haka duk wanda ya sabashi acikinku zai fuskanci hukunci mai tsanani kodajin wannan batu sai shugaban hadiman tsoho lamiz ya ciza lebensa cikin alamun takaici bai san sa'adda zancensa na zuci ya fito fili ba yace wannan shine kuskure na biyu da sarki shamsal ya tafka tsoho lamiz yayi dan tunani na tsawon yan dakiku kadan sannan ya dubi sarauniya anisa yace kafin mu shiga kowanne sako da lungu na wannan gidan sarauta don gabatar da namu binciken munaso kisa a tara gaba dayan bayi hadimai da barorinki awancan babban fili na wannan gida munaso suyi layi sahu sahu na maza daban na mata daban domin mu fara aikinmu akansu kodajin wannan batu sai anisa tayi murmushi tace wannan mai sauki ne nan take anisa ta kirawo sarkin dogarai ta bashi wannan umarni kafin cikar sa'a daya an gama tara wadannan hadimai acikinsu kuwa harda sarauniya badi'atul nauwara wacce tafito amatsayin baiwa bakar fata sanye da tufafi irin na bayi wulakantattu awannan lokaci badi'atul nauwara na kan gaba alayin farko kuma acikin jerin bakaken fata ta saje dasu babu yadda za'ayi mutum ya gane cewa ita baiwace lokacin da tsoho lamzis ya durfafi inda badi'atul nauwara ke tsaye sai zuciyarta ta kama daka domin ji take kamar lallai sai ya ganeta tundaga nesa ya kura mata idanu ya nufota gadan gadan harya iso daf da ita amma kuma saiya wuceta ya dubi ta kusa da ita yayi mata tambayoyi sannan ya kara gaba har suka gama binciken gaba daya barori da bayi bai sake dawowa kan badi'atul nauwara ba adai dai wannan lokacin akaji an buga tambari ashe sarki shamsal ne ya shigo cikin wannan babban fili tundazu ya farka daga barci amma sai daya gama kintsawa sannan ya fito kai tsaye sarki shamsal ya taho inda tsoho lamzis ke tsaye da zuwansa sai tsoho lamzis suka russina agareshi suka kwashi gaisuwa sannan ya dubesu cikin fara'a yace aikinku yayi kyau naji dadi danaga zuwanku kun fara gabatar da aikin shin yanzu kun kammala da wadannan hadimai ne? dajin wannan tambaya sai tsoho lamzis ya girgiza kai yace a'a bamu gama da suba saura baiwa guda daya wacce nake zargi akanta kuma nakeson nayi mata tambayoyi sarki shamsal ya ce wannan babu laifi kuci gba da aikinku nizan koma masaukina idan harkun gama gano abinda muke nema a aika min da sauri nazo lamzis ya rissina yace angama ya shugabana nantake sarki shamsal ya koma masaukinsa shikuwa tsoho lamzis saiya fito da badi'atul nauwara da hannunsa ya kirawota ta nufo inda yake tsaye zuciyarta tana daka ita kuwa sarauniya anisa wacce take zaune acan gefe daya bisa wata kujerar mulki ranta ne ya baci ta murtuke fuskarta kuma ta dora hannunta guda daya akan kufen takobinta jira kawai take taga asirinta ya tonu ta dau mataki awannan lokaci tsohuwa ummulkhairi tana zaune daf da ita a hannun damanta kawai sai ummulkhairi ta dafa hannun sarauniya anisa suka hada idanu tayi mata murmurshi gami da kada kai alamar cewa ta kyantar da hamkalinta lokacin da badi'atul nauwara ta iso daf da tsoho lamzis saita zube kasa bisa guiwoyinta saboda yasan cewa babu yadda za'ayi sarauniya ta durkisa masa tabbas tunda yaganta ya lura da tsawon ta da kwarjininta irin na badi'atul nauwara acan asaninsa badi'atul nauwara tana can birninta to tayaya za'ace harta rigasu isowa nan alhalin ita bata tsafi kuma tsafi baya tasiri akanta abinda baisaniba shine akwai hikimar da akayi waccan badi'atul nauwara dasuka gani ba gaskiya bace wata baiwace matukar kama da badi'atul nauwara afuska datsawo amma siffofin jikinsu sun banbanta aiun bayan badi'atul nauwara ta durkusa agaban tsoho lamzis a tsakaninta na bakar fata tana mai sunkwui dakai kasa saiya dubeta yace dago da fuskarki ki kalleni ba tareda wata gardamaba kuwa saita dago kai ya kura mata idanu nantake zuciyarsa ta sake karaya domin badi'atul nauwara daya sani kwayar idanunta fararene kal ! wannan kuwa bakine sannan waccan tana da yalwar gashin gira wannan kuwa dan kankanine abinda bai sani ba shine dattijuwa ummulkhairi ce tayi aikinta ta sanya wani abu acikin idanun badi'atul nauwara wanda ya maida su bakake kuma ta rage tudun gashin girarta tsawon 'yan dakiku lamzis yana nazari da mamaki sannan ya dubeta yaja num faa shi ya dubeta yace tsawon shekara nawa kenan kike bauta awannan gidan sarauta? cikin wata irin kakkausar murya badi'atul nauwara ta budi baki tace tun zamanin sarki dainus mahaifin sarauniya anisa aka kamo mahaifiyata awajen yaki alokacin inada shekaru hudu kodajin wannan batu acikin wannan kakkausar murya sai jikin tsoho Lamzis ya karayin sanyi ya dubeta yace tashi ki tafi banida sauran zargi akanki hakadai su tsoho lamzis sukaci gaba da bincikensu sai da suka shiga ko ina acikin gidan sarautar amma basuga su hatyan ba akarshene suka dudduba bayan gari ko zasu ga sawun kafa kona doki mai nuna alamar cewa basu ganiba bayan sun kammala wannan bincikene sai tsoho lamzis ya kadaìta dasu sarki shamsal amasaukinsa ya dubesu cikin nutsuwa yace ya shugabana babu ta yadda hatyan da 'yar uwarsa zasu iya ratsa wadannan birane har su fice daga cikin nahiyarnan tamu ba face da taimakon wasu daga cikin sarakunan mu da kuma bokayenmu ayanzu nagamsu cewa basu sami nasarar hakkaba da karfin tsafiba lallai akwai masu mulkin dasuka munafirceka sukayi amfani da tsananin hikimarsu da basirarsu wajen boye wadannan makiya naka ina ina mai tabbatar maka da cewa a yanzu su hatyan da yar uwarsa sun shiga wata nahiyar don haka sai kai tunani kaida bokanka kusan irin matakin daya kamata ku dauka, mu kam munyi iya yinmu babu sauran abinda zamu iyayi......... yauwa sai wani jikon idan baku gajiba munci gaba TARKON MUTUWA Littafi na Shida 6 Part 6 C . . Koda tsoho lamzis yazo nan azancensa sai zuciyar sarki shamsal ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda tsananin fushi don haka sai ya takarkare ya kwarara uban ihu dakyar boka arzur da tsoho lamzis suka rarrasheshi ya dawo cikin hayyacinsa sannan tsoho lamzis ya dubi boka arzur yace yanzu saikayi bincike ka gano inda su hatyan suke ayanzu kusan abinda zakuyi kodajin haka sai zuciyar boka arzur ta buga da karfi tsoro ya da baibayeshi saboda yasan cewa tsafinsa yaki yayi tasiri awannan birni kuma bai gayawa sarki shamsal gaskiyar al'amarin ba adai dai wannan lokaci dasu sarki shamsal sukeyin wannan tattaunawa ne sarauniya anisa ta dauki sarauniya badi'atul nauwara tareda dattijuwa ummulkhairi ta fitar dasu daga cikin birnin gaba daya ta wata barauniyar hanyar daban wacce tasa aka basu dawakai da guziri suka nausa daji suna masu tunkarar birnin sarauniya badi'atul nauwara kafin suyi bankwana saida badi'atul nauwara ta dubi sarauniya anisa cikin alamun tsananin damuwa gami da karayar zuciya tace yake kawata hakika bansan irin godiyar dazan miki ba bisa hadin kan da kika bani wajen kubutar da wadannan marayu wato hatyan da yar uwarsa sadirat babu abinda zance sai fatan alheri agareki idan baki mantaba abaya kince dani nayi tunani akan yadda zamu dinga bawa su hatyan kariya bayan sunbar wannan nahiyar har izuwa lokacinda hatyan zai iya dawowa ya dauki fansa akan sarki shamsal nikam banyi tunanin komaiba akan hakan amma nasan cewa ke tuni kinyi kuma kinyi shiru akan hakan saboda haka nabar miki amanar hatyan kodajin haka sai mamaki ya turnuke anisa tayi shiru kamar bazata ce komaiba daga chan kuma sai ta dubeta tace bazan iya karbar wannan amanarba face kin amsa tambayar danayi miki abaya cikin matukar kaduwa badi'atul nauwara tace wace tambaya kenan? anisa tace shin kin kamuda son jarumi hatyan ne? badi'atul nauwara tayi ajiyar numfashi tace saboda me kikayi mini wannan zargin kuma me yasa kike son sani? anisa ta sake yin murmushi tace saboda me zaki amsa mini tambaya ta da tambaya? badi'atul nauwara ta kada kai tace mubar wannan maganar yanzu kawata kije ki aiwatar da duk abinda kike ganin cewa ya kamata tana gama fadin hakan saita kada linzamin dokinta ta juya ta nausa cikin daji cikin hanzari ummulkhairi ta kada na ta dokin da sauri ta bita abaya ita kuwa sarauniya anisa hankalintane ya dugunzuma tabi badi'atul nauwara da kallo saboda tabbas yanzu ta tabbatar da abinda take zargi wato babu makawa kawarta ta kamu da son saurayin da fiyeda shekaru shida da suka gabata ita ta kamu da tsananin sonsa nantake tafada cikin kogin tunani………….. soyayyar sarauniya anisa ga jarumi hatyan ta samo asaline tun kimanin shekaru shida da suka shude wata rana sa'adda tayi badda kama ta shiga birnin bindal amatsayin yar kasuwa suna shiga cikin birnin sai keken dokinsu ya sami matsala yazamana cewa wilin tayar keken ya karye nan take aka basu shawara sukai gidan sarkin makera a gyara musu batare da bata wani lokaciba akayi musu jagora izuwa gidansu jarumi hatyan awannan lokaci anisa ta lullube gaba daya jikinta da wadansu bakaken tufafi masu kauri kuma ta rufe fuskarta da wani bakin kyalle mai dan shara shara idanunta kadai ake iya gani da isarsu sarauniya anisa kofar gidansu jarumi hatyan sai sukaga mahaifinsa a zaune acikin makera yanata aiki itadai sarauniya anisa sai tayi zamanta acikin keken doki hadimanta guda hudu da suke tareda ita sai suka sauko sukaje wajen baban hatyan suka sanar dashi matsalarsu nan take sarkin makera yaje ya duba wilin tayar daya karye sannan ya dubi shugaban hadiman yace nawa zaku biya na sauya muku wannan taya da wadda ta fita kwari wacce zata iya shekara goma nan gaba ba tarda ta sami matsalaba? kodajin wannan tambayar sai hadimin ya juya ya dubi sarauniya anisa don yaji ra'ayinta kawai sai tayi murmushi tayiwa hadimin magana cikin yaren kurame hadimin ya juyo ya dubi sarkin makera yace uwargidana tace tanaso ka sauya mata gaba daya tayoyi hudun kuma ka fadì nawa kake bukata zata biyaka kodajin wannan batu dai mamaki ya turnuke sarkin makera yace aransa duk yadda akayi wannan mata ba 'yar kasuwa bace wadda ta saba juya taro da sisi domin shi dan kasuwa baya kashe kudi haka sai dai basarake sarki makera ya dubi hadimin yace ku biyani dinare dari uku hadimin ya dubi sarauniya anisa ita kuma saita yi masa inkiyar ta yarda kawai sai hadimin ya bude jaka ya fiddo dinare mai yawa ya kirga dinare dari ukun ya baiwa sarkin makera sarki makera ya dubi yaransa biyu dake faman aiki acikin makera wadanda suka kasance samari masu karfi yace kuzo ku kwance tayoyin keken dokin nan domin a daura sababbi ba tareda bata wani lokaciba sai kartin biyu suka debo kayan aiki suka fara kokarin kwance notikan da suka daure tayoyin amma sai notikan sukaki kwantuwa saboda dukkansu sunyi tstasa tuni awannan lokaci anisa ta sauko daga kan keken dokin ta koma gefe daya ta zauna tana kallon abinda yake faruwa nan fa wadannan katti suka gaji ainun batareda sun iya kwance koda noti dayaba al'amarin daya ya bai wa kowa mamaki kenan awajen shikuwa sarkin makera sai yazo ya dudduba keken dokin ya kare masa kallo tsaf sannan ya dubi anisa yace ranki ya dade amma wannan keken dokin a birnin sin aka siyoshi ko? cikin mamaki babban hadimin ya dubi sarkin makera yace yaya akai ka sani? sarkin makera yayi murmushi yace ai babu wata babbar kasa aduniya wacce banje cikinta na koyi aikin kiraba wadannan yara nawa basu da karfin da zasu iya kwance notin birnin sin amma akwai wani yarona guda daya zai iya yanzu baya nan amma yana daf da dawowa kodajin wannan batu sai mamaki ya kama anisa ta kirawo babban hadimanta tayi masa rada akunne sannan ya dawo wajen sarkin makera yace uwargidana tace idan her yaron naka yazo ya iya kwance tayoyin wannan keken dokin zata baka ninki uku na kudin gyaran da zata biya yanzu idan kuma ya kasa kwancewa to ita zata kwance da kanta, amma ba zata baka ko sisi ba a kudin gyara da kayi ba tareda shakkar komai ba sarkin makera yayi murmushi yace nayarda da wannan sharadi gama fadin hakan keda wuya saiga jarumi hatyan ya dawo daga farauta yana sanye da wata tsohuwar riga wacce ta matseshi sosai awannan rana ya fafata yaki da wani murgujejen zaki adaji dakyar ya kasheshi kuma zakin yayi masa wani rauni guda daya agadon bayansa tundaga nesa hatyan ya karewa kowa kallo tsaf akofar gidan nasu koda yaga wadannan yaran mahaifinsa guda biyu atsaye agaban keken dokin suna ruke da kayan aiki sun hada zufa saiya gane abinda ke faruwa tun kafin ya iso gurin ya karewa anisa kallo domin ya gano budurwace ko babbar mace amma saiya kasa tunda arufe jikinta yake da tufafi masu kauri kuma ta rufe fuskarta da isowarsa ko kala baice da kowa ba saiya karbi abin kwance notin daga hannun daya daga cikin kattin biyu ya fara kokarin kwancewa dafarko saiyaji notin yaki kwantuwa amma daya tara karfinsa waje guda sai nan da nan notin ya juya alokacinda kwanjin hannayensa ya kumburo rigar tasa ta dare nanfa anisa ta kura masa idanu tana mamaki azatonta bazata sami sadaukin da zai iya kwance wadannan notikan ba........sai gashi ni 99% na kunce kuma anan zan tsaya sai wani jikon idan baku sake gajiyaba Daga taskar Shuraih Usman Inkiya 99% TARKON MUTUWA Abdulaziz Sani madakin Gini Post:- Shuraih Usman Littafi na Shida 6 Part 6 E . . lokacinda anisa tazo nan atunaninta sai ta juya ta koma cikin gidan sarautarta, ta wata boyayyiyar hanya ta musamman WANNAN SHINE ABINDAYA FARU ABIRNIN SARAUNIYA ANISA BAYAN TA SAMI NASARAR FITAR DA SU HATYAN IZUWA NAHIYAR GABANSU Al'amarin jarumi hatyan kuwa tunda suka fada cikin nahiyar gaba sai suka tsinci kansu cikin farinciki gami da kwanciyar hankali tamkar basu da wasu makiya dake farautarsu tunda suka nausa acikin dajin suna tafiya her tsawon yini guda basu hadu da wani mugun abuba sau tari idan ma suka hango wata dabbar daji mai hadari kafin su risketa sai ta sauya hanya ta basu wuri abu daya ne ya sosa musu rai ba komai bane face sauyin yanayi basu taba ganin daji irin wannan ba hatta duwatsu da bishiyoyi da tsuntsayen ma ba irin wanda suka saba gani bane sai da rana ta fadi sannan su hatyan suka yada zango abakin wata korama mai dauke da ruwa garai garai gwanin ban sha'awa yake saboda ni imarsa ta kyawawan bishiyoyi tsirai gamida koramu bayan hatyan da sadirat sunci abinci sun sha ruwa sai suka zauna abakin wannan korama suna kallon yadda ruwa ke kwaranya acikin nishadi tsawon yan dakiku dayan su baice uffan ba daga can sai sadirat ta dubi hatyan alokacinda idanunta suka ciko da kwalla tace yakai dan uwana yanzu shike nan bamu da ikon komawa birnin mu bare har mu nemi inda kabarin iyayenmu yake mukai musu ziyara? kodajin wannan tambayar sai nan take shima hatyan yaji idanunsa sun ciko da kwalla kafin ya ankara hawaye ya subuto masa don haka sai ya janyo sadirat ya rungumeta yace ki kwantar da hankalinki yake yar uwata nayi miki alkawarin komai daren dadewa sai mun koma birnin bindal mun dauko fansar ran mahaifinmu, kuma ina mai tabbatar miki da cewa bokana na nan araye bai mutuba kuma nasan ya binne gawar iyayenmu a inda babu wanda ya. sani kodajin wannan batu sai farinciki ya lullube sadirat ta janye jikinta daga nasa ta dubeshi cikin murmushi da nufin tace wani abu kwatsam sai suka ji wani irin gurnani mai ban tsoro ya cika dajin daga kowacce kusurwa kuma gurnanin ya dinga karuwa yana kusanto su al'amarin daya firgita sadirat kenan ta koma bayan hatyan ta kankameshi lokaci guda sai suka hango wadansu manyan zakuna sama da guda dubu daga gabasa da yamma kudu da arewan dajin cikin zafin nama hatyan ya mike tsaye zumbur yana mai goya sadirat a gadon bayansa ya ruga izuwa cikin koramar dake gabansu, suna fadawa cikin koramar sai suka ga ashe acike takeda wadansu irin manya manyan kadoji tunda suka zo duniya basu taba ganin kadoji masu girmansu ba kafin hatyan ya yi wani yunkuri tuni wani kada ya make sadirat da jelarsa sadirat tayi sama ta fada can gefen koramar ta baje akasa sumammiya jini na zuba akanta cikin zafin nama hatyan ya daka tsalle ya kamo reshen wata bis TARKON MUTUWA Littafi na Shida 6 Part 6 E . . lokacinda anisa tazo nan atunaninta sai ta juya ta koma cikin gidan sarautarta, ta wata boyayyiyar hanya ta musamman WANNAN SHINE ABINDAYA FARU ABIRNIN SARAUNIYA ANISA BAYAN TA SAMI NASARAR FITAR DA SU HATYAN IZUWA NAHIYAR GABANSU Al'amarin jarumi hatyan kuwa tunda suka fada cikin nahiyar gaba sai suka tsinci kansu cikin farinciki gami da kwanciyar hankali tamkar basu da wasu makiya dake farautarsu tunda suka nausa acikin dajin suna tafiya her tsawon yini guda basu hadu da wani mugun abuba sau tari idan ma suka hango wata dabbar daji mai hadari kafin su risketa sai ta sauya hanya ta basu wuri abu daya ne ya sosa musu rai ba komai bane face sauyin yanayi basu taba ganin daji irin wannan ba hatta duwatsu da bishiyoyi da tsuntsayen ma ba irin wanda suka saba gani bane sai da rana ta fadi sannan su hatyan suka yada zango abakin wata korama mai dauke da ruwa garai garai gwanin ban sha'awa yake saboda ni imarsa ta kyawawan bishiyoyi tsirai gamida koramu bayan hatyan da sadirat sunci abinci sun sha ruwa sai suka zauna abakin wannan korama suna kallon yadda ruwa ke kwaranya acikin nishadi tsawon yan dakiku dayan su baice uffan ba daga can sai sadirat ta dubi hatyan alokacinda idanunta suka ciko da kwalla tace yakai dan uwana yanzu shike nan bamu da ikon komawa birnin mu bare har mu nemi inda kabarin iyayenmu yake mukai musu ziyara? kodajin wannan tambayar sai nan take shima hatyan yaji idanunsa sun ciko da kwalla kafin ya ankara hawaye ya subuto masa don haka sai ya janyo sadirat ya rungumeta yace ki kwantar da hankalinki yake yar uwata nayi miki alkawarin komai daren dadewa sai mun koma birnin bindal mun dauko fansar ran mahaifinmu, kuma ina mai tabbatar miki da cewa bokana na nan araye bai mutuba kuma nasan ya binne gawar iyayenmu a inda babu wanda ya. sani kodajin wannan batu sai farinciki ya lullube sadirat ta janye jikinta daga nasa ta dubeshi cikin murmushi da nufin tace wani abu kwatsam sai suka ji wani irin gurnani mai ban tsoro ya cika dajin daga kowacce kusurwa kuma gurnanin ya dinga karuwa yana kusanto su al'amarin daya firgita sadirat kenan ta koma bayan hatyan ta kankameshi lokaci guda sai suka hango wadansu manyan zakuna sama da guda dubu daga gabasa da yamma kudu da arewan dajin cikin zafin nama hatyan ya mike tsaye zumbur yana mai goya sadirat a gadon bayansa ya ruga izuwa cikin koramar dake gabansu, suna fadawa cikin koramar sai suka ga ashe acike takeda wadansu irin manya manyan kadoji tunda suka zo duniya basu taba ganin kadoji masu girmansu ba kafin hatyan ya yi wani yunkuri tuni wani kada ya make sadirat da jelarsa sadirat tayi sama ta fada can gefen koramar ta baje akasa sumammiya jini na zuba akanta cikin zafin nama hatyan ya daka tsalle ya kamo reshen wata bishiya dake cikin koramar yana reto akanta ai kuwa sai wani kada ya wangame bakinsa ya kawo masa hadiya hatyan ya daka tsalle daga kan bishiyar ya kaucewa harin kadar koda kadan ya cafi bishiyar sai ya gatsata ta rabe biyu duk da cewa kaurinta yafi kamu ashirin hatyan na fadowa kasa sai ya tsinci kansa atsakiyar miyagun zakuna sama da guda dubu uku koda ya dubi can gefensa ya hango 'yar uwarsa sadirat kwance cikin mugun hali sai ya kwarara uban ihu cikin tsananin fushi yayi wuf ya zare takobinsa ya afkawa zakunan SHIN JARUMI HATYAN ZAI KUBUTA DAGA HANNUN WADANNAN MIYAGUN ZAKUNA DA KADOJI? WANE HALI 'YAR UWARSA SADIRAT KE CIKI! ? ZATA RAYU NE KO MUTUWA ZATAYI? YAUSHENE HATYAN ZAI SAKE SADUWA DA ANISA DA KUMA BADI'ATUL NAUWARA? YAYA ZAIYI DA SOYAYYAR MATAN BIYU? YAUSHENE ZAI DAWO BIRNIN BINDAL DON DAUKAR FANSA AKAN SARKI SHAMSAL? MU HADU ALITTAFI NA BAKWAI DON JIN CIGABAN WANNAN LABARI, INA MAI BAKU HAKURI MEMBER NA WANNAN GROUP DIN NA MAZA GUMBAR DUTSE MAI ALBARKA, END OF DISCUSSION TARKON MUTUWA Littafi na bakwai Part 7A . Lokacinda hatyan ya fadawa wadannan dubunnan manyan zakuna ya zamana cewa yana kai musu sara da suka ta ko'ina cikin bakin zafin nama da jarumtaka sukuma suka rinka kai masa mangari, cizo yakushi suna yanyameshi, amma saboda zafin namansa da tsagwaron jarumtakarsa sai suka kasa samun nasarar yakusarsa shimaa kuma duk da cewa yana makesu suna zubewa kasa saiyaga sun taso zumbur sunci gaba da kawo masa mugayen hare hare saida suka kusan shafe rabin sa'a suna mugun artabu ba tareda dayansu ya sami nasara akan dayaba awannan lokaci hankalin jarumi hatyan ya dugunzuma ainun saboda kaifi da tsini baya tasiri ajikin zakuna kuma. ko kadan babu alamar gajiya atareda zakunan kamar ko yaushe kara musu kuzari akeyi, shikuwa saiya fahimci cewa idan aka cigaba da wannan fafatawa ahaka her izuwa tsawon wani lokaci to tabbas zai iya jigata zakunan su cimmasa amma babban tashin hankalinsa shine batun 'yar uwarsa sadirat da take kwance magashiyan acan gabar koramar kuma baisan halin da take ciki ba nan take hatyan ya aiyan a ransa cewa lallai wadannan zakuna sihirtattune na musamman idan kuwa hakane to turosu akayi musamman don su kasheshi tareda 'yar uwarsa sadirat babu wanda ke dauke da wannan alhakin face sarki shamsal tabbas wannan dayane daga cikin irin mugayen tarkunan da sarki shamsal ya kafa musu koda gama ayyana hakan acikin zuciyarsa saiya fara tunanin hikimar dazai yi amfani da ita wajen ganin ya gaggauta kawar da wadannan zakuna dabara ta fadomasa ya gane cewa saidaifa yayi amfani da tsagwaron karfin damtsensa da kuma dabarun fada saboda yayi kokarin amfani da karfin sihirinsa na tsafi yakiyin amfani saboda ansha gabansa awannan fannin acikin shammace gamida tsananin fushi sai jarumi hatyan ya shammaci daya daga cikin zakunan ya gabza masa wawan naushi a idonsa guda daya saboda karfin naushin take ruwan idon zakin ya tsiyaye zakin yayi tsalle sama yayi wata irin kururuwa mai ban tsoro ya fado kasa tim ya baje wanwar ko shurawar kirki baiyiba koda jarumi hatyan ya ga ya sami nasara saiya kamu da tsananin farinciki kuma ya kara kaimi yaci gaba da bugun zakunan cikin zafin nama da jarumtaka aikuwa nandanan yaci karfinsu ya bazar da sama da guda dari shida tabbas idan kaji ana ki gudu to sa gudune baizoba lokacinda zakunan suka ga hatyan yana ragargazar 'yan uwansu suna zama gawa sai suka tarwatse suka kama gudu acikin daji dukkaninsu suna neman wajen buya koda jarumi hatyan ya ga zakunan sun watse daga wajen sunbar gawarwakin 'yan uwansu birjik saiya rugo da gudu izuwa inda sadirat ke kwance da isarsa daf da ita sai ya durkusa yana shirin tallafo kanta kenan saiyaga ta bude idanunta ta dubeshi cikin murmushin karfin hali cikin tsananin farinciki yayi sauri ya cire wani kyallen dake jikinsa ya daure raunin dake kanta saboda her asannan raunin bai daina digar jini ba sannan ya dauke ta da hannu biyu yakaita bakin wani dutse yayi sauri ya bude jakar guzurinsa ya fiddo magani ya shafa akan raunin nata kuma ya bata tasha ta hadiya sau uku faruwar hakan keda wuya sai taji karfin jikinta asannan ne ta sake dubansa cikin murmushi akaro na biyu tana mai gyara zamanta tace yakai dan uwana nayi farinciki dana ganka araye inda ace ka tafi ka barni bansan yadda zan cigaba da rayuwaba, koda ta tsawon dakika guda kuwa lokacinda sadirat tazo nan abayaninta sai jarumi hatyan yayi murmushi yace ai nine zance da kin tafi kin barni bansan yadda zan cigaba da rayuwaaba babu mamaki hankalina ya gushe nan take koma na hadiyi zuciya na mutu saboda bakin ciki tunda bani da sauran kowa aduniya sai........ kafin hatyan ya gama fadin abindake bakjnsa sai sadirat tayi sauri ta rufe bakinsa da tafin hannunta tace karka fadi haka domin inaji ajkina cewa muna da sauran rayuwa awannan duniya bazamu mutu ba harsai munga bayan makiyan mu alkawarine sai mun dawo birnin bindal mun dauki fansa akan sarki shamsal da dansa yayinda sadirat tazo nan abayaninta sai farinciki ya lullube hatyan ya rungume ta akan kirjinsa yana mai cewa, kinyi gaskiya yake 'yaruwata lallai duk wuya duk rintsi sai mun cika burin mu sadirat ta numfasa tace waishin yanzu menene abinyi agaremu? shin zamu yada zango ne anan tsawon wadansu 'yan kwanaki ko kuwa zamuci gaba da tafiyane har mu riski garin dake gaban mu dajin wannan tambaya sai jarumi hatyan yayi ajiyar zuciya sannan yace yake 'yaruwata ci gaba dayin wannan tafiya tamu ayanzu yana da matukar hadari saboda akwai matsananciyar gajiya ajikina sakamakon gwagwarmayar da nayi da wadancan sihirtattun zakuna koda jin wannan batu sai mamaki ya kama sadirat tace yanzu kana nufin kace duk wannan masifa da kuma shiga aiki ne na sihirine? hatyan ya gyada kai yace kwarai kuwa kuma wannan masifa somin tabi ce kawai abinda nakeso dake kawai shine lallai ko yaushe ki kasance kina tareda ni kada ki kuskura ki rinka nisanta dani koda kuwa da tazarar taku ukuce sadirat ta gyada kai tana mai nuna cewa zata kula WANNAN SHINE ABINDA YA FARU GASU JARUMI HATYAN BAYAN SUN SAMI NASARAR FITA DAGA CIKIN NAHIYARSU GABA DAYA INDA SUKA SHIGA SABUWAR NAHIYA TA BAKAKEN FATA Lokacinda tsoho lamzis ya fita ya bar boka daizur da sarki shamsal a zaune sai boka daizur ya kasa fiddo madubin tsafinsa kawai sai ya runtse idanunsa yayi kamar yana bincikene, al'amarin daya fusata sarki shamsal kenan ya daka masa tsawa yayi firgigit kamar wanda ya farka daka barci, sarki shamsal ya dubeshi yace kada ka bata mini lokaci abanza kawai ka dauko madubinka ma tsafi ka binciko mana mugun halinda su hatyan suke ciki tunda tuni mun aika musu da zakunan sihirin da zasu hallakasu aduk inda suke koda jin wannan umarni sai boka daizur yayi sauri ya zura hannunsa acikin aljihun wandonsa jikinsa na rawa ya fiddo madubin ya ajiye shi agabansa cikin matukar karfin hali kuma zuciyarsa na daka ya dora tafin hannunsa na hagu akan madubin ya shafeshi, ba zato ba tsammani sai boka daizur yaga madubin nasa ya washe daga duhu zuwa haske nan take saiga hoton duk abinda ya faru gasu jarumi hatyan nan acikin daji da yadda hatyan ya fafata da wadannan zakuna harya kashe wasu da yawa daga cikin su koda gama ganin abinda ya faru sai fuskar sarki shamsal ta kama gyatsine saboda tsananin fushi ya kasa cewa uffan harsaida boka daizur ya shafi madubin tsafin nasa yayi baki sannan ya dubeshi yace yanzun nan zamuyi shiri mubi su jarumi hatyan izuwa wannan nahiya da suka shiga ta bakaken fata lallai sai mun cimmasu nayiwa hatyan da 'yar uwarsa kisan gilla, kodajin wannan batu sai idanun boka daizur suka zazzaro ya dubi sarki shamsal cikin matukar firgici yace haba ya shugabana shin ka mantane cewar yana daga cikin dokokin magabatanka cewa jininku baya shiga wata nahiyar? idan kuwa ya shiga bazai dawoba araye kuma saiya rasa komai da kowa arayuwarsa idan her kabi su hatyan waccan nahiyar bazaka taba cika burinka ba akan sa kuma ba zaka koma birninka na bindal ba abinyi kawai shine muci gaba da tura musu mugayen tarkunan da basu isa su iya tsallakesu ba komai sa'arsu da nasararsu lokacinda sarki shamsal yaji wannan bayani na boka daizur sai hankalinsa ya dan kwanta ya sunkwui da kansa kasa yana mai tunani da nazari daga can saiya dago da kansa ya dubeshi yace jiya da daddare lokacinda muka dan runtsa nayi wani mafarki daya dan sosa mini rai lallai akwai wani bakon abu dayake faruwa abirnin bindal inaso ka duba mini yanzu domin muga ko menene abinda ya faru bayan tafiyar mu koda jin wannan batu sai boka daizur yaji zuciyarsa ta buga da karfin gaske, al'amarin daya sa shi kansa ya firgita kenan kuma ya kamu da tsananin mamaki domin bai san dalilin dayasa yaji tsoro ya shigeshi ba amma saiya dubi sarki shamsal cikin murmushi yace haba ranka ya dade yanzu her akwai wani abu wanda zai faru abirnin bindal ya baka tsoro aiko ma menene da zarar mun koma zamu kawar dashi cikin dakika daya kafin boka daizur ya gama rufe bakinsa, tuni sarki shamsal ya tari numfashinsa yana mai cewa ai dan hakkin daka raina shike tsone maka ido irin wannan sakacin nakane yasa hatyan ya wanzu abinrnin bindal ba tareda mun sani boka daizur ya rissina yace hakika abinda ka fada gaskiyane amma ka sani cewa taura biyu bata taunuwa alokaci daya domin hankalinka zai iya rabuwa biyu idan kuwa ya rabu ana samun rashin nasara zaifi kyau mu gama da matsalar su hatyan domin tafi kowacce matsala hatsari sa'adda sarki shamsal yaji wannan batu saiyaja dogon numfashi gamida ajiyar zuciya sannan yace yanzu menene mugun abu na biyu wanda zamu turawa su hatyan lallai inason su hallaka kafin su isa wannan

Chapter 7 of 11