Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 11
babban birni dake gabansu wanda ake kira da suna birnin kanyasi.. 7B Loading... TARKON MUTUWA Littafi na bakwai Part 7 B . Kodajin wannan batu sai boka daizur ya bushe da dariyar mugunta sannan yace ya shugabana abinda zamu tura musu bakomai bane face uwar macizan duniya na rantse da darajar gemun uban koda za'a tara irinsu jarumi hatyan guda dubu masu irin sa'arsa da karfinsa da jarumtakarsa sai wannan macijiya ta hallakasu farat daya ba'a tabayin macijiya mai girma, karfi da mugun hadariba aduniya tun daga farkon wanzuwar duniya kawo iyanzu kamar uwar macizai ba nine kadai zan iya fito da wannan macijiya daga cikin kogin da take zaune sama da shekaru dari uku da talatin domin akwai kalmomjn tsafi na musamman da za'a iya kiranta dasu kuma na gajesune daga wajen kaka na na bakwai kodajin wannan batu sai mamaki ya kama sarki shamsal yace, yakai dirkar birnin bindal nifa karamin yaro nakejin labarin uwar macizan duniya awajen iyayen da kakannina, ance in da zata mikar da tsawonta yakai kamu dubu ashirin kuma kaurinta yakai na katuwar bishiyar kuka sannan babu wani kwaro ko dabba mai karfin gudunta bisa doron kasa domin tana iya zuwa birnin sin daga birnin kisra acikin sa'a shida da rabi tana shekara goma sha daya akwance tana barci ba tareda ta bukaci abinci ko ruwa ba amma da zarar ta farka daga barci na tsawon shekaru goma sha daya sai ta cinye dabbobi kimanin guda goma dubu masu girman rakuma sannan take koshi, ruwa kuwa idan ta kafa kanta bakinta abakin karamar korama tana iya zuketa kaf acikin 'yan dakiku masana tarihi sun tabbatar da cewa sau daya wannan macijiya ta taba baiyana aka ganta sa'adda tayi tafiyar kasa daga birnin kisra zuwa sin ance awannan shekara duk wani gini dake cikin biranen biyu saida suka rushe, duk inda ta shafa da jikinta saidaya haifar da rami mai zurfin kamu dari gamida fadin kamu arba'in, tekuna da koramai da fadamai saida suka rika ambaliya suna hadewa da junansu bishiyoyi sai da suka kakkarye guda daya bata tsayaba duwatsu kuwa fashewa suka dinga yi suna bindiga saboda azabar zafin wutar dake fita daga cikin bakin uwar macizai kai atakaice ance wannan macijiya ita kadai zata iya hallakar da duniyar nan duk acikin kwanaki da basu wuce dubu da dari uku ba, ita dai wannan macijiya an tabbatar da cewa babu wata halitta a wannan duniya mai karfin ta kuma babu wani makami dazai iya daran jikinta ko ya hudata taya zaka iya fito da wannan macijiya alhalin ance sau daya ta taba fitowa tun azamanin kakana na bakwai yau shekara dari da ashirin kenan? tabbas inda zaka iya fito da itaka turawa su hatyan da 'yar uwarsa to tabbas na yarda cewa zata hallakasu acikin dakika daya jal koda kuwa sunfi kowa sa'a da tsawon rai lokacinda sarki shamsal ya zo nan azancensa sai boka daizur ya bushe da dariyar mugunta cikin nuna isa gami da yarda da kansa sannan ya dubi sarki shamsal cikin nutsuwa yace ya shugabana tabbas zan nuna maka cewa ni bokane, dan boka kuma jikan boka lallai zaka san cewa babu wani boka acikin duniyar nan da yakai ni karfin sihiri koda jin wannan batu sai sarki shamsal ya bushe da dariya sannan ya dubi boka daizur a wulakance gami da rainin wayo yace hakika ku bokaye akwaiku da kuri kuma kun iya zabga karya ko kunya bakwaji ,shin ka mantane cewar abaya sarkin mafarauta ya gagareka ka kasa hallakashi da karfin sihirin tsafinka saida ka shammace shi ka jeho shi kasan wannan rami mai tsawo? yayinda boka daizur ya ji wannan batu sai yayi murmushi yace ya shugabana hakika abinda ka fada gaskiyane amma inaso ka sani cewa kowanne mutum yana da irin baiwarsa komai karfin sihirinka kuma komai jarumtakarka bai zama dole ka zamo mai sa'a da nasara ba acikin al'amuranka ba kai da kanka yanzu matsalar da kake fuskanta kenan akan wadannan makiya naka gashi dai kafisu karfin sihiri dana damtse amma gashi sun gagareka saboda sun kasance masu sa'a koda boka daizur yazo nan azancensa sai jikin sarki shamsal yayi sanyi kuma yayi shiru tsawon 'yan dakiku kadan baice komaiba daga can saiya dago kansa ya dubi boka daizur yace inason naga uwar macizai a zahiri amma kafin nan ka nuna mini ita a madubin tsafinka a shekarar data fito daga kogonta dake birnin kisra taje birnin sin nikam inason naga abubuwan da suka faru sakamakon fitowar ta awannan lokaci sa'adda boka daizur yaji bukatar sarki shamsal saiyayi doguwar ajiyar zuciya ba tareda ya kara cewa komaiba ya fito da madubin tsafinsa ya ajiye shi agaban sarki shamsal ya shafeshi da hannun hagu, dajine mai matukar kwarjini saboda yanayinsa ya fita daban dana sauran dajijjikan duniya abinda yafi yawa wannan daji shine manyan tsaunika da koguna, da kuma ramuka masu zurfin gaske da fadi su kansu bishiyoyin wannan daji na musamman ne irin wadanda idanuwa basu saba gani ba kawai sai dajin gaba daya yayi girgiza, bishiyoyi suka rinka tunbukowa daga cikin karkashin kasa da kansu suna zubewa kasa duwatsu kuwa komai girmansu sai gashi suna mirginawa da gudu suna karoda 'yan uwansu da sauran bishiyoyi al'amarin daya firgita dabbobi da tsuntsaye kenan suka kama guje guje da iface iface, tsuntsayema ba shiri suka rinka sauya sheka amma duk da haka basu tsiraba sai dai kaga suna fadowa kasa matattu saboda wani irin huci mai zafin tsiya da yake fitowa daga jikinta ya mamaye sararin saman, ba komai ne ya haddasa hakanba face fitowar uwar macizai daga cikin kogon da take boye, shikansa kogon dutsen da farko saiya kama tsatstsagewa ,uwar macizai na motsa jikinta saiya fara rugujewa kafin ta gama fitowa daga kogon ya gama rushewa gaba daya ya baje kasa tana yin tafiya ne akan kasa dajin gaba daya ya hautsine koda sarki shamsal yayi arba da kan uwar macizai acikin madubin tsafin boka daizur yaga tsananin girmansa kuma yaga kaurin jelarta da tsawonta saiya firgita ainun baisan sa'adda yadan ja da baya ba domin gani yayi kamar zata faso madubin tsafin ta lankwameshi, ashe boka daizur ya ga yadda ya tsorata daizur bai san sa'adda dariya ta kwace masa ba shikuwa sarki shamsal saiya dake kuma ya murtuke fuskarsa yana maici gaba da kallon madubin tsafin abinda y kara daurewa sarki shamsal kai shine ganin yadda macijiyar takeyin azababben gudu akan kasa tamkar an harbo kibiya cikin dakiku kadan ta fice daga cikin wannan daji take ta fara shiga birane duk garin data ratsa saidai kaga ana girgizar kasa, mutane na hallaka gidaje na rushewa kuma gobara ta dinga tashi haka dai macijiyar tayi ta haddasa bala'i a duniya ta rinka baje kasashe harsaida ta isa birnin sin ta fada cikin wani teku sannan komai ya lafa masana tarihi da masu bincikesun tabbatar da cewa ba'a tabayin annobar mutuwa ba aduniya kamar wannan lokaci da uwar macizai ta bayyana lokacinda sarki shamsal ya gama ganin al'amarin uwar macizai WAI IDAN AGASKENE TAYAYA ZAKA TSIRA IDAN KA HADU DA WANNAN MACIJIYA A INDA KAKE ZAUNE KO KUMA ME ZAKAYI MATA? DAGA HABIBULLAH KBR acikin madubin tsafin boka daizur saiyaja dogon numfashi gamida ajiyar zuciya kuma sai nan take ya kamu da Tsananin farinciki ya dubi boka daizur yace na rantse da darajar kabarin kakana idan har ka iya fito da wannan macijiya daga ccikin tekun da ta shiga ka aikata izuwa su hatyan acikin dakika daya jal zata hallakasu kodajin wannan batu sai farinciki ya turnuke boka daizur ya kyalkyake da dariyar mugunta alokacinda ya sake shafar madubin tsafin da tafin hannunsa yayi duhu daga haske kuma ya dauke shi ya sashi a aljihunsa boka daizur ya dubi sarki shamsal cikin nutsuwa gamida alamun damuwa sannan yace ya shugabana fito da wannan macijiya abune mai sauki tamkar cire silin gashi daga cikin tandun mai amma fa akwai wata matsala guda daya, kodajin haka sai shamsal ya dubi boka daizur yace menene matsalar? daizur yayi ajiyar zuciya yace idan wannan macijiya ta fito awannan karon sai anyi asarar rayuka ninki ukun wanda akayi a wancan zamani sannan kuma wannan masifa zata iya shafar birninka na bindal babu mamaki ma ta shafi danka da matarka kodajin wannan batu sai sarki shamsal ya bushe da dariyar mugunta lokaci guda kuma sai ya turbune fuskarsa yace nifa akan biyan bukatata ran kowa da komai ba agabana yakeba kawai ka fito da wannan macijiya kodajin haka sai mamaki ya kama boka daizur amma sai yayi shiru baice kalaba... PART C LOADING..... TARKON MUTUWA Littafi na bakwai Part 7 C . ACan kuma dajin da su hatyan suke kuwa bayan sun gama tattaunawa sai suka kafa tanti suka shiga ciki suka zauna bayan sun bude jakar guzurinsu sunci sun koshi sai suka kwanta suka kama barci abinsu tamkar acikin gidajensu suke, abinka da gajiyayyu nantake barci ya dauke su basu suka farka ba saida gari ya waye hasken rana ya bugo cikin tantin sadirat ce ta fara farkawa koda taga hatyan yanata faman shara barci abinsa bashi da niyyar farkawa ma saita mike tsaye ta fito daga cikin tantin da fitowar ta saita kama kalle kallen dajin inda ya bata sha'awa matuka saboda kyawunsa da ni'imarsa wacce ta bambanta ainun da irin dazuzzukan dake nasu nahiyar abinda ya kara burgeta shine ko kadan babu sanyi awannan nahiyar wanda zai dami mutum sai wata irin iska mai dan karan dadi dake busawa sadirat ta daga hannayenta biyu ta mike gami da hamma tajin yunwa sannan sai ta fara tafiya acikin dajin tana maici gaba da tafiya acikin dajin tana mai ci gaba da kallon bishiyoyi, furanni da koramai masu yayewa dukkan bakin cikin ta ahakanne sadirat tayi dan nisa da inda tantin su yake bata saniba harta iso bakin wata korama mai ban sha'awar gaske itadai wannan koramar ruwan dake zubowa cikinta daga kan wani dutse yake zubowa kuma ruwane garai garai mai haske da sheki da haske hartana iya ganin fuskanta akan ruwan tamkar madubi koda ganin wannan koramar sai sadirat taji babu abinda takeso sama da tayi wanka acikin wannan koramar amma kuma sai tsoro ta kamata tace acikinta ya za'ayi na kwabe kayana acikin wannan daji na shiga wannan korama alhalin bansan abubuwan dake cikinsa ba kuma bansan abinda ka iya zuwa mini ba na bazato gama ayyana hakan keda wuya sai ta kama dube dube da leke leke saida ta duba gabas da yamma kudu da arewa kuma ta duba sama da kasa amma bataga komai ba kuma batajin motsin komai ba koda kuwa na kwaro ko tsuntsu kuma bataga alamar sawun wata halitta ba hakanne yasa zuciyarta tayi sanyi taji ta sami nutsuwa da kwanciyar hankali ba tareda fargaba ba saita kwabe dukkanin kayan jikinta ta rataye su ajikin wata koramar ta shiga cikin koramar ta kama yin wanka abinta… tsawon 'yan dakiku tana cikin hakan ba tareda fuskantar wata matsalaba sai kawai tajiyo muryoyin wasu mutane daga bayanta suna magana cikin wani yare wanda bata taba jin irinsa ba arayuwarta cikin firgici sadirat ta juyo kuma ta yunkura da nufin ta fito da gudu daga cikin koramar amma sai taga ashe tuni mutanen sun iso kusa da ita samari ne matasa su uku dukkaninsu bakaken fata ne wanda ke tsakiyarsu yakasance dogo wankan tarwada domin bashi da duhun fata kamarsu kuma dole asashi a sawun kyawawa da gani ba tambaya yanayin shigar da yayi ya fito daga gidan sarauta irin na wannan nahiya domin rigarsa da wandonsa masu tsadace kuma ya daura sarkar lu'u lu'u awuyansa yana da yalwar gashi tamkar mace wanda ya tattare shi ya daureshi agadon bayansa riger tasa mai yankakken hannuce hakanne ya bayyana surar jikinsa irinta sadaukai mai tarin kwanji, murdewa, su sukuwa rahowar matasan dake tatedashi shiga sukayi irinta dakaru kai da gani kasan cewa masu tsaron lafiyarsa ne kowannensu na ruke da takobi da garkuwa kuma suna sabe da kwari da baka abayansu shikuwa wannan dan sarki babu wani makami ajikinsa face kwari da baka ga dukkan alamu dai farauta ce ta shigo dasu cikin wannan daji koda wadannan samari uku sukayi arba da sadirat acikin wannan koramar sukaga tsananin kyanta kuma sukaga launin fatarta ba irin tasuba saiduk suka firgita suka ruga izuwa bayan wata bishiya suka buy suna leke atsakaninsu da ita itadai sadirat so take ta fito daga cikin koramar ta ruga izuwa inda ta rataye kayanta ta dauka ta sanya amma saboda kada suga tsiraicinta shiyasa ta kasa fitowa su kuwa tsammani sukayi aljanace ba mutumba domin basu taba ganin mace mai kyan sadirat ba ana cikin hakane idanun dan sarkin suka kaikan bishiyar da sadirat ta rataye kayanta koda tag suturarta sai ya gane tabbas wannan mutum ce ba aljana bace domin inda aljanace zata iya dauko kayanta da kanta daga inda take ta suturce jikinta koda gama ayyana haka sai dan sarkin ya kamu da tsananin mamaki ya sake tambayar kansa yace to tayaya akai tazo nan kuma daga ina tazo? ko kuwa aljanune suka satota daga wata nahiyar duniya suka kawota nan? saboda son jin amsar wadanan tambayoyi sai dan sarki ya fito daga bayan wadannan bishiyar da suka buya ya tunkari inda sadirat take koda sadirat taga dab sarki ya durfafota saita firgita ainun tayi zaton ko shima mai irin halayyar yarima zainur ne wato so yake ya lalata mata rayuwa nantake sadirat ta takarkare ta kwarara uban ihu mai karfin gaske, aikuwa sai iska ta dauki sautin ihunta ta kaishi har cikin kunne jarumi hatyan wanda ke kwance acan cikin tanti yana faman sharar barci kamar an saceshi nan take hatyan ya farka adimauce azatonsa mafarki yakeyi amma saiya sake jiyo sautin ihun sadirat daga can nesa hatyan ya mike tsaye zumbur ya fito daga cikin tantin aguje ya nufi bangaren da yake jiyo ihunta wohoho! mai abu da abinsa kura da kallabin kitse nanta hatyan ya dinga falfala azababben gudu na masifa irin wanda bai taba yiba arayuwarsa domin aduniya babu abinda daya tsana sama da abinda zai taba lafiyar wannan 'yar uwa yasa al'amarin wannan dan sarki kuwa lokacin dayaga sadirat ta firgita dashi ta kama ihu sai ya fara yi mata magana cikin yaren sa yana cewa ni ba cutar dake zanyiba tambaya zanyi miki abinda ya manta shine ai batajin yarensa da yaga ta rude sosai sai ya nufi inda ta rataye kayan nata ya daukosu da nufin ya kaimata ta suturce jikinta koda ya tunkareta yana murmushi ita kuwa tana mai ci gaba da kwalla ihu saikawai suka jiyo sautin gudu abayansu shida dakarun nasa kafin suyi wani yunkuri tuni jarumi hatyan ya gabzawa wadannan dakarun naushi afuskokinsu suka zube kasa alokacinda jini yayi fitar burgu daga cikin bakunansu, suka baje sumammu kuma ya dako tsalle a sama ya daki kirjin dan sarkin da kafarsa dan sarkin yaja da baya kadan yayi baya taga taga amma saiya tsaya kyam yana ruke da suturar sadirat suka fara kallon kallo da hatyan su kansu sunyi matukar mamakin yadda suffer jikinsu da tsawonsu yazo daya shida h hatyan su kansu sai da sukayi mamakin yadda tsawonsu yazo daya kamar hassan da hussaini banbancin kawai shine sun banbanta alaunin fata da kamannin fuska kai da ganin irin kallon da suke yiwa junan nasu kallone na shakkar juna itadai sadirat saita sakeyin kasa cikin ruwan koramar ta takure jikinta da hannayenta don boye jikinta al'amarin daya fusata hatyan kenan bisa ganin yadda dan sarki yaci gaba ruke suturar sadirat ahannunsa kuma ya kura mata ido kawai sai hatyan ya sake dako tsalle asama ya kawo masa wawan naushi a fuska cikin zafin nama dan sarkin ya sunkuya hannun hatyan ya naushi iska nanfa suka kachame da masifaffen yaki suka wanzu suna masu kaiwa junansu naushi da bugu hannu da kafa suna kokawa ,wannan ya dan wancan wancan ya danne wannan nanfa mamaki ya turnuke sadirat domin kawai gani tayi karfinsu yazo daya da zarar daya daga cikinsu ya naushi daya say kaga shima dayan ya rama daidai yadda akayi masa saida suka shafe lokaci mai dan tsawo suna wannan artabu ya zamana cewa sun hadawa kansu jini da majina amma babu wanda ya sami nasara akan abokin gwaminsa kuma her asannan wadannan dakaru biyu na dan sarki basu farfadoba daga suman d sukayi kuma suturar sadirat tana hannun dan sarkin... Part D Loading... TARKON MUTUWA Littafi na bakwai Part 7 D . Hatyan yaga wankan hula zai kaisu dare saiya ja da baya ya zare takobinsa yana mai gyara tsayuwarsa ko daganin haka sai dan sarki ya dakatsalle izuwa inda dakarunsa suke kwance a kas ya fisgo takobin daya daga cikinsu ,ya zareta kuma shima ya gyara tsayuwarsa a wannan lokacine ta razana ainun domintasan cewa wannan gumurzu bazai yi kyau ba. matasan biyu zasu iya cutar da juna sun rugo da gudu izuwa kan junansu sunt ruguntsume da sabom masifaffen yaki. kaico! yaro in baka yi bani wuri wanda ya iya ya huta kuma wahala sai jurarre, ba jinta sai kwarre ,lokacin da wadannan matasa biyu suka cakuma da yaki ya zamana cewa suna kai wa junansu sara da sukacikin bakin zafin nama juriya da bajinta sai hankankalin sadirat ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe domin yaki ne mai mugunhadari da ko yaya aka sami kuskure zasu iya yin ragas ko kuma dayansu ya sheka barzawu. saida suka shafe kusan rabin sa'a suna wannan gumurzu kuma kowannensu yana yakine da dukkan karfinsa kuma afusace duk wanda aka kawowa sara ya kauce ana samun bishiya saidai kaga an rabata biyu komai kaurinta saboda karfin saran a tsawon wannan lokaci babu wanda ya sami nasarar koda lakutar jikin daya bisa dole kanwar naki suka ja d baya taku biyar biyar sukayi cirko cirko kamar zakaru saboda tsananin gajiya kamar hadin baki sai da kowannensu ya buda hannayensa kuma suka daga takubbansu sama suka ruke hannayensu biyu kawai sai suka rugo da gudu izuwa kan ju na cikin tsananin fushi gami da mugun nufi kai da gani kasan cewa indai akayi wannan gamo dolene labari yasha banban kodai su yi ragas ko kuma dayansu ya sami nasara akan dan uwansa saura baifi taku biyuba kacal su hadu kawai sai sadirat ta kurma uban ihu hakanne ya janyo hankalinsu suka sauke takubbansu suka dubi inda take kawai kura musu idanu tayi tana karkarwar jiki sakamakon iskar data fara kadawa mai sanyi acikin dajin koda ganin haka sai dan sarkin ya cilla mata tufafin nata t cafe sannan ya juya mata baya ganin hakanne yasa jikin hatyan yayi sanyi ya mayar da takobinsa cikin kufe a lokacin d shima ya juyawa saditammrat baya tana sanya suturar tata shima dan sarkin ya yi jifa da tasa takobin sannan mikawa hatyan hannu suka gaisa cikin alamun rashin yadda hatyan ya bashi hannunsa suka gaisa adaidai wannan lokacin ne dakarun dan sarki su biyu suka farfado daga dogon suman da sukayi suna bude idanunsu sukaga shugaban nasu da hatyan suna gaisawa saisuka kurawa juna idanu suna mamaki aka rasa wanda zaice wani abu, alokacin ne sadirat ta kammala sa suturarta ajikinta ta fito daga cikin koramar ta taho daf da hatyan ta tsaya suma wadannan dakaru biyu sai suka matso dafda shugabansu suka tsaya kwatsam ba zato ba tsammani sai dan sarki yaji hatyan ya budi baki cikin irin yarensa yace yakai yarima nasmal da ga sarki damhas kayi sani cewa tuni abaya maigidana sarkin mafarauta na garin mu ya bani labarin ku kuma ya koyar dani yarenku tun ina yaro karami domin abinciken da yayi tun asannan yasan cewa nan da wasu shekaru zanzo nahiyarku ya gaya mini cewa ya taba zama a cikin wannan acikin wannan babban birni naku na tsawon shekaru uku tabbas zaka gasgata zancena idan na nuna maka wani abu yanzu duk da cewa kana yaro karami sa'adda mahaifinka ya baiwa sarkin mafarauta wannan abu lokacin da hatyan yazo nan azancensa sai sadirat da wadannan dakaru suka cika da mamaki domin basu taba zaton cewa hatyan ya iya wannan yareba shima yarima nasmal sai murna da mamaki suka kamashi ya dubi hatyan cikin murna da murmushi yace shin ku mutanen wani gari ne wanda ake kira da suna bindal? hatyan ya gyada kai alokacin daya bude jakar guzurinsa ya fiddo wani hatimin sarauta wanda akayi shi da karge zagayayye mai dauke da zanen tsuntsu da kibiya wanda ya kasance alamace ta masarautarsu ya mikawa nasmal cikin tsananin mamaki nasmal ya karbi wannan hatimin ya kalleshi dakyau nantake fuskarsa ta fadada da murmushi kuma ya kamu da farinciki kawai saiya rungume hatyan yana mai sumbatarsa tamkar wanda yaga wani dan uwansa na jini wanda ya dade basu haduba cikin hanzari da mamaki gami da dan fishi hatyan ya janye jikinsa daga jikinsa yace menene ma'anar wannan farinciki naka? maimakon nasmal ya baiwa hatyan am sar wannan tambaya da yayi masa saiya dubi wadannan dakaru nasa guda biyu yace maza ku koma gida ku sanar da sarki cewa jarumin da muke jira yazo yayi maganin masifar da muke jira ya iso ina tire dashi a daji yana gama fadin hakan sai nasmal ya dubi hatyan yace waccan yayarka ce ko kuma gudun hijira kukayo daga waccan nahiyar dajin wannan tambaya sai hatyan ya gane cewa lallai wadannan mutane suma manyan matsafa don haka kawai sai ya gyada kansa alamar cewa hakanne nasmal yayiwa sadirat wani irin kallo mai dauke da alamar tambaya wanda yasa nantake taji zuciyarta ta buga da karfi akaron farko arayuwarta a tsakaninta da da namiji nasmal ya juya ya dubi dakarunnasa biyu yace me kuke jirane tun dazu na baku umarni baku tafiba dajin wannan tambaya sai daya daga cikinsu ya budi baki da kyar muryarsa na rawa yace ya shugabana yanzu idan muka koma gida babu kai me kake zaton sarki zaiyi mana? zai iya zaton cewa cutar dakai mukayi yasa akashe mu ka sani cewa munyi rantsuwa akan cewa zamu tsare rayuwarka da lafiyarka kuma duk runtsi bazamu dawo gida babu kaiba sa'adda yarima nasmal yaji wannan batu sai yayi murmushi sannan ya mikawa daya daga cikinsu wannan hatimin sarauta yace kuna isa gida ku baiwa sarki wannan hatimin kuma ku gaya masa sakon dana baku farinciki zaiyi yasa ayi muku goma ta arziki kodajin haka sai farinciki ya lullube dakarun suka juya da baya suka ruga izuwa cikin daji nasmal ya juyo ga hatyan ya sake yiwa sadirat irin wannan kallo da yayi mata abaya sannan ya dubi hatyan yace nasan akwai tambayoyi abakinka agareni ka fadesu naji hatyan ya yi dab guntun murmushi yace kafin na fada maka tambayoyina zan baka shawara guda daya zaifi kyau ka nisanci 'yar uwata domin mallakarta ko mallakar zuciyarta daidai yakeda tunkarar mayakan duniya duka 'yar uwata bata taba son wani da namijiba domin zuciyarta batasan komaiba face son iyaye da yi musu hidima tundaga kuruciyarta zuwa girmanta na tsani naga wani da nimiji ya kusanceta sai saboda tsoron kada ya siye zuciyarta ya aureta domin idan ya aureta dolene ya rabani da ita alhalin bantaba rabuwa da itaba daidai da rana daya ba tun daga girmana kawo zuwa yanzu sa'adda hatyan yazo nan azancensa sai yarima nasmal ya bushe da dariya sannan ya dafa kafadarsa yace nayi murna daka gane cewa na kamu da son 'yar uwarka farat daya kuma nayi murna daya kasance batajin wannan yare da mukayi na ruki alfarma daya daga gareka da kada kasanar da ita abinda muka tattauna yanzu amma ka sani cewa ta sace zuciyata kamar yadda ka sace zuciyar badi'atul nauwara da sarauniya anisa haka itama 'yar uwarka ta sace zuciyata idan son masoyi laifine to kafara tambayar kanka meyasa kake begen badi'atul nauwara da anisa kuma ka tambayi kanka yadda zakayi da soyayyar 'yan mata biyu alokaci guda. tabbas zuciya bata da kashi kuma shi so barawone baya sallama bare asan sa'adda zai shigo gida atsayar dashi lokacin da yarima nasmal yazo nan azancensa sai jikin hatyan yayi sanyi matuka baisan sa'adda ya koma gefe daya ya zaunaba yayi jugum yana mamaki yadda akayi yarima nasmal yasan sirrinsa koda ganin haka sai itama sadirat ta matso kusa da hatyan tana waigen yarima nasmal tanayi masa wani irin kallo mai nuna alamar rashin yadda da kuma damuwa hakanne yasa hankankalin sa ya tashi yace a ransa yace tabbas zansha wuya kafin na siye zuciyar wannan yarinya domin akwai alamun cewa batasan menene ma soyayyaba sadirat ta durkusa agaban hatyan ta dafa cinyoyinsa tace ya dan uwana shin mai kuka tattauna da wannan saurayin kuma zaman me mukayi awannan wuri ba zamu cigaba da tafiyba don mu isa birnin dake gabanmu? sa'adda hatyan yaji wannan tambaya daga bakin 'yar uwarsa sadirat sai yayi ajiyar zuciya yace wannan saurayi da kike gani shine yarima nasmal babban dan sarkin dake mulkin babban birnin dake gabanmu farautace ta kawosu cikin wannan daji kuma dazu na yakeshi ne saboda rashin sani da zargin ko so yake ya cutar dake amma na gane cewa ba haka bane mahaifinsa aminin sarkin mafarauta ne hatimin da kikaga na bashi acikin jakata dazu na sarkin mafarauta ne ya banishi kuma ya bani labarinsu tun ina yaro karami haduwata dashi yanzu kaina ya daure amma sai naji amsar tambayoyin dazan yi masa yanzu sannan zan fita daga cikin duhun dana fada kodajin haka sai takaici ya kama sadirat ta ciza yatsa ba don komaiba sai don batajin yaren su yarima nasmal tabbas tasan cewa bakomai hatyan zai sanar da itaba bisa abindake faruwaba hatyan ya mike tsaye ya koma wajen nasmal ya dubeshi yace wacce masifa ce kuke tunanin zan kare muku ita? tambayoyi na sungi guda goma agareka amma duk wannan tambayar tafi sauran mahimmanci kodajin wannan batu sai dan sarkin yayi murmushi yace me kakeci na baka na zuba? kayi hakuri zan baka amsar wannan tambaya taka amma say bayan munje wani wuri anan gaba kadan kafin mu isa birnin mu na nuna muku wani abu ka sani cewa daga nan zuwa birnin mu tafiyace ta kwanaki uku kacal shiyasa na tura dakaru na sukai labarin zuwanku kafin mu isa domin a sami damar shirya muku bikin tarbarku cikin mamaki hatyan yace kawai saboda ni almajirin aminin mahaifinka ne sai a shirya bikin tarbarmu? nasmal yayi murmushi yace itama amsar wannan tambayar tana cikin ta farko ku tashi mu tafi mu fara wannan tafiya domin kwana uku ba tafiyar sa'a uku bace dajin haka sai hatyan ya dubi sadirat yace 'yar uwa zakiyi tafiya da kafafunki ko kuma na goyaki sadirat tayi murmushi wanda ya bayyana tsananin kyawunta tace ai yanzu nafi sha'awar nayi tattaki domin na rinka kallon ni'imar wannan daji da kyau kafin hatyan ya budi baki yace wani abu tuni yarima nasmal ya juya masa baya ya nausa cikin daji da sauri da ganin haka sai hatyan ya kama hannun sadirat sukabi bayan nasmal da sauri kamar yadda nasmal ya fada haka al'amarin y kasance wato tafiyar kwana uku kacal sukayi suka iso wani tsohon gari wanda gaba daya. TARKON MUTUWA Littafi Na Bakwai Part 7 E kafin hatyan ya budi baki yace wani abu tuni yarima nasmal ya juya masa baya ya nausa cikin daji da sauri da ganin haka sai hatyan ya kama hannun sadirat sukabi bayan nasmal da sauri kamar yadda nasmal ya fada haka al'amarin y kasance wato tafiyar kwana uku kacal sukayi suka iso wani tsohon gari wanda gaba daya gidajen cikinsa sun rushe duk wata bishiya dake cikin garin ta tunbuko daga cikin karkashin kasa ta bushe wasuma sun kone duwatsu kuwa sun farfashe babu komai a cikin garin kuma babu wani abu mai rai face tsirarun kwarangwalolin bil'adama ko ina acikin garin kai da gani kasan cewa fiye da shekaru dari baya rayuwa awannan wuri babban abinda daurewa hatyan da sadirat kai shine sunga wani wawakeken rami mai zurfin kamu saba'in ya ratsa tun farkon har zuwa karshen garin to shin mutum miliyan nawane sukayi aikin haka wannan rami? wane irin masifaffen yaki akayi a wannan gari her aka rushe gidajensa gaba daya her aka konashi? ta cikin wannan rami mai girman gaske aka shiga dasu hatyan koda suka iso karshen garin sai sukaga ramin ya nufi wani katon kogi wanda ya nausa her zuwa wata nahiyar daban suna zuwa daidai wannan wuri ne yarima nasmal ya ja tunga ya tsaya sannan ya dubi hatyan yace wannan rami da muka shigo ta cikinsa ba komai bane face sawun wata macijiya wacce babu wata macijiya mai girmanta aduniya ana kiranta da suna uwar macizai kodajin wannan batu sai hatyan da sadirat suka zazzaro idanu hatyan ya dubi nasmal yace anya kuwa baka samu tabin hankaliba? ya za'ayi asami macijiyar da zata haifar da wannan rami amatsayin sawunta kawai ya kamata idan zaka gillara karya ka yi wacce za'a yarda dakai domin ba mahaukata bane agabanka nasmal yace ba hauka bane lallai zaka gasgata zancena idan lokacin ganin zahiri yayi makiyinku wanda ya turo muku zakunan sihiri domin su hallakaku shine yanzu zai taso wannan macijiyar daga cikin karkashin teku ta biyoku har birninmu ta hallaka ku idan tazo baku kadaine zaku hallaka ba komai da kowa dake birnin mu indai mai raine saiya hallaka bama birnin mu ba kafin macijiyar ta iso birnin mu saita baje birane dubu ashirin da daya akan hanyar ta ya kasance anyi asarar rayuka sama da miliyan dubu dari bakwai, yakai abokina binkice ya nuna cewa kaine kadai zaka iya tserar da wadannan dubunnan miliyoyin rayuka amma kaima din saika haye wadansu jarrabobi da zamuyi maka acan birnin mu koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke hatyan baisan sa'adda maganar zuci ta fito filiba yace tayaya ni kadai zan iya kare miluyoyin

Chapter 8 of 11